Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

askandariya tafiyace tatsawon uni guda mamaki yakamamu domin mu atunaninmu muna shiga zamu tadda birninne Gimbya zabba u azababbiya tace yaku taron mazaje lallai kowannenku yagyara damarasa tabbas mun shigo lardin askandariya take mazaje sufara yindamara gami da sanya guraye da layu dakuma sauran tsunburikai kamar ana jira mugama kintsawa sai mukaji wani raxananniya kara gami da kururuwa irinta manyan jarumai wohoho ai tsanani kara saida bakidaya tawagar tarazana dawaki sufara furgita suna kokarin futa da gudu bayan danwani lokaci sai komai yadawo daidaikwatsam sai mukai kicibis da wani kyakyawan saurayi yana kan wata katuwar giwa tabbas nataba ganinshi shine Nazbir ammada yakariso sai nasha mamaki yadaga murya yace yaku bakin tsinannu masu bakin burin dauka mana yaya mata tokusani sam bazaku iyaba inkuma zaku iya to gawasunan kawai sai muga wasu tsala tsalan yammata sunbaiya tabbas matannan sugomane amma duk inda kakai da nazarinka baka isa kace gawanda tafi wata kyauba tsayinsu daya farinsu daya tafiya tufafinsu duk iridayane kai komur mushi daya taimaka anjimadaya itama tamaka to zakaga iri dayane yammata sujeru agabanmu sufuskacemu wohoho ai bakidaya aljanu da mutane sai mukidime kuma murude daganin kyan suran yammatannan dayawa wasu sun fara futa ahayyacinsu koda gimbiya Zabba u taga halin da tawagarta tashiga sai tadakama Jama ata tsawa tace yaku rundunan aljanu da mutane yakamata kusancewa kuna dabda fadawa tarko dan haka kushiga taitayinku take kowa yasami natsuwa gimbiya Zabba u tadubi kyakkyawan saurayinan tace kai samarikasani sam baxaka yaudaremu da yammatannanba koka futo dasu koka boyesu lallai yau sai muntafi da budurwa daya na wannan birni kaico ai sai saurayinnan yafusata yakwarara ihu yazaro wani dan madai daicin gatari yace dakyau yammata lallai ni Marwan nikadai inhar ina raye tabbas bazaku iyadaukan koda yar tsanan kasarnanba yadaka mana tsawa yace kutaho mugwabxa yaki muga waye zai mutu sannan waye zai rayu kamar ammana usur sai mukai kansa da wani mugun nufi yajadabaya sannan yafalfalo aguje yataho mutaho zamui arangama saida yarage saura kadan mu hadu kawai sai Marwan yadaka tsalle yatashi sama tamkar tsuntsu saida yaxo tsakiya rundunarmu sannan yadira wohoho wuyar aiki ba afaraba nanne naga masifa dabala in yaki inda kasan wuta takama karmami haka Marwan ke babbake jarumai ba mutum ba aljan duk wanda yakaftama sara toba bukatan akaramai sara take zai sheka lahira kaico maza gumbar dutse Marwan yajadaga yai runfa yadinga tura mutane da aljanu kiyama zancen gaskiya wannan yaki yafi karfina saboda haka bakidaya ina gefe inda kururuwa da iface iface mazaje yacika gurin kura taturnike gurin jini yashiga kwarara gawawwaki suyawaita duk wannan masifa da bala i da ake ruftawa ko kwarzane ba aima Marwanbaa kai wani abin mamaki sai kara daukan zafi yakeyi hakayake hada kawunan aljanu da mutane biyar alokaci guda yana sarewa kai koda masifa tai masifa sai aljanu sutashi sama daniyar guduwa amma saboda bala i inda kasan tsuntsu haka marwan yabisu bakidaya yakakkabosu kasa gawawwaki koda mutanen dake kasa suga masifar data samu aljanu sai suzubar da makamansu sannan suwatse kowanne yai nsa guri tirkashi lallai hatsabibi dai hatsabibine kawai sai marwan yarabu iya yawan dakaru dasu watse daya bayan daya saida yasadasu da ajalinsa duk wannan markabu da miyata da ayi nida GIMBIYA zabba u muna gefe lokacin da zabba u taga bala inda yamu mutanenta sai takwarara ihu tazare