Join Our WhatsApp Group

Idan ku ka ga kun taba wani wuri ya fitar daku a shafinmu, sai ku danna back kuyo baya, ku sani yanzu muna amfani da tallan Popunder a shafin, so karatu zai muku dan wahala, amma ta hakanne kadai zamu iya cigaba da rike shafinnan. idan har bakwa son talla sai kuje ku yi subscription na shafinnan akan karamin kudi ku runga downloading kawai. SUBSCRIBE


DOWNLOAD

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register
DOWNLOAD

garine da yake cikin Qasar Mali So garin yazamo kamar Biddah a Nigeria sunyi qaurin sunan asiri da maita Wanda ba dukkan garinne suke da wannan hali ba su masu yinma sune kaso mafi qanqanta.
Baffana attajiri ne a garinmu a zahiri bama maita bama tsafi Amma saboda dukiyarsa yasa ake cewa shine shugaban mayun garinmu Baffa Garbu wato babansu Aishatu surukarki yaron babana ne hakan yasa yabashi aurena tunda nazo garin lkcn baa auro uwayen su Aishatu ba matan gidan suka tsangwamin Kuma Allah dabawa mugu dama haka akayita rashe rashe a gabar tun baa yarda har suka amince da gaske ni mayyace hakanan na haifi Aysho ranar dana haifeta Garbu bayanan uwarsa tasa aka daukemu akaje bayan gari aka yasar damu daqyar na iya komawa Mali daga Senegal naci gaba da rainon Aysho Garbu nasona Amma bashida ikon dawo dani domin babana ya fusata hakan yasa Aysho nada shekara goma ya karbeta a gurina sai labari naji ya auradda ita ga dan qanwarsa ya taho da ita Nigeria tun daga wannan Rana nakebi akaini inganta nakasa samun dama dakaina nazo Nigeria neman Ayshatu na ban dace ba a qarshe dai nama hqr domin jikina na bani Ayshatu bata raye don da tana raye inni ban nemeta ba ita zata nemeni, bayan na rasa Ayshatu ne qulafucina da son naganta yasa na komawa Alh Garbu shine har na sake haihuwar Kharimatu, Aminatuh yanzun komai ya wucce bayan ansha wuya kema idan kikayi hqr watarana zai wucce"...........




Juhud is not free read... regular 300 VIP 600 via👉🏼 0255526235 Fauziyya Tasiu Umar GTbank



Then you show ur evidence via WhatsApp 09013718241...



Juhud ba littafin kyauta bane kada ki biya 300 regular VIP 600 kafin ki karanta ta wannan account din 0255526235 Fauziyya Tasiu Umar GTbank ko katin MTN pls ban buqatar vtu hoton katin ko digit number ta WhatsApp number 09013718241.....



*Oum Hairan*
[8/2, 6:36 PM] Oum Hairan: *0026* Jinjina kai Juhud takeyi da jin wannan rikitaccen al'amari tabbas duniya ta cika da mutane marasa tsoron Allah saidai kayi fatan Allah ya dada maka Imani kawai, dubanta Mom tayi tace “Kumbo Hami itace ta riqeni tun bayan rasuwar mahaifiyata banida uwar data fita a duniya Meenah" sosai Meenah taji dadi da ganin dangin surukar tata hakanan taji tanayi musu wata qauna me game jini suma sosai suke nuna mata qauna da kulawa sun jima sosai a sashin nata sunata hirarsu gabadaya su anan suka qarashe bikinsu basajin Hausa sosai hatta Rasheed fullanci yakeyi musu wannan tasa Juhud sajewa dasu.
Kwana uku aka dauka ana bikin qofar falo Rasheed hana Juhud zuwa yayi da sunan biki to itama bata matsa ba ganin Mom ta goya masa baya a gdanta tayi nata bikin saidai tasa ta cire kawai idan yaga garara mutane sunwa bangaren sauqi yasata a corner yayita hadanta aiki ta rasa a wanne bigire zata aje Rasheed irin mazan nan ne masu jarabar nacin masifa shi indai zaki dagansa qafa to bakida matsala dashi idan har kaga Yana ciccin mazu to ya nema anyi masa rowa ne.
Tunda ta fahimci haka itakuma taci alwashin kozata wahala indai ya nemi haqqinsa zata bashi domin shima Babu ta inda ya tauyeta ya tsarenta mutumcinta fiye da yanda ma ya tsare nasa, ranar da biki ya watse aka kai amare gdajensu washegari su Kumbo Hami suka shirya tafiya Juhud har tafi Mom shiga damuwa da tafiyar tasu da anyi mata mgn sai hawaye lkcn da taga sun kusan gama shiryawa sulalewa tayi tabar gidan ta koma sashinta tasa Rasheed a gaba da kuka wai ita bataso su tafi.




