Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

cikin yaranta babu wanda ke sonta kaman yanda Khairy ke sonta, idan Khairy tadawo gida batanan wani zubin har zazzabi takeyi, Son da Khairy ke mata dabanne, gabaki dayan kawayenta baki suka sake suna kallon Khairy yanda ta kankame mamanta cikeda murna tana rawa kaman wata yar karaman yarinya, murmushi kawai Maman takeyi ganin yanda kawayen ke kallon Khairy sabida wayan nan wasu new set ne basu saba ganin haukanta agidaba yasa Mama tace “ke dalla cikani kije kitchen kitaya Ladidi ku kwaso abinci kiyi serving friends naki kuci” sakin Mama tayi ahankali tana murmushi dake bala’in kara mata kyau tana kallon Mama tace “tom Mama” sanan tawuce kitchen da ihunta ta shiga kitchen din. “Ladi kwas kwas!” Tsabagen yanda Ladidi tafirgita batasan lokacin data saki cokali data rike a hannunta kasa ba, kwashewa da dariya Khairy tayi ganin yanda Ladidi tafirgita, Ladidi ta watsa mata harara tana dafa kirjinta da hannu jin yanda yake bugawa tace “aniyarki tabiki Khairy bani zaki sawa bugawan zuciya ba wlh” dariya Khairy tayi tadauki spoon tazo kusa da ita tana kallon tukunyar tana murmushi tace “uhmm smells good, let’s have a taste” abincin tadeba takai baki tana lumshe ido, harara Ladidi tabita dashi tana kallon long full lushy eyelash dinta dazakaji kaman ka cire kasama naka sabida kyau, dan murmushi tayi tace “yayi dadi Khairy? Kinga nasa coconut milk dakikace nadinga sawa” bude idanu Khairy tayi ta kalleta sanan ta yatsine fuska tace “yayi dadi ba laifi amman ba kaman nawa ba” batarai Ladidi tayi hakan yasa Khairy tafashe da dariya tace “ki zubamana nida kawayena kizo ku gaisa” hararanta Ladidi tayi tace “Malama ki tsaya ki dauki abincinku ki kaimusu ba inda zani nagaji da gaisawa da kawayenki, nibansan ko kamfani gareki na kawaye ba” turobaki Khairy tayi tace “bakinciki kikemin kinga inada kawaye masu sona ke bakida kawa ko daya” dasauri Ladidi tanuna kanta tace “ni Khairy bakin ciki ana zaune lafiya, kawayenki sunfi dari, ni idan Allah yabani kawaye ko sama da biyu ne bansan yanda zanyi dasu ba” hararanta Khairy tayi tadauki Baban tray da Ladidi tajera musu different abinci akai a different plate guda 5 tafita dasu taje takai musu sanan tadawo ladidi na kallonta tace “yanaga kin dawo” akufule tace “su tara ne plus ni goma, kuma is just 5 plate of food nafita dashi” kasa magana Ladidi tayi kawai tashiga zuba wasu sababbi tass abincin yakare Ladidi tace “yayyinki suka dawo maizasuci” “oho” ta amsata akufule tafice abinta takaimusu abinci suka shiga ci suna hira shaaaa kakeji sun cika falon da hayaniya kadauka biki ake kowani liyafa aka hada, lekosu Ladidi tayi daga kitchen kwafa tayi tace “yo wlh ban kara daura wani girkin barima kiga tafiyata zanyi, masu gida nakema aiki ba kawayenki ba, yarinya kowani kare da doki kawayenki ne, mijinki zai sha fama Khairy” tai maganan tana komawa ciki, hada yan kayanta tayi a handbag dinan sanan tabi takofar kitchen tafice abinta daman inhar tagama aikin yamma indai Hajiya na sama tafiyanta take saidai in tana kasa ne saitaje tamata sallama tawuce.


