Join Our WhatsApp Group

Idan ku ka ga kun taba wani wuri ya fitar daku a shafinmu, sai ku danna back kuyo baya, ku sani yanzu muna amfani da tallan Popunder a shafin, so karatu zai muku dan wahala, amma ta hakanne kadai zamu iya cigaba da rike shafinnan. idan har bakwa son talla sai kuje ku yi subscription na shafinnan akan karamin kudi ku runga downloading kawai. SUBSCRIBE


DOWNLOAD

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register
DOWNLOAD

kuma amana ce a gare ku abin tambaya a gobe
kiyama idan ku ka cutar da ita ku ka wofintar da rayuwarta
wallahi sai Allah ya kama ku a kan hakan duk dakuwa
kukukahaife ta. ' Baba, Saudat tana da masu sonta da aure
a nan garin, da kuma ni kaina, sannan Saudat yarinya ce
qarama Baba bai kamata ku_ tankWare rayuwarta ku zaba
mata mijin da bai cancanta da ita ba don kawai saboda,
wani dalili naku ka yi haquri Baba na san kuna da hakkin
zaba mata mijin da ya yi muku, amma Baba’ zaba " mata
mijin da ya‘ dace da rayuwarta don Allah don Annabi Baba
ka dubu girman Allah ka yi wa rayuwar yarinyar nan
adalci ' Tunda Malam Bala ya sadda kansa bai dago ba,
komai yake tunani oho! Inna Lame ‘ wadda take labe a
tsaye hannunta dafe da kofa . tana sauraren duk bayanan
Dr. tace, “To muna godiya Alaramma, Allah ya biya. Sai a
tashi a tafi umma ta gaida assha, kuma abin da . :ka yiwa
"yarmu Allah ya sa ayi wa taka, mun . kai diya aiki ka hure
mata kunne ka lalatata ka
maida mana, ka iske kuma za a yi mata aure kana Kokarin
hanawa kai shaida, saboda dandin bai iske ka ba? To ta
fada mana komai, kuma ba abin da za muce maka sai mu
ce ka je Allah Ubangiji ya yi mana sakayya".
Dr Ahmad wanda ya ji maganganun tamkar: saukar
markade, ya dago da sauri yana kallonta cike da mamakin
maganganunta ya
Kasa cewa komai, su Malam Bala ne ya
Daga kai yana fad'a, “Ya Isa haka Laure, koma cikin gida
don Allah”
Inna Laure ta ce, “Ka bar ni da wannan‘ babbab shaidanin
mai munafurcin kashe aure ya maida mana diya karuwa,
kuma saboda rashin imani ya biyo ta har gida ya ce kar a yi
mata aure‘ tunda bai gaji da lalatar ba. Malam ka
kalli Saude sosai na rantse maka da Allah cikine daita”.
ldanuwan Malam suka yo warwaje * saboda tsabar dukan
da maganar tata tai masa a
Kirjinsa. Cikin rudu ya mike yana fadar“Laure ki shiga gida
haka wuce ki tafi” Ganin maganganun nata sun yi tasiri a
zuciyar Malam yasa ta juya tana matsar kwalla a
munafurce ta gefe tana kallonsa “
Malam ya dubi Dr. Ahmad zuciyarsa na huci yace “Malam
mun gode kwarai amma don Allah ina rokonka ka tashi ka
tafi don Allah”. .
Dr ya danne mamakin da ya cika masa zuciya, cikin qarfin
hali ya bude baki da niyyar yin magana.
Malam ya daga masa hannu cikin tsananin fushi ya ce.
“Babu abin da za ka fada don Allah don
Annabi ka tashi ka fita ko na samu zuciyata ta sassauta”.
