Join Our WhatsApp Group

Idan ku ka ga kun taba wani wuri ya fitar daku a shafinmu, sai ku danna back kuyo baya, ku sani yanzu muna amfani da tallan Popunder a shafin, so karatu zai muku dan wahala, amma ta hakanne kadai zamu iya cigaba da rike shafinnan. idan har bakwa son talla sai kuje ku yi subscription na shafinnan akan karamin kudi ku runga downloading kawai. SUBSCRIBE


DOWNLOAD

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register
DOWNLOAD

Babu me cewa wani qala garama shi da Khamil suna hira jefi² inda suka sauka ta tsaya tana kallo bata taba zuwa Lagos ba hakanan takejin to Ina ya kawosu?" Bai bata damar tunanin mafita ba motar office dinsa tazo ta daukesu suka nufi unguwar da yake da zama tasha mamakin gidan da aka kaisu ta tsaya tana qare mawa gidan kallo.




Plat ne me kyau sosai Rasheed akwai son qyale² ya qawata gidan tsaf ta tabe baki tajishi ya saqali hannun Muneefah ta sakar masa ita ya nuna mata dakunan yace gasunan keda yaranki duka sun isheku fatan nasara" dakinsa ya shige da Muneefah tabisa da kallon takaici ta gyada kai ta bude dakin kusa da ita ta shiga komai na dakin a tsare yake sosai abin gwanin birgewa gefe ga wasu manyan set na akwatuna guda 12 ta zubawa akwatunan idanu tana tunanin to na meyene?" Tabe baki tayi tace “nima dai da son wahalar da kaina kulle dakin tayi ta cire kayanta ta bude akwatun da ta taho da ita ta dauko wata qaramar riga Mara hannu ta shafanta turaruka ta nufi bayi tayi wanka ta fito ta shafa mai ta zura rigarta ta haye gado taja duvet tunda ba sallah zatayi ba nan take baccin gajiya yayi gaba da ita batasan sanda ya shigo ya kwantar mata da Muneefah ba sai wajen hudu ta farka taganta kwance ya cire mata riga daga ita sai Pampers tanata baccinta.




Yunwa ce ta fafareta ta miqe ta fito tana hamma ta nufi kitchen din taji qamshi na tashi ta qarasa da sauri ganinsa tayi dagashi sai boxes da headphones a kunnensa ya zage sai yankan alayyahu yakeyi ta juya zata tafi ashe ya ganta taji yace “kije ki huta idan na gama zan sammiki nasan cikinki ne Babu alert shiyasa kika fito
Yayi tsammanin zata kulashi yaga ta juya tayi tafiyarta ta koma dakinta yaci gaba da girkinsa Yana waqoqinsa bayan ya gama ya jera a dinning ya bude dakin ya isheta tana waya daga yanayin wayar yasan da Mom dinsa takeyi ya shafa kansa ya juya ya fice, koda ta idar bata nemesa ba har ya sake gajiya ya shigo ya tararta ta hade kai da gwiwa tanata jan zuciya ya matsa gabanta ya tsugunna yasa hannu ya dago kanta ta zame kannnata yayi mata murmushi yace “kinajin meye game dani?" Batace masa komai ba ta fara qoqarin tashi ta nufi parlourn yabi manyan bombom dinta da kallo yana lasar lips dinsa ya lumshe idonsa Yana tunano rayuwarsu ta baya da irin soyayyar da sukewa juna, zuciyarsa ce tayi baqi idanunsa ya kada yayi ja daya tuna Kuma fah irin abinda takeyi masa shine tayima Kareem shima ko?" Tuni hasken zuciyarsa ya disashe yaji wani qunci a ransa a fili da qarfi yace “Oh God meyesa hakan ta farune..........."





Juhud is not free read... regular 300 VIP 600 via👉🏼 0255526235 Fauziyya Tasiu Umar GTbank



Then you show ur evidence via WhatsApp 09013718241...



Juhud ba littafin kyauta bane ki biya 300 regular VIP 600 kafin ki karanta ta wannan account din 0255526235 Fauziyya Tasiu Umar GTbank ko katin MTN pls ban buqatar vtu hoton katin ko digit number ta WhatsApp number 09013718241.....



