Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

din motan kasa tana kallonshi, dukowa yayi yana kallon fuskanta kafin ahankali yace “thanks for the gift” gyadamai kai tayi tana juyarda kanta ganin kallon dayake mata, murya chan kasa ta yanda dagashi sai ita zasu iyajin maganan dasuke ko Adamu bazai iyaji ba yace “I love you so very much My kunya budurwa” hannu tasa ta tureshi yadan koma baya yace “stop it, Adamu muje” gwalo tamai yana kallonta yana murmushi suka wuce sanan tamai bye, bye shima yamata kafin yawuce motanshi zama yayi sanan yabude jakan data kawomai da tuntuni ke hannunshi yana kallon congratulations din da aka rubuta sanan yadaye ledan yabude kwalin agogon murmushi yayi sosai agogon is very classic he loves everything about it sanan yabude kwalin glasses din, murmushi yasakeyi shi kadai yasan yanda yakeson Ummulkhair danko ita bata saniba, maida komi yayi cikin jakan ya ijiye sanan yadauki wayanshi text yamata.
“I love my gifts wholeheartedly, Nagode Miss Khairy, Aliyu’s Pickle❤️” ijiye wayan yayi amota yawuce yafita dan zuwa daukosu Gwaggo su wuce sitafi gida.



Harsuka gama exam aka basu one week break yakare bataje gidansu tasan zata koma but batajin she’s ready ba, tana bala’in jin dadin zama da Mom, ga Batool ga Zara’u she’s not alone anan bataso takoma gidansu tadawo all alone kuma.
Ita gidan nan har mantawa da Ammi take bamatason abinda zaisa Mom ta tuna ta aikata side din gaida Ammi wani zubin ko Mom ta turata waje zataje tadade sanan tadawo tace taje. Itada Aliyu ko soyayyan su kawai gaba takeci, yau one eeek kenan basu hadu ba sabida yabi Abban shi suje lagos yin wani aiki amman cikin satin nan da aka shiga yace mata zai dawo.


Fadowa kanta Batool tayi wuraren 9 nasafe tace “ba dole ki kasa tashi ba yarinya baki barina bacci sabida wani soyayya da Aliyu” tureta Khairy tayi tace “Wlh zansa yayi arresting naki idan baki dena damuna ba kema banaki soyayyan kike da Umar ba” dariya Batool tayi tace “wai this week ma baxaki je school ba” “lectures is not yet serious leave me alone Batool please I am sleepy” tai maganan tanajan bargo zata rufe kanta back fizge bargon Batool tayi hakan yasa tawani tazo ihu Batool tayi tafice dagudu itama tabiyota tace “wlh saikin sani” dariya Batool keyi tana gudu tana sauka daga stairs itama tana binta Mom dake zaune afalon sama tace “kuyi jakanci da kyau wlh duk wacce tafadi cikinku bazan bata magani ba” kaman badasu Mom keyi ba sukai falo Batool na dariya tana gudu tace “ko banza natadake gashinan ma ina sAki morning workout” kulewa Khairy tayi tayo kanta ganin tana neman kamota yasa Batool tai wani uban ihu tabude kofa tafice waje Khairy tabita aguje itama sukai hanyar bayan gidansu suna guje guje kaman yara Khairy taki hakura Batool taki dena mata dariya tana gudu sukai backyard da akai shanya na zannuwan gado da labulaye a igiyoyin hakan yasa abin yazaman musu kaman hide and sick, dazaran Khairy taga alamun mutum zata daga kayan da aka shanya saitaga babu Batool saitai tsaki, hango alamun mutum datayi abayan wani thick zanin gado yasa ahankali sadaf sadaf taje wajen saida taje daidai wajen sanan tasa hannunta takama hannun Batool din gam tana wani irin murna tana dariya tace “ubanwa nakama, nikike tsokana ko wlh yau saikin sani Batool” tawani finciko hannunta, jin ko alamun motsi hannun da tarike baiyiba yasa taji wani kalan tsoro daidai nan Batool tabude tsakiyan wani zanin gado da aka shanya tafito dukta jike takalli Khairy tace “ke dawa kike magana gani nan fa” danjuyowa Khairy tayi takalli Batool data fito ta tsaya ruwa yajijjika kanta da rigan baccin jikinta sanan ahankali tajuyo da kanta kalli gabanta sanan gently hannunta harwani irin rawa yake tashiga sakin hannun data rike Adan tsorace jitayi an kama hannun nata gam kafin tai motsi taji anwani fincikota zanin gadon yawani damke fuskanta da jikinta taji wani irin sanyi sabida lema lema dake jikin zanin gadon igiyan, sai chan taji an yaye zanin gadon ankara fizgota tashigo wajen wani irin mugun faduwa gabanta yayi ganin Ya Zayn dagashi saiwani gajeren towel fari a waist dinshi yana gaban pipe din dake supplying ruwa to his flat daya fito ya kunna dan baisan waya kashe ba, wani irin faduwa gabanta yashiga yi dan ita bata taba ganin namiji hakaba bakaya kwata kwara kosu Yayyinta bata ganin su haka, kauda kanta tayi gefe dasauri bakinta har rawa yake tace “uhmmmm so…..sor….” Kasa karasa maganan tayi ganin Batool datayi tayaye zanin gadon ta shigo wajen da sauri itama ganin Zayn yasa atsorace tace “Ya Zayn laaaaaa yaushe kadawo good morning” wani mugun kallo yamata sanan yakalli Khairy from head to toe tana sanye dawani pink gown na bacci mai gajeren hannu daya tsayamata iya guwiwa kanta babu dan kwali sai lafiyayyen kitson dake kanta, ga lema lema ajikin rigan na makalewa da zanin gadon yayi ajikinta lokacin daya fizgota big boobs dinta tsaye warrr babu any bra aciki ko vex, jitayi wani kunya ya shige ta ga tsigan jikinta natashi at the same time dayasa taji jikinta yadan soma rawa. Cikin wani irin kakkausan murya yace “idan kinsan bazaki natsu ba kibar gidan nan, I hate mutum mara natsuwa, bar nan wajDen!”