takobi taikan marwan tabbas hausawa sunyi gaskiya dasuce motsi yafilabewa domin saida zabba u da Marwan sudau tsawon rabin sa a suna tafka yaki mai ban tsoro amma da lissafi yacanxa sai marwan yajefar da makamin hannunsa zabba u takawo mai wawan sara da takobinta caraf yasa hannu yarike kuma yasa karfi yakarya takobin kamar walkiya yacafki wuyarta yashaketa yadagata sama da hannu daya take tafara jin kanshin mutuwa tafara gani daya abiyu tafidda rai darabo ai koda naga idanunta sufur futo tana neman bazawa lahira sai na kwarara ihu nafalla aguje naje na gabzama Marwan naushi aciki tabbas yaji naushin domin saida yai wurgi da Zabba u taje tabigi katangar askandariya take tasuma damasifan gudu naje narungumeta nasabi sambatu da kalamai na tsafi take natashi sama da ita nakama kokarin hayewa katangar askandariya sai Marwan yabiyomu nanfa mukasa tsere asararin samaniya yakure mana gudu yasa hannu yakama kafata najijjiga daya kafan namakamai abaki take bakinsa yafashe Marwan yafusata yadunkule hannu yagabzamin naushi aruwa ciki wayyo ai tsananin zafindukan da yami saida mutsallake katangar askandariya Sarkin yaki Makau yadubi dakin taro yaga kowa yaitsit yana sauraransa cikin aljabi Saiyace yaku taran manyan sarakuna da mashahuran mayaka kokunsan ayaya muka fado kuma memukatara abaya katanga askandariya bakida akai shiru yai mur mushi yace zanfada muku baya nasha shayi TOAI NIMA SHAYIN ZANSHA KUMABATAYI BA BISMILLA DOMIN MADAM TACE SHAYI NANE NIKADAI WAYYO DADI GASKIYA SHAYIN DADI *;;;;;**YAKIN DUNIYA PART 1H***;;;;Lokacinda Marwan yawatsomu tasaman katangan akandariya sai nasha mamaki domin agabansa mufado baiyi watawataba sai yasanya hannayesa yakama kafafuwanmu nida Zabba u yaita wuriwuri damu saida bakidayammu musuma sannan yai watsidamu iya karfinsa saida mukai kolikoli sannan mufada wani kwazazzabo wanda wani ruwa maimasifan karfi yake gangarawa tabbas tsananin sa a danisan kwana sune kawai susa murayu ruwannan yatafidamu yakaimu wani fili yawatsar bansa iya adadin dakikai da sa o i dakuma kwanaki damukayi awannan filinba rana tsaka nafarfado dakyar nabude idanuna sai nai arbada zabba u tabaje arana tamkar gawa dakyar natattaro iyakarfina namike naje wurinta idakasan ana gasata haka naji jikinta zafi rau gashi bata komotsi nanfa hankalina yatashi nashiga waige waige ina zanga ruwa can nahango ruwa naigudu nasanya salkata nadibo ina zuwa nadiddila mata taiwani mika gamida zambarma take farin ciki yalullubeni bansan sanda narungumetaba saida nai watanni tara inajinyanta sannan tasami sauki saida tacika shekara guda sannan tawarwa re yadubi jama a yace yaku taron sarakunan duniya kusani daga lokacin danafuta neman birnin askadariya zuwa warkewa gimbiya zabba u to shekara hudune daganan bayan tawartsaketa saitacemin yakai namijin duniya gashi narasa jama ata bakidaya sannan badan kaiba datuni namutu tun acikin birnin askandariya yanxu meye abinyi zamu koma gidane koko zamu fuskaci askandariyace najinjina maganarta sannan nace yake gimbiya zabba u azaba kisani ni Sarki yaki Makau bantaba guduwa afilin yakiba kuma sam ni bantaba bantaba faduwa afilin yakiba saboda haka yaki da mutane askandariya lallai yanxu muka fara kawai sai Zabba u tafara tafamin tana cewa gaisheka Makau me banmamaki sannu gwarzo uban mazaje lallai nayarda kaine dirkan birnin Farisa lokaci guda tadaure fuska tahaderai kamar zata mutu takalleni tace yakai dodon maza kasani Zabba u tuntana yariya batataba alkawari tasababa kodako wanene tama alkawari to saitacikishi