Join Our WhatsApp Group

Idan ku ka ga kun taba wani wuri ya fitar daku a shafinmu, sai ku danna back kuyo baya, ku sani yanzu muna amfani da tallan Popunder a shafin, so karatu zai muku dan wahala, amma ta hakanne kadai zamu iya cigaba da rike shafinnan. idan har bakwa son talla sai kuje ku yi subscription na shafinnan akan karamin kudi ku runga downloading kawai. SUBSCRIBE


DOWNLOAD

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register
DOWNLOAD

taso masa, shi da ya sani
Allah ya jarabce shi da soyayyar Saudat, irin son
da
ba zai iya misaltuwa ba, wai yau Saudat dinsa ce
ta zama haka? Rayuwa kenan.
Ana kiran sallar azahar suka iso gida, don haka
Alhaji Ashiru na sauke su ya wuce masallaci don
ya bada farali, su kuma suka shige gidan, Momy
ta wuce bangarenta su ma suka nufi nasu
Bangaren don gabatar da sallah a cikin lokaci.
Bayan sallar la’ asar kuma Shukura ta koma gida
saboda gobe tana da lecture a school.
Kwanansu uku da dawowa ya kama ranar
alhamis, Saudat na kwance a falonta ita da Nabil
da Nabila tana kallonsu suna home work da aka
ba su daga makaranta, Momy ta shigo felon
kafadarta na rataye da katuwar jaka, ‘sai rigar
likitoci sagale a dayan hannun da alama
dawowarta daga ofis ke nan. Duka yaran suka
zabura suka nufe ta a guje
suna fadar, “Oyoyo my Momy, welcome".
Ita ma da fara‘a a kan fuskarta ta rungume yaran
a jikinta tana shafar kawunnansu.
Saudat ta yunkura ta mike ta nufi inda " ' Momy
ta ke ta karbi jakar hannunta da Iafkwat dinta:
‘da mayafin jikinta ta nufi Sangarenta kai tsaye
kicin ta nufa ta jero kulolin‘ .abinci a babban
faranti tareda kwalin lemo', da ruwa masu sanyi
ta nufo falon, inda ta samu’ . Momy har ta yi wa
kanta masauki saman tallausan ' kafet din falon,
yaran duk sun zagaye ta suna ta_ shirmensu. ‘
Saudat ta ajiye mata kayan abincin a gabanta, ta
soma bude kulolin tana mata sannu da zuwa.
Momy ta rike farantin tana fadar.
“Barshi kawai Saudat, kije falon waje
Hamid nanan ya zo zaku gaisa” . . Saudat ta
washe baki tana fadar. ' ~ “Kai Momy, ashe bai
mance dani ba, yau fa kwana uku . ke nan da
dawowarmu daga -Dandagora, amma bai zoba shi
da ya ce ‘a * washegari zai zo?”
Momy ta ce “Ah to, ni kaina da na ganshi a
yanzu sai da nayi mita, amma dai yace ba ya
garine shi ya sa, dawowarsa kenan. Tashi ki je
kar yaga an barshi shi kadai.
_ ‘ Saudat ta yunkura ta mike ta nufi kan gadonta
ta jawa farin mayafinta ta yafa, ta saka
takalminta flat Shoe shi ma fari
A tsaye ta same shi cikin falon ya nannade
hannayensa a qirji ya zuba wa qaton hoton da ke
jingine a bangon daki ido, na su Nabila da Nabil
ne wanda .aka yi musu a harabar wurin
shakatawa da
ke cikin park dukkansu sun yi matukar
kyau tamkar ‘ya’yan da ke rayuwa cikin dusar
qankara.
Saudat ta qaraso cikin falon da ‘yar siririyan
sallamarta, bakinta na dauke da murmushi.
Hamid ya yi saurin waigowa yana kallon mai
shigowarr tare da amsa mata sallamar Saudat ta
tsaya dan nesa da shi tana fadar, “Saudatu ya
tabbata kan Yaya Hamid wanda ya manta da ita
tsawon kwanaki uku babu shi babu alamarsa”. .
