Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

dolene komu kosu wasu sumutu tadaga murya tacekutabbata kungano wadannan gurare gobe domin ayanxu haka Sarki,Kurungu shida tawagar Shaidanun,matannan sun bayyana afilin daga,atunaninsu mungudune amma gobe zasui toxali da ajalinsu lallai dolene gobekotahalin kaka mukashe tsinannunmatannan bakidaya lokacinda gariyawaye sai Dakarummata sukai yowaje sunarike damiyagun makamai kawai sai sukai toxali da samarin askandariyya cikin shirin fama dankari nanfa afara hararan juna abinka da tunxurarru kawai atare kowani bangare yakwarara ihu yaikan abokin gabarsa,wohoho nanfa bakin artabu yatashi sushiga farautan rayukan juna tabbas awannan karanma samarin askandariyya sunyi iya kokarinsu sunjarraba iyadabaransu amma sunrasa logan matannan yaki yarin cabeyakaxanta dakarun mata sukaima samarin askandariyya lagalaga Hankali,Axifa yatashi takwarma ihu gamida kwalama yaranta kira tanacewa yaku samarin askandariyya lallai jariri yana iya rayuwane kawai idan yasha nunon uwarsa kufarmaki matannan a nononsu tabbas yau Sai sun mutu Samarin askandariyya sukai ihu sufarma yammatannan,damugunnufi Yarima ma,arufne yafara tsinkema wata nono tai ihu jini yabarke yasatakobi yasare kanta Hankalin sarki Kurungu yatashi yatakarkare yakwarara ihu dankari aitsakanin ihunsa darufe bakisa samarin askandariyya sun kashe samada mata DUBU,GOMAΞΞΞΞYAKIN DUNIYA PART 9BΞΞΞ
Samarin askandariyya sukaci gabadaragar gazan yammatannan kamar guguwar annoba iface iface yawaita kururuwa da karaji yacika ko,ina jini yakama kwarara gawawwakin yammatannan yayaaita Sarki kurungu arude yakWarma ihu gamidadakama daukacin dakarunsa tsaa yanacewa mutun da aljan dodannida koma wacce irin halitta ku afkama tsinannum yarannan da yaki maitaken kurun kus bakidaya dakarun suka kwarara ihu gamida jinjina makamai suka afkama Samarin askandariyya da mugunnufi tabbas maxa suke maganin maxa domin,samarin askandariyya sai sukasance tamkar yanxu suka fara yakin sufara badadi darayukan maxaje basakyale mutum basa,dagama aljani kafa duk wanda sukai arangama dashi to yaxamo tarihi yarima Sauban yadurfafi makiya yana sauke musu axabar yaki tamkar wani aljanikamar Shaidani duk inda yaratsa saikaga jini nafeshi kawuna natashi sama gangan jiki naxubewa kasa Masuduka kaji yarkarama dabala ii domin harwani tashi sama takeyi tana sarfatan rayukan makiya tana sadasu da ajalinsu yaki yatsananta yarima Ma,aruf shida Ma,arufa suka afkama jama,ar aljannu da masifa da bala i tayadda tsananin munin kisandasukeyi kafin sukai kan aljani sai yayarda takobinsa yatashi sama domin neman tsirada rayuwa saidai kayya badama domin Maxrukane keruwan kibau daduk wani dakare dayake kokari kawo musuhari tasama ko yai,kokarin guduwa to itace ajalinsa dankari koda yaki yakazanta kisa yai yawa masifa tai masifa Sarki Kurungu yaga irinkisan gilla gamida kisan kiyashi da samarin askandariyya kema jama,arsa sai hakalinsa yatashi Zuciyarsa tahassala yakama cika yana batsewa yatakarkare yakwarara ihu mai furgitarwa tsabar furgitarwa saida yaki yatsa cik sarki kurungu yasabi karanto wasu dalamusan tsafi yanadamdam yana wani hamham yahiga mimi dabaki yatakarkare yadaki kasa dahannunsa take kasa takama xillo tanagirgixa dankari lallai tsafi gaskiyar maishikawai sai iya shashin da Samarin askandariyya suke tsaye yaburma take kasa