Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

shima Zayn yakalleta uppan Baffa baice mata ba hakama Baba duk kallonta suke da Mom da Anty Mariya dasauran yaran.

Hannun kujera Ammi tadaka cikeda bala’in dakin na amsa masifanta jikinta na girgiza tacigaba da magana. “Idan zuri’a kukeso kuhada abotanku yadawo tajini inace nan nan nan ga Batool nan diyar kace maisa baka hadata da Manaf ko Mu’az ba koma Maheer sai akan d’ana Zayn dina, kasan plan din danake dashi , buri danaci akan yaron nan nawa dazaka hadashi da yar gwal dinku? Kasan wace yarinya nakeso Zayn ya aura kasan matsayin Baban ta anan Nigeria kuwa kaga kyan Aisha? Wlh bazaka maidani karaman mutum a idanun kawata ba” takalli Zayn cikeda ihu tace “Zayn kalli fuskan mahaifinka kacemai bakason auren nan yanda sukayi suka hada auren subi haka su warware” shiru Zayn yayi kanshi nakasa shi bazai iyama cewa farin ciki yake ba ko bakin ciki all he knows is yaji dadin wanan labarin dayajita bagatatan haka kaman daga sama.

Wanan Littafin na kudi ne karki karanta batare dakin biyaba kika karanta min littafi ban yafeba.

wa.me/+2347012181461
To chat me up on watsapp

This novel is 1k
Pay 1k into 3107021073 aisha Muhammad saiki turomin evidence of payment ta watsapp number na 07012181461
Thank u❤️


Baki Ammi tabude zata kara magana Baffa yadaga mata hannu cikin fushi, anatse yace “kinsan maisa duka wanan ihun dakike yi danki tozartani bazai taba bani kunya ba”? Dan murmushi yayi yace “sabida agaban dan uwana da yarana kike ko zaginane zaki iyayi” Baffa yasake murmushi yace “auren nan ba marigayiya kadai tai tunanin shi ba har mu nan, duk duniyan nan babu wanda zai rike Khairy amana kaman dan uwanta kuma Yayanta Zayn! Bata fita daga family ba zamu riketa amana dan dan uwanta take aure, banda kwanciyan hankali daya wuce nasan d’ana ke auren Khairy da mahaifiyarta tabani amana, nasanki karki manta na zauna dake tsawon shekaru danmu na farko shekarun shi 36 so babu wanda zai iya bada labarin halinki kaman ni, nariga nasan bakison mahaifiyar Khairy hakan zaisa bazaki tabaso auren shi da yarta ba abu nafarko dayasa naji bazan taba fadamiki ba kenan sai ranan da zan hada yaran nan nafada musu kisani kema, dan haka kome zakiyi kiyi Zayn mijin Ummulkhair ne nan da wata daya za’ayi walima ta tare agidanshi, kutashi kutafi” cikin yaran babu wanda ya iya cewa uppan duk mikewa tsaye sukayi banda Khairy data kasa mikewa tsaye tana kallon Baba idanunta sunyi jazur Baba shima yana kallonta, hannunta Batool takamo zata dagata tace “tashi muje Khairy” ahankali Baba yace “barta Batool” tashi yayi ahankali sanan yadauki wata yar jakan dake kusada shi yabude wani littafi yaciro tana kallon littafin ta tunashi Dairy Mama ne, karasowa gabanta Baba yayi ahankali sanan ya tsugunna agabanta yana kallonta, ahankali cikeda so dakuma tsantsar kaunar yarshi yace “Khairy kingan mu nan we are not bad parents idanma abinda kike tunani kenan, all abinda kikeji azuciyanki yanzu nasani, kina tunani tayaya aka miki aure tun kina karama baa taba sanar dake ba, auren ma da Yayan ki Zayn, wanda baki taba kallo da fuskan so ba, wanda bakisan koshi yana sonki ba” dan murmushi yayi yace “kituna babu aure mai albarka kaman wanda iyayenka suka zaba sanan suka maka banda haka kiyi tunanin auren nan mahaifiyarki dakikafi komi so aduniyan nan tahada ita tama miki shi Ummulkhair, and lastly mahaifiyarki tace nabaki Wanan abin ki karanta idan rana irin tayau tazo gashi” Baba yasamata book din a hannu, wani irin kankame book din tayi gam gam sanan Batool tadagata bin Batool kawai take suka wuce mota suka shiga suka zauna itama ahankali Anty Mariya tashigo taxauna tana kallona Khairy da idanunta suka bushe babu hawaye ko digi bazama ka iya tantance metake going through ba, chan saiga Baba yafito tareda Baffa motansu yazo yashiga yaja suka tafi sanan Baffa yawuce yakoma ciki biyoshi Ammi tayi tafara surfafa bala’i amman tak bai cemata ba