*Oum Hairan*
[8/28, 8:41 PM] Oum Hairan: Dafe kansa yayi ya koma ya zauna kalmar Innanillahi wa Inna ilaihir raji'un tana kaiwa da komowa azuciyarsa shi kansa Yana jinjina baqin kishinsa baya iya jurewa abubuwa game da Meenah tun kafin takai haka, qwafa yayi ya miqe ya fito falon tana zaune Muneefah tana wasa ya nufi inda yarinyar take ya dauketa suka nufi dinning ya hadansu abinci yanaci Yana bata tanajan gemunsa Meenah na satar kallonsa har suka gama ya miqe suka fice ta Isa ga abincin ta diba daidai cikinta ta shige dakinta taci tasha yourghut dinta taje tayi brush ta sake kwanciya Basu suka shigo gidan ba sai Tara na dare tana kwance Muneefah ta shigo Yana biye da ita da qatuwar yar tsanarta ta fada jikinta ta miqe tana mata dariya tace “sarkin yawo kin sama abinda kikeso ko Ina kukaje"
Gwarancinta ta rinqayi ya nemi guri ya zauna batako kallai ba taci gaba da wasa da yarta shikuma Yana kallonsu ganin ba zai samu arziqin kulawa ba yasashi miqewa ya fice ya shiga dakinsa ta miqe tana murmushin mugunta ta nufi bathroom tayima yarinyar wanka tasa mata kayan bacci ta kwantar da ita ta kulle dakinta da key ta kwanta,. Ba wuyar bacci gareta ba nandanan bacci ya dauketa sai Kuma kashegari da safen ma shine ya tasheta ya shigo cikin shirinsa na tafiya office tunda ya shigo suka hada ido ta kawar dakai tare da lumshe idonta ya matsa kusa da Muneefah yayi kissing nata ya zubawa fuskar Meenah idanu yana ganin yanda take qifqifta idanu yaja fasali ya sauke bakinsa a kuncinta yace “kin tashi lfy" ajiyar zuciya ta saki wata kasala na saukar mata tace “normal" murmushi yayi yace “gud zanje office me kuke buqata"





Kada masa kai tayi ya zaro kudi a aljihunsa ya ajiye mata yace “is ok akwai ma'aikata a gidannan idan na fita zanyi musu mgn zasuzo kowa zai gabatar miki da aikinsa idan kina buqatar wani abu ko baby akwai dan aike saiki bashi" jinjina kai tayi ya sake sunkuyawa yayi kissing Muneefah ya fice tana binsa da kallo ita mamakin sanyinsa takeyi cikin kwanakin nan ta lura ya sauko sosai don ita kanta tasan da Rasheed din dane rainin hankalin da takeyi masa da tuni ya ladabtar da ita Amma yanzun ta fahimci kamar bama abun na damunsa.
Da wannan tunanin ta miqe ta shige bayi tayi wanka ta gyara jikinta ta fito tasa kayanta ta sanya dankunne ta nufi kitchen ga mamakinta a dinning ta tarar da kayan Karin kumallo ta fara budewa ko baa fada mata ba tasan aikinsa ne doya ce da taji qwai sai miyar albasa da attaruhu sai ruwan tea a flast da kayan hadi a gefe taja fasali ta zauna ta fara bawa cikinta haqqinsa taji dadin break din sosai tana Shirin tashi ma'aikatan suka shigo mace daya maza biyu suka gaisheta ta amsa musu macen tace “ranki ya dade ni sunana Jummai daga Daura Yallabai ya kawoni nan aikina shine shara da mopping da wanke² sai kula da Muneefah yace tsarin gdansa baa masa girki shine yakeyi ko Kuma ke kiyi" jinjina kai tayi dayan yace “nikuma sunana Hadi duk abinda ya shafi fita unguwa da aike zuwa waje alhakinane" juyawa tayi da dayan yace “nikuma dan ruwa ne aikina shine kula da fulawa da wanki da guga ranki ya dade sunana Badaru" yanda yayi mgnr yabata dariya tayi murmushi tace “yayi kowa yaje yayi aikinsa"