Sai wuraren 6 sanan kawayen nata suka fito bayan takaisu sama sunma Mama sallama har compound tarakosu inda sukai parking motocin su duk suka shishiga, daya daga cikinsu taleko bayan tama motarta benz key tace “wai Khairy yaushe zaki farajan mota kine eh? Gamu duk mu munaja ke kadaine kullum driver ke kawowa” kaman zatai kuka tace “ba su Mama bane da Baba wai tsoro suke su barni nafara tuki wai nacika rawan kai kumafa na iya wlh Paddy” dariya dukansu sukayi wacce ta kira da Paddy tace “ke da karfin hali zakisa su barki kifara tuki wlh daukan mota kawai zakiyi wataran ki fice, Babe magrib tayi bari muwuce see you tomorrow at school” hannu tadaga musu tace “see yah girls” gateman dinsu yabude musu gate suka fice motoci biyar daidai kuma motocin yayinta na shigowa gida na Baban su biyeda su, washe baki tayi tana tafi ahankali tana kallon motar Baban su dake shigowa last tace “oyoyo Baba” motan na parking tai wajen motan da gudu batare databi na yayyinta da kallo bama.
[6/16, 7:55 PM] +234 701 275 3212: 💫 ALKAWARIN ZUCIYA 💫


PROMISE OF THE HEART 💔


✍🏻M SHAKUR


4️⃣


Kafin ma Baba yabude kofa tasa hannu tabudemai kofan jikinta har rawa yake tanajin dadi. “Baba oyoyo, Baba sannu da zuwa” wani magidancin mutum ne babba sosai yana sanye da babban riga yanada gemu dayacika da furfura, ga kuma katon ciki irin na manya wayanda suka manyanta dinan, exactly idanunsu iri daya da ita manya saidai nashi daya soma kankancewa sabida tsufa, wani kalan kyayataccen murmushi yasakin mata, cikin kamilallen muryanshi irin na magidantan nan yace “yarinyar Babanta” yay maganan yanajan dan hancinta, murmushi tayi sosai tace “sannu da zuwa Baba” fitowa daga motan yayi yace “to akwasomin kaya akai ciki” gyadamai kai tayi tace “to Baba” yawuce yana kallon yaranshi maza su uku da duk suke tsaye suna jiran fitowanshi, Manaf wanda yake Babba yanada 27yrs, sai Mu’az shima 27yrs twins ne shida Manaf saidai ba identical twins ba ko kadan ma basuyi kamaba idan baa gayamaka yan biyu bane bazama ka yardaba, Manaf na kama da Mama, Mu’az na kama da Baba, sai Maheer dakenan 24yrs, dukansu sun gama makaranta duk a company Baba suke aiki yanzu.

Gaida Mahaifin nasu sukayi cikeda girmamawa kana ganinsu kaga yaran dakeda tarbiya dakuma natsuwa. Cikin so da kauna ya amsasu yana tambayan kowa ya aiki sanan suka wuce masallaci, itakuma kayan Baba su files da wasu yan tarkace tafito dasu daga motan sanan tai cikin gida.

Sama tayi direct zuwa lafiyayyen hadadden falon Baba, ijiye kayan tayi sanan tajuyo tabude kofa ahankali, ganin Mama tsaye abakin kofan kaman ita take jira daman yasa takarasa fitowa tareda maida kofan tana rufewa tana kallon fuskan Mama dake kallonta tana murmushi, harara Mama ta watsa mata tace “ba murmushi nace kimin ba, quietly go to that kitchen kidafa sabon abinci wanda za’aci agidan nan this night tunda wanda aka dafa dake da kawayenki kun cinyeshi tatas” dan turobaki tayi dan wlh tagaji ahankali kaman zata rushe da kuka tace “Mama maisa Ladidi bata dafa wani ba wlh nagaji school fa naje” cikin fushi sosai Mama tace “are you stupid Umma? Inba so kike na makeki ba kiwuce yanzun nan kafin raina yabaci kije ki daura abincin daza’aci this night, I am talking to you kina gayamin Ladidi tadafa, kin zaci sabida ke nadauki Ladidi aiki kokin dauka jakace ita batasan ciwon kanta ba dazata zake tai girkin gida keda kawayenki kuzo kutasa abincin agaba ku cinye tas, yanzu ina gayamiki kije ki daura wani kina neman kawomin gabli da ba’adi, to the kitchen my friend!” Mama tadaka mata tsawa kaman zata kurma ihu tawuce hawaye sun cika idanunta tass tai kasa, harara Mama tabita dashi sanan takada kai kawai tawuce tashiga dakinta.

