Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register


An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels

Ubaidu maleek_*UBAYD MALEEK*_
_(Royalty versus love)_
*_Mamuhgee_*

_Bismillahir-rahmanirraheem_

*1*
Qoqarin sauke kayan dake kan jakinsa yakeyi fuskarsa cikeda annuri da farin cikin jikinsa ma na nuna hakan sbd yanda yake sauke kayan da kuzarinsa da dukkanin himmarsa.,
Fitowa bayi matarsa Kuma uwar yayansa tayi tana kallonsa cikin tsananin mamakin ganinsa adaidai wannan lokacin,
Kallon sama tayi tana son kwatanta lokaci idan ta kwatanta daidai zata Kira lokacin da guraren uku zuwa hudu na yamma,
Duban uban kayan daya shigo dasu da jakin tayi tana sake bayyanarda mamakinta a fili na ganinsa Rana tsaka batareda lokacin zuwansa ganinsu yayi sbd a qaidancen aikinsa sai bayan sati bibbiyu yake zuwa ganinsu yayi kwana daya ya juya sai Kuma bayan satin biyu,
Yau kwanansa shida da komawa Amma gashi tana ganinsa harda kaya haka,
inda yake ta fito tsakar gidan tana ajiye butar hannunta tana Dan sake fuska kadan ta qarado tana karban qaton akwatin qarfensa dayake qoqarin saukewa daga kan jakin tana Dan nishin nauyin akwatin tace"

Abal Kaine yanxu?

Kallon kayan data sauke tayi tana maido kallonta kansa tace"

wannan dukannin kayan fa??
Fatan dai lafiya?

Yana qarasa aje daurin karshe dake kan jakin ya jasa zuwa wata rumfar dake can nesa da dakunansu wadda sukai daure dabbobinsu lokacinda suka taba kiwo yakaisa ya dauresa yadawo Yana zama kan saqin data shimfida Masa Yana cewa"

Alhmdlh ya ubangiji.

Ruwa taje tadebo Masa a qaton kofi me nauyi takawo gabansa ta ajiye tana zama gefensa cikin sauke ajiyar zuciya tana sake gaishesa wannan karon cikin yarensu na amheric tace"

_Dehina metahi_
(Barka da dawowa)

Shan ruwan yayi sosai Yana jinjina mata Kai Yana cewa"

Yawwa barkanku da gida,
Nasameku lafiya?

Alhmdlh"tace tana sake Masa kallon tambaya sbd gabaki daya hankalinta baa kwance yakeba da ganinsa gida yanxu sbd tafi kowa sanin tsanin qarfi da ikon masarautar delah take dashi akan ma'aikatansu Dan shekarunta ashirin harda yan Kai batareda mijinta ba saidai yazo yaganta duk bayan sati biyu yakoma saidai idan tace takai Masa ziyara wadda kafin tagansa ma aikine saiyanzu da shekaru sukaje saidai yayansu suje sugansa duk bayan kwana biyu saigashi yanzu tana ganinsa kwatsam haka ba tsammani.

Sauke numfashi tayi ahankali zatai mgn ya rigata da kallonta cikin tattara Yar nutsuwa a fuskarsa ta dattijantaka yace"

Jamila nasan hankalinki ba'akwance yakeba da ganina adaidai wannan lokacin,
Ki kwantar da hankalinki lafiyace tasanyani dawowa,
Babu wani abu daya faru kamar yanda kike tunani,
Nadawone gida wannan karon gabaki daya da yardar Allah shikenan zansamu yancina zanyi rayuwa taredaku cikin iyalina,cikin nutsuwa.

Wani guntun numfashi ta sauke wannan karon dukkanin jikinta nayin sanyi dajin abinda yake fada Wanda tasan ba iyakacin maganar kenanba akwai babbar maganar dake gaban wannan daya fara ta dago murya a sanyaye tana kallonsa tace"

*_NEGES?_*

'Dan dauke kai yayi ahankali cikin 'Dan jin nauyinta ya jinjina Kai ahankali yace"

Eh negestati.

