Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

shi da kallo kaman yanda shima Yaya na yabi sa da kallo sai faman gyara mayattacen binjimar sa ta tshohuwar shaddar sa fara ce amma saboda tsufa har ta koma ruwan toka .



"Allah sarki Allah baiyi zamu had'u da Baba ba duk shekaru nan ba sai yau" naji Yaya na ya katse min tunanin da nake.


Murmushi nayi ina gyada kaina.


"Amma nima ban kyauta ba da ban tab'a tambayan shi ba all this while,wallahi yanzu dana gan shi sai naji ban kyauta ba sam" ya kara fad'a cikin damuwa sosai.



"Laa! Kada ka damu Allah ne baiyi zaku had'u ba tun farkon amma yanzu daya so ba gashi kun had'u ba" na bashi amsa ina murmushi.


Shiru kawai yayi dan shi a tunanin shi rashi da iyali ne yayiwa Baban yawa shiyasa ya zama haka bai san cewa duk wani yanayi da hali da mutum zai gan shi a ciki shi ya jefa kan sa ba.



Har muka gama hiran mu a ranan yana cigaba da nuna min rashin jin dad'in sa ni kuma ina nuna masa ba komai da zai tafi dubu ashirin ya bani wai in bawa Inna ta ajiye min in case wai ko goben ba zai samu dawowa ba, na nuna mishi muna da komai ba sai ya bani kud'i ba amma yaki karb'a saima shopping bags daya maida farilla wajan kawo min su ya lodo min kusan su 3 yana complain wai dole ya nemawa inna fridge ko dan saboda rana irin ta yau, kasancewar na saba kullum sai ya kawo min ice cream na sha toh gashi gobe baya nan da Inna tana da fridge sai ya sayo dayawa a saka min a ciki ko na kwana nawa ne.



Amma tunda ya bani 'yan canji a hannu in naga ba zan iya hakura ba sai inje today's ko sidis in sayo abina in sha tunda na saba sha.


Ni dariya nayi ta masa ganin duk ya damu akan wai kawai ba zan sha ice cream gobe ba, in ba dan ba dan ba a da ina na san wani ice cream a rayuwa ta, dan gobe kad'ai ban sha ba me zai same ni, bai kyale ni.ba sai da nayi masa alkawarin zan je in sayo a today's d'in sannan ya hakura mukayi sallama ya tafi tare da bani hakurin inda zai tafi babu service dan haka ba zamu waya kaman yanda muka saba ba.



Haka ya wuce duk sai naji na damu domin sosai na saba kullum sai naji muryan shi nake iya bacci yanzu haka muryan sa shi ke tada ni a bacci.


A tsakar gida na tarar da Gwaggo Aisha da wata 'yar figaggiyar kaza guda d'aya ta saka a tire ta d'auko sharb'eb'iyar wuka sai faman kacan canawa take tana ta hura hanci,ni dariya ta bani ban ma kalli inda suke ba nayi shegewa ta d'akin mu anan na iske Baba yana zaune yana zaman jiran in shigo yaji karin bayani dan duk yanda yaso ji Inna kin bashi had'in kai tayi saboda ta san ba dan Allah yake neman sanin ba.


"'Yar albarka har kin shigo kenan"


"Eh Baba sannu da hutawa" na amsa ina ajiye kayan hannu na kusa da Inna amma kud'in yana hannu na cikin hijabina.


Ko kallon kayan Inna taki yi ta cigaba da d'inkin hulan ta hankali kwance, gefe na samu na zauna shima Baba zama ya gyara yana jiran Inna ta bud'e yaga menene a ciki amma ta basar, can daya gaji da zama ya ce," 'yar albarka me kika shigo mana dashi ne?"



"Kayan dad'i ne Baba na" na bashi da murmushi akan fuska ta ina kallon Inna ta gefen ido da take harara ta.



"A'a toh...toh... Wato Bintu yau kuma rashin kirkin ne ya tashi muna ji muna gani zaki hana mu kayan dad'i?" Cewar Baba cikin raha, Inna dai bata ce k'ala ba ta cigaba da d'inkin hulan ta.


