Join Our WhatsApp Group

Idan ku ka ga kun taba wani wuri ya fitar daku a shafinmu, sai ku danna back kuyo baya, ku sani yanzu muna amfani da tallan Popunder a shafin, so karatu zai muku dan wahala, amma ta hakanne kadai zamu iya cigaba da rike shafinnan. idan har bakwa son talla sai kuje ku yi subscription na shafinnan akan karamin kudi ku runga downloading kawai. SUBSCRIBE


DOWNLOAD

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register
DOWNLOAD

da
saba,in ake saida ita
Cikin sanyin jiki nace yabada kudin babu kuma
vata lokzaci ya qirgo kudi a aljihunsa ya _
mikamin nakirgasu naga sun cika sannan najuya
nasoma tafiya.Saidaifa inda gizo ke saqar bansan
gidanwa
zannufaba, gadai kudi ahannuna ammabanda
wurin zuwa don haka najana zauna asaman wani'
dakalin dake wajen kasuwar na kira mai abinci na
.siya na ci na qoshi, na sha ruwa na ci gaba da
kallon titi, wannan mota ta wuce, waccan ta wuce
a haka fa aka yi sallar magriba da isha, dare ya
soma duk ina a zaune a nan fa fargaba ta fara
shiga ta.
‘Banyi auneba naji andafani,harna dan firgita ashe
mutumin dana siyarwa waya ne. ya zauna a kusa
da ni yana tambaya ta, “Wai lafiyarka kuwa
Rabi’u?”
Jin ya kira sunana ya sa nayi saurin kallonsa, sai
a lokacin na shaida shi ashe Yasayyadi ne dan
dan oganmu wanda nake aikin Kasa a wurinsa.
To in takaice muku nan na sanar da shi halin da
nake ciki, na korata da mahaifina ya yi har tsintar
wayar da nayi. Ya yi matuqar tausaya min, a nan
yace in tashi mu tafi shi zai taimake ni.
Yasayyadi ya kai ni shagonsa da yake kwana
wanda ke like jikin gidansu ta waje nan na ci
gaba da zama, kwanana uku Yasayyadi ya ba ni
shawara da na fara sana’a, ni ma ya ga kamar
masu shi go da shinkafa a Kasar nan suna samu
k0 zan fara? Na amince, ya hada ni da wani
abokinsa muka fara safarar shinkafa daga qasar
Nijar zuwa Najeriya da ma ina da jari a hannu.
Allah Ubangiji kuma ya sa min albarka, sai ga ni
cikin fan kankanin lokaci na tara kudi masu kauri
a hannuna, a lokacin ne na sanar da Yasayyadi
ina son. shiga makarantar boko, shi ma ya yi
na’am da
shawarata, don shi a lokacin yana shekarar
Karshe ta kammala digiri. Shiyayi duk wanicuku-
cukun da akeyi na hada takardun firamare natafi
js3 kaitsaye cikin yan watanni nazana. JSCE
sannan na wuce SS one na maida hankali sosai a
karatuna, wanda bai hana ni neman kudina ba.
Abin ma kamar harda sa hannu don duk abin da
na taba cikin ikon Allah sai ya zama kudi, a haka
naci gaba da karatuna zan shiga aji biyar na
tsallake na wuce aji shida. Ina kammalawa na
zana jamb na yi sa’a kuwa na bugo point din da
ake so, wato 200 point don haka ban " samu
wani matsala ‘ba wurin samun admission a
Umaru Musa ‘Yar 'Aduaa university suka ba ni
Mass
Com na soma karatuna cikin nasara ina level 2 na
fara shigo da motoci daga waje zuwa Najeriya a
lokacin ba zan rasa jarin da ya wuce naira
miliyan ashirinba, don harnafara aje yara suma
sunaci a qarqashina nayi gida nayi mota na tashi
daga gidan su Yasayyadi na koma. gidana, a
lokacin shi ma ya yi aure ya samu aiki da
hukumar zabe ta qasa yana zaune da matarsa a
lokwas din kofar: Maruba.
A lokacin da na gama digirina aka turani garin
Lagos in yi sabis dina, na tattara na tafi watana
biyar aka bamu hutu naxo gida mahaifina ya
sakemin korar kare a karo na biyu nanna bada
sakon' kaya da wayagidan Inna mai danwake a
ajiya miki'
na juya na tafl ina kuka jin wai an tura ki aikatau,
kwanana biyu na koma Lagos.