[6/26, 12:39 PM] +234 701 275 3212: 4️⃣8️⃣




Koda sukakai gida kasama fitowa daga motan Khairy tayi duk Baba na kallonta da taimakon Anty Mariya da Batool suka fito da ita sanan suka shiga ciki Anty Mariya tace “tafi da ita dakinku Batool” wucewa da ita sama Batool tayi sanan tajuyo takalli Baba zatai magana Baba yadaga mata hannu anatse yace “Zayn shine best husband da Ummulkhairy will ever wish for, please karkimin wata magana aikin gama yariga yagama beside auren nan mahaifiyanta tamata shi” shiru Anty Mariya tayi tana kallon Baba saikuma ahankali tace “ok” sanan tajuya tawuce sama abinta.

Suna shiga daki Batool tazaunar da ita abakin gado sanan tamaida kofansu tarufe tasa key sanan tazo gaban gadon da gudu tazauna akasa kanta tadaura kan kafan Khairy tace “Khairy why are you not crying Innalillahi wa innailaihi raji’un, yanzu Khairy kefa matan aure ce, matan Ya Zayn, Khairy what about Aliyu? Ya Aliyu yaya zakiyi dashi? Khairy I am so sad for you not because Ya Zayn is a bad person but because of soyayyan da kukeyi da yanda kike sonshi da yanda Ya Aliyu yake sonki, Khairy how are you going to tell him eh? How”? Sai alokacin wasu kalan hot hawaye suka zubomata, jikinta harwani tsuma yake tana kuka mara sauti itama Batool kasa hanata kukan tayi saima rungumeta datayi suna kuka sosai, sun dade ahaka ganin asma ta na neman tashi yasada sauri tasaki Khairy tawuce tadauko mata inhaler ta dake kan drawer takawo mata tace “shaka and stop crying” ahankali ta shaka but takasa daina kukan, wani kalan bakin ciki da damuwa ne taji ya lullube mata zuciya littafin Mama ma sai kallonshi take takasa karantawa, da kyar da daddare ta iya shan tea tana zaune kallon wayanta kawai take idanunta sunyi jazur sun kumbura, wuraren 10 Batool tai bacci ta barta, tana zaune awajen tana kallon wayan shadaya nayi wayanta yahau ringing wani irin lumshe idanu tayi batare data kalli screen dinba hawaye taji sun zubomata sharrrr ajiki, tunda tasan Ya Aliyu kullum doki take yakirata yaune rana na farko dataji tana tsoron tadauki wayanshi ma dan gani take dazaran yaji muryanta zan gane and tayaya zata iya fadamai Wanan bakin labarin da tasan halinshi yanda yakeda mugun kishi idan wani abu yasameshi this night fa, kozata fadamai labarin nan she needs to think it through sanan tasami hanyan dazata iya fadamai batare datai breaking heart nashi ba dan batason wani abu yasameshi.
Wani kiran nashine yashigo ahankali tadauki wayan, maida wayan silent tayi gabaki daya sanan tasauka daga kan gadon ahankali tadauki littafin Mama, gaban wardrope taje tazauna ahankali akasa tana rikeda book din tana kallo tsoron ma karantawa take hawaye ta share dasauri sanan tabude book din ahankali tafara ni tana karantawa.