Tunda Hamid ya waigo ya ganta ya kasa koda
kyafta idanunsa balle ya janye su daga kanta,
girman da Saudat ta Kara da cikar jikinta shi ya
fi . komai daukar hankalinsa, da kuma shigar
alfarmar da ke jikinta. Ba komai bane a jikinta,
illa wani tsadadden code lace dark blue mai
ratsin fad-fad a jiki, dinkin riga da siket, kalar
leshin ta dace da yanayin farar fatarta, don haka
dinkin ya yi matukar kwantawa a jikinta. Yafi
mayafin da ta yi
Ya zauna kafadarta ya dace da ita, ya fito da
sigarta ta nutsattsiyar budurwa.
: Hamid ya lumshe idanunsa ya bude guda yana
fadar, “Allah ya huci zuciyar Saudat, wai kin ga
yadda kika ka koma kuwa?’ ‘
‘ ‘ Saudat ta yi murmushi har da sunkuyawa ta
zauna tana fuskantar katon teburin da aka
qawata
da kayan ciye-ciye dana sanyaya makoshi. ~ ~
“ ' ‘ Hamid ya durqusa a gabanta yana kallonta
da idanunsa dake fallasa asirin zuciyarsa, ya kira
sunanta .
“Saudat, wallahi ina sonki, irin son da ba zai .
misaltu ba, daidai da daqika guda ban taBa '
mancewa da keba a rayuwata, kina nan makale a
zuciyata wallahi ranar da kuka zo gidanmu a
ranar na bar Katsina na tafi Abuja, isowa ta ke
nan wallahi. Saudat zuciyata ta gaza hakuri sai
da nazo ki yarda da ni don Allah kyakkyawata".
Dariya ceta kwace wa Saudat saboda ganin
yadda duk Hamid din ya bi ya rude kamar wani
zautaccce, shi ma ‘yar dariyar ya yi yana sosa
qeya alamar ya danji kunya shi ma.
A daidai nan ne kuma Dr. Ahmad ya sawo kai
cikin falon da‘ yar siririyar sallamarsa, waddai ta
makale amakoshi. * '
Saudat ta dago kanta a dan razane ta dubi ' inda
yake Wani razanannen kallo ya watsa mata ta
cikin siririn farin gilashin da ke manne a
fuskarsa,
Lokaci guda ya dauke kansa tamkar allah bai
ajiye ’
Awajen ba, haka ya gifta su ya shige falon cikin
gidan.
Saudat ta sauke wani gwauron numfashi tare da
maida hankalinta inda Hamid yake
Murmushi ya sakar mata tareda fadar, . “Wannan
shi ne abokin takarar tawa kenan?”
Saudat ta sunkuyar da idanunta qasa tana dan
wasa da bakin gyalenta don har ga Allah Hamid
yana da muhimmanci a rayuwarta, duk da ta sani
sarai ba za ta iya hada soyayyar Dr. Ahmad da
ta kowa a zuciyarta ba.
Hamid ya yunkura ya mike hannayensa zube a
cikin aljihunsa yana kallonta da fararen
idanunsa.
Saudat ta yi qasa da idanunta ta kasa hada ido
da Hamid din sai kawau ta tsinci kanta da jin
matukar nauyinsa.
Hamid ya yi wani malalacin murmushi
Wanda ya tsaya iya labbansa kawai, muryarsa na
dan sarqewa ya ce “Tsananin son da nake miki
Saudat, da dumbin qaunarki da ke zuciyata ba
zai ingiza ni ga take gaskiya ba. Saudat na yi
miki rantsuwa da Allah ke ce kadai macen da na
tabaa so a rayuwata, kuma haryau bana tunanin
da akwai kwatankwacinki. A ranar da kuka zo
gidanmu kuka ganni a ranar aka daura aurena da
Kausar ‘yar qanin mahaifina
'Amma nasa qafa na bar Katsina zuwa Abuja‘
ban“ sonta, banida muhallin da zan iya
:ajiyeta a a zuciyata, tunda na. tafi sai jiya na
dawo. A yanzu haka mahaifina ya yi fushi , , don
haka mahaifiyata ta ba ni shawara na tafi
Kaduna Wurin matata, wannan ne ‘ kadai abin
dazai Shirya tsakanina da mahaifina. Yanxu’ haka
tafiyar tawa ce zuwa Kadunan shine na kasa
daurewa har sai na tsaya na ganki sannan na
wuce. Saudat ba zan shiga haqqinki ba, idar har
kin ji zaki iya aurena a yadda nake a ‘ yanxu na
ba ki sati daya ki yi shawara duk abin da ‘ kika
”yanke zan dawo sai ki sanar dani”.
