Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

tashi yayi yafita babu wanda ya iya cemai kala, Manaf yayi yayi yarike kukan nashi but yakalli Mama yaga yanda tadawo but dudda haka she’s still faking smile musu kawai yaji zuciyanshi yay breaking, fuskanshi yakifa akan kujera kusada Mama sai kuka yake da Mu’az dahar lokacin shi yama kasa shigowa cikin falon yana wajajen kofa, ahankali Mama tasa hannu takamoshi wani irin rungumeta yayi sanan tamikama Mu’az hannu alamun yazo zuwa yayi shima kuka wiwi ajikinta babu wanda ke iya magana cikinsu har Maman dan kumburin da fuskanta da wuyanta yayi yasa bata iya magana.


Ranan dukansu suna zaune a falon nan babu wanda ya iya motsi har asuba sanan tai bacci, daki suka Kaita suka keantar da ita sanan Baffa ya kwashi iyalinshi suka tafi gida, suna shiga alwala yadauro kawai yawuce masallaci.


Wuraren karfe 8 nasafe yafito daga masallacin, gida yawuce dayake yana dakin Ammi ne nan yayi bata falo yasan ta kwana hakan yasa yay sama zuwa dakinshi, zama yayi kan wata kujera ta musamman dayake da ita adakin nashi datake nan kaman gado shiru yayi yana tunani, ahankali yamika hannunshi yadauki wayanshi yay dailing number dayay saving da Zayn dayake nan international number, wayan na gab da katsewa yadauka anatse yace “Abba” dan ajiyan zuciya ABBA yasauke anatse shima yace “Zayn nasan is late ko wajenku” gyadamai kai Zayn yayi yana ture shishan dake gabanshi yatashi daga wajen yay bedroom dinshi zama yayi kan study chair nashi jin muryan ABBA somehow couple with the fact Abba baima Saba kiranshi da night ba most time da safe ABBA ke kiranshi ko darana, ahankali yace “Abba what is it are u okay”? Ajiyan zuciya Abba yasauke yace “Zayn Maryam matan Baffan ku batada lafiya, she’s seriously ill, inaso kome kakeyi yanzu kabarshi find any available flight dazaka samu dazai taho naija gobe be it PJ ko normal flight ne kadawo gida” tunda yafara school that’s tun lokacin dayake degree Abba baitaba demanding yadawo gida ba sai this time hakan yasa ahankali yace “okay Abba, but meke damun Mama”? Zayn yay tambayan ahankali dan yanason Mama she’s one humble woman da he admires alot dudda he’s not that close to her shi aduniyan nan ma only Ammin shi ne he’s close too. Ahankali Abba yace “she has blood cancer! Just few days takeda shi left inji Doctors, anyway just come home kayi few days Saika koma tunda baka fara finals dinka ba, good night son” “night Abba” yay maganan ahankali feeling down, yadade ahaka sanan yatashi.


