Join Our WhatsApp Group

Idan ku ka ga kun taba wani wuri ya fitar daku a shafinmu, sai ku danna back kuyo baya, ku sani yanzu muna amfani da tallan Popunder a shafin, so karatu zai muku dan wahala, amma ta hakanne kadai zamu iya cigaba da rike shafinnan. idan har bakwa son talla sai kuje ku yi subscription na shafinnan akan karamin kudi ku runga downloading kawai. SUBSCRIBE


DOWNLOAD

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register
DOWNLOAD

mike da hanzarinta za ta shiga bandaki
ta ji kukan wayarta, don haka ta dawo ta dauka. '
Tun kafin ta qarasa sallamar ya katse ta ta hanyar fadar,
‘To yaya kin taho k0 kuwa yanzun ma ba ki samu damar
ba? .
Saude ta sauke numfashi tare da fadar, ‘Nina fada maka
Yaya Hamid insha Allahu yau zan bar gidan nan duk rintsi,
saboda ni kaina nafi ka kaguwa dana bar gidan nan don
Allah ka kwantar da hankalin ka insha Allahu babu abin da
zai faru.’
Ya ce, ‘Hmm! Saudat kenan na lura ba ki san irin son da
nake miki ba shi yasa har kike fadar kar in damu wallahi
yanzu kasancewa ta da ke ne kawai zai ba ni farin ciki a
rayuwata, don Allah Saudat kada ki ci gaba da nisanta kan
ki dani please; ’
Tausayinsa ya kama ta ita kanta ta soma jin irin yanda
yakeji yanzu don haka cikin sanyin murya
ta ce, “Kayi hakuri Yaya Hamid ni kaina. ina jin
yanda kake ji a yanzu, kuma nan da wasu ‘yan
awanni zan maka kyakkyawan albishir.”
. Hamid ya ce Allah yasa ki gaggauta kin ji?”
’lnsha Allahu.” Ta ce cikin sanyin murya, sannan ta. kashe
wayar ta mike da nufin maida ta wurinta, zuciyarta ta yi.
wata mummunar bugawa.
A tsaye yake jikin qofar ya harde hannuwansa a kirji ya tura
mata idanuwansa da ke sanye cikin farin gilas gaba daya ya
tattara duk wata nutsuwarsa a kan Saudat ta ji.tamkar ta
kurma ihu saboda tsaba: tsor da kaduwa duk ta
dabarbarce,.
, Dr. Ahmad ya take a hankali har zuwa gabanta ya mika:
mata hannu, “Ba ni wayar.”
Ba musu ta miqa‘ masa wayar hannunta na rawa. Ya ce,
‘miqo min har da waccan da na baki.’ Jikinta na faman bari
ta juya ta dauko masa, ya karba kawai ya juya ya fiCe
abinsa ba tare da ya ce da ita komai ba
Saude ta fada saman gadon jagwab kamar an zuba kayan
wanki har wata zufa ke tsatstsafo mata, ta daura hannu a
kai .Wayyo Allah na! Ya Ubangiji gani gare“ ka
, Asma. ta fado kamar an an jefo ta, ' ' Saude ta Zabura ta
miqe a tsorace tana kallonta,
Ta tsaya tana watsa mata wani malalacin kallo. Saude ta
durqushe a gun, tsantsar firgici ta bayyana a fuskarta
bakinta sai kyarma yake wurin fadin
‘In...ina... ina wuni
Asma ta tabe baki tare da jan wani dogon tsaki, ta shiga
zagaye dakin tamkar mai neman wani abu ta kai ta kawo ta
kai ta kawo, ta dinga binciken ta sai data gaji sannanta
juyatafice batare datace uffan ‘ba.
Saude ta yi suman tsaye, me keson faruwa ne da ita ne? Ta
yi masifar firgita, ita dai ta san ta shiga . tsaka mai ‘wuya,
don da za a auna ta a lokacin babu abin da zai hana a
tabbatar da hawan jininta, kukan ma ya gagare ta sai
muzurai kawai take yi.
' Wasa-wasa lokaci ya soma tafiya tana nan zaune, ” tabbas
idan ta yi wasa lokaci zai qure mata, don gangar jikinta ce
kawai zaune a gun amma zuciyarta na wurin Dr. Ahmad.
