Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Aliyu yawani zama police ba yaron dayay lafiyayyen karatu yakuma gama da good result, kwanciya ahankali tayi tana kwalama Yar aikinta kira dan tazo ta danne mata kafa.


Bangaren Gwaggo shima yanada girma sosai, da sallaman nan nashi chan kasan makoshi yadaga labule ya shiga dakin ko kadan Gwaggo dake zaune tana kada lagwani bataji alamun shigowan mutum ba kawai karan kwas kwas na takalmin dake kafanshi taji akan tile din dakinta afirgice takalleshi tana “Innailaihi wa innailaihi raji’un, waikai Aliyu wani irin murdadden yaro ne eh, bama wanan ba dan ubanka koma ka cire shegen takalmin nan naka dazaka shigomin dashi falo ina salla a ko’ina afalona dan tsarki ne dashi wlh” ko kallonta baiyiba saima hawa kan dogon kujeran ta dayayi yay kwanciya abinshi yanadan lumshe idanu, ijiye komi Gwaggo tayi tamike tana gyara zani tazo kanshi zatahau mai bala’in idanunshi daya lumshe tabi da kallo ganin sundanyi ja yasa tace “kai yaron nan zazzabi kake yine”? Dan bude idanunshi kadan yayi yakalleta dauke kanshi yayi yaki kulata, dasauri ta kalli agogo ganin ko shabiyu batayiba yaron da dazun nan dasafe yafita aiki yasa tace “wlh bakada lafiya Hydar zo meke damunka”? takai hannunta da duk audugan lagwani yake kai zata tabamai fuska dasauri yatashi zaune yace “karki tabani da hannun dattin nan Gwaggo” dan sassauta murya tayi kaman ba ita kemai ihu ba cikeda damuwa tace “meke damunka eh Hydar? Duk wanda yasanka yana ganin Wanan idanun naka yasan bakada lafiya, meke maka ciwo” tashi daga kan kujeran yayi yace “tunda bazaki barni nai bacci ba bari na barmiki dakinki” yay maganan yay hanyar fita tana kwalamai kira kaman badashi takeba, cikeda damuwa tace “ai idan bakaji nawa ba zakaji na ubanka, yaro sai bakin zurfin ciki da shegen share mutane sabida yaga nadamu dashi” duk yanajin ta tana surutunta bai amsata ba flat dinshi yawuce bude kofa yayi yashiga cikin dakin da babu abinda yakeyi sai kamshi ko’ina a gyare kaman babu wanda ke zama adakin, bedroom nashi yawuce yana shiga adaddafe yacire rigan yan sandan ya Yar anan kasan dakin sanan yazauna takalmin kafanshi yacire yazaro wayanshi yadaura saman side drawer sanan ahankali ya kwanta yanadan yatsine fuska bala’in ciwon kai yakeyi daya rasa na menene amman sai uban dauriya, har bacci yasoma daukanshi yaji wayanshi na ringing da kyar yadaga hannunshi yakai wajen wayan dauka yayi batare dayama kalli screen dinba yakai wayan kunne ahankali yace “Hello” daga tachan bangaren muryan wani magidanci ne yace “Aliyu meke damunka?” Dan yatsine fuska yayi yanaji kaman ya rufe Gwaggo da duka akan me zata fadiwa Abba dan gyara muryanshi yayi yace “Abba I am fine” cikin rashin gamsuwa Abba yace “Aliyuuu” dagashi sai Abba sukasan meaning din anytime yakirashi da Aliyuuu hakan yasa gently ya fuzar da dan iska ahankali yace “Abba kaina hurts so bad” anatse Abba yace “is that all”? Ahankali yace “yes Abba” “okay I am coming yanzun nan nadubaka” dasauri yace “no Abba I am fine kazauna please zansha magani” dan jim Abba yayi yace “Aliyu haryau banga wanda yakaika tsanan magani ba” sanin tsaf Abba zaibar hospital yazo yasa yace “Allah Abba zansha I promise” cikeda gamsuwa dan yasan Aliyu baya promise yaki cikawa yace “okay kasha I will call Ogan ka zance mai yabaka the rest of today da gobe kahuta, this work is draining you Aliyu banason shi, anyway that will be another day talk, kasha maganin ka kwanta” ahankali yace “to Abba” Allah kara sauki kaji gyadama Abba kai yayi tareda katse wayan, hannunshi yasa yajawo drawer gefen gadon shi sanan yadauki paracetamol ya ballo guda biyu yana kallon maganin a hannunshi kaman yay amai, yadade yana kallon maganin sanan yasa hannu yadauki goran ruwan dake kan side drawer yabude kurba yayi sanan yajefa maganin da kyar ta hadiye sanan yasa goran abaki saida yasha kusan duka ruwan sanan yaji maganin yatafi ahankali ya ijiye goran kafin yakoma ya kwanta ya lumshe idanunshi bai wani dade ahakaba bacci ya kwasChe shi.
[6/16, 7:56 PM] +234 701 275 3212: 1️⃣8️⃣


