Join Our WhatsApp Group

Idan ku ka ga kun taba wani wuri ya fitar daku a shafinmu, sai ku danna back kuyo baya, ku sani yanzu muna amfani da tallan Popunder a shafin, so karatu zai muku dan wahala, amma ta hakanne kadai zamu iya cigaba da rike shafinnan. idan har bakwa son talla sai kuje ku yi subscription na shafinnan akan karamin kudi ku runga downloading kawai. SUBSCRIBE


DOWNLOAD

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register
DOWNLOAD

fata, kayan
manyan mata kuwa wannan daga qasashen
Larabawa ta ke hada su. Ke dai bari ‘ mu je za ki
gane wa idonki” Saudat ta ce, “Ita kuma amarya
har wani . gyara na daban ake mata.” , Shukura
ta yi wani takaitaccrn murmushi kafin ta ce “In
ban da abinki Saudat, idan akwai . macen da ta
ke bukatar gyara a bayan amarya ta ke ko kuma
macen da ta haihu ita amarya ana bukatar ‘
komai nata ya xama na musamman ne tun ba ke
da"
Zakiyi aure gidan kishiyaba, ya kamata ta ko’ina ,
mijinki' ya san da bambanci, tun daga tafukan ,
hannunki, labbanki, fatar“ jikinki, da kuma
fuskarki, sai kuma can ainahin wanda wannan
kuma aikin manyan mata ne musamman idan
auren na Soyayya ne
Abin da dai nake so ki gane shi ne ranar bikin
kowace mace to awurinta wannan babban ra'na
ce da babu irinta a rayuwarta, musamman idan
auren na soyayya ne.
A ranar daurin aurenki kowa burinsa ya ga irin
kwalliyar da zaki yi, kek0 da ‘yan gidanku ne suna
son qare miki kallo a wannan ranar, shi yasa
wasu matan tsabagen son gyaran jiki har gyaran
‘sai yazo ya yi yawa, ya feSo musu 'da quraje a
fuska k0 da ba bata da wadannan kurajen a da.
Don
haka a matsayinki na aMarya ya kamata ki kula
da kanki, akwai sirrikan abubuwan da ke gyara
amare na farko a matsayinki na amarya ana
bukatarki da yawan sham ruwa sirrin hakan shi
ne, kar jikinki ya yankwane. Sannan ana bukatar
amarya da cin “ya yan itatuwa hakan zai taimaka
wa fatar jikinta matuka, ‘ sannan ana bukata:
amarya da ta yawaita sham , kankana, ita ma za
ta taimaka mata matuka wurin gyaran fatar
jikinta, haka kuma cin ganye irin su. latas da
kabeji, suma za su taimaka kwarai.
Ta yinkura ta nufi bandaki tana fadar “Bari in fara
watso ruwa mu shirya tun
kafin Momy ta sake biyo mu” . Ta zame kayan
jikinta ta shige bandakin don
watsa wa jikinta ruwa. lko sai mai tsaga ido Allah
Almusawwiru, mai yadda Ya so, tabbas na yarda
komai nufi ne na Ubangiji, kuma al’amarin aure
tamkar layin . kasuwa ne idan layi yazo kanka k0
bakaso sai an maka, kamar yadda arziki bai isa
ya guje wa ‘mai shiba, haka shi ma rai bai isa
yaqi mai shi ba, haka matar mutum ba ta isa ta
guje‘masa ba k0 ana ’ ha-maza ha-mata, auren
da Ubangiji ya qaddara to fa sai an daura shi duk
tsananin wuya, kuma duk dadi don duk nisan dare
gari zai wayr. Hakan ce kuma ta kasance don yau
ita ta kasance ranar juma'ar da za a daura auren
Saudat a asabar
In ka duba gidan Dr. Mariya acike yake da yan
uwa da abokan arziki na kusa da na nesa, don ‘ a
ranar ne za a yi kamu, wanda Dr. Mariya ta
shirya . Biki ne ake ba wai na wasa ba, don kudi
ta ke kashrwa tamkar tana tsinto su
mafiyawancin abubuwan da ake yin amfani dasu
a wurin bikin duk
daga qasashen waje ta bada saqonsu aka taho
mata‘ ‘ dasu
DukvWanda ya ”san Saudat kuwa yancu” idan*
ya ganta da wuya idan zai iya ganeta Cikin sati
~daya ta yi wani fitinannan haske, don har wani
.yalo-‘yalo ta ke, fatar jikinta ta yi wani luwai-
luwai
’sai sheki ta ke tare da daukar ido tamkar jikin
tarwada, cikia lokaci guda ta rikide tamkar wadda
aka Kara wa kyau da fari.