Sama numfashinta yayi cikin wani irin yanayi na tsoro da muguwar bugawar da zuciyarta tayi ta sunkuyar dakai idanuwanta suka fara qoqarin cikowa da hawaye
Ya kalleta Kai tsaye yace"

Mahaifina yayi bauta a delah tun yanada kuruciya har tsufa ya kamasa Saida yakai baya iya wata bautar Ni yabayar ya yanci kansa a bautar dela,
Nayi bauta a delah tun Ina qaramin saurayina harna zama cikakken saurayi harna aureki muka Tara yaran dake gabanmu,
Nayi shekaru sama da talatin Ina bauta a delah,
Kinyi shekaru kusan ashirin ko fiye kina zaman kadaici batareda mijikinba,
Yarana sun taso Basu zauna da mahaifinsuba suka samu dukkanin kulawarsa,
Shin kina ganin bai kamata ba Nima nasamu yanci nadawo gidaba na huta 'daya daga cikin yayana ta fanshi 'yancina?
Jamila kinfi kowa sanin daganan har lokacinda Rai zaiyi halinsa ba barin delah zanyiba matuqar ba Wanda zan bayar maimakon yancina
Da inada 'da namiji bautar da mahaifina yayi haryabar duniya Nima nayi Shima ita zaiyi da haka zuriarmu zataita tafiya fa Amma yanzu daga kaina inshallah wannan gadon bautar yaqare sbd nine me 'yaya mata su ba bauta zasuje yiba *_NEGESTATI_* zasu zama.

Rintse idanuwanta tayi ahankali tana maida hawayenta sbd kada yaga rashin hakurinta ko rashin hankalinta ta dago batareda ta kallesaba tace"

Neges?
Acikinsu biyun waccece kazaba data zamo din?

Numfashi tasauke ahankali tana bayyanarda dukkanin damuwarta afili muryarta tayi tsananin sanyi tafara cewa"

Abal, dukkaninsu su ukun nice na haifesu,
Na rainesu,
Na zauna dasu nasan halin kowacce daga cikinsu,
MERIYAM bata cikin lissafi sbd itace qaramarsu gabaki daya shekarunta goma cif,
*_PADIMA_* da *_NURU_* sune ake magana akai.

Wani tsananin sanyi murya taqara zuciyarta tayi nauyi tanaji tun yanxu dukkanin burikanta da fatanta akan 'yayanta yana rushewa tareda dukkanin kuzarinta,
Hannu tasa ta dauke hawayen dasukeson sauko mata ta dauke kai ahankali tace"

Dukkaninsu inada burin ganin aurensu Kamar wanne 'yaya,
Nayi tanada da fatattaki akan rayuwarsu da aurensu,
bantaba kawo wani tunanin inda mahaifinsu yakeba zai iya juya qaddarar daya daga cikinsu daga zama Matar aure kamar kowace 'ya zuwa neges wato *_MACEN SARKI KO 'DAN SARKI KO JIKAN SARKI WADDA IYAKACINTA DASHI KWANCIYA DA HAIHUWANE_*,
Bantaba tunanin acikin yayana akwai wadda batada rabon igiyoyin aure su rataya akantaba saidai tazama _Negestati_ *(Kings mistress/kwarkwarah/abokiyar kwanciyarsa/abokiyar nishadin shimfidarsa).*

Kasa riqe hawayenta tayi wannan karon dukkanin jarumtarta saidai tanajin nauyi da kunyar bayyanarda damuwarta akan wannan hukuncin nasa sbd idan tayi Masa adalci ya cancanta ya huta Shima sbd ya bautu,
Ya hidimtu,
Ya wahaltu duk Dan qari sbd su da farin cikinsu baikamata ta nuna damuwarta afili ba duk da tasan aikin gama yariga Yagama tunda harya baro tasan yariga ya karbo shedar musayan yanci.

Abal kayi hakuri.

Girgiza mata Kai yayi Yana gyara zama yace"

Karki bani hakuri Jamila Dan dama dole zakiji ba Dadi saidai duk kuyi hakuri hukuncin Dana yanke kenan,
Maganar rashin jin Dadi anan dayace wato ta rabuwa da 'danka Amma kinsan irin rayuwar jin dadin da negestati keyi a daular nan banbancinsu da matan sarautar aurene Amma nawane suka sauya kaf zuriar danginsu daga talakawa zuwa attajirai.,
Banda burin 'yata tashiga delah dan ta maidamu attajirai saidai inada burin samun yancina Nima na huta daga bauta idan arziki yazo takawo Mana bazan qiba sbd kowa nason arziki kowa nason hada jini da delah dan haka Nima bazanqi naso samun jikoki daga delah ba sbd tabbaci ne na har abada da yardar Allah zuriarmu tagama bauta tashiga Kuma cikin littafin tarihin delah.