Qokon ta daya Allah yasa ya yanke mata hukuncin da za ta
iya dauka. Wasa-wasa ta lurawankin hula zai iyakaita
dare,don hakata yanke shawarar tashi ta je ta ba shi hakuri,
ba yanda ta iya haka ta lalalBa ta mike: jikinta amace ta
nufi Gangaren nasa.
Sallamar da take shirin yi ta makale a
makogoranta, tsaye yake goye da hannayensa a baya
wadanda ke rike da wayoyin da ya karba wajenta, duk da
bayansa take saboda ya bada
baya, amma hakan bai hana ta fahaimci yana cikin yanayi
marar dadi ba, tsoronta ya qaru matuka tana fargabar ya yi
mata mummunan zargi.
Jin shigowarta yasa Dr. juyawa a hankali yana kallonta da
jajayen idanuwansa ba tare da ya ce mata kala ba. Saude
ta durkusa a gabansa muryarta a sanyayc ta ce ‘Don Allah
ka yi hakuri Yalla6ai wallahi ba...
Dr. ya yi saurin daga mata hannu alamar ta dakata, ya yi
taku daya zuwa uku ya matso gabanta cikin razananniyar
muryarsa wadda ke fita a hankali ya fara magana.
“In yi hakuri laifin me ki ka yi min? Kina tunanin raina ya
baci ne don na kama ki kina kula maza?” Ya girgiza kai.
“K0 daya Saudat ko a jikina, ko da kuwa duk mazan duniyar
nan samarinn ki neba zai rage ni da ‘ komai ba, illah dai
kawai na tausayawa rayuwarki da ke qoKarin rugujewa, ke
yarinya ce Saudat ba za ki gane waye da namiji ba sai ran
da ya buga miki irin nasa tambarin, ranar ne zaki fahimci
irin wautar da ki kai a baya.
Ni ba zan takura ki ba in ce dole sai yanda nake so za ki yi
rayuwa ba, a baya wauta na yi da rashin bincike wanda
yasa na dauka zuciyarki shararriya ce
babu wani datti a cikinta, ashe ban sani ba tuni kin shigar
da soyayyar da take nema ta makantar da ke ta
kai ki ta baro ki.’ Ya dan yi shiru yana kallonta yana girgiza
kai, sannan ya mika mata wayarta.
“Ungo ga wayarki.”
Hankalin Saude ya qara masifar tashi ba ta san lokacin da
idonta ya kawo kwalla ba, sai dai ta ji zubar
su saman kuncinta. Dr. ya waro ido cike da mamaki
kafin ya ce ‘Kukan me za ki kuma Saudat ai na dauka
firgicin ki‘na raba ki da masoyin ki ne da na yi kuma sai na
ce na bar ki da shi, to me ye kuma abin kuka?”
Saudat ta sa hannu tana share hawayenta, wanda sukaqi
tsayawa ta soma magana cikin kuka. “Ka yi hakuri wallahi
ba da wani namiji nake magana ba Hamid ne.”
Nan ta kwashe labari ta ba shi tun daga sakon da ya aiko
Dillaliya da shi har zuwa wayar da suka yi. ~ Dr. ya ja
numfashi kafin ya ce ‘Saude kenan, a dan labarin da ki ka
ba ni na fahimci kina son Hamid shin haka ne?”
Saude ta ji tamkar ya dora mata Dala da Gwauron Dutse
aka, ta rasa abin da za tace masa ma.
Dr. ya sake cewa, ‘Da ke nake magana fa Saudat kin mini
shiru
Da kyar ta iya dagowa ta kalle shi, ya yi mata masifar
kwarjinin da ba za ta iya kallon idanuwan shi ta fadi abin da
ke zuciyarta ba. Murya: shi a sanyaye ya sake maimaita
mata tambayar a karo na uku, ba ta
san yanda a kai ba sai dai ta samu kanta tana mai girgiza
masa kai, alamar a’a.