Free page
Wuraren 3 na rana yafarka, ahankali yake bude idanunshi yanabin dakin da kallo jin anrike hannunshi yasa yajuyo da kanshi ahankali wata yar budurwa ce da zatakai 22yrs zaune gefen gadon dake bala’in kama dashi kana ganinta kasan kanwanshi ce takama hannunshi gam tarike tanadan gyangyadi, tana sanye da doguwan rigan atampa, Meena kenan he’s sure Gwaggo ce tagayamata baida lafiya saisa tataho daga dawowanta daga school, dan murmushi yayi sanan ya fizge hannunshi da karfi afirgice tabude idanunta takalleshi tana kara ware idanu tace “Ya Hydar katashi sannu yajiki” hararanta yayi yace “meya kawoki dakina” cikeda damuwa tace “yanzun nan muka dawo daga school muka tarar Gwaggo na kuka wai batada lafiya shine nazo naga kana bacci, cha tayima na sata a keke nakawota wurinka nasan damunka kawai zatayi saisa naki” dan jim yayi yace “jeki cemata tadena kuka I am fine” murmushi tayi sosai tana kallonshi tana kokarin tashi dagakan gadon tace “Ya Hydar kanason Gwaggo amman kullum fada kukeyi baka nuna mata kana sonta maisa” hanyar bathroom dinshi yawuce yace “kafin nafito kibarmin daki inba hakaba jikinki zai gayamiki” tashi tayi ranta namata dadi ganinshi lafiyanshi kalau tace “Ya Hydar zaka kaimu Jabi lake mall din? Kagama sai Gwaggo takara yarda lafiyanka kalau ko” “go and get ready” yafadi murya chan kasa duk ya gaji yakosa tabar dakin dansai sashi surutu take, shigewa bathroom din yayi abinshi yamaida kofan yarufe, tashi tayi cikedajin dadi tai hanyar fita, sai yanzu tama lurada riganshi akasa dakin tsugunnawa tayi tadauka sanan tamakalamai a hanger tabude wardrobe dinshi tasaka tawuce tafice danta gayamusu su shirya.