Murmushi yayi ya shafa kanta yace “ke har yanzu yarinya ce Meenah to yanzu Kuma kawai saboda bakison su tafi sai su zauna? Kiyi hqr idan kika haihu zan dauki dogon hutu zan kaiki garinsu nima rabona da Mali nafi shekara ashirin" da haka ya samu ta sake har sun shiga mota Kumbo Hami ta fito ta kama hannunta hakanan takejin yarinyar a jininta tace “kici gaba da hqr mijinki Yana sonki Ni shaida ce Meenah idan Allah yasa watan hsihuwarki ya kama da rai da rayuwa zan dawo ni zanyi miki biqi kinji jikata" dariya tayi itama tayi dariya suka tafi suna dagawa juna hannu tana kwance bisa kafadar mijinta.
Taso rakasu airport fir yaqi saboda yasan idan taga tashinsu tsaf zata rikice masa, suna komawa kuwa ya fara hadansu kaya ta dubesa tace “yada hada kaya?" Dubanta yayi yaja numfashi yace “tafiya muma zamuyi" komawa tayi ta kwanta yaci gaba da aikinsa bayan ya gama yazo shima ya kwanta sukaci gaba da soyayyarsu sai biyar na yamma sannan sukabar gidan Muntaz ne yakaisu airport suka daga zuwa Enugu.
Sun sauka da dare suka samu motar taxi takaisu masauki suna zuwa ta kwanta zazzabi ya rufeta Saida ta kwana uku tana kwance yana jinyarta har ta samu ta samu sauqi sukaci gaba da rayuwarsu gwanin dadi.




Aikam tana ganin qauna da soyayya ririta cikin nan yakeyi kamar me, lkc ya rinqa turawa cikin nata Yana qara girma komai yanayi mata wuya shine yake yi mata komai kafin ya fita hatta abinci daya barta ta girka gara yaje ya siyo musu, October watan haihuwarta ya kama tsakiyarsa suka dungumo suka dawo Daura kwanansu uku kuwa da dawowa Kumbo Hami ta dira a Daura sunyi murna sosai sunata farin ciki kwanansu uku ya tafi ranar daya tafi kuwa cikin dare ciwon naqudar na gaske ya tashi.
Wayyoh anci wuya matuqa kwana tayi ta wuni tana naquda har Saida suka yanke shawarar ayi mata aiki sun gama komai sun shiga da ita ubangiji ya kawo mata sauqi cikin taimakon Allah ta sunkuto qaton danta namiji wayyoh farin ciki gurin Mom da Mai Martaba da Ya'isha hatta Muntaz yayi murna da wannan haihuwa kwananta daya a asibitin aka sallameta suka dawo gda Kumbo Hami na kulawa da ita shikam gogan saboda farin ciki har kuka yayi gashi bayada damar dawowa bama ya qasar Yana sauka aka turashi Africa ta kudu.