takama hadiyesu tashin hankali Axifa takwarma ihu inda sarki kurungu da daraunsa suka kama babbaka dariya kassa taci gabada hadiye Samarin askanda riyya harta wuce kwaurinsu kawai sai Azifa tasabi karanto wasu sirrika natsafi datsananin sauri take karantowa saida ta ambaci kalaman tsafi dubu arba in acikin dakika arba in adaidai lokacin kasa takawoma samarin Askandaryya kugu kawai sai Axifa tadaki kasa gamida nuna yankin dada yaranta kekafe kasananema hadiyesu taiwani tsawa gamida ambaton wata hardaddiyar kalamar tsafi cik kasar tatsaya amma kasar tarikesu kam basu dadamar motsawa samarimarin askandariya sukai iyakokarinsu akansu kwace amma abin yafaskara domin duk motsawa kasarma dada matsesu takeyi sai Sarki kurungu yadubesu yabushedadariyar mugunta yadaga murya yace yaku tsinannun askandariyya lallai kundade kuna aika maxaje lahira tokuma yauce ranar mutuwanku tabbas yau sai kummutu yadakama dakarunsa tsawa yace bakidayanku ku afkama tsinanannun yarannan lallai ayau konamansu bana bukatar gani atare kuma alokaci guda sukwarara ihu sukanufi Samarin askandariyya kamar shanun tashi suna wani ihuda kururuwa dankari hakalin samarin askardariyya yatashi domin baxasu iya aikata komaiba sai Azifa takwarma ihu tanacewa yaku yayana kudaki kasa dahannayanku take atare sudaki kasa kawai sai wasu baka da kwari subayya aganbansu Azifatace kudauki bakanda kwarin kuimu wankan wuta take kowa yadamki nasa sushiga sakima makiya ruwan kibau tamkarruwansama suka hana kowa motsawa dankari tsananin masifa wata mahaukaciyar wuta takama dakarun sarkin kurungu tamkar karmami haka wutar ke babbake gungun mutum da aljan wohoho sarki Kurungu yai duk abida xaiyi amma ina wutarnan saida takone dakarunsa bakidaya tai musu kurmus sai yarage afilin daga Saura Sarki Kurungu Aljana dufal Aljani Murgui Sarkin yaki Makau Sarki daji Daxau Zabba,u axabar yaki ,Dodo Surkum sai kuma sarauniyar binnin mata Marsuba su hadu aguri daya su bakwai Samarin askandariyya suka daki kasa kasa tadare sukai wani kumaji suka futo sai suka jeru da uwarsu Azifa yarima Ma,aruf Ma,arufa Yarima Sauban Maxaruka, yarima amsal dakuma yar auta Masduka sumasuka jeru su bakwai AKAFARA HARARAN JUNA DANKARI SHAIDANU GOMA SHAHUDU SUN FUSKANCI JUNA LALLAI XA,YITA BARI INCI ABINCI DOMIN YAU XA,AYITATAKARE INBA AGATARIBA AKOTA BALA IIIIIIIIIII AKWAI CASKALEWA ABOKAI KUJIRANI INDIBI GIRKI¥¥¥YAKIN DUNIYA PART 9 C¥¥¥
Lokacin da Shaidanu shahudu sukarage Axifa dayaranta Sarki Kurungu da na Hannun damansa hatsavivai shida sai suka fuskanci juna daniyar saukema junamasifa dakata ii aka xubama juna idanu na tsawonsa,a guda anama juna kallon kiyayya datsananin tsana can Sarki Kurungu yahassala yacika yabatse yatakarkare yakwarara ihu yazare wasu takubba gudaBiyu yanuna Axifa da tsinin takobi yace ke tsinanniyala,ananniya lallai yau anxo karshe kuma kwanakinku Sunkare,aduniya tabbas yausai kunmutu sannan,bama mallakan yammatan Bininkuba bakidayansa Birnin shineXaikoma Fadata tabbas sai nakashe duk wani namiji dakebirnin Askandariyya immaida matan Birnin matayena in aikata abin danakeso Kawai Sai Axifa tabushedadariya akarshe takwarara ihu takama kirari tana cewa wane mutum wane alja askandari Birnin Mazaje ita,daMusa ba girma axava atabaku ashakashi mugidan runa atona agudu tadaga murya tace tabbas mumunfi karfin yaro Saidai uban yaro takara Bushewadadriya