"Mu kam bama zuciya kuma ba inda zamu je sai mun ci kayan dad'i ko 'yar albarka?"


Dariya nayi ina kallon Inna da tayi kicin-kicin da fuska dan ita al'amarin Baban mu sosai yake bata takaici da haushi, ya za'ayi ace wai kana ganin 'yar da ka haifa ta shigo da kaya masu yawa haka kuma kasan daga hannun saurayi ta samu, baka damu da binciken waye shi ko kuma ya akayi ya bata ko meye tsakanin su ba, saima jiki na b'ari kake son handame abinda ta kawo koma menene kai ba damuwar ka bane.



Cike da takaici halin sa da surutan sa daya ishe ta, ta bud'e d'ayan jakan da ta riga ta gane tambarin su kasancewar kullum ana kawowa, ba tare da ta lura da ko kaza nawa ne a ciki ba ta d'auko guda d'aya ta saka mishi a wata leda da babban roban juice d'aya duk ta had'a ta mik'a mishi .



Ba batun fushi ko zuciya yasa hannu yana washe baki ya amsa har zai fita na tsaida shi nima na jawo d'ayan jakan sanin cewa nawa shi saboda kullum aka kawo Inna bata tab'awa tarkacen kayan zaki na ne a ciki, roban ice cream babba dasu chocolate dasu snacks ne a ciki nima na cika mishi leda na mika masa harda dubu biyar na saka masa a kasan ledan bayan na faki idon Inna.



Ai Baba yanda kasan yayi hauka haka ya koma saboda murna dan akan idon shi na had'aa mishi kud'in yayin da Inna kuma hankalin ta yana kan hulan ta saboda dukkan mu haushi muke bata.



Fita yayi yana baza babban rigan shi, zai wuce Gwaggo Aisha ta tare shi da cinyar kaza a hannu cike da jin kai ta ce," Mallam tsaya ka saka albarka kaga 'yar ka Hajara Allah yayi ta samu saurayi mai mota, shine daga zuwa zance ya kawo mata gashasshiyar kaza na rabawa yara shine nace bari kai ma in kawo maka ka saka albarka".



"Amma Aisha kike kowa? Wallahi kin matukar raina ni, ni zaki tara ki tsamma wannan abu sai kace kin samu wani kwadayayye ko maye, toh tsaya kiji ni na fi karfin wannan abin naki mai kama da cinyar fara.


Dubi kiga inda ake cin arziki da kaza kuma aka san darajan miji ba watsatsu irin ku ba" yana magana yana nad'e hannun babban rigan sa nan manyan ledojin suka bayyana.




" Kinga wannan dakwaliyar kaza ce ta gidan gona da taji gashin inji ga lemon roba mai dad'in gaske, sannan kinga nan kuma kayan makulashe ne da sai in rantse da Allah ko wuka aka d'aura miki baki tab'a ganin irin su ba balle ki san sunan su, bayan nan kalli kasan kiga" yace yana nuna mata kud'in kasan ledan sannan ya mike tare da mai da komai cikin ledan ya cigaba da masifa," na dai gaya miki kada ki kara tare ni da maganan banza ko ranki yayi mugun b'aci ba abinda kika iya sai shegen surutu tsiya " nan ya shige d'akin shi ya bar Gwaggo Aisha da mataceccen jiki.



Tabbas sai sun sake shiri babba ma kuwa dan bata tab'a sanin haka Bintu tayi nisa ba,gaskiya dole ne ta nemi shawaran aminiyar ta dan samun mafita ko kuma suna ji suna gani wankin hula zai kai su dare.



Dariyan yaran gida ne ya dawo da ita hayyacin ta, sun had'a kai kusan su biyar suna mata dariyan yanda Baba ya bar ta da cinyar kaza a hannu, bata kula kowa a cikin su ba ta shige d'akin ta dan ji tayi gaba d'aya jikin ta ya mutu.