Wanan Littafin na kudi ne karki karanta batare dakin biyaba kika karanta min littafi ban yafeba.

wa.me/+2347012181461
To chat me up on watsapp

This novel is 1k
Pay 1k into 3107021073 aisha Muhammad saiki turomin evidence of payment ta watsapp number na 07012181461
Thank u❤️



Sakin hannunta yayi dawani irin sauri tajuya gabanta nafaduwa dum dum Batool sai hadiye dariyanta take ganin yanda duk Khairy ta birkice sanan suka wuce suka shiga flat dinsu, suna shiga Batool tafada kan kujera tana dariya tana kallon Khairy datai kuriii jikinta har lokacin bai dawo daidai ba, kallonsu Mom data fito daga kitchen tayi tace “ya akayi” cikeda dariya Batool tace “Mom Khairy taje takankame Ya Zayn tadauka nine saura kiris yamaketa bakiga yanda dukta rude” hararan Batool Mom tayi tace “wlh daya makemin mu danama mai godiya, yara daga tashinku kunbi gida kuna guje guje ko kayan bacci baku cireba ku wuce kuje kuyi wanka kuchanza kaya kafin na sassaba muku” Khairy tafara gaba kafin Batool tabita abaya, hartahau stairs sanan tajuyo takalli Mom tace “Mom yaushe Ya Zayn yadawo”? Batare da Mom takalleta ba tace “around 2 nadare ya shigo gidan nan kuna bacci lokacin” wani irin tsalle Batool tayi tace “yanzun nan bai wanka zanje nasame shi Mom yabani kudin ankon Na’ima” “kinfi kusa” Mom tai maganan tana shiga kitchen abinta itakuma Batool tajuya tai dakinsu, shiga tayi ganin babu Khairy afalon yasa tafada kan gado tana jiranta tafito daga wankan.