“' Ba tareda ya tsaya sauraran abin da zata
cebaa ya zaro ambulan daga cikin aljihunsa ya
dora mata a hannu sannan , ya juya ya fice
abinsa. Saudat ta mike jikinta a kasale ta ‘ nufi
qofar shiga babban falon gidan. Ba ta ankara ba
sai dai ta ji sun yi karo yana qokarin fitowa ita
tana qokarin shiga, ta yi saurin ja da baya tare da
dafe goshi, kallo daya yayi mata ya Juya ya
dauke kai da sauri ya raBa ta zai wuce. . Saudat
ta yi saurin rufa masa baya tana ' kiransa baida
alamar tsaya ba balle harya .sauraré ta hakan ya
sa ta Kara da gudu~gudu ta , sha .gabansa.
'Don Allah ka tsaya ka saurareni
Ta yi magar tamkar zata rusheda kuka. Dr.
Ahmad yasa ya tsaya a gabanta yas‘hannayensa
a aljihu tare da kafa mata ido. Saude ta
langwabar da kai ' “Don Allah kar ka horar dain
da fushinka, wallahi ba zan iya jurewa ba” . . Dr
Ahmad ya watsa mata harara kafin yace“Idan
har ni ban horar da zuciyarki da fushina ba, ai ke
kya tarwatsa tawa zuciyar da masifar kishinki
kauce ki bani hanya in wuce : Ya qarasa
maganar tare da sa hannu yana ture ta daga
gabansa
Saudat ta Kara tokare hanyar cikin muryar ' son
fashewa da kuka ta ce “Haba don Allah yallaBai,
Yaya Hamid ne fa ba wani ba”.
Dr. Ahmad ya qara watsa mata. wani kallo,
“Okey, Yaya Hamid ne shi da yake ba namiji
baneba k0? K0 kuma shi din ba sonki yake ba
ko? Da Allah matsa bani wuri malama na wuce”.
Wani irin qululu ya tokare zuciyarta ganin yadda
ta ke rarrashinsa yana qars botsarewa. ta juya
da hanzarinta tana sharar kwalla ta shiga ciki.
Dr Ahmad yabita da idanunsa dukda ‘ zafin da
zuciyarsa keyi bai hana shi jin tausayinta ba, sai
dai shi kansa bai san kalar zuciyar shiba da kishi
yakan sa ya kasa sarrafa kansa ba yadda ya
' iya haka ya juya ya fice daga falon
YAR. TALLAH
CHAPTER30
Saudat'na Shiga falon taga Momy zaune
hannunta rike da waya da alamar. magana ta
gama tana shirin giftata. ta wuce, Momy ta rika ,
hannunta. saudat ta waigo da sauri tana kallonta,
'don haka ta dawo ta raBa ta zauna zuciyarta
babu "dadi. ,
~ Momy ta kira sunanta, “Saudat dan rigimar nan
naki ba zai miki haqurin ki fara karatu ba, naga
alamar rigimamme ne na gaske, don haka nayi
tunanin a tsaida magana kawai in yaso ko a
gidanki kya yi karatunki idan kina da rabo har
gaba da sakandire sai ki wuce a gidanki don haka
yanzu zabi yana wurin ki shin tsakanin Hamid da
shi Ahmad din waye kike jin kina so a cikinsu”
Saudat ta dago a sanyaye ta dubi Momy
kafin ta ce, “Duk ina sonsu”. Momy tayi wata
tatacciyar dariya ta ce,
“To idan kina sonsu duka Saudat wa ki ke son
aura
A ciki kuma?”