Wuraren 8:00 na safe tabude idanunta ganinta adakin yayyinta saida abin yabata mamaki, murmushi tayi ta tashi zaune sanan ahankali ta sauko daga gadon lallai tagaji ko lace din jikinta bata chanza ba tai bacci, jakanta tadauka tawuce tafita daga dakin tana tafiya ahankali, flat dinsu tashiga babu kowa a falo sama tayi dakinta tashiga alwala tayi tai salla tukunna sanan tacire kayan wata doguwan rigan bacci ta tasaka sanan tafito direct hanyar dakin Mama tayi bude kofan tayi tace “Mama tun jiya nan ganki ba adakin su Ya Manaf na kwana” akan gado taga Mama ta jingina da hango ta sanya sweater tai fayau da ita da hulan sanyi akanta batasan mesa ba but gani tayi Mama tamata wani iri a idanu, karasowa tayi gaban gadon saikuma ta tsugunna takai hannunta tai tagumi tana kallon Mama, hararanta Mama tayi da kyar ta iya dagewa tabude bakinta tace “me haka”? Ahankali tana kallonta still tace “Mama wlh kin chanza, lips dinki are so dry, Mama wai bakida lafiyane kike boyemin kinyi wani iri eh sabida kinsan zan damu, bazan damu bafa Mama ai yanzu na girma saima na kula dake” dan shiru tayi tana kallon Maman dake kallonta tanaso tai magana amman azaban datakeji awuyanta yasa takasa, dasauri Khairy tace “zan damu kadan but zan kulada ke bakid lafiyane Mama” tai maganan idanunta na rau rau dan she’s really believing Mama bata da lafiya, ganin haka yasa Mama tamikamata hannu sanan tahadiye duk wani azaban datakeji tace “lafiyana kalau kawai gani nayi my little Khairy has grown so sooo big, yarinya na tai girma she can even take care of her Mama come here” dasauri ta tashi hannun Mama takama sai kawai tasaki hannun tafada jikin Mama ta kankameta sosai ahankali tace “Mama wlh ina bala’in sonki, without you bansan ya zan kasance ba, Mama ko idan na kalli wasu yaran ko sai inga they are not lucky sabida bakene Maman su ba, Mama u are the best Mama I the world, u are the coolest Mom, the softest, the sweetest, bakida fada, gashi kina sonmu, we are ur everything Mama, Mama kinsan menene” girgiza mata kai Mamantayi, Khairy tace “all mothers are mothers, but not all mothers are like Mamana, cus Mamana tafi takowa dadi, Mama kinga duk girman dazanyi I will always be ur baby, Yar autan ki, kinga na gama school nafara aiki zan dinga miki komi, Mama nasan kinje makka but zan kaiki makka da kudina da aka biyani albashi wajen aiki” dariya Mama tahauyi sosai dayasa Khairy wani kalan murna, sanan tace “Mama yauma ni zan miki breakfast mezaki ci na dafa miki” ahankali tace “fate nakeso” wani tashi tayi tasauka daga gadon sanan tai juyi tace “then fate it is bari naje” tajuya dasauri tai hanyar kofa hartasa hannu zata bude kofan ahankali Mama tace “Ummulkhair” faduwa taji gabanta yayi hakan yasa ahankali tajuyo takalli Mama tace “naam” dakai Mama tamata alamu tazo dasauri taje gaban gadon, hannu biyu Mama tasa tai cupping face nata tana kallonta kafin ahankali takai goshinta saitin bakinta sanan ahankali ta manna mata kiss a goshin, murya chan kasa tace “I love you Ummulkhairy, Allah yamiki Albarka, Allah ya haskaka rayuwanki, Allah ya tsaremin ke” ahankali tana kallon fuskan Mama tace “Ameen Mama” takasa tashi, ganin kaman she’s trying to read something from Mamas face yasa Mama tace “Oya tashi kije kimin fate na yunwa nikeji Madam kokin fasane tunda kin tasani gaba kaman kin sami talavijin” da sauri ta tashi tana dariya tafice daga dakin.

Bana tagani agaban dakin murmushi tayi tace “good morning Bana natafi yima MaUma fate”.
[6/16, 7:56 PM] +234 701 275 3212: 2️⃣4️⃣


Free page
This book is 1k to join my group pay 1k into 3107021073 aisha Muhammad first bank saiki turo evidence of payment ta watsapp number na 07012181461


Chat me up directly by clicking on this link
wa.me/+2347012181461

Wuraren 11 tagama faten daya cika gidan da kamshi, fito da kulan falo tayi Mama tagani da Baba zaune afalo saisu Ya Manaf sunama Mama hira, tashi Maheer yayi yatayata suka fito da komi tsakar falo sanan suka zazzauna karban na Mama Baba yayi da kanshi yadinga bama Mama faten bashi kadai ba harsu Manaf sunyi mamakin yanda tasha faten dan tadena cin abinci, tass ta shanye sai dadi Khairy keji saida kowa yagama sanan ta kwashe komi itada Maheer sukakai kitchen tarema sukai wanke wanken tace “lallai yau mutanen mutuncin ka na nan kusa Maheer” hararanta yayi yawuce yafita daga kitchen din itama tabiyoshi tafito, Baba dake kallonsu yace “go and get ready Khairy malamin ki zaizo by 12” sama tawuce agurguje ta shirya tafito falo lokacin ba kowa Baba yakai Mama dakinshi, by 4 malamin yatafi su Manaf suka fita da ita basu dawo gidan ba sai around 10 tana zuwa lafiyan gado tabi.