A d'aki kuwa Baba yana fita Inna har ta juyo da niyyan yi min fad'a dramar su da Gwaggo Aisha ya dakatar da ita, bayan sun gama ya wuce ya bar ta na ce," haba Inna ta, me yasa kike fushi haka yanzu fa kin zama 'yar lele a gidan Mallam".



Waje na fice da gudu da roban ice cream d'ina d'aya a hannu ina dariya ganin Inna ta shiga neman abinda zata buga min a kusa da ita bata samu ba.



Ciki na shiga b'angaren su Dije muka zauna sha muna hiran Yaya ina bata labarin yanda yau muka rabu da juna dan kawai zaiyi tafiyan kwana d'aya.


"Hmmmm gaskiya ke kam Zareefa Allah ya baki, ki ga yanda yake mutuwan son ki kuma yake nuna kulawa yake tarairayan ki, a gidan ku ma ya kula dake haka ina ga ya aure ki ya killa ce ki a gidan sa abin ba magana". Cewar Dije kenan.



"Allah gaskiya soyayya akwai dad'i Dije, kin san yanda nake jin sa a cikin raina kuwa? Allah ya nuna min ranan auren mu" duka Dije ta kai min a gadon baya na tana dariya tace.



"Shegiya Zareefa har nawa kike da zaki zauna kina maganan aure?" Murkud'a mata baki nayi ina ," eh d'in kema ai shirin yi miki ake nan da shekara d'aya idan munyi sauk'a, toh nima ina gama secondary shekaru biyu da rabi suka rage za'ayi mana ni da Yaya naaa" na karasa ina rungume hannye na biyu a kirji na tare da rufe ido nayi baya kaman zan fad'i Dije ta taro ni tana tafa hannu ta ce," ke yarinyan nan haka kika zama baki tafasa ba zaki kone mana mu shiga uku?"



"Wai da kike fad'an haka shekaru nawa kika bani da kike ta cika baki tun d'azu , ina biyu ne kawai harda wani ........ zaki kone mu shiga uku" na fad'a cikin kwaikwayon muryan ta, ta kai min duka na goje haka muka cigaba da shan ice cream muna hiran mu cikin raha..


Dije itace babban 'ya a wajan Maman Dije ta bani kusan shekaru biyu amma hakan bai hana mu zama kawaye ba domin yaran gidan dukan su iyayen su sun hana su wasa dani tun muna yara dan haka babu wani shakuwa ta 'yan uwan taka tsakanin na dasu sai dai kallon kallo.



Ba Yaya na kad'ai ba nima na shiga damuwa sosai na rashin sa a kusa da ni, cikin kwana biyu da yayi baya nan duk sai na zama kaman ba ni ba abinda yafi tayar mun da hankali rashin samun sa a waya, duk da ya gaya min inda zai tafi ba service amma hakan bai hana ni kwana da waya a hannu ina gwadawa ba, Inna tana ankare dani amma bata ce min cikan ki akai ba.


A ranan da ya cika na uku ne kiran shi ya shigo min yana fara ringing na d'aga cikin d'auki na ce," wayyoo Yaya naaa"


"Na'am k'anwa taaaa" shima yaja kaman yanda nake jan nashi.


Dariya muka sanya dukkan mu sai da mukayi mai isar mu kaman sabobbin kamu sannan ya ce," na kusan shigowa gari k'anwa ta, insha Allah gobe war haka muna tare"


Tsalle na daka da wayan a kunne na na ce," yessss Alhamdullilahi Allah ya shigo da ku lafiya Yaya na" da Ameen ya amsa sannan ya katse kiran.


Dije da take gefe tana min dariya tare da min signal ga Maman su a kusa inyi a hankali ko kula ta banyi ba, ita kuma Maman Dije murmushi kawai tayi tana girgiza kai ta shige kitchen d'in ta ta kyale mu tana mamakin wai yarinya kamata da iya soyayya, hmmm duniya kenan in da ran ka zaka sha kallo.



