Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

tafiya wani aikin hadin gwiwar qasa da qasa zuwa Togo yaso tafiya da ita Mom tace gara yaje yaga yanayin gurin tukunna inyaso sai yazo ko ya aiko tabisa.
Hakanan suka rabu bason ransu ba wani abin almara tunda ya tafi wayarsa bata shiga da farko sun dauka yanayin aiki ne tafi tafi da tafiyarsa ya dauki wata biyu babu waya babu aike, sosai hankalin Juhud yaqi kwanciya hakanan wata faduwar gaba ta aureta Mom ma tana cikin damuwar rashin jin labarin dannata hakanan take daurewa tana kwantarwa da Meenah hankali, tafiya na qara tsayi har aka tafi wata shidda Babu waya Babu amo Babu labari. Qa'idar aikin nasu yace watanni shiddan ne gashi sun wucce nan fa Mai Martaba ya tashi takanas yaje barikinsu inda ya dawo cikin matsanancin tashin hankali suna ganinshi Meenah dake zaune ta dora kanta saman cinyar Mom tana aikin kuka ta miqe tana cewa “Mai Martaba kaganoshi Yana cikin qoshin lfy?"




Sunkuyar dakai Mai Martaba yayi yana kwance rawaninsa yace “lamarin akwai daure kai fah naje barikinsu duk sojojin da aka tura Togo sun dawo tsiraru ne suka mutu Amma shi bai dawo ba dana matsa da bincike ma a data na aikinsa tun sunada wata biyu da tafiya wani mugun ciwon kai ya sarqeshi shine dalilin da yasa aka bashi hutu da zummar zai dawo gda tsayin watannin nan bai dawo ba....." Yanke jiki Meenah tayi ta fadi qasa sumammiya gabadaya sukayi kanta Mom ta dauko ruwa ta fara yayyafa mata daqyar ta dawo hayyacinta ta miqe zaune ta dubi Mai Martaba cikin gushewar hayyaci tace.
“Me kakeso kacemin Mai Martaba mijina ya taho gda daga filin daga Kuma baizo gidaba to Ina ya tsaya Kuma wayoyinsa basa shiga tun satin daya tafi?" Gumi Mai Martaba ya sharce yace “shine abinda nima nake tambaya kada ki tashi hankalinki na sanar da duk Wanda ya kamata na sanarwa wannan isue din Kuma sun fara bincike daga yau insha Allahu komai zaizo da sauqi...." Cikin kuka tace “ta yaya zan kwantar da hankalina bayan rayuwata tana cikin garari nikam don Allah ku fitomin da mijina wlh inason kayana" daqyar suka samu suka lallasheta shima ba shiru tayi da kukan ba kawai surutan ta daina hakanan aka duqufa babu ji Babu gani nemansa ta kafofin sadarwa na Internet da duk wasu hanyoyi da zaa samu bayaninsa Amma shiru Babu amo Babu labarinsa.




Gabadaya hankalin gdan sarautar Babu na kwance wannan baqon alkaba'i daya fado musu Babu zato ya girgiza zuciyar kowa a gdan daga yara har manya hatta wadanda ke nuna adawarsu irinsu Hajiya Bilki a zahiri suna nuna alhininsu tare da jefar da maganganu na zargi a fakaice suna alaqanta batan nasa da Juhud da take kwance cikin halin jinya bata kwana uku da lfy saboda tashin hankalin da take ciki duk ta qare sai qasusuwa gashi kullum lkc qara tafiya yake babu wani amon labari tun daga sama ga manyan sojojin da suka baza idanunsu a kowanne lungu na Africa domin ganoshi zuwa gwamnati da itama take hobbasa wajen ganin an samo bakin zaren saidai kullum labarin daya ne baya canzawa daga inda yake.
Malamai kuwa da suke aiki da addu'ar Allah ya fito dashi sunfi dari suma kullum amsar daya ce a qara hqr lamarin daya Sanya Juhud a wani hali ga shayarwa gashi ko abincin bata iyaci dole tasa sarki yanada shekara daya da wata hudu Mom tayi masa yayen dole aka dorashi akan abinci aka qyaleta da damuwa daya gabadaya ta quntata kanta kullum bata da aiki daga sallah karatun qur'ani sai kuka