Gabaki dayan gidan yau basuyi bacci ba sabida yanda jikin Mama yay tsanani, amai tadingayi na jini both tabaki da hanci, jikinta yay zafi sai maganganu take dabama sa ganewa, saida safen nan bacci ya dauketa.

6 ta tashi tana kallon agogo mamaki ma take ya akayi take lattin tashi late this days, wayanta dataga yay haske yamika hannu tadauka 2miss calls tagani na Aliyu saikuma message dayamata bude message din tayi. “I miss you” murmushi tayi ta ijiye wayan sanan ta tashi tawuce bayi wanka tayo tareda alwala Dan yau tanada morning lectures, tana fitowa tasa kaya tai salla sanan tabude kofa tafito su Ya Manaf tagani a falon sama kwakkwance kan kujera suna bacci, mamaki tayi amman ta tabe baki tai hanyar dakin Mama bude kofan tayi zaune taga Baba kan kujeran dakin yabude Al Qur’ani yana karantawa itakuma Mama na kwance kan gado tana bacci yarufa mata bargo, saida yakai ayar sanan ya kalleta tace “Good morning Baba” murmushi yamata yace “morning daughter, Mama is sleeping jiya dukanmu bamuyi bacci dawuri ba munata hira yayyinki na nan falo suna bacci suma” gyadamai kai tayi tace “eh nagansu” Gyadamata kai yayi yace “jeki breakfast yau Monday 8 kikeda lectures i want you to be serious kigama da good grade” gyadama Baba kai tayi sanan tajuya tafita tana kallon fuskan Mama dake bacci peacefully sanan tasauka falo ahankali, kitchen taje tea tadafa musu duka sanan ta soya chips zama tayi dinning zataci amman hakanan taji takasaci jikinta yamata wani irin sanyi kodan ita kadai ke yin breakfast dinne oho, tashi tayi tawuce sama tana kallon su Manaf da still ke bacci ta shiga dakinta dan shiryawa.


Shiryawa tayi tsaf cikin wani black abaya mai bala’in kyau tai rolling gyalen akanta ko kadan batai kwalliya ba but she looks kaman wata Somalian queen, jakanta tadauka sanan tafito, dakin Mama tabude takalli Baba dake karatu har lokacin tace “Baba natafi” saida ya idasa Ayan sanan yadago kudi yaciro yamika mata karba tayi tana murmushi tace “thank u Baba, kacema Mama natafi idan ta tashi bye” murmushi Baba yayi yace “to yarinyar Mama” maida kofan tayi tarufe yasauke ijiyan zuciya Noo yagaji Khairy deserve to know Maman ta is sick, he’s tired of hiding it from her, bari Maryam ta tashi zai gayamata is time sufadi ma Khairy, Khairy is grown up she can handle it.


Fitowa tsakar gida tayi tana tafiya ahankali hakanan jikinta kawai yamata sanyi yasaki tarasa mesa kawai she’s feeling sad and week ma yanzun nan, karasawa wajen motanta tayi Adamu na shiga itama tana shiga baya daidai sunajin horn mai gadinsu na budewa, motar Baffan ne ke shigowa gidan Hafiz ke tuki, sai motar Ammi biyeda su da driver ke parking sai kuma motan Mom, bude kofan motar tayi tafito tana murmushi da saurin ta tai wajen motan Baffa, daidai lokacin Baffa na bude baya yana fitowa yana mata murmushi yace “yan makarantan bokoko” dariya tadanyi tace “Baffa ina kwana, Ya Hafiz Baban Baby ina kwana, Laaaa Ya Hassan da Ya Hussain harda ku akazo yau” kafinma suyi magana Baba yace “wuce tafi school karki latti” yanuna mata motarta da Adamu yatada yana jiranta shiga motan tayi tana waving Mom dake saukowa daga motanta dan har yanzu motan Ammi bama abude ba kuma bamata iya ganin cikin banda driver shima ta glass din gaba taganshi dan motan tinted ne, jan motan Adamu yayi suka tafi nai gadi yamaida gate din gidan yarufe daidai lokacin Baba da Manaf suka fito.