Zama nayi tare da rafka tagumi ina tunanin ya kamata nima ko sau d'aya ne in kyautata mishi yanda yake kyautata min kullum ko ba komai shima zai ji na damu da shi.



"Ke kuma lafiya, ba yanzu naga kina murnan masoyi zai dawo ba kuma inga kin zabga tagumi kina tunani kaman wacce akaiwa mutuwa?" Cewar Dije kenan.



"Dije kawai so nake inyi wani abu da zai faranta ran Yaya na tunda bai tab'a tafiya ba shiyasa nake son inyi wani abu na tarban shi".



"Gaskiya kinyi tunani mai kyau Zareefa in dai akwai kud'i a hannun ki ni zan taya ki ko abinci ne kiyi mishi".



Cikin jin dad'i na amsa mata da akwai kud'i a waje na, nan da nan muka tsara yanda zamuyi da abinda zamu girka masa.



Da washe gari tare muka je kasuwa muka sayo doya da nama sai kwai creast d'aya da mai muka dawo, gidan Maa muka kai kayan da muka sayo da taimakon Dije mukayi mishi yam balls da kwai cikin kwai da yake shine sana'an da suke ta kware sosai, Maa kuma tayi mana dambun nama mai dad'in gaske.



'Yan kulolli da Inna ta fara min tarun su nan gidan Maa na fito da set d'aya muka zuzzuba a ciki muka shirya a cikin tiren plastic mai kyau shima cikin kayan tarun muka d'auko.


"Kinga yanda kayan nan sukayi kyau kuwa kuma sunyi dad'i da zamu had'a da kunun aya mai sanyi zai fi tafiya" Dije ta kawo sabon shawara nima ba b'ata lokaci na amince sanin yanda shima Dije ta kware da yin sa shima suna sayarwa amma a lokacin zafi.



Da yake mu biyu ne bamu b'ata lokaci ba shima muka had'a ta muka zuba jug na glass haddade muka saka kankara, ni sai a ranan ma nasan na san cewa Inna tayi min taru dayawa haka, sai da muka gama tsab sannan muka wuce gida dan inyi wanka in shirya ita kuma Dije zata fita sana'a ta.



Sai da na shigo Inna ta rutsa ni da tambayoyi ina naje tun dazu?


Na amsa mata da ina gidan Maa tace karya nake bata yarda ba ta kira yaro ina gani ta tura gidan Maa dan a tambayo mata ni dai na shige wanka dan ina gudun kada Yaya na ya dawo ban shirya ba.



Ko da na fito daga wankan bata kuma kula ni ba da alama an tambayo mata Maa,sai da nayi sallah naci ado na da riga da skirt na lace pure cotton dark blue ya sha adon flowers pink, sosai kayan suka min kyau domin Yaya na ya iya zab'en kayan da zasu yi min kyau.



Inna duk tana kallon sabon falli da nake bata min magana ba sai da na gama sannan ta zaunar da ni ta fara min nasiha kan rike mutunci na na 'ya mace a duk inda nake, duk da ta amince da Abdulbasit amma tace kada in kuskura in bar shi ya rike min ko da hannu nane tunda shi ba muharrami na bane kuma ba aure na yayi ba, in ko na bari hakan ta kasance toh tabbas ciki ne zai bayyana a tare da ni wanda har jikokina zan barwa wannan bakin fenti.



Sosai Inna tayi min nasiha daya kashe min jiki ba shiri na fad'a mata duk abinda mukayi a gidan Maa, nan tace ai ba wani abu bane kyautatawa wanda yake kyautata maka,kar inji komai in dan wannan ne ko yaushe na tashi yi inyi anan gida bai sai naje gidan Maa ba.



Cikin jin dad'in fahimta da tayi muka zauna muna hira cikin dabara ta cigaba da wayar min kai akan zaman duniya da kalubalen da yawanci 'yan mata ke fuskan ta wajan kwad'ayi da bin maza kuma daki-daki suke shiga kaina, kiran wayan Yaya na ne ya katse mana hiran na saka hijabi na fito.