‘ Dr. ya mike tsaye cikin halin jarumtaka,
don gabadaya zuciyarsa' rugurguza ‘ta ,ke
tamkar za ta Balle Kirjinsa ta fito fili. Ya danne
abin da ke yunkuro masa kafin ya iya Karfin
halin fadar “Ka yi hakuri Baba, wallahi tallahi na
rantse maka da Allah ban aikata abin da kuke zargina da
aikatawa,ba kuma na amince zan tafi amma don Allah ka
bani minti biyu in magana da Saudat a gabanka
Malam ya zabum masa “Kai Malam ka ga ka bar nan tun
muna shaida juna, don
wallahi Saude ba za ta sake fitowa ba sai idan za,a tafi da
ita dakinta, ka ji na gaya maka".
Dr Ahmad yaji tamkar anwatsa masa tafasassan ruwan zafi
mai qona zuciya. Ya lumshe idanuwansa yana jin tamkar
mala’ikan mutuwa ya taho ya zare masa ransa koya’ huta,
ya bude idanuwansa da kyar
‘wadanda suka ida rikicewa ba ka ganinkomai ‘ cikin shi sai
tsananin ja tamkar garwashin wuta.
Ya zura hannunsa cikin aljihu ya zaro ' gabadayan canjin da
suka yi masa saura, yasan bazasu haura dubu hamsin ba,
ya ajiye a kasa
' tare da fadar kayi hakuri a bata wannan canjin insha l
Allahu ko tana gidanta ne zan yi mata aike” Ya juya ya fice
yana kokarin dauke kWallar da ke neman~zuraro masa .
Malam ya duka ya dauki kwalin yana . faman juyawa a
hannunsa, Laure da ke labe tana jiran ta ji yadda zasu qare
ta zabura ta yo ' c'iki'n soron ta yi caraf da kudin tana fadar
yauwa "‘KaWo su nan Malam". ‘
Shi hatta ma ba shi tsoro ya sakar mata
~ ya tsaya yana kallonta, ta soke a zani tana . fadar
“Allah ya ga tsimurmular da muke muna ta fama da Tv
Stand ba kayan kallo yanZu k0 ka ga
wad‘annan sai a siyo ma ‘yar baba irin wannan talabijin din
wadda ake lika wa jikin bango da ‘ kafet din tsakiyar daki su
kadai ne dama ba a siya ba”
. Malam Bala ya ce“Haba Laure, yarinyar nan ita aka ba wa
kudin nan, kuma kina sane daga katifa da zanin gado da
labule babu abin da aka sai mata, yanzu wadannan ba ' sai
a Kara a sai wani abun ba?”
Inna Laure ta ce, “Haba Malam ka sani fa sarai irin
mutumin da ‘yarbaba ta aura, dan masu da shi fa dan gidan
hali, ne za su rike; mana ita da mutunci? Ita ko Saude Garba
ne fa ka sanni na sanka, kar ce ta san kar to mu wahalar da
:kanmu na me? Dakunan fa naji ‘yan jere na fadar daki daya
ne ya ware mata mai girma, to me za mu zuba a cikin daki
daya? Ai da ma
Dan gado ne da katifa toga katifar nan ko zuwa gaba ai:
idan Allah ya hore ai sai mu yi mata gadon k0 ya ka ce
Malam‘?" ’
Malam Bala ya ce, “Shikenan aje a yi k0 ma . ‘ me za a yi.
ni dai na rabu da yaran nan lafiya
nan da awa daya za a wuce da su gidan Yaya Maje”. . ‘
Laure ta amsa da, “An gama Malam ’Sannan ta juya ta nufl
cikin gidan ta bar shi yana kwashe tabarma.
Tunda Dr Ahmad ya fita ya fada , motarsa ya kifa kansa
saman sitiyarin motar bai sake dagowa ba,» duniyar
gabadaya «ta shiga juya masa, ya rinka jin tamkar ana sa
guduma ana sassaka masa kirji
Ya dauki tsawon lokaci a kife tamkar matacce jijiyoyin
kansa suka tattashi rado rado abunka ga jar fata, kamar an
zana su, wani irin ciwonkai mai zafi ya sauko masa, ya.
dagO‘ kansa da Kyar wanda ya ke jin ya yi masa bala’in
nauyi ya mika hannunsa a kwabar jikin .motar ya dauko biro
da takarda ya yi wani dan rubutu layi biyu ba tare da ya flta
ba, ya kira yaro cikin dasasshiyar muryarsa ya ce, “Ka san
Saude?" ‘ "‘
.Yaron yace, “Yar talla, wadda ku ka zo
yanzu tare? Dr». ya ce, ‘Ita don Allah karBi ka kai
mata, ka tabbatar ka ba ta hannunka da nata, kar fa ka ba
wa kowa kaji?” '
Yaron ya amsa da, “To". Sannan ya juya ya nufi gidan a
guje.