Kodayake irin manyan kudin da Dr. Mariya
ta saki wurin gyara ‘yar tata sun isa ace ta
maf1 ; haka. don k0 gyaran jiki sau uku aka mata
arana, safe da yamma da kuma lokacin kwanciya
bacci, don daidai da Kunshi daga Abuja ta dauko
mai zanen da ta yi musu, gyaran gashi ne aka yi
musu ’ a babban wurin gyaran gashin da ke G. R
A,abinka da ma da mai abin don haka gashin ya
isa saukowa , har tsakiyar bayanta, ga wani baKi
da sheqi da yake na musamman. Haka dinkunan
fitar .biki duk a Lagos ta ba da aka dinko mata
wasu kuma a -. Dubai sai shaddojin ne ta bada
aka dinkosu a Maradi. Yanzu haka Saudat ce da
Shukura baje a falo suna duba kayan fitar kamun
da za su sanya a yau, Momy ta turo kofa ta
shigo da sallamarta, ta ' tsaya daga bakin kofa
jikinta a sanyaye ta ce
“Direba Ya daWO yanzu‘ amma har yau dai mai .
danwake ba ta dawo ba, sai dai maigidanta ya
’tabbatarda cewa, duk abin da aké ciki ba za ta
rana ita yau ba tare da ta dawo ba" ‘
Cikin nutsuwa Saudat ke kallon mahaifiyar tata,
cikin sanyin jiki da sanyin murya ta amsa da,
“Allah ya kai mu Momy, Allah Ubangiji ya
bayyana mana shi ma kafin lokacin” .
, Momy ta amsa da,“Amin”. Kafin ta dau wani
nannauyan numfashi tana kallon Shukura ta *
ce “Ya kamata fa ku yi azamar shiryawadon Karfe
hudu daidai za a fara kamun”.
Shukura ta amsa, “Insha Allahu Momy
yanzu za mu shirya”. ' ' Momy ta juya ta fice
Shukura kuma ta mike tana fadar, “Tashi‘ yar
uwa ki fara shafawa jikinki ruwan lallen nan kafin
in fito daga wanka”
K0 motsi Saudat ba ta yi ba ballantana ta sa ran
amsawarta, hakan ya sa Shukura waigowa ta
dubi inda Saudat ta ke, tare da fadar,“Lafiya dai
Saudat. " "
A hankali ta dago kanta tana kallon Shukura kafin
ta ce, “Babu komai”.
