Join Our WhatsApp Group

Idan ku ka ga kun taba wani wuri ya fitar daku a shafinmu, sai ku danna back kuyo baya, ku sani yanzu muna amfani da tallan Popunder a shafin, so karatu zai muku dan wahala, amma ta hakanne kadai zamu iya cigaba da rike shafinnan. idan har bakwa son talla sai kuje ku yi subscription na shafinnan akan karamin kudi ku runga downloading kawai. SUBSCRIBE


DOWNLOAD

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register
DOWNLOAD

wannan abun
ya razanar daké, na san za ki iya yin abin da ma yafi wanda
aka saka ki, idan dai har kin sawa ranki zakiyi, za ki yi
Saudat, please zo muje.” Saude dai ba ta tanka mata ba ta
juya ta bi ' bayanta suka nufi wani sashi daban, ta tura wata
'» kofa sai ga su sun fada wani dan falo irin na ' Sauden. ‘
Aunty ta bud‘e wata loka da ke jikin bango sai ga kayan
kwalliya kamar su ci kansu, ta dauko leda ta dibar mata
masu yawa, tun daga man shafawa, sabulan wanka, kayan
kwalliya har da turarurmka, sannan ta bude wardrobe ta
ciro dan qaramin hijabin nan mai tsayawa iya wuya wato
himar kalar ja ta
mika mata tana fadar
“Ki yi sauri ki je ki gyara ki tafi, dan na san yanzu haka
akwai abubuwa da dama da yake buqata.” Saude ta karBa
ta fice jikinta amace.
Sai data sake wani wankan sannan ta fito ta shafa mai a
jikinta ta kawo wata ‘yar qaramar powder fara ta shafawa
fuskana, ta sa man lice a bakinta, sannan ta mike ta mayar
da kayan jikinta, ta dauki qaramin hijabin ta rufe kanta.
Wani irin abu ya cunkushe mata zuciya, tunda take a duniya
bata taba irin wannan shigar ba ace kana dan Musulmi
amma ka flta a haka, kai duniya! Takaicin kanta ya kamata,
k0 tsayawa ta dubi kanta ba ta iya ba ta dauki turare ta fesa
guri uku kawai sannan ta fice zuciyarta na faman kai kawo.
Tsoronta ya qara tsananta lokacin da ta iso bakin sashin
nasa ta daure ta yi ta maza ta sa kai cikin falon cike da
fargaba. Turus! Ta ja ta tsaya ‘yar sallamar da take shirin yi
ta makale mata a makoshi,
wani irin tsoro da fargaba mai tsanani suka dirar
mata Kwance yake tsakiyar falon saman kafet ya yi
daidai. daga shi sai gajeran wando ba k0 singlet jikinsa, ya
yi matashi da hannayensa fuskarshi na kallon sama,
idanuwan shi a lumshe suke kamar mai barci.
Saude ta runtse: idanuwanta ba ’tana shirin ta juya da sauri
ta-«koma sai kuma ta tuna
Da
maganar Asma da take fadi“Wallahi idan kika sake
Yaqi amincewa dake a matsayin yar aikinsa sai kin fuskanci
fushina. "
[1/24, 9:31 AM] A A Dboy: 📚📚DAGA GROUP OF HYPE HAUSA NOVELS BOOK WHATSAPP 08064400100📚📚
[1/24, 10:13 AM] A A Dboy: *YAR TALLA*

*CHAPTER 16*

Saude ta ja ta tsaya tare da juyowa , muryarta na rawa ta
sake yin wata sallamar, Ahmad ya bude idanuwansa
wadanda suka kada sukai jawur, yana kallonta, kallon da ke
tabbatar da tsananin tsananta cikin idanuwansa ya sake
she idanuwansa kafin ya soma magana tamkar wanda yake
sanyin rada.
“Ba cewa nayi kar ki bari in sake hada hanya da ke ba?
Okay ba kiji ba kenan, shi ne ki ka dawo k0?”