Ba Shiba ita kanta taso ace yana kusa yaga dansa yasa masa albarka hakanan dai akaci gaba da hidindumun haihuwar wani abin mamaki babu wani daga bangaren Addah Abulle daya leqo barkar wannan haihuwa lamarin ya bawa kowa mamaki itako Meenah batasa a ranta ba balle abin ya dameta domin ba iyakar su kadai bane duk Wanda ke gdan sarautar Babu Wanda ya leqo musu barka tasan saboda itane Kuma tariga tayi forget na komai dazai sanyata damuwa dane dai ta haifi abinta Kuma ubansa da shaqiqan danginsa suna murna da zuwansa duniya.
Duk wani gata da maijego yar gata take samu Meenah ta samu samansa Babu abinda zatacewa surukarta da Mai Martaba sai gdy domin shima ya taka rawar gani gaya a wannan haihuwa, duk abinda uba yakeyi shine ya dauki nauyi donma komai na buqata Rasheed ya tanadi abinsa sai dan abinda baa rasa ba Kuma ya zuba mata kudi masu kauri a account dinta ko zata buqaci wani abu.
Ranar kwanaki uku ne suna zaune da Mom da Ya'isha da Aunty Hamida a falo Juhud na feeding din babynta ya kafeta da ido qurr yana qare mata kallo suna dariya Kumbo Hami tana cewa “wannan ja'irin yaron quiya zaiyi tun yanzun Yana qarewa uwarshi kallo da shegen wayonsa aka haifesa" itadai saidai tayi dariya kawai.
Sallama akayi a bakin qofar suka daga kai suka kalli me shigowar Hajiya Bilki ce ta shigo ita da Dada Hanne babbar yayarsu Mai Martaba Mom ta taresu fuska a washe tana musu sannu da zuwa ta basu gurin zama Dada Hanne ta tabe baki tace “ashe an haihu?" Da yanayin rashin jin dadin tambayar Mom tace “eh wlh yau kwana uku" tabe baki sukayi Dada Hanne tace “eh tun ranar aka fadamin shine dai yau na daure nace Bari nazo Ke Bilki bani ruwan qanzon nan" dukkansu kallonta sukayi ta miqa hannu ta dauki yaron a cinyar Juhud tana harararta kawai ta bude bakin yaron ta dauki ruwan zata dura masa Meenah ta miqe da sauri tayi kukan kura ta warce danta Dada Hanne ta kuwa dauketa da mari tace “kutmar ubancen ke dan uwarki ni zaki qwacewa yaro a hannu koda yake ba banza ba dama anfada ance indai da abar a jikinki bazaki Bari a karyawa danki ba gashi kuwa munga alama to wlh baki Isa ki bata Mana zuri'a ba dolene abawa yaron nan ruwan qanzon nan Kuma daga yau an daina bashi wannan baqin nonon na tsiya a nema masa Madara ko abawa Fadila ta shayar dashi shidai Rasheedun da kwadayin farar fata da kyauwun banza yakaishi ya dauko to ta qare masa akansa...."




Tana qoqarin fusgar jaririn Juhud ta qara qanqame abinta ta saki wani kuka me sauti tace “wlh bazaku kashemin daba duk abinda zakuyi saidai kuyi....." Mom ce ta karbe da cewa “Dada Ina ganin mutumcinki ki fita daga lamarin halwata kafin na hada dake na tsince muku zarafi yaran nan daga ita har mijinta basu damu da lamarin kowa ba ku kun damu dasu to waima Ina ruwanku da abinda ta Haifa ne ince dai nasu ne su suka Samar da abinsu ke yanzu bakiji kunya ba gotai gotai dake kizo kina yada girma gaban jikarki"
Hayayyaqo mata Dada Hanne tayi tana cewa eh dama Mana dole kice haka Aisha ai kinci kin qoshi mun kaiki matsayin da baki takaba a baya to dake da Mahfuz da Rasheedu da duk wani Wanda yake yaruwa a gidannan a qarqashin darajata yake balle wannan yar galaulawar da kuka kwaso kuka manna Mana saboda haka wlh muddin Ina raye Kuma Rasheedu daga tsatson sarki Waziri ya fito to dole ne a bani dannan mu karya masa maita takanas nayi tattaki har Kankia na karbo wannan maganin don tseratar da ahllinmu daga gurbacewa irin maita ai bala'i ne bazamu sake a lalata Mana halwa da son zuciya ba" Hajiya Bilki ce ta cafe da cewa “yo Dada Hanne da kike wannan mgnr jinki zasuyi ne ko zaa barsu su gane me kike nufi da gatan da kikeson yi musu ne ai anriga an lashe kurwas basuda katabus hatta Mai Martaban bashi da fuss indai akan wannan tsintacciyar magen ala qaqai dince kina gani fah saboda a samu a ceto yaron nan nabawa Alh Aminu shawarar yafadawa Mai Martaba tunda yaqi Hidaya ga Dijenan babu makusa in batafi ba bazaa fita ba ya aurawa Rasheed Amma yaron nan ya debemin albarka ta sama data qasa har Yana cewa indai halwata ce to har abada bayaso......"