Shin meye dalilin saude na cewa batason hamid mu tara
donjin yaddah zataci gaba da kayawa
[1/27, 10:11 AM] A A Dboy: 📚📚DAGA GROUP OF HYPE HAUSA NOVELS BOOK WHATSAPP 08064400100📚📚
[1/28, 12:05 PM] I love my mum: *YAR TALLA*

*CHAPTER 20*

Dr Ahmad ya ajiye wata nannauyar ajiyar zuciya kafin ya ce “Ki je zan neme ki.’
Saude ta share hawayenta ta mike a sanyaye tafi Dr. Ahmad ya bi ta da rinannun idanuwansa wanda sukai jawur.
Saude tana shiga dakinta ta fada kan gadonta ta fashe da wani irin kuka mai sauti, ita kanta ba za ta iya misalta tashin hankalin da take ciki ba, zuciyarta na wurin Hamid ta san dole ya neme ta tunda ta sanar da shi yau za ta bar gidan, shin idan ya kira ta bai same ta ‘ba wane irin zargi zai mata? Kila ma ya rabu da ita. Wayyo ni Allah na! Ta Kara rushewa da wani sabon kukan. Yinin ranar haka ta yi shi babu wata walwala a tare da ita.
. Da yamma liqis Dr. Ahmad ya aiko aka kira ta, don haka ta wanke fuska ta murza mai da hoda, duk wai don karya gane kukan data sha, sannan ta fice.
Da sallamarta ta shiga falon nasa, yana zaune saman daya daga cikin kujerun falon, ya harde tamkar wani basaraken Balarabe, shigar ta manyan kayan ta yi masa masifar kyau ta Kara fitowa da cikar kamalarsa da kwarjininsa.
Saude ta durqusa dan nesa da shi kadan kafin ta ce, ‘Sannu dahutawa YallaBai.’
Dr. Ahmad ya dan zuba mata idanuWansa kafin yace, ‘Me ya samu idanuwan ki Saudat, kuka ki ka rinka yi tun tafiyar ki k0?"
Da sauri ta girgiza masa kai alamar a, a ‘Hmmm! Saudat kenan me yaSa kike san boye mini damuwarki alhalin duk wani motsin ki sai zuciyata ta fassara mini shi Ya girgiza kai tare da fadar ‘Tashi mu je ki min rakiya cikin gari.’ ,
_ Da hanzarinta ta yi saurin daga kai tana kallonsa Dr ya mike; tare da fadar kar ki ce komai biyo ni kawai. Saude ta mike. jikinta a sanyaye tana shirin fashewa da kuka yana kallonta bai kula taba ya yi gaba abin sa.
’ Saude ta bi shi tana matsar kwallarta ita dai so yake kawai ya jaza mata tashin hankalin da ba za ta iya dauka ba kawai. Suna fitowa harabar gidan ta samu masu tsaron lafiyarsa wadanda suke a lungu da sake na gidan sun nufo sa, wasu kuma sun nifi wurin motocinsa wadanda yake fita da su
Dr. Ahmad ya daga masu hannu kawai ya nufi wata shareriyar Jeep mai qofa takwas fara mai bakin gilas, daya daga cikin masu gadin nasa ya take da gudu ya bude masa kofar baya '
Dr Ahmad ya juya yana kallon Saude wadda ke tanya tamkar‘ yar kaciya, ya yi mata nuni da hannu alamar ta shiga ta ji tamkar ya dora mata dukkanin tashin hankalin duniya ta ja ta tsaya cikin
tsananin kidima
Dr Ahmad ya dan matsa daf da ita muryarsa Kasa
kasa ya ce ‘Za ki shiga k0 k0 sai na dauke ki na shiga dake da kaina?” .
Ganin yanda ya matso ta ya tabbalar mata zai iya yin abin da ya fada din don haka ta janyo dauriyar duk duniyar nan ta dorawa kanta, ta taka a sanyaye ta ’ shiga motar, tana zama shi ma‘ya shigo aka maido masu kofar aka kulle
Saude ta ji ta yi mutuwar zaune idan ta ce bata cikin tsananin rudu da kaduwa ta san ta yaudari kanta. Ta lumshe idanuwanta tana sauraren bugun zuciyarta ta san ita yau tata ta Kare ba abin da zai hana Asma na samun labari tasa bindiga ta. Harbeta
Shiru babu wanda ya yi magana a cikinsu. Sai Dr. Ahmad neya dan mika hannun shi ya latsa gefen motar, sai ga wasu hadaddun labulaye sun zagaye motar , ya mika hannu ya bude na’ura mai KwaKwalwa (Computer) din da ke gabansa wadda ke jikin motar ya kunna, sannu a hankali ta kama tamkar talabijin din bango.