A yanzu haka yau satina guda da kammala sabis
dina inda na samu saqon tashin hankali, wai Allah
ya yi wa Yasayyadi rasuwa, mutuwar ta gigita ni
ba kadan'ba, don haka na dora wa kaina nauyin
kulawa da iyayensa kasancewar bai taBa haihuwa
ba, sai ga sakon kuma farin ciki ya same ni, wai
mahaifiyata .da qanwata sun bayyana, wallahi
farin cikin da na tsinci kaina bazai misaltu ba”.
Saudat ta cce “Allah sarki yayana ka sha wahala,
kuma ka samu duniya, shi ya sa na ga ka zama
wani dan lukuti”.
Duka suka sa dariya sannan Saudat ta ba shi
labari tun daga ranar da ya tafi har ya zuwa
aurenta.da Dr. Ahmad, Rabi’ u har kuka ya yi
saboda tausayinta, don haka ya ce Dr. ya yi
musu .alfarma gobe su je Dandagoro ya ga
mahaifinsa, kuma ya ga Hamid; Dr. ya amsa da
Allah ya kaimu sannan ya mike ya yi musu sai da
safe.
Momy ta ce “Au dana. 'zata a nan zaka kwana?"
Dr. ya dan yi murmushi tare da fadar, Momy na
riga na yi bukin a Katsina Hotel".
Momy ta ce, “Amma da ka daure ka kwana
Ahmad Abbanka ba ya qasar k0 Bangarensa ba
sai ku sauka ba?”
Ahmad ya ce, “Ayi haquri dai Momy? da safe zan
dawo” " Ta ce, “To Allah ya kai mu” Ya amsa da,
“Amin” Ya yi wa Rabi’u sallama ya fice. . Saudat
ta sabi takalma ta bi shi da‘ zummar suyi sallah;
yana tsaye bakin motarsa har ta Karaso ya bude
mata qofar motar yana fadar, “Muje Saudat,
wallahi na yi bala’in gajiya”. ‘ Saudat ta waro ido,
“Muje fa kace Yallabai? Haba don Allah, ni
gaskiya bazan iya binka ba”. ' Dr. ya zuba mata
ido a raunane yana fadar, “Kin yi min adalci ke
nan Saudat? Kin san dai a ‘ yanzu ina buKatarki
kusa dani, ki tuna fa tsawon lokacin da na dauka
ba mu tare”. ‘ Saudat ta langwabe kai a
shagwabe._ tana , fadar, “Allah YallaBai ni dai
kunya nake ji, kuma yau dai daya don Allah ka
barni in gaisa da dan uwana". . Dr. ya kada kai
tare da fadar, “Shi ke nan Saudat sai da safe”. Ya
juya ya fada motarsa ya ja ta a hankali ya fice,
zuciyar Saudat ta yi matuqar rauni sai dai ba
zata iya yin abin da yake son ba, tajuya ta nufi
cikin gidan ta ja ta zauna suka dasa hira da Yaya
Rabi’ u da " Momy wadda da ta gaji ta mike ta
shige dakinta ‘ Amma su kam yadda suka ga
rana haka suka‘
, ga dare, sai da aka kira sallar asuba sannan shi
ya tafi
~ , masallaci, ita kuma ta nufl Bangarenta in da
ta dauro'
alwala ta yi sallah, kana tahau kan gado ta
kwanta. Sai dai ta kasa runtsawa, tunanin halin
da ta jefa mijin nata a jiya ya tsaya mata a
zuciya, ta lura tamkar fushi ya yi da ita don haka
ta lalubo wayarta ta soma rubuta masa saqo
kamar haka.
‘Tuba nake mai gidana, banji dadin abinda nayi
makab wallahi yanxu haka ina kewarka kamar
yadda kake kewata, ina bukatarka fiye da yadda
kake buqatata, saboda a duk Iokacin da nake
manne dakai sai injini na zama kamar wata
tauraruwa,a cikin taurari
Tana gama rubutawar ta yi murmushi tare da
tura masa saKon ta koma ta kwanta, sai dai k0
minti biyu ba a yi ba sai ga amsa ta shigo, ta yi
dariya don ta san da ma za a rina ta jawo wayar
ta soma
karantawa kamar haka.