" Shukura ta girgiza kai, “A’a ban yarda ba
Saudat, na lura damuwar fan uwanki na damunki
amma ya kamata ki yi wa Momy uzuri, saboda
yadda ta ke iya bakin qokarinta bai kamata ki
Kara , daga mata hankali da damuwarki ba. Kina
kallo tun ‘. ranar daki kace mata yayanki ya‘
bada sako
gidan mai danwake a ajiye miki Momy kullum sai
ta tayar da direba ya je gidan, amma har yau ba
a yi nasarar sa'mun mai danwaken ba, tunda an
ce ta je
garinsu Ki kara haquri don Allah Saudat, insha
Allah zaki ga sako mai dadi wurin mai danwake
da
zarar ta dawo tashi ki rage kayan jikinki in taya ki
shafa
‘ Ba musu Saudat_ ta yun kura ta mike don ta
sani haquri ya zame mata dole, k0 da ba a ba ta
ba ita. ta ba wa kanta tunda dai babu wanda ya
san inda Rabi’ un yake. Shi kansa Dr. Ahmad din
yanzu iya kokarinsa yake mata a kan“ cigiyar dan
uwan nata' saboda yadda ya ga ta damu a
kansa. , ’ Da taimakon Shukura da kuma na
matar da ‘ . Momy ta dauko mai kwalliyar amare,
aka gyara amarya Saudat cikin wani tsadadden
cotton lace mai laushin gaske kalar dark pink an
qawata shi da bakaken fulawoyi da wasu
qananun duwarwatsu, masu kama da yarfin gwal,
daurin kallabin da aka kafa mata duk wanda ya
kalla ya san daurin‘shago ne don ba irin wanda
muka sabayi bane gashin ’ nan nata an saki
kadan gefen fuskarta sauran kuma an nade shi an
saki jelarsa a kan gadon bayanta inda
aka kawata wuyanta da kunnenta zuwa yatsun
hannunta da tsadaddun gwala-gwalai Sannan
suka dora ta a kan bakin takalmi mai
matsanancin tsini sai ka ce wadda ta hau tsani
sai yar qaramar jakarsu wadda ba ta wuce
girman tafin hannuba
Amarya kam ta fita batun bayyana irin
kyawun da ta yi ma bata lokaci ne, don k0
lokacin .da ta ke zama a kan kujerar da aka
tanada
' don amarya, saf ta zauna tamkar mutum-
mutumi, ko ace aljana don kyau, kai ka zata zana
ta aka yi ba ‘ wai mutum bace
“Ana kiran sallar magriba aka tashi daga kamun,
a lokacin ne kuma Dr. Ahmad da abokansa ' '
suka iso gidan cikin tsadaddun motocinsu, don
haka gidan ya kara rikicewa, Shukura ta shiga
busy
don ganin ta karrama angwayen da abubuwan
ciye ciye da tande-tande.
Saudat kuwa duk kunya da nauyin Dr Ahmad ne
ya hana ta sakewa da kyar Shukura ta samu ta je
ta gaishe shi shima sai da ta yi da gaske a
lokacin da ta shiga falon da aka sauke su gogan
nata yana kishingide saman doguwar kujera
abokansa sun sa shi a gaba suna ta hayaniyarsu,
' inda shi kuma yake ta faman kallonsu yana cin ,
tuffa apple.
Saudat ta ji tamkar ta nutse a lokacin da suka
hada idanu, sai taga ma tamkar shima kara masa
kyau akayi, farin yadin neke jikinsa ya Kawatar Da
kyar ta yi ta-maza suka gaisa da abokan nasa
sarakan surutu kamar zasu hadiyeta
Kowa burinsa ya fadi albarkacin " bakinsa ita dai
ta gaza tofawa sabuda kwarjinin da angon nata
da ya cika falon, ji take duk girman dakin ya yi
mata kadan, sauqinta ma daya Shukura da ta
tare ma rigimar domin don kuwa ita
wurin dan banzan surutu ba ‘daga baya ba. Dr.
Ahmad wanda tunda ta shigo falon bai * ,tanka
ba har sai da ya lura zolayar abokan nasa za
‘ ta iya nutsar da Saudat cikin qasa don kunya, ~
sannan ya yunqura ya mike a kasale tamkar
wanda aka yi wa dukan tsiya.
, Ya nufi inda amaryar tasa ta ke nutse cikin
kujera ya sa hannu ya tayar da ita tsaye yana
fadar, “taso mu bar nan Madam kada su samin
ke ciwon kai
Kamar jira suke suka yi kansa, amma bai kula
suba yana rike da hannunta suka fice daga falon
kai , tsaye harabar waje suka nufa, ya jawo musu
wasu fararen kujerun roba suka zauna cikin
rumfar da aka tanada don hutawa
Dr Ahmad ya yi wani murmushi mai kama
‘ 'da dariya lokacin da yake Kokarin lallai sai ya
hada , ido da ita amma ta Ki yarda shi dariya ma
ta ba shi, ya tallabe kuncinsa yana fadar, “Oh ni
Ahmad na ga ta kaina, haka zamu yi dake
kenan?”
