Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register


An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels

: BABBAN YAYA
An dauko wannan littafi daga shafin www.dlhausanovels.com.ng ku ziyarci shafin na www.dlhausanovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya

Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,

Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan
Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490

A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,

Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu

Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC

Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from www.dlhausanovels.com.ng
You can download more hausa novels there
Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online
It is free we do not charge for uploading novel
Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services

Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us

Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it

Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT

Writing By Amnah El Yaqoub





Dedicated to
Fauziyya S Madaki
Real Esha

Special Gift to Its Sadeek


Bismillah... Ina farawa da sunan Allah Mai Rahma maijin qai, BABBAN YAYA qirqirarran labari ne, yanda muka fara wannan littafi lafiya, Allah yasa mu gama lafiya, Allah ka haneni da rubuta abinda bazai amfani al'ummah ba, idan anga labari yayi daidai Dana rayuwar wata, to akasi aka samu, Allah yasa mudace

A taqaice, Babban Yaya labarin soyaiya ne,yan'uwan juna makusanta, kwatsam soyaiya tashiga tsakanin su, akwai rikitarwa aciki, saikin karanta Zaki gane wanene masoyinki na gaskiya acikin samarin ki? Saikin karanta Zaki gane ta wacce hanya ne namiji zaibi Dan gujewar auren yarinyar da bayaso salin Alin batare da damuwa ba? Abubuwan sunada yawa, koda kudin ka saida rabonkaπŸ’ƒπŸ’ƒ

PAID BOOK

1&2


"Wato Alhaji Umaru Naga alama saboda Ina zaune aqauye ban'isa na fadi magana a aiwatar da abinda nayi umarni ba"

Daga d'ayan bangaren Wanda aka kira da Alhaji Umaru yadafe goshinsa,(πŸ€¦πŸ»β€β™‚οΏ½?) waye Kuma yata6o musu Babban yayan nasu?
Ajiyar zuciya ya sauke tareda gyara Zaman wayar dake kange a kunnansa yace "Yaya meyake faruwa? Kaida waye?"

"Au tambayata ma kake meyake faruwa? Umaru dakai da Usmanu kunfi kowa sanin abinda kuka aikata, tayaya zaku bar yaro agabanku shekara da shekaru yana zaune babu iyali? Shekara d'ai d'ai har shekara Talatin da shida NAUFAL yana zaune yana abinda yaga Dama yaqi aure, kukuma saboda ku 'Yan boko ne kun rabu dashi yana abinda yaga Dama, ni danake Nan qauye ba zance kuyi abu kuyiba, a'a Sai abinda kukai niyya"

Cikin ladabi Alhaji Umar yace "Wallahi tallahi Yaya Bahaka bane, mu kanmu muna bakin kokarin mu akansa, bamu San Yaya zamu yi masa ba, munyi munyi dashi yakawo yarinyar dayake so Amma yaqi"

Cikin fishi Wanda aka kira da Yaya yace "zancen banza zancen wofi, kunje can qasar turawan dayake rayuwa ne kunganshi akame awaje daya? Tayaya yaro baligi irin NAUFAL zaku zuba masa ido? Yafada muku shi gunki ne kokuma dutsi da bazai buqaci mace ba? Jinake haka muke ganinsu a TV tsangal tsangal da gajeran wando suna tamola Waida sunan sana'ah, to Kana katse wayata, ka kirashi kafada masa cewa ni Abubakar yayan mahaifinsa Kuma me iko da fada aji acikin dangin Arabo, nace yakira yarinyar Amini na su daidai ta, idan ma 'yar bokon yake nema irinsa itama yarinyar ba'a qauye tatashi ba bare ya rainata kamar yanda ya raina ni, zan sako Maka lambarta katura masa "

Alhaji Umar yace"To Yaya, insha Allah zanyi yanda kace, ga Alhaji Usman ku gaisa"
Yafadi maganar yana kokarin janye wayar daga kunnansa
Cikin sauri Yace "A a, barshi kawai, ai duk bakinku d'aya" daga haka yakashe wayar sa.

Alhaji Umar yadago Kansa ya kalli Usman batare da yace komai ba, kallo daya zaka musu ka tabbatar su din jini daya ne, kama suke da juna sosai kamar harta 6aci, basuda jiki sosai kasancewar su asalin buzaye

Alhaji Usman yace"magana yake akan Naufal ko?"