Saudat ta yi shiru zuciyarta naci gaba da
' harbawa, ta. sani sarai soyayyarta a yanzu
tanaga
’ wurin Dr.“ Ahmad, to amma ta juya wa Hamid
baya ‘
' anya ta yi wa soyayyar da ya yi mata adalci?
To shi kuma Dr din fa?
‘ ‘ “ Momy ta katse mata tunanin da cewa
. “Ki yi tunani da kyau Saudat, duka mutanen biyu
duk suna qaunarki amma ni a nawa gamin
Ahmad shi ne wanda ya cancanta ki aura, amma
ki yi tunani da zuciyarki".
Saudat ta dago kai tana kallon Momy zuciyarta
na faman harbawa ta ce “Momy na zabi Dr din in
har ke ma ya yi miki
Momy ta dora hannu saman kafadarta ta dafa ta
tana fadar, “Hakan shi yafi cancanta
Saudat, tashi kije Allah ya yi miki albarka".
Saudat ta amsa da, “Amin”. Sannan ta mike cikin
sanyin jiki ta nufi dakinta, ta fada kan gadonta a
rufda ciki ta dafe kanta da hannaye biyu tamkar
mai shirin kurma ihu, ta lumshe idanu tana jin
zuciyarta na bugawa da qarfl, tamkar za ta ballo
Kirjinta ta flto waje. Sai dai ta samu taimakon
wata dunkulalliyar damuwa da ta tokare ta ta
hana ta baro kirjin harta fito fili, tana so ta ji
halin da Dr. Ahmad yake ciki, amma kuma tasan
babu dama.
Tana nan kwance har aka kira sallar magriba don
haka ta miqe ta nufi bandaki ta dauro alwalla ta
fito ta nufi kan sallayarta ta zura dogon hija‘binta
ta tayar da sallah, tana gamawa ta kishingida a
saman sallayar ta Iumshe idanunta tamkar mai
jin bacci, amma babu komai a zuciyana sai
dumbin damuwa. .
Ta yi nisa a duniyar tunanin da ta lula ta ji an
kwalla kiran sallar isha’I, a dole ta mike don ba
‘ da farali.
., saida ta gama sallar harta mike ba, zata Kara
kudundunewa akan sallayar tamkar mai jin ‘
sanyi, inda rai da zuciya keta aikin rarrabe
tsakanin Aya da tsakuwa anya dana dauki Dr.
Ahmad ta bar Hamid ta'yi wa soyayya adalci? ‘ ‘
Ba ta ji shigowar Nabila ba, sai dai ta ji ta dafa
ta tana fadar, “Aunty kizo inji Ya‘ya yana falo
yana jiranki” ' Saudat ta yi saurin tashi zaune
tare da rike hannun Nabilar tana fadar, “Wane
falon Nabila?”
‘ “Falon Daddy da baki”. Ta ba ta amsa. » Saudat
ta dan yi jim tamkar mai nazarin wani abu
tamkar kuma wadda aka tsikara ta zabura ta
mike ta shuri takalmanta ta fice ta nufi falon da
yake ta sa kai ta shiga tare da ‘yar siririyar
sallamarta, ba don Allah ya yi ta ita din mai ji
bace sosai daba yadda za a yi ta iya jin amsa
sallamar da ya yi a can qasan makoshi irin ta
wanda damuwa ta galabaitar da shi. ‘ Jikin
Saudat ya yi sanyi matuqa, ta zubawa fararen
idanunsa ido, yana zaune saman kujera ya ,
tallabe kansa da hannaye biyu ya zuba wa kaifet
ido. Jikinta a mace ta IallaBa ta zauna. saman
kujerar da ke gefenta, ta kasa dauke idonta a
kansa. sawon mintuna biyar falon tsit baka jin
motsin komai a ciki sai iskar A. C zaman shirun
ya fara damunta tana son kawar da shirun, amma
kuma bata san k0 ta Wacce hanya zata biba, to
k0 hakuri zata ba shi? Idan ma hakurin ne ta ya
ya za ta ba shi? K0 Shukura za ta kira ta bashi
kan wayar ta
"lallasar mata shi..