Ya Kara sa dariya, “Lallai yarinya aiki ya , ganki
bama kadan ba, amma fa kin yi kyau don‘ lokacin
da ki ka shigo falon sai da nayi suman wucin
gadi har wani kishi na ji ya yunkuro min yadda na
ga kartan nan na kallonki shi ya sa na harna
.gaza magana
, Duk yadda zuciyar Saudat ta ke cike da
alkunyarsa sai da dariya ta kwace mata jin yadda
ya kira wayayyun abokansa da qartai, Dr. Ahmad
ya kafe ta da manyan idanunsa yadda ta ke
dariyar ’ tata cikih nutsuwa
kallon da yake mata ya sa a dole ta gimtse
dariyarta, hakan ya yi daidai da sauke wani
gwauron numfashin da ya yi tare da lumshe
manyan fararen idanunsa ya shafi sumar qeyarsa
yana kallon farar moter da take shigowa cikin
gate din ’gidan a dan nesa da su kadan aka faka
motar daga ita har shi idonsu na kan motar.
Zuciyar Saudat ta yi wata mummunar bugawa
lokacin da mutumin da ke cikin motar ya fito shi
da wata zukekiyar mace kai tsaye inda suke
zaune suka nufo har a lokacin kirjin Saudat
bugawa yake ta gaza k0 da kwakkwaran motsi.
“Hamid dinne k0? ’
, Dr. Ahmad ya watso mata tambayar yana .
kallonta Kai kawai ta iya daga masa don a
lokacin har sun qaraso cikin sallamarsu inda
Hamid ya
miqawa Dr Ahmad barin fuskarsa ‘dauice da fara
a suka yi musabaha Hamid na riqe da hannun '
Dr Ahmad ya taya shi murna tare da yi masa
fatan aikhairi cikin sanyin jiki, Saudat ta gaishe
shi amma ga mamakinta har a lokacin da fara,a
akan fuskarsa ya amsa mata a. tare da yi mata
fatan aikhairi ya nuna zukekiyar macen dake
tsaye " wadda akalla shekarunta ba zasu haura
ashirin da daya ba . Yacé, “Ga Kausar nan
takanas 'muka taho‘ tare don ta taya ni murnar
aurenki, ita ce amaryar ' tawa“. Ya juya kan
Kausar din, “Kausar ga Saudat ’ Da‘ fara’a a
fuskarta ta miqa wa Saudat hannu suka' yi
musabiha cikin sigar zolaya ta dubi Dr. Ahmad
tana fadar, “Godiya mara: adadi, .ka taimake ni
tunda ka kasa‘ angona don da yanzu Kausar ta
shiga cikin jerin sahun matan da za ayiwa kishiya
a wannan watan,na gode ‘ Dariya suka yi su
dukkansu ganin yadda Dr. '"‘ Ahmad ya Saki
fuska babu alamar damuwa a yanayinsa ya sa
Saudat ta saki jiki ta mike ta riko hannun Kausar
tana fadar, “Bismillah‘ yar uwa mu
shiga daga ciki mu gaisa sosai " Dr Ahmad ya
mike shi ma tare da miqa wa Hamid hannu yana
fadae “Ni ma abokina. mu shiga
daga ciki gida na kula abin yar wariyar launin
jinci ce”. , Duka dariya suka sa suka rankaya
suka nufi
cikin gidan
Zuciyar Saudat fes, ba qaramin dadi tajiba
Ganin yadda Dr. Ahmad ya karBi Hamid din cike
da ‘ farin ciki. Ba Karamin mamaki‘ ta yi ba
yadda Hamid ya samu labarin aurenta, kodayake
auren da kullum sanarwa ake a gidajen tal'abijin
da radiyo lallai ita kanta ta san ba Karamin
matsayi Hamid yake da shi a Zuciyarta ba, har
cikin ranta ta ji Kausar ta kwanta mata don
kawai tana matar Hamid hatta rasa inda’za
ta_saka ta, ta kawo mata wannan ta' kawo
wancan har sai da Kausar ta dakatar da ita, ita
kuma Shukura ta ci gaba da dawainiya da Hamid
din. ' . Ba su suka bar gidan ba sai qarfe goma
na
dare don sai da suka gaisa da Momy da Alhaji .