balle wannan alkawarin dan uwana namai cewa tabbas bakawa saina sato mai daya dagacikin yammata askandariya duk rintsi tadaga murya tace lallai akan inkoma gida batare danacikama dan uwana burinshiba tabbas gwara namutu awannan daji sai kawai nida ita murungume juna sanna bayan wani lokaci mufada ckin dokar daji wanda ahali yanxu basuma san inamunufaba kwatsam muna garari adokardaji saida mukai wata guda aciki dokar daji kawai watarana munacikin tafiya sai mutsinci wani dan madaidai cin gari atsakiyar daji kai tsaye munufi cikin garin haba ai muna tunkaran garin sai muji an kwarara ihu gamida tsawa cak mutsaya gamida waige waige amma bamuga mai ihunba kawai sai muji gaba datunkaran garinnan kwatsam sai mukaga wasu mayaka sunkama bulbulowa tako ina kafin kace haka tuni sunkewayemu furda furdan kattine gajeru masu kiba da faffada kirji zasu kai kimanin sudari hudu makamansu kafta kafta tamaka makamin samudawa sukama zaga yamu sunamana muzurai gamida zare idanu ahankali suna matsomu take muja daga gamida yin rummfa aikawai sai suriftomana dasara dasuka tirkashi nanfa yaki yabarke take nasa kafa nabanke wani kato koshurawa baiyiba nadauki makamisa yayinda wani yakawomin wawan sara nagoce gamida maimar damartani take nakille kansa yafadi matacce Zabba u tadau makamins kai inkaga girman makamin yafi tsawonta gamasifan nauyi ammada yake basadaukiyane tuni takama sarrafa makamin tana aikawa da mazaje lahira tabdii jam aki gamai kareka aituni mukashi mutanannan bakidaya kona tsuwa bamuyiba kai kyakkyawan nunfashi bamu maidaba sai mukaji an rangada guda sau uku saban zance kenan furda furda katti tako ina sama da kasa bulbulowa sukeyi mazada mata dattawada matasa wasu takar kashe kasa suke ketowa wasu tacikin dokardaji suke ketowa wasu tasarari samaniya suke bullowa kowannansu rikeda miyagun makamai bakiya kammu suke tunkarowa dawani irin mugun nufi da tsananin gudu suna kartan kasa nakalli zabba u nace kishirya shirin yaki tamkar zaki yaki da mazajen duniya takalleni gamai dawani gamsashan murmushi tace dakyau jarumin maxa lallai yau mutuwa zataci kasuwa rayuka jini zai malala jikkuna zasufadi kasa kawuna zasu tashi sama tamkar tsunye daidai lokacinne dakarun sukariso suhadu sutaru sukaimana rufduguuu kai inkaga irin rufdugun dasukai mana saikadauka konamanmu baza asamuba amma damukai wani gunji muakai kora dama da hagu gabas da yamma kudu da arewa mukai zarya atsakiya sai ga kattinnan nayawo asararin samaniya suna zubowa akasa matattatu tamkar yayan kanyaaaa bala iiiiiiii Gaskiya NAFURGITA SAI DA SAFE ABOKAINA *****YAKIN DUNIYA PART 1(I)*****Dankari ai sai dakarunnan sukara kukankura surufarmana da sara da suka tamkar munrusamusu abin bautansu nida Zabba u muhaukace muzama tamkar zakuna a akurkin kaji sai kakkabar darayukan dan adam mukeyi tamkaR wasan yara duk inda zabba u tasa gaba saikaga jijjkunafadi kawuna nazuba gawawwaki suyawaiTa jini yakama kwarara cikin lokaci ahada kogin jini koda yaki yaitsanani sai akaji wani wawan ihu gamida kuruwa mairazanarwa gami da furgitarwa cik yaki yatsaya saiwani shirgegen mutum yabaiyana duk inda zaka musalta girmansa datsawonsa yawucenan amma hannun daya gareshi babu riga ajikinsa bakidaya ilahirin jikinsa tabone na manya manyan yankada sara gamida suka kai hatta fuskansa yaikaca kaca dasara mutumin yakallemu yace gaisheku jaruman fama shinku suwaye acikin jaruman duniya lallai inason insan koku suwaye daga cikin jaruman duniya nakalli jaruma Zabba u sai taimin alama mufada mushi komu suwaye take nace