tadubi yaranta tace yakusamari askandariyya Shin dame kugirma mecece kawarku kuma mene Sana arku sannan mene abin alfaharinku kuma menene burirku abin sha awarku Atare alokaci guda suka fara magana ya ummu askandariyya mumungirmane tareda mutuwa sannan yaki shine Sana armu kuma KasheMakiyi shine abin alfaharimmu lallai mutuwa domin kare rayukan jama,armu wannan shine babban burimmu abin sha,arwa kowani Saurayi akasar askandariyaAxifa tadakama Sarki Kurungu tsawa tace kai wawa mai gajeran Bure kai askandariyya kakeso kakwatanikuma da yayana Somuke mu mutu akakare Askandariya tadaga murya tace idan kashirya mutuwa tabbas yau zakamutu kaida tsinannun mashawartanka,wohoho sai Hankalin Sarki Kurungu yatashi yakwarma ihu yace yakuMashawartana kushirya shirin yakinkarshe take suka zare makamansu yace ku,afkama tsinannu yarannan lallai mukashesu a Nahiyar Shammace Dankari ai sai subakai ihu suja baya taku goma samnnan atare bakidayansu sukai kanSamarin askandariyya harda Sarki Kurungu za,ayita takare Azifa tace yara kushirya tarban makiyanku kushayar dasu gidauniyar mutuwa lallai ayau mutabbatar mungama da makiyammu bakidayansu hoho aisai suma suka jadabaya suka sheko aguje suna ruri gamida ihu suka tunkari Makiya tsananin gudu harkasa na girgixa bishi yoyi na kakkaryewa,halittun kewayan suka furgice gamida rudewa suka baxama cikindaji ahaukace tabbas ajannun yakin da dabbobi da tsuntsaye Sunyi zaton tashin Duniyace taxo dakankari,akai wani irin haduwa maitaken Haduwar hatsabibai hoho kowa yafuskanci jarumi guda daya Azifa taruftama Sarki Kurungu sukacameda Yakin maitaken na sallama rayuwata Ma,aruf ya afkama Sarkin yaki makau dawatairin zuciya tamkar dutse Ma,arufatafadama aljani Murgui inda Sauban sukacameda yaki Shida dodo Darkus shikuma Sarkin daji Daxau yana kafsa yakine da Amsala inda Xabba u tafadama Maxruka Itako Yar auta Masduka Sai sukai Kwaramda Sarauniyar Mata Marsuba wohoho yakine mara kangado yasarke Tamkar yakin Duniya ihukawai ketashi da kururuwa maxaje Saikaran Haduwar takubba mai baraxanar kashe dodan kunnin mutum ko aljan tabbas yaki yatsananta kuma babu wani wandaba,aimar yanka Samada gomaba ajikinsa jinine kexuba akowani Sashi amma Saboda naci da musiba Yakin akoyaushe kara tsananta yake taredadaukar zafi dankari Sarki Kurungu Da Azifa karfi yaxo daya domin dukkansu Sungalabaita kuma sunjigata anacikin Wannan yakine Aljani Murgui yainaran Soke Amsala akahon Zuci tai wani Irin kara gamida Ruri tafadi matacciya aljani Murgu yakwarmaihu kayya Azifa Samarin Askandariyya sukwarara ihu atare Kuma alokaci guda suka sanya kafafu suka banke abokannin karawansu kamar walkiya sai gasu sunkewaye aljani Murgui dankari aikamar kiftawar ido sunsanya takubba sunyi kaca kaca danaman Aljani Murgui kokashinsa bai tsiraba Sarki Kurungu da jama,arsa suka fasa ihu sukayo kansu Aizifa tamike takalli Gawar amsala tace kaicommu Lallai Dakika talatin nabamu banaso nakara ganin makiyimmu aduniya dankari Samarin askandariyya sukai wani kumaji gamidaGunji Sukanufi makiya ana haduwa Azifa tasoke Idan Sarki Kurunguda tsininmashi yakwarma ihu tasa kafa tabankeshi yai sama tabishi saman taimasa wankan wuka Ma,aruf yasa takobi yazabtarema makau kafada tafadi kasa Makau yabaje akasa yana kakarin mutuwa Ma,arufa tai Kwance kwance ta sare kafafuwan zabbau bakidayansu Takwantsamamata gatari aka take