Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

not her spec, yana mata magana yana wani wawware fingers kaman yana rapping yana kama tsakiyan baggy wandonshi, ko kiranshi amatsayin boyfriend nata ma bataso ta tsani taji anyi, bakin ciki da haushin shi yamasa tama kasamai reply kawai tajuya ta gefenshi zata wuce dan sometimes idan abu is really annoying agareki rasama abinda zakace kake, kawai ji tayi yariko hannunta “don’t go baby wait” wani irin juyowa tayi batai wata wata ba kawai ta daukeshi da mari jikake tass! Wani irin ihu abokanenshi sukayi suna waige waige ko there’s anyone there dayaga Marin datama Ahmad dan zai zama abin kunya ance wata tamari hiphop rapper. “Ke celebrity kika mara” fizge hannunta tayi tana kallon yanda yadaura hannunshi kan kuncinshi yana wani irin kallonta da idanunshi dasukai jajir dan marin ya shigeshi, rawa jikinta yafara da sauri tajuya Ahmad daya bala’in zuciya yace “ku bita” jin haka yasa ta kwasa da bala’in gudu acikin parking space din dababu kowa tana kalle kalle, kaman ance takalli right side dinta, hango wani dogon mutum tayi yabata baya Awani lane na motoci yana tsaye jikin wata suv waya a kunenshi da alamu waya yake, wani irin kwana tayi tana gudu tai lane din dayake batai wata wataba tana kaiwa daidai inda yake batai wata wataba tawani zaga ta gabanshi ta shige kirjinshi at once tana boye fuskanta akirjinshi jikinta ko’ina narawa sosai sabida tsoro yanda maza har biyu komatace uku suka biyota, cikin Yar siririyan muryanta that is trembling sosai tace “please save me…..plss…….I’m sca…….” tana maganan tana nishi da sauri da sauri dayake jinshi harcikin fatan kirjinshi don fuskanta gabaki daya na wajen ne, daidai lokacin daga boys din Ahmad din har Ahmad din dukansu sunzo wajen sun tsaya agabansu suna maida ijiyan zuciya sabida gudun dasukayi, One by one mutumin ke binsu da kallo batare daya furta ko a word ba har lokacin wayan nakan kunneshi bai cireba, faduwa gaban Ahmad yayi ganin fuskan mutumin dake kallonsu, ahankali yajuya sadaf sadaf daso samune ko takalmin shi da kasan wajen karma suyi motsin nuna alamun yana moving sanan ya yafito abokananshi da hannu yace “let’s go guys” dasauri sukace “marinka fa tayi Boss” da saurinshi kaman ana hankadashi yawuce yace “shikenan nidai natafi ku ku tsaya” ganin yanda yake tafiya da saurin bala’i tun bayan yaga fuskan mutumin yasa suma sukasha jinin jikinsu suka juyada sauri suka wuce.

“Eh Gwaggo ina jinki sorry ba shareki nayiba, Abban nake jira nariga nakawo shi…” ahankali tashiga dagoda kanta kaman wata mara gaskiya cikeda kunya jin mutum na wayanshi ta tsokano fada tazo tafada jikin shi, kanta akasa ahankali sadaf sadaf tashiga fitowa tana matsawa baya kafin gently kanta nakasa batare data kalleshi ba tace “thank you” sanan ahankali tajuya tashiga tafiya har lokacin gabanta nafaduwa sosai. “You!” Taji kaman daga sama mutumin yakirata chak ta tsaya batare data juyoba, “turn around” taji muryanshi anatse yet with authority batasan mesaba amman kasa ketare abinda yace tayi tayi hakan yasa gently tajuyo sanan ahankali tadaga fuskanta takalleshi, wani dogon saurayi ne fari sol dashi kaman balarabe yana sanye da jumper na farar shadda bugaggiya kanshi babu hula gashinshi akwance baki sidik sai kyalli yake hannunshi rikeda iPhone 13 yazubamata idanu dababu alamun wasa daidai da digi acikinsu, hakanan jitayi takasa jure kallon mutumin dataga kaman ta sanshi amman ta manta a ina ta sanshi ta sauke kanta kasa, anatse yace “the next time I will see you making trouble I will arrest you!” dasauri tadago kanta ta kalleshi saida yafidi kalman arrest sanan police din ranan yafado mata arai, dauke kai yayi daga kallonta sanan yabude kofar motan daya tsaya jikinta ya shiga ciki tareda rufe marfin motan da sauri dayadan firgitata sanan ahankali tajuya tacigaba da tafiya ahankali.