Center kofan gidan mu yake kallo fuskar shi d'auke da murmushi na musamman, yana gani na ya kara fad'ad'a murmushi nasa cikin sabon takun da na koya saboda shi na karaso gaban shi sai dai ina zuwa na b'ata fuska ta.



Cikin d'an damuwa yake tambaya ta me ya faru kuma nake b'ata fuska?



"Ba kai bane yau baka kallon waya na fito balle in tsorata ka yanda na saba" na bashi amsa a shagwab'e.



Dariya yayi yana shafa gashin kansa da hannun sa ya ce," ayi min afuwa k'anwa ta yau d'in ne nayi missing d'inki dayawa shiyasa na kasa hakuri har ki ban tsoro"


"Nima nayi missing d'inka sosai Yaya naaa"



"Ina son ki k'anwa ta"



Rufe fuska ta nayi ina dariya kasa-kasa sannan na bashi amsa da ," nima ina son ka Yaya naaa".


A take na bud'e fuska ta tunawa da nayi da abincin da na had'aa mishi a gidan Maa.


"Dan Allah bani minti biyu ina zuwa" ban jira amsar shi ba nayi gaba na kira Bakura wani yaron makotan mu muka tafi tare na d'aura mishi tiren akai ni kuma na d'auko jug d'in muka dawo wajan shi.



Tunda muka fito yake kallo na da mamaki har muka iso bai iya d'auke idan shi daga kaina ba,



"Ban san a ina zan ajiye maka ka ci ba,ko zaure zan saka maka tabarma?"


Girgiza kai yayi tare da nuna min motan shi, ban musa ba yayi gaba muka bi bayan shi ya bud'e seat na bayan motan ya karb'i tiren akan yaron ya saka a ciki sannan ya min nuni da in shiga ciki nima.


Sororo nayi da jug a hannu na kasa shiga kasancewar ban tab'a shiga motan shi ba kuma ga nasiha da Inna ta min d'azu, sai da ya shiga ya zauna ya ganni nan tsaye banida niyyan shiga.



Kara cewa in shiga yayi nayi shiru ni ban shiga ba kuma ban tafi ba sai raba ido nake nan ya fahimci cewa tsoro nake,sai da ya nuna min cewa tunda ban yarda da shi duk shekaru da muka d'auka tare in d'auke abinci na baya ci.



Ganin kaman ran shi ya b'aci yasa na d'an dosana duwawu na kad'an na zauna, yana murmushi yace toh in bud'e yaga me na dafa mishi mai dad'i.



Ina bubude mishi ya ce," iyye lalle k'anwa ta an girma,ke kika girka min ko Inna ce?"




*Albishirinku mata masu son kamshi da gyara ga dama ta samu zamu fara classes na koyar da turaren wuta kala-kala humra shima in different colors dilke gyaran amarya man gashi nd lots more kada ko yarda a baki labarai akan 300 kacal zaki zama pro na kan ki, duk mai bukata ta tuntubi wannan no 08172724281 sai mun ji ku*.
[9/23, 4:26 AM] Ummee Yusuf: 🦚🌹🦚🌹🦚🌹🦚🌹
🦚🌹🦚🌹🦚🌹
🦚🌹🦚🌹
🦚🌹
🦚
*BA SONTA NAkE BA*
🦚
🦚🌹
🦚🌹🦚🌹
🦚🌹🦚🌹🦚🌹
🦚🌹🦚🌹🦚🌹🦚🌹