Yadade abayin sanan yafito wani simple jallabiya yasaka yay salla sanan yatashi ahankali har yanzu kanshi namai ciwo sosai daurewa kawai yake, shiryawa yayi cikin wani milk yadi mai bala’in taushi danshi baya iyasaka kaya masu karfi, feffesa turare yayi sanan yadauki wayanshi yana dubawa ganin baida miss calls yasa yafito yana tafiya one one, tundaga gaban kofan dakin Gwaggo Meena ke kallonshi ganin yay wani kalan kyau tana murmushi ohh God duk duniyan nan batada wanda takeso kaman Yayanta Hydar, hararanta yayi alamun kallon fa wuce kigayamusu su shirya hakan yasa tawuce tashiga dakin Gwaggo tana kallon Gwaggo dataci gayu itama tana zaune kan tabarman data shimfida akan lafiyayyen carpet din dake falon, girgizakai kawai yayi baitaba ganin rigimammiyan tsohuwa irin Gwaggo ba, gatada carpet amman tsabagen kauyanci saita shimfida tabarma akai, idanko yawone ko jikokin nata wani zubin da gangan sukekin gayamata zasu fita dan tsohuwarnan Allah ya zubamata son zuwa yawo kaman taci kafan kare.
Wasu yammata guda biyu ne zaune agefenta suma kyawawa dasu Amal dakuma Khadija duk sunci gayu kansu daya, zama yayi abinshi Gwaggo tabishi dakallo bata kulashi ba shima bai kalleta ba yakalli su Amal dake kallonshi suna gaidashi yace “kawomin abinci” tashi Amal tayi dasauri zata fita yace “ina zaki”? Ahankali tace “falon Mami zani nadebo maka” girgiza mata kai yayi yakalli fuskan Gwaggo yace “bani na Gwaggo” daure fuska Gwaggo tayi takalli Amal tace “jeki uwardaka na abincinshi na cikin kula sabida ku na boye kafin ku cinye mai yara saikace mayu barinma wanchan mai idanun kutaren” tanuna Meena tabe baki Meena tayi daga ita har Khadija, Amal tawuce tadauko mai takawo, kafinma Gwaggo tai magana Khadija ta tashi tadauko mai ruwa da drink daga fridge na Gwaggo ta kawomai bude abincin yayi dambu ne lafiyayye yanasan dambu hakan yasa yaci ba laifi Gwaggo tana zaune tana kallonshi ganin yadanji sauki yasa hankalinta ya kwanta sosai saida yagama ci sanan suka kwashe kayan sukai kitchen dashi shikuma yafice suka biyoshi abaya suka fito Gwaggo natafiya ahankali dan kafafun sun dawo a lallaba bata iya tafiya sosai saisa ko’ina za’aje da ita da keken guragun ta tareda ita.


Mami suka gani a tsakar gida kan wani hadadden chair da table agabanta tadaura kafanta kan table din Yar aikinta na gyaramata nails na kafa tana danna wayanta tana tauna cingum tana murmushi, jin sahun tafiya yasa tadago kanta binsu tayida kallo tace “Hydar daga kannenka sai Kakar ku kakeso nibaka sona saisa ba’a taba fita dani ba” tai maganan tana kallon Aliyu dayamayi gaba abinshi kaman badashi akeba, kaman jira Gwaggo take taballamata harara tace “akanme zai soki ke kika haifeshi jimini ikon Allah” dan dariya Mami tayi tai kara da cingum dinta tace “Hajiya Gwaggo maida wukan a dawo lpy” “Mami mun tafi” yaran suka mata sallama, “saikun dawo” Mami ta amsa yaranta tana murmushi tabisu da kallo tana hararan bayan Gwaggo, saida sukai nisa sanan ahankali tace “Allah yakasheki mayyar tsohuwa kawai na huta, mata takai kusan shekaru dari amman taki mutuwa” tana zaune tana kallonsu yaja mota suka wuce sukabar gidan.



On a normal speed yake tuki yau danji yayi kanshi yasoma ciwo sosai amman yadaure dan baiso Gwaggo tagane ballema tadamu, ahaka harsukakai jabi lake mall din wuraren 5:30. Parking yayi wurin parking sanan suka fiffito, ganin yazauna aciki yasa Gwaggo tace “muje mana” yatsine fuska yayi yafito yabude boot yaciro kekenta yana sata akai yace “zan jiraku anan akwai wayoyin office dazanyi” yay maganan yana bama Meena ATM card dinshi yace “idan kuka kararmin dakudi Abba zansa yabiyani da monthly allowance dinku” dariya sukayi sanan Meena ta tura Gwaggo suka wuce tace “bye Ya Hydar” shiga mota yayi yazauna tareda kwantar da kujeran yana kara karfin Ac sanan ya kwanta kanshi najuyawa ya tsani rashin lafiya saisa baimaso ya kwanta ma wanan, ajiyan zuciya ya sauke ahankali yanaji zuciyanshi natashi cikinshi najuyawa kaman zaiyi amai, jin amai yazomai dawani irin sauri ya yunkuro yabude kofa yafito sai amai, kwaro amai yashigayi anan wajen motanshi sosai idanunshi sukai ja…..