Murmushin qarfin hali tasaki tana qoqarin miqewa takawo Masa kunun madarar nonon raqumi da sabuwar danyar shinkafarsu tace"

Allah yasa hakan ne mafi alkhairi abal.

Amin" yace Yana gyara zama ganin ta dauko tasar kunun Yana hango haskensa tun daga hannunta.

Aje Masa tayi tafara kwashe kwayan dayazo dasu takai daki tadawo kenan su NURU din na shigowa gidan kowacce sanye da dogayen rigunan asalin yadin kuta,
Padima ce agaba kyakkyawar asalin brown/chocolate kalar fata,
Doguwace tanada jiki kadan musammn kirjinta acike yake Wanda yasa bayyanarda shafewar cikinta.
NURU ce abayanta hannunta riqe dana meryam,
NURU doguwace itama kyakkyawa me yellow brown skin asalin kyakkyawar amhara,
Batai jikin padima ba Amma tafi padima bajewar qugu Wanda yasa tafi padima suturta jikinta da kaya masu Dadi da rashin kamawa sbd boye irin kalar siffar da Allah yayi mata ta Jan hankali,
Tafi padima manyan idanuwa da fuskar marasa hayaniya sbd koyaushe fuskarta is simple sabanin ita padima da daka ganta zakasan tanada rawan Kai da jiji da Kai tareda jin kanta sbd kyawunta datake alfahari dashi duk da dai NURU da meryam sunfitashi haddama hasken fata sbd su kamarsu daya sosai da sosai sbd su mahaifinsu suka dauko shine asalin amhara wato asalin Ethiopian sai ita ta dauko mahaifiyarsu asalin hausa data surka da amhara din.
NURU da meryam kusan halinsu daya na rashin karauniya kuma meryam tafi shaquwa da NURU sbd itace Bata dukanta ko mata fada sabanin padima da Bata daukar raini ko kadan fada take mata musamman akan yanayin yanda takeson gudanar da rayuwarta.

Akwai saquwa sosai da kauna a tsakaninsu su duka da iyayensu,
Suna son junansu matuqa,
Suna kulawa da junansu tareda tsayawa junansu ako yaushe,
Kaman yanda ake karatun addini Dana boko Suma sunada wani qarin karatun wato karatun al'ada,
Sunyi karatun addini daidai misali,
Sunyi na bokon Wanda duk fiyeda rabinsa na aladunsune Dan haka gabaki daya idan kagansu Kai tsaye bazaka tantance sudin musulmaine kokuwa Dan al'adunsu a bayyane suke sosai tattare dasu.

Ganin mahaifinsu zaune yasa dukkaninsu tsayawa cak suna kallonsa cikin mamaki Banda meryam data qaraso da gudu ta fado kansa tana Masa sannu da zuwa cikin yare.

Kallon mamaki sukam suke Masa musamman dasukaga amminsu itama su take kallo zuciyarta fal da tunanin to shin cikinsu waccece za'a bayar amatsayin negestati,
NURU batada hayaniya,Bata iya doguwar hayaniyaba bare rigima baiwar Allah bazata iya da gidan sarautaba musamman delah dake cikeda fitintinu na mulki da sarauta sbd yawa da girman delah din idanma anbarta anan delah din idan Kuma asalin can daular dake qasar waje aka kaita inda asalin masarautar delah din take zuba zallan mulkinta Babu yanda NURU zata iya rayuwa a acikin asalin zuriar delah Sam Sam NURU bazata iyaba.,

Idan Kuma padima ce to itama akwai babban akasi sbd padima mace ce me tsananin son juya kanta bazata iya rayuwa acikin wainda mulki da iko yagama ratsa jininsuba sbd ita din zata zama bakowa bace acikinsu zasu juya rayuwarta Kamar suna juya kujeran zamansune Wanda taurin Kai da bakin padima zai hallakata acikinsu cikin qanqanin lokaci gashi a iya saninta babban burin padima shine auren mijinda yagama fita hayyacinsa akan Sonta wanda itace zata mulkesa acikin gidanta,
Burinta na biyu samun gidan arzikinda zata juya rayuwarta ta moru kyawunta bayyanardashi duniya tasanta acikin jerin kyawawa shiyasa babban burinta yakasance auren Koda bawane dake asalin delah dake qasar waje wato GIZAH,
Tanada burin komawa can Dan acan ne zata samu rayuwar datake shiyasa takeda kyakkyawar alaqa me qarfi da Ahmed Dan babban sarkin fada dake can giza Wanda ta shirya ta aminta da aurensa tabisa delah ta giza inda zaibi mahaifinsa yasamesa acan Wanda sai mai rabo ne keda sa'ar zuwa can.