_A story about love and sacrifice._



_Written by_ *UMMEE YUSUF*
_(Maman Yusuf)_


_*From The Fantastic Writer of*_

```FARHAT```
```KAMACE```
```UKUBAR KISHIYATA```
```UMMU~SALMA```
```UWANI```

*_And now_*


*_BA SONTA NAKE BA_*



*✍✍ G̾O̾L̾D̾E̾N̾ P̾E̾N̾ W̾R̾I̾T̾E̾R̾S̾ A̾S̾S̾O̾C̾I̾A̾T̾I̾

*w̶̶є αr̶̶є вєαr̶̶єr̶̶'s̶̶ σf̶̶ s̶̶σ g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶*🖊
*w̶̶є w̶̶r̶̶ít̶̶є αs̶̶s̶̶íd̶̶íσu̶̶s̶̶l̶̶ч p̶̶єr̶̶c̶̶єív̶̶є n̶̶σ p̶̶αín̶̶,*
*s̶̶σ m̶̶αg̶̶íc̶̶αl̶̶ σu̶̶r̶̶ c̶̶r̶̶єαt̶̶ív̶̶є g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶* ✍ *,вєh̶̶σl̶̶d̶̶ σu̶̶r̶̶ w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶.α p̶̶r̶̶σd̶̶u̶̶c̶̶t̶̶ σf̶̶ σu̶̶r̶̶ p̶̶єn̶*̶ 🖊 *,s̶̶αv̶̶σu̶̶r̶̶ σu̶̶r̶̶ w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶, f̶̶σr̶̶ ít̶̶ w̶̶íl̶̶l̶̶* *c̶̶αu̶̶s̶̶є чσu̶̶ n̶̶σ p̶̶αín̶̶.*


*~INA MASOYAN LITATTAFAN ƘUNGIYAR GOLDEN PEN?~*

*NESA TA ZO KUSA, TUNANIN RASHIN SAMUN NEXT PAGE YA ƘARE!.*


_Kasance mutum na farko da zai fara karanta sabbin littattafan marubutan mu, a duk lokacin da muka yi typing. Kina/Kana iya samun wannan damar ce kawai idan ka bi wannan links tare danna *LIKE* a shafin mu na Facebook_. 👇


https://www.facebook.com/101594048306878?referrer=whatsapp


_Sai kun zo, kar ku manta a koda yaushe comments da sharhin ku yana ƙara mana ƙarfin gwiwa a wajen rubutu._

*Addu'ar Cin Abinci*

Idan mutum zai ci abinci sai ya ce;

بِسْمِ اللهِ.

Bismi l-lahi.
Da sunan Allah

Idan ya manta to sai ya ce (yayin da ya tuna)

بِسْمِ اللهِ فِي أَوَّلِهِ وَآخِرِهِ.

Bismi l-lahi fi awwalihi wa akhirihi.
Da sunan Allah a farkonsa da karshensa.


Wanda Allah ya azurta shi da abinci ya ci, to ya ce;

اللّهُمَّ بارِكْ لَنَا فِيهِ وَأَطْعِمْنا خَيْراً مِنْهُ.

Allahumma barik lana feehi wa-at'imna khayran minh.

Ya Allah! Ka sanya mana albarka a cikinsa, kuma Ka ciyar da mu wanda ya fi shi alheri.

Wanda kuma Allah ya azurta shi da madara ya sha, to ya ce;

اللّهُمَّ بارِكْ لَنَا فِيهِ وَزِدْنا مِنْهُ.

Allahumma barik lana feehi wazidna minh.

Ya Allah! Ka sanya mana albarka a cikinta, kuma Ka kara mana ita (madarar)



*10*



Rufe fuska ta nayi da hijabi na ina dariya ba tare da nayi magana ba,shima dariyan yayi ya d'auki yam ball d'aya ya kai baki ya gutsura ya fara taunawa har da lumshe ido wai dad'i ya kawo sauran baki na cikin sauri na kawar da kai na duk kunya ya gama mamaye ni.


Yaci ba laifi dambun naman da kunun ayan ne dai yace su kam gida zai tafi dasu sunyi dad'i sosai ya kara da cewa duk ranan da zai zo toh ya daina cin abinci anan zan rink'a mishi yana ci, koda ya gama muka sha hiran mu yauma kaman kada ya tafi haka nake ji amma haka muka hakura da zai tafi wani babban jaka ya bani yace in bawa Baban mu sannan muma ya bamu namu tsaraban mu nida Inna ya tafi.



Sai da na nemi taimakon wasu yaran sannan muka shiga da kayan cikin gida Gwaggo Aisha da sauran 'yan koron ta suka bini da harara wanda ban san ma sunayi ba.