Fashewa tayi da kukan munafurci nandanan Mom ta zuciya Mom akwai hqr da kawaici Amma tanada mugun zafi idan aka kaita qarshe ta miqe tace “Hanne ku fice daga bangaren nan tunda baa ginashi da sunan dayanku ba da sunan Dana Abdulrasheed aka ginashi Kuma iyalinsa ne a ciki munji ko Meenah zata rinqa sakatarmu da daidai munasonta a haka tunda danmu yanaso munafiki ya ciji yatsa maqi gani ya rintse ido insha Allahu Meenah saita haifi sarkin gobe a gdannan muga shegen daya Isa ya Hana Allah ikonsa magani ne bamaso mun gode bazaa bawa yaron nan ba indai ta jikin dana ya fita muga Wanda ya isa ya gwada ikonsa a gidannan"
Tana fadin haka ta karbe yaron a hannun Meenah data hada kanta da center table taketa kuka wannan cin mutumci da take jawa uwar mijinta yayi yawa itakam da tana da dama data fita daga cikinsu ko da samu salama to tunanin halin da Rasheed zai shiga shine yake takanta burki ya dauki amanar kansa da komansa yabata sun jibanci lamarinta sun yarda da kowanne irin cin mutumci indai akanta ne idan tace zata gudu tabbas batayi musu adalci ba domin ta kwaranye musu baya magautansu zasu samu damar yi musu dariya.



Kumbo Hami ce ta matsa jikinta ta riqe kafadunta tana jinjina girman halin da yarinyar take a ciki bata taba tunanin abun yayi qamarin haka ba dole yarinyar ta kasa sukuni cikin wannan ahli lamarin rashin kararsu azumin ne basa da mutumci ko kadan sosai kalamin Dada Hanne sun girgiza Kumbo Hami ta dago Juhud jikinta ta shige jikinta cikin kuka tace “don....don Allah Kumbo ki taimakeni kice da Rasheed ya hqr da zama dani tunda danginsa basa qaunata wlh zuciyata zata buga idan naci gaba da zama a cikinsu ya sukeso nayi ne da wanne zanji? Yaushe zanyi farin cikine yaushe zan samu salamar rayuwa nima kamar kowa, Allah inason mijina Amma lkc yayi da zan barsa na nemawa kaina yanci ina zangansu??"
Bubbuga bayanta Kumbo Hami takeyi cikin jimami tace “ki daina tuhumar ubangiji akan abinda bai kawo qarshensa ba Meenah meye laifin mijinki ne da zaki zabi jefashi cikin garari yanasonki baitaba kallonki da abinda wadannan debabbun ke kallonki dashi ba surukarki ta karbeki ta yarda da komai daya jibanceki kada ki bata rawarki da tsalle koda bazakiyi hqr domin Allah ba kiyi don wadannan ahlin mijinki mahaifiyarsa yan'uwansa da suka fito daki daya nasan Allah zai baki ladan saka Alkhairi da Alkhairi kada ki zama butulu rayuwar butulu bata qarshe me kyau kinji?"
Kwantar dakai tayi cikin yanayi na nadamar kalami tace “yanzu shikenan ni tawa qaddarar kenan Kumbo haka zanta rayuwa cikin tsangwama a cikin ahlin da ba nawa ba haka zan qare rayuwata ni a qunci halwata a qunci?" Murmushi tayi tace “kada ki cire tsammani daga rahamar ubangiji insha Allahu komai zaizo qarshe" da hikima irin tasu ta dattijan da sukaga jiya sukaga yau suke sa ran ganin gobe ta kwantar mata da hankali ta kwanta kanta na ciwo Aunty Hamida ta dauko Sarki junior ta kawo musu Kumbo Hami ta karbeshi ta zubawa yaron ido dan kyakkyawa dashi kamanninsa na ubansa hasken fatarsa na uwarsa.