Alhaji Umar ya daga masa Kai, sannan yafada masa yanda sukayi dashi, batare da damuwa ba yace" Babu damuwa, katura masa number kawai, ya kira yarinyar, idan munyi sa'ah Wannan Karon andace shikkenan, mu Dama fatanmu ace yayi auren "


*** ** ***


Sanye yake da Jessy ajikinsa fara tas me dogon wando,kafarsa na d'aukeda farin kambos, kunnansa d'aukeda wani Bluetooth fari me shegen kyau, jogging yake Kansa aqasa, Amma duk da haka mutane Sai magana suke masa yana daga musu hannu kasancewar sa marar son surutu, wayar sa tafara qara yana duba Screen din wayar yaga ansa My Dady, dole ya dakata da gudun dayake tareda riqe waist dinsa yana Dan qaramin haki, dago Kansa yayi tareda amsa wayar bakinsa d'aukeda sallama

Sai a lokacin nasamu damar qare masa kallo, fari ne sosai ko'ina na jikinsa farine tass, hadaddan Gaye ne na fitar Hankali, yanayin tsarin idonsa ma kadai ya'isa yasa Nan take yasiye zuciyar yanmata, inde ka Kalle shi sau daya, dole saika sake waigawa domin sake kallon sa, gaida mahaifin nasa ya farayi Amma yana magana dimples dinsa suna futowa.

Alhaji Umar yace "akwai number wata yarinya Habiba Dana turo ma yanzu, kakirata ku daidaita, Yaya ne yace abaka number, yarinyar aminin sace, idan kun gama daidaita wa saika samu lokaci kadawo gida a tsaida maganar aure, banason jin wata magana Kuma daga baya"

Yana gama yimasa Wannan jawabin yakashe wayarsa

yasan dalilin dayasa Dady yakashe wayarsa, duk lokacin dasuka masa maganar aure Sai yasan irin maganar da yayi yaroqesu akan su qara masa lokaci, to lokaci har yanzu shiru yaqi zuwa πŸ€”

Wata zazzafar is'ka ya furzar daga bakinsa, cikin wata daddad'ar murya wadda daqyar zakaji meyake fad'a yace "ita Kuma wannan ta wacce hanya zanbi narabu da'ita?" wani tunani yayi, Nan take ya dauki shawarar zuciyar sa yayi Dialing number da'aka turo masa ta Habiba

Bugu uku ta dauka, batare da tayi sallama ba tace "Hello waye"

Sai yaji wani iri banbarakwai, kamar shi ace yakira waya Ana tambayarsa waye, Kuma ba kowa ke tambayar sa waye ba Sai budurwa, shida a koda yaushe yanmata sune suke bibiyarsa saboda su samu kusanci dashi Amma basa gabansa,ya tabbatar inda ace tasan asalin Wanda yake kiranta to babu makawa zata Iya zuba ruwa aqasa Tasha saboda tsananin murna.
Jin shiru har yanzu ba'ayi magana ba yasa tace "Hello wake magana ne?"

Saida yaja wasu second sannan yamotsa pink lips dinsa yace "Sunana Naufal Umar Arabo"

Saida taji yace Arabo sannan tace "Okay, ko kaine Yaron Dan'uwan Alhaji Habu Wanda yake zaune a qauye?"

"Yes"
Shine kawai abinda yace

Daga Nata bangaren tace "Ai sunyi magana da Abbanah, yace zai turomin d'ansa naganshi idan yamin Sai manya su shiga cikin maganar" (πŸ˜±πŸ˜‚)

Baqin ciki ne yakama shi,ya yatsina fuskar sa, yaso ace yayi tozali da wannan yarinyar yaga me take taqama dashi har haka, har shi zatacewa idan yayi mata? Takuwa San waye shi?
Lumshe Idonsa yayi, hakan da yayi saiya Bawa gashin Idonsa damar bayyana, Zara-Zara dasu dogaye kamar na mace, fuskar Nan tasa murtuk babu alamar fara'ah yace "Yes, nine"