' Ba ta ankara ba sai dai ta ganshi a durkushe a
gabanta, kirjinta ya yi wani mummunar bugawa
saboda yadda yawa Kafafuwanta, ta yi saurin ja
da baya cikin kujerar, hakan ya yi daidai da riqo
hannuwanta duka biyun da ya yi, tare da kiran
sunanta cikin wata irin kasalalliyar murya wadda
ta tilasta mata dago kanta ta kalle shi, gabanta
ya yi wani mummunar faduwa, fararen idanun
nan nasa tamkar an watsa barkono, gabadaya ya
birice, ya canza tamkar ba shi ba ne wannan
tsayayyen daktan jarumi mai razanar da ita ba.
Ta runtse idonta da karfi saboda wani irin abu da
ta ji yana tsurga mata zuciya.
Dr. Ahmad ya kira sunanta da wata irin
dakusasshiyar murya, “Saudat ki bude idonki ki
kalle ni don Allah, kar ki tsane ni wallahi ina
sonki, irin son da duk duniya babu mai yi miki
kwatankwacinsa. ,
Saudat ki taBa zuciyata za kiji ki saurari zuciyata
zakiji, ki kalli zuciyata za ki game irin guguwar da
ke binne a cikinta, Saudat ina sonki
son da zan iya salwantar da rayuwata a kanki, ..
wallahi Saudat ina cikin fargaba tunda na bar
gidan '
Karkiji yaddah zuciyata kr cikin baqin ciki a dole
na dauro alwala na zauna ina ta ambaton Allah
Saudat na yi sa’ a bakin .cikin ya gushe, amma
damuwar da nake ciki ba ta barni ba har a
lokacin nan na kasa runtsawa, gani nake
zuciyarki na wurin‘ Hamid; da alama kuma za ki
iya barina ki “ koma gare shi a kowane lokaci,
wannan tunanin ne ya tilasta min dawowa Saudat
don in sanarda ke cewa, idan har kika kuskuren
juyawa zuciyata baya, to tabbas’ a ranar zakiji
mummunan labari ~cewa na rasu, don ba zan iya
rayuwa ba matukar
babu ke a tare danibs
Shirun da Saudat ta ji ne ya tilasta. mata bude
idanunta tare da kallon inda ta ke sa ran' yana
zaune, amma da mamakinta tuni har ya kai bakin
kofa, ba ta san lokacin da ta mike ba, tare da
kiran sunansa.
Ya waigo da sauri tare da daga mata hannu.
Karki ce komai Saudat soyayya ta zarce duk
yaddaki ke tunaninta, don soyayya gamon jini ‘
ce ba wai gamma gambiza ba, so haduwar
zuciyane ba wai tilasta shi akeyi ba Kuma
linzamin so ' hankaline ba wai son rai ba. Saudar
kar ki tilasta wa kanki ki soni don kawai kina
tunanin ya kamata ki so ni, ba zan kasance mai
son raiba na tilasta miki
aurena ba alhalin ba nine a zuciyarki ba. Tun
ranar da na soma sonki na kasance bani da. wani
buri da
Daya wuce son nagana dauwar dafarinciki
‘ zuciyarki, na dandana miki zaqin rayuwar da ba
ki taBa dandana ta. Va
Kuma kp a yanzu haka abin yake Saudat, dolene
na baki farin cikinki k0 da hakan yana nufin
rugujewar tawa rayuwar dole zan ba ki shi, kuma
na yi miki alkawarin sadaukar wa Hamid da
soyayyata matukar shi ne farin cikin rayuwarki”,
Saudat taji wani abu ya tsarga mata zuciya mai
kama da tsinin mashi, hawayen da suka tarar
mata a idanu tun dazu suka samu damar biyo
kuncinta, kuka nena gaske ya kwace mata,
Wanda ta rasa dalilin yinsa.