Muryar Saude na rawar disko ta ce
hajia ce tace min Ba ta qarasa fadar abin da za ta ce ba ya
zabura a
Qufule yana fadar, “Wuce ki bar falon nan,‘idan kuwa ki
ka bari raina ya baci za ki hadu da abin da baki yi tunani
ba. Gate out! ” ‘Yan cikin Saude suka Kara Juyawa, wannan
shi ne gaba kura baya hayaki, wasu irin hawaye suka biyo
kuncinta ta durqusa a gabansa cikin kuka tana ‘ fadar, “Don
Allah don Annabi ka‘yi min rai ka yi haquri wallahi idan na
koma na ce mata ka kore ni kasheni za ta yi don Allah ka yi
hakuri ” . Ahmad’ya tsaya yana kallonta tsawon lokaci yana
jin tamkar ya shake ta saboda takaici, don a duniya idan
akwai abin da ya tsana‘to bayan kuka
Ne k0 cikin film baya Kaunar ya. ga ana kuka, '
Ya ja tsaki mts! Tare da fadar “Tashi na ji ya ishe ni haka.”
Muryarta a raunane ta ce “Na gode. ”* Bai tanka mata ba
ya juya ya koma kan kujera ya yi kwanciyarsa abinsa
tsawon Iokaci babu wanda ya
Tanka can dai Saude da ta lura idan za su kwana a haka
bai damu ba sai ta mike ta dan matsa kusa da shi kadan ta
durkusa tana fadar, ‘Ko kwai abin da ka ke buqata in kawo
maka?”
Ahmad ya dan tsura mata ido= kadan, kamar wadda ta
zage shi sannan ya juya tare da kada mata yatsun hannun
shi ba tare da ya yi‘ magana ba, zuciyar Saude ta Kara
tsurewa, don ta lura mutumin ya tsane ta da wuya idan
kuma zai bata mazaunin mai aikin nasa.
Kwalla ta cika mata idanuwa cikin muryar kuka ta soma
magana, “Don Allah to in kawo maka wani abu mai sanyi.” "

“Na ce miki a’ a, a’a shin wai k0 dole ne?” Yanda yake mata
maganar ya firgita ta, saura kadan da ta fadi saboda
razana. hawayen da suka taru a kwarin idanuwanta suka
samu damar biyo kuncinta.
' Ahmad ya ja wani gajeran tsaki yana fadar, “Oh! My God,
jeki kawo mini koma meye zaki kawo, k0 baki Jiba?” Ya
fada a harzuke
Saude ta mike a razane ta nufi gurin firij din ta , bude,
lemuka ne kale-kale sun fi kada ashirin jikinta sai rawa yake
ta rasa wane za ta dauko masa, can idonta ya sauka kan
fresh milk ta kwali, tasa hannu ta dauko masa tare da kofi
na tankaran guda mai gindin turmi ta rufe firij din ta nufo
inda yake. Ta durkusa a gabansa tasa hannu ta gage
hawayen da ke zuba a idanuwanta sannan ta balle murfin
ta tsiyaya masa fiye da rabin kofi din, ta miqa masa, ba
musu ya sa hannu ya karba
Saude ta sauke wata nannauyan ajiyar zuciya, wadda ta
janyo hankalinn Dr. Ahmad ya dan zuba mata idanuwansa
kadan sannan ya dauke kansa. Ta yunkura ta mike tana
fadar, ‘Sai da safe.”
K0 uffan baice mata ba har ta fice Kai tsaye dakinta ta nufa
ta kwanta zuciyarta ta lula duniyar tunanin abin da ya faru
dazu ya rinqa dawo mata ita kanta ta ba kanta tausayi dan
zama tare da miskilin mutum irin wannan ba Karamin aiki
ba ne, shin k0 yaci abincin ma ko k0 haka nan ya kwanta?
Allahu ‘A'a lamu.