Tunda aka haifeta Mama tafara rubuta mata book dinan, taushe bakinta tayi jin wani mugun kukan dayake zuwan mata, sanan tacigaba da karanta littafin page after page, Mama na bata labarin komi wahalan datasha rayuwa kafin tahadu da mahaifinta, da ranan da ciwonta zai tashi da ranan da ciwonta zai lapa haka takebin littafin nan word by word tana taushe bakinta hartakai pages na karshen dataga yanayin rubutun mama ma ya chanza.
“Ummulkhair bansan maisa ba but anytime nake rike da littafin nan dakuma alkalamin nan babu abinda bana iya fayyace miki, yanzun nan kika fita kika tafi makaranta, lokacina yakusa ni kaina inaji ajikina saisa nace bari namiki Wanan one final rubutun. Ummulkhairy inaso kisani cewa duk cikin yaran dana haifo duniya babu wanda nakeso kaman ke! Nasan ance babu kyau uwa tafadima yaranta tafison Wanan kan Wanan nafadamiki hakane sabida inaso ki natsu aduk lokacin da Littafin nan zai sameki. Khairy ni mahaifiyanki nine na zabamiki miji Zayn sanan umarnina ne agareki kiyi zaman aure dashi!” Wani irin sakin book din Khairy tai akasa kawai tashi tayi dagudu tafada bayi ta kunna ma kanta shower tana wani irin kuka tamai sosa zuciya ahankali tace “Mama whyyyyyyyy? Mama Ummulkhairy ki Ya Aliyu takeso, Mama whyyy” wani irin kukan datayi batajin koda Mama tarasu tayi irin kukan nan ba, takai kusan awa daya abayin karkashin ruwa kuka take sanan da kyar ta lallashi kanta tafito bayan ta tube kayan tadauki towel tadaura akirji tabude kofa Littafin taci karo dashi ahankali ta tsugunna tasa hannu tadauka sanan tabude tacigaba da karantawa.
“Nasan bama kiwani san Zayn da kyau ba amman tun kina yarinya Zayn na bala’in sonki kuma yanaji dake, Zayn nada tausayi, yanada Imani sanan yanada kirki ni mahaifiyar ki na yarda da Zayn, karki tunani babu soyayya a tsakaninku so yakanzo daga baya, Khairy kaman yanda nafadi miki abaya na zaba miki Zayn ne sabida inaso hankalina ya kwanta aduk inda nasami kaina nan gaba dan haka y’ata don’t reject Zayn! Accept him and accept the marriage do that for me Ummulkhairy, do it for world best Mom dinki! Karki tadama Baban ki hankali ko yayyinki trust me nasan Baban ki will be going through alot kinsan kuma farin cikin ki shine farin cikin mahaifinki da yayyinki karki basu damuwa kinji Khairy na” Awani irin hankali ta gyadama Mama kai wasu sansanyar hawaye nabin idanunta suna saukowa kasa sanan tasake kallon book din.
“Allah yamiki albarka, inhar kayi abu for the sake of iyayenka dan ka farantamusu rai Allah zai albarkace ki, sanan zai baki kome kikeso cikin sauki, Khairy don’t stress your heart kiyi tunanin anything kibi umarnina dana mahaifinki bazaki taba tabewa ba Allah yamiki albarka daga mahaifiyanki Maryama”



Ahankali ta maida littafin tarufe sanan ahankali ta tashi tamike tsaye jinta take kaman iska zai kadata tafadi wardrobe tabude tadaga karkashin kayanta ta tura littafin sanan tajawo wani dogon Riga tasaka na bacci kafin tazo gado ahankali ta zauna tana kallon wayanta, ahankali tasaka hannu tadauka sanan ta danna 5miss calls tagani na Aliyu saikuma messenge, message din ta danna ahankali.
“Pickle are you sleeping? Maisa kikai bacci dawuri haka? Wait are you fine are you okay? Wani abu namiki ciwo ne??? Umm I am worried”
Hawayen daya gangaronata ta share ahankali sanan gently tashiga scrolling tundaga farkon message din dasuka farama juna harzuwa na yau tana karantawa wani irin jefar da wayan tayi kan gado takifa kanta kan gadon tana kuka, idan ta tuna Aliyu ta tuna yanda yake sonta da yanda yake mugun kishinta saitaji she can’t hurt him, bazata iyaba bazata iyaba! Ganin tana nema ta shige yasa tashaki inhaler ta sanan ta tashi tashiga bayi tadauro alwala wato idan kaga bala’i rasa bacci kake hijabi tasaka kawai tahau kan dadduma tana kuka tana fadima Allah komi itadai tasan tanata salla wajajen asuba barawon bacci yasaceta anan kaHn dadduman.🥰
[6/26, 12:40 PM] +234 701 275 3212: 4️⃣9️⃣