Mai Martaba da yayansa maza musamman Kareem daya dawo daga Saudia ya gama karatunsa kullum basa Kano basa Abuja basa Lagos Basu kotono Basu Togo Basu Burkinafaso tafiya kullum qara miqawa takeyi Abu ya tafi shekara guda, watarana suna falo suna zaune Meenah na rungume da Sarki junior Amrah da Fadila suka shigo suka zauna aka gaisa suka jajantawa juna Dada Hanne dake zaune ta rafsa tagumi ta dago tana kallon Juhud tace “lamarin nan da ban mamaki Mahfuz batan Abdulrasheed kamar batan toka a ruwa gsky abinnan da lauje cikin nadi Anya ba mutuwa yaronnan yayi ba"
Duk Wanda ke falon Saida ya dago karma Juhud taji labari da kaduwa tasata zamewa daga kujerar ta sauko qasa tayi dabar tana kallon Dada Hanne. Harara ta watsa mata tace “eh Mana biri yayi kama da mutum to nidai tunda abinnan ya faru nake biyar malamai da yan bori idan suka hau bori suka jirge sai suce ai saqale kurwarsa akayi akayi bandarsa" gabadaya hankalin kowa sai ya dawo kan Juhud da itama take jujjuya mgnr a kwakwalwarta Dada Hanne tace “kuma fah cewa sukeyi makusancinsa ne yayi masa wannan abin kawai saboda yanason cin gado to nidai naga kaidai Mahfuz bazakayi wannan abu ba itama Mom din yara bazatayi ba saura da me dama Kuma ku hudune magadan nasa....."




Miqewa Kareem yayi yace “don Allah dakata Dada kada kizo Mana da surkullen hauka cikin wannan lamari ke Ina kika taba ganin anyi bandar mutum banda sakarcinku na mata? Kuma ma meye Rasheed ya Tara da har zaayi tunanin kasheshi don gadonsa haba dallah ku rinqa auna mgn kafin kuyita Mana" Yana fadin haka ya miqe zumbur ya dubi Addansa daketa harararsa ya dubi Mai Martaba da Mom yace “wlh daukan alhakin Meenah zakuyi indai kuka zargeta yarinyar nan batada wani abu da ta sani game da batan mijinta haba ai abinda zai yuwu ma dagaji ansanshi" ficewa yayi daga gdan idanunsa nakan Meenah da keta jan zuciya tunda mijin nata ya bata take cikin masifa komai Yana neman koma mata baya gdan an qara tsangwamarta da Mom kawai takejin dadi sai Kareem daya mayewa Sarki junior madadin bsbansa komai ya tarkato Sarki.
Ana haka Mai Martaba yaga zaman ya fara tsayi Abu ya tafi shekara biyu ya Sanya Kareem ya nema mata admission bayan sun biya mata an zana mats jamb lkcn da sukayi mata mgnr karatun fir qi tayi tace ita bataso daqyar Mom da Kareem sukasha kanta ta yarda ta fara zuwa Alqalam University Katsina bata jima da fara zuwa ba abubuwa suka fara canzawa Dada Hanne da Alh Aminu suna zuga Mai Martaba baiyi furuci ba Amma gabadaya ya janyewa Meenah tallafi babu Wanda yasan dalili Mom ce taci gaba da dawainiya da karatun nata ita da Kareem.