Ahankali ita kadai take tafiya a parking lot din wayanta na kunnenta tana sauraron kwatancen da Glory kemata na inda venue su yake acikin wajen, bakaramin kyau tayiba tana sanye dawani english gown daya kaimata har kasa red yabi jikinta sosai ya bala’in fito da shape nata dudda bawani kamata yayi ba amman sabida kalan yadin yasa yanayin jikinta yafito, fuskanta yay wani kalan kyau yana glowing dudda bata shafa hoda ba dan ita hoda nasata kuraje a fuska saisa tama daina sawa but ta gyara eyebrows dinta sanan tasa kwalli dayawani irin haska fararen idanunta suka fito wallll, sai pink lipstick data kara kan pink lips dinta dayasa lips dinta yay wani kalan crazy baby pink daya kara fito da fuskanta sosai, ta gyara gashinta daya gama hargitsewa tai styling frontal hair din da gel dudda dama gashinta a kwance yake but karawa da gel datayi yasa tai kyau fuskanta yafito sosai takawo wasu simple pearls earring silver tasaka, tayana light peach karamin veil akanta dayadan zame kadan kasa sabida iskan da akeyi uwa za’ai ruwan sama gashi bahadari just that garin is looking damn cozy, tasaka heel dayama kafanta kyau silver dayafito da fine fine sexy toe nails dinta, tana tafiya ahankali tarataya wani karamin handbag na LV a shoulder ta sai goran bottle water na Eva data rike tasha kadan aciki dan she was thirty ahanya ma tasaya yanzun nan dazasuso.

Kaman daga sama taji kakarin amai na mutum chak ta tsaya at the same time taji kirjinta yawani buga dum! Tsayawa tayi chak sanan ahankali tace “ok I am coming now nagane wurin” katse wayan tayi sanan tajuyo tana kalle kallen inda take ganin bataga kowaba sai shiru dataji yasa tacigaba da tafiya abinta, karajin kakarin amai datayi yasa tasake tsayawa chak ita kanta she don’t even know why take tsayawa amman kaman something is pulling her, komawa baya tashigayi ahankali tana waige waige kafin chan tahango wani Babban mutum dan that doesn’t look like a small boy tsugunne in between wasu manyan jeeps guda biyu yabata baya yana amai, tsigan jikinta taji yawani tashi, tun tana Yar karaman Yarinya ta tsani taga mutum naciwo, part of the reason why kowa is her friend a school kenan inhar Khairy tasan u are sick to far she die there Khairy is damn caring idan mutum naciwo saitamafi mai ciwon damuwa.


Takai almost 20second tsaye tana kallonshi yanda yake amai tsigan jikintai natashi tun yana amai abu na fitowa har kawai amman yake babu abinda kefitowa, ahankali tadaga kafanta zata wuce ta tafi samin kanta tayi dasake juyowa takalli bayanshi sanan takalli bottle water hannunshi kafin ahankali tana tafiya gently tawuce lungun motoci adaidai bayanshi dab dashi ta tsaya tana kallonshi bakinta nadan rawa dan tsoroma takeji mutum na amai tazo meruwanta amman still tadaure ahankali tace “Sir do you want some help nakira maka security”? Batare daya kalleta ba koyajuyo ba ya girgiza mata kai alamun no, jitayi zuciyanta yamata wani nauyi kaman tai kuka tasake dukowa kanshi sosai anatse tace “but u are very very sick, do you want some water, I have water, here gashi” tai maganan da sauri tana budemai goran ruwan tana mikamai ta gaban fuskanshi, goran ruwan yabida kallo, murya chan ciki dabaya fitowa sosai yace “thanks” goran tabida kallo ganin bai karba ba yasa ahankali tace “ka karba ka wanke fuskan ka u will feel better, haka Mama kemin idan banda lafiya nai amai” jiyayi kanshi nawani irin ciwo, azuciye yawani juyo da jajayen idanunshi dake cikeda zazzabi yawani taso kaman zaki zai cinyeta baya tayi atsorace ruwan hannunta yafadi heel din kafanta ya turgude dawani dutse hakan yasa kafanta ya turgude tai baya zata fadi atsorace hannu daya yasa ya chapko hannunta dasauri yana kallon fuskanta da jajayen idanunshi kaman yanda itama a bala’in firgice take kallon fuskanshi kirjinta nabugawa fast fast lips dintaI narawa sosai ganin police man dinaCn ne.
[6/16, 7:56 PM] +234 701 275 3212: 1️⃣9️⃣