Samin kanshi yayi da binta da kallo ta madubin motan, yanda take tafiya ahankali har lokacin bata dawo daidai ba, sanan ahankali yadauke kanshi daga kallonta jin wayanshi na ringing again screen din yakalla ganin Grandma yasa yabude motan yafito yace “this woman will not allow me leave in peace”.

Garden din takarasa tun daga nesa kawayenta dasuka hangota suka kwalamata kira hakan yasa takarasa zuwa inda suke zama tayi sanan tadauki bottle na ruwan dake gaban Farida tabude takai bakinta ta kwalkwale duk kallo suka bita dashi, saida ta shanye goran ruwan tass sanan ta ijiye tana sauke ijiyan zuciya, Farida tace “daga ina kike haka duk kinyi zufa kaman kin fito daga yaki” dan yatsine fuska tayi kaman bazatai magana ba ganin yanda suke kallonta yasa tace “Ahmad na mara shine yabiyoni and someone…..” tadanyi shiru kafin ahankali tace “wani mutumi yataimakeni” atare dukansu all the 5 friends sukace “wani mutumi” shiru tayi sai chan tace “oho nima ban sanshi ba” dukansu dariya sukahau yi dasauri takallesu tace “me” hada baki sukayi sukace bakomi, sharesu tayi kawai cus she doesn’t even feel okay batasan mesa ba, duk suna zaune wata kawarsu tashigo eatery dagudunta tana haki tace “kufito kugani yan sanda sun shigo school dinan anzo ana kwashe su Ahmad da Gang dinsu” dasauri Farida tace “ke haba let’s go video it musashi a internet” dukansu tashi sukayi itama ta tashi tabisu suka fice daga cikin garden din, van suka gani na police gaban wani eatry dake kusada garden din dasuke ciki, dasauri suka karasa gaban eatry din student sun cika wajen suna kallon Van din police, suna tsaye wajen dayay cha da mutane sukaga an fito da Ahmad da akasamai handcuff a hannu an sashi a van din sai abokanen shi na dazsu dasuka biyota guda biyu saikuma wasu guda biyu daban yan sandan sun fito dasu ana sakasu a van din saiga police man dinan shima yafito daga eatry har lokacin yana sanye da kayan dazu farin shadda waya a kunenshi still, hada idanu sukayi batasan mesaba jitayi gabanta yafadi dasauri ta sauke kanta kasa tareda juyawa ahankali tamabar wajen bata kara juyowa ba kawai tai hanyar class nasu, daidai lokacin ana shirin fara wani lecture kujera tasamu atsakiyan ajin ta zauna sanan tabude jakanta taciro note nata da pen aka fara lecture ko kadan takasa concentrating batasan mesa ba she just keep seeing police man face din da what happen today, gabaki daya all through da day har yamma ita kanta tasan yau ba school tazo ba takasa natsuwa tunanin shi da komi yacika mata kai, wuraren 5 na Yamma Adamu direba yazo daukan ta shiga motan tayi ahankali tace “Adamu please kafara kaini Coldstone nasayi ice cream nasha saimu wuce gida” cikeda girmamawa yace “to Miss Khairy” daura kanta tayi akan kujeran tajuyar da kanta tana kallon hanya tareda fuzar da ijiyan zuciya, she just hope tanashan ice cream dinan sanyin shi zaisa brain nata yay sanyi tadena all tunane tunanin datakeyi tun safe.