ni sunana Makau kawai sai yadakatardani yace kaine Sarkin yakin farisa lallai inajin labarinkada jarumtarka da hatsabibancinka kuma yau natabbata dacewa kai jarumine amma da sauranka mamaki yakamani yadubeni yace kana mamakine to kasaurareni saikuma yadubi Zabba u yace kekuma waceceke tai murmushi tace nice Zabba u itama yadakatat da ita yace Zabba u azaba kece gimbiya kuma kece jaruma kuma durkan birninku tabbas kema inajin labarinki da jarumtarki dakuma hatsa bibanciki toamma afage najarumta tabbas da sauranki itama mamaki yakamata yai murmushi yace kina kokontone amaganatar toki saurareni yai taku uku sannan yanunani yace zo nataho sai yajehomin takobinsa nakamata zan dauka nanfa nasha mamaki domin dakyar nadaga takobinnan saboda tsananin nauyi yakalleni yai murmushi yacemin yaro taho mugwabza wayyo aisanaji wani fusataccen karfi yazomin jin yace mini yaro najijjiga takobinnan nai sama da ita nakama sarrafata ina juyata tamkar ina wasa da kara saida nai rabinsa a inawasa datakobinnan sannan nanunashi datsinin takobi nace maikai kanimi yaro tundare baimakaba domin yaro na bayan uwansa nakwarara ihu nakarci kasa naikansa afusace komotsawa baiyiba har nakarisa gurinsa nafara kaimai sara da suka shikuma yana karewa tabbas yarainani ammada nacanzamai salon yaki sai yashamamaki domin tilas yamaida hankali yakama kawomin naushi tunda dama bairike makamiba wohoho ainan nagane ruwa batsaran kwandobane nanfa yashiga saukemin kwandon naushika wanda tuni yakumbura min jiki gamida ciremin hakora biyu raina yabaci namike nakwarara ihu nafalfala da gudu nadaka tsalle kafin katonnan yadaumataki tuni nahaye kafadarsa nakaftamai sara awuya jini yai tsartuwa yasa hannu yamakoni nabaje akasa tuni nasuma sai yadubi Zabba u yace ya yammata kema zaki jarrabane tai murmushi tace wannan aidolene yawurgo mata takobi take taimurmushi kawi saitasa hannu tadauki takobinnan inda kasan bata dauki komaiba shikansa saida yai mamaki ganin inda taima takobin daukan oki tafalfala aguje ta afkamai dasa dasuka kankace haka tarikitashi tarudashi hartaimai suka uku yaduba yaga jini nakwarara sai ransa yabaci yatarijin yacika hannunsa yakurbe yai wani gyatsa yadurkusa yadibi kasa yacike gurabe dtasokeshe dakasa kawai sai yanufeta afusace takawomai sara yadamki wuyanta dahannu daya yadagata sama yafidda hannu yadinga kifamata mari har saida tasuma yaijifada ita yasa akwararamana ruwa mufarfado mukai mika mutashi muxauna yadubemu yace yakece dadariya yace gaisheku jaruman fama kokunsan konini wanene muka girgiza kai alaman bamusaniba yace tokusani nine na miji uban mazaje Sarki Kurungu mai mulkin kasar Balwan take mumike gamida saramai sannan muka fadi mukai gaisuwa SAKIn yaki Makau yadubi taron sarakuna da hatsabiban mutane yace shin kunsan Wanene Sarki kurungu nakasar BAHALWAN KAFIN MUSAN KOWAYE SHI TO SAI NA DAN MOTSAJINI DOMIN DAYUWAR INTAFI BIRNIN ASKANDARIYA *****YAKINDUNIYA PART 1F****** Sarkin yaki Makau yacigaba dabada labari to kusani Sarki kurungu shiyakasance kafin yazama sarki wani shahararran barawone wanda yagagarI duk sarakunan duniya tumbatsaRsa yakai inda yatare awani daji yakafa kasarsa yasamai suna bahalwana Kurungu tun yana dan shekara goma yake sanyada hular karfe kuma tunda yafara sa hulan karfe baitaba cirewaba har sai ranan damukai gaba da gabadashi wannanne yasa kowa yasa sunansa amma babu wanda yasanshi afuska yashara aduniyar jarumtane lokacinda yaji labarin wata sarka da take fadar sarkin aljanu Kal ana itawannan sarka takasance ansarrafatane