Ya koma ya jingina ya ci gaba da latselatsensa ba tare da ya kalli inda take zaune ba, kowa da abin da
yake sakawa a zuciyarsa.
Ba ta san sun iso ba sai dai ta ji an bude masu qofar, Dr. ya rufe computer din ba tare da ya kalle ta ba ya ce ‘Fito mu je. ’ Bai tsaya ba ya sa kai ya fito don haka ita ma ta ziro qafafuwanta ta fito tana kallon harabar wurin da suka shigo.
wurin gyaran jiki ne wanda ya amsa sunansa a cikin garin Abuja daga sama an yi rubum da manyan ..
baki a jikin wani karfe ANNURI beauty QUEEN rubUTun ya bada hasken
‘ Dr Ahmad ya yi gaba Saude na biye dashi har suka iso cikin masu take masa baya daya yayi saurin isa ya bude musu qatuwar kofar ta gilas tareda gaishe
suka shiga qaton wurin mai kamar an gina shi da' zallan gilasai Da kyar Saude ke dosana kafarta’ dan gudun kar ta fasa gilas din
Suna shiga ciki su kabi wata qofa mai kama da ofis,‘ Dr. ya tsaya gaban wata mata cikin Harshen turanci su kai magana sannan ta miqa masa wata yar lakarda ya yi wani dan rubuce rubuce ya miqa. mata itasa hannu, ’ sannan ta mike ta yi masa nuni da wani kujerar dake gefe da dan tebur dinta guda a gabanta; wanda aka dora News paper a sama, ta kawo masa lemu da cake sannan taja hannun Saude. .
“Come and enter my frnd Saude ta ce ikon Allah ai ke kika san shi
Tasa hannunta cikin na Saude suka shiga cikin wani qaton wuri nena gaske wanda aka zubama duk wani" injin ‘ k0 wata na’ura ta gyaran jiki ‘Matar ta kira wata babbar mace Bahaushiya wadda ba zata wuce shekara arba in ba ta nuna mata Saude su
Sukai kai magana cikin harshen turanci da matar ta mikawa Saude‘hannu da murmushi a fuskarta tana fadar.
“You are welcome my sis. '
Saude ta yi sukuti tana kallonsu cike da takaicin turancin banzan da suke mata. K0 matar ta lura ne? Oho ta canja harshe zuwa Hausa.
“Sannu da zuwa ‘yar uwa mu je k0?”
Ba musu Saude ta bi ta suka nufl Bangaren gyaran gashi, ta zauna a kai mata gyaran gashi sosai sannan suka wuce Bangaren gyaran jiki, inda a kai mata dilka da halwa lokaci guda, daga nan a kai mata gyaran qafa
da na akaifa. Tun kafin a qarasa dama Saude ta gama tsurewa da
tsabar kyan da ta gani kwance a jikinta, ita kanta ba ta taBa sanin haka ta hadu ba sai yau, don k0 Indiya sai
haka, saboda idan baka san ta ba aka ce maka Ba’indiyace ba yanda za ai kai musu. '
Ita kanta ta san sun ci lokaci, don k0 da ba ta duba agogo ba ta san dare ya ja sosai. Ana gamawa suka fltO inda Dr. Ahmad ke zaune rike da jarida yana dubawa suna Karasowa ya ajiye jaridar ya mike yana kallonta tamkar wadda ta fado daga sama, lokaci guda kuma ya lumshe idanuwansa ya bude ya juya ya koma wurin ‘yar Baturiyar nan wadda ke ta latse-latse cikin computer ya mika mata A.T.M dinsa tasa ta cire kudin sannan suka flto daga wurin.
Ita dai Saude kallonsa kawai take, amma tambayoyi ne cike fal da cikinta, wanda ta tabbatar ba *
ta da mai amsa mata su sai shi kadai. Suna mota wanda suka shiga kamar dazu direba ya ja su suka fice daga » harabar wurin Saude ta lalubo duk wani karfin halinta kafin ta iya bude baki ta kira sunansa.