Ashiru sannan suka tafi a cewar gobe Hamid zai
maido , Kausar gaskiya su duka sun yaba da ‘
matar Hamid din don ba qaramar kyakkyawar
mace ya samu ba, wayayyiya kuma yar boko. ’
Ba Saudat ba hatta Momy da Shukura sunyi _
mamakin irin makudan‘ kudin da Hamid din ya
baiwa Saudat wai ta. siyi abin da ta ke So, tunda
‘bai _ samuya siya mata komai ba. Lallai Hamid
ya
dauka Saudat da muhimmanci a rayuwarsa, haka
da ma al’amarin Ubangiji yake
.Washegari ita ta kama ranar asabar da misalin
qarfe daya na rana aka daura auren " Saudat da
angonta Dr Ahmad Mukhtar ; daurin aure ne
wanda ya tara manyan mutane kala daban-daban
tun daga gida Najeriya har zuwa sauran
Kasashen qetara abbas daurin auren ya kafa
tarihi a cikin Dandagoro ‘
Motoci suka dauki amarya da tawagarta zuwa
gidan mahaifinta da ke Dandagoro don wai a can
ne za,a dauki amarya, kamar yadda Alhaji Ashiru
ya bukata ba don ran Momy yasoba ta amince
Haka manyan motoci suka kwashi amare aka nufi
gidan mahaifinta, amarya’ Saudat dake lullube
'cikin mayafl Kirjinta ya shiga dukan tara-tara
don ba tasan irin tarbar da dandazon Jama,ar
zasu samu a gidan nasu ba. Haka suka shiga
cikin
gidan mahaifiyar Shukura da DR murja qawar
Momy na riqe da amarya har cikin gidan. Inna
Laure da ke durkushe bakin murhu na ganinsu ta
zabura ta mike tsaye tamkar sabon kamun hauka
' : Fuskar nan tata dukta gauraye da majina da '
hawaye saboda hayakin wuta ciki kaduwa take
fadar, “Wannan dandazon haka fa sai kace na
masu zuwa yaqi na menene?
' Dr Murja tace“Au maigidan naki bai
Fada miki bane? To amarya ce aka kawo gidan
ubanta a dauke ta a ciki”.
‘ Kida a ruwa mai tada haukan dodo tana
fadar haka Inna Laure ta yo kanta da masifa, ‘
‘Amaryar ukan abun uba za a kawo gidan ubanta,
k0 ita uwar amaryar bata sanar muku ba ‘yar
tata ruwa biyu bace? Ai ba ta da uba don haka
an dai daura aure a gidan nan amma babu dan
iskan da ya isa ya-shigo min gida don a ci min
zarafi
Mahaiflyar Shukura ta kwantar da murya ta ce,
“Haba baiwar Allah meye kuma abin cin fuska
don' dai kawai dan zaman da za a yi wanda bai
=wuce na minti talatin ba?”
Ai kamar jira ta ke ta koma kanta, “Ke rufe mani
baki kin ji tsohuwar banza, ai da ma garin 'banza
a farau-farau din wofi yake qarewa, gida dai nawa
ne, kuma dole ku bar min abuna in ba haka
"ba'wallahi sai in cinna wa gidan wuta mu hadu
mu duka mu qone za ku fita k0 kuwa ba zaku fita
ba?” Ai kafin wani ya ba ta amsa ta kwaso itacen
da ke cikin wuta ta yo kansu * *‘ Malam Bala da
ke kokarin shigowa cikin gidan ya yi wani kukan
kura ya yi kanta ya rike ta ta 'baya, hakan ya
sata fasa wani razanannen ihu tana kokawar
kwacewa, ya murde hannunta ya na cewa
[8:43AM, 06/02/2017] 🙆🏼‍♂@lh@ji🙆🏼‍♂: YAR. TALLAH
CHAPTER32
Complete
Bakida hankaline ya kwace itatuwan tana ihu tana
tirje~tirje da zuba ~ munanan ashariya ya danna
ta dakinta ya kulle, ko,a haka aka barta ya ishe
ta azaba saboda tsananin zafin da ake
kwararawa a garin ga shi dakin ba shi da tagar
shan iska k0 kadan ’ Malam Bala ya nufo su
yana basu hakuri akan abin da Inna Laure ta yi
musu, ita kuwa Saudat idonta na kan mahaifinta,
za ta iya cewa tunda take da shi ba ta taBa
ganinsa ya yi irin kayan da ya yi ba, saboda
tsadadden yadin da ke jikinsa wanda aka yi wa
dinkin yar ciki da babbar riga, kayan sun sha
aikin hannu.