A hakadai da dadi babu dadi take gurgura karatun cike da samatsi da qalubalen rayuwa kullum addu'a takeyi Allah ya bayyana mijinta itama ko ta samu hasken zuciya. Yau da gobe ce tasa Kareem bawa Mom shawarar kama mata hostel saboda karatun nata na Law yanajan kudi sosai hakan kuwa akayi suka kama mata hostel ta koma can da zama Sarki junior na gurin Mom yanata girmansa inda a lkcn Ya'isha ta ta haihu Zahran Kareem ma ta haihu taso zuwa daidai lkcn suna exam hakanan ta hqr sai bayan Exam akayi hutu ta shirya domin zuwa tayi barkar ta nufi Daura cike da kewar gudan jininta da sallamarta ta shiga falon Sarki ya taso da gudu ya rungumeta ta dagashi tana juyashi suna dariya tayi kissing nasa tace “miss you love inata kewarku"
Lakace mata hanci yaran me shekaru hudu yayi yace “yaushe zaki dawo?" Narkar dakei tayi tace “saura semester guda Son ka matsu na dawo ne?" Turo baki yayi yace “Addah Fadila ce tacemin na daina zuwar mata gidanta kada na cinye mata su Jabir Momy wai tace kece kika cinye Dad Ina ya bata....." Gwabe bakinsa Mom tayi tace “ba nace maka idan na qarajin mgnr nan a bakinka saina yankaka ba" riqe bakinsa yayi alamun yayi shiru ta daukeshi jikinta a mace ta nemi guri ta zauna suka gaisa da Mom ta miqe tace “zanje nagano babyn Ya'isha" miqewa itama tayi tace “nima abinda ya kawoni kenan hutunmu na sati daya ne Kuma tun shekaran jiya akayi" dungumawa sukayi suka fita suna fitowa Muntaz na shigowa Mom tace “yawwa zo ka kaimu gdan Ya'isha"




Babu musu yaja suka tafi suna taba yar hirarsu tace “Jiya Hafeez abokin aikin Baffa'am yakaimin ziyara" murmushi Mom tayi tace “nan ms yazo gurin Mai Martaba yazo ne da wani shirme wai qa'ida shekara hudu ne idan mijin mace ya bata alqali zai bata damar tayi aure ke anbaki dama ne? Tsaki taja me zafi tace “shege sai naci kutumar ubansa ni ce masa akayi mijina bazai dawo bane nifa Mom bantabaji a Raina Baffa'am ya mutu ba Yana raye kawai dai Allah ne be gama ganawa ba" numfashi Mom taja tace “nima haka nakeji so naga Mai Martaba ya saduda shiyasa nima na fidda rai da tsammani" shiru ce ta dan gifta suka Isa gdan Kareem ta jinjina haduwar gdan karo ns farko data sanya qafarta a gdan tun aurensa da Zahrah kasancewar Zahra mugum baqin kishi takeyi da ita to itama shiyasa taja jikinta.
Da sallama suka shiga aka Amsa musu Dada Hanne na dagowa taga Juhud tayi maza ta dauke jaririn tasa a bayanta suka gaisa tayima Zahrah barka tana amsawa a yatsine ta aje kayan data siyowa bebin tana satar kallonsa a bayan Dada tanason jariri a rayuwarta bata samu arziqin daukan jaririn ba Kareem ya sauko tunda ya fito idonsa na kan Juhud dake wasa da yatsunta yace “aa Meenah Ina cewa zanzo na daukoki ashe kina hanya" murmushi tayi masa tace “wlh na matsu nazo naga baby's din da muka samu shiyasa na biyo motan haya" shafa kansa yayi yace “insha Allahu cikin satinnan motarki zatazo haihuwar nan cema ta dan takemin birki" gdy tayi ta miqe saboda bata cikason zaqewa a lamarinsa ba ganin haksn yasa Mom miqewa sukayi sallama ya biyosu har jikin motarsu yanajan Sarki da wasa suks shiga suka tafi shikuma ya juya suka nufi gdan Ya'isha.........




Juhud is not free read... regular 300 VIP 600 via👉🏼 0255526235 Fauziyya Tasiu Umar GTbank



Then you show ur evidence via WhatsApp 09013718241...



Juhud ba littafin kyauta bane ki biya 300 regular VIP 600 kafin ki karanta ta wannan account din 0255526235 Fauziyya Tasiu Umar GTbank ko katin MTN pls ban buqatar vtu hoton katin ko digit number ta WhatsApp number 09013718241.....