“YallaBaii’ ,.
Dr. Ahmad ya dago da idanuwansa daga saman wayarsa yana kallonta kan ya ce, ‘Ya dai Sande?"
““ Ta dan sha Jinin jikinta kafin ta ce ‘Ina so in dan ‘ yi wata‘ yar tambaya.” ce
Dr ya dauke kansa daga kanta kafin yace, ‘Tun » kafin ki yi tambayar na san abin da za ki tambaya don haka ki yi haquri ki hadiye zan ba ki amsa da kaina ‘ idan lokaci ya yi.-’
Za ta sake magana ya daga mata hannu, hakan yasa ta ja bakinta ta tsuke a dole, ta bar zuciyarta na faman‘ dukan tara-tara. Suna isowa gidan ta .kwasa da sauri da niyar ta riga shi shiga gidan, Dr. ya yi saurin tsayar da
ita ta hanyar kiran sunanta, ta ja ta tsaya cak ‘ Da kansa ya Karaso har inda take ya daidaita tsayuwarsa a gabanta kafin ya soma magana, ‘Ki shirya gobe da safe za mu fita.”
Saude ta yi saurin dago da fuskarta tana kalloh shi shi ma ya zuba mata idanuwan nasa wanda babu alamar fargaba a cikinsu,idanuwanta suka kawo kwalla cikin muryar kuka ta soma magana.
“Ni wallahi ,ba zan je ba na gane so kawai ka ke ka jaza min bala’in da ba zan iya dauka ba na rantse da . Allah babu inda zani .... ‘ Ta Kara rushewa da kuka.
“Don Allah don Annabi ka taimake ni kar ka jaza min bala‘in matarka don Allah...’
Dr. Ahmad ya yi wani murmushi wanda ya tsaya iya laBbansa kawai kafin ya ce, ‘Ashe kina da baki haka? Da kyau. To ki dai shirya‘ fita gobe koma me ye zai faru ai kina iya daukarsa idan kuma ba ki zoba to ki tabbatar ni da kaina zan shigo in dauke ki kin san kuma zan iya, don haka sai da safe.’ .
Ya juya ya yi gaba ya bar ta tana masa rakiya da kallon da ke cike da mamakinta karara, don a yanzu hawayen ma sun daina zuba. Mamaki da fargaba suka kashe ta, ita kanta ba ta san tsawon lokacin da ta dauka a tsaye ba, don sai da ta yi da gaske sannan ta iya jan qafafuwanta ta yi gaba.
Tunane-tunane da damuwa yau su suka hana Saude barci da wuri, shekarunta sun yi Karancin da za ta iya yankewa kanta hukunci, da ta gaji da tunanin sai ta kifa kanta samaun filo ta shiga kuka mai sauti, sai da ta yi mai isarta sannan ta yi shiru don kanta, babu wanda ya lallashe ta, sai ajiyar zuciyar da take ajewa akai akai. A' haka barci barawo ya sure ta ba tare da ta sani ba. '
Tun da garin Allah ya waye Saude ke zaune saman gadonta ta zuba uban tagumi da hannuwa bibbiyu, kana kallonta za ka tabbatar da tsantsar damuwarta, ba « ta ankara ba taji an turo kofa za a shigo. ,
Gabanta ya yi mummunar faduwa ta zabura ta miKe tana faman muzurai don duk a zatonta Dr. Ne
Aunty ta turo Kofa ta shigo da sallamarta Saude ta ja wata ajiyar zuciya sannan ta koma ta zauna Aunty ta ‘ ‘dube ta da kulawa kafin ta ce, “Lafiya kuwa Saudat?"
‘ Saude ta dake kafin ta 'ce, ‘Me kika gani Aunty?” ‘Na ga duk kin yi wani wurjanjan ne kamar ba kya cikin hayyacin ki.” '
Saude ta girgiza kai ‘A’a lafiya ta qalau kawai dai
.tunani me.” ~ Aunty ta dan zuba mata ido kafin ta ce, ‘Kai Saudat ban yarda da ke ba jeki gaban madubi ki kalli ‘ kanki da kyau, ki ga yanda kika koma, wannan kyan da daukewar lokaci guda na mene ne?”