Dr.Murja ce ta ja mayafin Saudat ta rufe mata
fuska, wanda haukan da Inna Laure keyi ya sa ta
budewaba tare datasani ba
Malam Bala ya kwasa ya nufi dakinsa yana yana
raWar jiki, sai ga shi ya dawo dauke da manyan
tabarmi shi da kansa ya shimfida mnsu a tsakar
gidan suka zazzuna shi ‘kuma ya juya ya gita
baifi minti sha biyar ba sai ga shi ya dawn do.
wasu almajirai dauke da ledojin pure water dana
kwalayen ‘ ,lemuka katan-katan‘ aka jibga musu,
ita dai Saudat ta cika da mamakin abin da kr
faruwa sun kwashe mintina talatin a gidan
sannan angwaye suka zo daukar amaryarsu don
haka Shukura da mahaifiyarta suka tasa Saudat a
gaba
har zuwa zaure inda mahaifinta yake don ta roqi
gafararsa.
Saudat ta durkusa a gabansa jikinta ya yi sanyi
ba ta san abin da za tace da mahaifin nata ba,
abubuwan da suka faru ne a baya suke dawo
mata cikin zuciya, tamkar a yanzu ne suke
faruwa.
Tamkar Malam Bala ya san abin da ta ke tunani,
sai ga shi yana furta, “Don Allah don Annabi
Saude ki yi hakuri ki yafe min duk abin da na yi
miki wanda ki ka sani da wanda ma ba ki sani
ba. Na san na zalunce ku sai dai~ na san sharrin
shaidan ne, don Allah don Annabi ki yafe min
kafin na mutu wallahi ban san abin da-zan cr da
Ubangijina ba, tabbas na ga ishara a rayuwata,
kuma na yarda zakaran da Allah ya da chara k0
ana muzuru ana shawo sai ya yi, Saude ki yafr
min don Allah don Annabin rahma
“sunyi mamakin yadda kuka ya ci qarfinsa ba
suboda tun yana maganar muryarsa ke rawa, ba
karamin‘ sanyi jikin Saudat ya yi ba jin kukan
dattijon. nata don haka ba tareda zuciyarta ta
qara tuna mata komai ba ta ce “Ka yi hakuri
Baba, ni
ban rike ka da komai ba, wallahi na yafe maka’
Cikin kuka Malam Bala yace ‘Wallahi ni “ ba kiyi
min komai ba Saude, inma kinmin ba yafe
miki Allah Ubangiji ya yi miki albarka, Ya ba ku
zaman lafiya da zuri’ a dayyaba Saudat bata iya
amsawaba, sai dai Momyn
Shukura ce ta amsa sannan ta kama Saudat ta
mike suka rankaya aka nufi mota da amarya ,
Masu kai amarya suka dunguma a motoci, amma
abin mamaki sai ga wasu daga cikin jama’ ar ,
unguwar cikin masu rakiyar amarya babu goro “
ballantana katin gayyata
Har motocin daukar amarya zata dags Malam
Bala ya kwaso da sassarfa yana daga musu ‘
hannu, suka tsaya ya nufi motar da Saudat
ke‘ciki, ta taga ya mikamata wani Kunshi a baKar
leda. Ta karBa cike da girmamawa, sannan
motocin , suka rankaya da amarya sai garin
Abuja, alqawarin, Allah ya cika, don karfe biyu na
rana a gidanta ya yi mata wanda yake a unguwar
‘yan majalissu.