Bayan sunyi sallan asuba tareda Baffa da Zayn suka fito daga masallaci, tun bayan hatsarin nan haryau Baffa fushi yake da Zayn bayama amsa gaisuwan shi sai sa’i sa’i suna shigowa gida hannun Baffa Zayn yakama ahankali yace “Abba listen to me please” chak Baffa ya tsaya sanan ahankali yakalli Zayn din yay shiru, hannu Zayn yakai yakama kunnenshi ahankali yace “Abba nasan namaka laifi amman dan Allah ka yafemin and listen to me” wuceshi Baffa yayi zuwa kujerun dake garden na tsakar gidan masu kyau yazauna sanan yanunama Zayn daya daga cikin kujerun alamun yazo yazauna, ahankali yataho wajen yazauna yana kallon Abba, anatse Abba yace “Zayn shaye shayen ka bani kama laifi ba ubangijin daya hallito mu kamawa” murya chan kasa yace “Abba I know! Tun bayan abin yafaru I couldn’t live up to myself, Abba anytime naji inaso nayi I remember cewa abin yasa kanwata dat I care for wacce mahaifiyanta tabani amanan ta tace na kula da ita takusan mutuwa kan shan shishana, Abba ba lallai ka yarda ba wlh tun ranan ban kara marmarin shan shisha ba I even hated myself for shan shishan, Abba I am sorry” shiru Abba yayi yana kallonshi dan ya yarda da maganan shi dari bisa dari dan idanun Zayn basatabamai karya, ahankali Zayn yasa hannunshi yakama hannun Abba murya chan kasa yace “Abba I love Ummulkhairy tun kafin namasan da zancen auren and I want to promise you abu daya” yadanyi shiru sanan yace “Abba nasan bakada yanda zakayi ne daka tana auren mu tunda kagano ina shan shisha, Abba listen to me I have amended my ways wlh, and Abba namaka alkawari zan rike Khairy amana, bazan bari any harm to fall upon her ba, and I promise you Abba I will forever cherish and care for her batare dana bari Ammi ko anybody yatakurata ba and I will talk to Ammi zata yarda all those drama zata daina kaji Abba” hannunshi ahankali Baffa yakai kan bakinshi ya sumbace shi ahankali yace “Allah maka albarka Zayn” murya chan kasa yace “Ameen” tashi katafi, tashi ahankali Zayn yayi yawuce Baffa na kallonshi jiyayi duk wani nauyi da zuciyanshi yamai ya saukar tunda har Zayn din dakanshi yazo yay accepting mistakes nashi and promise to work on kanshi Abba jiyayi hankalinshi ya kwanta yanzu Ammi kadai tarage yasan ko itama she will come around.