da lu ulu gamida zinare da azurfa anyi itfakincewa awannan lokacin babu wani abu mai darajar sarkan tabbas da za a saida sarkannan da akema lakabida sarkar Girma to sai an azurta rabin mutanen duniya dakudin sarkan ansha yake yake akanta wanda akarshe takoma dunyar aljanu wanda hakan yahaifar da bala i da masifa adunyar aljanu rayukan aljanu miliyoyine su salwanta tabbas zaman lafiya yaikaranci tashe tashen hankula yayawaita wanda akarshe Sarki Kal ana yayaki jama ar aljanu damasifa yamallaki Sarkar Girma yagina wani katon gida wanda yai girman gari yaaje sarkar girma sanna aka sana anta wasu miya tattun hatsabiban tarkuna marasa adadi wanda duk jaruntar mutum da hatsabibancinsa kafin yakai ga sarkan Girma tokuwa sai yahalaka tunda aka gange sarkan girma awannan gida jarumanduniya da hatsabiban duniya dagaaljanu da mutune sunta kokarin zuwa wannan gida domin mallakanwannan Sarka amma babu wanda yainasara anyi itifaki cewa rayukan aljanu da mutane sama da dubucasa inne susalwanta akokarinsu na mallakar Sarkar Girma tun jarumai nakokarin zuwa harsu hakura kwatsam watarana da giyar mulki da sharafar jarumta dajiji dakai sudibi Sarki Kurungu yabigi kirji yakwara ihu yamike yabigi kirji yadubi fadawansa kuma dakarunsa yace lallai kowa yashirya nanda kwana bakwai zamu fuskanci duniyar aljanu lallai zamu nufi birni kib domin ina bukatan inmallaki Sarkan girma tirkashi bakidaya dakaru sufurgita sufuta ahayyacinsu sukama sambatu Sarki kurungu yadaka musu tsawa bakidaya sushiga taitayinsu yace lallai zamutafi birni KIB NAnda cikar kwanaki bakwai rana tazagayo dakarun da yawara guda dari bakwaine kacal zaiyi wannan tafiyadasu take yakama wani surkulle gamida sarkakkun kalamai daga kalmomin tsafi take kasa tafara girgiza samatai bakinkirin hankalin kowa yatashi kwatsam sai wain bididdigin aljani yabayyana asararin samani tamkar hadari girmansa da fadinsa bamusali yasauko Sarki kurungu yadubi aljani yace gaisheka alja Barku take yai umurni da jarumai daribakwai suhaye bakidaya suka haye bayan aljani Barku tamkar sun shiga katon jirgi ruwa ahaka sutsinci kansu abayan aljani Barku Sarki Kurungu yakwarara ihu yai kirari yai tsalle yahaye bayan aljani Barku yace muje zuwa wai mahaukaci ya haukura Aljani Barko yai sama yalolaka yabace bat acikin gajimare saida sukai kwanaki talatinsunaketa hazo da tsula gudu asararin samaniya haka suke wuce wurare iri iri wani gun suji tsanani sanyi tamkar zasu kame wani gurin kuma suji tsananin zafi tamkar zasu narke wani karon abarke daruwan sama kwatsam sai aljani barku yace yakai sarkin sarakuna lallai akwai matsala babba agabammu domin nanda wasu yan sa anni zamui karo da tawagar aljanu Sadauki Bahajur wasu aljanune mayu masu cin naman aljanu da mutane lallai sunada hatsari sosai tabbas sai mundage Sarki Kurungu yafashedadariya yace barsu sukariso ba abunda zasu tarar sai mutuwa yana rufe baki sai da tawagar aljani Bahajur sun iso wasu munanan aljanune bakake hakora zako zako halcensu kamar na kannika kaida ganinsu kaga mayu kallo daya zakaimusu tabbas bazaka sakeba Sarki kurunguyamike yakwarara ihu yace yaku dakaruna kuzauna kusha kallo lallai yau sai mayu sunsan sun hadu da sarkin mayu yafalfala dagudu akanaljani Barku tamkar yana bisa kankasa saida yakure tsawon aljani Barku yadaka tsalle yafada tawagar Bakaken aljanu nanfa yaki yasomaNIKUMA NAFIRGITA NALALLABA NA SHAFCE TO AI HEKENAN MUKWANA LAFIYA YAKIN DUNIYA PART 1[ J ] Sarki Kurungu ya afkama tawagar aljanunan da sara dasuka suma surufarmasa sukacame da