Saudat ba ta kasa gane gidan ba duk da kuwa
canje-canjen da ya qara samu, haka suka
rankaya Zuwa bangaren amarya, sai dai mucr
barakallahu fihi, masha Allah don Dr.» Mariya ta
murza naira wurin fiddo da ‘yar tata don haka‘
tsarin gidan zuwa tsarin kayan ya qawatar da
falukan da aka zuba suka yi dace da juna, don
komai an sa shi cikin tsari, don haka duk wanda
ya je kai amarya sai da ya firgiga wai ahakan ma
donyawancinsu sun saba shiga irin gidajen amma
‘yan Dandagoro
kuwa sai ga su darshe a kan marbles suna ta
faman zare na mujiya, Shukura dai na rike da
amarya, Saudat wadda ta ke jinta tamkar a
saman gajimare wasu daga cikin dangin ango ne
krta faman dawainiya da su tun daga abubuwan
ci zuwa na sha harna tande-tande irinsu dambun
shinkafa dambun nama, shinkafar kaza, soyayyun
kaji, farfcsun kaji, donut, meatpie spring roll, fried
rice, hadadden salad chips din kwai da dankalin
Turawa, fruits kala-kala har da wanda ba su taBa
gani ba da sauran kwalayrn lemuka da robobin
ruwa masu sanyin gaske.
Saudat dai da ke cikin mayafi tana jin karadin
Farida qanwar Ahmad don ta fi kowa kai wa da
kawo wa an agama sallar la’asar motoci suka
kwashe ‘yan kai amaryar don dawo da su gida
bayan an cika su da sha tara ta arziki.
Sai a lokacin kuka ya zo wa Saudat ganin duk za
su watse su barta, Shukura ce ta rungume ta tare
da yi mata rada, sai ga ta tana kuka da dariya,
lokaci guda duka suka rankaya suka tafi suka bar
Farida rungume da Saudat kowa ya watse
Su Farida da wasu ma ’aikatane ke ta faman
gyare-gyaren gida, sai ga shi cikin dan lokaci
Bangaren nata ya zama very need, babu abin da
ke
fita a cikinsa sai qamshin room freshner mai
sanyin
Farida ta dawo bedroom din da Saudat ke ciki ta
zauna gefenta cike da kulawa ta ce “Aunty
Saudat ki shiga bandaki ki watso ruwa sai ki
dauro alwala don lokacin sallar magriba ya yi”:
Saudat ta Ki k0 motsawa haka kawai take jin
gabanta na faduwa ba ta da wani kuzari.
’ Faridat ta yi murmushi tana fadar, “Ho Aunty
anya wannan dari-darin da ki ke a cikin * gidanki
zai fisshe ki kuwa?”
Ta Kara murmusawa, “To yi hakuri dai muje na
raka ki ki watso ruwan” .
Ta sa hannu ta riko Saudat din don haka ta
sauko daga kan gadon tana Kokarin bin qofar fita,
Farida ta ce, “Ina za ki kuma? Ki shiga bandaki
din nan mana dama don kar a Bata. mikine ya sa
na ce su shiga wancan bandakin da ke dayan
falon”. ' Saudat ta dan yi sororo don ita dai ‘a iya
ganinta ba ta ga wata‘ kofar bandaki ba don
tsakanin falo ma da bedroom gilas ne ya raba ‘
tsakaninsu, don haka duk cikin falon babu wata
alamar kofa.
, Faridat ta mike ta nufi wurin gilas din ta danna‘
yar wata alama sai ga shi ya raba kansa biyu ya
fidda wata‘ yar hanya wadda ta zarce har cikin .
bandaki Farida ta shiga ciki, don haka itama: _
Saudat ta bi bayanta. Farida ta gwada mata.
yadda
Zatayi amfani da komai na bandakin sannan ta
fita dan ta samu damar watso ruwan ' Tana
fitowa ta samu Faridat ta qara gyara gadon har
ta ciro mata kayan da zata saka don haka
Saudat ta nufi inda sallaya ta ke ta yi sallar
magriba ta zauna, har lokacin isha ya shigo
sannan ta yi sallar tare da shafa’ i da wutiri
wadda Momy ta . koya mata tare da wasu daga
cikin ayyuka na addinin musulunci tana idarwa ta
mike ta nufi kan gado inda Farida ta ajiye mata
kayan da za ta saka, wasu lallausan yadi ne
kalar baki mai taushin gaske wanda aka kawata
shi da wasu fararen duwarwatsu masu haske.