Miqa mata shi tayi tasa masa nono ya kama Yana zuqa tana cije lebe zafi takeji sosai idan yanashan nonon hakanan take daurewa take shayar dashi bata jima da kwanciya ba bacci barawo ya dauketa cikin baccin taji ana shafa fuskarta tayi miqa tare da tallafe kan yaron ta zare masa nonon a bakinsa ta daga kai ta sauke idanunta da suka kumbura sukayi luhu² a kansa shima ita yake kallo yakai hannu ya dauki Mahfuz ya zubawa yaron ido yanajin qaunarsa data mahaifiyarsa na nunkuwa a ransa ya sake shafa fuskarta yace.
Kin biya Aminatuh Allah yayi miki albarka ya rayani tare dake" ajiyar zuciya taja me qarfi ya sake zubanta ido yace “naji labarin komai daya faru don Allah ki taimakeni kiyi hqr ki dainasa damuwar wadannan mutanen a ranki kinji" lumshe idonta tayi tare da lasar lips dinta daya bushe yace “talk me Mana" kallonsa tayi idanunta na tsiyayar hawaye tace “idan ya kasance nice matsalarka a duniyar nan Abdulrasheed meye yasa bazaka datseni cikin tarihinka ba ko ka samu record me kyau?" Sakin baki yayi yana kallonta ta zame daga gadon tace “don girman Allah mu hqr da zaman nan tunda mun kasa samun farin ciki a cikinsa Abdulrasheed bantaba zama silar farin cikinka ba saidai na akasinsa tunda ka janyoni ka hadani da rayuwarka taka ta gurbata ta ahlinka ta gurbace inda kai kadai ne da sauqi tunda kaine kaji ka gani Amma meye yasa saboda son ranmu da son zuciyarmu mu zamo silar yankewar farin cikin wasu Baffa'am Munjefa Mom cikin tsaka me wuya mun jefa Mai Martaba mun jefa kanmu mun jefa duk wasu masoyanmu. Please don Allah don girman Allah mu hqr kabarni na rayu da yanci kaima ka rayu da salama kaji"......




Juhud is not free read... regular 300 VIP 600 via👉🏼 0255526235 Fauziyya Tasiu Umar GTbank



Then you show ur evidence via WhatsApp 09013718241...



Juhud ba littafin kyauta bane kada ki biya 300 regular VIP 600 kafin ki karanta ta wannan account din 0255526235 Fauziyya Tasiu Umar GTbank ko katin MTN pls ban buqatar vtu hoton katin ko digit number ta WhatsApp number 09013718241.....



*Oum Hairan*
[8/3, 9:13 PM] Oum Hairan: *0027* Tunda Juhud ta durqushe gabansa ta riqe qafafunsa tana kuka tanayi masa magiyar jikinsa ke rawa ya kafeta da manyan lumsassun idanunsa ya kasa furta mata ko kalma daya da zata zama salama ga ruhinta saboda gani yake duk furucin da zauyi yayi kadan wajen goge mata radadin ciwon dake cin zuciyarta wanda harya sanyata zabar rabuwa dashi fiye da rayuwa dashi. Kwantar da kanta tayi a cinyarsa ta dora hannunta a fuskar Sarki junior ta sake rushewa da kuka tace “idan ya kasance kalaminka sun qare ni Kuma Ina kakeso nawa suje Baffa'am kaine duniyata kaima kana neman zamewa daga gareni tabbas rayuwata babu kai akwai rudani a cikinta Amma zan zabi na rayu da quncin rashinka fiye da rayuwa da haqqin wasu nikam banajin dadin yanda zamana dakai ya zamo silar rarrabuwar kawunan ahlinka Baffa'am meyesa Allah bai qadarta zamowata Alkhairi gareku ba?"
Lumshe idonsa yayi ya bude ya saukesu akanta ya miqe hannunsa dauke da dannasu yana sake shigar dashi jikinsa yace “abune da bazai taba yuwuwa ba kike furtawa Meenah shiyasa nake ganin asarar bata lkcna wajen baki amsa" yana fadin haka ya fice daga dakin ya nufi nasa ya zauna a gefen gado ya yaye fuskar Mahfuz yayi masa addu'ar da baisamu yayi masa ba ya kwantar dashi tare da miqewa yasawa dakin key ya cire kayansa ya shiga bathroom ya watsa ruwa ya dawo yana shiryawa yana kallon yanda yaron keta wutsil²n dinsa na jarirai yayi murmushi a fili yace “girman rabo Ina Mai Martaba da yakeson yakaimin wannan Soldier da zai fita daga jikina ya shiga na Meenah ta qinqishemin shi? Da a Ina yakeso na saka wannan kyakkyawan qwan da bai cancanci qinqisar kowa ba saita rayuwata?" Bayan ya gama shiryawa yayi sallar Isha da baisamu yayi ba yayi shafa'i da wuturi ya haye gadon ya kwanta tare da daukan yaron ya dora a qirjinsa yanajin qaunar gudar tsokar tasa har cikin bargonsa, zubawa p.o.p idanu yayi yana nazarin kalaman Meenah tabbas lamarin yau me girma ne Meenah da bakinta ta furta masa gara rabuwa dashi akan rayuwa dashi wannan abu yanayi masa ciwo duk wata matsala ta gidansa bata zuwan musu a kankin kansu saida wasu su qirqireta idan yace zai dauki mataki a hanasa wannan wacce irin rayuwa ce ne?"




