Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

daga dakin ya koma waje ya rafsa tagumi jikinsa sai tsuma yakeyi Yana tausayin kansa Amma yafi tausayin Meenah saboda tafisa shiga damuwa ya jima zaune a gurin kafin likitan ya iso suka shiga tare likitan ya dubata ya sake bata kulawa ya fice daga dakin ya dubi Juhud datake zaune take shan tea yace mata “sannu" bata ko dubesa ba ya nemi guri ya zauna Suna taba hira lkc zuwa lkc suna taba hira da Ya'isha Mom tana Sanya musu baki itako ko kallo bai isheta ba hasali ma tunda ya zauna takejin wani qunci aranta ji takeyi kamar ta fice daga dakin bata son ganinsa.
Kwanciya tayi taci gaba da saqa da warwara a ranta sai yamma Ya'isha tace zata tafi mijinta yazo daukanta sukayi sallama suka tafi Mom ta tafi rakasu ya taso ya matso jikin gadon yace “duk da nasan ni mai laifine a gurinki Meenah Allah ya sani inasonki tun kafin yanzu Amma bantaba yimiki fatan ki dawo gareni ba Allah shine ya tsara hakan saboda haka na karba Kuma nayi masa gdy kema inaso ki karba kiyi masa gdy......" Miqewa tayi zaune zuciyarta na tafasa tace “akanme zanyi gdy akan abinda ba zabina ba bankuma nema ba? Why da zakace dole saina karbeka? Kareem da zaka manta dani ka fice cikin rayuwata da mun taimaki kanmu wlh banyi farin ciki da samunka matsayin miji ba kada kaji a ranka na karbeka bazan taba karbarka ba Rasheed shine zabina shine rayuwata......"




Hannunsa ya dora bakinta yace “stop Meenah ya isheki don Allah kada ki fasamin zuciya da kalamanki kiji a ranki wannan bayin kaina bane yin Allah ne..... Wayarsa ce tayi ring ya zaro a aljihunsa number Zahrah ce yayi kamar ya kashe saidai zuciyarsa ta raya masa ya daga qila wani abune Important yasata kiransa danna wayar yayi ya Kara a kunnensa ta cikin wayar Meenah take jiyo gunjin kukanta tana cewa “Allah ya isa tsakanina dakai Kareem ka cutar dani kaine wlh kaine sila tunda kaine ka rakitomin ita cikin rayuwata harta cutar dani, na dauki ciki watanni tara na Haifa matarka ta kashemin yata wlh bazan yarda ba kaji na rantse maka wayyoh Allah na Zainab ta mutu Aminah ta lashemin yata......"
Qit ya kashe wayar idanunsa ya ciko da hawaye ya dubi Juhud data zubawa TV idanu a zahirinta ba TV take kallo ba kalaman na Zahrah ne sukeyi mata yawo a kwanya yace “kinji sauqi likita yace zaki iya komawa gida zanyiwa Mom mgn ta shirya mu tafi Zainab ce ta rasu...."




Bata ko kallesa ba taci gaba da wasa da yatsunta yaja numfashi ya fice a dakin suka hade da Mom a reception ya tsaya Yana dubanta da jajayen idanunsa da damuwa biyu tasa suka kada tace “yanzu ake fadamin Zainab ta rasu ya kamata kazo ka tafi kaima tunda jikin nata da sauqi" girgiza kai yayi yace “ban yarda da hankalin Meenah ba Mom zata iyayin komai Ina tsoron kada na tafi tayi tunanin guduwa tabarni wlh mutuwa zanyi a wannan karon Mom ke shaida ce na wahala a karon farko dana rasata don Allah ki tausheta ta soni koda kwatan Wanda nakeyi matane ni basai yakai rabi ba inasonta a haka"