Itama tace "Sai cewa kake kaine kaine, kakasa cewa komai, kana magana kamar me koyon magana, yanda baka son had'in Nan nimafa baso nake ba, karkayi tsammanin sonake, kanamin magana daqyar Kanata wani yauqi saikace mace, fadamin zakai yaushe zaka zo naganka, bawai Kiran waya ba, saboda ni ba'acemin zaka kirani ba, ance min ne zaka zo naganka ko zakamin "

Zuwa wannan lokacin Kam ransa yagama 6aci,(πŸ˜–πŸ˜–)
Amma wani bangaren na zuciyarsa dad'i yakeji, ko babu komai yasan yarinyar bazata bashi matsala wajan rabuwar su ba tunda itama bata so, sassauta muryarsa yayi, ya dedeta Kansa, kamar me koyon magana yafara magana a rarrabe"Mene..ne yauqi?"

"Uhm au bakama San menene yauqi ba? Tabdi jam, Allah kenan mehada budurwa da samari Kala Kala,yau Kuma da Wanda nahadu kenan, nikuwa naso ace naganka bawan Allah,Inga mutumin dabai San menene yauqi ba, kafadamin yaushe zaka zo?"

Be damu da wannan dogon surutun Nata ba, asali ma so yake su qarqareta ayau dinnan kowa yakama gabansa, ahankali yace"ni... ni banda lokacin zuwa"

Daga Nata bangaren tace "to Ahaka zamuyi aure bakada lokacin kaina?"

Wani irin murmushin gefen baki yayi, cikin ransa yace anzo wajan, a fili kuwa saiyace "Banda lokaci, Ina wajan neman kudi, kinsan kudi sune gaba da komai, ni kaina banda lokacin kaina bare in samu lokacin wani, kawai neman kudi nasa agabana"

Tace "Okay, kana so kacemin kudi sune abin so fiye da komai arayuwarka?"

"No, ba rayuwa ta kadai ba, harma da rayuwar Wanda yake kokarin shigo wa cikin rayuwa ta, kudi sune gaba da komai awajena"

Tace "to Malam Naufal Umar Arabo, inban manta ba haka kacemin sunanka ko? to Ina ganin Bama Sai kazo ba, kayi zamanka kawai, Allah yahada kowa da rabonsa" qit takashe wayar ta

Baisan lokacin da wani farinciki ya lullubeshi ba, har dimples dinsa suka lotsa, cikin murna yace "yessss" sannan yaci gaba da Jogging dinsa


*** ** ***
Labarinsu


Alhaji Abubakar Arabo,Alhaji Umar Arabo, dakuma Alhaji Usman Arabo, uwarsu daya ubansu daya, 'Yan asalin qasar Niger ne, buzayen dasuke rayuwa cikin Sahara, sunada mutuqar dukiya da Tarin shanu, sau Tari mutanan Nigeria suna zuwa wajan su siyan shanu domin su kiwata su siyar dasu da tsada, kasancewar inda suke rayuwa babu isasshen abincin dabobi, daga baya sukai hijra suka dawo Nan Nigeria, sukaci gaba da juya dukiyar su har Allah yayi mata Albarka suka zama manyan masu kudi da ake damawa dasu ayau.

Alhaji Abubakar shine Babba, suna kiransa Baba Habu, yana zaune a Jigawa shida matarsa da yaransa maza guda biyu sa'annin Naufal ne Amma sun dade da aure harma sunada yaransu

Saikuma Alhaji Umar shine na biyu, suna kiransa da Dady yanada Yara guda bakwai, NAUFAL shine Babba, Suna kiransa da Babban Yaya, Sai Yan biyu maza,Sa'ad da Sa'eed, Sai Anty Maryam, tayi aure tanada yaro daya,me sunan Naufal, suna kiransa da junior, Sai Yan biyu mata, intisar da ihsan, saikuma yar auta WAHEEDA

Sai Alhaji Usman Arabo, shine Dan qaramin su,suna kiransa da Uncle Usman, Allah bai bashi haihuwa ba, yanada matarsa guda daya, suna cemata Hajiya Anty, ma'aikaciyar Asbiti ce