‘A kodayaushe ki dinga tunawa ke daban ce a
cikin duniyata, erro lets go am sorry plz
Saudat ta maimaita karanta sakon ya fisau goma
kafin ta tura wayar a cikin jaka ta koma ta
kwanta, ba ta jima ba kuma bacci mai nauyi ya yi
awon gaba da ita, wanda ba ta tashi farkawa ba
sai
sha daya. na safe. Tana mikewa bandaki ta nufa
ta watsa ruwa ta fito, ta sake shiryawa cikin
atamfarta ta
sannan ta flto Sai dai da mamakinta ta samu
Momy da Rabi’ u da Dr a falo suna hira, da alama
sun
dade suna hirar ; Ta durkusa ta gaishe su daya
bayan daya, sannan taja gefe ta zauna tana
fadar, “Da ma kun tashi Momy ba ki tayar dani
ba?” ' ‘ Momy ta ce “A’a na barki ne ki hantse
tashi ki karya maza ku wuce don ku daga can za
ku wuce”. Saudat ta yi saurin dagowa ta kalli Dr.
sai dai k0 inda ta ke bai kalla ba, hakan ya tilasta
mata mikewa ta nufi dinning ta zauna ta karya,
sannan ta dawo cikin falon Momy ta dauko mata
jakar da Rabi’un ya ba ta, ta qara mata da ‘yan
tarkacen tsaraba, sannan ta rako su. * , Saudat ji
take tamkar kada ta tafi, sai dai ba ta ~ da
yadda ta iya, haka ta shiga motar Dr. shi kuma
Rabi’u ya shiga tasa motar sabuwa dal mai suna
206 suka rankaya suka tafi Momy na musu fatan
alkhairi. ~ Sai dai lolkacin 'da suka iso gidan
Saudat mamaki ya kashe' ta, ganin yadda ya
canza ya dawo ginin bulo da bulo aka kawata shi
tamkar gidan wani dan karamin ma’aikacin
gwamnati, kanta bai ida daurewa ba sai da suka
shiga cikin gidan wanda aka canzawa tsari duka
falukan gidan aka hade su cikin guda, aka kaWata
su da sabbin kayan alatu na rayuwa, duk kan
Saudat ya kwance shi kansa Rabi’un
bin gidan yake da kallo, ‘Yarbaba wadda ke zaune
a““ gidan ita ta yi musu iso cikin falon tana ta
faman rawar jiki, sannan ta nufl wata kofa don ta
kira musu Malam Bala.
Saudat ta cika da mamakin ganin ‘Yarbaban a
gidan, lokacin da Malam Bala ya flto ya yi ido
hudu da Rabi’u sai ga shi ya. xube ya fadi kuka
yake wiwi kamar karamin yaro, yana roKon
gafararsu kan Saudat bai ida kwancewa ba sai
data ga ‘Yarbaba ta turo Inna Laure a keken tura
guragu, Saudat ta rude . ta shiga tambayar abin
da ya faru tunda ga Inna Lauren nan dai babu
alamar rashin lafiya a jikinta, . amma daga Inna
Lauren har ‘Yarbaba kuka ya hana
su magana sai Malarn Bala ne ke fada musu.
‘ “Lalurar hawan jini ceta kayar da Inna Laure tun
a lokacin da ya kulle ta a daki ranar da aka dauki
Saudat zuwa gidanta yana zuwa ya bude 'daki ya
ganta a sume hankali ya tashi aka kwashe ta aka
tafi asibiti nan fa aka sanar mana jininta ya yi
matukar hawa kuma qafafunta sun riqe don inba
wani iko daga Allah ba, ba za ta sake taka su ba.
Mijinki yaxo Saudat a lokacin muna asibiti, shi ya
yi ta dawainiya ya ba da kudi aka wuce da ita
asibitin Aminu Kano da ke cikin jihar Kano ya ba
da .makudan kudade, kuma shi ya yi mana
wannan gyaran, amma a asibitin can ma sun ce
iya bincikensu
ba su ga abin da ya rike Kafafuwanta ba, don
haka suka sallame mu, k0 kwana hudu ba mu yi
ba da dawowa gida sai ga ‘Yarbaba cikin wani
mummunan
‘ hali, wai mijinta ya kwashe kayan dakinta ya
siyar, ta yi magana shine ya yi mata dukan tsiya
duk ya raunatata, ya yi mata tsirara ya turota
waje ya ce ya sake ta Saki uku, sai dai makota
ne suka ara mata tufafin da ta iso gida dashi.