Murmushi Mom tayi me dauke da hawaye ta dafa kansa tace “Abdulkareem to Banda abinka Meenah yanzu ai taka ce kasan dai ba cikakkiyar lfy gareka ba don Allah ka rage damuwa da duk abinda zatayi zai hucce kasan kaima dole zaa fuskanci wannan qalubalen tunda ba ita taga damar auren nan ba Ni kaina Meenah fushi takeyi dani ban damuwa domin nasan gata Mai Martaba yayi mata kaidin dama kaine ka dace da ita Hukuncin Allah ne yabawa Rasheed da Kuma rabon Sarki junior Kuma ma ai tanasonka tun a baya kawai yanayin da take cikine yasa zakaga kamar batasonka"
Murmushi yayi yace “hakane Mom na gde am Dr yace zamu iya tafiya gda nikam zanfi samun nutsuwa tana tare dani" batason jayayya dashi shiyasa ta aminta su tafi din ta shiga dakin ta fara hada musu kayansu Meenah na kallonta harta gama ta dubeta tace “mu tafi mijinki ya matsa saidai mu tafi gabadaya" daqyar Mom tasha kanta ta miqe suka tafi baya ta shiga yana kallonta yayi murmushi sai Mom ce ta shiga gaba suka nufi Katsina da suka isa Daura ta samu ta fita a mota tayi wuf ta shige dakin da take ta fada gado ta rushe da sabon kuka tana tuna wai yau ita ce matar Kareem bata Rasheed ba meyesa qaddararta kullum ita baibai ce a fili tace “lkc yayi da zan nemawa kaina gata dole na nemi su Baffa Ribado ko zasu kasheni su fitomin da dangin mahaifiyata"




Qwanqwasa qofar taji anayi ta miqe ta bude qofar ganin Kareem ne tayi saurin mayarwa ta datse yaja baya da sauri tare da cije lebe ya juya a kasalce ya fice daga gdan ya nufi gdansa babu kowa kamar yanda ya tsammata yayi murmushi ya nufi gdansu Zahrah acan ya tarar da yan karbar gaisuwar bai wani zauna ya dade ba ya nufi gidansa ya kwanta a gado Yana saqawa da warwarewa akwai aiki a gabansa.
Meenah batashi takeyi ba baya a lissafinta ga Addah Abulle ta takura masa da Kira har takai baya daga wayarta saboda yariga yasan mgnrta bata wucce akan qiyayyar aurensa da Meenah tana qara tuna masa tun tana budurwa an hanashi sai yanzu data zama saura ragowa sannan ga rashin asali kalma daya yake fada mata Babu komai Addah inasonta a haka ba meenah ce ta qini ba a farko fin qarfinta akayi saboda hska nima bazan qita ba" idan ya Fadi haka Adda ji takeyi kamar ta kasheshi shima gashi Mai Martaba yaqi sauraronta balle yaji kokenta hasali ma fushi yakeyi da ita wannan tasa ta zare hannunta daga lamarin Kareem din ta zubansa ido tare da cin alwashin indai itace ta haifeshi to Meenah ta gama kwanciyar hankali a duniyarta saisun takurata sun azabtar da ita ita da yan'uwanta babban abinda yake daganta hankali Zahrah yar wanta ce ta nemawa Kareem aurenta don huce haushi yanzun Kuma ya samu abinda ransa yakeso bayama ta ita tunkan tafiyar tayi nisa.




Wadannan dalilan suka hadu sukayiwa zuciyar Kareem yawa abinka da mara isasshiyar lfy nandanan zazzabi ya rufeshi shi kadai a gda yayita murqususun ciwo yana dafe qirjinsa wayarsa ma ya kasa dauka ya kira wani, baa Ankara ba Saida ya kwana shidda yana fama da ciwo shi kadai a gda sannan ubangiji ya kawo masa sassauci a galabaice ya lalubi wayarsa ya Kira layin Zahrah bugu yafi biyar tana gani taqi dagawa ya hqr ya Kira na Meenah itanma yayi mata misscall yafi goma tana kallon wayar taqi ta daga qarshe ma ta kasheta gabadaya ya jinjina kai cikin azabar ciwo ya Kira layin Mom dan yasan idan ya Kira na Addah ma itanma kamar yanda matansa Basu saurareshi ba itama ba saurararsa zatayi ba.
Bugu daya Mom ta daga tace “dan halak kaqi ambato Ina ka shigene inata nemanka bana samunka....." Nishin da taji yanayi ya fadar mata da gaba tace “ya salam kardai bakada lfy ciwon ne ya tashi Kareem....." Cikin rawar murya yace “Mom....ki....ki taimaka ki kawomin Aminatuh don Allah kada ta zamo silar ajalina sonta zai kasheni...."
A gigice tace “o.... Ok ganinan don Allah kada ka mutu Kareem mukam mun shiga uku da wannan masifa" kashe wayar tayi ta zari mayafinta ta fice a kidime ta nufi dakin Meenah tana zaune tana koyawa Sarki Homework ta dago ta dubi Mom tace “Lfy Mom?" Sharce gumi tayi tace ”taso ki rakani unguwa"