Numfashi ammyn ta sauke tana dauke kanta daga kansu suna qarasowa ciki da mamaki suke Kiran sunan baban nasu cikin bayyana farin ciki da mamaki NURU tace"

Abal kana lafiya dai Ina fata?

Murmushi yasaki Yana cewa"

Alhmdlh nake NURU ganinku nazo yi.

Ajiyar zuciya padima ta sauke tana qarasowa itama sbd da har zuciyarta tafara shiga wani fargaba jin abinda yace yasata sakewa ta qaraso tana sakin murmushin farin ciki ta zauna gefen ammynsu tana cewa"

Abal harnaji tsoron ganinka sbd jin labarin yau anrabar da shedar sauyin yanci.

Daga abal din har ammy tare suka dago suka kalleta da sauri zuciyar ammyn na harbawa sbd sanin akwai akasin ra'ayi a alamrin musamman sbd yanda suka sabawa yaransu da rashin takurawa.
##MAMUH#
*_Haske writersπŸ’‘_*



ZAFAFA BIYAR! ZAFAFA BIYAR!! ZAFAFA BIYAR!!!



Ina masu tambayar yaushe za'a fara? Ina masu jiran ranar? Toh gata fa tazo, mun zo muku da salo na daban wanda bamu taba zuwa muku da irin sa ba.

Me kike jira yar'uwa? Biya naki ki karanta halaliyar ki a nutse cikin kwanciyar hankali da jin dadi. Karki bari a baki labari, maza mallaki naki ta hanyar da aka tanada domin biya.

Littafan dai suneπŸ‘‡πŸΌπŸ‘‡πŸΌπŸ‘‡πŸΌπŸ‘‡πŸΌπŸ‘‡πŸΌπŸ‘‡πŸΌπŸ‘‡πŸΌπŸ‘‡πŸΌπŸ‘‡πŸΌπŸ‘‡πŸΌπŸ‘‡πŸΌπŸ‘‡πŸΌπŸ‘‡πŸΌπŸ‘‡πŸΌπŸ‘‡πŸΌπŸ‘‡πŸΌπŸ‘‡πŸΌπŸ‘‡πŸΌπŸ‘‡πŸΌπŸ‘‡πŸΌπŸ‘‡πŸΌ




*_β˜… AL-ƘIBLA_*πŸ’˜
_Na Safiyya Huguma_

*_β˜… MABUƊIN ZUCIYA_*πŸ’–
_Hafsat Rano_

*_β˜… DALAAL_*πŸ’
_Na Miss xoxo_

*_β˜… UBAYD MALEEK_*πŸ’“
_Na Mamu gee_

*_β˜… MAKAUNIYAR ƘADDARA_*πŸ’”
_Na Bilyn Abdull_

Lalai daga ji babu tambaya bana ma ZAFAFAN ku da turirinsu suke tafe. Dan dagani kasan za'a ragargaza cakwakiya, soyayya. Tare da nishaΙ—iπŸ’ƒπŸ»πŸ’ƒπŸ»πŸ’ƒπŸ»πŸ’ƒπŸ».

Gasu duka akan farashi mai rahusar gaske.

Kamar hakaπŸ‘‡πŸ»πŸ’ƒπŸ»

Ɗaya___300
Biyu____400
Uku_____450
HuΙ—u____500
Biyar_____700

Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na bankiπŸ‘‡πŸ‘‡

0225878823 Hafsat Kabir Umar GTB

saiku turawa wannnan numban ta whatsapp shedan biyanku(evidence of payment/Account name)πŸ‘‡πŸ‘‡

*_08085405215_*

IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKUπŸ‘‡πŸ‘‡

0903 234 5899

πŸ’ƒπŸ»πŸ’ƒπŸ»πŸ’ƒπŸ»πŸ’ƒπŸ»πŸ’ƒπŸ»
TEAM----ZAFAFA BIYARπŸ”₯😘πŸ₯°πŸ˜
*_UBAYD MALEEK_*
_(Royalty versus love)_