Dr. Ahmad ya maida murfin motar ya rufe ya yi mata key,
ya ja sannu a hankali ya bar unguwar.
Saude wadda tunda ta shigo gidan ta fada dakinta wanda
aka maida shi na zuba tsummokara ta zube a Kasa ba tare
da ta damu dadattin dayayiba, tashiga rusarkukamai ‘ tada
hankali ji ta ke gabadaya ta tsani rayuwar.
Yaron ya shigo tsakar gidan inda jama'a ke ta hidimarsu ya
tambaya, “Ina! Saude?”
Inna Lami ta nuna masa dakinta, yaron ya nufi dakin, ya
iske‘ ta kwance Kasa~ tana sharBar kuka, ya ce “Ga shi inji
mai mota a waje ya ce na kawo miki”.
Saude da ke kife tana kuka a dago da kanta a hanzarce
tana kallon yaron ta karBi takardar hannunta na kyarma
tana qokarin warwarewa kamar tasan abin da aka rubuta ta
zuba wa kyakkyawan rubutun ido wanda ta ke jin tamkar
shi ne ta ke gani, yaron ya juya ya tafi ya barta tana kallon
rubutun da ba zata iya karantawa ba, illar jahilci”. Ta fada
ta qara durkushewa ‘ta dukunkune takardar ta sake
Ta qara fashewa da wani sabon kuka mai ban tausayi..
Yaya Rabi’u ya fado mata a zuciya, ta tuna rayuwarta da
shi, da irin yadda yake rudewa idan ya ga hawayenta ya yi
ta rarrashinta, rayuwa ke nan, ga ta yau tana kuka ba ta da
wanda zai ce ki yi shiru balle har ya rarrasheta.
Yau ta yi' kuka kamar ikon Allah idanuwanta suka kumbura
suka yi luhu-luhu, ga bangaren kanta da ya dauki ciwo a
dole ta saurara da kukan saboda yadda ta ke jin kan nata
kamar zai rabe biyu.
Ta tashi zaune ta jingina da bango ta ‘ rafsa uban tagumi
tana tunani mai tarwatsa zuciya, Inna Lami ta tah0 dakin ta
turo mata robar tuwo wanda aka yaba wa miyar taushe ta '
ce, “Ga shi nan idan kin gaji da kukan ki dauka ki ci da
sauri, don yanzu za a wuce da ku gidan uban wanka”.
Ta wurgo mata bakar leda, “Ga wannan atamfar uban
wanka ceda takalma ‘yan Maradi da abaya wanda za ki
saka a tafi, maza don ba ke za a tsaya jira ba”.
Tana gama fada ta juya ta yi gaba abinta ta bar Saude na
bin ledar da tuwon da kallo, a
yanzu idanuwanta sun KeKashe babu abin da suke sai zogi
da radadi mai ciwo k0 motsin kirkibatayiba, har Inna. Lami
tadawota ~ dauki sallallami, “Wai Saude ya ki keso da
mune, kefa kawai akejira,karma kici tuwon
kanki kidaukikayan kisaka mushine ‘ matsalarmu”
Ta yi tsaki ta juya abinta.
Saude ta Ki motsawa daga inda ta ke don yadda ta ke ji.
zuciyarta k0 kashe ta za su yi ba za'ta saka kayan ba, har
yanzu ji take kamar a mafarki ne komai ke faruwa. Ba ta
fidda rai ba da za ta farka a kowane lokaci ta ganta a gidan
Dr. Ahmad don haka ta soma linke takardarda
Dr. Daya aiko mata ta daure a
haBar riga tamau. ' Inna Lami ta dawo ta tsaya daga bakin
Kofa cike da masifa ta ce “To sai ki fito tunda ba zaki sauya
kayan ba, wlh ko,a tsirara ne sai mun kai ki, ehe”. .