Godiya sukayi suka fita kowa ya kama aikinsa Jummai ma ta fara gyaran falon ita Kuma ta shiga dakinsa ta gyaro ta kunna masa turaruka ta fesa na fesawa ta wanke toilet ta fito ta shiga nata shima ta gyara biyun da suke rufe ne kawai bata shiga ba ta koma tayi kwanciyarta ta rashin aikinyi har daya sannan ta fito ta dora girki Jummai nayi mata hira har suka gama suka Muneefah nata wasanta tayi wanka ta shirya cikin wata atampa blue tayi mata kyau dinkin doguwar riga me aljihu tayi sallar la'asar ta kunna kallo tana kallo tana chat har biyar sannan taji tsayawar motarsa ya shigo da kaya niqi² a hannunsa Jummai ta miqe tana masa sannu da zuwa itakuwa hakimar kawar dakai ma tayi yasan tayi ne don yaji haushi yayi murmushi ya aje kayan yace “barka da gida ranki ya dade Allah ja kwana ya qara lafiya fulanin gobe" duk yanda taso da shareshi dole Saida yasa tayi murmushi tace “sannu da shigowa" cire rigarsa ta sama yayi ya rage dagashi sai singlet ya qarawa A.C gudu yace “nasha wahala yau inata qoqarin naga tafiyar nan bata ritsa dani ba Amma Saida ta fado kaina Meenah banson tafiya nabarki wlh....." Ai tuni ta fara hada gumi ta juyo da sauri tana cizge dankwali tace “tafiya Kuma Baffa'am tab wlh aa bazaa Kuma sakani a tara ba nikam qafata qafarka"





Murmushi yayi Yana kallonta a zucci yace yar iskar qarya zanyi maganinki ta ruwan sanyi ni zakiyiwa hauka! Amma a fili sai yace “to ya zanyi Meenah Babu damar tafiya da iyali Australia sunada mugun sanyi dole sai kaje kaga yanayin gurin tukunna ko zaka dauki iyalinka Kuma ma Banda abinki mu ai zaman gaba mukeyi Inna tafi dake amfanin me zakiyimin abinda bakaso ai nesa kakeyi dashi ko?" Girgiza kai tayi ta zame qasan kujerar tace “nikam mubar batun wasa wlh nasha wahala a wancan karon har zaucewa Saida nayi Saida Mom da Mai Martaba suka rinqa sawa ana yimin addu'a sannan na dawo hankalina ya Rasheed don Allah ki million nawa ne kabasu subarmin kai a gida ni idan bamaka dashi zansai da shanuna da Kaka ya karbarmin gurin dangin mahaifi na nabaka kabasu subarmin kai kaji?" Tana mgnr muryarta na rawa.
Shima zamowa yayi ya zauna a gabanta ya riqo hannunta yanajin wani spark na jijiyoyinsa saboda rabonsa da riqe hannun mace haka shekara an tafi takwas kenan, jan wani numfashi yayi yace “kinaso na ne?" Tambayar ta daketa ta dago da sauri idanunta ya kawo ruwa yayi saurin dora hannunsa a bakinsa yace “aa ba kuka ba tambaya ce my Meenah kinasona?" Daga masa kai tayi ta fada jikinsa ta rushe da kuka tana cewa “don Allah don Allah Ya Rasheed please kada ka sake tafiya kabarni wlh zaucewa zanyi....." Hade bakinsu yayi ya lumshe idonsa yanajin wata natsuwa na shigarsa shaidan na qoqarin tuno masa da abubuwa Yana yaqarsa daqyar yayi galaba akansa ya koreshi ta hanyar zarmewa wa tabe²nsa itakam lumshe idonta tayi banda hawaye Babu abinda takeyi ganin Yana qoqarin zaqewa Kuma tasan kowanne lkc Muneefah ko Jummai in sunji shiru zasu iya fitowa yasata janyewa.