*_Mamuhgee_*

*3*
Tafiya takeyi cikin nutsuwar datafi Kama da jin Kai da taqama musamman yanda jikinta ke girgizar daukan hankali shiyasa duk Wanda ta hadu dashi a hanya yake hadiye Mata yawu musamman wainda sukasan padima ai tafi karfinsu sbd kyanta da ikonta tareda sanin Wanda suke soyayya dashi din daga delah yake wato Dan babban sarkin fadawa bama Wanda yake Nanba na can gizah.
Daga gurin karbo baqin lallensu take sbd koyaushe ita mace ce da Bata rabuwa da qyale qyale shiyasa yanada wuya kaganta Babu lalle faratanta na hannu Dana qafa shiyane qarin banbancin tsakaninta da NURU wadda duk wannan ta daukesa Kamar bayyanarda kyawu ne Wanda ita tafi ganin burgewarsa idan kayi aure kayi acikin gidanka.

Daga bayanta taji anriqo hannunta ta tsaya cak tareda wani juya idanuwanta wani qayataccen murmushi na sauko Mata sbd sanin Babu Wanda yake iya riqota haka sai mutum daya saidai kafin ta juyo ta hango su NURU tafe da sauri ta juyo ta jasa da gudu suka boye bayan wata qatuwar bishiya tana Dora Masa hannun abaki qasa qasa tace"

Shihhh su NURU na zuwa.

Wani shu'umin murmushi ya sakar Mata Yana gyada Kai kafin ya juya ya zubawa NURU mayun idanuwansa dukkanin yawunsa na katsewa akan NURUn,
Meyesa ba NURU ce wadda Allah yabasa sa'a akantabane Dan wlh baitaba jin mugun kwadayin maceba Kamar NURU gashi padimanma tai Masa Amma da zaa basa zabi da NURU zai zaba Dan duk Wanda yagama samunta a Mata ko a abokiyar haihuwa yagama dacewa,
Mummunan faduwa gabansa yayi daya tuno da hadda abal dinsu acikin yan sauyin 'yanci take ya waiwayo da sauri ya kalli padima Yana girgiza Kai Dan wlh bazai yadda yabarta tashige zuriar delah ba tabarshi Dan har abada bazai taba samun kyakkyawar mace kamarta ba tunda dai NURUn yasan ba samunta zaiyiba Kuma dai dole cikin dayan biyun ne ko padima ko NURUn,.

Ina Ina ina""yafada cikin ransa da sauri Yana girgiza kafin ya maida kallonsa kan bayan NURU data wuce Yana tunano da kaf delah yanzu duk Wanda za'a kaiwa negestati Babu Dan yaro yaro sbd yara yara shekara daya kenan cif da aurarda yayan masarautar delah din su goma sha daya Kuma a qaida saikayi shekaru uku da aure zaka fara karban negestati sai wainda basuyi aureba sukuma baa Basu negestati sai sunyi aure.

Kallonsa padima tayi da manyan idanuwanta tana cewa"

Yaya dai?
Tunanin me kakeyi?

Wani murmushin bazata ya sakar Mata Yana sake jawota jikinsa Yana shafa hannuwanta Yana matsawa ahankali ya kashe ido Yana cewa"

Padi padi,
Padi nidai maganar gaskia zanje nasamu abal dinku yasan da maganarmu sbd so nake kafin kwana talatin dinsa tacika kinzama tawa mun wuce gizah..

Da wani kallo ta katsesa tana Dan zamewa idonta akansa tace"

Kwana talatin kamar dai wadda aka gaji da ita,
Amed nafada maka banason auren gaggawa sbd inason aurena yazama abinda zai burge kowa,
Banice baiwa ba abal dinane bawa Dan haka Ni inada damar yin bikin aurena kamar na kowanne 'yantacce,
Hakama Ina buqatan shiga boyon wankan ruwan madarar nono na tsawon sati biyu hakama Ina buqatan siracin nonon raqumi na tsawon sati biyun Shima sbd ranar dazan fito muka isa gizah aranar za'a tabbatarda nafi fiyeda Rabin matan sarautar kyawu.

Wani murmushin manufa tasaki tana sake riqe hannuwansa cikin kisisina Dan kuwa itadai babban burinta tasamu isa delah gizah inda asalin arxiki, mulki da sarauta suke
Kyawunta shine zai cika Mata burinta shikuma amed shine mukullun tafiyarta.