Dukansu mutum ukun Nan Abubakar, Umar, Usman, suna kyautatawa junansu, matansu na can Niger sune de har yanzu atare dasu, suna mutuqar girmama juna, gaba dayansu kama suke da juna daga matan, har mazan, dakuma yayansu, duk fararene, saide na wani yafi wani, Amma dukansu farare ne, kana ganinsu zaka San buzaye ne na asali, tsabar kyawun dasuke dashi ne yasa ake Kiran Family din nasu da Suna (Arab Family) , Amma dasuka dawo Nan gida Nigeria, Sai Yan Nigeria suke cewa Arabo Family πŸ˜ƒ

Kamar yanda nafada Naufal shine babba acikin yaran Alhaji Umar (Dady) shekararsa Talatin da shida, beyi aure ba, iyayen sunaso yayi aure kasancewar sa babba a gidan, yana kula da qannansa yanda me karatu baya zato, shiyasa ko wani abu ne yafaru saide kawai iyayen su fada masa, shikuma zai warware komai, kwata kwata baya wasa da yan'uwan nasa, idan kaga ya ware yana fira wasa da dariya to da abokan sa ne, musanman yayan Baba Habu dasuke jigawa, koda yaushe fuskarsa a daure take, bala'in tsoransa sukeji musanman qannansa mata, kana laifi kadan zai daka Maka tsawa, shiyasa suna ganinsa kowacce take shiga taitayinta, babu ruwansa duk wacce tayi masa laifi zaneta yake, suna komai duk abinda suke so, saide yahanasu kula Samari, yahanasu saka mayafi, saide Hijab, Kuma suna kiyayewa mutum daya ce take bashi ciwon Kai acikin qannansa, itace auta WAHEEDA, itace tafara kiransa da BABBAN YAYA, daga Nan kowa yake fada masa, babu Wanda zakaji yace Yaya Naufal, saide BABBAN YAYA.πŸ‘ŒπŸ»

Cikakken Dan qwallon qafa ne Wanda akeji dashi afadin qasar tamu ta Nigeria dakuma kewayen ta, lokacin daya gama Degree dinsa na biyu, (Masters) iyayen sunso yayi aiki a qarqashinsu, domin su qara habbaka kasuwancin su, Amma BABBAN YAYA yace inaaa! Shifa harkar qwallo zai fara, saboda Dama can tun yana qarami abinda yake so kenan, daga Alhaji Habu na qauye har mahaifin sa Alhaji Umar Qin bashi goyon baya sukayi, daqyar Alhaji Usman yadage akan su harya shawo kansu suka yarda, da farko Yan kano pillars yabugawa Ball, daga baya wata qasar ta daukeshi, daga Nan Kuma yakoma qasar Spain, Bayan wasu shekaru yakoma qasar dayake a yanzu yana buga musu Ball inda yake daukar albashin sa Mai tsoka duk sati.

Lokacin dazai fara Ball babu sunan daya fad'o masa Arai sai Wanda fitnanniyar qanwar sa WAHEEDA tasaka masa, BIG BROTHER, shiyasa jikin Jessy dinsa, p-cap dinsa,sunan BIG BROTHER ne ajiki, Yan gari, Yan unguwa, fan's dinsa na ko'ina kowa Big Brother yake ce masa, inde yashiga cikin jama'ah kawai haquri yake, saboda yanada masoya masu dimbin yawa, kawai Yan gidansu ne suke kiransa da BABBAN YAYA, Amma jama'ah kowa da kowa Big Brother ake ce masa,yanmata kuwa kullum cikin kiransa suke, yana alfahri da hakan.

Iyayensa sunaso yayi aure saboda shekaru irin nasa, Amma yace shi har yanzu baiga wacce ta kwanta masa ba, tun yana qarya yana cewa zai kawo wacce yake so aqara masa lokaci, har iyayen suka dawo daga rakiyarsa suka fara hadashi da yaran abokai da Kuma yan'uwa, Amma har yanzu duk wadda aka hadashi da'ita yasan irin dabarar dazai mata Dan su rabu cikin hikima, kamar de yanda ya kasance a tsakanin sa da Habiba Yanzu πŸ€ͺ
Duk cikin yanmatan da'ake hadashi dasu babu wadda yataba baiyana mata Kansa, inde yakira wayar su yana fada musu cewa sunansa Naufal, baya cewa Big Brother saboda yasan cewa muddin yafadi wannan sunan, to babu Wanda bai sanshi ba, wannan kenan