Yau satinta guda da dawowa shi yasa ku ka
ganta ta yi kyan gani, amma kwanakin baya idan
ku ka ganta sai kun zubar mata
» da hawaye, ni nasan haqqinku Saudat ba' zai
barmu ba matukar ba ku yafe mana ba, don Allah
Rabi’u ka yafe mana ba don mu ba ba don
halinmu ba”. ‘
Rabi’u ya ce“Ai ni ban' rike ku da komai ba baba,
wallahi na yafe har cikin zuciyata”.
Inna Laure ba ta da ta cewa, sai kuka sai ma
‘Yarbaba ce ta yi Karfin halin bude baki ta nemi
gafararsu. Sun dade a gidan kafinsu yi musu
sallama. za su tafi, Dr. ya yi musu kyautar
makudan kudade, haka shi ma Rabi’u naira dubu
hamsin ya bawa mahaifinsa da zummar idan ya
dawo zai’ ga abin da ya kamata ya yi musu,
Saudat kuwa dumtsowa kawai ta yi ba tare da ta
san k0 nawa ba ne ta bawa mahaifin nata, ta ba
wa Inna Laure sannan ta miKa wa ‘Yarbaba ‘yan
sauran da suka rage.
Ai k0 sun sha godiya da sa albarka, haka suka
bar gidan kowa zuciyarsa cike da alhini, da ma
haka rayuwa ta Kunsa, idan kai ne yau gobe ba
kai bane, idan ba ciwo akwai ajali idan ba ajali
akwai tsufa haka rayuwa take tAfiya a kwana a
tashi mai maida yaro tsoho.
Dr ya dauki matarsa suka koma gidansu suka Ci
gaba da rayuwarsu cikin nagartacciyar soyayya
da kaunar juna, Saudat tana bawa mijinta irin
kulawar data kamata dukda karatunda takezuwa
baihanata ba shi duk wata kulawar da ta san zai
iya bukata dagagare ta ba. A yanzu karatunta ya
yi zurti, don kuwa har ta kammala Basic Illetrate
ta karbi certificate ta kuma ci gaba da karatunta
na wata tara Wanda za ta karanci Social welfare,
don haka ta dage “*dakaratun ta donma canjin
jikindata'samu narashin kwarin jiki wanda likita
ya tabbatar da ta samu shigar cikin wata uku,
wannan albishir din ba qaramin faranta zuciyar
Dr. yayi ba, an inda labarin cikin Saudat har a
cikin ‘yan uwansa, ‘ saboda tsabar rawar qafarsa
a kan haihuwa.
Cikin Saudat yana da wata takwas ta kammala
karatunta na wata tara a lokacin an soma siyar
da
form din jarabawar waec external da kuma jamb
din
ta cike abinta ba su zana jarabawar ba Saudat ta
haihu' wata tara daidai ta sunkuto qaton danta
mai kama da ubansa sak tamkar ya yi kaki ya
tofar
' ‘ Ai k0 a wannan lokacin Saudat ta ga gata da
soyayya don Dr, da iyayensa sun saki bakin
aljihuna sun mata bajinta, kuma sun gwada mata
ita din ta zama tasu ta zama wani Bangare na
jikinsu wanda bai
kankaruwa Ranar suna tazo yaro yaci sunan
mahaifin Dr. wato Mukhtar, suna kiransa da
Khalifa.
A ranar Saudat ta ga dandazon jama’a ta ko’ina‘
daga danginta zuwa dangin mijinta, hatta Hamid
ya kawo matarsa shi ma Rabi’u ya kawo Shukura
wanda Saudat ta fahimci soyayya mai karfi ta
shiga tsakaninsu, duk da Rabi’u ba wani girman
Shukura ya yi ba bai wuce ya bata shekara hudu
ba, sai dai Shukura ta ba ta Kwakkwarar amsa
cewa yanzu auren met ake yayi, abin da ya sa
Saudat dariya matuka, ta kuma tsuke, bakinta
daga nan tunda ta lura abin yi za,ayi. .