Ta daga kanta tana kallon agogon dake manne a bangon
dakin karfe goma da‘ yan mintina, ta qara ' juyawa sosai a
kan gadon, dan to san saura ‘yan mintina lokacin shan
coffee dinsa ya yi, yanzu dan kawai zai sha wani coffee har
sai wani ya je ya
hado masa saboda san kai kawai irin na masu kudi
1page is missing
Saude ta zabura ta durgusa tana gaida shi, k0 inda take bai
kalla ba ballantana ta sa ran zai amsa, don haka taja
bakinta ta tsuke tana kakllonsa ya isa gaban firiji ya bude ya
dauko robar ruwa guda, ya murde murfin ya daga sama
yana kwararawa cikinsa ya sha ya kusan rabi sannan ya
ajiye ya waigo da niyar wucewa. Saude ta yi saurin
sunkuyar da kanta ta ci gaba da abin da take, don tsoron
kar ya ‘ kama ta tana kallonsa. '
Bai kula ta kanta ba ya haye sama abinsa. Saude ta girgiza
kai a zuciyarta tana mamakin miskilanci irin nasa, don har
ma ya zarce matar tasa , ' tunda ita duk abin da kai za ta yi
magana, amma shi sai dai ya kore ka. Ta girgiza kai ta ja
gefen kafet ta zauna tana muzurai; ,
Da misalin Karfe goma saura minti biyar Ahmad ya sauko
daga sama kamshin turarensa ya mamaye falon gaba daya,
Saude ta dan dago a hankali ta saci kallonSa sanye yake da
wani yadi mai laushin gaske sky blue, ya sha aiki da farin
zare. Yadin mai Sharashara ne hakan ne yasa akan iya
hango farar singlet dinsa da short nirker din da ke jikinsa,
farar fatar . nan ta yi wani luwai-luwai kamar jikin Jariri. *
* Ya ja ya zauna kan kujera da waya rike a 'kunnensa yana
magana cikin harshen Turanci, Saude ta yunknra ta mike ta
fita daga falon ta bi wata ‘yar kwana da ke gefe sai ga ta ta
Bude qaton dakin dafa .
abinci wanda ma‘aikata ke ciki, harsu uku duka mutum
daya ne Bahaushiya a cikinsu. To su wai me yasa ba sa son
daukar Musulmai zalla aiki ne?
Ba ta da mai amsa mata wannan tambayan, don ‘ haka ta
karb0 break din yallaBai din sannan ta fito. A bakin kofa su
kai karo da Aunty ta zo daukar wa Hajiya nata suka gaisa,
sannan ta wuce, ta nufi falon nasa. : :
Yana zaune kamar yanda ta bar shi har yanzu bai gama
wayar ba, Saude ta dora tiren kayan abincin saman dinning
table sannan ta koma can gefe nesa da shi ta zauna tana
jiransa ya gama wayar amma da alama bai da niyar
gamawa har wani kashe murya yake yana zuba shagwaBa,
sai. kace wani qaramin yaro, duk kunya ta ishe ta, ji take
tamkar ta zuba da gudu, don duk da ba ta. san abinda yake
cewa ba, ' amma zuciyarta ta ba ta da matarsa yake wayar
Ashe dama yana dariya irin haka? Lallai k0 da wa yake
wayar nan, to an jiKa ta a shanye Ba ta ankara ba tana
duniyar tunani sai dai ta ji muryarsa na fadar, “Kawo
abincin nan
Saude ta zabura har tana neman faduwa ta mike, ta nufi
dining din ta dauko kayan karyawar tazo ta gabansa ya
nuna mata kan kafet din ta aje masa anan sannan ta koma
ta zauna
Ya watsa mata wani kalla mai, kama da harara kafin ya ce,
“Waye kika ajiye ya yi serving din. "
Saude ta waro ido tana kallonsa cike da razana don ita dai
ba ta san abin da yace ba, ya ja tsaki tare da fadar, “Na ce
waye zai zuzzuba abincin?”