Dr. Ahmad ya yi saurin nufo ta, jikinsa na.
kyarma yana Kokarin riko ta, ta yi saurin ja da
baya
tare da fadar “Karka taBa ni don Allah na rokeka,
idan‘ har son da nayi maka bai gamsarda dodon
kunnenka ba don Allah ka fadamin kalaman da
zan yi amfani da su don su gamsar da kai, ni dai
in har na san abin da so yake nufi, to saboda kai
'ne in har dai abin da nakeji a zuciyata shine so,
to YallaBai na soka, so kuma kai kadai irin wanda
ba zai taBa Karewa ba har abada" Shi ‘kuma
hamid din fa ya zaki yi da shi Saudat? Yana
sonki kamaryadda nake sonki, babu wani dalili da
zaisa ki amince da daya daga
acikinmu don kawai kina ganin rashin
kyaumtawar ki guje masa Saudat ni na fadada
bakina na aminca miki ki zaba wa 'zuciyarki abin
da take so, k0 da ‘ kuwa hakan yana nufin bani
za ki zaBa ba, kuma hakan ba zai sa na karya
alkawarin dana dauka ba, na daukaka darajarki da
duk.......
“Ya isa don Allah ya isa haka!” Saudat ta yi
maganar muryarta a sanyaye cikin kuka ta ci
gaba da fadar, “Don Allah ka kyale ni haka, idan
na ce ban so Hamid ba YallaBai karya nake, sai
dai ina
so ka gane abu guda shine, irin son da nake wa
Hamid ba shi nake maka ba, sonka a cikin
zuciyata ya sha bamban da irin nasa, don kuwa
ka san shi murmushi yafi dariya. _
Abu guda kawai na sani shine, ba zan iya rayuwa
ba inba tare da kai ba, idan har ina da rabon
samun farin ciki da ‘ jin dadi a rayuwata to kai ne
farin cikina, kai ne jin dadin rayuwata”.
Da sauri ya nufe ta tamkar ‘zai kamo ta, sai ka
ce wani zautacce, muryarsa harsarkewa ta ke
Wurin fadar, “Da gaske Saudat kin amince za kl “
zama tawa? Za ki kasance da ni yanzu da har
abada? Saudat don Allah ki amince ki zama tawa
ni . kadai, wallahi a yanzu kece farin cikina, ke
kadai kika ragemin, kin amince min na turo da
‘ da sadakinki gobe, ki fada min Saudat, ke nake
saurare”. Kai kawai ta iya daga masa ba tare da
ta bar
zuciyarta ta yi wani dogon tunani ba
Farin cikinsa ba zai misaltu ba a lokacin ita kanta
Saudat ta tabbatar da hakan saboda yadda ta ga
ya dawo cikin nutsuwarsa lokaci guda ya koma
kan kujera ya zauna tare da sauke wata
nannauyar ajiyar zuciya. Ya jingina kansa akan
makarin kujerar yana sauke numfashi cikin
nutsuwa, idonsa na kan Saudat wadda ta kasa
zama.
Dr. Ahmad ya qakaro wani dan murmushi kafin
ya ce, “Kin min tsaye akai kina kallona k0 so ki
ke ki gano munina ne?”
Saudat ta yi saurin janye idanunta a kunyace tare
da‘ yar dariyarta Kasa~qasa.
Dr. Ahmad ya dan. kishingida kadan a kan kujcrar
yana fadar, “jeki samo min dan wani abu in ci
kada yunwa ta san yadda ta yi dani
A, dan sanyaye Saudat ta kalle shi, shi ma
'idanunsa a kanta suke adole ta juya ta nufl kofa
don kwarjininsa ba zai barta ta furta abin da ke
bakinta ba. Kai tsaye kicin ta nufa ta soma
dawainiyar sama masa can abin da ta san zai iya
ci, sai dai babu komai akicin din sai sauran
farfesun dare wanda ya ji kayan yaji, don haka ta
zubaruwa a kettle ta kawo garin citta da karunfari
da ganyen
ta zuba, sannan ta jona a wuta ‘ Tana nan tsaye
harya tafasa sannan ta juye masa“ta dora saman
tire ta dora kofi daya tare da cokalin shan tea,
sannan ta dora kular farfesun tasa filet da
madaidaicin spoon sannan ta bude tirij ta dauko
cake manya guda biyu ta dora a gefe, sannan ta
dauka ta shiga falon da yake da sallamarta har a
lokacin yana nan a kishingidensa; . Saudat ta
durkusa a gabansa ta zuba masa tare da
tsiyaya’masa ruwan zafl a kofi ta sa masa lipton
da coffe tare da madara da sukari kadan ta juya
ta miqa masa ya sa hannu ya karBa, bakinsa
dauke da murmushi ya ce “Na gode kwarai”
Murmushi kawai ta yi ta mike ta koma kujerarda
ke fuskantarsa ta zauna.