All through ranan akan gado tayishi takasa fita school, takasa daukan wayan Aliyu takasa cin abinci gatanan ne kawai, wuraren magrib Anty Mariya tashigo dakin tana kallon Khairy dake kan gado maida kofan tayi tarufe sanan takaraso tazauna agefen gadon tana kallon idanun Ummulkhairy dasuka kumbura har lokacin hannunta takai tadagota tazauna sanan ahankali tace “maisa baki fadima Baban ki Aliyu kikeso ba” shiru Khairy tayi tana kallonta dan batasan ya akayi tasan aliyu takeso ba, ahankali Anty Mariya tace “nasan kinason Aliyu shima yana sonki tun a asibiti na karanci all of that, maisa baki fadiwa mahaifinki ba eh Ummulkhairy?” Ahankali tace “Anty kona fadamai is too late bazasu iya komi akaiba” shiru Anty Mariya tayi tana kallon Khairy she just wish tanada wani karfi dazata iya magance this whole case but her hands are tight, ahankali tace “Yaya zakiyi da Aliyu”? Wani irin ajiyan zuciya tasauke dasauri takai hannunta tashare hawayen daya zubomata sanan taja hancinta danji tayi majina zai gangaromata tace “zan gayamai gaskiya” ajiyan zuciya Anty Mariya tayi tace “to ki gaggauta fadamishi dan kinsan bai kamata kina magana da namijin daba naki ba ko” gyadama Anty Mariya kai tayi, ahankali Anty Mariya tashafa kumatunta tace “karki damu duk wanda yabi iyayenshi bayaci baya kinji” gyadama Anty Mariya kai tayi, Anty Mariya ta tashi tace “yanzu zan Aiko Batool da abinci yakawo miki kici” sanan tawuce tafice daga dakin, abinci Batool takawo mata kadan taci sanan tai sallan isha’i ta kwanta yau by 9 ma Aliyu yashiga kiranta, kallon wayan Batool tayi sanan ta tashi ahankali tafita daga dakin danta basu waje suyi magana, kasa daukan wayan Khairy tayi a third call dinne tadauka takai kunne.
Cikeda damuwa Aliyu yace “I am sick worried, Pickle what’s happening? Tun jiya I’ve been calling you baki dauka sokike ciwon zuciya yakamani” girgizamai kai tayi da sauri muryanta na rawa tace “n…..o” shiru Aliyu yayi hakan yasa dasauri ta taushe bakinta tana kokarin hana kanta kukan datakeji, yakai kusan 1min yay shiru kawai, kaman daga sama yace “waya saki kuka”? At this point zare hannun kawai tayi daga bakinta tafashe dawani irin kuka Aliyu knows her so well, if she’s happy yasani, if she’s sad yasani, if she cried yanajin muryanta yasani, shiru yayi yana sauraron kukan ta kaman yashiga wayan yazo inda take yakeji, almost good 2min yabarta tai kuka yanda takeso sanan ahankali cikeda iya lallashi yace “I always tell you I am here for you, why will you be crying haaa? Oya yishiru kinji” gyadamai kai tayi tana kokarin Hana kanta kukan, murya chan kasa ahankali yace “maiya sameki why are you crying”? Jitayi wani kukan yazomata tasake saki, cikeda damuwa sosai Aliyu yace “Pickle wai kasheni kikeso kiyi? U want my life eh? Kinsan yanda kukan ki ketabamin zuciya kuwa? Did you have any idea wlh idan kikaji ance I slump and die kece” rage sautin kukan tayi ahankali dan tasan ko karya daya baiyiba, cikeda lallashi yace “tell me menene, nazo gidanku naganki” dasauri ta girgizamai kai dan tasan wlh zai iya tace “a’a” ahankali yace “to what’s the matter”? Batasan yaya ma akayiba jitayi tace “cikina ke ciwo” tasake taushe bakinta jin takasa fadamai gaskiya for the first time yau tama Aliyu karya, shiru yadanyi sanan ahankali yace “sorry, is it MP? All this menstrual cramps shi?” Gyadamai kai tayi ahankali tace “eh” murya chan kasa yace “sorry, sannu, stop crying, kinsha magani kona siyo nakawo miki” ahankali tace “nasha” murya chan kasa yace “then it will stop soon, hey you this MP cramps I command you to leave my Pickle alone or I arrest you, nayi arresting nashi”? gyadamai kai tayi tana dan murmushi tace “eh” murmushi yayi jin tadanmai murmushi yace “okay MP u are under arrest for disturbing the peace and harmony na Miss Khairy, for taking away her smile and bringing her kukan banza back” dan dariya tayi, hakan yasa yace “yes koba kukan banza bane kikemin ba, idan kika ganni saiki kara wani narkewa kina kuka just to worry my heart Khairy angayamiki ban sani bane” at this point wlh tama manta itane mai kuka dariya tafara sosai, ganin haka yasa yace “haka ranan nazo asibiti u were very fine fa hira ma kike, kina ganina kika kokkobe fuska ashagwabe zaki faramin kuka sabida kawai ki rudani this girl keko don’t worry eventually zan saki kukan mai dalili” dariya tayi dan ita bamata gane last maganan ba, ahankali yace “kinci abinci”? Gyadamai kai tayi tace “but small baran iyaci dayawa ba” murya chan kasa yace “tom anjima idan yalafa sai ki karaci ko” tom, murya chan kasa yace “if it persist tell Batool tasa towel a warm water tamiki massaging abdomen it will stop” gyadamai kai tayi ahankali tace “tom” ahankali yace “gobe zaki school” girgizamai kai tayi tace “no sainaji sauki” Gyadamata kai yayi yace “okay, bari na barki kihuta idan pain din yadawo call me but don’t cry for me again” murmushi tayi tace “saina maka bye” dan dariya yayi ahankali yace “I love you Ummukhairi” katse wayan yayi dip, ahankali tajanye wayan daga kunnenta takasa koda kwakkwaraZn motsi.🥰