Sayde ta yi maza tana faman muzurai, tana faman kaiwa da
kawo wa, idonta ya sauka inda su ‘Yarbaba suke tsaye da
.qawayenta, sun sha anko ana ta shewa.
Yar baba ta watsa mata harara tare dajan
dogan tsaki
Saude ta sunkuyar dakanta bataredata kula ta ba, Inna
Lami ta ce ‘Taho nan, ‘Yar baba mu je ai muku nasiha gaba
daya
Ta sa hannu ta rike ta Saude na biye da ‘ susuka shigadakin
da Lauretake.
Badai wata'nasiharkirki bace duk habaici ne ta ke yaba wa
Saude, ta yi abinta ta gama sannan lnna Lami tatisasu gaba
har~ wurin Malam Bala shima nasiha ce dakuma 'jankunne
kada waddatasake talullubo zaninta wai da sunan yaji balle
wani abu wai shi jaWarci, duk wadda ta sake ta kashe
aurenta, to saidai tasan indazata nufa sannan yayi musu ,.
fatan alkhairi daga nan aka dauke su da motoci ’zuwa gidan
uban wanka, shi ma'ya yi musu nasihar tasa. Ana gama
sallar magaruba ” .motocin kai amarya suka zo, qananan
motoci ~ masu shegen kyau guda biyar, mijin ‘Yarbaba
yaturo dasu na daukar amarya.
Shi kuwa Garba gurgu a kori kura ce kwara guda daita za a
dauki amaryar adauki ‘yan gidansu don haka mutane duk
suka kwashe suka nufl motocin‘ daukar ‘Yarbaba da. Kyar ..
aka samu wasu mutum biyu dattijai wadanda za su raka
Sauden.
Haka aka kwashe aka tafi da amaren, Saude ta lumshe
idanuwanta kukan ma ya Ki yiyuwa, idanuwan sun qafe sai
radadi suke, zuciyarta sai faman bugawa ta ke da sauri da
sauri tamkar za ta tarwatse. ‘
Direba ya ja wani dogon birki kiyyyy! Ya tsaya a kofar gidan,
ginin kasa wanda aka shafe da farar kasa, tsohuwa ta riko
hannunta.
“Fito mu je ‘yar nan ki shiga da qafar dama, da kuma
bismillah”.
Saude daina ‘ jin maganganun nasu tamkar amSa kuwwa a
kunnenta,ne fuskarta na . rufe da hijabi suka shiga cikin
gidan mai dogon zaure wanda doguwar kwata ta raba biyu.
Suka isa tsakar gidan ‘yan tsaffin na fadar, “Gafaranku dai
masu gida”.
Babu wadda ta kula su daga cikin matan
gidan sai‘ yan yara ne ke ta tsallen murna, an kawo musu
amarya su suka nuna musu dakin nata aka shiga da ita,
cikin dakin wanda duk
cikin gidan shi kadai ne ya ci arzikin aka filasce shi da
siminti, aka goga masa ‘yar farar
Qasa ciki da bai, babu komai a dakin sai tsohon yadin zanin
gado da fululuwansa guda biyu, dakin ya sha sabuwar ledar
Kasa an kuma zagaye bangon dakin da sabuwar sitara sai
‘yan kayan ma’aikacinta a gefe.
Tsohuwa Iya ita da kawarta' hare suka zaunar da Saude a
gefen katifar ba tare da sun zauna ba, ta ce, “To mu za mu
wuce Saude sai mu ce Allah Ubangiji ya ba da zaman laflya,
a yi ta dai hakuri da rayuwa a duk yadda ta zo watarana sai
labari, mu dai mun wuce”.