Kitchen din tashiga tamaida kofan da mugun karfi tarufe kaman zata Balla kofan sanan ta jingina da kofan tana maida numfashi takai kusan 5min sanan tawuce ta kwaso kayayyaki tashiga shirin hada girki.


Saida akai Isha’i sanan Baba da su Manaf suka shigo gida, afalo suka tarda Mama zaune gaidata duk sukayi, Mama ta gaida mijin nata zama duk sukayi, Maheer yace “Mama me aka dafa yunwa nakeji” ahankali Mama tace “Khairy na kitchen tana girki, itada kawayenta suka cinye duka abincin da aka dafa tass shine yanzu dannace taje tadafa wani abincin take kumbure kumbure” dan murmushi Baba yayi yana duba wayanshi ganin yanada miss call, cikeda kufulewa Maheer yace “wlh Mama Allah zan zane yarinyar nan, duk randa takawo kuchakun kawayenta tashiga kitchen tamusu girki da kanta ba abincin muba” cikin fushi shima Mu’az yace “ni I don’t even know wani kalan brain Khairy keda shi, ni tunda nake bantaba ganin wacce takai Khairy yawan kawaye ba, kawayenta sunfi dari biyu, tamaida mana da gida nanne majallisar kawayenta ai gobe Saturday Allah sa takawo mana wata gidan nan wlh daga ita har kawar saina kakkaryasu” Baba daduk ke jinsu yana taba wayanshi wayan ya ijiye yakalli Mama yana murmushi sanan yakalli su Maheer yace “ku kyale yarinyar nan she’s just a small girl, idan making friends makes her happy so be it, abincin gidan banike siyaba taita kawo kawayenta sunaci is no big deal, and you wife” yajuyo yakalli Mama yace “idan abincin gida da kawayenta keciki ki kara yawan abinci since kinsan yarki mai mutane ce, ta yanda zasuzo suci su koshi sanan muma muzo muci okay” tabe baki Mama tayi tace “daman babu wanda ke bata yarinyar nan saikai kacigaba” Mama tai maganan da fushi dan murmushi Manaf da tuntuni baice komiba yayi ganin yanda ran Mama yabaci yace “Mama kudena making issue out of this small thing please bagashi yanzu tana kitchen tana dafa mana wani ba, is just friends ta tara bawai wani bad hali ko dabi’a takeyi wanda yaran yanzu sukeyi ba Mama, please ku kyaleta, she’s still a small girl, inda ace bata gama secondary school dawuri ba da har yanzu bamata shiga university ba ballema tazo hartana final year, ku barta please Mama ahankali zata gyara” murmushi sosai Baba yayi yanajin maganan da Manaf keyi, Manaf nada dabi’unshi sak, ga hakuri ga iya tafiyar da gida gashi da halin manyanta halin Baba, amman Mu’az da Maheer jin kansu suke kaman sa’onnin Ummul Khairy. Baki Mama tabude zatai magana aka bude kofan kitchen din aka fito Khairy ce tadauko wani hadaden warmer, ko kallonsu batayi ba sai uban turo baki take tawuce zatakai warmer dinning Baba yace “zo kawo kulan nan Umma anan falo zamuci” ahankali tajuyo tazo Mu’az da Maheer sai uban ballamata harara suke tana karasowa ta ijiye kulan Baba na kallonta yace “yauwa sannu da aiki Yanmata na” Maheer dake kallonta yace “yi sauri kije ki kawomin plate dina da fork” dasauri ta kalleshi da manya manyan idanunta harara ta watsamai wani irin mikewa tsaye yayi kaman zaiyo kanta dasauri tai baya tareda dan sakin ihu. “Wayyo Ya Manaf kaganshi ko” hararanshi Manaf yayi batare dayay magana ba hakan yasa Maheer yakoma yazauna yana kwafa, Manaf yakalleta yace “go and bring the plate and serve us” gyadamai kai tayi tajuya tana turo baki daga Baba har Mama suka bitada kallo, bata wani dade ba tafito dauke dawani babban tray da plates spoons, bottle water da drinks ke kai sanan takawo tsakiyan falon, sanan tabude kulan wani kamshi ne yadaki hancinsu tadafa wani lafiyayyen taliya da nama, zuzzubama kowa tayi sanan ta tashi, Baba yace “ina zaki zauna kici naki” ahankali tace “nakoshi naci shinkafa dazu, wanka zanje nayi Baba nagaji” “jikiyi yarinyar kirki” wucewa tayi sama sukuma sukahau ci, saida Maheer yajuya ganin hartama shiga dakinta yasa yajuyo yace “at least she’s good in one good aspect, wato girki” murmushi Baba yayi yakalli Mama yace “akwai wacce zata zauna da Wife bata iya girki ba ballema yarta” murmushi kawai Mama tayi batacemai komiba, saida suka gamacin abincin tsaf sanan Maheer ya kwashe komi yakai kitchen kafin su tashi suma iyayensu sallama suka wuce side dinsu.