. Saude ta yi saurin matsowa tana fadar, “Yanzu zan zuba.”
Ta dauki kofi ta zuzzuba kayan tea, sannan ta zuba ruwan
ta cika kofin d taf-taf ta juya da cokali ta mika masa.
Ahmad ya zuba mata dara-daran idanuwansa cike da
takaici ya ce, “Yanzu duk wannan Waye zai shanye shi? Kin
tattakura kin shaqare kofl da ruwan tea dan rashin hankali
mts!’ Ya karBi shayin ya rage fiye da rabi a wani kofl din,
sannan ya soma sha.
Jikin Saude ya Kara yin sanyi, tana tsoron ta zuba
masa abincin ya gwasale ta, muryarta a sanyaye ta‘ ce,
“Abincin kamar yaya za a zuba?”
Bai kalli inda take ba ma ballantana ta sa ran zai tanka
mata, zuciyar ta ta Kara tsinkewa, ta yi ta maza ta dauki
plate da cokali ta bubbude kulolin, soyayyar doya ce da
miyar swse sai daya kular yam ball ne Wanda ya ji nama da
kwai, sai dayar farfesun nama ,ne da dankalin turawa,
wato~ papper chicking, sai
gasashshen biredi an masa wani yanka mai kyau an dora
saman plate, wato sandwich.
Saude ta turo masa . plate din biredin, sannan ta zuba
masa farfesun naman a plate din sai ta debi
yam ball din ta zuba masa a gefen bredin, ta maida saman
ta rufe.
“Bai tanka mata ba ya rinqa cin abincinsa sannu a hankali
har ya gama, sannan ya dago ya dube ta kamar wanda aka
tilastawa sai ya kalle ta ya ce, “Tashi kawo mini morning
fresh
‘Yan hanjin Saude suka duru ruwa, yau na shiga uku! Wani
abu ne kuma haka? Yanda ya kafa mata idanuwa yasa a
dole ta yunkura ta mike. To ina za ta dosa? ‘
Ta tsaya cikin falon tana faman diminiya, tadan juyo kadan
ta ga idan yana kallonta su kai ido hudu, gaba daya ya
tattara nutsuwarsa a kanta, ai kuWa take ta Kara tsurewa to
k0 dai tsintsiya yake nufi, don ta lura da ya yarda wani dan
qashi a kasa. ‘
Ta ja wata ajiyar zuciyar samun mafita, sannan ta dauko
‘yar tsintsiyar da take share-share da ita a falon ta nufo shi,
ta durkusa tare da fadar, “Ga ta.”
Haushi da takaici suka kashe Ahmad. ya watsa mata wani
mugun kallo wanda yasa duk wata laka ta! jikinta ta mutu
ya ja tsaki mts! Yana fadar. ‘
“Ke jakar ina Ce? Wannan ita ce morning fresh din? Idan ba
ki sani ba ba za ki tambaya ba, sai kawai ki je ki ta
shashanci, ki kawo mini tsintsiya inyi tsiyar me da ita?”
Ya girgiza kai cike da takaici yana fadar, “Kai Allah dai ya
wadaran dakikin mutum stuppid girl ni
Fice ki bani wuri, na daina hada ido da ke, sakarya kawai.”
Zuciyar Saude ta Kara karyewa idanuwanta suka ciko da
hawaye muryarta na rawa tace, “Ka yi hakuri don Allah. ”
Ya watsa mata idanuwansa tare da Jan wani dogon tsaki
“Mts!” ‘
Saude ta yi saurin sunkuyar. da kanta Kasa, yana kallonta
cikeda tsanarta ya ce, “Ki fadawa Madam, ina da meeting
yau kar ta ga ban sa an kawo mata sakon nan ba sai, zuwa
gobe komai kr nan mu hadu ta network.”