azabebben yaki nanfa Kurungu yafara asaran rayuka yana kakkabo aljanu kasa matattu yakutsa tsakiyansu yai zarya sau uku tirkashi ai sagashi yaimusu mummunanan barna domin acikin kaso goma yakashe kaso hudu ranshugaba mayun aljanu yabaci yakwarar ihu yakama wasu hardaddun kalmomi yana wan sambatu gamida surkulle take sai aljanunan sukara girma datsawo kuma wani hatsabibanci kawai sai kowan aljani yarabu biyu nanfa sukara yawa sukara muni sukai kururu sutunkari Sarki kurungu ganin haka saiki kurungu yakwarara ihu yasabi wasukalamai natsafi yai wani girgiza kawai sai zaka girma yazama wani zabgegen basamuden kato yakwarara ihu yakara girgiza take wasu fuka fukai subaiyana akafadunsa dawasu mahaukatan wukake amadadin gashi wasu kumbuna zaro zaro sufuto ahannayesa dakafafuwansa take ya afkama aljanunnan dayaga dasuka take yafitinesu yagallabesu yashiga hallakasu kamar kwari cikin lokaci kankani sarki kurungu yai kaca kacadasu yakarardas sannan yadawo kan aljani BARKU YADIRE dakarunsa sumike suka saramai aljani Barku yakyalkyale dadariya yace tirkashi gabada gabanta wai aljani yataka wuka yace nagaida kurungu uban mazaje lallai kayi bajinta awannan yaki ammafa kasani ba ama fara yakiba tabbas kofa kawai ka kwankwasa sarki Kurungu yafashe da darriya yace nasani dama awannan tafiya dole inyi karo da maza kuma karo damaza badadi amma ni sarki kurungu sai na kara aljani Barku yafashe dadariya yakara lolakawa samaniya saida sukai tafiyar mako uku batare da sun hadu damatsalaba kwatsam suna cikin tafiya sai aljani Barku yaka layi gami da rangaji alamar zaifado kasa yayi iya kokarinsa amma saida yarikito kasa sarki Kurungu da mutanensa sudire shikuma aljani Barku yakama birgima yana gungure akasa yakama kauri take yakama da wuta yakone kurmus wohoho ran Sarki kurungu yabaci ganin babban hadiminsa wanda sude atare tunsuna yara yaugashi yamutu agabansa yakasa komai yakumbura yacika yabatse yatakar kare yakwaeara wani ihu wanda saida cajin wayata yajanye TO AIHIKENAN S *****YAKINDUNIYA Part 2A***** Lokacinda sarkI Kurungu yaga aljani Barku yakone kurmus sai yatakarkare yakwarara ihu wanda bakidaya dajin saida yahargitse bishiyoyi sufara kadawa koramu sukama tambal tambal dabbobin daji suka wrude dajin yacika da hayaniya koda Sarki Kurungu yakalli tokar Aljani barku sai yadora hannu aka jikinsa yasaki gababuwansa sudaina aiki sai yadurkusa bisa guiwowinsa yafashe dakuka tirkashi adaidai wannan lokacinne gungun tarin wasu jinsin jajayen aljanu masu kama dagarwashi wuta subayyana kowannensu yana rike da wasu misalan gatura masu tsanani kaifi da tsini hannu bibbiyu sutunkaro rundunar Sarki kurungu afusace damugunnufi shiko sarki kurungu kokallonsu baiyiba kawai yacigabane da rusa kukan bakin ciki koda jajayen aljanu sukariso sai su afkama dakaru dari bakwai na sarki kurungu wohoho lallai an gamu kuma hadin yai daidai domin wani bala en en yakine yakaure guri yahadu yakaure kura taturnuke ko ina karan takubba yayawaita masifa ta riski bala ii lallai ba abanzaba Sarki kurungu ya zabo wayannan zakakuran mayakaba guda dari bakwai domin lokacin da jajayen aljanunnan su bayyana inkadubi yawansu dakuma zubin kiransu sai kadauka ahaduwan farko zasui wakaci katashi da jaruman Sarki kurungu amma da akahadu akai kwaram aka gwabza karfi yahadu dakarfi karfe ya gogi karfe maza su hadu da maza sai lissafi yacanxa domin ruwan masifa da bala i da da dakarun Kurungu ke saukema aljanunnan yayi yawa sun wanzune suna masu sare musu kawuna dakafauwa gamida tsiresu a inda