Cikinsu duka babu wanda ya iya wani motsi yana rikeda hannunta yana kallon fuskanta kaman yanda take kallon nashi, ganin iska nawani irin kadawa sosai gyalen ta gabaki daya yay baya iska na neman fizgeshi yay sama dashi yasa yay wani irin pulling dinta ta taso saura kiris tafada kirjinshi da kyar ta iya maintaining posture dinta gabanta nafaduwa sosai tasauke idanunta kasa, tundaga yatsunta datake wasa dasu tana yakushin riganta dasu yake kallo har zuwa fuskanta da lips dinta dake rawa sosai zuwa gashinta dakeda bala’in kyau datai parking tai donut da jelan gashin dayay yawa kana gani kasan tanada suma sosai gyalen na wuyanta, ganin yanda ake iska sosai ta sandare awurin not her self yasa murya chan ciki yace “cover ur hair” gyadamai kai tayi ahankali batare data kalleshi ba takai hannunta takamo gyalen daga wuyanta zata yana akanta kwace gyalen iska yayi da karfi saikan fuskan Hydar dasauri tadago kanta, ahankali ya lumshe idanunshi jin wani sassanyar kamshin da gyalenta ke fitarwa da atake yaji ya kwantarmai da tashi da zuciyanshi keyi duk wani amai dayakeji yakoma, gently yakai hannunshi yadaura akan fuskan nashi yadauki gyalen sanan ahankali yamika mata, kallon fuskanshi tayi kafin ahankali takalli hannunshi dake dauke da gyalenta dayake mikamata sanan tasa hannunta ahankali ta karba daidai wani kalan mugun ruwa sama ya sauko da karfinshi dayama firgitata dasauri takalli sama sanan takalleshi kafin tajuya da sauri zata wuce. “Ummulkhair!” Taji yakirata amugun natse dayasa taji gabanta yawani kalan fadi, tsayawa tayi chak ruwan nadukanta sanan gently tajuyo takalleshi gani tayi yabude mata bayan jeep dinsu shima yana tsaye ruwan na dukanshi, batasan mesa ba but kasa mai musu tayi ahankali ta tako tazo har gabanshi sanan tashiga ciki ta zauna, bayan shima taga yashigo dasauri ta matsa chan gefe yamaida kofan motan yarufe, daganan inda yake yadan mika hannu ya kunna motan sanan ya kunna AC motan yadauki wani bottle water yadawo yazauna yadan bude kofan motan kadan ya kuskure bakinshi kafin ahankali yamaido kofan yarufe sanan ya ijiye goran ruwan akasa ya kwantar da kanshi yana sauke ijiyan zuciya ahankali dukansu suna sauraron yanda ake ruwa da mugun karfi harda kankara ma.