Yana gama fada ya mike ya sa kai ya fice ya bar Saude a
tsaye, wasu siraran hawaye suka biyo
kuncinta tadurkushe a gun. Wayyo ni Allah na ya. Ubangiji
ga Saude na san baka mance da ita, ba ya Allah Ubangiji ka
cire ni daga' wannan rayuwar qangin“ bautar da rashin
galihu.’ A hankali ta fashe da wani irin kuka mai cin zuciya,
sai da ta yi mai 'isarta bata da mai lallashinta sannan ta
share ’hawayenta.
Ta diba tiren abincin dake gabanta t duba ba wani da yawa
yaciba sannan itama ta zauna ci tsakura kawai tayi saboda
yanda take jin zuciyarta babu dadi. Tana gamawa ta mike
ta fita da kwanukan sannan ta dawo ta gyara falon tamkar
ba a taba shigowa ciki Ba sai da ta gyara ko’ina ta yi
turaren Wuta ta sassaki labulayen tagogin ta qara gudun AC

a koina sannan ta rurrufo falukan ta fice, ta nufi can
Bangaren. , Babu kowa a falon qasan sai Aunty tana turaren
wuta, ta gaishe ta cike da girmamawa, Aunty ta bi ta da.
kallo tamkar mai karantar, wani abu. Muryar Saude a
sanyaye ta ce “YallaBa‘i ya ce“A fadawa Madam ba zai
dawo ba sai gobe
Aunty ta ce, “To ki hau sama ki fadawa Hajiyar da kanki.”
Saude ta dan yi jim cike da tsoro.
Aunty ta katse mata tunanin da fadar, “Kije mana Saudat
tunanin me ki keyi haka?”
Saude ta girgiza kai sannan ta wuce ba tare da ta ce uffan
ba, ta tattaka matattakalar benen ta haye sama. A karo na
farko kenan da ta fara hawa saman. ‘ Haka kawai ta tsinci
gabanta na faman faduwa,_ wani irin tsoro mai tsanani ya
dirar mata, ta rinqa bin falon da kallo aljannar duniya, lallai
ba banza ba masu kudi ke mantawa da ni’imar da Ubangiji
ya yi masu ba. Muryarta na faman sarkewa ta yi sallama‘
har sau biyu. Babu wanda ya amsa ga shi kuma tana jiyo
hayaniyar mutane a falon da ke gefe, don haka ta Kara
matsawa tare da yin wata sallamar.
Tun kafin ta karasa rufe bakinta ta ji an watso mata wata
dunkulalliyar ashariya cikin ta ya duri ruwa, kafin ta yi
tunanin juyawa ta ga Asma gabanta, tun kafin ta karasa
tantance ta, ta ji saukar
wani mahaukacin mari a kuncinta gefen dama da hagu.
Saude ta durkusa ta dafe kuncin lokacin da ta ga wata wuta
ta gifta mata a idanuwa, cikin takaici Asma ke fadar, “You
are very" stupid, ke jakar ina ce? Da ina meeting za ki shigo
ki distubing dina banza sakarai shashasha, uwar me aka yi
ne da ta sa ki ka shigo mini har falo?”
Saude ta durkusar da kanta qasa daga duqen da take,
hawaye suka soma zarya a kuncinta, cikin muryar kuka ta
ce “Ki yi haquri dama Yallabai ne ya aiko ni, ya ce ya yi
tafiya sai zuwa gobe da yamma za..
‘So What! Na ce sai me? Da ya aiko ki sai ya ce ki iske ni
duk inda nake ki fada mini, iye?’ Ta ja wani dogon tsaki mts!
Kafin ta ce, “Da alla gate out on my parlour’ Ta sake kwatsa
mata tsawa, “I say
gate out k0 ba kya jine?” saude ta zabura ta mike ta bi
hanyar da take nuna
mata jikinta na rawa, Asma ta sake jan wani tsaki tana
fadar, ‘Stupld kawai.’ Sannan
ta juya ta koma ciki abin ta.