*** *** ***



Tafe suke hannunta dauke da wani yaro Wanda bai wuce shekara uku ba, Sanye take da hijab pink colour, me hula, ta gaban hijabin kadai zaka iya sanin cewa Allah yayi mata tarin suma da yawa, kasancewar wuyan yayi mata yawa kadan, yarinya ce bazata wuce 18 years ba, ranar datake dukansu itada Yaron yasa ta yatsina fuska, Amma duk da haka kyawun fuskarta yana Nan, duk da babu kwalliya kodaya a fuskar, Sai haki take da alama Yaron yamata nauyi, suna zuwa bakin get din gidansu ta sauke Yaron, kudi tafuto dashi daga cikin handbag taware 5k tabawa Yaron sannan taja hannun sa suka qarasa gida, babu kowa afalon nasu, Kai tsaye dakinsu tashige, mutum uku ne zaune a Dakin, 'Yan biyu daya tana yiwa daya tsifa, saikuma wata Babba tana duba littafin azkar, gaba dayansu kama suke da juna, kana ganinsu kasan jini daya ne, hijabin jikinta ta cire ta wullar dashi anan, lokaci daya tsantsar dirin jikinta ya baiyana, mace ce har mace, gata yar qarama Amma Allah yamata baiwar kyakykyawan jiki.
Yaron yatafi da gudu wajan mamansa yace "Momy munje Kuma anbamu kudi da yawa, Nima anty Waheeda tabani, kingani?" ya qarasa maganar yana nuna mata kudin hannun sa

Murmushi tayi tace "Lalle Waheeda kice kudi kuka samo keda junior"

Zama tayi a bakin gadon tareda cire ribom din kanta, hakan yabawa dogon gashinta damar zubowa gadon Bayan ta

Tace "eh Anty maryam, dubu goma aka bamu, shine naraba mana"

Kafin wadda aka kira da Anty Maryam tayi magana, daya daga cikin Yan biyu tace "Qarya kike Waheeda, Anty wallahi qarya take, kawai cutar Yaron tayi, kamar bakisan halin Waheeda ba, Allah qwace masa kudin zatayi"

Cikin rashin kunya ta kalli me maganar, duk tsananin kamar dasuke kasancewar su identical twins Sarai Waheeda take ganesu, tace "to Ihsan na qwace din, ai tare aka aikemu da junior din ko? Kiyi abinda zakiyi"

Anty Maryam ta kalleta tareda riqe ha6a, tace "lalle Waheeda wuyanki ya'isa yanka, yayun naki kike fadawa haka?"

Wadda ake yiwa tsifar ce tatashi ta nufi Waheeda tace "Na hanaki daukar min hijabi na Amma kinqi yarda ko, tsabar masifa da naci kinada hijabai bazaki saka ba kin goge su kin 6oye saide ki dinga daukar namu kina sakawa saboda Kin raina mana Hankali, nayi Miki last warning karki sake daukar min hijab, sannan Ihsan ba sa'arki bace karki sake mata rashin kunya "

Cikin tsiwa tace"wallahi yanzu nafara saka hijabi saide in bangani ba, baki Isa kimin in qyale kiba intisar"

Anty Maryam tace "Waheeda kanki daya kuwa? Dama rashin kunyar Taki haryakai haka?"

Ihsan tace "rabu da'ita Anty, ai taga kanmu daya ne,Mp muke itama shi take yi, brezia muke sakawa itama shi take sakawa,taga ta girma tafimu nonuwa, tayi tsawon qafa, Gani take shekarunma daya muke da'ita, yau kuwa zakici ubanki, zaki San kin mana rashin kunya"

Tashi tayi tsaye ta kallesu ta watsar tace "ai Dama ba yau kuka fara hademin Kai ba, Naga su Sa'ad ma qarewa, balle ku Yan biyun qarshan zamani, qarqari kumin taron dangi kumin duka, to bazaku birgeni ba saikun kasheni kun kaiwa uwata gawata"

Anty Maryam tatashi tsaye tace "lalle Waheeda kullum girma kike kina sake zama marar kunya, zan fadawa ummah abin naki yayi yawa, yanzu har takai su Yaya Sa'ad ma sunansu kike fada" tana fadar haka tafice daga Dakin cikin fishi