Ahankali aka bude kofar motar Ammi, wani clean white kafane ya sauko dake sanye cikin wani hadadden sandals na Prada black, nails na kumban kafan are so fresh and white, gently yakarasa saukowa daga cikin motan yana yatsine fuska yana gyara bakin sun glasses na idanunshi na kampanin rayban, yana sanye cikin milk color yadi dayay dinkin jumper dashi daya bala’in amsan jikinshi, yanada tsayi dan wajen gabaki dayansu yafisu tsawo babu wanda baya ganin kanshi, yanada cika dakuma fadin kirji, kana ganinshi kaga Ammi kaman tai kaki ta tofar saisa yafi kannenshi kyau dansu Hafiz da Baffa suke kaman, yanada wani irin black very very dark saje dake kyalli kaman na bature, lips dinshi is so pinkish, gashin kanshi a kwance suna shinning, hannunshi ya daura agogo Rolex akai, ita kanta Ammi anytime ta kalleshi she feels proud da Allah yabata Zayn as her son, Zayn is definition na handsome guy, kyakkyawan namiji da babu macen data isa tamai yanga, ganin Baba yataho wajensu yasa ahankali yakai hannunshi yazare eye glasses na idanunshi yadan sunnar da kanshi kasa Baba nazuwa cikeda mamaki yakama hannun Baffa yace “d’ana Zayn nake gani haka” murmushi daga Baffa har Ammi da Mom sukayi, Baffa yace “da asuban nan yashigo gida” anatse Zayn yace “ina kwana Abba”? Hannu Baba yabashi ahankali yasa nashi hannun cikin na Baba, daidai sukaji muryan Maheer yana ihu. “Babaaa” Dawani irin sauri Baba yasaki hannun Zayn yay ciki Baffa da kowama suka bishi sama sukayi, dakin Mama Baba yashiga yatarar da Mu’az yarike Mama dake aman jini sosai tai lakur babu karfi kodaya ajikinta, wajenta Baba yayi yakamata daga hannun Mu’az yadau tissue yana share mata bakin ganin tadena aman, shigowa dakin Mom tayi takalli Baba tace “Alhaji bari mu chanza mata kaya” girgiza kai Mama tayi ahankali tana rike Baba gam batare datai magana ba, kallonta yayi sanan yakalli Mom yace “abarshi tukunna” karasowa gaban gadon Baffa yayi yaja kujera yazauna yana kallon Mama dabata iya bude idanunta da kyau yace “Maryam mutafi asibiti”? Girgizamai kai tayi ahankali, ajiyan zuciya yasauke yay shiru, shigowa ciki Ammi itama tayi tasami gefen gadon tazauna ahankali tana kallon Mama murya chan kasa tace “kina bukatan wani abu Maryam mezaki ci?” Girgizama Ammi kai tayi hakan yasa itama tai shiru, ahankali Baffa yajuya yakalli Zayn daya tsaya chak abakin kofa shima yana kallon Mama sanan Baffa yajuyo da kanshi ya kalli Mama yace “Maryam ga Zayn dakika ce nakira miki yazo” dan yunkurowa kadan tayi da duka karfinta, dasauri Baffa ganin haka yasa yace “Zayn come” karasowa gaban gadon Zayn yayi ahankali sanan gently ya tsugunnawa gaban gadon yana kallon Mama dake kallonshi kallon dakasan baa hayyacinta takeba yace “Mama I am here” hannunta daya tacire daga jikin Baba data rikeshi gam gam jin haka yasa Baba yatayata , kama hannun Zayn tayi hawaye yazubomata daga idanunta sanan kadan tabude bakinta dasauri Zayn da zuciyanshi ta katse yace “Mama I am here mekike so tell me” yakai kunenshi saitin bakinta, magana tashigamai a kunne wanda harta Baba dayake rikeda ita baiji abinda ta Fadima Zayn ba sanan takoma jikin Baba ta kankame shi, Maheer dataga yana kuka sosai mara sauti abakin kofan ta kalla hannu tamikamai ahankali yataso yazo kawai kankameta yayi yahau kuka sosai ahankali yace “Mama dan Allah kiwarke, Mama please karki mutu kibarmu” motsi sosai bakin Mama yafara hakan yasa Baba ya janye Maheer daga jikinta kankame Baba tasake yi takama hannunshi tarike gam gam kaman dats the only thing dake mata dadi sanan cikin wata kalan murya dabata fita da kyau dan hakoranta sun datse tace “Baffa, Ammi, Mom, dukanku yarana ina rokonku gafara ku yafeni idan nataba bata muku, idan Ummulkhair…..” wani kalan nishi tayi tana kuka sosai dabayama fitowa sosai tace “kuce mata nace tayakuri tayafema Maman ta, i hide everything sabida nasan idanda tasan banda lpy bazata dauki abin da kyau ba, Baban Manaf” tai maganan tana kankame Baba tace “ka kulamin da Khairy dan Allah, Baffa nabaku amanan Khairy da duka yarana, Khairy is fragile, and innocent please ku rikemin yarinyata amana ita nafiji araina, zanbar duniyan nan amman Khairy ce araina sabida ita kadaice diyata mace yayyinta maza ne” ajiyan zuciya Mama tasake saukewa sanan ahankali tace “idan narasu Khairy taki kwantar da hankalinta kabata Littafin nan danabaka ka ijiye mata Baban Manaf” gyadamata kai Baba yayi ahankali hawaye na taruwa a idanunshi Baffa ya bubbugamai kafa alamun karyay kuka, ahankali Mama tace “Baffa kamishi aure dazaran na rasu banson yarana su rasa uwa, Manaf kurike Matar da mahaifinku zai aura kaman ni kada kubata ciwon kai” gyadamata kai Manaf yayi, Ammi kallon Mu’az yayi dake bakin kofa tayi ya tsugunna idanunshi sunyi jajir tace “zo wajen mahaifiyar ka Mu’az” mikewa yayi tsaye da kyar shigowa yayi zuwa wajen gadon kawai yadaura kanshi kan gado yadaura hannunshi kan nata dan that’s what Maheer da Manaf duk sukayi, yanda tazo tana nishi yasa Baffa ya gyadama Baba kai ahankali Baba yasoma karanto mata kalman shahada, saukar da kanshi kasa Zayn yayi, ahankali Mama ta amshi kalman shahadan karfe 12:03 daidai tacika da imani daidai lokacin Khairy ta tashi daga kan kujera sun gama lectures zasu fita jitayi kafafunta sunyi sanyi kawai tai baya zata fadi kaman tai paralyze Rabi dake bayanta ta tareta tace “ke Khairy are u okay” ? rike Rabi tayi tana taba kirjinta tace “gabana fadi yakeyi sosai kafana ba karfi” zaunar da ita Rabi tayi tace “kinyi breakfast kuwa”? Girgiza kai tayi hakan yasa Rabi da sauran kawayenta sukai dariya tace “yunwa ce muje kici abUinci”.
[6/16, 7:56 PM] +234 701 275 3212: 2️⃣5️⃣