Cikin marairaice fuska yace"

Padima bazan iya Bari kwana talatin din abal dinku yacikaba sbd zai iya zamtowa kece zai bada bazan iya rasakiba padima mutuwa zanyi idan bake.

Wani kallon rashin fahimta take binsa dashi fuskarta na sauyawa tace"

Badawa Ina?

Gyara tsayuwa yayi Yana sake tamke hannunta yace"

Abal dinku ya karba shedar sauyin yanci.

Wani irin bugawa kirjinta yayi tana qwace hannunta daga nasa cikin son qara tantancewa tace"

Negestati??

Gyada Mata Kai yayi Yana cewa"

Eh padima Kuma Nanda kwana talatin ne za'a karba wadda zai bada kowane lokaci za'a zo afara gyaran ko ke ko NURU.

Wani irin daure fuska tayi zuciyarta na harbawa da qarfi a matuqar zabure take cewa"

Meyasa abal zai Mana haka?
Meyasa zai yanke hukuncin badamu negestati baiyi shawara damuba bama wannan ba"" da sauri ta rqio hannunsa son tabbatarwa tace"

Amed ko kasan waye za'a karbanwa negestati din?
A delah tanan ne ko a delah gizah be?
Fadamun da sauri amed inason sani ne idan a delah gizah za'a Kai.

Kallo biyu yake Mata,
Kallon Sonta da kallon yasan manufarta akansa Dan haka cutar cuta za'ayi yasani Sarai sbd yace gizah zasu take taredashi ta yanda idan an isa zatasan yanda zatai ta watsar dashi ko negestati ta zama acan din ta yarda shikuma Yana sane Sarai ba gizah din dazashi hakama yasan wannan tambayar datake Masa Dan taji idan Wanda za'a kaiwa negestati a gizah ne tsaf zata samu abal dinta tace abadata Amma yasan yanda zaiyi da ita ko taqi ko taso ita din tashi ce shi daya.

Bata fuska yayi kalar tausayi ya riqota Yana cewa"

Padima shiyasa bazan iya Bari abadaki ba sbd anan delah ne za'a bada Kuma qarin cikin abin a yanda naji abeela za'a kaiwa qila mutuminda shine kusan babba acikin jikokin delah ya tsufa ko me zaiyi da mace yanzu?,
Padima bazanso kije rayuwarki ta gurbata ba Zaki samu arziki da mulki Amma baida amfani sbd bazaki more rayuwarki yanda kikeda buri ba gwara muyi aure mutafi gizah acan nasan rayuwa zatai Mana dadi.

Jin Wanda za'a bawa negestati din yasake daga hankalinta tafara girgiza Kai tana cewa"

Badai ni padima yonas ba,
Sam rayuwata bazata mutu ba agurin bautawa tsohoba duk ya zugemin kyau da quruciyaba,
Padima darajata ta wuce Nan wlh bazan yardaba saidai NURU koma meryam za'a bada abada nidai wlh bazan yardaba.

Juyawa tayi ta nufi hanyar gida cikin tsananin tashin hankali batareda ko takansa tasake biba,

Duk rashin hankalinta da girman kanta bazata iya bijirewa iyayenta ba saidai zata fada musu bataso idan sun nace bazata iya musu taurin kaiba saidai
Abu biyune tasani matuqar aka bada ita negestati to rayuwarsu kaf tana cikin hadari sbd duk Wanda aka kaiwa ita ya kwana da ita zaijita ba budurwa ba Wanda hakan babban laifine hukunta kisa itada iyayenta duka idan sunada jini acikin delah wadda ta taba zama negestati shine zata roqar musu sassauci baza'a kashesu ba saidai za'a koresu daga qasar gabaki daya to gashi basuda Yar uwa ko daya delah dama burinta ta auri amed sukoma gizah inda tasan kyawunta saisa kaitsaye tasamu Dan sarauta bayan tasan yanda tayi ta rabu da amed yanzu ga wannan babbar maganar ta bullo yau ita wazata fito tafadawa kada abadata sbd ita din ba budurwa bace.

Koda ta isa gida har wani murdawar tashin hankali cikinta keyi tayi danasanin bawa amed kanta yafiso cikin kwando dari Dan kuwa Sarai tasan masifar hakan a addinance dakuma al'adance.