Mutuwa taitadiba tana watsawasu kiyama kai inkaga irin yakin da mutanen sarki kurungu sukeyi dagani kasan cikakkun jarumani kuma hatsabiba shahararru kuma matsafane domin wani irin salon yaki sukeyi inda sukasu mutum dari dai suzama gida bakwai tirkashi inda dari ta fuskanci Gabas tana zubAr da maza dari tafuskaci yamma tana dibar rayukan aljanu haka dari ta kalli kudu suna fafatawa inda dari sufuskanarewa suna tataburza sannan dari uku sushiga suna kewayawa suna kutsawa cikin aljanu suna fake cikinaljanu gamida feke kawuna mazajen aljanu kai koda masifa tai masifa bala i nawan zuwa kai aikoda shugaban jajayen aljanu yafahimci tunda akafara wannan yaki jama arsa kawai ake kashewa sai yatakarkare yakwarara ihu yakama wasu maganganu cikin yare na aljanu waiye hoho aisai bakidaya rundunan aljanu susauya salon yaki suwatsar da gaturansu wasu bakaken takubba subaiyana ahannayensu tikarshi aisai yaki yakoma sabo nanfa masifa ta auku lissafin yaki yasauya jajayen aljanu surikita rundunan mutane suhausu dasara da suka kafin kace haka sunkashe mutane gomadankari aikoda Sarki Kurungu yakyalla ido yaga anakashemai mutane hargoma sai yamike yakwarara ihu yai girgiza jijiyoyin jikinsa sumotsa sukai burdu burdun idanunsa suka juye sukoma farare tas gashin kansa yamimmike yakara surfafa ihu yamikar da hannayensa take wasu gatura na karfe subaiyana ahannayensa yafalfala aguje tunkafin yakarisa yatakura yajefa gaturannan gaturan sutafi aaune sufada cikin rintsin mayaka hodijan tsafi gaskiyan maishi ai sai gaturannan sushiga dagar gazan jajayen aljanuabin bakyan gani saida takugaturannan suhallaka aljanu dubu uku wani abin mamaki shine duk lokacinda gaturan sutunkari mutum sai sukauce amma suna gamuwa da aljani to sai lahira sarki kurungu nakarasowa cikin filin daga sai gaturannan sudawo hannun hannunsa woohoho ai yakwarara ihu mai tsorata maza bisa tilas dakarunsa suka jabaya shikadai yafuskanci jajayen aljanu suja tunga sukara gyara tsayuwa shima yagyara tsayuwa yatada kura yai wani burza yaja baya yafalfalo damasifan gudu yana kwararara ihu suma suka ja baya taku bakwai surugo aguje sutunkari Sarki Kurungu suna wani karajin fusata za ai haduwar mutum da aljan KAI ABOKAINA IRIN WANNA IHUN DA ALJANU KEYI GASKIYA BAZAN IYA KALLOBA NAFECE KUMA KARKUCE INDAWO

An dauko wannan littafi daga shafin www.dlhausanovels.com.ng ku ziyarci shafin na www.dlhausanovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya

Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,

Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan
Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490

A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,

Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu

Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC

Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from www.dlhausanovels.com.ng
You can download more hausa novels there
Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online
It is free we do not charge for uploading novel
Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services

Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us

Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it

Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT

An dauko wannan littafi daga shafin www.dlhausanovels.com.ng ku ziyarci shafin na www.dlhausanovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya

Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika

Please Login or Register in order to submit comment