ta mutu Maxruka Tai gunji gamida karaji tadaka tsalle tatsinke kan dodo Durkas Kamar katuwar bishiya yafadimatacce Yar auta Masduka taiwani tsalle tawatsama Marsufa wasu kananan taurari masu dafi take taurarin suka sauka amamunanta tai ihu tafadi amace Yarima Sauban yasokama Aljana Dumal mashi akirji aljani yafasa ihu Sauban yasatakobi yasare kafar tsinanne guda daya Kaf dakarun Sarki Kurungu Sun mutu saura Sarki Kurungu da Sarkin yaki Makau dakuma babban aminin Sarki Kurunguda Wato aljani Domal wanda dukansu suna gabar mutuwane Tabdi Shaidani Shaidanine koda Sarki Kurungu yatabbatar mutuwa Xasuyi sai yadaki kasa take shida Makau Da aljani Dumal Wata bakar Guguwa tasuresu tabace bat Samarin Askandariyya sukwarara ihu To maikaratu indai baka mantaba bakidayaWannan labari Makaune kebadashiga Sarakunan duniya da bokayeN duniya dasu taru afadar Sarki Himarul karni suna kulla yadda zasutunkari Birnin askandariyya suyakesukowa yamallaki macen askandariyya to anan Makau yai shiru yaga bakidaya jama,ardake Fadar sunkaraya dahatsabibancin Azifa da yayanta sai yai murmushi yace yakutaran sarakunan Duniya shinko KUNSAN SARKI KURUNGU HATSABIBI UBAN HATSABIBAI YANA WANNAN FADAN AIGABADAYA SAI AKAMIKEYAKIN DUNIYA PART 9D
Lokacinda Sarki yaki makau yace ahalin yanxu Sarki Kurungu yana cikin wannan fada bakidaya Sai jama,ardake Fadan suka mike afurgice illa mutum daya yanaxaune jikinsa yasha sara dasuka yanada ido daya dayan yatsiyaye tabbas shine Sarki Kurngu dankari Aisai daukacin Sarakunan duniya da jarumai da matsafa gamida hatsabiban mutane da aljannu sukai Sujjada ga Sarki Kurungu sukoma suka tsaitsayacan Sarki Kurungu yamike yamike bakidaya jama,ar fadan suka xauna shuru akayi nadan wani lokaci sannan Sarki Kurungu yafara magana yana cewa yaku Sarakunan duniya da sauran al umma lallai kusaniakwai aiki agabammu domin tunkarar birnin askandariyya daidai yake da tunkarar ajali Lallai Azifa dayaranta shaidanune da suffan mutane tabbas sundade da mutuwa domin kare kasarsu wannan shiyasa aduk lokacin da kukai arangama dasu to baxaku tabagalaba akansu domin kullun suna sanya kansune alayin matattu aduk lokacin da sukadauki makami to abokin mutuwa suke nema kuma kusani mutanene masu tsanain sa,a da rabo sannan sugaji tsawon rai gamida ketare siradin mutuwa yadaga murya yace mutukar munaso muma mallaki Matan askandariyya tokuwa saidai in Azifa da samarin askandariyya basa kusa Wani jarumin maxa mai jinkansa yamike yace to bakidayammu mudungumma mufuskacesu ayita takare komo kosu in muinasara shikenan inko sukai nasara akammu sunxauna lafiya Sarki Kurungu yabushedadariya akarshe yace kai yaro lallai kasani duk taurikanka da jarumtarka kana bayan Sarki Kurungune amma sau uku muna gabada gaba da tsinannu yarannan amma abin kunya dakyar nake guduwa sarki Kurungu yakwarma ihu yace lallai muna bukatar shawaran masu hikimane ba Jarumtaba sai wanitsoho yamike fuskansa cike yakeda faringashi harkiji yamikeyace nine Boka Sirdadu lallai akwai hanya daxamu mallaki yammatan askandariya amma saidai akwai hadari Sarki kurungu yace mutukar zamu mallaki yammatannan hadari ba,abin duba wabane domin indan har muka tarwatse babu yadda zasuyidamu dole su hakura BokaSirdadu yacezamu iya tsafe wasu yammata sukoma tamkar yammatan Binnin askandariyya sannan sai musanya aljannu surikida suxama,Sarki kurungu da Sarki