Almost good 10min na silent ne yacika dakin, at this point Baba jiyayi kaman shima yamutum ne dan he could feel yanda hannayenta suka sassandare ajikinshi kasa koda motsi yayi hakan yasa Baffa yay taking over, daga Baba tsaye yayi, ahankali Baba yasauke kanshi kasa yana kallonta in disbelief, yadade ahaka sanan yakai hannunshi ya kulle mata idanu kafin yaja bargon yarufeta saikawai yazauna akasa dabas baimasan mema zaiyi ba dan he’s still in shock idan ya kalli su Manaf daduk suke kuka saiyaji zuciyanshi yakara tsinkewa, kafadanshi Baffa yakama ya matsa hakan yasa ya fuzar da iska kafin ahankali yasa hannunshi yakamo su Manaf daya bayan daya duka yarikesu ajikinshi kam kam, juyawa Baffa yayi yakalli Hafiz dashima yay mutuwan zaune hakama su Hassan ahankali yace “Hafiz jeka dauko Khairy daga makaranta”
Tashi Hafiz yayi ahankali yafice daga dakin tafiya yake but jiyake kaman iska ke kadashi yana tuna all memories dinshi da Mama shikenan daba danta data haifa ba balle kuma yaranta yaya zasuji.

A famfon gaban flower ya tsaya saida ya wanke fuskanshi tass sanan yakarasa wajen mota shiga yayi yatada motan yana kallon yanda mai gadi ke budemai gate he just wish yanada karfin sanar da su, amman ina motarshi yaja yafita daga gidan zuwa school din su Khairy, har gaban department dinsu yaje accounting yay parking yakai kusan good 20min zaune acikin motan baida courage na facing Khairy, da kyar ya iya gyara mood dinshi sanan yakashe motan yafito yamaida yarufe yana kallon ko’ina kafin ya shiga ciki, Khairy nabashi labarin how popular she is a school so yasan ganinta bazai tabamai wahala ba, wasu yammata guda uku dasuka sauko daga bene yatare yace “hello ladies dan Allah kunga Khairy” daya daga cikinsu ce tace “yanzun nan muka rabu da ita ga ajinsu chan wanchan floor din suna lectures” thanks yace musu sanan yawuce sama zuwa gaban class din excuse yay taking hakan yasa lecturer yafito dan yana ganinshi yasan Wanan baimai kala da dalibin makarantan nan ba, dawowa cikin ajin lecturer yayi yace “Ummulkhair” dasauri Khairy dake zaune ta kwantarda kanta kan table takalli lecturer tace “yes sir” waje yanuna mata yace “ana nemanki” tashi tayi ahankali tana daukan jakanta tafito tana tafiya kadan kadan dan sosai kafafunta basuda karfi ganin Ya Hafiz yasa tabude baki cikeda mamaki takarasa gabanshi da sauri tace “Ya Hafiz mekazo yi a school dinmu”? Hararan ko’ina yayi yay gaba abinshi tana binshi da sauri yace “me zanyi a school dinan naku Baffa yace nakawo ki” dasauri tace “Allah sarki Baffa yana ina tare kukazo kenan” “yana gida” yafadi kai tsaye batare daya juyo ya kalleta ba daidai suna karasa sauka kasa tana binshi abaya tace “Ya Hafiz wani laifin nayi ne wanan da dazu dasafen nan nabar Baffa agida mekuma nayi” juyowa yayi yakalleta daidai yabude mota yay murmushi yace “yarinya laifi dayawa” zare idanu tayi cikeda tsoro tace “hala saisa gabana keta faduwa wlh” tada motan yayi tashigo ganin duktai wani irin yasa yace “common babu abinda kikayi so relax” murmushi tayi dasauri tana sauke ijiyan zuciya but dudda haka she’s not just feeling ok hakan yasa tai shiru kaman ba itaba danda tacikashi da surutu shima shiru yamata baice mata komi ba ahaka har suka shigo layinsu, tundaga nesa take hango tulin mutane ata kofar gidansu maza na alwala hakan yasa ta gyara zama tace “Ya Hafiz maiya faru a anguwan mu”? Hango gate din gidansu abude awangale gakuma mutane yasa taji kawai gabanta nafaduwa ba kakkautawa, shiga cikin gidan sukayi daga baki baki Hafiz yay parking dan compund din yacika da mutane wasu tsaitsaye wasu zazzaune hango mai gadinsu da Adamu direbanta na kuka yasa kawai taji wani karfi yazo mata tawani bude kofan taduro juye juye tafara tana juwa juwa tanabin all mazan da idanunta kan sauka akansu tana kallo, kaman daga nesa taji dodon kunenta yaji wani magana. “Itace diyar Hajiyar data