5️⃣0️⃣

Wanan Littafin na kudi ne karki karanta batare dakin biyaba kika karanta min littafi ban yafeba.

wa.me/+2347012181461
To chat me up on watsapp

This novel is 1k
Pay 1k into 3107021073 aisha Muhammad saiki turomin evidence of payment ta watsapp number na 07012181461
Thank u❤️

Ranan ma bacci barawo yasace ta da kyar ta tashi dasafe tai salla, tana zaune da safe ita kadai akasa taji an bude kofanta hakan yasa takalli kofan Baba ne, shigowa dakin yayi hakan yasa ahankali tace “Baba ina kwana” zama yayi akasa kusada ita shima ahankali yana kallonta yace “yauma bazaki school ba” gyadamai kai tayi ahankali tace “bama komi sai ranan exam zanje” shiru yayi yana kallonta hakan yasa ta saukarda kanta kasa, ahankali yakai hannunshi yatallabo fuskanta yana kallon kwayan idanunta yace “have you been crying Ummulkhairy”? Dan murmushi takakalo sanan ta girgiza mai kai, baki Baba yabude zaiyi magana dasauri ta girgiza mai kai tana hadiye miyau sanan tasa hannunta ta goge hawayen daya zubomata da sauri sanan takalli Baba murya chan kasa tace “Baba nariga na karanta Littafin Mama na karanta komi naciki” shiru tadanyi sanan tasauke ijiyan zuciya ahankali, murya chan kasa tace “Baba babu abinda bazan iyama mahaifiyata aduniyan nan ba she’s my number one dan haka karkaji komi” tasakeyin shiru tana saukar da ijiyan zuciya ahankali tace “I accept Ya Zayn amatsayin mijina wanda kuka auramin Baba” tai maganan tana danne hawayen ta, wani irin farin ciki dataga ya lullube fuskan Baba yasa tasakinmai murmushi ahankali, rungume ta yayi yana mata addu’a sanan yacirota yace “kome kikeso nasaya miki Ummulkhair kifadamin ko yaushe I will buy it for you, I know Maman ki is very very happy dake, Allah miki albarka, bari naje nafadima Anty ki dan ta shirya tafiya Dubai yomiki shopping zaki bita kutafi tare” girgixamai kai tayi tace “zanyi karatu for final exam Baba” “ohhh hakane nama manta tsabagen farin ciki bari naje” Baba yay maganan yana fita daga dakin cikeda farinciki datama dade bata ganshi da irinshi ba tun Mama nada rai, hannu tasa tashare fuskanta ahankali tace “Ya Aliyu I am sorry” ko kadan batasan tayaya zata fadima Ya Aliyu ba ita batamajin zata iya fadamai ba bama tasan tayaya zatai avoiding nashi ba tana zaune tana tunanin Batool tashigo dakin ganin idanunta sunyi jajir yasa Batool tamaida kofan tarufe tazo inda take zaune akasa tazauna tace “Khairy zakije kisawa kanki wani ciwo ne wai, kin fadama Ya Aliyu”? Girgizamata kai tayi cikin muryan kuka tace “Batool I don’t know Tayaya zan fadamai, I can’t hurt Ya Aliyu, I can’t hurt him, I don’t even want to imagine what he will go through Idan yaji wanan zancen, banson wani abu yasameshi” ta karashe maganan tana goge kwalla duk Batool na kallonta tace “to tayaya zakiyi avoiding nashi yanzu I am sure sabida shine kika kasa zuwa school, Khairy you need to think of something” hawaye tadan share sanan takalli Batool tace “na chanza SIM card”? Dasauri Batool tace “ko kin chanza SIM card ai yasan