Fitowa Khairy tayi daure da towel dinta pink akirji ko kallon Batool din batayiba tawuce wajen wardrobe dinsu, tashi Batool tayi zaune tana kallonta tace “towai fushi kikedani danna tadaki daga bacci sorry to” juyowa tayi ta balla mata harara tace “ni gidanmu zan ma koma Wanan da wanchan Yayan naku yafaramin gorin gida daga ganina bazan dauka ba” dasauri Batool ta tashi dan idan akwai abinda ta tsana shine taji Khairy tace zata tafi gidansu, dasauri ta tsaya kusada Khairy dake shafa mai ahankali tace “ke dalla don’t mind Ya Zayn, wlh Ya Zayn nada bala’in kirki barshi dai da iyaji da kanshi amman yanada kirki kinga duk wulakanci Ammi baya biyemata wlh, Bakiga yana shigowa nan ya gaida Mom ba dudda Ammi bataso shi baruwan shi kuma yana sonmu, yana bani kudi koban tambayeshi ba hakama Zara’u, har dakinshi tana zuwa taitamai surutu wlh baida wulakanci, dan Allah karki kara cewa zaki tafi” kwafa tayi tajuya mata baya tanasa bra sanan tajuyo binta da kallo Batool tayi tace “ke Khairy ai wanan Bra yamiki kadan, kinada nono wlh Khairy kaman muyi musanye” dan tsaki tayi tadau riganta tana sawa, Batool cikeda tsokana tace “iyye su Ya Aliyu zai more” dawani irin sauri tajuyo zata dakamata duka ihu Batool tayi tawuce dagudu tafada bayi, dan murmushi tayi tana kallon kanta a madubi saikuma akunyace tamake kafada tace “ni bazan ma taba bari yaganni bama rigaba balle ma yaganni” karasa shiryawa tayi abinta cikin wani plain dogon rigan atampa ja batare data daura dan kwali ba tafito zuwa saukowa tayi kasa Mom ce kadai tanashan tea a dinning dayaji kayan kamshi ganinta yasa tace “ko kefa jibi yanda kikai kyau” dan murmushi tayi Mom tace “oya zoki zauna kiyi breakfast” karasowa wajen tayi tace “Mom ni indomie zandafa” baki Mom ta tabe tace “Allah dai yay wadaran naka yabaci, nidai kinga tafiyata bari naje natado Baban ku daga bacci, yadan kwanta shima yazo yay kari” kitchen tawuce itakuma Mom tai sama abinta.