*Oum Hairan*
[8/6, 10:48 AM] Oum Hairan: *0029* A gdan Ya'isha suka shantake sunata fira Basu suka baro gdanba sai gefin magrib suna shiga gdan gaban Juhud ya fadi batare da tasan dalili ba suka nufi parlourn da sallamarsu a tsaitsaye suka tarar da Addah Abulle da Fadila Juhud na Shirin mgn taji an shaqeta ta baya batare da sanin waye ba suka rinqa kokawa daqyar Mom da Muntaz suka rabasu Fadila na huci ta nuna Juhud da ta zubanta ido tace “muguwa azzaluma Ni dama tunda akace kinje barka nasan ba Alkhairi ne yakaiki ba ace daga zuwanki jaririya ta kama cuta kwana uku da haihuwarta batayi ba sai yanzu da kikaje to wlh ki sakar Mana kurwar yarinya ko mu aikaki lahira shegiya baqar kadara"
Cafewa Addah Abulle tayi da cewa “to waima meye yakaita barkar waye yace Yana buqatar barkarta gsky nikam wannan lamarin na gdannan ya isheni Abu ya wucce kan wadanda suka jajuboki ya dawo kanmu shekara uku dayin auren nan baa haihu ba shine daga kinji an haihu zaki lashe musu ya tab wlh bazai yuwu ba dole ma Mai Martaba ya zaba a gdannan ko mu da muke dolensa ko Kuma ita da suka liqawa mutane" tunda suka fara mgn ta fahimci inda suka dosa jikinta yake rawa hawaye ya kasa tsayawa a idanunta mgn takeson yi Amma bakinta ya sarqe zuciyarta wani zafi takeyi hakanan takejin a ranta yau ko zata fita a kasheta sai tabar gidan lamarin ya fara wucce yanda zuciyarta zata dauka. Juyawa tayi ta shiga dakin da take taja akwatu ta fara hade takardunta tana wani irin kuka me ciwo itakam tagaji da wannan quntattaciyar rayuwar shekaru ashirin da biyar na rayuwarta ta qaresu a qunci shekaru tara Mom na hadiyar baqin ciki akanta meye yasa bazata gushe ba kota samu salama da sanyin ruhi suma masoyanta su samu?
Tanayi tana jan zuciya tana tunano yanzu hakanan zata fice tabar gudan jininta daya tal a duniya meye makomar rayuwar Sarki idan ta tafi ta barsa? Dagowa tayi bayan ta gama hada kayan ta zuge ZIP din trolley din ta miqe ta dauki hijjab dinta ta zura taja akwatin takai hannunta zata bude qofar Mom ta bude ta shigo idanunta na tsiyayar da hawaye tace “duk wani abu daya kamata nayi miki Meenah nayi miki domin Allah meye yasa qaramin Abu yakesaki jin tafiya kibarni shine mafita? Me kikeso nacewa Rasheed idan Allah ya bayyanashi yaji abinda kika aikata? Haba Meenah nidai Ina ganin indai kika yanke barina to tabbas baki biyani haqqina ba Kuma kin basu damar yimin dariya ne......."





Wani kuka ta saki me ciwo tare da durqushewa ta kifa kanta jikin akwatin tanayinsa babu furuci kalma batada ita a bakinta da zata iya furtawa zama Mom tayi tana bata baki tana rarrashinta Amma kamar tana zugata, aka bude qofar aka shigo Mai Martaba ne ya shigo fuskarsa Babu alamun wasa yace “ke Aisha tashi ki bani guri inason mgn da ita" miqewa Mom tayi ta fita tana kallon Meenah data dunqule tanata aikin kuka ta girgiza kai ta fice daga dakin ya nemi guri ya zauna Yana nazarin yarinyar da yanda duk jikinta ke rawa jikinsa yayi sanyi shi kansa yanajin kunyar kansa irin biyayyar da yarinyar takeyi masa bata cancanci haka daga gareshi ba ta daukeshi kamar mahaifi tanayi masa biyayya fiye da yanda yayan daya Haifa sukeyi masa to waima meye yasa yake yarda da jita jita akanta ne?"
Gyaran murya yayi yace “ina kike Shirin tafiya yanzu?" Cikin kuka tace “inda ubangiji ya kaini don girman Allah karka hanani Mai Martaba na gaji wlh na gaji da qaddarorin nan masu wahalar dauka inaji a jikina banida wani rabo na farin ciki a rayuwata Mai Martaba idan ka hanani zan rasa kaina zuciyata zata buga....." Jinjina kai yayi cike da tausayawa yace “meye yasa kika yanke wannan hukuncin?" Dagowa tayi idanunta akansa bakinta ba rawa tace “Baffa'am shine mutum na farko dayayimin gata ya zabi farin cikina akan komansa Mom ta dora sunci baqin ciki akaina sunama kan ci wlh koda bana tare da mijina inaji a jikina duk inda yake hankalinsa yana gareni Mai Martaba bazan zama silar bacewar da na zama silar macewar uwa ba idan naci gaba da zama da Mom baqin cikin abinda ke faruwa Dani zai iya taba tata rayuwar nikam na riga na zaba na yankewa kauna da samun wani jin dadin rayuwa kubarni naje na rayuwa ni kadai abinda kukayi a baya na gde....."