Sunkai almost good 6min a motan babu wanda yacema wani wani abu kanta nakasa tana fidgeting yatsunta, shikuma yana zaune gefenta kanshi naciwo amman kallonta yake kaman an ijiyemai TV, ganin yanda ta takure tanajin sanyi sosai sabida ruwan dayadan daketa kadan sanan ga sanyin AC motan daya kunna yasa ahankali yadan yunkuro hannunshi yamika ya kashe AC sanan yadauki jacket dinshi na kayan yan sanda that is always acikin motan sanan ahankali yawarware shi matsowa yayi kusada ita yana kallon fuskanta bala’in firgitata tayi jin mutum kusada ita sosai dayasa takalleshi dasauri kallonta shima yake ko kyafta idanu bayayi ahankali yadaura mata jacket din kan kafadanta yarufamata shi da kyau yana kallonta kaman yanda take kallonshi tana nishi da sauri da sauri dayakejin hucinshi akan fuskanshi sanan yadan matsa baya zai koma wurin dayake da zama kaman daga sama ahankali murya chan kasa fa inda ace akwai mutum na uku amotan nan bazai tabajin metace ba tace “u are sick” kallon kwayan idanunta yayi kaman baigane metace ba, gyadamai kai tayi idanunta sun cika da kwalla sosai ahankali tace “wlh bakada lafiya, ur body is hot, let’s go to the hospital please” tana karasa maganan hawaye ya gangaro mata daga idanu sharrrr, hawayen yabi da kallo kaman wanda baitaba ganin mace tai kuka ba, murya chan kasa batare daya koma ba he’s still very much close to her ahankali yace “you don’t want me to be sick” gyadamai kai tayi ahankali wasu sababbin hawayen nakara taruwa a idanunta, murya chan chan ciki yana kallon kwayan idanun nata dasukenan farare fat kaman farin gajimare yace “why”? Girgizamai kai tayi saikuma ahankali tace “I don’t know, seeing u sick is making my heart to hurt” dan lunshe idanu kadan yayi sanan yabude su yadaura akan nata, lips dinshi sukai motsi kaman whistling yana kallon yanda take kuka mara sauti yace “stop crying” gyadamai kai tayi ahankali tana kokarin tsayar da hawayen, hannunshi yasa yaciro handky daga aljihunshi yamikama mata yace “here” karba tayi takai kan fuskanta tana goge hawayen saida yaga tagoge tass sanan yakoma gefenta yazauna da kyau yace “mekikazo yi anan?” ahankali tace “today is Glory’s birthday my friend she’s celebrating it anan” dan juyowa yayi yakalleta kaman mai nazarin wani abu yace “how old are you” kallonshi itama tayi kafin tasauke kanta ahankali tace “20” kaman daga sama taji yace “small Gurl” dawani irin sauri takalleshi tabe baki taga yayi batasan mesa ba abin saiya bala’in bata dariya she don’t even know why, dan murmushi kadan tayi sanan tahadiye shi kallonta yayi ganin yanda dimples dinta keta lotsewa alamun murmushi take amman tana hadiyeshi, kaman daga sama taji yasake jefo mata tambayata anatse. “Are you in any relationship”? Dasauri takalleshi, kallonta shima yayi fuskanshi looking he’s serious da tambayan, murya chan kasa yace “kinada any man dakikeso…..or yake sonki”? Yay maganan muryanshi na breaking cus shi kanshi baisan mesa yakema tambayanta this kind of wired question ba, dauke kanta tayi, sanan ahankali ta girgiza mai kai alamun no, dan murmushi kadan yayi yanajin duk wani ciwon kan dayakeji yana tafiya, jakanta dake in between them yasa hannu yadauka yabude wayanta yaciro Dasauri takalleshi numbershi yasaka sanan yakira kanshi, danne danne taga yanayi awayanta kafin yamaida ya ijiye cikin jakan, ganin ruwa na tsagaitawa yasa tadan kalleshi ahankali tace “zantafi” yana kallonta right in the eye yace “where is ur driver? U should head home” gyadamai kai tayi sanan ahankali tace “yanata chan bangaren” inda take nunamai da hannu yakalla, ahankali yace “ok” bude kofa yayi yafita cikin yayyafin da akeyi yakoma gaba kunna motan yayi yaja motan har gaban motansu yakaita sanan yay parking jacket dinshi tacire ta linkemai ta ijiye ahankali tace “thank you” sanan tabude kofan zata fita kaman daga sama taji yakirata. “Ummulkhair!” Faduwa gabanta yayi batasan mesaba duk idan yakirata sai gabanta yafadi, juyoda kanta tayi takalleshi shima ita yake kallo, ahankali yace “I am a very very jealous Man! Be mine only Khairy! I am in luv with you! Good night!” Dawani irin sauri har hannunta narawa tamaida kofar tarufe sanan tajuya tabude bayan motarsu ta shige kafin yaja motar nashi yawuce.
[6/16, 7:56 PM] +234 701 275 3212: 2️⃣0️⃣
Free page


Wucewa yayi daidai lokacin wayanshi na ringing ganin Meena ce ke kiranshi yasa yamaida kanshi kan tukin inda yasan zai gansu chan yawuce, atsaye ya gansu da alamu shi suke jira, kashe motan yayi yafito yana kallon Gwaggo dake binshi da kallo ganin ya wartsake sosai yace “lpy” hararanshi tayi tace “munafuki nidai sani a mota” sata yayi a mota yana murmushi kasa kasa sanan yamaida kujeran boot su Meena suka saka ledojin abubuwan dasuka siya a boot sanan yarufe kowa yakoma yashiga motan yaja motan zuwa gida yana parking yafito baima tsaya bi takansu ba masallaci yawuce dan yasan zasu tafi da Gwaggo ciki.