Bayan sati biyu da haihuwar Saudat ta tafi ta
zana jarabawa cikin ikon Allah kuma kwalliya ta
biya kudin sabulu don kuwa ta samu credit biyar
a ciki har da Maths da English a jamb dinta kuwa
Allah ya taimake ta ta buga point dari da cas'in
da kyar aka sha dai ke nan, don haka Dr bai bata
lokaci ba ya samar mata gurbin karatu “ jami’ar
Gwagwalada za ta yi difloma dinta a kan social
management, karatunta ta ke haikan Khalifa ya
girma sosai, don kuwa ba inda bai zuwa da
qafafunsa, don
haka yana da shekara daya da wata shidda ta
yaye shi, Wanda da kyar mahaifinsa ya amince. '
Hajiya Zakiya tana zaune a falonta tana karatun
mujalla ta ga Asma ta sauko daga saman ‘ bane
tana sanye da baqar jallabiya fuskar nan ta yi
kozai-kozai alamar ta sha kuka harta gaji,
hannun
na" riqe da hand bag sai makullin meta, k0 inda
Hajiyar tata ta ke ba ta kalla ba ta nufi hanyar
ficewa daga falon Hajiya. Zakiya ta kwalla mata
kira, “Ke Gidan wa za ki haka kamar korarriya?” .
Asma ta waigo tana kallon mahaifiyarta da
idanun da suka ciko da' hawaye, cikin muryar
kuka ta soma fadar, “Gidan mijina zan koma
Umma, na gaji da zaman da nake a gidan nan
marar ma’ana, ni ba mai aure ba, ni ba bazawara
ba, tunda Ahmad yayi alkawarin ba zai sake niba
Umma tursasawar da ake masa ta isa haka,
kuma kema ya isa ki gane mijina yana sona,
Umma na gaji da zamA nan gidana zan koma in
rungumi Kaddarar da Ubangiji ya dora min tun
kafin inyi batan bagatattan”.
Hajiya Zakiya ta zuba wa ‘yar tata ’idanu wadda
ke ta faman sharar kwalla ta girgiza kai kafin‘ ta
ce, “Ke yanzu don zubar da kai Asma mijinki yaqi
zuwa bikonki shine zaki debi kafa ki koma da
Kafarki wato ki nuna masa. bakida aji a kansa ke
nan. ”
Asma ta kada kai cikin kuka ta ce, “K0 daya
Umma, zuwa biko ya wuce wanda iyayensa suka
zo ki kaqi sauraransu, haba Umma ki tuna fa yau
shekarata biyu a gidan nan amma kek0 kadan ba
ki damu ba, Umma to ni na gaji gidana zan koma
in rungumi mijina da abokiyar zamana tun kafin
ta
mallake min miji ita daya ya aiko min da farar
takardar da ke kike buqata, tunda nazo gidan nan
sau daya Ahmad ya taba zuwa bai kuma wara
dawowa ba sai dai ya turo min kudi ta account
dina, haba Umma yaushe kike tunanin zai so inda
nake? Wallahi ni ba zan tsaya jira ba. . .”
Ta juya a sukwane za ta bar falon.
Hajiya Zakiya ta daga murya, “Asma tsaya ki Jl’.
. ~ ‘ Asma tajata tsaya itakuma tacigabada
fadar,“Kiyi haquri kidaina kukannan indai kina son
mijinki na amince ki koma amma ki dan daga
komawar taki k0 gyaran jiki ne in kaiki in kuma
sake miki kayan bangarenki gabadaya yadda
zuciyarki za ta sassauta, ni ba na son ganin kina
damun kanki nima sai inji hankalina ya tashi”.
‘ Asma tagirgiza kai,“Wallahi Umma bazan iya
tsayawaba saidai duk abinda zakimin ki iskeni da
shi daga baya, amma gidana zan koma ni ma ko
na haihu na ga gudan jinina don na gama shan
kwayoyin planning har abada..