Tashi Baba yayi yana kallon Mama datai shiru yace “please kidena sa zancen shirmen Khairy aranki, is just like what Manaf said at least friends kawai ta tara bawani mugun hali ba” dan ijiyan zuciya ta sauke sanan ahankali tace “Alhaji still yawan kawaye basu da amfani wlh” ahankali Baba yace “I promise duk randa nai sensing wani bad behavior kokuma wani abu nida kaina zan rabata dasu, please this matter of her friends shouldn’t be an issue again ok” Ahankali Mama tace “ai shikenan dama kaine ke bata Umma ai” Mama tai maganan tai gaba abinta binta yay abaya yace “wifeyyy common” bata biyemishi ba tabude kofar dakinta ta shige, murmushi yayi kawai aranshi yace “I will handle u later” sanan yay hanyar dakin Khairy, knocking yayi ahankali tareda kiran sunanta. “Umma” jin shiru yasa ahankali yabude kofan dakin, dakine nai kyau dakana gani kasan dakin Yar gata ne anyimai Fenti pink dakuma design na flowers everywhere, tana kwance kan lafiyayyen gadonta mai kyau tana sanye da dogon gown na bacci tana bacci hankali kwance ga dakin uban sanyin AC tachure alamun sanyi takeji, karasowa gaban gadon yayi yace “Umma Umma, mamar ki dake fada ita batasan rashin jin maganan ta kika daukoba” yay maganan yanajan bargon gadon yarufa mata sanan yadau remote don AC yarage AC sosai kafin ahankali yajuya ya kashe wuta sanan yarufe mata kofan yawuce dakin matarshi!!!!

💫 PROMISE OF THE HEART 💫


ALKAWARIN ZUCIYA 💔


✍🏻M SHAKUR


5️⃣


Da asuba kafin Baba yawuce masallaci yashigo yatadata wanda hakan yakeyi kullum.
Da farinciki ta tashi yau sosai kaman ba itane ta kwana da fushi jiyaba, murna take sosai sabida yau zataje bikin kawarta Zainab.