Babu musu ta miqe ta dauki mayafin doguwar rigarta ta sanya ta kama hannun Sarki suka fito ita kejan motar Mom na fada mata inda zasu tana fahimtar gidan Kareem suka nufa hasken fuskarta ya dauke ta hade rai donma Mom tafi qarfin musu ne a gurinta shiyasa tayi shiru har suka isa gdan suka Mai gadi ya bude musu sukayi parking Mom ta fito itakam gyara zamanta tayi Mom ta dakanta tsawa tace “bafa nason sakarci Meenah ki fito mu shiga nace"
Tana qunquni ta fito suka shiga cikin tun daga falon taji gabanta na faduwa komai a hargitse tabi falon da kallo taja tsaki Mom ta haura saman tabi bayanta tana kallon tsarin gdan bude wata qofa Mom ta Kuma yi qofofi ne guda biyu suna kallon juna ga mamakinta nan dinma falo ne sai wasu qofofin biyu tsayawa Mom tayi tana tunanin wacce zata bude Sarki yace “Mom ga dakin Uncle nan" Yana mgnr Yana murda qofar suka shiga a tare itakam guri ta samu ta zauna a falon tana hura hanci.
Yanayin da Mom ta isheshi yayi mugun tada mata da hankali ta saki wani kuka tace “innanillahi wa Inna ilaihir raji'un Abdulkareem meye hakan kashe kanka zakayi a gda kai kadai" gaban Meenah ya sake faduwa lkcn da Mom ta qwala mata Kira ta miqe a razane ta shiga dakin tare da zaro ido Yana kwance a qasa magashiyan cikin wani mawuyacin yanayi ya bude idonsa ya saukesu akan Juhud tare da sauke ajiyar zuciya ya fara yunqurin miqewa Yana cewa “Am.... Ami...na...tuh zo... matso gareni please...." Janyewa tayi tayi baya idanunta na kansa Mom ta tura ta fada jikinsa ya lumshe idonsa tare da sanya hannunsa ya zagayeta yaja wata ajiyar zuciya me qarfi tana qoqarin qwacewa ya bude bakinsa yace “na...na gode Mom ke kadai kike tausayina a duniya Mom Meenah bata sona...." Juyawa Mom tayi ta fice saboda yanda taga Yana qara matse matarsa a jikinsa abin yabata tausayi da kunya ta lura da Rasheed da Kareem tafiyarsu daya Basu da kunya akan abinda sukeso.......




Juhud is not free read... regular 300 VIP 600 via👉🏼 0255526235 Fauziyya Tasiu Umar GTbank



Then you show ur evidence via WhatsApp 09013718241...



Juhud ba littafin kyauta bane kada ki biya 300 regular VIP 600 kafin ki karanta ta wannan account din 0255526235 Fauziyya Tasiu Umar GTbank ko katin MTN pls ban buqatar vtu hoton katin ko digit number ta WhatsApp number 09013718241.....