Saude dai dake kife saman katifar k0 dagowa ba ta yi ba
ballantana su sa ran za ta tanka su ma ba su saurari
tankawar tata ba suka fice abinsu. A soron gidan suka hadu
da ango an sha sabon farin yadi da sabuwar hula, bakinnan
an cika shi da dusar goro, fuskar nan tasa babu annuri sai
sambatu yake, “Yo harni za a yaudara? Ai karya ne wallahi,
duk wanda ya ci tuwo dani miya ya sha. Yauwa bayin Allah
da ma ku na biyo, ku koma ciki yadda ku ka Kunso
tsohuwar karuwarcan ku ka kawo min haka za ku koma ku
dauko ta ku koma da ita, ba a gidan Garba ba, k0 da ku ka
ganni haka nakasasshe to ban gaji da rayuwar duniya ba".
' Tsohuwa Iyah ta tafa hannaye tana fadar, ‘Muhammadu
dan Abadallah, Malam Garba me ya yi zafi haka?”
Garba ya taso mata, “Abin, da ke cikin wuta, kin ga tsohuwa
ina ganin girmanku kar ki sa in dankara miki ashar ku shiga
ku fiddo ta in ba haka ba wallahi zan yi abin da ba a
tunani,don dukan mutuwa zansa ai muku a cikin gidannan
harda ita tsohuwar karuwar ku fiddo ta in kulle dakina kon
tsinke
‘babu babu abinda zai fita bayan ita in kunje ku fada wa
tsohon banza na ce na ba shi nan da kwana uku
k0 ya aiko min da duk abin da ya san na kashe
ko kuma in sa kayan dakin a kasuwa ku fada masa na sake
ta saki uku”.
Daga nan ya juya yana tsangala qafar ya . bar su a sore
Hare ta dafa Iya tana fadar, “Yau munga takanmu ni hare
kinga koma kifitoda yarinyar nan mu maida ta hannun
iyayenta, " wannan nakasasshen banzar zai iya fiye da duk
abin da ya fada”
Don daman ance gurgu yafi mai qafa iya shege
Iya ta ce, “Aikuwa na gani bari in fito da
ita". Ta Juya ta koma cikin gidan.
Lol jama,a ya abin yakene ku biyoni donjin yaddah zataci
gaba da kayawa
[1/30, 10:24 AM] A A Dboy: 📚📚DAGA GROUP OF HYPE HAUSA NOVELS BOOK WHATSAPP 08064400100📚📚
[12:17PM, 02/02/2017] 🙆🏼‍♂@lh@ji🙆🏼‍♂: [1/30, 4:30 PM] A A Dboy: *YAR TALLA*

BOOK 3

*CHAPTER 23*

Saudat na kife a katifarta tana rusar kuka, Iyah ta shigo,
“Saude tashi maza mu tafl" ,, Saudat ta dago da sauri tana
kallon Iyar da jajayen idanuwanta, ji take tamkar zolayarta
ta ke Iyah kuwa ta mika hannu ta kamo hannun Saudat tana
fad'ar, “Tashi. maza mu tafi, yau mu ai mun ga ikon Allah”.
‘ Saudat ba ta iya yin musu‘ba ta mike ta bi Iyah suka fito,
inda suka iske har hare ta kai qofar gida don haka suka rufa
mata baya suka rankaya, Saudat jin abin ta ke tamkar cikin
mafarkinta, to me ke faruwa ne? "‘
""""""""""". '""""""""
Tunda Dr Ahmad ya yi wa motarsa key ya dauki hanya
tafiya kawai yakr amma ba tareda yasan irin tunaninda
yakeyiba gudu yake saman titi ba na wasa ba, tamkar
wanda ke dambe da iske,, Allah dai ya kawo sa garin Abuja.