Saude na fita kai tsaye bangarenta ta fada
kan gado ta fasheda Wani irin kuka mai cin zuciya wayyo
Allah yau ta ga ta kanta, wannan wace irin rayuwa ce ta
samu kanta a ciki me cike da qaskanci
da wulaqanci ni Saude? Kuka take ‘sosai bata da mai
lallashinta. Rayuwa kenan.
,,,,,,,,,,,, ,,,,,,,,,,,,,,
Haka rayuwar Saude ta ci gaba da tafiya cikin kaskanci da
rashin galihu, kullum tana cikin bauta, ita da bayi ba su da
bambanci, ’sauqin‘ ta ma tun a gida ta riga ta saba da
wahala.
Yanzu haka rakube take gefen kujera bayan ta gama. gyara
falon ta gaji, ta rakube gefe tana kallon tashar Saudiyya,
wani shiri da suke yi duk karfe biyar na yamma. ‘
Dr. Ahmad ya sauko daga sama yana sanye da kayan
wasanni na kwallo, gajeran wando da singleti sai takalmin
‘yan kwallo, Saude ta saci kallon shi kadan. Kayan sun
masa kyau sai ka ce irin turawan , nan da ke buga wasan
kwallon kafa, ba tare da ya kalli inda take ba ya wuce
abinsa yana fadar.
“Ki biyo ni da robar ruwa mai sanyi.”
Saude ta zabura ta mike ta nufl wurin kantar da -ake ajiye
lemoka ta bude ta Ciro robar Faro guda kwalin lemo guda
tare da kofi guda daya tabi bayansa
A qaton filin wasan‘ dake gefen lambun gidanta“ same shi
yana ta faman tika kwallo shi daya, duk
ya hada gumi, Saude ta rakube gefe rungume da tirenta
hannu tana kallon ikon Allah, zuciyarta na _
raya mata wasu abubuwa da dama cike tàke da mamakin
Yallabai din tana mamakin yadda duk abin da ya yi sai ya yi
masa kyau, tunda take bata taba ganin muninsa ba, kullum
ma kamar~kara masa kyau ake. Shin dama akwai mutum
irin haka? Ba ta ankara ba sai dai ta jiyo sautin muryarsa
na fadar.
“Wai ke k0 kurma ce ne?’
Saude ta zabura da saurinta ta nufe shi jikinta na rawa, ta
durkusa‘ gabansa cikin rawar murya tana ~ fadar, “Ga ni.”
Ya ja tsaki cike da takaici kafin ya ce, “Hankalin ki yana ina
ne lokacin da na wage murya nake ta kwalo miki kira? Me ki
ke kallo ne a jikina wanda har ya dauke miki hankali?
Tunanin me ki ke’?” ‘
' Ya sake jan wani dogon tsaki ya gif‘ta ta ya‘wuce yana
sharce gumin goshinsa da hannunsa, ya bar ta a duke da
tiren lemuka tana faman rarraba idanuwa, tsoro ya kama ta
dan ba ta san irin hukuncin da zai yanke mata ba.
Haka ta daure ta dake zuciyarta ta bi bayansa, tsaye yake
gaban na’urar sanyaya ruwa, ya tara kofinsa yana zubowa,
Saude ta durkusa. gabansa muryarta a raunane ta ce, “Don
Allah don Annabi
YallaBai ka yi hakuri, insha Allahu na yi maka alkawarin ba
zan Kara ba.”
nazarin wani abu a fuskarta, ba tare da yace uffan ba ya
dauki ruwansa ya durawa cikinsa ya ajiye kofi din ya yi
mata nuni da hannu alamar ta wuce kawai, ya yi gaba
abinsa ya haye sama. Saude ta girgiza kai zuciyarta na cike
da mamakin miskilanci irin na dan adam. Duniya kenan.
‘ Da misalin Karfe tara na safe Saude ta kammala
ayyukanta gaba daya, ta kunna turarukan wuta a ko’ina
sannan ta dauko room freshner ta faffesawa labulayen
falukan da kujerun‘
Dr. Ahmad ya shigo falon daga shi sai dan qaramin gajeran
wando duk ya hada gumi, da alama daga motsa jiki yake.