Agaban wani Babban joint na coldstone Adamu yay parking hakan yasa tabude motan tafito ta shiga ciki, daidai wani Babban Jeep na shigowa wajen parking yayi kusa da Benz da Adamu ke ciki, bude gaban motan yayi yafito ahankali wanan karan yana sanye da kayan yan sanda Rolex din dake daure a hannunshi yakalla shidda saura, sanan yazaga zuwa boot din jeep din yabude keken guragu yaciro ya ijiye ya maida boot din yarufe sanan yadawo bangaren baya yabude motan wata kyakkyawan tsohuwa ce fara sol kaman balarabiya zaune abayan tasaka Riga da zani irin na tsofaffi anmai dinkin Bubu kafafunta da hannayenta sunsha lalli, hannunshi yamikamata batare dayace mata uppan ba hararanshi tayi tana kama hannun nashi tamike tsaye da kyar tana masifa tace “idan kaga dama kai gaba dani dagayau har jibi Ice cream dai saika kaini nasaiwa jikoki na ja’irin yaro kawai” ko kala baice mata ba da taimakonshi ya daurata akan keken sanan yamaida kofan bayan yarufe da karfi tace “kama balla motan baban karfi, ubanka zai sayamin wata Alhamdulilah Allah yamai arziki rufin asiri danasha takaici” cikeda masifa yace “wlh Goggo in baki shiru ba anan zan barki na shiga ciki nasayo” wani kalan murmushi tayi tamaka bakinta tace “yo ai nadauka gaba kake dani to muje nadena” dan murmushi kadan kawai yayi sanan yashiga turata zuwa gaban entrace din dakenan divided into 3, staircase ne gefe da gefe sai tsakiya a bit sloppy floor dazaka haura ka shiga cikin shagon, daidai lokacin security na budewa Khairy kofa tana fitowa rikeda paper bag na ice cream din dakuma handbag dinta rataye a shoulder dinta, saiga wasu yara su biyu maza dabazasu wuce 8yrs ba suna guje guje kowanne rikeda ice cream dinshi dayan kawai ya mamayi brother shi ya fizge ice cream din hakan yasa brother yay ihu yabi dan uwanshi da gudu Khairy dabude mata kofa kenan tasa kafa tafito zata fara sauka daga staircase din kawai yaran suka fito suka mugun bangajeta dayasa ita kanta tasaki wani irin ihu kafanta ya gicce abunku da tiles kawai ta kifo zata fadi da mugun sauri Gwaggo tace “Subhanallahi” dawani irin sauri yasaki wheelchair Gwaggo daidai kanta zai daki dakaIUlin stairs din…
[6/16, 7:56 PM] +234 701 275 3212: 💫 ALKAWARIN ZUCIYA 💫


✍🏻 M SHAKUR

Dan magana da M shakur
wa.me/+2347012181461


1️⃣5️⃣


Yasa hannunshi daya awajen kanta ya daki tafin hannunshi bayan hannunshi yadaki stairs din sanan yakai dayan hannunshi yakama waist dinta yajuyo da ita hakan yasa ta mirgino side tafado jikinshi.