Saida tai salla tai karatu sanan ta gyara dakinta tsaf tafito kasa ta sauka a kitchen ta tarda Mama tsaye zata fara aiki dawani irin gudu taje ta rungume Mama. “Mama good morning” murmushi Mama tasakeyi this is another aspect na halin Umma datakeso ko kadan batada riko, tureta Mama tayi tace “waike karyani kikeso kiyi” dariya tayi tace “Mama dadi nakeji yau bikin Zainab Kawata, Beaty wacce nai ankon ta kin tuna”? Baki Mama ta tabe tace “ina zan tuna wata Besty Bestotin kin sunfi dari, keda kullum cikin bikin kawayenki ake, idan babanki ya shigo kije ki tambayeshi izini baruwana da zuwa bikinki, bani tukunya nidai kiga” dasauri tadaukoma Mama tukunyar nan suka shiga hada breakfast tanama Mama surutu wuraren 8 suka gama komi suka jera a falo daidai nan su Baba suka shigo gidan duka zama sukai a falo suka shiga kari sai bayan an gama ta kwashe komi takai kitchen sanan tadawo da saurinta tazauna kusa da Baba, fuskanta kadai yagayamai dawani abu hakan yasa yace “Ya akayi Khairiyya?” Murmushi tayi tace “Baba yau bikin Zainab kawata shine nakeso nagayamaka” idanu Baba yazuba mata yace “amman kinsan yau yakamata kije gidan Baffan kiko” gyadamai kai tayi dasauri ahankali tace “Baba gobe zanje gidan tunda yau inada biki please naje Baba”? shiru yayi sai chan yace “ok kije, but by 4 kidawo gidan nan ban yarda kije kai Amarya ba” murmushi tayi tace “Baba ai daman bazanje ba itada za’akai Kano, kumama ana daura aure wai zaa tafida ita kaga kenan kafin 4 nadawo ma” jinjina kai Baba yayi yace “duk kincikani da surutu, okay to adawo lpy, ki kama kanki banson kula maza okay” dasauri tace “to Baba, bari naje na shirya to” tai maganan tana tashi tai sama, tashi Manaf yayi yace “bari naje na kwanta Mama” binshi Mama tai da kallo yawuce yafita shikuma Maheer da Mu’az Kwallo suka kunna a falon suna kallo abinsu, Baba kuma na duba wasu files dayasa Mama tadaukomai daga dakinshi.



Wanka tasakeyi sanan tashirya cikin wani hadaden ashobe, skyblue, dogon riga aka mata daya kamata daidai ita ya bala’in mata kyau, yabi jikinta sosai, zama tayi gaban madubi tana kallon kanta, dan tsaki tayi takai hannunta tana shafa siman rigan da akabi da net da kana iya hango tudun saman boobs dinta ahankali tace “I hate style like this dake nuna jikina, I will use gyalena narufe Mtsww” tasake jan tsaki sanan ta zauna tai wani lafiyayyen dauri dazaka dauka make up artist ce tayi, kwalli ta zizara sanan tadau wani lipgloss tasaka dayasa lips dinta shining pink din jiki yafito sosai dazaka dauka janbaki pink tasaka, wayanta dake gaban mirror kiran samsung note 22 ta dauka, ganin 10miss calls yasa tace “OMG guys gani nan zuwa kunata kirana” ganin battery ta yay ja yana nuna 10% left yasa takara jan tsaki tace “ohhh namanta bansa chaji ba” arayuwanta babu abinda take kiwuyan sawa irin chajin waya wani zubin sai wayan ya mutu russ ne shine zata dauka ma tasa a chaji, jefa wayan tayi a shinning handbag dinta dake ijiye kan mirror sanan tajawo wani hill na dolce gabana tasaka sanan tamike tsaye, dan karamin gyalenta tadauka ta warware sanan ta yafashi ta gaba tsaf yarufe mata kirji sanan tadauki turarukanta ta feffesa kafin ta maida komi yanda yake tafito lokacin 12:48PM.