Kai tsaye ya wuce ya tsiyaya ruwa a kofl ya sha kusan kofi
biyu, sannan ya wuce abin sa. Har ya taka step din da zai
kai ka falon shi na sama ya waigo ya kalli Saude fuskarsa
ba yabo ba fallasa yace “Kije ki sanar da kuku yau ina da
baqi da misalin qarfe sha daya na safiyar nan ya tanadi duk
abin da ya san za a iya bukata." Yana gama fada ya yi gaba
ba tare da ya tsaya ya saurari amsawarta ba.
Saude ta maida kayan sannan ta fice da sauri dan isar da
sakon da aka aike ta. Tana dawowa ta same shi tsaye a
falon sanye da farar jallabiya a jikinsa yana waya ta ja gefe
ta zauna.
Ya‘yi wayarsa ya gama sannan ya matso inda
~ take ya‘ mika mata wani key yana fadar, “Karbi
wannan key din ki bude wancan falon ki gyara anan zan
sauke bakin nawa.”
Saude tasa hannu biyu ta karba, ya juya ya koma sama, ita
kuma ta mike ta nufi kofar: da niyyar budewa, amma abun
ya faskara, saboda gaba dayan kofofin gidan odar waje ne
in ba wanda ya saba ba.
’don ko wancan karan da za ta shigo falon nasa ’anty ce ta“
bude mata, Ta dan nutsu tana tunanin
* .yanda Suka bude a wancan karon', cikin ikon Allah ta
~samu ta bude kofar sannan ta shiga.
Katafaren falo ne dogo mai girma wanda ya ji
kujerun silba masu kyau sunkai ashirin sun sa wani
dogon char a tsakiya. Kai da ganin haduwarsu ka «san odar
waje ne. Ga falon ya ji wani lallausan kafet ya mamaye
gaba dayan falon wanda aka Kawata shi Dukda falon ba
wani datti ya yi ba, amma haka Saude ta gyara shi sosai ta
goge ko’ina da ina ,hatta jikin bangwaye wadanda gaba
dayansu “tayil ne sai da ta goge, gaskiya ta sha wahala
sosai harta samu ta gama, ta zauna ta turare falon da
turaren wuta ta feshe shi da air frshner masu kamshin.
gaske ta kunna A.C din falon, gaba daya
falon ya shiga fitar da wani sanyayyan kamshi mai ni’ima. .
” Saude ta juyo da niyar tifowa shi kuma ya shigo ta yi
saurin matsawa ta zube Kasa tana'fadar, “Sannu da fitowa
YallaBai an kammala.” Bai tanka mata ba ya Wuce ta yana
bin falon da
kallo da alama shi ma yanda falon ya dauki qamshi ya
burge sa, shi yana kallon falon ita. kuma tana kallonsa,
tunda take da shi ba ta taBa ganin yasa qananan kaya ba
sai yau, dan sai ta gama yafi mata kyau fiye da kullum.
Ganin zai juyo sai ta yi saurin dauke idanuwanta tamike tayi
gaba, bataredata bariya kamata tana satar kallonsa ba.
Tana fitowa ta ja gefe ta zauna a falon tana kallonsa ya fito
yana wani takawa tamkar wanda ba ya san taka qasa.
Ba tare da ya qaraso inda take ba ya ja. ya tsaya
hannayensa zube cikin aljihu, cikin sanyayyar muryarsa ya
ce, “Akwai katon din lemma da , robobin ruwa da aka kawo
suna cikin‘ kanta, za mu shiga meeting karfe sha daya, kin
ga yanzu Saura minti goma ina so sha daya da rabi ki
dauko lemu da ,ruwa kizo ki jajjera a gaban kowacce
kujera, lemo daya robar ruwa guda. Akwai meat pie an
nadeshi guda biyu cikin tissue sai ki ajiyewa kowacce kujera
guda'a gaban teburinta. Ina fatan kin gane?”