Batajira abinda Umman tata zatacebata fice a
guje ta bar falon bata tsaya a ko’ina ba sai cikin
mota ta tayi mata key taja ta bar harabar
gidan. ‘
Saudat na tsaye a harabar gidanta tana manne
da
Khalifa a kafadarta duk da kuwa kibar da yaron
ya
mulka tamkar dan turawa ga shi jajawur da shi
kamar « ya hada iri da zabaya. Rakiya cd sukayi
wa Dr wanda zai tafi kaduna taron .bude wani
sabon kamfaninsa.
Saudat na ta zuba masa shagwabar ya tafi da su
shi kuwa sai dariya yake mata yana zolayarta wai
ba inda zaitafi daita saitayi kiba don Khalifama
yafita nauyi, in ya yi wani zillon har kusa kayar
da ita yake shi ya sa kullum yana hannun mai
rainonsa. ~
Saudat ta ce Allah YallaBai gorinka ya fara isa ta
hakanan, kodon kaganka kai yaddakazama wani
dankareran katone? Allah ka kai kilo dubu ni
Wallahi ma kana kwarata”.
_ Dr. Ahmad ya kece dawata irin dariya jin Sharri
irinna Saudat Ahaka kuma masu gadi sukabude
get motar Asma ta danno cikin gidan dukkansu
sukabi motar da kallo, Dr. ya gane ta don ga
sunanta nan Baro-baro a saman lambar motar
Asma ta faka motar: ta bude ta fito cikin matuqar
sanyin jikinta ta nufo inda ~ suke. Kallo daya
Saudat tayimata taganeta, k0 kadan
'zuciyarta babu alamar fargaba k0 firgici don
kuwa a yanzu tana jinta daidai da kowace kalar
mace duk matsayinta k0 iliminta, kuma a yanzu
ba ta bakin cikin Asma tadawo su zauna
dondama batun yanxu take wa Dr maganar dawo
da Asma yana cewa zai dawo da ita,ba amma sai
ta yi hankali.
Asma na qaraso ta rusuna ta gaishe da Dr wanda
mamaki ya kashe shi, wai yau shi ne Asma ke
gaidawa, lallai ruwa ya daki babban zakara, ta
juya kan ‘ Saudat ta mika mata hannu tana fadar,
“Saudat bani dana inganshi”.saudat tamiqa
matashi,ammayaro da iya shege yaqi zuwa sai
ma ya sa kuka. Dr, yace
shi yana fadar, “Kai Khalifa kuka za ka yi wa
Antyn taka, ba ka kyauta ba”.
Saudat ta juya tana fadar, “Ako ni nayi ciki Aunty
Asma ki tafi da shi tunda Kuka zai miki
Asma ta yi murmushi cike .da jin dadin
karramawar Saudat a gare ta, ta ce“Ai k0 godiya
nake Maman Khalifa, kyautar surbudeden 'da
kamar Khalifa, aiko nayi da kanaji fa”.
Murmushi ya yi tare da fadar “Kema inda vaki sa
duniya a gabanki ba Asma da yanzu kin ajiye uku
irinsu”. Asma ta langwaBar da kai kafin ta ce, “Ka
yi haquri don Allah Ahmad, wallahi duk sharrin
zuciya ne, insha Allahu hakan ba zai Kara faruwa
ba, don Allah ka yafe min”. Dr. Ahmad ya kade
kafada tare da cewa, “Allah yace na yafe miki
Asma, ni dai har abada bazan taba sakinkiba don
ina sonki, ba zan iya rabuwa da ké ba”.
‘ Zuciyar Asma ta cika da farin ciki ta dafa
kafadarsa ta sumbaci Khalifa a kumatu tana
fadar, “Na gode kwarai my dear".
Al’amarin rayuwa ya sauya, Asma da Saudat sun
samu fahintar juna, Asma ta cire duk wani girman
kai ta taya Saudat tattalin maigidan nasu, a
yanzu haka Saudat ta kammala diplomarta ta ci
gaba da digiri cikin kwanciyar hankali, inda ta
Kara haihuwar ‘yarta mace akasa mata sunan
Asma.
Tammat bi hamdu lillahi,

Saikuma mun sake haduwa a wani sabon littafin Thanks all my friends

Pls my fan's prayer for me Allah ya cikamin burinada kuma Allah ya cika muku burikanku na Alkairi Ameeeeeen *BISSALAM*
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels

DOWNLOAD
DOWNLOAD

Please Login or Register in order to submit comment