Wani karamin tukunya tadauko sanan tashiga store dinsu tadauko indomie daya da kwai guda daya tafito sanan ta tara ruwa tukunna gas don tadaura sanan tawanke kwan a tap tazo tasaka a ruwan pot din tarufe pot din sanan takoma store, albasa tadauka awajen, wani black wukan datagani ijiye tunkwal shikadai a store din tadauko tace “hala Mom ta manta da wukan nan a store ne baga wajen wukake duk suna nan ba” takalli cabinet din wukansu wucewa gaban tap tayi tadauraye wukan sanan tasa wukan ta yanke kan albasan sanan tabare albasan tass, kafin tasa wukan taraba albasan biyu ta ijiye rabi akasa sanan tadauki rabi daya tasa wukan tafara yankawa cirrrr wukan yawani irin yanketa a tafin hannu lafiyayyen yanka dayasa batasan lokacin data saki wani azababben ihu ba daga wukan har albasan nafadi akasa daidai lokacin Zayn na shigowa falon yana sanye da 3quater dawata faran riga, jin ihu acikin din Mom yasa yay kitchen din dasauri ganin Khairy tana yarfe hannunta da jini ke tsayaya ya diddiga ko’ina a kitchen din tana ihu tana kuka ga wuka da albasa akasan kitchen din yasa yay kitchen din da sauri hannunshi yasa ya karbe hannun nata data yanke dasauri yay tap da ita kunna tap din yayi ya tare hannun kasan ruwa wani kalan fashewa da kuka tayi zata kwace hannun amma yaki yana wanke jinin daidai lokacin daga Mom har Baffa dasukaji ihunta sun shigo kitchen din dasauri wukanda Mom tagani akasa yasa tai salati. “Innalillahi waya fito da wukan daga store” cire hannunta Zayn yayi daga tap but still jini zuba yake ganin haka yasa Baffa yace “kawo first aid kit dinan Wife” fita Mom tayi daga kitchen din, ahankali Zayn dake rikeda hannun yakalli fuskanta yanda take kuka da yanda har gumi yafeso agoshinta dan ita anytime she’s stress or in pain tuni zakaga gumi yaketo mata a goshi, yanda gumi yasa gashin gaban goshinta ya kwanta ga hawaye na gangarowa daga idanunta datake gogewa da bayan dayan normal hannunta idanunta duka suna kan hannun da jini kefitowa dagakai yasa yaji beat din heart dinshi na raguwa, ahankali kaman wanda wani abu ke controlling yakai hannun saitin bakinshi kafin ahankali yadaura bakinshi kan hannun wajen yankan yanashan jinin yana kallon fuskanta, wani irin sanyi taji bakinshi yayi akan yankan kaman yadaura ice akai shiru yadena mata zafin dayake dawani irin sauri takalleshi tana ware manyan idanunta duk wani hawaye datakeyi ya tsaya chak Baffa dake bayansu tsaye ya tsaya chak yana kallonsu daidai nan kuma Mom tashigo dagudu tace “gashinan Zayn” firgigit! Kaman wanda yadawo hayyacin shi, bakinshi yazare dagakan ciwon, sanan yana rikeda hannun nata yakarbi spirit din da Mom kebashi yazuba mata akan hannun wani kalan ihu tayi dasauri yashiga hura mata hannun da iskan bakinshi hakan yasa tai shiru, auduga yakarba daga hannun Mom yadaura kan hannun sanan yasa plasta akai kafin ahankali yakalli Baffa yace “Abba akaita tayi tatanus injection” Dawani irin sauri Khairy tace “Baffa no dan Allah dan Allah Baffa kar Amin allura” dan dariya Baffa tayi yace “Khairy Khairy, ai Khairy tun tana yarinya batasan allura wuce kije ki zauna wai mema tazo yi a kitchen din” Mom tace “wai indomie zataci ga abincin normal mutane amman Khairy indomie zataci wuce tafi nadafa miki, wukan nan sabida yanda nasan kaifinshi yasa naboyeshi a store ko ya akayi tafito dashi oho” Mom tai maganan tana daukan wukan itakuma ahankali tawuce tafita hannun namata zafi, Baffa yakalli Zayn dayadan saci kallonta yace “let’s go Son, yaushe kashigo” dan murmushi yayi yace “yanzun nan nazo gaida Mom ne shine naji yarinyar chan na ihu kaman bera”



Juyowa dasauri Khairy tayi jin ita yake kwatantawa da bera, mugun kallo Baffa yamai yace “karka kara kwatantamin y’a da bera” zama tayi a dinning ahankali Baffa da Zayn suka wuce falo suka zauna akan kujera.
Baffa yace “yanzu tunda kagama komi yaushe zaka fara company and start managing everything, I want to retire nima nahuta” anatse yace “Abba bari nadan huta” atsanake Baffa yace “I am giving you just 2 weeks to rest Zayn am I clear” gyadama Baffa kai yayi cikeda girmamawa, saikuma chan yamike tsaye ahankali yace “bari naje wajen Ammi” gyadamai kai Baffa yayi yace “okay yaushe zakaje gaida Baffan naka” dan ware idanu Khairy tayi jin ana maganan gidansu, ahankali Zayn yace “anjima da yamma” ganin yanda Khairy ke kallonsu yasa yace “zakije” dasauri ta gyadamai kai tana murmushi kallon Zayn Baffa yayi yace “to kaje da Khairy idan zaka tafi” dasauri daga Zayn din har Khairy suka kalli juna dan bata taba tunanin Baffa saice Zayn yaje da ita ba ita tazaci kawai zaice taje idan ta shirya Adamu yatafi da ita, wani kalan mugun kallo Zayn yamata sanan yawuce yafita daga dakin.