Ihsan ta kalli Intisar, basu tsaya wata wataba suka rufe Waheeda da duka, intisar takama gashin ta tanaja, Ihsan kuwa Sai dukanta take, dama haka suke, hadin kaine dasu sosai, duk lokacin da Waheeda tamusu rashin kunya haduwa suke suyi mata shegen duka

Hajiya Anty ce tashigo gidan, tana Sanye da kayan likitoci komai fari, tana Sanye da glass fari a'idonta, kana ganinta kaga mace yar Gayu, da alama daga Asbiti take wajan aikinta, da kukan Waheeda tafara cin Karo, Kai tsaye Dakin nasu ta nufa, 'Yan biyu suna ganinta suka daina Dukan Waheeda, haka tadago kanta idonnan yayi jajir tace "Kuma wallahi saina Rama, bashi kuka dauka"

Hajiya Anty batace dasu komai ba taja Dakin tarufe, tawuce wajan ummah, Sai a lokacin ummah tashigo Dakin nasu taji ba'asin fadan, da alama Hajiya Anty ce ta turo ta, Dan lokacin dazata shiga Dakin nasu ma mita take tana cewa fitinar Waheeda ta isheta☹️



Da yamma sukai baqi daga qauye, a lokacin hajiya Anty tana nan bata tafi ba, megadi ne yayi musu jagora har cikin falon gidan, Anty Maryam de Takoma gidanta, Amma gaba dayansu yaran suna Nan, 'Yan biyu suna zaune waje daya suna ganin wani abu a wayar ihsan, Waheeda kuwa tana zaune agefe cikin kujera ita daya, tunda 'yan'uwan suka daketa taketa kumburi, taso ace ummah da Hajiya Anty basa Nan, dasai tahada wa 'yanbiyu wata muguntar da bazasu taba mantawa da'ita ba, yanda ta zauna waje daya tayi shiru zaka rantse wata kamilar yarinya ce, saboda ta nutsu sosai kamar ba'ita ba,itace tafara tashi takawo musu lemuka da ruwa, sannan ta gaishe su, aikuwa suka amsa cikin girmama wa, tasake komawa wajan zamanta ta zauna, Ummah takalle su cikin sakin fuska tace "Saide kuyi hakuri fa, Amma bamu gane Kuba"

Namijin ne yafara dariya yace "Hajiya ai 'yan'uwan kune daga wani gari Kaburma, ai Alhaji Habu ne yace duk lokacin da muka shigo Garin naku, mu qaraso mu gaisa nida iyalina, aini kamar qani nake awajansa" yafadi maganar yana Kallan Waheeda

Waheeda ta Kalle shi dakyau, Bama qanin bane kenan, kama ce, tunda yace kamar qani yake a wajan Baba Habu, Kai Shima de Baba Habu da yayime-yayime yake, ita Kuma umma Sai washe musu baki take

Hajiya Anty tace "Amma kun kyauta wallahi, ai Gara daban wuce gida ba, yanzu gashi munga juna"

Matar datake gefen namijin tace "Eh wallahi, ai Baba Habu akwai zumunci, Amma wadannan Yan biyu ne ko?"

Ta qarasa maganar tana Kallan Yan biyu

Dariya sukayi sannan suka amsa mata, Tajuya tasake Kallan gefen da Waheeda take zaune tace "kekuma fa qawata kinyi shiru babu ruwanki da kowa"

'yanbiyu ne suka hada ido suka kwashe da dariya, Wai Waheeda ce babu ruwanta, shine abunda ya basu dariya

Matar tace "yakuke mata dariya, ai Naga tayi shiru da alama zatayi hakuri,qawata ya sunanki?"

Waheeda tayi murmushi tace"sunana Waheeda"

Kallan mijinta tayi tace "Baban Halima kaji suna me dadi, idan nasake haihuwa Nima ka sakawa yarmu irin wannan sunan"

Dariya yayi, ya kalli Yan biyu, ya kalli Waheeda, yace "yanzu Nan duk 'ya'yanane?"

Dariya sukayi kawai, babu wadda tace masa komai, yace "toku Yan tagwaye wayece babba acikin ku?"

Ihsan tace "nice babba, Sai Intisar, Sai qanwarmu

Please Login or Register in order to submit comment