Daga yaran, security, iyayensu dasuka biyosu da sauri, Gwoggo dakekan wheelchair duk sandarewa sukai danba karamin faduwa zatayi ba inda Allah bai kiyaye ba, yanda yakeji yanda take nishi a hannunshi yasa ahankali yazare hannunshi daga waist dinta gently yakai hannun kan fuskanta yadago fuskanta yana kallon face dinta yanda ta kankame idanunta gam gam cikeda tsoro pink lips dinta nawani irin shaking dayasa dimples dinta na lotsawa tana nishi sama sama dayake jinshi akan hannunshi, murya chan kasan makoshi while looking into her face yace “are you okay”? Muryan dataji yadaki dodon kunnenta yasa kadan kadan tashiga bude idanunta danta gasgata abinda taji kafin tabude su tass tadaura white fararen idanun nan nata manya manya dasukenan kaman an wanke da madara tadaura su akan fuskanshi, jitayi numfashinta ya makale somewhere in her throat ganin fuskanta dab da nashi yana kallonta as if he’s trying to check something, yatsanshi yakai saitin nose nata jin bata numfashi kawai takafeshi da manyan white eyes nata yasa dasauri yakalli security man din yanunamai jakanta dake kasa chan yace “give me her bag” dasauri yakawo jakanta yamikamai juye jakan yayi kasa inhaler ta yafado dasauri ya dauka yacire marfin yakai bakinta ahankali yace “breathe in Ummulkhair!” Wani irin bugawa zuciyanta yayi jin yanda yakira sunanta kaman sunanta dayakira ne yay reviving nata batasan lokacin datawani saki numfashinta data rikeshi amakogoronta ba yafito mai kara sanan taja inhaler, zagayesu mutane sukayi barinma parent din yaran da jikinsu yay sanyi ganin Yarinyar da yaranta suka ture is even asmatic, ganin yanda mutane suka cika kansu duk ana kallonta yasa ahankali takai hannunta batare data kalle fuskanshi ba tana kokarin karban inhaler daya rikemata abaki, ganin haka yasa gently yasakin mata ahankali yaran dasuke tsaye sukace “Anty sorry” dan murmushi tayi tana cire inhaler daga bakinta duk dasauri tana kokarin tashi tsaye, tsugunnawa Maman yaran tayi tace “rest a bit please” tai maganan tana maida mata kayan jakanta back aciki tareda daukan mata jakan ice cream dinta da sauri ta mike tsaye tana karban abubuwan ta daga hannun matan tace “I am okay thank u” Gwaggo dake kallonta tace “sannu kinji inane gidanku mukaiki nida jikana” dasauri tace “direbana na nan nagode Ma” sanan tawuce da sauri hartana tuntube tai wajen motansu da Adamu ya kwantar da kujera yanata hira awaya abinshi batare dayamasan meke faruwaba, saida yaga tabude motan ta shiga sanan yakoma wajen Gwaggo yatura keken sukai ciki tace “ohh yara da rashin wayau Hydar, inda badadan kaiba da sunja Yar yarinyar nan tafasa goshi wlh, itama yarinyar uwa batacin abinci yoo nakema wanan maganan haka rainon indomie ce daga ganinta, ace daga yan yara sun bangaje budurwan yarinya haka kawai sai faduwa uwa lagwani, ace yara suci tuwo suki duk irinku ne ai gashinan kaga yara sun taso basu da karfi ko kadan, kai Allah dai ya wadaran naka subaci, Allah dai yasa kai aure ka haihu, wlh tun yaranka na wata biyu zan fara basu lafiyayyen tuwo da miyan kuka dataji daddawa” hararanta yayi baima cemata komiba ya sassayi ice cream din sanan suka fito tace “minene Wanan abin danaga kanata matsamata abaki” kin kulata yayi yasa ta amota ya maidata gida sanan yafito yatafi aiki.