. ~ Babu inda ya yi wa tsinka sai gidan iyayensa; yana faka
motar tasa ya kulle murfin , motar ya sa qafa ya shiga
tamkar'wani mara lakka‘
ya na cikin gidan nasu, da ‘yar siririyar sallamar da shi
kadai ya san yayi ta. ‘ Babu kowa a falon shiru babu komai
sai kukan AC,kamar wand aka
hankada ya fada saman doguwar kujera ya rungume fitan
kujerar ' tare lumsha ,idanuwansa tamkar wanda ya sha
wani abin maye, yana shakar sanyayyen qamshin turaren
wuta dake tashi,sannu ahankali yana falon tsawon
mintunan da suka haura talatin babu wanda ya fito falon ,
sai can Hajiyarsa ta fito daga falonta da alama ma ma fita
za ta yi don’ sanye ta ke da atamfa super Holland wadda .
aka yi wa dinkin riga da siket, ta da wani qaton mayafi
wanda tsadarsa ta tasar wa dubu talatin. Hannunta na riqe
da hannunta na riqe da qaramar jaka bazaka taba cewa ta
haura shekaru arba”ba, amma nan sittin ne hard ‘yan kai. <
Kodayake k0 shi uban gayyar a yanzu talatin da shida ne ke
kanshi Ganin Dr a falon ya bawa Hajiyar mamaki Dr. ya
bude idanuWansa da gyar yana . kallonta tamkar wanda ya
yi cutar shekara guda
wuyansa tana fadar, “Lafiyarka kuwa Ahmad? Me ke
damunka ne "
Dr. ya dago hanunsa da kyar ya dafa kansa .kafin ya ce
“Momy kaina kamar zai rabe biyu, zuciyata fashewa za ta
yi”.
Hajiya ta dimauce ta soma kiran sunan
Allah tana fadar, “Yau ni na shiga uku Ahmad tashi mu je in
kai ka Maitama District Hospital a duba min kai".
Dr. ya girgiza mata kai, “No Momy ki kyale ni don Allah,
ciwona ba na asibiti bane, bugun zuciya ne idan na dan
samu relive zai damau. .
Ta ce“Kamar ya zai daina Ahmad? wacce irin damuwa ce
wannan da ta ke qokarin kai ka kabari?”
Dr. ya ja dogon numfashi kafin ya ce “Momy sun hana ni
Saudat, wallahi Momy ina sonta, taBa zuciyata ki ji yadda
ciwo ke‘ nuqur kusar zuciyata".
Momy ta dan zuba wa dan nata ido, kafin tace “To ita
Saudat din sukace bazasu baka ita baka ita ba sai kace
wani mai
mugun hali? Duk duniyar nan da ma akwai inda zakaje
neman aure ahana ka?”Dr. ya girgiza kai “Wallahi Momy
baza su barni na auretaba don Allah Momy ki ba ni
shawara, ya zan yi?” .. Hajiya ta sauke wata nannauyar
ajiyar zuciya kafin ta raBa kusa da shi ta zauna, ta cusa
hannunta 'cikin sumar kansa tana sosa . masa cikin Sigar
rarrashi ta ci gaba da fadar. “Don Allah ku zamo mai
tawakkali Ahmad, ka zamo mai juriya da rungumar abin da
Allah ya qaddara maka, ka sani bai hana ka Saudat don ba
ya sonka' ba, sai don kawai ya jarrabe ka Ya gwada
imaninka, haba dana kai _ din fa mai kwarin zuciya ne, ina
kwanjin dana ’ Sanka da shi? Haba dana ka zamo mai juriya
kaji?" ‘ ' Kai kawai ya iya daga mata ta ce ’ “Yauwa nawan
daure ka tashi mu tafi aSibitin ’ Doctor ya duba ka yanzu
mu dawo” , Baimusa ba yayunkura dakyar tana riqe da
hannunsa suka fice ta sa direba ya jasu 'cikin babbar Jeep
dinta suka nufi asibitin.
Iyah na"riqe da hannun Saudat har suka isa gidan, ita dai
tafiya kawai ta ke, amma ba ta san inda ta ke jefa Kafarta
ba, sunsa qafa cikin zauren gidan ta ji gabanta ya yi wata
mummunan faduwa, irin wadda ke sa mutum ya yanke jiki
ya fadi.
Suna shiga tsakar gidan suka yi karo da Inna Laure, wadda
ke qoqarin hada hankalin gidan kasancewar duk ‘yan bikin
sun watse tunda har isha ta karato ga shi kuma hadari ya
gangamo a garin. Suna shiga tsakar gidan Inna Laure ta
zabura ta mike tana fadar, “Me nake gani haka kuma ni-
Laure, ba ku kai ta gidan nata ba ne k0 ya ya aka yi?”