yaki makauDa aljani Dumal su giftata gaban Azifa da samarin Askandariyya Hakan xaisa subibayan aljannun karyannan masu daukeda matan karyana askandariya lallai wayannan aljannu bazasu tsayaba har sai bukatanmu tabiya wato sai mun shiga Birnin askandariyya mum mallaki yammatan askandariyya domin mutukar sukatsaya Azifa da yaranta sugano Shirimmu kafin biyan bukatammu tokowa acikimmu sai yamutu koda Sarki Kurungu yaki wannanshiri Sai yabusheda dariya yace wannan Shawara takatayi lallai ninexan kirkiri aljannu masu tsanani gudu wanda idan sukafara gudu tosu bama xasu tsayabasai sunje bangon duniya kawai Sai bakidaya Fadar akadinga babbaka dariya marakangado saida Sukai dariya ta ishesu sannan fadar taitsit take agabato da wasu yammata guda bakwai Sai boka Sirdadu yakalli yamamatannan yarika karanto wasu kamantsafi yanatofawa acikin wani kuttun tsafi saida yaixufa sharkaf sai yadubi yammatannan yaduddula musu ruwannan aka dankari tsafi gaskiyar maishi aisai yammatannan sukarikide kamanninsu yajuye sukoma tamkar yammatan askandariyya wohoho dukda kowa yasan ba yammatan gaskiya bane amma saida maxaje suka rude gamida kama Sambatu suna kokarin afkama yammatannan Kaii Sarkin yaki Makau yadaka tsawa afadar mai furgitarwa gamida tsoratarwa take kowa yakoma cikin hayyacisa Sarki yaki Makau yakalli tarin jama,a sunata kallon yammatannan natsafi suna lasbaki gamida hadiye yawu Sai yabusheda dariya yace lallai jama,a aduk lokacin dakukai arba da yammatan askandariyya na gaskiya bamakawa sai kun haukace yasake bushewa dadariyya Sai Sarki kurungu yamike yakama kiran wasu sunaye takewasu aljannu subayyana kimanin su dubu arba in sannan acikinsu akwa aljanuuku da daya yaikama da Sarki Kurungu daya yaikamada Sarkin Yaki Makau daya kumayai kama da aljani Dumak Sarki Kurungu yace yaku aljannun gudu kudauki wayannan yammatan guda bakwai kada Kaukesu ako ina saikundangana dabangon Duniya Aljannun suka sungumi yammatannan sukabace batabacewarsu keda wuya sai sarki Kurungu yai tsawa yace yaku tawagarsarakuna da jaruman duniya gamida bokayan duniya mudauki harma mutunkari Birnin askandariyya dankari aisai runduna tadauki hanya tai gaba kai inkagansu saikarantse mutanen duniya ne bakidaya sukaihijira daga wata duniyar zuwa wata Duniyar dankari tafiya suke babu sassauci tsananin yawansu koaljanu kodabbobi idan sukaga wannan runduna to saidai sugudu kokuma abitakansu ba,amasan anbi takansuba al,amarin Azifa kuwa itada Samarin askandariyya sunakan hanyasu tadawowa Birnin askandariyya kwatsam sai sukaga tawagar aljannu sun gifta tasamansu sun wuce kamar wulkawar walkiya amma tsananin kiyayewa irinna Ummu askandariya harta ga komai takwarara ihu tai girgixataxama wata karamar tsuntsuwa tai sama tabibayan aljannunnan damasifar gudu dankari aituni Samarin askandariyya suma sunkai Girgixa sunxama kananan tsuntsayennan subi bayan Azifa dagudun masifa nanfa akasa tsere tsakanin aljannu masu dauke da yammatan askandariyya nakarya acankuwa Sarki Kurungu da jama,arsa sun isa birnin askandariyya to sai suka raina kansu domin sunyi iya yinsu susami wata kofar daasushiga birninaskandariya,amma sunrasa sungwada tsafi sunyiSurkulle amma abanxa dominwani lokacimma birnin bacemusu yakeyi dakyar suke laluboshi Ran Sarki Kurungu yabaciyakwararawani uban ihu yakama cika yana batsewa yana wanidam yana waniham saiyakara kwarma ihu saidakowa yafurgita NIMA NAFURGIta NAFECEEEEEEEEYAKIN DUNIYA TAKUN KARSHEE