*Oum Hairan*

[8/7, 7:18 PM] Oum Hairan: *0031* Da qyar ta samu ta janye daga jikinsa idanunsa suna lumshe hawaye yake zubarwa ya riqe hannunta yace “Nayi tunanin kedin me yarda da qaddara ce da hukuncin ubangiji Meenah ashe ba haka bane Meenah ko bazakiji tausayina ki daina azabtar da ruhina don na cancanta ba ya kamata kiji qaina don qaunar da nakeyi miki inasonki ne Meenah da jinina da rayuwata" Yana mgnr numfashinsa ba kakkatsewa hakanan taji bazata iya jure cigaba da kallonsa a wannan yanayin ba ta miqe zata fice ya Kira sunanta ta tsaya ya dauki wayarsa ya miqa mata yace “idan tafiya zakiyi ki kiramin Amrah ko Urwat ko Muntaz wani cikinsu yazo ya zauna dani Ina cikin yanayin da komai zai iya faruwa dani"
Harararsa tayi ta fice a ranta tana cewa “badai ni ka zaba ba wlh saidai ka mutu yanda uwarka da yan'uwanka ke qina haka nima nakeji game daku ban shirya zama da wannan ahlin ba abarni na rayu da zabina koda baya tare dani nasan Ina kwance a zuciyarsa" sauka tayi qasan ta tarar da Mom da Dr Razaq suka dubeta tare sukace “ya me jikin" a gajarce tace “yana ciki" ta juya ta fice ta shige mota shiru dogon lkc ya wucce basu fito ba can taga mota ta shigo Mai Martaba ne da Arman suka shiga suka daukoshi suka fito dashi. A mota suka sanyashi suka fice Mom ta shiga mota Juhud taja suka fita sosai ta qular da Mom da halin ko in kula din data nuna akan mijin nata bata taba tunanin zuciyarta tayi soyewar haka ba.




Saida sukaje gda ta juya zata shiga dakinta Momy tace “bantaba tunanin hakan daga gareki ba Meenah mijinki zabinki a baya banga zafin da rayuwa tayi tsakaninki dashi ba da zaki zabi azabtar dashi Meenah koda a yanzu baki zabeshi ba cancanta aka duba aka zabanki shi kada kiyi wasa da damarki inaji a jikina Kareem zai sharenki hawaye don Allah Meenah indai da gaske kin daukeni matsayin uwa a gareki kiyima mijinki biyayya ki rintse idonki ki ninka hqrnki akan wanda kikayi a baya. Tabbas akwai qalubale cikin zamanku to Amma qaddara ta riga fata haka Allah ya shirya mana addu'a Rasheed yake buqata kawai daga gareki"
Sunkuyar da kanta tayi tana sauraron Mom harta gama fadar abinda zata fada
Ta juya ta fita ta kwanta rigingine zuciyarta na hasaso mata abubuwa da dama da suka faru a baya lkc zuwa lkc tana dauke hawaye a fuskarta itadai batasan sanda bacci ya dauketa ba wajen biyun dare ta farka tayi alwala ta tayar da nafila tana roqon Allah ya shiga lamuran Rasheed a duk inda yake ya tsareshi da tsarewarsa ya bayyana shi cikin aminci da salama bayan ta idar ta zauna tana lazumi taji wayarta tana ring takai hannu ta dauka lambar Kareem ce taja tsaki ta katse wayar ya Kuma Kira ta dauka zata kashe maganganun Mom suka rinqa dawo mata tayi qarfin halin dorawa a kunnenta