[6/20, 10:24 PM] +234 810 499 3160: DUK WACCE TAKARANTA MIN LITTAFIN NAN BATARE DATA BIYABA BAN YAFEBA




Dakin Ammin shi yawuce, tana zaune as usual cikin shiga na alfarma kaman matan shugaban kasan Nigeria waya a kunnenta tana waya, kan stool na gabanta kuma fruits ne yankakku da spoon aciki da alamu sha take sai wayan ya tsayar da ita, zama yayi kusada ita sanan yadauki bowl na fruit din nata yafara sha abinshi wayanshi yaciro yana dubawa miss calls yagani like 9 daga number daya shiru yayi yanaji ranshi na baci baisan ya akayi Faisal yabama that Aisha girl number shi ba, bayan yabar Abuja lokacin da Mama tarasu daya koma baima sauka agidan ba hotel yakoma da zama dan he’s tired of yanda yarinyar keep stalking him school gida kaman zata haukace akanshi, he just had sex with once which he paid which infact ma bashi yama nemeta ba, Wanan halin datakeyi yasa kwata kwata bayama neman yaran naija, all babes dinshi achan turawa ne cus sunsan menene sex for fun not sex for attachment, dan tsaki yaja ganin tasake kiranshi ya ijiye wayan Ammi datagama call tace “kai lafiya kana neman fasa wayanka” ahankali yace “Ammi damuna wata mayyan yarinya take ne wlh” dan murmushi Ammi tayi tace “kai haka kakema yammata wulakanci ahaka zaka sami matan kayi aure, danni wlh tasaka zanyi agaba Kwanan nan zakai aure dan bazan barka hakama yaro kanada 36 kana neman 37 ace ba mata ina, akwai ma wata yarinyar kawata danakeso kaje kadubo bakaga yarinyar ba kaman baturiya” ijiye bowl na fruits din yayi yace “Ammi please don’t start niba yaro bane dazaki dinga nemomin mata ba I will get married but lemme take my time baaa rushing ayi aure, I still young bawai tsufa nayiba” tunda yake maganan Ammi ke kallonshi tace “wai kai Son na lura bamaka son Auren nan gabaki daya” murmushi yayi ya kwanta akan kujeran yana daura kanshi kan cinyanta ashagwabe yace “Ammi kaina kaikayi sosamin” hannu tasa cikin soft gashin nashi tana sosamai scalp tace “daga ina kake dan na aika dakinka bakanan” ahankali yana lumshe idanu yace “dakin Mom” tsayarda susan tayi tace “akanme zakaje gaida matan nan ita yaran datake zama dasu bata taba turosu sun shigo sun gaidani ba barinma Wanan mai idanun mujiyan Khairy” shiru yayi yana jinta baice komiba yace “ita tanaso yarana sudinga girmamata ita batasa nata sunyi hakaba” murya chan kasa yace “common Ammi nowww, yaran gidan nan waye baya tsoronki masifanki yasa babu wanda keso yashigo side dinki ya gaidake” ture kanshi tayi dagakan cinyanta tace “ni uwarka kake kira masifaffiya eh” maida kanshi yayi kan cinyanta yace “Ammi ok bazan kara zuwa ba cigaba damin bacci nakeji wlh” yanda takeson Zayn yasa shi kadaine bata iyawa masifa da wanine yau daya shiga uku, cigaba da sosamai kan tayi baidauki cikakken 4min ba yay bacci ahaka, ta tasashi gaba tana kallo ahaka Baffa yashigo side din yana kallonsu murmushi yayi yace “kin sangarta yaron nan dayawa wife” murmushi tayi tace “wai nan lallabashi nake yaje yadubo yar kawata idan tamai mu musu aure koya kagani dan wlh Alhaji na lura Zayn bayason yau aure at all” tunda tafara maganan Baffa yay gim yana kallonta, ganin yanda yayi yasa Ammi tace “tunanin me kake bakace komi ba” dan murmushi yayi yawuce sama sanan yace “idan bayaso karki takuramai” binshi da kallo tayi dan reply din Baffa seems strange, dan tabe baki tayi tace “zaimaje kuma zai sota atoh”.