Saudat ta saka yadin a jikinta Wanda aka yi'wa
dinkin riga da siket yadin ya bi jikinta ya lafe a
farar fatarta. Farida ta shigo tare da ‘yar siririyar
-sallamarta hannunta na rike da wani
madaidaicin faranti da ke dauke da ‘yan wasu
kananan kwanuka ns tangaram. Ganin Saudat ya
sa ta ta saki murmushi, “Yauwa Aunty Saudat k0
ke fa? Ki dan yi make up k0 ya ya ne Murmushi
kawai Saudat ta yi ta nufl gaban ,dressing mirro
ta ja kujera ta zauna tana kallon gaban madubin
.wanda ke shake taf da kayan x kwalliya irin na
wayayyun mata da suka san kansu.
Body lotion kawai .Saudat ta dauka ta murjawa
jikinta, sannan ta murza wa fuskarta wata yar
karamar hoda wadda ta ida fito da tsabar kyawun
fuskarta, sannan ta shafa wa laBBanta wetlips
gloss, sai da ta Kara gyara gashin kanta ta dame
shi da farin ribbon kwara guda ta sake shi a baya,
sannan ta yi sassaukan daurin kallabi a kanta
wanda ya Kara fito da ita, ta dauki ‘yan qananan
‘yan kunnayenta da sarqa na diamond ta maqala
a kunnenta ta 'saka ‘yar qaramar sarqa ta dauki
turarenta body spray ta mammatsa a‘ gaBObin
jikinta, ita kanta ta san ta yi kyau irin wanda ke
nutsar da zuciyar maigida, ta juyo ta nufo inda
Faridat ke tsaye tana tattara ‘yan komatsanta.
Muryar Saudat na rawa ta soma fadar,“ina kuma
za ki je don Allah : naga kin yi lullubi kina tattara
jaka?”
Faridat ta mike tana kallonta da murmushi a
kan fuskarta, “Maigida ya yi kira Saudat, amma fa
kin yi kyau sosai, nasan yayana zai yaba don
Allah kada dai a yi masa rowa". Tayi maganar
tana dariya tare da shafar beauty point din
Saudat din ta juya a gurguje ta fice tana fadar,
“Don Allah ki ci abin da na hado miki, please
Auntyna".
Saudat da ke tsaye ta bita * da , idanunta masu
kama da madara harta ta fice ba
yadda ta iya haka ta sadakas ta koma da baya ta
zauna a kan gadon nata wanda kr fitar da ,
sassanyan Kamshin bed freshner Ta miKa hannu
ta janyo tiren da Faridat ta ajiye mata ta soma
dudduba abin da ke cikin‘ yan kwanukan da
kofinan, na farko gasasshen nama ne wanda ya ji
kayan yaji, sai na biyu wani' irin nama ne Wanda
aka yi wa 'wata irin dahuwa mai danko, sai' kofi
na farko tsumin markadaddun ‘ya'yan itatuwa ne,
dayan kuma danyar madarar shanu ce , mai kyau.
“ Duk da ba ta fahimci amfanin abubuwan a gare
ta ba, ta daure ta ci sosai kamar yadda Faridar
ta roKa. Ta dauki tiren ta fice da shi ta mayar da
shi a kicin da ke falonta na biyu, ta tsaya tana
kallon kicin din, komai na ciki tsab.tsab gwanin
kyau, ko falon wani mai kudin sai haka, don haka
maimakon ta bar kayan a haka, sai ta soma tara
ruwa ta wanke ’su cike da sha’awar komai na
kicin din Ba ta ji motsin shigoWar mutum a kicin
din ba sai dai ta ji an
DOWNLOAD
DOWNLOAD

Please Login or Register in order to submit comment