Lokacinda Sarki Kurungu yarafka,,ihu yasabi karanto kalaman tsafi yanuna katangar askandariyya yaitsawa take wani haske yadaki katangar taruguje dakaru suka barke da ihu Sarki Kurungu yace wane mutum wane aljan lallai yautarihin wannan Birni xaikarya yadaga murya yace kuxo muje maxaje bakidaya tawagar suka kutsa cikin birnin askadariyya dankari aisai sukasha mamaki domin suntararda Birnin babu kowa acikinsa, kaza babu aBirninaskandariyya Sarki Kurungu yakwarara ihu yanacewa Karyane lallai yau mutanen askandariyya sama kushiga ko kasa kunutse dolene Saina kwakuloku yakara kwarma ihu yadauko madubin tsafi yashafashi yana wani Simi simi dabaki dankari tsafi gaskiyar maishi ai sai hoton Al ummar Birnin askandariyya tabayyana amadubin gasunan kwansu da kwar kwatansu Sunnufi dajin Kanda har inda akai yakin Duniya na farko wohoho Sarki Kurungu yakwarma ihu yace yaku taron Sarakunan duniya da jaruman Duniya lallai Mutanen Bininan sunyi Hijara zuwa dajin Kandahar kutaho mubisu yasaki Linxamin dokinsa yafuta aguje bakidaya runduna tabibayansa Mutanen askandariya na isa Filin Kandahar Dakarun Sarki Kurungu na karasuwa ah kicibis mugun gamo nanfa akama kallon kallo Sarki Kurungu yafuskanci Jama,ar askandarya yakeceda dariya akarke yakwarara ihu yadakamsu tsawa yanacewa kai yaufa karyanku takare lallaifa kusani lokaci yayi da maxajen Duniya zasu huce haushinsu akaN yammatan Birniku tabbas yasaina mallaki mata goma acikinku yadaga murya yace yakai Sarki Isnadshin xaka turo mana yammatanneSalim alim koko sai mun daka muku wawa munkar kashe maxajenku mukwashe matayenku jinjira baxamu kyaleba Kawai Sai Sarkin askandariyya Sarki Isnad yabushe dadariya yadubi Sarki Kurungu yace kai wawane axatonka akwai wani mahaluki mutum ko aljan da ya isa yatabi yammatammu alhali Azifa da yayana Suna raye yadaga Murya yace to gwarafa kudu domin bala ii da masifa nadab da fadamaku lallai maison ransa yaitakansa kafin UMMU ASKANDARIYYA da yayanta sukariso Sarki Kurungu yabushe dadariya kamar yaxare akarshe yadakama Sarki Isnada tsawa yace kai tsoho lallai kasani Azifa da yayanta sunnufi bangwan Duniya kozasukai nanda sheakuru Hamsim bakidaya dakarun Sarki Kurungu sukabushe dadariya tamkar mahaukata ran Sarki Isnad yabaci yatakarkare yakwarara ihu gamida dakamusu tsawa gum sukai Shiru Sarki Isnad yace kai gayyar tsiya lallai inkunhaukacene togwara kudawo cikin hankulanku yace kukasa kunninkubakwajin sauti kamar saukan ruwayace to baruwa bane mutuwarkune inkuma kuna shakka kudaga kawunanku sama lallai xakui toxali da mutuwarku dankari bakida har Sarki Kurungu suka daga kansu Sama,sai sukai toxalida Ummu askandariyya Axifatul Axifa da samarin askandariyya sunyo kasa hoho Sarki Kurungu Sarkin yaki Makau aljani Dumal sukwarara ihu domin susan bakyau ba dadi Azifa da yaranta sudira agaban makiya nanfa afara kallon kallo Azifa takalli Sarki kurungu tace kai axatonkaxaka yaudaremune tobabban kuskurenka shinetaban katangar askandariyya domin dajinin jikimmu aginata mutukar katabeta toko a,ina muke saimuji,tadaga muryatace matsoraci ina fata kashirya mutuwa kaida jama,arka ran Sarki Kurungu yabaci yakarara ihu yai umurni da afara yaki dankari bakidaya taron sarakuna da jarumai bokaye kowa da kowa sukai kan Samarin askandariyya suna ihu Axifa