Tana kallonsa sai da ya cinye komai ita kanta ta
yi mamakin irin yunwar da ya kwaso, shi .kansa
ya lura da irin kallon da ta ke masa. Ya mike
tsaye da dan murmushinsa yana kallon agogon
dake daure a hannunsa, ya ce “Ni zan wuce, idan
har kallona da ki ke me cike da tuhuma ya
wadatar da ke Murmushi kawai ta yi, ta mike
tana tattara, kayan daya ci abincin, ya dan
mirgina kai ‘
”‘idan kin shiga gida ki sanar da Momy
manya zasuzo gobe insha Allahu misalin qarfe
hudu na yamma”
Allah ya kai mu’ amsa a takaice tare da bin
gefensa za ta wuce saboda kwarjininsa da takrjin
ya cika mata falon. Shi kansa ya lura da hakan,
cikin zolaya ya ce. “Ba sallama kuma Madam ko
har na angwance tun yanzu ne?” Ba ta juyo ba
ta yi gaba abinta saboda dariyar da ta ji yana
mata, ta tabbatar zolayarta yake son yi, don haka
ta yi cikin gida abinta. Washegari misalin karfe
sha daya na ‘safe; Saudat na kwance a falonta
saman kafet ta' yi matashi da filon kujera tana
kallon wa'azin Shekh
Ja’afar da aka sanyo na Sunna T.V mai taken‘
‘Suffatus salatun nabiyi'. '
A Kasan zuciyarta kuma tunani ne barkatai, tun
jiya data yi mafarkin Yaya Rabi‘u’ ta kasa
nutsuwa, tunanin dan uwan nata ya addabi '
zuciyarta k0 karyawa ta kasa yi, burinta bai wuce
na ta koma Dandagoro bA don ta karb saqon da
Hamid ya sanar da ita Yaya Rabi’ u ya bada
makotansu a ajiye mata, ta san gidan ba zai
wuce gidan Inna mai danwake ba, don gidanta ne
ke manne da nasu, kuma nan ne kadai gidan da
suké ' shiga ita da Yaya Rabi u alokacin suna tare
Bataji shigoWar Momy a falon ba, sai dai‘ ta ji ta
dafa ta tana fadar, “Bacci ne k0 kuma dogon
tunani?’
“” Saudat ta yunkum ta tashi zaune tana kallon ,
mahaifiyar tata wadda ke kokarin zama a kan
kujera, ta ja remote ta rage sautin akwatin
talabijin
‘ din tana fadar.
‘ “Yanzu Alhaji ke sanar da ni yau za su je wurin
Babanki don nema wa Ahmad aurenki, ni dai cewa
ma, na yi,,kawai a kyale shi aCi gaba da
,hidima a nan, Alhaji ya ce ba zai yiwu ba, dole a
ba
shi hakkinsa a matsayinsa na mahaifi.
* Ya ki ke ganin za a bullo wa tsarin bikin, don
rana kawai za akira ban da asabar din gobe ta
sama za a daura auren, kin ga dole musan abin
da za a shirya don kar IOkaci ya qure mana. Ki
min lissafin duk abin duk abinda kike so, don zan
tura a Dubai . za a hadp komai” ,. .
' Saudat ta sunkuyar da kanta tana wasa da
yatsu. Momy ta kafa mata idanu muryarta a
saayaye ta ce, “Saudat lafiyarki kuwa, me ke
damunki?”
‘ A hankali ta d‘ago kanta ta kalli mahaifiyar '
Kata da idanunta, wadanda suka ciko da kwalla,
ta ,
hadiye dunkulalliyar damuwar da ta ‘tokare mata
.
zuciya, kafin tace “Momy yanzu shi kenan Yaya
Rabiu ya bace kenan har abada?”