Iyah ta ja hannun Inna Laure ta damqa mata Saudat.
“Ga amana mun maido, yarinya mijinta yace ya mata saki
uku saiku nemi dalili a wajensa, mu kuwa mun tafi Allah ya
ba mu alheri”.
Suka juya suka yi gaba abinsu.
Inna Laure ta hankade Saudat da ke
hannunta tana kwalla wa Malam Bala kira, wanda ke
qoKarin fitowa daga dakinsa yana
zuba sallallami, kira yake“Me kunnena ke jiye min Laure?”
Inna Laure ta taBe baki.
“Abin da ka ji Malam ni ma shi na ji”.
Malam Bala ya nufi Saude ya nuna ta, “Ke kuwa wannan
yarinya ban ji dadin haihuwarki ba, wannan nan uwarki ta
haifa min jaraba da alaqaKai, kalu’inna lillahi wa"inna ilaihi
raji’un, keko yau sai kin bar gidan na gaji ba zan iya ba
wallahi na gaji. . .”
Saudat ta fashe da wani dan marayan kuka na rashin sanin
madafa, ta dora hannuwa biyu a kai, ta rasa abin da ke
mata dadi, tashin hankalin da ta gani Kiri-Kiri a idanuwan
mahaifin nata shi yafi firgitar da ita, ta zuba wa Malam Bala
ido wanda ke jin zuciyarsa tamkar za ta tarwatse saboda
tashin hankali, wasu irin hawaye masu zafi suka biyo
kuncinsa, cikin tsananin takaici da bacin rai ya ce. ; “Ai dole
ya sake ki Saude, don idan ba dan iska irinki ba babu
namijin da zai iya zaman aure da ke, amma ina so ki sani ni
na riga na sauke nauyin da Ubangiji Ya dora min a kanki,
don haka sai dai ki nemi inda zaki
amma ba dai gidana ba, yadda ki ka taho haka 'zaki juya ki
tafi duk gidan uban da zaki, kuma tsakanina da ke Allah ya
isa ban yafe miki ba” Saude ta ji kalamansa tamkar saukar
. ruwan zafl a jikinta ta durkushe a gurin tana wani gunjin
kuka. ' “ Malam Bala ya dube ta a fusace, “Eh ’zamama
kikayi kenan kina kukan rashin kunyar, ai ko zaki bar gidan
nan a nakashe”. Ya juya ya rarumo muciyar Inna
Laure‘kafin ta yi yinkuri ya muka mata a baya .Saude ta
fasa wata uwar Kara ta sheme a qasa Malam Bala ya hau
maka mata muciyar ‘ ' iya Karfinsa, ya hau fadar, “Ni za ki
dauka dan iska? Ni zaki kawo wa shakiyanci a cikin gida? ‘
‘ Ganin yana shirin kisan kai yasa Inna Laure ta riae‘Ke shi,
ta soma ba shi haquri, sai data yi da gaske sannan
tasamuya ya. kyaletaya ta nufi dakinsa yana sharar gumi,
duk da kuwa ba ’
«lokacin zafi bane a lokacin. ~ , .
Saude kuwa ko kwakkwaran motsi ba ta yi, saboda
doguwar sumar da ta yi. Haka duk suka shige ciki suka
barta ayashe tsakar gida kamar ba dan mutum ba.