Saukowa tashiga yi daga Mama sai Maheer afalon yana kallon wrestling shima Mu’az yatafi ya kwanta, kamshin dayaji yasa yajuyo ganin Khairy yasa yasaki baki yace “ke kece amaryan Wanan kwalliya haka, Wanan ko ranan aurenki banjin zaki irin wanan kyan ba” hararanshi tayi takalli Mama dake binta da kallo tace “Mama kin ganshi ko” hararan Maheer Mama tayi hakan yasa yay shiru itakuma takaraso wajen Mama tace “Mama zan tafi ina Baba?” Ahankali Mama tace “Ya kwanta, ga kudi ya ijiye miki” tanuna mata bandir na yan 200 dasauri tadauka tana murmushi tace “Allah sarki Babana he’s the best, Mama natafi” tai maganan tana wucewa zatai kofa, Mama tace “ke” dasauri tajuyo takalli Mama dake kallonta, Mama tace “kindaiji abinda Baban ki yace ko, 4 tamiki agida Umma, kuma ki kama kanki, baruwanki da maza ko abokan ango, saura kuma naji kin wuce wani gantalin daban, wlh kika saba any of them bikin dazakije na karshe kenan ban kara barinki fita” dasauri tace “Mama I promise, nida keda bukukuwa I will not jeopardize that Mama, bye, Mama zan kawo miki alkaki” hararanta Mama tayi tace “banso, wuce Direba na jiranki” kofa tabude tafice, Already Adamu Direba harya shiga cikin motan ita kawai yake jira, wata lafiyayyen bakar Benz tabude baya tashiga sanan tace “gidansu Zainab zamu Adamu” “to Hajiya” yay maganan yana tada motan yaja, saida sukahau kan titi sanan taciro wayanta dake nuna 9% yanzu sabida uban kiran dasuke mata, kafin tama danna wayan wani kira yashigo da suna Zainab, daukan kiran tayi tana dariya tace “Amarya kinsha kamshi da turare, kuma wani gida ne gani ahanya” shiru tayi sai chan tace “Okk” sanan tace “Adamu suna gidansu Amal wai” ahankali tace “to” dan babu gidan wata kawarta dabaisani ba, tafiya kai nisa sukayi sanan suka shigo wani hadadden estate daya cika da mutane kana gani kAsan biki ake wani Layi daban ya shiga sanan yay parking agaban wani hadadden gida, murmushi tayi tace “yauwa, Adamu bani key motan narike” dasauri yajuyo ya kalleta, ganin kaman yanaso yaganota yasa tace “zan taimaka musu dashine, ana kwaso one or two things dazamuyi amfani dashi, idan zan dawo zan kiraka saikazo mutafi” tai maganan tana mikamai hAnnu, ahankali yazari key motan yabata karba tayi tace “yauwa katafi to dan sai yamma zan kiraka” tai maganan tana fitowa daga motan shima fitowa yayi sanan tarufe motan ta danna lock tawuce cikin gidan abinta shikuma yawuce yatafi zuwa bakin titi ya tsaye abin hawa yahau.


Tun kafin tashiga gidan takejin tashin kida, murmushi tayi ta shiga gidan an gyara anyi decorating ga yammatan Amarya sai rawa suke suna hangota aka wani hau ihu. “Khairy, Khairy ta iso, ke join us” wani irin murmushi tayi kaman abinda take jira kenan dasauri tai dance floor din, DJ yasakan musu wani mad song rawa sukahau yi suna ihu suna hotuna idan kaga Khairy zaka dauka taje dancing school ne, suna haka saiga Amarya tafito wani mahaukacin ihu sukasa aiko tashigo itama sukahau rawa kaman mahaukata, Amaryan ta rungume Khairy tana mata magana a kunne, hakan yasa taciro wayanta tana video ganin wayan na nuna mata 1% yasa tai tsaki ta maida bag sanan taciro kudi tana ihu yara sai kallonsu suke taba manna ma amaryan. It was fun she love her friends and she loves wedding har buri takeci irin na shagulgulan da zaayi idan bikinta yatashi.