tadaga murya tace yara kushirya shirin fara yakin duniya atare Samarin askandariyya da wasu maxaje na kasar sukai ihu su afkama Makiya wohoho aisai akacameda kaxamin yaki masifa takullusamarin askandariyya suxama tamkar Shaidanu duk inda sugilma saidai kaga gawawwaki nxuba jini yadinga kwarara kawauna surika tashi Sama dankari aiki saida kayan aiki domim Azifa rikidewa tayi takoma tamkar Shaidaniya domin saidatarabu gida dari ko ina kaduba itace takema makiya kisan kiyashi gamida kisan gilla bakyau badadi mutuwa tarika shawagi tana sarfatan rayukan maxaje tana turasu kiyama tirkashi saida akwana biyu anawannan yaki to ananne Sarkin yawa yai aikinsa domin samarin askandariya sungaji sai tangadi sukeyi jiri nadibarsu dakyarma suke iya kare kansu itakanta Axifa tagama tagayyara domin yanka ajikinta yafi dari jiri kedibanta amma saboda naci ahaka take kaimakiya lahira,anahakane Sarki Kurungu yashammaci Azifa yasoka mata mashi abaya takwalla ihu tawaiga afusace tasare hannunsa yakwarma ihu yasa kafa yabanketa taisama tafado kasa komotsi batayi dankari yaki yatsa cik samarin askandariyya sukaraya jikinsu yai sanyi sukasa aikata komai sarki Kurungu yaitsawa yacekuikaca kacada tsinannu yarannan bakidaya Dakarun sukai kansu damugunnufi kwam sai aji wani tsawa gamida tashin kabbarori take Sadauki Nawas yabayyana shida wasu maxaje su afkama jama,arSarki Kurungu dasara,da suka suna kabbara ai sai yaki yadawo sabo Sarki Kurnguyakwarma ihu gamida kururuwa yakaima Sadauki Nawas Sara tuni yakauce cikin hanxari yasa takobi yare hannun Kurungu sarki Kurungu yakarara ihu kawai sai yai arba da Ummu askandariyya Azifatul axifa agabansa tsananin mamaki sarki Kurungu yakasa motsi domin yadauka tamutu aituni tasa takobi tama Sarki Kurungu tsargan rama tarabashi gida biyu dankari aisai mutanensa sukaraya suka xubar da makamansu wasu sushige daji wasu suka xube bisa guiwowinsu don mika wuya yaki yacisu Axifa taruga aguje tana ihu tarungume Sadauki Naawas tana cewa nayi imanida unbangijinka Allah ubangijin halittu akadunguma akoma birnin askandariyya kowa da kowa yamusulunta inda Sadauki Nawas ya auri Azifa DUNIYA TAXAUNA LFIYA SAMARIN ASKANDARIYYA SUSHIGA DUNIYA YADA ADDININ,MUSULUNCI to abokai Muhadu Alittafi Na gaba NGD


An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya

Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,

Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan
Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490

A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,

Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu

Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC

Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng
You can download more hausa novels there
Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online
It is free we do not charge for uploading novel
Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services

Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us

Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it

Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT

This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng
For feedback and support
Facebook : https://facebook.com/taskarnovels
Twitter : https://twitter.com/taskarnovels
Telegram : https://t.me/taskarnovels

Please Login or Register in order to submit comment