Ajiyar zuciya ya sauke lkcn da tayi masa sallama ya Amsa cikin wata irin murya me tsananin sanyi shiru taci gaba da wanzuwa wadda harta sabbaba mata tunanin kashe wayar can taji ya sake jan zuciya yace “nayiwa Mai Martaba mgn game da tariyarki yace nayi miki mgn shiyasa na kiraki a wannan lkcn me kike shiryawa meye plan dinki?" Shiru tayi kamar bazata ce komi ba shikuma yayi kasaqe Yana jiran jin cewarta alamar da yaga na ba mgnr zatayi ba yasashi cewa “ok bakida wani tsari ga dukkan alamu ni inadashi yau Litinin na baki zuwa juma'a ki gama komanki zaki tare a gdanki kici gaba da ibada kamar kowacce mace, ki duba account dinki na tura miki wasu yan canjika Basu da yawa kiyi hqr dasu idan basu isheki shirye²nki ba zanyi qoqarin qara miki insha Allahu"
Katse wayar yayi daga haka tabi wayar da kallo cikin mamaki lallai ma Kareem dinnan yana fama da kansa yana fama da bala'i shikam dama ya hqr ya barta anan inda take da yafi musu kwanciyar hankali dukkansu. Qwafa taja ta duba alerting din da akayi mata dazun ta zare ido tare da cewa “wht? Me zanyi da kudaden nan ni Aminatuh 2 millions ta meye ce?" Komawa tayi ta kwanta baccin da bata koma ba kenan washegare wayewar Litinin ta fara shiri don komawa makarata Mom na kallonta batace mata komai ba harta gama shiryawa ta dauki jakarta ta saba tace “mom zan koma school" murmushi tayi tace “da izinin wa?" Kallon Mom tayi da sauri tace “izini Kuma?" Daganta kai tayi tace “mijinki ya kirani da asuba yace kada ki koma makaranta kiyi shirye²nki juma'a zaki tare a gdanki Litinin me zuwa zaku tafi Saudi zai koma can da zama abinda yayi saura na karatunki yayiwa H.O.D na department dinku mgn zaayi bakin qoqari" zama tayi dabar a gurin gumi na karyo mata tace “ni Kuma Mom in bisa Saudi haba Mom don Allah kice masa aa inada abubuwan da sukafi binnasa muhimmaci anan Mom inason in nemi dangina su hadani da dangin mahaifiyata idan naci gaba da zama a haka akwai matsala please Mom kisa baki don girman Allah"




Murmushi Mom tayi tace “wannan duk me sauqi ne ni na daukar miki alqawarin bibiyarsu har zuwa lkcn da zaa dace kibani address nasu" sunkuyar da kanta tayi hawaye wani nabin wani itadai bataso ba taso tayi komanta da kanta miqewa tayi ta koma dakinta ta kishingida zuciyarta na zafi haka yinin ya kusan qarewa kiran duniya da yakeyi mata taqi dagawa itafa bayan zafin tsanarsa saboda mahaifiyarsa da tayi harma da ganin rashin dacewar wannan auren nasu duk da tasan ba haramci a ciki Amma wata halal din ta cancanci bari don kunya.
Da la'asar tana kwance Mom ta turo qofar ta shigo da sallamarta ita da wata mata Meenah dake kwance ta miqe suka gaisa da matar Mom tace “wannan itace nakeyi miki mgn aurenta na farko yazo a wani yanayi baayi mata komai ba so data haihu an gyarata Amma anja shekaru kusan shekara antafi biyar shine yanzun nake buqatar ki qure fasaharki wajen gyarata ko nawa ne mijinta yace zai biya" suna hirarsu wannan Hajiyan na fito da saiwoyi da magunguna tana yima mom bayani tare da turaruka itadai tabe baki kawai takeyi bata yarda abin gaske ne ba Saida taga an dauki wani qoqo an zuba wani ruwan tsumi an dauko wasu barbade barbade anyi an gwamutsa da danyan madarar shanu wai sun miqo mata tasha.
Ta dubi Mom da idanunta daya kawo ruwa zatayi mgn ta kuwa daure fuska tace “aini dama nasan ban isa dakeba Aminatuh nunamin bani na haifeki b...." Da sauri ta karbi qoqon maganin jikinta na rawa ta kafa bakinta ta shanye daqyar tana kakarin amai matar tayi murmushi tace “wannan shi kadai ma idan Tasha na kwana biyar ya wadatar bare zaa hada da wasu tun daga wannan rana Juhud ta bani ta lalace da magunguna wasu tsarki wasu Sha wasu dafawa itadai bakinta har daina tantance dandano yayi cikin kwanakin batada aikin daya wucce kuka.