Kafin ta gama daidaita natsuwarta ya sunkuceta sai dakinsa ya azata a gadonsa ya turmusheta tana tureshi tana komai yaqi barinta sai rawar jiki yakeyi da ta murya Yana cewa “Mee.... Meenah.... please..... Long time banci ba wlh tunda nabarki banqaraci ba banqara sha'awar ciba sai da kika dawo rayuwata kibarni naci naji da...din...ki...."
Batada mafitar data wucce qyaleshin duk da tanajin fargaba koda yake tasan duk masifar Rasheed baikai Kareem ba saidai shi dabanne Yana bata nutsuwar da takeji a ranta Babu me bata kamarta sambatunsa kadai ya isa gamsar da mace me gajeran zango, Rasheed ya mayar da qwalamarsa a wannan yammaci anci amarcin gaske taji a jikinta koda komai ya kammala gumi ta rinqa hadawa ga ciwon jiki tare sukayi wanka yanata narke mata kunyarsa ma ta kamaji saboda ta fahimci shi baya da kunya ko kadan akan wannan abun.
Bayan sunyi wanka sukayi sallar magrib da ake binsu sukayi Isha sannan suka nufi dinning sukaci abinci yanata zubanta shagwaba itakam duk jikinta yayi sanyi ta dago idonta tace “amma Ya Rasheed ka fasa tafiyar ko?" Murmushinsa na Izza yayi mata yace “sai yanda ta yuwu"





Miqewa tayi ta shige dakinta ta haye gado ta zauna ta zuba uban tagumi itakam ta tsorata da wannan al'amari batajin zata iya yarda ya tafi ya barta idan ta tuna da hakanma hawayenta nunkuwa sukeyi ita da kanta takeji ashe zuciyarta tashice har yanzu ashe Baffa'am dinta bashida na biyu har gobe a duniyarta to meye yasa da ta farajin haushinsa?"
Jinjina kai tayi tana qissima ta yanda zata fara rayuwa cikin zulumi sai ta dauki wayarta kamar ta kira Kumbo Hami ta fada mata sai Kuma taga kamar bai dace ba haka ta rinqa saqawa da warwarewa har dare ya fara nisa ta shiga tayi wanka ta dawo ta kwanta abinka da farar fata idanunta har sun kumbura koda Jummai ta kawo mata Muneefah cewa tayi taje su kwanta tare ganin kwanciyar bazata kaita bane tasata tashi ta sake alwala ta dauki qur'ani tana karantawa tana hawaye.
Shigowa yayi dakin mamaki ya cikashi jin shassheqarta ya kunna globe din da sauri yaganta rungume da qur'ani tana rera kukanta ya qarasa gareta ya zare qur'anin ya aje ya dagota ya mannata da jikinsa yace “meye kikewa kuka Meenah kinsani ko a baya bana qaunar kuka ko?" Maqalqaleshi tayi tana qarawa kukanta gunji tace “ni don Allah kace ka fasa tafiya kabarni wlh zanyi maka duk abinda kakeso" dariya tabashi sosai ya shafa kanta yace “to na fasa saime Kuma?" Rungumeshi tayi tana ajiyar zuciya tace “shikenan idan sun matsa ka bar musu aikin kawai kaji?"




Daganta kai yayi ta shafa sumarsa tace “na gode Baffa'am...." Janta yayi suka zube a gado ya fara luguiguiceta ta saki masa jiki kuwa suka raya Daren da wata irin azababbiyar qauna me narkar da zuciya sun gurji juna sosai tanajin sabuwar qaunarsa na ratsata, tun daga wannan dare komansu ya fara saituwa cikin ruwan sanyi da dabara ya shawo kanta riritashi takeyi kamar qwai bata yarda ta tabashi saboda karma yaji yanason tafiya yabarta shima mugun tattalinta yakeyi Abu daya yaso Basu damuwa tanason zuwa Daura watanni sun fara nisa tanason taje taga Mom Amma fir yaqi tun tana lallabashi har Saida suka daina mgn ta daina kulashi da ya matsa mata sai ta kama kuka tace don yaga batada galibi ne batada uwa bata da uba shiyasa yakeson ya nuna mata Mom ba ita ta haifeta ba.
Sosai ya fahimci Meenah yar sharri ce ta qaro wulaqanci dole ya shiryanta tafiya Katsina aikuwa tayita murna shikuma yayita kumburi zuciyarsa na basa kawai so take taje taga uwar mijinta ta tuno da ubar yarta Kareem idan zuciya ta raya masa haka sai kawai yaji koma me zatayi tayi bazai barta ba ranar data shirya tafi tun asuba take shiri yayi kwanciyarsa yaqi fitowa harta shirya ta shirya Muneefah ta shiga dakin nasa da sallama ya Amsa mata a ciki ta zauna tace “Baby na shirya banga kana shiri ba Kuma kace kaine zaka kaimu airport" iska ya furzar yayi miqa yace “ina zakije ne?" Da sauri ta dubesa tace “Ban fahimta ba Daura Mana" hade rai yayi yace ba yau ba..." Ai baigama rufe bakinsa ba ta miqe tana cewa “haba don Allah Ya Rasheed kada kayimin haka wlh na fadawa su Mom dasu Ya'isha yau zanzo har Sarki junior fah na fadawa yanata murna hatta Amrah da Addah Abulle sunata murna zasuga Muneefah....." A fusace yace “shut-up Meenah nace bazakije ba yau ki fita ki bani guri dama nasan dokinki kije kiyi hirar tsohon mijinki kiji dadi ko? To bazaki ba idan kika matsamin ma wlh zan iya cewa keda Daura har abada muga ta tsiya"