Har suka shigo anguwan su badaidai takeba yau sau uku kenan tana ganin mutumin nan, saida suka shigo gida tukunna sanan taji wani kalan dadi, parking sukayi sanan tafito dasauri tana kwaso kayayyakin ta tana kwalama Mama kira. “Mamaaaa! Mama nadawo” daga Mama, Baba, Baffa da yayyinta da Hafiz duk suna zaune a falo dan basu dade da dawowa daga asibiti ba babu wanda yama iya wani kwakkwaran motsi, ita tsabagen murna batama lura da Karin mota kan tagidansu ba tai hanyar flat dinsu tana shouting Mama. “Mama nayomiki tsaraba yau nasayo miki ice cream kuma best flavor naki mint ban miki adding any thing ba ayanda kike sonshi plane” tai maganan tana bude kofan falo tana shiga tana kiran Mama. “Maaaam……” kasa karasa kiran Mama tayi ganin mutane a falon ga Mama zaune kusada Baba tana kallonta tana murmushi, hararanta Hafiz yayi yayi yace “inda ace ke kadai keda Mama aduniyan nan Khairy da munsha takaici” cikeda wasa Baffa yace “kagamin d’a kai kanama namiji ka more taka Maman balle ita mace kuma auta, ina tsaraban dakika kawoma Maman bazaki zo kibata ba kin wani tsaya awajen” akunyace takaraso cikin dakin wani irin rungume Mama tayi tana murmushi akunyace ganin duk ana kallonta yasa tadaurama Mama paper bag na ice cream din akan jikinta akunyace ta sauko dagakan jikinta tace “Baffa ina wuni” murmushi yayi yace “diyar Mamanta ya makaranta” ahankali tace “fine” sanan takalli Hafiz tace “Ya Hafiz ina yini ya baby kuma, dan Allah ya Hafiz kasa mata sunana” dasauri yazaro idanu yace “waaaa niii rufamin asiri Khairy sokike y’ata tazama fitinanna irinki” dariya aka hauyi adakin ahankali Khairy tace “Baffa kaga Ya Hafiz ko” kafin Baffa yay magana Baba yace “karya yayi to Khairiya” turo baki tayi kaman zatai kuka Baffa yace “sharesu Yar albarka, sun lashe basusan baiwan dake tattare da sunan ki bane saisa suke magana ahaka” wani kalan murmushi tayi tace “yauwa Baffa” sanan tajuyo takalli Mama tace “Mama kin sha maganin kan yadena miki ciwo muji” takai hannunta tana taba goshin Mama with so much care, gyadamata kai Mama tayi tace “yadena, cikani maza tashi kai ice cream din kisa a fridge kije kiyi wanka kiyi salla idan bakiyi a school ba saiki sauko kici abinshi” gyadama Mama kai tayi sanan ta tashi tana kallon yayyinta dataga sunyi wani iri harzata wuce tace “Ya Manaf kungaji ne haka naga kunyi wani iri, Ya Maheer idanunka sunyi ja kaman kayi kuka” hararanta yayi hakan yasa ta murgudamai baki tawuce abinta sama itama, dayake yana takanshi dayaji ciwon Mama yatashi yau baima biyemata ba!

[6/16, 7:56 PM] +234 701 275 3212: 1️⃣6️⃣

Free page
😉 enjoy

Kofan dakinta tabude ahankali ta shiga tanabin dakin da kallo yanda ko’ina tsaf tsaf an gyaramata sai kamshi dakin yake, shiga ciki tayi sanan tamaida kofan tarufe kafin awani irin gajiye cikeda sanyin jiki tasaki handbag dinta akasan dakin tafada kan gadon batare data cire takalmin kafanta ba tawani kalan kankame jikinta tanajin wani irin sanyi na shiga jikinta, she don’t even know why amman hakanan fuskan police man dinan take gani a idanunta muryan shi namata yawo a kunne da kanta gabaki daya yana kiran sunanta Ummulkhair breathe in, runtse idanunta tayi gam gam tana feeling yanda bones nata ke cringing to each other tana ganin fuskanshi namata yawo a idanu kafin idanunta suna hasko lips dinshi wani kalan ihu tayi. “Ahhhh stop!” dasauri ta tashi zaune tana wurwurga kafafunta cikeda damuwa tace “Stopppp noooo what’s wrong with me”? Wani irin zabura tayi ta tashi tsaye kawai tawuce dasauri tafada bathroom, wanka tayo sanan tafito daure da towel tana tunanin yaushe Mama zatasa amata Kitso dan gashin ya isheta daga tsifemata jiya, wani simple dogon Riga tasaka sanan tasaka hijabi tai salla tana idarwa tafito falo tawuce ganin duk basu tasan sun tafi masallaci sallan magrib, dinning tawuce zama tayi tana bubbude kula rice tazuba kadan sanan tasa nama tafaraci saida tacinye sanan takai plate din kitchen kafin tafito ahankali tai stairs, knocking dakin Mama tayi sanan tabude kofan ganin Mama akan gado ta lullube da bargo yasa tashigo da sauri tace “Mama menene” wani kalan kallo Mama tamata tace “bacci zanyi nagaji” hawa gadon tayi tana kallon fuskan Mama tace “Mama kibari ayi isha’i tukunna nima bacci nakeji” gyadamata kai Mama tayi tana kallon gashinta tace “weekend zakiyi kitso tunda ke kin dawo yarinya daga tsife miki kai kanki yadawo kaman na mahaukaciya” gyadama Mama kai tayi tana hamma, ganin haka yasa Mama tace “Oya tashi kije kiyi sallan to gashinan ana kira saiki kwanta tunda kin gaji, kinmasha ice cream din” girgizakai tayi agajiye tace “gobe zan sha Mama nagaji, gud night world best” night my baby girl, Mama tai maganan tana binta da kallo wucewa tayi tafice daga dakin tana salla ta kallabi tahau gado sai bacci.