Wayar ma da Kareem ke kiranta ta jefashi a blacklist ko ya Kira baya samunta hakan tasa dole ya qyaleta yasan duk inda yau takai da jimawa gobe tana tafe yanaji a jikinsa wataran wannan qiyayyar zata shude tunda da babu ita daga baya ta wanzu to watarana itanma zaa nemeta a rasa, da wannan tunanin ya tattarata ya zubanta ido akayita shirye²n tariyar tata shine da Mom da Ya'isha da Aunty Hamida suketa digiminsu dakin uwar ango da yan'uwansa Babu me ko lale da bikin hasali ma ko bangaren da ake shagalin basuyi itama amaryar haka saidai idan Mom tayi mata dole sannan take dan motsawa hakana aketa kaiwa da komowa su Ya'isha sune yan jeran amarya har zuwa lkcn Zahrah bata dawo ba aka gyarawa Juhud dayan bangaren kamar yasan zaiyi mata biyu dama tsarin mace biyu yayiwa gidansa bayan sun gama gyarawa sun zubanta duk wasu kayan alatun rayuwa suka kullo suka taho gda sunata yabawa da kudin da Kareem ya narkar a furniture dinta lallai ba qaramin so yakeyiwa Meenah ba.
Ta dauki gyaran jiki na ban mamaki abinka da farar fata har wani yellow takeyi yanda Mom ke rawar jiki a wannan bikin ko Rasheed ne ya dawo ba lallai tayi ba ko lalle da akayi mata dishi² ya kama jikinta saboda tsabar gyara hatta gyaran gashi a gda akayishi yin duniya suje gurin gyaran taqi tana maqale a daki kamar wata mara gsky ko yaushe cikin kukan rashin mijinta take da anbarta da wannan damuwar ma da tafi mata fiye da wannan da aka qara mata




Ranar juma'ar Mom taga ikon Allah yini Meenah tayi tana kuka tana kiran Rasheed duk dauriyar da Mom takeyi a wannan karon Saida ta kebe itama taci kuka ta gode Allah Mom bata qara tsinkewa da lamarin Aminah ba Saida magrib da Kareem ya turo da motocin daukar masa amarya tunda ta fice a sashin su Mom din aka nemeta aka rasa babu wanda hankalinsa bai tashi ba amarya ta bace da aka fadawa Kareem neman zaucewa yayi ya nufo gdan afujajan suka shiga nemanta lungu da saqo domin sun tabbatar da cewa tana cikin gdan kasancewar masu tsaron qofofin gdan sunce Babu wacce ta fita gabadaya sun gama karade gdan babu dalilinta sai a qarshe Mom tace aje bangaren Rasheed ko can tayi haka Kareem da Mai Martaba suka nufi part din ga mamakinsu suka tarar dashi a bude suka kalli juna babu furuci suka kutsa ciki yayi qura sosai part din haka suka rinqa dubawa can cikin wani daki suka rinqa jiyo shassheqarta har rige² sukeyi wajen shiga dakin sukaja sukayi turus dukkansu ganinta zaune gefen gado rungume da wani hoto a qirjinta sai kuka takeyi me ban tausayi.
Wani abu me nauyi ne yazo ya tokarewa Kareem maqoshi ya furzar da iska me zafi ya juya ya fice daga dakin sai Mai Martaba ne ya qarasa shiga ya kamo hannunta Babu musu ta miqe tanaci gaba da kukanta idonta lullube da alqyabba ya fito da ita harabar gdan Ya'isha ta nufosu da sauri suka sanyata a mota tana qarawa kukanta sauti tana Kiran sunan Baffa'am Sarki junior dukkan wanda yake a gurin hatta Mai Martaba Saida tasashi sharar hawaye.