rasu” kafafunta da tun dazu sukai sanyi jitayi karfi yazo mata acikinsu kawai tahau gudu tai flat dinsu dataga kofar abude tashiga uwa an jefota tanabi kowa na falon da kallo matan anguwansu ne makotansu sunci mayafai some da charbi a hannu, stairs tayi dawani kalan mahaukacin gudu kawai neman mutum daya take dan gidansu she wants to know what’s happening idanunta ma sun rufe zuciyanta na bugawa batama ganin gabanta bum! Taji sunci karo da mutum da sauri takoma baya sanan tazaro idanunta tadaga kanta takalli wanda ke gabanta kaman yanda shima yake kallonta, batasan wayeshi ba but she could see kamannin shi da Ammi wani kayatyaccen kamshi nafitowa daga jikinshi, ahankali bakinta ke motsi numfashinta na neman gagaranta yi sabida yanda kirjinta ke bugawa ba kakkautawa ahankali tace “I……ina…….ina….”? Idanunta ne suka sauka kan gawar dataga an shimfide anan falon sama da aka suturta, sai yanzu ma talura da mutanen dake falon saman, Baffa, Baba, Ammi, Mom, Ya Manaf, Ya Mu’az, Maheer, Ya Hassan da Hussain Mama ce kadai batagani, still numfashinta na bala’in katsewa tabi idanun kowada kallo barinma Maheer dake kallonta yana wani irin kuka harda majina da she just think that answers her question, gently tadaga kafanta tana wani kalan kyafkyafta idanuwanta tana dambe da numfashinta dake kokarin daukewa tana kokarin tai taking just a step forward kawai tajita blank tai baya straight, wani irin tareta yayi dawani irin sauri Baffa yataso yana kallon Zayn daya tareta yace “Zayn kwantar da ita akasa she’s asmatic, Manaf get me her inhaler” dakinta Manaf yashiga yafito da sabon inhaler dago kanta Baffa yayi yadaura akan kafanshi yakai inhaler bakinta yana bubbuga kumatunta da kyar ta shaka tai wani irin nishi tadawo Baffa takalla tashi tayi zaune kaman bata hayyacinta tace “Baffa ina Mama na”? Ganin Baffa yay shiru yakasa bata amsa yasa takalli Ya Manaf tace “Ya Manaf ina mama ya akayi banganta ba” saukar da kanshi kasa yayi, ahankali Baffa yace “Ummulkhair” wani irin gyadamaikai tayi jikinta ko’ina na ta rirrike Baffa, all this while Baffa has been mai taurin zuciyan but for the first time yaji Khairy kaman itace zata karyashi, dakewa yayi yace “listen to me Khairy, kinaji” gyadamai kai tayi jikinta har kafafunta bari suke ta rirrike Baffa wani irin zufa na keto mata agoshi, anatse yace “dukanmu anan da mazajen dakika gani a waje ke kawai ake jira domin inaso kima mahaifiyarki addu’a, Ummulkhair inaso kizama yarinya mai Imani da kaddara mai kyau ko mara kyau sanan kisani cewa kullu nafsin za’ikatul maut, i want you to calm down don’t shout and don’t cry kinga kinada Asma karkije kima kanki illa, Ummulkhairy Allah yayiwa…..” Baffa yadanyi shiru ganin yanda tazaro ta kwalalo manyan idanunta waje kaman zasu fado kasa yanda jikinta ke rawa zaka dauka ajikin injin markade take, daurewa Baffa yayi ahankali yace “Allah yayiwa mahaifiyar ki, Maman ki rasuwa Ummulkhairy”.

[6/16, 7:56 PM] +234 701 275 3212: 2️⃣6️⃣



Wani kalan shuuuuu taji kunenta nayi, itadai tasan taji koke koke, taji maganan Baba, su Ya Mu’az har maganan Ammi tasan taji sama sama kafin chan kuma taga tabude idanunta tana kallon kowa dake kanta, kala batace musu ba rarrafe ta shigayi har zuwa gaban gawan zama tayi dirshan tana kallon farin likafanin hannu tamika zatakai tabude saikuma tai shiru kafin ahankali tasa hannunta taja likafanin kasa fuskan Mama ya bayyana tai wani haske ga alamun murmushi tanayi wani kuri tayi da idanu kaman tahaukace sai kawai idanunta aukahau mata yana kaman Mama murmushi take mata dariya tayi sanan tajuyo ta kalli Maheer dake kuka tace “Ya Maheer dena kuka kaji zoka gani ga Mama nan namin murmushi, Mama bata mutu ba bacci take wlh gashinan zoka gani” babu zuciyan wanda bai tsinkeba adakin ahankali takai bakinta saitin fuskan murya chan kasa

Please Login or Register in order to submit comment