Da asuba tana tashi salla tafarayi sanan takoma bacci dan yau batada lectures sai 10 and she wants to sleep sosai cus kanta yay clearing tadena all this banzayen tunanin nan datakeyi.
Karan wayanta yatadata by 9, da kyar ta iya bude idanunta ta kalli wayan rabon data danna wayanta hartama manta one thing dabai dameta aduniya kenan ba waya, she’s not just a phone person, itadai barta da physical surutu, yawo rawa haaba anan ake samin Khairy, hannunta tamika da kyar tadauko wayan ganin Besty yasa taji duk wani kalan bacci datakeji yafice daga idanunta dasauri tai picking call din tace “Iyye su Besty Amarya ai nadauka kin manta dani yar rainin hankali saisa na shareki banma nemekiba” kuka Besty tasaki awaya dayasa dasauri ta tashi zaune adan tsorace tace “ke menene Besty, what happen? Kinasa inajin tsoro why are u crying?” Cikin wani kalan muryan ban tausayi Besty tace “Khairy wlh nafasa auren mutumin nan kasheni zaiyi tun ranan da aka kawoni abu daya ake har yau nagaji” dan ware idanu Khairy tayi tanajin maganan wani banbaram itadai barta da rashin ji but duk wani harka na maganan banza da Iskanci bata aciki, adan kunyace cikedajin nauyin magannan tace “to ba ance ana sabawa ba” tai dan shiru saikuma ta turo baki tace “idan yaki kihadashi da Maman ku” wani gajeren tsaki Besty taja cikeda masifa kaman tabugama Khairy dundu tace “I don’t even know why I called u you are crazy Khairy, da zancen party ake da yanzu kingama tsara komi, lemme call Amal” tana maganan ta katse wayan, hararan wayan Khairy tayi ta ijiye saikuma chan kaman ta tuna wani abu wayan ta dauka dailing number Besty tayi back ringing daya tadaga, ahankali tace “sorry Besty kinji I seriously don’t know what to tell u or how to advice u” cikin muryan damuwa Besty tace “wai Khairy when will you learn all this stuff eh, u are just hella wired Umma, u are just leaving life kaman bamace ba gashi duk munata aure Khairy keko saurayi bakida shi sai wanan Wizzy dake binki” hararanta Khairy tayi tace “nacemiki kidena hadani da wanan yaron” dan dariya Besty tayi kaman ba itane mai kuka yanzun nan ba tace “naji nadena, yanzu dai kinyi wani saurayin”? Dan shiru tayi kaman mai tunani harta bude baki zatai magana saikuma tai shiru hakan yasa Besty tace “ohhh wowww, Khairy this is something new, tell me who is he? Dan tunda nake dake duk aka miki tambayan saurayi direct kike cema mutum baki dashi wanan dakika kasa magana tell me wayeshi” dan murmushi tayi tayi dan juyi akan gado tana dan lumshe ido saikuma ahankali tace “wlh Besty banda kowa kawaidai wani Police man ne naketa haduwa dashi this days amman ko magana bamayi kawai dai he always saves me from trouble ne I don’t know if that means anything amma dai ba soyayya muke ba ko magana ma bamayi” ahankali akuma natse Besty tace “ohh my Goddd! Khairy kinji yanda harwani natsuwa kikayi kina bani labarin police man dinnan kuwa, My world Khairy you love me! Wlh….” Dan yatsine fuska Khairy tayi dasauri tace “stop it! Mutumin dabanma sanshi ba, yaushe zaki dawo school nidai” dariya Besty tayi sosai tace “tunda u are avoiding maganan ai ba matsala, this weekend zai dawo dani but every weekend zai dinga zuwa” gyadamata kai Khairy tayi tace “sai kinzo bye” tai maganan tana katse wayan da sauri dan tasan Besty bazata taba hakura da topic dinan ba, ijiye wayan tayi ahankali sanan ta mirgina zuwa dayan gefen gadon tana tunani.