Miqewa yayi ya dauki Mahfuz daya farka a bacci yake neman uwarsa ya fita ya nufi dakinta ya bude ya shiga ga mamakinsa ya isketa zaune can qarshen gadon ta zuba uban tagumi ya zubanta ido tausayinta da qaunarsa na qara nunkuwa a zuciyarsa ya haura gadon ya kwantar da Mahfuz ya sanya hannunsa ya janye mata tagumin ya janyota jikinsa ya rungumeta yana sunsunar sumarta yanajin wata natsuwa na kwararo masa yace “idan na rasa gatan kowa a duniya baikamata na rasa naki ba Meenah bai kamata na zamo mara galihun nunawa duniya a gurinki ba bayan kin kasance mace daya tal dake mulkin zuciyata please na roqeki ki daina jin a ranki akwai abinda zai rabamu qaddarar mutum Babu me tayashi dakonta ni kece qaddarata nima nine qaddararki bazan hanaki kuka ba akan abubuwan da suke faruwa Amma dai ki rinqaji a ranki iyakar rintsin rayuwar duniya ni nakine ke kadai Babu wani tsanani da zaisa na rabu dake saidai qaddarar mutuwa idan ta gifta saboda haka banson sakejin wadannan kalaman naki don Allah kinji?" Zamewa tayi a jikinsa ta miqa hannu ta dauki Mahfuz tayi Bismillah ta Sanya masa nonon ya kama yanasha shikuma yana aikin kallonsu.




Kwanciya tayi badon tayi bacci ba saidon tabawa zuciyarta hutu shima kwanciya yayi a bayanta ya maqaleta da haka sukayi bacci washegari da wuri ya fice daga gdan duk cika ta gidan sarautar idan ka shiga barayin Rasheed bazaka taba cewa sabuwar haihuwa akayi ba saboda yanda gdan yake a yashe daga ita sai Kumbo Hami suketa harkokinsu Rasheed bai dawo ba sai bayan Isha lkcn har sun kwanta ya shigo ya kirata ta miqe ta nufi dakin nasa yana safa da marwa ta samu guri ta zauna shima ya zauna a gabanta ya dubeta sosai yace “nasa anzo an kama Hajiya Bilki da Dada Hanne....." Dafe qirji tayi da sauri tace “na shiga uku Baffa'am me sukayi maka?" Share zufa yayi ya miqe yace “saboda a koya musu hankali su fita daga harkata da iyalina" yana mgnr yana hada kayansa ta miqe ta Isa gabansa jikinta na rawa ta durqushe tace “wlh wannan abin baikai ka dauki wannan matakin ba Abban Sarki ana barin halal ko don kunya please kada kayimin haka wani bala'in zaka qara jefani a ciki kasa a sakosu wlh ni na yafe musu...."
Rufe mata baki yayi yace “ke zaki iya yafewa saboda bakisan ciwon kanki ba nikam ban yafe ba Yana fadin haka ya shige bathroom yabarta sake da baki wannan mutumin kwai dan neman jarfa anason kashe wata yana neman zunguro sama da kara