Tana shiga gida dakinsu tayi da sauri ta ajiye kayan hannunta tafito ta zari buta ta nufi bayi tana kaucewa kallon inda abal da amminsu ke zaune suna binta da ido.
Koda tashiga bayin kasa yin komaima tayi tafito tana qoqarin sakewa tazo gurinsu abal din ganin su NURU sun dawo ta zauna anacin gasasshen dankalin dasukeci da ita.

Kallon NURU abal dinsu yayi hakanan yake sakejin hankalinsa yafi kwanciya da zuwan NURU sbd ita din tafi cancanta duk da baisan waye za'a kaiwa ita ba Amma dai yasan delah basuda tarihi mara kyau Dan haka duk Wanda za'a kaiwa baida fargaba ko shamaki.
Padima yakalla yasake kalla zuciyarsa nasake tabbatar Masa da kamar kaita wani kuskure ne koba komai yafison yabarta ta aura Wanda take Dan burintane ita Kuma NURU bada ita ba'a shiga haqqintaba sbd batada wani buri sai wanda su iyayenta suka yanke akanta.

Ajiyar zuciya ya sauke tareda kallonsu cikin nutsuwa yafara koro musu bayani komai tareda dorawa da cewa"

Padima kiyi hkr da wannan al'amari daza'a Kira da qaddararre sbd tabbas kowane uba zaiso ganin ya aurar da dukkanin 'yayan da Allah ya azurtashi dasu,
Naso ganin hakan Nima kamar kowane uba saidai Allah be nufa zanga na dukkanin 'yayana ba saidai biyu daga ciki Dan haka padima Ina Baki hkr dakuma umartaki dakiyi biyayya wa Ni mahaifinki dakuma al'ada da dole ki karbi wannan qaddarar dan haka saiki nutsu Zaki daina fita daga gobe sbd za'a fara Miki wanka da siracin sabuwar Madara za'a fara kawowa daga DELAH.

Tsit sukayi dukkaninsu kamar ruwa ya cinyesu musamman padima da jikinta yadauki mazari tafara hada zufan tashin hankali Wanda yasa umminsa shiga tunani me firgitarwa kafin wani yayi magana padimar ta bude Baki murya na rawa tace"

Abal...abal NURU.... NURU..Ni inason A....zungurinta umminsu tayi tareda katseta da cewa"

Kutashi kuje kuyi tunani inshallah Zakiyi farin ciki da hakan ba dama gidan arziki da mulki kikeso ba Inshallah zakiji Dadi.

Cikowa idanuwanta ke neman yi ta girgiza Kai tana cewa"

Ammi ba hakan bane ni...Ni..

Kuje nace padima.

Kamata NURU da jikinta yagama sanyi tayi Dan ita gabaki dayama ta firgice dajin abinda yake faruwa sbd ita ko delah akace za'a saitaji duk ta firgice bare ace itace zata shiga delah ta zama jininsu Sam firgici ma tunanin hakan yasata shiyasa tausayin padima yashigeta me tsanani duk da tasan padima ita zata iya duk da idan tashiga ita din ba komai bace Amma dai gwara ita zata iya.

Suna shiga daki padima ta zube kan shimfida tana sake shiga tashin hankali wlh Bata shirya mutuwaba,batason mutuwa Ina zata saka kanta dole ta samo mafita.

Duk irin lallashi da kulawarda NURU ke Mata cikin tsananin tausayawa Sam Bata fahimta sbd hankalinta baya jikinta.
Abu biyu da biyu ga zama negestatin tsoho mara amfani,ga tsoron agano ta taba kwanciya da wani Kuma ta shiga delah ga tsoron hukuncin hakan duk saitaji tana neman haukacewa wlh bazata iyaba Gwara abada NURU Dan ita tunda duniya Bata dametaba zata iya rayuwa da tsoho ko baida amfani itadai ba ruwanta can su qarata.

Har gari ya waye Bata rintsa ba sbd tsananin tashin hankali Koda ta fito da safe babu Wanda bai fahimci Bata hayyacintaba duk ta firgice gashi tanason ganin amed suyi magana Kamar me ba halin fita Dan idan Bata samu magana dashiba komai lalacewa zaiyi.

Da maraice saiga manyan bayin delah kusan guda goma sha biyu sunkawo tarin kayan wankan Madara daza'a fara Mata washe gari tana ganin hakan hankalinta yasake tashi jama'ar gari kuwa suna gani suka tabbatar aka fara zarya gidan tayasu ammy murnar samun yancin abal da murnar shigar 'yarsu delah.

Kwanaki

Please Login or Register in order to submit comment