Gaban Saude ya kara mummunar bugawa duk ta dabarbarce ta rasa abun fada. '
Aunty ta girgiza kai tana wani murmushi wanda ‘bai kai zuciyarta ba ta ce, ‘Saudat ke nan ni ba tun yauwa ba na fara zargin ki, sai dai a yau na kara . tabbatar da zargina, Saudat gyaran jiki ki kaJe,”
Gaban Saudat ya Kara wata mummunar bugawa a “ karo na biyu, idanuwan nan suka yo warwaje . Aunty ta ce“Hmmm! Saudat kenan me yasa ki ke
Kokarin yaudarar kan 'kine? Me yasa ki ke nema ki dorawa zuciyarki wahala ne? Shin Saudat kin yi tunanin wannan kyan naki zai iya daukar hankalin maigidan nan ne? K0 kusa wallahi k0 da wasa don Yallabai ya wuce duk wani tunaninki ’ ki Don idan har kyau na daukarsa to duk inda ake Zuwa auro: kyakkyawar mace a fadin duniyar nan:
'yana da kudin da zai iya aurarta ke k0 siyowa ake yi yana da kudin siyan ta.
Saude duk yanda baki tunani ba Yallabai ya wuce da sanin ki nasan YallaBai tun kafin ya auri Asma’u asalina ‘yar aikin gidan su ce. Saudat wallahi . wallahi yar gidan shugaban Kasa har falon Hajiyarsa ta zo nemansa, amma ya fice ya bar mata gidan bai kula ta kanta ba. Saudat duk yanda ki ke ganin YallaBai ya wuce ’nan, don jin kansa da mazantakarsa ya wuce yanda kike ganinsa a cikin gidan nan, don ni kaina ba zan iya kirga yawan ‘yan matan da ya yi ba tsakanin Abuja da sauran jahohinnan ba. Saudat ina guje miki daukar Dala da Gwauron Dutse aka, don idan ki ka bari Asma’u ta samu labari ina mai tabbatar miki sai kin raina kanki.
Don k0 da ki ke ganin kamar ba su damu da juna ba, to wallahi suna son junansu don kuwa auren soyayya su kai kamar za su cinye junansu. ‘
Asalin Asma ‘yar asalin nan Abuja ce mahaifinta shi ne Ministan kudi na Nigeria a lokacin kafin ya sauka daga kujerar. Mahaifinta abokin mahaifin Yallabai ne ba zan taba mantawa ba sun taba zuwa gaishe da mahaifin Yallabai da Asma da mahaifinta da mahaifiyarta a lokacin shi mahaifin Yallabai yayi yar rashin lafiya.
Anan ne suka hadu da Asma da Yallabai, tun farkon soyayyarsu sun ‘tiffita qasashe masu yawa,
Soyayyarsu ta dauki tsawon lokaci kafin a tsaida maganar aurensu A lokacin ne kuma iyayensu suka sanya su harkar Siyasa Cikin sati biyu a kai bikinsu aka gama cikin ma ’aikatan da aka bai wa Asma Hajiyar Yallabai ta ‘ hada masu dani na dawa gidansu da zama.
A lokacin basa wannan kasa basa wancan kasa cikin wata guda ba baifi su zauna nigeria sau biyu ba Daga baya ne kuma aka fara kamfen to sannan ne suka zauna aka fara yaqin neman zabe ita da shi duka kowa yana neman tasa kujerar shi yana neman dan majalisar tarayyar Abuja, kuma cikin ikon Allah kowa ya samu.