Hakanan suka nufi unguwar da gidan nasa yake Mai gadi ya bude musu suka shiga sukayi parking Aunty Hamida ce take riqe da hannunta har cikin gdan suka haura da ita saman itama kamar dayan sashin dakuna biyu ne sai wani qarami da alamun local kitchen ne wanda koda zaka buqaci wani abu da dare basai ka sauka ba, daya cikin dakunan suka bude suka shigar da ita sosai Hajiya Kulsum aminiyar Mom ta qara yimata nasiha akan biyayya ga mijinta itadai Babu abinda da takeyi sai kuka da rawar sanyi zazzabi ne yake neman rufeta Ya'isha ta matso jikinta ta sunkuya tace “ke banza ce wlh Ni banga abin kuka ba to kukan mafita ya zame miki kome?" Dagowa tayi ta sauke idanunta sa suka jima da komawa jajaye saboda kuka tace “shi....shikenan da gaske na rasa Baffa'am dina Ya'isha Kuma akeso nayi rayuwar farin ciki....." Muryarta ne ya kama rawa Ya'isha tace “mun shigai Aunty Hamida ku Kira mijinta zata tayar mana da aljanu" yanda jikinta ke tsuma ne yasa Hamida yarda ta Kira wayar Rasheed ya daga muryarsa can qasa shima rawar tasa muryar takeyi yace “ya aunty Hamida ya akayi?" Cikin zaquwa tace “Meenah ke neman rikice Mana mun kasa gane kanta don Allah kazo idan kana kusa" kashe wayar yayi dake dama Yana gdan duk motsinsu yanaji ya dauki doguwar riga ya saka ya bude qofar ya fito idanunsa kamar garwashi saboda ja dake duk yafisu Rasheed haske shi fari ne sosai daka kalleshi zaka gane kukan shima yakeyi.
Kuka Fadila ta saka da ganin yanda yayan nata ya zama wani kalar tausayi tace “tunda yarinyar nan ta shigo zuri'armu muka daina cikakken farin ciki Ya Kareem kaima duk ta susutaka yanzu kukannan don ita kakeyinsa....."
Hanya ya saita mata cikin zafin zuciya yace “kowa yaje na gde" binsa sukayi da kallo ya dubi Hajiya Kulsum yace “Mama wlh idan akaci gaba da hayaniya a gdannan tsaf zan haukace brain dina tana neman daina aiki" sumsum suka rinqa ficewa daga gdan saida suka fice gabadaya ya tsaya yana jin tashin motocinsu gabansa faduwa yake daqyar ya tura qofar da sallama ya shiga dakin ya tsaya tsakiyarsa Yana qarenta kallo tana zaune ta dora kanta jikin gado sai tsumar jiki takeyi a sanyaye ya isa gareta ya tsugunna gabanta yakai hannunsa zai dago kanta gabansa ya fadi ya janye ya sake saita idanunsa akanta yace “meye yake damunki?" Kamar me jiran yayi mgn ta dago kumburarrun idanunta suka shiga cikin nasa ya kawar da kansa ya dake zuciyarsa yakai hannunsa jikinta yajishi zafi zau yaja numfashi ya miqe ya dauki wayarsa Yana zagaya dakin can yace “Inada petiant a gdana kazo da wuri don Allah" da haka ya kashe wayar yaci gaba da zagaya dakin can yaji ana qwanqwasa qofar ya sauka ya bude suka shigo tare Dr Razaq ya fara tambayarta yanayin da takeji tayi masa shiru shikam Kareem ido ya kafeta dashi can da tambayar ta isheta tace “Kaje Dr Razaq bakada maganin matsalata Allah ne kawai zaimin magani" wata iska Kareem ya furzar ya juya ya fice Dr Razaq ya biyosa yaganshi tsaye ya hade kai da garu ya dafashi yace “ka daina Sanya wannan damuwar a ranka Ranka shi dade kanada heart problem idan komai zaike damunka to rayuwarka tana cikin kwale²"
Juyowa yayi ya dubi Dr Razaq yace “kana nufin Meenah zata soni nima?" Dariya tambayar tabawa Razaq yace “kama qaddara a ranka tasoka fiye da kowa ta gama karfa ka manta kaine ta fara so a rayuwarta ko ka manta Karin mgnr hausawa da suke cewa so baya tsufa saidai masoyan su tsufa bature kuma yace true love never end" wani murmushi yayi yace “na gde Dr Razaq zan jira lkcn da zan gasqata hakan".............




Juhud is not free read... regular 300 VIP 600

Please Login or Register in order to submit comment