Juhud is not free read... regular 300 VIP 600 via👉🏼 0255526235 Fauziyya Tasiu Umar GTbank



Then you show ur evidence via WhatsApp 09013718241...



Juhud ba littafin kyauta bane ki biya 300 regular VIP 600 kafin ki karanta ta wannan account din 0255526235 Fauziyya Tasiu Umar GTbank ko katin MTN pls ban buqatar vtu hoton katin ko digit number ta WhatsApp number 09013718241.....



*Oum Hairan*
[8/29, 8:00 PM] Oum Hairan: Tsayawa tayi ta zuba masa idanu tanajin ciwon yanda yake canzawa duk motsinta fassara hadiye wani abu tayi me daci ta juya ta fice daga dakin ta koma nata ta hade kai da gwiwa tanajin baqin cikin wannan wulaqancin na Rasheed Shi komansa baya aikatashi da lissafi kawai abinda yayi masa dadi shine yake aikatawa, kwanciya tayi tanajin Muneefah na buganta qofar taqi budewa tasan abinda zatayi masa kawai ta bata masa rai kenan.
Ilai kuwa yarinyar ta riqa kuka ya taso ya fito ya isheta a qofar dakin taqi bude mata ya dauketa ya juya ya shiga dakinsa yasa kayansa suka fice so take y kulata bakuma zai kulata dinba, tun tana tsammanin dawowarsu harta hqr ta tashi ta shiga kitchen ta dora musu abincin Rana sai daya da rabi ta gama tayi wanka tayi sallah ta dawo parlour Kiran Mom ya shigo kasa dagawa tayi saboda takaici meye ma zatace mata? Da wannan tayi qarfin halin daga wayar suka gaisa tace “munjiku shiru" kukan da take hadiyewa ne ya kwace mata tace “mom zamuzo Amma ba yau ba" tana fadin haka ta sauke wayar a kunnenta ta kwanta taci gaba da karatunta.
Sai biyu da rabi suka shigo da tarkacen kayan wasansu ya aje yarinyar ya zauna a gefenta daga kallo daya bata qara kallonsa ba ya sanya hannunsa ya dage rigarta da sigar zolaya yace “ 4 mouths kinqi karbar ajiyata sai zuba miki vitamin nakeyi kina shanyewa Babu wani good result" sake dauke kanta tayi daga gareshi tama fara yunqurin miqewa ya saqaleta ta baya ya miqe ya hadeta da jikinsa yace “meye kuma ya faru My Meenah Baffa'am dinki baison fushinki kin sani"