Daganta hannu yayi yaja zuciya yace “naji Meenah ki cire wannan tunanin a ranki Babu inda zakije kinanan" miqewa yayi ya fita daga dakin yana fita ta koma ta kwantar da kanta jikin gado tana wani kuka me ciwo, tana jiyo hayaniya da fadan Mai Martaba a falo saidai bata fahimtar meye yake cewa sama sama taji yana cewa “ni na haifi Rasheed na haifi Kareem dukkansu ikona ne duk da qaddara tasa Meenah bata zama mallakin Kareem a farko ba hakan bazai zama hujja ta cin mutumcinta ba wlh tallahi Zainab duk ranar da wani abu makamancin wannan ya Kuma faruwa zakisha mamaki na Kuma babu wanda ya isa hanani zartar da abinda nayi niyyah a gobe juma'a zan yanke abinda nayi niyyah kai nama fasa yau dinnan idan da Wanda ya isa ya Hana"
Bata fahimci komai ba Amma sosai taji wata faduwar gaba ta darsar mata ta miqe ta shiga bathroom ta watsa ruwa ta dawo ta kwanta damuwa tasa zazzabinta na qa'ida ya dirar mata wanda likitoci sukayi ittifaqin zai iya haifar mata da ciwon zuciya saboda Yana yawan kumbura zuciyar tata.
Bacci ne ya dan dauketa sama sama kasantuwar ba sallah zatayi ba tanaji ana Kiran sallar Isha a masallacin Fada ta sake gyara kwanciyarta bacci me nauyi ya dauketa batasan meye yake faruwa ba sai ji tayi ana yiwa qofar bugu na hauka ta miqe zunbur tana son tantance dalilin bugun taji muryar Addah Abulle tana cewa “billahil lazi la'ilaha illahuwa indai nice na haifi Kareem bazai taba zama da wannan tsinanniyar yarinyar ba matsayin mata wlh Allah saidai idan na kasheta nima a kasheni"





Muryar Mai Martaba taji Yana cewa “bazama takai ga kisan ba kizo ke ki fita a gdannan ki tafi gdan naki uban aure ne na daurashi Babu dalilin fasashi" bude qofar taji anyi ta sake zabura ta zubawa me shigowar ido Kareem ne ya shigo idanunsa akanta itanma shi take kallo ido cikin ido ya mayar da qofar ya rufe ya nufota taja baya da sauri yaja ya tsaya Yana kallonta ya dan saki fuskarsa batare data tsammata ba taga wasu hawaye sun kwaranyo daga idanunsa ya daga hannu sama yace “Alhmdllh Meenah duk da banyi tsammanin zuwan wannan lkc da wuri ba Ina tayamu murnar samun kanmu a sabuwar rayuwa matsayin da naso samunsa a farko ubangiji bai amince ba wato ma'aurata.........."
Ai bai rufe bakinsa ba ya tsinceta a qasa warwas yayi kukan kura ya isa gareta Yana jijjigata Addah Abulle ta danno qofar tayo kansu da wuqa tsirara a hannunta ya miqe da sauri ya tareta Mai Martaba da Muntaz suka tayashi riqeta ya damqe kaifin wuqar da hannunsa tana wani kuka me cin zuciya tana cewa “wlh saina kasheta mayya cikin zuri'a ta bazan taba lamunta ba......"