Ajiyan zuciya tasauke sanan ta tashi tasauka daga kan gadon zatai bathroom wayanta yashiga kuka cikeda masifa tadawo tace “mekuma kike sake kirana eh” wayan tadauka ganin Glory yasa tai picking wayan takai kunne kafinma tai magana Glory tace “hello fine girl, melanin goddest, pop skin with those sexy milky eyes” dan dariya tayi, Glory is her friend masters ita take a school nasu ta girmeta far far amman tana bala’in son kawance da Khairy, dan murmushi Khairy tayi tace “Hey! Where have u been i haven’t seen u in school this days” dan dariya tayi tace “I travel naje PH chan gida, Khairy u don’t know I am angry with u ba” dasauri Khairy tace “what happen? Why” kaman zatai kuka tace “today is my birthday Khairy” Adan kunyace Khairy tace “ohhh Glory, sorryy happy birthday darling” dasauri Glory tace “come to my party and wish me there, zamuyi a jabi lake mall a cikin jirgin ruwa, dress code is red 4pm sharp” wani kalan juya idanu Khairy tayi tace “ohh okay then bye see u later” ta katse wayan sanan tawuce bayi da gudu wanka tayi agurguje sanan tafito cikin wata doguwan rigan atampa ta shirya tafito tana tunanin yanda zatai planning zuwa party zata dawo gida by 2 wuraren 5 saita tafi tadawo 6.

Tea kawai tasha sanan tawuce school dan tayCi latti sosai.
[6/16, 7:56 PM] +234 701 275 3212: 1️⃣7️⃣


Free page
Ahankali yake tuki ganin ya shigo cikin estate dinsu, saida yakarasa gaban wani dankareren gate sanan ya danna horn, budemai gate da akayi yasa yaja motan zuwa cikin gidan dakeda bala’in kyau kuma babban gaske ga flowers dasuka karama gidan kyau sosai, parking yayi abangaren parking sanan yakashe motan yana kallon cikin gidan dababu kowa sai gardener dinsu daketa yayyanke flowers yana gyara su, yakai kusan 1min cikakke zaune a motan yay shiru sanan ahankali yabude kofar motan yafito yamaida kofan yarufe sanan yafara tafiya dai dai yawuce zuwa babban flat dakenan shine first flat a gidan, bude kofa yayi ahankali tareda sallama chan ciki sanan yashiga babban falon da babu kowa ciki, falon ya bala’in hadu yaji furnitures, saikuma dan kara dayakeji a kitchen da alamu mai aikice ke wanke wanke, juyawa yayi zai fice kaman daga sama yaji ankirashi. “Aliyu” dan juyoda kanshi yayi ya waigo, wata matace doguwa mai jiki fara kal da ita taci gayu da sarkan gwal a wuyanta wacce bazata wuce 40 ba tana sanye da lace ja da baki ke saukowa daga benen, kallo daya yamata yadauke kai yace “barka da rana Mami” dan murmushi matan tayi sanan takalli agogo bangon falon ganin is just 11 yasa tace “Lafiya kadawo gida ware haka Aliyu”? Batare daya kalletaba ahankali yace “lpy lau Mami” gyadamai kai tayi tana kallonshi still tace “tom shikenan, mezakaci a aiko maka dashi”? Batare daya kalleta ba har lokacin yajuya yace “zanci abinci wajen Gwaggo” yana maganan yajuya yafice tareda rufo kofan binshi da kallo tayi ta jikin window falon har saida yay side din Kaka yabace mata daga gani sanan tasami kujera ta zauna tanadan karkada kafa tunda take bata taba ganin wanda uniform na police kemai kyau kaman Aliyu ba, haryau tarasa maisa

Please Login or Register in order to submit comment