To a lokacin ne fa kowa ya kama gabansa, haduwa ma sai ta yi masu wuya suna cikin gida daya, amman sai suyi wata wani lokacin basu hadu ba, sai dai k0 cikin dare, amma idan wannan yana Nigeria to shi wannan ya bar kasar,idan wannan ya dawo to wannan ya tafi wurin meeting. Haka dai abin ya ci gaba da kasancewa
Kafin zuwan ki Asma ta samarwa YallaBai ‘yan ' aikin da zasu rinka kula da shi sun fi biyar duka an karesu kowacce da tata matsalar har zuwa kanki Saudat da ki ke ganin Asma ba qaramar mai arziki ' bace duk yanda ki ke tunanin rashin mutuncinta ya
wuce nan musamman a kan mijinta‘ Don tana da masifaffen kishin da ba ki tunani zata iya yin komai a kansa, don haka Shawara ‘nake baki
Don ina sonki saude ki kama kanki tun kafin
Yallabai ya lura da takun ki, idan kunne yaji Ta tabe baki tare da juyawa ta fice
Saude ta saki wata ajiyar zuciya mai qarfi shin in ban da abun Aunty ma ita ko giyar wake ta sha ai ba ta fara hada kanta da YallaBai ba, balle da hankalinta .dama abin da take gudu kenan mummunan zargi, shin yanzu ma idan suka sami labarin fitarsu jiya ya kenan? Ta girgiza kai cike da fargaba ta yunkura ta mike don tsoron kar ya zo da kansa ya Kara jaza mata wani zargin, ta zura takalmanta sannan tafi ta nufi bangaren nasa. :
Tana shigowa falon shi kuma yana saukowa daga
matattakalar benan, sanye yake da shigar qananan kaya, koriyar riga da bakin wando sai takalmin qafarsa “ na fata, yau babu gilas a fuskarsa don haka kana ganin fararen idanuwansa fat masu kama da farar takarda, sumar kannan tasa ta sha gyara sai sheki take hannunsa na rike da makullin mota. , Saude ta durkusa a qasa jikinta a sanyaye tana gaishe shi. Dr. Ahmad ya amsa mata cike da kulawa kafin ya ce, ‘Saudat ya na ga kamar kina cikin damuwa laflya dai k0?” '
Kai kawai ta girgiza masa alamar ba komai Dr. Ahmad ya Kara matsowa daf da ita ya sa hannu ya mikar da ita tsaye cikin raunanniyar muryarsa ya ce,‘ “Ban yarda da babu komai ba Saudat, ki fada mini me .ke damun "ki, ?" Ya yi tambayar yana nuna kansa,’ , Saude ta girgiza masa kai alamar a’a. ‘
Ya CE to waye?" Idonta ya kawa kwalla ta yi
shiru ba tare da ta yi magana ba, dan tana motsa ~ bakinta kuka ne zai kubce mata
Zuciyar Dr ta cika da tausayi muryarsaa sanyaye ya ce ”‘Saudat kina cikin damuwa na fahimci yanda ki ke ji a tawa zuciyar kiyi hakuri insha Allahu komai ya kusa zuwa qarshe Taso muje Saudat.
Ta yi saurin kallonsa da idanuwanta dake cike taf ‘da kwalla tana qokarin yin magana ya dora danyatsansa saman labbanta alamar ta yi shiru kar ta ce komai, sannan ya yi gaba abin sa. Saude ta lallaba ta mike ta bi shi tana goge kwallarta.
Yau da kan shi ya ja motar cikin wata qaramar mota ‘yar dunkulalliya mai‘ kofa biyu wato sport car, iya shigar mutum biyu ce mai bakin gilas irin wanda duk nacin ka ba ka isa ka gane wanda ke ciki ba.
_ Kai tsaye wurin da suka je jiya ta ga sun nufa ita ‘dai kallonsa kawai take kamar jiya haka suka shiga ya' yi rubuce~rubucensa aka shiga da ita wajen 'Washing and dressing. > ‘ Cikin awannin da ba su fi uku ba aka gama mata ’ kwailiyarta tsab cikin wasu hadaddun kaya . ready made riga da siket English wears bakin siket da falmaran mai jinin kart. Falmaran din ya kawo mata ‘har kusan kugu mai dogon hannu sai bakin siririn gyale wanda aka nade mata tamkar nadin Larabawa ya tsaya iya wuyanta Gyaran gashin da , akai mata ya zubo ta gefen fuskarta ya sauka har
fadarta; Rigar ta ciki ta kamata sosai surarta dukta bayyana ta bi ta lafe jikinta, falmarar din mai budaddan gaba ce hakan yasa babu abin da ta rufe
. Takalmin kalar baqi ne mai mai tsini sai jakarsu ‘yar Post mai dan girma. Suna‘ gama mata suka sa
DOWNLOAD
DOWNLOAD

Please Login or Register in order to submit comment