Tureshi tayi tace “ai dama nasan bakaso Baffa'am ka rabu dani please kada kasa na fada maka mgnr da ubangiji zaiyi fushi dani" qwacewa takeson yi yaqi sakinta saima qwalawa Jummai Kira da yayi yace ta dauki Muneefah, itadai kunya kamar ta nutse shikam Babu kunya ya dagata cak ya nufi cikin dakin baccinsa da ita ya cillata a gado ya bita ya hade bakinsu tana kuka tana tureshi yaqi turuwa saima zuge zip na rigarta da yayi ya cafki boobs dinta ta rintse idonta bataso yake taba mata nono kwana biyunnan zafi sukeyi mata gashi shi Kuma mayensu ne tanaji ya dora bakinsa a kuncinta yana tsotse hawayen har ya gangaro qasa ya sanya harshensa tsakiyar qirjinta Yana lasa zuwa kan nipples dinta, takasa qwatar kanta dole ta hqr tanajinsa yayita karakaina a sassan jikinta Yana bawa kansa nishadi taqi kulashi taqi tayashi sarai yasan yau dama tunda ya tabata itama saita tabashi shiyasa bai damu ba yayi abinda zaiyi ta kwanta masa kamar gawa ya gama ya sauka taja bargo ta rufe jikinta, waishi me zuciya ya rinqa jan tsaki tanajinsa tayi banza dashi yaje yayo wanka ya dawo ya dubeta yace “ki shirya jirgin biyar zamu bi zuwa Katsina"
Banza tayi masa tama sake gyara kwanciyarta ransa ya sosu sosai yace “wai meye yasa kika rainani mgn fah nakeyi miki Meenah" dagowa tayi ta watsansa wani matsiyacin kallo tace “bazani bane nakeso ka gane" murmushi yayi ya juya zai fice Saida yaje bakin qofa yace “ni nake baki umarni kike cewa bazakiyi ba ko Meenah lallai kin kawo qarfi saura qiris ki fara dukana" baiyi tunanin zatayi mgn ba yaji tace “idan iyakar dukan ma zan tsaya ai da sauqi"




Tsayawa yayi kamar zai dawo sai Kuma taga yayi gaba taja tsaki ta tashi tayi wanka ta koma ta kwanta har hudu da rabi Yana jiranta a parlourn baiji motsinta ba ganin lkc nata shudewa Babu ita yasashi nufar dakin a fusace ya isheta kwance abinta ya tsaya akanta Yana kallonta taji shigowarsa tayi masa banza takaici ya cikasa yace “kefa nake jira Tun dazu nayiwa Hadi mgn yanacan yana jiranmu" tabe baki tayi ta miqe tace “Allah ya tsare hanya ku gaishesu" zubanta ido yayi Yana qanqancesu cike da bala'i yace “kada ki fusata zuciyata ki tashi nace kafin ranki ya baci" murmushi tayi ta miqe tace “aini Raina ya dade da baci saidai naka ya baci zuwa ne bazani ba duk abinda zakayi kayi" duk yanda yake tunanin zata sauko taqi saurararsa ya rasa yanda zaiyi da ita baitaba tunanin kafiyarta takai hakanba ganin wankin hula na neman kaisu dare ya kira Kumbo Hami ya fada mata abinda yake faruwa ta Kira wayarta tanata yimata fada kan dole ta fito suka tafi har sukaje Babu me yiwa wani mgn.




Sosai kowa yayi mamakin zuwan nasu musamman Mom da ta gama fidda rai murna gurinsu baa cewa koma suna hutawa ana gama gaisawa ya dubeta yace su tafi gdansu shi ya gaji da dawo da safe, Babu yanda ta iya haka suka tafi Mom tanata Sanya musu albarka duk yanda Meenah taso ta gaisa da Addah Abulle hanata yayi sai Muneefah yabari anan a cewarsa ai itace dolensu.
Bata tankasa ba saboda ta lura sanadi yake nema suka Isa gdan batasan da ya ginashi ba ya qawatu sosai iyakar qawa anci uban naira s ginin gdan suna zuwa ta shige dakin da yayi mata ta kulle ita a dole har yanzu fushi takeyi shikuma gashi da baqin naci hakanan yabita suka kwana sunajin haushin juna dake yasan tun farko shine ya tabata bai wani damu ba da safe ma ya fice yabarta da sabuwar motar daya siya mata mahadin lefan da yayi mata na dawowarta yace idan ta gama abinda takeyi ta tafi shi akwai wani aiki daya bayar akeyi masa zaije ya gani.
Bayan ya fita ta gama abinda zatayi ta shirya ta fice can ta tarar da Amrah da Ya'isha suka baje sunata hirarsu sunata yimata tsiya waitayi qiba ta zama uwar mata sai shirga qiba takeyi saidai tayi murmushi kawai.