gidan nan, saidai” tai shiru dasauri Khairy ta kalleta tace “saidai me”? Ahankali Batool tace “call him up kifadamai zakuyi tafiya kauyen su Mama garin kuma babu service gobe zaku tafi ba lallai idan yakira yasameki ba saiki kashe wayanki kawai, karki kara zuwa school din saikun fara exam baduk idan kina exam baya zuwa school wajen kiba” gyadamata kai Khairy tayi tace “to kingani dazaran an gama exam din karki kara fita kawai nasan idan aka kaiki gidan Zayn zai chanza miki layin waya shikenan, idan bai ganki ba daga baya yaji kinyi aure zai hakura” shiru Khairy tayi tana kallon Batool Wanan shine simplest thing datasan zata iya dan she can never ever hurt Ya Aliyu, hannu Batool tasa akan fuskanta ta sharemata hawayen tace “kirashi yanzu” ahankali tadauki wayanta tai dialing number Aliyu, saida wayan ya katse sanan yakirata back, ahankali yace “good morning Miss Khairy yaya jikin I was about calling you Boss dina yarikeni a office annoying man kawai, cikin yadena ciwo”? Gyadamai kai tayi ahankali tace “eh” sanan tai shiru dukan cinyanta Batool tayi hakan yasa dasauri tace “Ya Aliyu zamuyi tafiya yau” dan shiru yadanyi kafin ahankali yace “ina zakuje”? “Kauyen su Mama zamu” ahankali yace “ina ne kauyen”? Dan shiru tayi tana kallon Batool data Balla mata harara dan tana jin maganan Aliyun daga inda take, ahankali tace “uhmmm namanta sunan kauyen, nataba zuwa sau daya da ita secondary school” ahankali yace “ok yaushe zaku dawo”? Murya chan kasa tace “sai Baba yafada I don’t know” hararanta Batool tayi hakan yasa tace “Ya Aliyu kauyen babu network” danjim yayi kafin ahankali yace “Tayaya zan dingajin muryan ki to” hawaye taji yazo mata ahankali tace “nima bansani ba” jin yanda muryanta yayi zatamai kuka yasa yace “to shine zakiyi kuka? Ki tambayi Baba sunan kauyen saiki fadamin kafin kutafi duk randa naji nagaji da rashin jin muryanki I will just enter road and come cus I can’t survive this life banganki ba kuma banji muryanki ba, so don’t cry okay” ita kanta jikin Batool wani sanyi taji yayi ko itane she can’t hurt a guy kaman Aliyu haka with pure heart gashinan so cool and calm. Ahankali Khairy tace “okay” murmushi yadan mata yace “mai kukan banza, lemme get back to office kafin boss dina yay firing nawa in the middle of minute nadauki excuse nafito, bye I love you Miss Khairy” ya katse wayan da alamu sauri yake ajiye wayan zatayi taga kiranshi yashigo ahankali tadauka gudu taji yanayi yace “I forgot to tell you Allah kiyaye hanya, kidauki mosquito cream, insecticide and mosquitoe net kauye akwai sauro I don’t want them biting you, and go with indomie da some cereal incase bazaki iyacin abincin kauye ba, and again go with some bottle water karkisha ruwan rafi kinji, take care of yourself for me kinji Ummulkhair” gyadamaikai tayi ahankali tace “naji Ya Aliyu thank you” dan murmushi taji yayi sai chan taji ya tsaya dagudun yace “shitt! Pickle my heart kinda feel sad, I guess I am

Please Login or Register in order to submit comment