"Ni ba wai bana son yayiwa Mallam alkhairi bane ba a'a yanzu Baban ku yazo yaga wannan tulin kayan da sunan nashi, gaba zai iya neman gidan yaron yace zai je maula ya zubar miki da mutunci gaba d'aya" Inna ke fad'an haka bayan na nuna mata jakan da Yaya na yace na Baban mu ne.



Shiru nayi ina tunanin maganan dan na san gaskiya Inna ta fad'a, zuwa can na fara murmushi ni kad'ai saboda na samo mana mafita.



"Inna in kin bashi kayan kice mishi a hukuma Yaya na yake aiki, kinsan yanda Baba yake tsoron hukuma na tabbata daga wannan rana ba zai yarda su had'a hanya ba balle har ya roke shi" na karasa ina dariya sosai dan na tuna yanda Baba yake bala'in tsoron su ban san kome yasa b ba.



Dariya Inna kanta tayi bata kuma ce min komai ba nima ban kara magana ba na kwashi tulin kayan da Yaya na ya kawo min da sunan tsaraba na fara jerawa cikin babban trolleyn kaya na.


Bayan sallah magariba Baba ya shigo d'akin mu ina gama mishi sannu da zuwa na wuce wajan Dije abina na basu waje wanda sam Inna bata san hakan domin ina barin wajan zai fara kokarin canza salon hiran nasu dan haka ba b'ata lokaci ta d'auko jakar kayan tsarabar shi ta ajiye a gaban shi ta koma can nesa dashi ta zauna.



Fara bud'e jakan kayan yayi yana mitan wai Inna ta maida shi dodo da zaran sun kasance su 2 a waje d'aya sai ta koma can gefe.........



Kasa magana Baba yayi saima jikin sa daya fara b'ari ya zaro ido yana kallon jakan in shock kawai, Inna da ta watsar da lamarin sa tana wasu sabgogin ta bata san halin daya shiga ba sai da ta juyo, a tsorace ta mike ta nufo shi tana," Mallam lafiya meya faru?"



Bai motsa ba kuma bai bata amsa ba sai da ta saka hannun ta a kafadar shi ta jijigashi da karfi tana," Mallam.... Mallam..." Sai a wannan lokaci ya firgita yaja dogon numfashi ya d'ago da kai yana kallon ta ba tare da yace komai.



"Kamin magana mana Mallam meya faru nace?"


Ajiyar zuciya yaja ya sauke kusan sau uku sannan ya ce," Bintu wayan nan kayan masu tsada kuma masu yawan da nake gani duka nawa ne kika ce?"


Ajiyan zuciyar itama Inna ta sauke jin cewa ashe wai kayan ne suka firgita shi ta koma wajan zaman ta ta zauna sannan ta amsa mishi da nashi d'in ne.



Firfito da manyan shaddodi da suke ciki ya fara bakin sa kuwa kaman gonan auduga sai da ya fito da guda shida suka kare sai takalma suma masu kyau guda 2 da huluna mu had'u a banki guda 2 da kud'in d'inki a kasa dubu hamsin.



Suma ne kawai Baban mu baiyi ba a wannan rana ya rasa ya zaiyi da rayuwar sa ya d'aga wannan kaya ya kalla sai ya d'aga wancan ga kud'in kuwa ya rike a hannu gam ya kasa ajiyewa kaman wani ne zai kwace mishi.



"Bintu.... Bintu Allah yayi miki albarka yanzu wannan duka a dalilin 'yar albarka na samu dama ai wannan yaron kana ganin

2 Comments On BA SONTA NAKE BA
avatar
maryam-4

2 years ago

Reply

How to download it

avatar
daiy

2 years ago

Reply

replying to @maryam-4 you must sign in in order to download

Please Login or Register in order to submit comment