[6/16, 7:55 PM] +234 701 275 3212: 💫 PROMISE OF THE HEART 💫


ALKAWARIN ZUCIYA 💔


✍🏻M SHAKUR


6️⃣

Wajajen 3 aka wuce da Amarya Kano, ita kanta Khairy saida tadanyi kuka cus Besty tabata tausayi, bayan an wuce da ita tama Maman su sallama tawuce dan zuwa chan gidan dasukai party inda motanta yake a pake, ahankali take tafiya ta bala’in gaji sabida rawan dasuka sha, ita kadai kemagana tace “yanzu inda Baba yabarni da hardani za’akai Zainab Kano, gashi akwai more event a Kano” dan murmushi tayi ita kadai tace “Allah kaimu bikina wlh 2 weeks zaayi ana event hmm” dan murmushi tasakeyi tace “nidako saurayi banda shine nake planning biki na” ahankali ita kadai tace “saikace wata mara farin jini, inada samari dayawa but duk mazan Nile ne, basu hadu ba gasu yan rainin wayau saisa i don’t even talk to them” tai maganan tana murguda baki daidai lokacin ta iso wajen motan, ahankali tace “I want to marry hadadden namiji, classic , handsome, miji dat will make mata jealous of my catch” tsayawa chak tayi takalli motan gabanta yadan fadi, saikuma chan tace “don’t be scared Khairy you have to show Baba u can drive sabida yabarki kidinga jan motarki” tana maganan tabude gaban motan tashiga tazauna tana sauke ajiyan zuciya sanan tamaida kofar motan tarufe kafin ahankali tace “Ohhkay let’s see” sitbelt tasaka still gabanta nafaduwa bata taba tuki bafa kawai tasha ganin yanda akeyi sanan Maheer idan tashiga mota dashi yana nuna mata yace “kihaka kihaka this and that” ahankali tace “Bismillahir Rahmanir Raheem” sanan ahankali takunna motar gently gabanta na dum dum tashiga yin reverse kadan kadan kana gani kasan wacce bata iya tuki bane acikin motan nan sanan ahankali taja motan tana tafiya ahankali wani irin murmushi tayi cikeda jin dadi tace “see ba gashi nan na iya ba ina tuki perfectly like a pro” Ahankali takejan motan feeling a bit too sad sabida su Mama basu Bari takai Zainab ba ahaka hartakai gate din estate din tasa kan motarta tafice tana kalle kallen main road din gabanta na faduwa, ganin motoci kowa na zuba gudu na wucewa yasa sabida irin karfin hali irin nata tasa motan ta shige cikin titin sanan tafara gudu Adan hankali, ganin tana gudu kan titi smooth babu wani tangarda yasa tai murmushi tace “wlh na iya” sanan tawani kara uban gudu tana murmushi, ko kadan bata lura dawani keke napep dake bullowa daga wani layi da mahaukacin gudu ba kawai danno kan keken shi yayi batare dayama kalli titin ba rawa jikinta ya dauka dudda da akwai tazara kadan tsakaninta dashi amman sabida yanda jikinta ke rawa tanason takara kara rage gudun datake kawai ta danna sauri before the blink of an eye jikake kwarap!! Motanta yadaki bayan keken da bala’in karfi tacigaba da tura keken gaba jikinta nawani irin rawa tama kasa taka burki. “Innalillahi wa innailaihi raji’un” tafadi arude kaman walkiya sanan ta ci wani mahaukacin burki dayasa dabata saka sit belt ba data buga kanta a siteri, ganin motan ya tsaya chak yasa dawani irin sauri ta murza key ta kashe motan gabaki daya tana wani irin sauke ijiyan zuciya da sauri dasauri tana kallon keken dake manne da gaban motanta zufa nawani irin keto mata daga goshi takasa ko motsi still in shock.


Dawani kalan sauri direban keke napep din yafito yaci Kwalli a idanunshi yana sanye da Yar singileta daya koma brown tsabagen datti da jeans passengers shi maza biyu suma dake baya duk suka fito yana kallon yanda bayan keken shi yay condemn, sauran motoci sukuma sunata wucewa abinsu tunda dai Allah yakawo sauki hatsari ne da babu wanda yaji ciwo to su karata chan anata wucewa ta gefensu.


Saida mai keken yagama duba kekenshi tass yakalli yanda duka kwan fitilan dake bayan keken suka faffashe sun fadi akasa sanan ahankali yadaga kanshi yakalli glass din gaban motan ranshi amugun bace yana kallon Umma dahar lokacin takasa motsi sai numfashi datake maidawa ita kadai tasan yanda cikin jikinta ke rawa, kafinma mai keken yay magana daya daga cikin passenger yace “durun uwanchan amman matar nan yar bala’in rainin wayau ce Auwal, muna tuki abinmu lami lafiya tazo ta dakan mana keke tamana Wanan uban asaran sanan ta zauna hankali kwance a motanta batama fitoba balle ta duba asaran datayi mana ba”……..




Wani hadadden hilux baka dakana ganinta zaka gane da security personnel ne ke gudu akan titin, ganin titin is congested

Please Login or Register in order to submit comment