Wuraren 4 tana zaune adakinta tana waya da Aliyu da this is the third time yake kiranta tun bayan text datamishi dazu kan ta yanke duk yadamu harda cemata zai dawo tahanashi karya dawo dudda haka yaki yarda, turo kofa Batool tayi tawani fado gadon tace “Malama Ya Zayn yace kifito kuje” ahankali tace “kije kicemai nafasa zuwa” hararanta Batool tayi tace “wacece Yar aikenki ni kinga tafiyata wajen Mom bye” Aliyu dakejin maganan su yace “waye Zayn? Ina zaku”? Dan yatsine fuska tayi tace “gidan mu zani wajen Baba, Ya Zayn kamanta Babban yayanmu dandan Baffan mune” dan ijiyan zuciya taji yasauke kafin ahankali yace “go and tell him u are not going, gobe Adamu yakaiki” gyadamai kai tayi tace “tom bari naje” katse wayan tayi ta ijiye kan gado sanan taja wani gyalen Batool data jefar kan gado tadaura akanta dababu dan kwali tazura silipas tawuce tafita”.



Yana zaune cikin mota yakafa black sun glasses a idanunshi kaman wani makaho yana kallon kofar flat din Mom, sai uban kamshi yake yasaka wani gizna mai ruwan toka ajikinshi kaman wani ango, bude kofan flat din Mom da akayi yasa ya gyara zama yana kallon flat din da kyau, fitowa tayi babu komi a hannunta sanye dawani pink bathroom slippers da kumbunan kafanta sukai Zara zara sukai kyau aciki, har lokacin tana sanye da gown din dake jikinta dazu, hannunta dataji ciwo saiwani kaffa kaffa take dashi kaman Yar yarinya daga ganinta kasan bata sabajin ciwo ba and she hates getting injured, fuskanta looks so innocent and so beautiful tana wani irin glowing idanunta subyi fari kal kaman tana wankesu da hypo, pink lips dinta ko daganan zaune amota da bakin glass dinan a idanunshi yana iya ganinsu, gani yayi ta tsaya takalli waya nan tsuntsayen dayagani anan barandan Mom acikin cage dinsu masu kyau dankoshi dazu dazai shigo saida ta tsaya ya kalli tsuntsayen dan sunyi kyau, murmushi tayi sosai da he could see all side dimples nata na lotsawa jerin gajejjerun white baby teeth nata sun fito tana kallonsu sanan ta tashi tajuyo tana saukowa daga staircase din, ahankali yakai hannunshi yadaura kan kirjinshi dayaji every step datai taking yana jinshi a heart dinshi, tunda yake shi he never baitaba jin haka on anygirl ba, shi baima taba tsayawa yakalli any girl kaman yanda yakalli Khairy yauba, he don’t know mesa kawai he just like how innocent she is, dan iska always know dan uwanshi idan yaganshi but anytime yakalli Khairy he sees yarinya that doesn’t know anything, yayi nisa acikin tunanin yaji tai knocking glass din motarshi wani irin daure fuska yayi batare daya saukarda glass din kasa ba yay unlocking car din hakan yasa tabude kofar motan kallo daya tamai sanan tadan sunnar da kai ahankali tace “Ya Zayn baranj…..” “you don’t talk to me daga waje get in kafin nabata miki rai” jitayi ranta yabaci ahankali tashigo motan tazauna zata fara magana yace “rufemin kofan mota” rufe kofan motan tayi ahankali kafin tai magana yatada motan yaja ana budemai kofa dasauri tace “Ya Zayn bazani ba shine abinda nazo nafadama” batare daya kalleta ba yace “idan munkai kidawo” dan jim tayi ranta nabaci, batare daya kalleta ba yace “sit belt Miss” jan sit belt din tayi tasaka sanan ahankali tamaida kanta tana kallon hanya.


[6/20, 10:24 PM] +234 810 499 3160: 4️⃣1️⃣




Babu abinda ke tashi amotan sai cool music da AC dataji yamata yawa sanyi ma takeji, kiran wayanshi da aka farayi yasa wakan ya tsaya dan yay connecting wayan da motan ne, harya gama ringing bai daukaba saiga another call shima bai daukaba sai ga third call din again, ganin idan bai daukaba this girl bazata barshi ba yasa yamika hannu yadanna wayan ta jikin motan sanan yakoma yazauna dakyau yana tuki abinshi.
“Hi Zayn” Ayshu tafadi ahankali, shiru yamata bai amsaba, ahankali tace “Faisal told me kagama komi kakoma naija, nima this week zan gama komi nadawo gida, nima a Abuja gidan mu yake” shiru yakarayi baice komiba, ahankali tace “Zayn please I know ina damunka but all i am asking for is kadinga daukan wayana, I love you beyond words” dan zaro idanu Khairy tayi tana tabe baki lallai ne!