Abinda Mai Martaba baitaba yiba yau shine yayi mata allurar yan maza ta motsa abinka da tsohon soja baisan sanda ya saketa ba yayi bal da ita taje ta daki gini ta dawo qasa tana qoqarin tashi ya sake nufarta Kareem da hannunsa keta zubar jini saboda riqon da yayima wuqar ya nufeshi da sauri shida Muntaz suka riqeshi daidai lkcn da Arman ya shigo shima yayi kan Mai Martaba Mom ce da Salman sukayi ta Juhud suka kimkimeta Kareem ya saki Mai Martaba har yanzu kuka yakeyi yace “don Allah Mai Martaba kada kayi abinda kayi niyya ka qyaleta tayi duk abinda da tayi niyya aurena da Meenah ne Allah ya riga ya daurashi babu abinda zai kwanceshi saidai mutuwa ko qaddarar data raba auren Rasheed da ita"
Fita yayi da sauri ya shiga motarsa yabi bayan tasu Mom suka nufi asibiti sukayi emergency da ita likitoci suka rufu akanta numfashinta suketa qoqarin saqalowa abin ya gagara faduwar da tayi taja mata shiga doguwar suma, ranar daga Kareem harsu mom Babu Wanda ya koma gda anan suka kwana gurinta gabadaya ya rude hankalinsa yaqi kwanciya Yama manta da lissafin yar jaririyar yarsa da take asibitin itama ta Juhud din kawai yakeyi Muntaz ya tafi gda suka dawo da Hamida da Mai Martaba Addah Abulle bata gdan hankali ma baya kanta balle asan Ina ta nufa.




Mom da Hamida ke jinyarta tsayin kwanakin biyar batasan waye akanta ba Kareem ya canza mata asibiti yakai uku qarshe Asibitin Mal Aminu Kano ya mayar da ita acanne suka samu ta fara motsa gabbanta sai lkcn ya samu nutsuwar tunawa da iyalinsa har zuciyarsa nutsuwarsa ta rabasa da tunanin komai sai lfyr Meenah babban tashin hankalinsa da likita yace masa zuciyarta ce take barazanar daina aiki saboda ta cunkusa mata damuwar da tafi qarfinta tunaninsa ta yanda zai fara nasa aikin ya goge mata duk wata damuwa dake buwayar rayuwarta ya sanyata farin ciki kamar yanda ya shirya yi a farko Allah bai amince masa ba burinsa bai wucce Meenah ba cikin duniyarsa gata ya sameta Amma Kuma wasu abubuwan sun danni soyayyarta gareshi tsabar qin da takeyi masa ne yasata shiga wannan yanayin dajin cewa shine matsayin mijinta ko meye dalili?
Wadannan tunane²n sune suka sanyashi ramewa cikin kwanaki biyar din.









Ranar kwana biyar din ranar ta kama sunan Matarsa hakanan ya nufi Katsinan bashi da wani kuzari dake yasan dama ba taron sunan akeyi ba har zuwa lkcn Zainab sunan yarinyar kenan sunan mahaifiyarsa yasa mata tana asibiti ciwon gendis yayi mata kamun gaske anyi mata juyen jini Amma duk da haka taqi lfy inda likitoci suka tabbatar da a cikin mahaifiyarta ta samu matsala Amma su sun dauki alhakin ciwon kacokan sun dorawa Meenah musamman su Dada Hanne da dangin Zahrah da sukayi tsalle suka dire suka dauke yarsu cewa bazata zauna da Meenah ba shidai daya yakabo yaje ta qare masa,
Bai damu ba koda yaje gdan nasa ya tarar dashi a kulle domin ya riga ya shiryawa zuwan wannan Rana a baqin kishi irin na Zahrah ba Meenah data tsans fiye da kowa a duniya ba ko wacce mace ya auro sai anyi wannan rikicin shiyasa baisa abin a ransa ba taje tayita zamanta a gdannasu idan ta gaji ta dawo. Kwanan Meenah bakwai a Kano ta bude idanunta tana kallon kowa daidai a lkcn tunaninta bai dawo ba bama kowa take ganewa ba hakanan ta rinqa rarraba ido kan mutane.