Tananan zaune ya fito daga wankan Yana tsane ruwa ta sake dubansa zatayi mgn ya nuna mata hanya yace “jeki ma hadu da safe inason zanyi yan nazarce nazarce" miqewa tayi jikinta a mace ta koma dakinta ta ishe Kumbo Hami tana sallar Isha ta zauna bayan ta idar ne take tambayarta meye yake faruwa ta kuwa zayyane mata komai tayi shiru na dan lkc sanna ta dago tace “banji dadin kaisu qara da yayi ba shima hakan qarin wata fitinar ce daya qyalesu watarana sai lbr"
Miqewa tayi ta Sanya Sarki junior a gadonsa tana cewa “nima abinda naso ya fahimta kenan yaqi bani hadin kai koroni ma yayi Kuma tunda yayi niyya Babu me hanashi" da wannan tayi addu'a ta kwanta sukayi baccinsu itadai da zullimi ta kwana aikam abinda take gudun ne ya faru da safe Yana fita Hidaya da Khadija sukayiwa gdan tsinke suka rinqa zaginta sunacin mutumcinta Meenah babu baki sai hawaye kawai da takeyi suna tsaka da wannan tujarar ne Kareem yazo musu barka don shi sai ranar ma yakejin lbrn haihuwar gurin Fadila aikuwa ranar Khadija da Hidaya sunji a jikinsu domin dukan mutuwa yayi musu kamar shine sojan daqyar Mai Martaba ya qwacesu barkar da baiyi ba kenan ya fice daga gdan rashin mutuncin gdan ya fara girmewa tunaninsa ace Babu Wanda ya isa ya fada aji anbi an tsangwami yarinya akan abinda bashida tushe balle makama aikam ranar hatta Addah Abulle Saida taji kunyar irin rashin albarkar da Kareem yazo ya zazzage mata a gdan akan rashin zuwa taga Dan da aka haifawa Rasheed yan uwansa kuwa gda gda ya rinqa binsu yana ci musu mutumci Yana fada musu ai ba Meenah suke qi ba Rasheed suke qi tunda shine ya dauko Meenah Kuma yakeson kayarsa sannan ba Meenah kadai ta haifi Mahfuz ba Rasheed shine silar zuwansa duniya saboda haka shine basaso"




Basu wani dauki mgnr da muhimmaci ba ba Kuma su risuna ba sukaci gaba da dabdalarsu rikici yaqi qarewa cikin wannan family har ranar suna akayi sunan babu wani armashi kamar abin arziqi dangi suka hadu ranar Meenah Saida ta gwammace ita dama mutuwa tayi da wannan baqin cikin data riska wannan Rana a qarshe baa gama sunan da ita lfy ba sai a gadon asibiti ta qarashe sunan jininta yayi mugun hawa hawan da Rasheed bai taba tsammani ba ya shiga tashin hankali matuqa da yanayin da yaga matar tasa a ciki, da dare aka sallamesu suka dawo gda kanta na ciwo sosai da Rasheed da Mom da Kumbo Hami sunata rarrashinta da kalami na kwantar da hankali bacci ya dauketa washegari badon yaso ba ya shirya yabar garin ya koma wajen aiki yabarsu cike da kewar juna................




_Kuyi hqr da wannan_





Juhud is not free read... regular 300 VIP 600 via👉🏼 0255526235 Fauziyya Tasiu Umar GTbank



Then you show ur evidence via WhatsApp 09013718241...



Juhud ba littafin kyauta bane kada ki biya 300 regular VIP 600 kafin ki karanta ta wannan account din 0255526235 Fauziyya Tasiu Umar GTbank ko katin MTN pls ban buqatar vtu hoton katin ko digit number ta WhatsApp number 09013718241.....



*Oum Hairan*
[8/4, 8:56 PM] Oum Hairan: *0028* Kwananta sittin da haihuwa Kumbo Hami ta koma Mali inda ita Kuma taci gaba da rainon danta cikin kulawa da tattali a hankali lkc yaketa tafiya qaunarta da Rasheed tanata qara gaba inda aiki ya riqeshi kusan watanni biyar sannan ya waiwayosu ranar anyi qara'in rayuwa kamar bazaakai gobe ba yayi musu sati biyu ya shirya domin
DOWNLOAD
DOWNLOAD

Please Login or Register in order to submit comment