Tareda Abba suka shigo gidan daga masallaci magidancin mutum ne yana sanye da suit baki dan daga wajen aiki yake, falo suka wuce, duk su Mami da yaran na falo gaida Abba duk sukayi, ganinshi yasa Mami tace “akawo abincin yanzu Alhaji” girgiza matakai yayi yay hanyar stairs yace “I am coming tukunna muje Aliyu” binshi Hydar yayi har zuwa sama wani babban falo suka shiga wanda kana gani kasan na Baban shine, zama yayi akan kujera Abba yazauna kusada shi yakai hannunshi yabude idanunshi yana haskawa dawani dan tocula dankarami yana dubashi, dan jim yayi sanan yace “you have typhoid Aliyu, I think zan saka on injections tunda bakason magani” yatsine fuska yayi ahankali yace “Abba wlh naji sauki, kainafa kadai ke ciwo kuma yadena” “yimin shiru my friend” Abba yay maganan yana tashi wani babban first aid box yadauko yabude sanan yahada wani allura Aliyu naji yana gani Abba yamai allura, sanan Abba yace “Aliyu this work is draining you, akan me u are a Barrister kawani kama kashiga aikin police with just mukamin ASP eh, why will you choose a police man job Son common talk to me” yay maganan yana kallon Aliyun cikeda damuwa, Aliyu ne kadai danshi namiji, yaranshi duka takwas aduniya, Aliyu ne nafarko he’s 32yrs sai kannenshi mata guda bakwai hudu sunyi aure dukansu baa Nigeria suke aure ba Saura 3 agida suna school, ganin yay shiru yakasa cewa komi yasa ahankali Abba yace “tashi katafi, but make sure kaci abinci kafin ka kwanta kaji” gyadamai kai yayi sanan yatashi yawuce yabude kofa shikuma Abba yashiga cire kaya dan yay wanka duk bayajin dadi.


Yana fitowa da Mami yaci karo anan falon sama tana zagaye, kallo daya yamata yadauke kai yashiga sauka kasa itakuma tawuce tashiga falon Abban da sauri tanabin ko’ina da kallo dan Abba yariga yashiga bayi, ganin allura da first aid box abude yasa tasauke ijiyan zuciya taje gaban wardrobe tana budewa dan samoma Abba kayan dazai sa….
**

Tana komawa gida kayan jikinta tacire tayo wanka sanan tai salla tasauko kasa gabaki dayansu duk suna zaune a falo suna dinner gaida kowa tayi sanan tazo kusada Mama tazauna tana kallon Mama dataga tasaka sweater turtleneck black daya rufe har wuyanta tasaka hulan sanyi shima baki kafanta da bakin safa, kallonta Mama tayi jin ajikinta ana kallonta hannu tasa taja hancin tace “ke abinci zakici ko kallona kikazo yi” dan dariya kadan tayi tace “Mama sanyi kikeji ne AC akashe” gyadamata kai Mama tayi batare data bata amsan tambayan ba tace “mezan zubamiki” kallon abincin tayi sanan takalli madaran da Baba kesha tace “Mama madara zansha banson naci abinci” Madaran da Baba Kesha a cup da zafinshi ma yamika mata da sauri ta karba tana murmushi tace “thank you Baba” hararanta Mama tayi tace “kwadayi Khairy, aikin ki kenan tun kina Yar kankanuwan ki sabida babban ki kullum yanashan dafaffen milk kema kikesha” mikewa tsaye Baba yayi yace “bagashi nan saisa she’s so bright ba ga kwanya, milk is good for children barin ma Wanan na Shanu damuke sha dababu mix, bari naje nai salla” yakalli su Manaf da duk suka tashi suma sukawuce suka tafi masallaci, madaran ta shanye tass sanan ta tashi ta tattara kayayyakin dasukaci abinci takai kitchen sanan tadawo tana kallon Mama dahar lokacin take zaune inda tabarta tace “Mama tashi mutafi sama” ahankali Mama tace “wuce kitafi akwai wani program na wa’azi dazan kalla yanzu za’a fara” sanin Mama da kallon tashoshin wa’azi yasa tawuce stairs abinta tace

Please Login or Register in order to submit comment