‘ Saude. Ta daga masa kai alamar eh ya ce “Okey, kuma
idan za ki shiga ban da surutu, ban ce ki yi wa kowa
magana ba da akwai kayan da zaki karba ki canza.’ Oya
ban san wasting din time je ki.” ‘ ‘ Saude ta lallaBa ta mike
ta fice abin ta tana jinjina girman wadannan bakin a
wurinsa.
Tana shiga'Aunty ta miko mata leda ta karba ta nufi ciki, ta
watso ruwa ta flto. A tsaitsaye ta shirya duk da yanzu ta
dan nutsu ta shafa hoda da dan mai
‘a labbanta, ta sawa idanuwanta kwalli, tunda ta lura bakin
kunya ne za a yi, ta zazzage kayan daga ledar Suit ne irin
na jikinta, amma na yanzu wando ne da siket ba, kuma
bakake neba sai rigar.cikin ce mai kalar jini,‘ harda belt irin
ta mata. Mamaki ya. kama Saude shin k0 sun manta ita
diyar Musulmai ce ba arniya ba?
Taja ta zauna gefen gadon tana mamakin yanda za ta ratsa
mutanen nan da wadannan kayan, ta dafe kai tana jin
tamkar ta zabga da gudu. Bugun agogon dakin yasa ta yi
saurin dago kai qarfe sha daya daidai ta buga, Saude ta yi
saurin miqewa ta saka kayan wanda suka zauna mata a jiki
cif da cif tamkar
dama an auna ta, ta saka bakin takalmin kayan sawuciki
bakake marasa tudu
Ta janyo karamar himarta ta saka, wadda take ganin ta yi
mata qankanta nesa ba kusa ba,
bayan da ta Karasa ta fice da hanzarinta, tana faman rawar
jiki, sai kace angon kare
Karfe sha daya da rabi daidai ta dauki katon din lemo guda
da katan din faro tan nufi falon taron wanda take jiyo sautin
magana sama-sama a yi da
Hausa a yi da Turanci.
Saude na shiga ta ji tamkar ta zabga da gudu, saboda
yanda ta ga mutane sun kai ashirin Turawa bakar fata, shi
kuwa uban gayyar yana zaune a kujerar da ke tsakiyarsu,
da abun magana a gefen teburinsa, tsoro ya kama ta abin
ka da bagidajen mutum ta samu ta yi ta maza, ta shiga
zabga sallama, babu wanda ya amsa a cikinsu, mamaki ya
kama ta to su kuma wadannan wane irin mutanene da ba su
amsa sallama? Ta sa kai ta shiga tana faman muzurai
kamar wata marar gaskiya. ‘
Ta durkusa “Ina kwananku?" Babu wanda ya . kalli inda take
ma balle ya san abin da‘ take hankalinsu na kan jawabin
Dr., wani irin abu ya yi wa Saude tsaye a Kahon zuciya, don
ita a ganinta su ma sun yi niyar ci mata fuska ne. Don haka
ta shiga jera ruwa da lemon kamar yanda ya fada mata, ta
koma ta Kara dauko wasu sannan ta qarasa jerawa ta
koma ta dauko meat pie din su ma ta jejjera. Tana gamawa
ta tsaya gaban Dr. wanda ke dan rubuce‘ rubuce a saman
wani Karamin littafl, sannan ta dan rissina.
YallaBai a kawo maka abincin ka nan ko sai ka
fito zakaci Wani irin kunya da haushi da takaici suka taruma
Dr Ahmad ya ji tamkar qasa ta tsage ya shiga ciki. Jin ya
yi. shiru yasa Saude tunanin k0 bai ji bane ta sake
maimaitawa. “Yallabai nan za a kawo ma abincin ko,,,,,,,,
Tunkafin ta karasa rufe
DOWNLOAD
DOWNLOAD

Please Login or Register in order to submit comment