Rasheed bai shigo gdanba sai dare turakar Mai Martaba ya wucce suka taba hira har goma sannan ya shigo suka qara gaisawa da mutanen gdan Sarki junior ya maqale yace sai antafi dashi suka fice dole nan tabar tata motar ta shiga tasa da yaransu biyu suka tafi suna tafe yana satar kallonta Yana hira da yaransa wai ita fushi takeyi har yanzu, da sukaje ya budewa Sarki junior dakinsa rakashi yaron ya kwanta bacci ya daukeshi ita Kuma ta shige nata tayi wanka tayima Muneefah suka kwanta cikin bacci taji wayarta na ring ta wawura ta dauka yayi miqa tare da cewa “Ina buqatar tea" miqewa tayi tayima Muneefah addu'a ta nufi kitchen din ta hadansa tea ta nufi dakinsa ta bude Yana kwance bisa kujerar hutawa ta aje masa ta miqe ya riqota ta fada jikinsa ya matseta yana shaqar qamshinta me ratsa zuciya yace “ya kamata a daina fushin nan haka please na tuba" turo baki tayi yasa harshensa ya lashi lips dinta yace “kinsan cewa idan kina fushi kyaunki qaruwa yakeyi idan Kuma kikayi murmushi wane Sarauniyar kyau my Meenah inasonki saman sosai meye yasa muke yawan samun matsala ne?"




Kwantar da kanta tayi jikinsa tace “idan kana bari zuciyarka na rinjayarka kana fassarani inda ban nufa ba zankejin ciwo Ya Rasheed naqi samun nutsuwa naqi kwantar da hankalina na kasa zama lfy da Kareem saboda kai Saida takai ko mgn idan ba taka Ya Kareem zaiyimin ba banida lkcn hira dashi shi yasani ya zauna dani Kuma a haka a qarshe daka bayyana na dagansa hankali da taimakon mahaifiyarsa da bata qaunata dashi muka rabu badon yanaso ba, nasan Ya Kareem yanada yaqinin idan ya matsamin zan iya komawa hannunsa tunda bashi da haqqina Amma a hankali ya rinqa bina a qarshe ya fadamin ya barni ne saboda yasan kai nakeso bashi ba kuma bazan iya canza hakan ba saboda son ba shawara yayi ba wajen shigata, Ya Rasheed sai nake tuhumar kaina meye yasa kaidin Dana zaba Kuma ka kasa yarda dani kullum rigimarmu akan shudadden abune wanda yariga ya wucce har abada bazai dawo ba?"
Jikinsa ne yayi sanyi ya shafa dogon gashinta ya hura mata iska a fuskarta ta bude idanunta akansa ga mamakinta sai taga qwallah nabin kuncinsa tasa hannu ta share yaja numfashi yace “ina tsananin kishinki ne Meenah wato ubangiji yayi gaskiya daya zartar da wannan hukuncin tabbas da a gaban idona qaddarar rabon Muneefah yasa na rabu dake Kareem ya aura wlh tallahi zan kasheshi ne har lahira so sai Allah ya boye al'amarinsa shin waima kinsan cewa Hajiya Bilki tana gdan yari?"
.



Zaro ido tayi tace "Akan me?" Murmushi yayi yace “saboda ta cutar dani ashe duk abinda ya faru dani sa hannunta ne kawai don naqi auren yayanta Meenah ta rabani dake bayan ta rabani dake ta cillani duniya na tafi matsayin mara galibi bayan na bace Kuma rashinki ya sanya tunanina zama me rauni har takai na samu matsalar data zamemin tambari da bazai goge ba iyakar cewa da rubutawa cikin files dina na taba ciwon hauka da loosing memories kadai ya isa cutarwa balle rabanin da tayi dake"
Numfashi ya sauke yace kuma kinsan cewa yarta Khadija itace ta tona musu asiri wai taji suna qulla zasu farraqa tsakaninmu susa Mana tsanar juna shine tazo ta zayyanewa Mai Martaba komai shikuma baiyi wata² ba yasa aka kamesu yanzu haka shari'a zaa fara ranar Litinin" sosai lamarin
DOWNLOAD
DOWNLOAD

Please Login or Register in order to submit comment