Mom sai sannu take jera mata tana binta da kallo da la'asar Kareem ya iso asibitin shida Ya'isha tun daga harabar asibitin ya hadu da Lado drivern Mai Martaba yayi masa albishir din Juhud wani farin ciki da murna daya dade baiyi irinsu ba suka cika zuciyarsa har gudun motarsa ya qara don ya isa gareta yayi parking baikai ga rufe motar ba ya nufi ciki sai Ya'isha ce ta rufe masa motar cikin tausayinsa ko lkcn da Meenah take matsayin matar Rasheed Kareem baya zama cikin nutsuwa muddin tana guri Allah ya jarabceshi da qaunarta gashi Kuma yanzu tasan ba qaramin rikici ya saukowa kansa ba don tabbas Meenan da ba itace yanzu ba batajin zai samu kanta da sauqi duk wannan rawar qafar da yakeyi akanta ba gani zatayi ba tunda bashine a zuciyarta ba hasali ma ita a lissafinta ma Babu aure.
Yana shiga bai saurari kowa ba ya nufi gadon da take kwance idanunta a lumshe yaja wata ajiyar zuciya tare da binta da kallo me nuna tsantsar qauna da kulawa yace “Aminatuh" jin saukar muryarsa tayi kamar muryar Rasheed ta kuwa juyo da sauri tare da bude idanunta ta saukesu akansa yanayi mata gizo cancanzawa yakeyi daga Kareem ya koma Rasheed ta kasa gane taqamaiman waye a gabanta.




Tun farkawarta bata iyayin furuci ba sai yanzu da bakinta ya bude da furta “Abdulrasheed....." Daga haka ta sake lumshe idanunta ta kwantar da kanta a pillow kuka me ciwo ya qwace mata daya Sanya Mom dake shigowa nufota da sauri tace “Subhanallahi waike yanzu Aminatuh bazaki daina Sanya damuwar nan a ranki ba kenan kullum ke kenan cikin jinya" wata ajiyar zuciya me qarfi Kareem ya sauke ya nemi guri ya zauna gumi na karyo masa Yana sharcewa Ya'isha dake shigowa tace “ya Kareem motar taka baka rufeta ba ka barota" shafa sumarsa yayi yace “wlh hankali nane baa jikina ba ince kin rufe" dagansa kai tayi ta nufi gadon da Meenah ke kwance ta riqo hannunta tace “amaryar Ya Kareem sunqi Allah yaso meye yayi zafi da doguwar jinya haka?" Zame hannunta tayi a na Ya'isha ta sake gyara kwanciyarta taci gaba da jan zuciya abubuwan da suka sabbaba mata ciwon suna dawo mata a fili tace “Aure, Ni Mai Martaba Ya Kareem Innanillahi wa Inna ilaihir raji'un Allahumma ajirni fih musibati wlh banaso don Allah ku taimakeni ku rabani dash.........




_Nasani wannan page din ba kowa zatayima dadi ba so Amma a babin qaddara wannan daidai ne shi ubangiji Yana zartar da hukuncin da yake daidai batare da la'akari da abinda Wanda ya zartar da hukuncin akansa zai nazartawa zuciyarsa ba kada ku manta matar mutum kabarinsa Kuma shi rabo ajali ne yakanyi kisa ma idan qarfinsa yakai._
_So kada kuga laifin alqalamina haka abin yake kamar yanda kuka ganshi a rubuce kada ki manta 50% is true life story._




Juhud is not free read... regular 300 VIP 600 via👉🏼 0255526235 Fauziyya Tasiu Umar GTbank



Then you show ur evidence via WhatsApp 09013718241...



Juhud ba littafin kyauta bane ki biya 300 regular VIP 600 kafin ki karanta ta wannan account din 0255526235 Fauziyya Tasiu Umar GTbank ko katin MTN pls ban buqatar vtu hoton katin ko digit number ta WhatsApp number 09013718241.....



*Oum Hairan*
[8/6, 9:00 PM] Oum Hairan: *0030* Miqewa Kareem yayi ya fice

Please Login or Register in order to submit comment