Tsawon lokaci wani irin iska mai hade daguguwa yataso
tare dasaukar wasu ruwan sama masu qarfi tsawon lokaci
ruwan na dukan Saude kafin ta fara motsawa sannu a
hankali ta bude idanuwanta a hankali abubuwan da suka
faru suka rinka dawo mata tamkar bidiyo. Ta runtse
idanuwanta da sauri tanajin tamkar zuciyarta zata tarwatse,
ta yunqura ta mike da kyar wata irin tsanar
’mahaifin natane maitsani ne tarinqaji zuciyarta batada
wata bukatar data wuce barmasa akurkin gidansa dukda
wani irin
masifaffen ciwon da jikinta ke mata amma
hakata takarkare ta fito daga gidan dukda
juwar da ke faman rufe mata idanuwa. ga
kuma tsananin ruwan saman, ga-tafiyar tata tamkar: ta ‘yan
kayo saboda tsamin da jikinta yayi Cantaji andanno mata
oda abayanta da qarfin- gaske Saude ta ji har cikin dodon
kunneta tamkar zai rabe biyu gashi kuma an
danne odar an Ki saki. Saude taji tamkar ta zuba da gudu
saboda yadda ta ke jin hatta ‘yan ‘ cikinta na amsa kuwwar
odar sai dai ba qarfin jikin da za ta iya yin gudun, don haka
ta durkushe a gurin.
Cikin takaici Hamid ya Balle murfin motar ya leko da kansa
cikin ruwan cike da masifa yana fadar, “Ke k0 wacce irin
mace ce ‘ ana miki oda ba ki ji, kawai ki zauna saman
hanya k0 aljana ce ke ai kin kauce daga saman hanya
donkar waniyazo ya takaki cikin rashin sani”.
Saukar muryarsa a dodon kunnen Saude ya sa‘ ta saurin
waiwayowa don tabbatar wa cikin wata rikitacciyar murya
Hamid ya kira sunanta tare da zabura ya fito daga cikin
motar ya nufo ta yana fadar, “Saude ke ce kuwa, ko dai gizo
ki ke min?”
Ya durkusa a ‘gabanta, “Lafiya Saude me ya fiti dake daga
gidanki cikin wannan damunan?”
Cikin kuka Saude ta some fadar. "Sakina ya yi Hamid, ya
sake ni".
Hamid ya dafe kai, “Innalillahi wa’inna ilaihirrajiun
Wayaji miki wannan ciwon a jiki haka? Dubi yadda jini ke
zuba a jikinki”.‘ ‘ Sai a lokacin ma ta lura da wani irin
kwasheshen ciwo da ta ji a gwiwar hannunta. . Hamid ya ce
“Tashi !maza mu tafi asibiti kada jininki ya Kare”. '
Ganin tana ta KaKaniyar tashi ya sa ya sure ta da kuzarinsa
ya sata a mota ya maida ya rufe, ya zagaya gidan direba ya
shiga ya ja, kai tsaye ya nufi medical center da ita.
Cikin .ikon Allah yana zuwa ya samu likita Dr. Mariya ta
karBe ta aka wuce Emergency room da ita, abu kamar wasa
sai da ' aka shafe fiye da awa guda Hamid na nan' zaune
babu wanda ya fito, tsoro ya cika masa zuciya tun yana
addu’a a zuciya har ta fara fitowa fili. . .
Can cikin ikon Allah sai ga Dr. Mariya , ta fito,Hamid ya
zabura ya miKe ya nufe ta yana fadar,“Lafiya dai k0 likita?”
Dr: Mariya ta yi murmushi kafin tace
*‘Ka kwantar da hankalinka Malam Hamid * insha Allahu
‘yar uwarka za ta samu sauKi ‘ amma yanzu ka biyo ni ofis
akwai wasu yan ; tambayoyi dazan maka
Cikin karyayyar zuciya hamid ya amsa da, “To". Sannan
yabi ta ofis din
Sai da ta zagaya ta zauna ta cire gilashin fuskarta sannan
ta nuna masa wurln zama, Hamid ya ja kujera ya zauna
yana kallon magidanciyar matar, wadda a qallah ba data
wuce shekaru arba‘in. Ba
Dr. Mariya ta gyara zamanta tare da tattaro duk wata
nutsuwa, kafin ta ce “Malam Hamid don Allah akwai wasu
‘yan tambayoyi da nake so in maka, da fatan za ka yi min.
uzuri, ka kuma fada min gaskiya, amma fa kayi hakuri".
Hamid ya qara tattara nutsuwarsa sosai yana kallonta,
kafin ya
DOWNLOAD
DOWNLOAD

Please Login or Register in order to submit comment