Ahankali Ayshu tace “take care Zayn I love you so very much” akufule yace “thanks” sanan yamika hannunshi yakatse wayan yacigaba dajin wakanshi tabe baki Khairy tayi aranta tace “dan wulakanci kawai”
Wuraren 5:20 sukakai gidansu horn yayi mai gadi yabude musu yaja motan ciki yay parking wani dadi taji ya lullubeta ganin Baba zaune kan kujera a tsakar gida jarida yake karantawa but hangosu yasa yarufe jarida yana murmushi, dan satan kallonta Zayn yayi ganin yanda take murmushi tana kallon Baba yasa yay unlocking motan dawani irin sauri tabude kofan tafito sanan tatafi dagudu tana murmushi batai wata wata ba tawani fada jikin Baba ware idanu Zayn yayi saikuma yadan tabe baki yabude motan yafito ahankali yana cire glasses dinshi sanan yataho ganinshi yasa Baba yace “ke cikani katuwa dake ko kunyan yayanki bakiji” juyowa tayi takalli Zayn murgudamai baki tayi tareda juyamai idanu karaf akan idanunshi sanan tawuce ciki abinta shikuma Baba yashiga gaisawa da Zayn.




Baba bai bari sun tafi ba sai bayan sallan isha’i sabida su Manaf sun dawo suma duk aka taru a falo anata hira, rakosu duk sukayi Matan Baba nama Khairy tsiyan tasaba alkawari tana bata hakuri sanan tabude mata motan tashiga, Baba sai murmushi yake bude musu gate akayi sanan suka fice Khairy nama yan uwanta bye bye.


Kaman ba itane tagama surutu agidansu ba kaman aku shiru tayi tai lamo akan kujera tana kallon hanya, agaban wani babban waje dataga an rubuta Variety Pot Zayn yay parking, kallonta yayi daidai itama ta kalleshi dan batasan mesukazo yi ananba, ganin sun hada idanu yasa dasauri tadauke kanta, ahankali yace “stay in the car I am coming” maida motan yayi yarufe yashiga cikin wajen bayan yabar motan a kunne dan yabar mata AC akunne, wajen tabi da kallo bata iya ganin komi naciki tadaiga maza daban daban na shiga ciki harma da mata, tabe baki tayi ta gyara zamanta abinta babu abinda kemata dadi data fito da wayanta da yanzu takira Aliyu tamasan ya kikkirata yanzu Mtsww.



Tana zaune shiru almost 30min tacika tai fam sabida yanda ranta yabaci bacci ma harya soma kwasheta sama sama taji anyi knocking kofan motan tareda bude motan gabaki daya dan Zayn bai rufe motan ba dama sabida AC daya barimata a kunne, bude idanunta tayi takalli mazaunin direban dan tama zaci shine yadawo, ganin wani saurayi yashigo ciki kaman an wurgoshi yana sanye da Riga da wando irin rugget dinan yadaura handkerchief a goshi yazauna gakuma wani ta kofan inda take tsaye yana kallonta hannunshi daya rikeda sigari yana busamata a fuska, saikuma taji an bubbude kofofin bayan motan guda biyun wasu maza biyu suma sun shigo sun zazzauna suna rufe kofan back yasa taji kirjinta yabuga da mugun karfi, wanda yazauna mazaunin direban ne yakalleta yace “Madam rufin asirinki shine ki sauka daga motan nan batare dakince ko uppan ba” dudda gabanta nafadi dan tagane barayi ne saida tadaure tace “akanme zan sauka daga motan gidanmu saidai ku ku sauka” hannu wanda yake gaban kofan motan

Please Login or Register in order to submit comment