YAR. TALLAH
CHAPTER31
Momy taja wani gWauron numfashi kafin tace
“Inji wa ya fada miki Saudat? Ni naji a jikina
Rabi,u yana raya, kuma yanzu haka na_ baza ‘
*cigiyar‘sa tun daga gidajen talabijin, radiyo,
mujallu da kuma jaridu tare da ofisoshin jami,an :
tsaro insha Allahu Saudat zai bayyan, ki
kwantarda hankalinki kinji Saudat ta daga mata
kai kafin ta ce, “Tun *’ ina Abuja Hamid ya sanar
da ni Yaya Rabi’ uv ya ba da sako a makwabta a
bani nasan gidan Inna mai danwake ne shine
nakeson inje inkarbo Momy ta ce, “A‘a ba zan iya
barinki ki je ba, sai dai inwa Alhaji magana ya sa
k0 direba ne yaje ya karbo miki hakan ya yi
miki?" ‘ Kai kawai Saudat ta iya daga mata
alamar eh. ’ . ' Tace “Okay lissafo min abubuwan
da ki ke *bukata, kodai kin bani wuqa da nama
ne? . Saudat ta amsh da, “Eh Momy”. Dariya
Momy ta yi kafin ta ce ‘Wannan fillancin naki ya
yi” yawa Saudat, anya kuwa?” ‘ ‘ Dariya kawai
Saudat ta yi mahaifiyar tata ta fita ta barta ,
Misalin karfe budu na yamma Shukura taxo , “
gidan da‘ yar qaramar jakar kayanta, dadi ya
cika' Saudat don kwana biyun da tayi babu ita
ba’ " 'qaramin kewarta tayiba
Shukura ta sauke jakana a kan gado tana
fadar “Amarya kin sha kamshi, wannan fara arfa
duk ta murnar amarcin ne?” Saudat ta waro ido
cikin dariya ta ce“Kai _
don Allah meye na zolaya kuma? ’ ‘
' Shukura ta fadakan gadon tare da rungume ta
tana fadar, “Ba wani nan zolaya, gaskiya na fada”
' Saudat ta tabe baki ta zauna a kan kujera tana
fadar, “Ai da ma Hausawa sunce idan baka
iya sharri ba ka koyi kage” .,
Shukura ta ce, “Ba wani nan, haka nan ki ke nuna
wa Momy kauyanci amma irinku sululu kasau
kunfi kowa iya shege
Saudat ta yi dariya tana fadar, “Yau kuma da
mita ki kaxo gidan kenan?”
Shukura ta ce “Ai dole in miki iya shege, don
Momy ta kira ni wai na tattaro na taho mu zauna
don ta lura kina bukatar huduba ta, ni kuwa
Tasan ba wani nan k0 karya na fada?"
Saudat ta mike tayi hanyar‘fita daga falon tana
fadar, “Ni ban iya abin da kika iyaba”. 1
Shukura ta tuntsure da dariya don ta san ta
Qular da ita.
, Washegari da safe suna zaune a falo Shukura na
karanta wa Saudat wani littafin Hausa mai suna
KADANGARUN BARIKI, Momy ta turo
Ta turo .Kofar ta shigo tare da fadar, “To sai ku
tashi ku shirya yanzu maza direba ya kai ku
gidan Maman ‘ Sumayya maida tsohuwa
yarinya” . ' ' Shukura ta zabura tana fadar, “Wow
Momy! Da gaske?” . ‘ Momy ta yi murmushi tare
da Juyawa tana fadar, “A’a da wasa”. , ~
Shukura ta dafe Saudat tana fadar, “Kai . amma
wallahi Momy tanaji dake Saudat, lallai zaki rudar
da DR wai baki taba jin labarin Maman Sumayya
a Abuja ba?" Saudat ta girgiza mata kai a
hankali, don ita ‘ dai ba ta fahinci inda maganar
tasu ta dosa ba. , Shukura ta ce, “Lallai, da
mamaki don a * fadin Nigeria babu jihar da sunan
matar nan bai , zaga ba, kaya ta ke siyarwa ‘yan
gaskr, tun daga kan, gyaran gashi, gyaran fata,
sabulluka zuwa mayukan gyaran
DOWNLOAD
DOWNLOAD

Please Login or Register in order to submit comment