Join Our WhatsApp Group

Idan ku ka ga kun taba wani wuri ya fitar daku a shafinmu, sai ku danna back kuyo baya, ku sani yanzu muna amfani da tallan Popunder a shafin, so karatu zai muku dan wahala, amma ta hakanne kadai zamu iya cigaba da rike shafinnan. idan har bakwa son talla sai kuje ku yi subscription na shafinnan akan karamin kudi ku runga downloading kawai. SUBSCRIBE


DOWNLOAD

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register
DOWNLOAD

ya zubo mata ba.




Tasbihi da taslimi yayima ubangiji Sarki daya me ikon zartar da komai a lkcn da yaso ya juya gareta ganin yanda take sharar hawaye duk sai ta Sanyaya masa jiki ya kama hannunta suka tafi suna zuwa gda ya dubeta idanunsa sun kada sunyi jawur yace “bakyaso ko?" Girgiza kai tayi da sauri tace “ba haka ban...." Katseta yayi da cewa to mene?" Kuka ta saka ta fada jikinsa tace “babu fah kawai Ina jinjina girma da buwayar ubangiji Ya Kareem meye kayimin da zanqi jininka" ajiyar zuciya ya sauke yajata suka zube ya share mata hawayen yace “ki daina kina sani a tunani kinji" dagansa kai tayi yace “me zakici?" Kallonsa tayi tace “azumin fah" kallon magungunan yayi yace “ok idan bazaki iyaba ki hqr Allah yayi muku uzuri fah
Dagansa kai tayi yini sukayi yanata tattalinta da riritata wannan ciki Yana ganin boni komai yagani ya rakito mata kayan baby kuwa abin har yazama hauka abinda ya bata mamaki Mom ce kadai tasan da cikin har yakai watanni biyar a lkcn ne Kuma wani baqon al'amari ya sakosu a gaba hakanan sai taga Kareem yayi tagumi ya tsunduma duniyar tunani idan ta tambayeshi dalili sai yace mata Babu komi Tasha zuwa ta tarar dashi Yana kuka a daki shi daya tambayar duniya sai yace mata Babu komi dole ta zubansa ido a dan ritsin ne Kuma ya kama rashin lfy sosai itadai Saida ta Kira Mai Martaba ta sanar dashi domin an bashi gado baisan waye akansa ba wani abin mamaki daya razana duniyarta ranar da Mai Martaba yazo tana tsaye jikin gadon da Kareem yake riqe da hannunsa tanayi masa addu'a taji sallamar Mai Martaba ta dago da sauri cak ta tsaya komanta ya tsaya hatta da numfashinta lkcn da tayi arba da wanda yake takewa Mai Martaba baya cikin bugawar zuciya tace “Baffa'am!" Kallonta yakeyi da alamun rashin fahimta ta nufesa da sauri tana cewa “Ya Allah Mai Martaba yaushe akaga Baffa'am dina Amma aka boyemin meye yasa akayimin haka ashe akwai abinda zaa iya boyemin game da Baffana....."




Tana mgnr tana nufarsa shikam ya saki baki ne Yana kallonta zuciyarsa na wani irin bugawa da mugun qarfi qara waro idanunsa yakeyi yanason ya ganeta ya kasa tana Shirin kai hannunta jikinsa taji yace da Mai Martaba “mai Martaba itan wacece?!" Ba itaba shi kansa Mai Martaba Saida tambayar ta dakeshi ya dubeta yaga tayi mutuwar tsaye hawaye nabin kuncinta bakinta yana rawa alama ta magana takeson yi ta kasa kama hannun Meenah Mai Martaba yayi yace “ki nutsu Meenah Rasheed fah ba qalau yakeba duk duniya Babu wanda yake ganewa" zubawa Mai Martaba ido tayi tace “meyesa aka boyemin bayyanarsa?" Murmushi Mai Martaba yayi yace “akwai hikima cikin hakan yanzun ma banso kikasan da bayyanarsa ba so dandai ya matsa ne saiya biyoni"
Zubewa tayi ta rushe da kuka tace “Allah na gde maka daka bayyanamin shi a raye Mai Martaba Amma ya gane Sarki junior ko?" Murmushi yayi yace “ni kaina da zan fita na dawo saiya tambayeki waye ni" zubawa Rasheed ido tayi da yake bin dakin da kallo yace “Mai Martaba shima wannan dakin bansanshi ba shikuma wannan da bashi da lfy waye?" Yana mgnr yanakai hannunsa ga Kareem dake kwance kamar gawa riqe hannunsa Mai Martaba yayi yace “bakasanshi ba?" Daga kai yayi yayi murmushi yace “wani qaninka ne Kareem ja tunasa?" Dafe kansa yayi kamar zai tuno ya dago yace “ok shine wannan wanda mukayi yaqin tare dashi aka sacemu tare aka kaimu Sudan kace sunan gurin ko?" Murmushi Mai Martaba yayi ya dubi Juhud data kwantar da kanta a jikin gadon tana kallon ikon Allah.




Likitan ne ya shigo suka gaisa da Mai Martaba suka fita suka barta ita da Rasheed abin yana tsuma jikinta da ruhinta wai gata ga Baffa'am dinta Amma baiko kallonta harkar gabansa kawai yakeyi ta miqe tanajan tsohon cikinta me watanni takwas ta matsa bayansa ta sassauta muryarta tace “Abdulrasheed" juyowa yayi ya zubanta ido tare da dibanta ya watsar hawaye ya sake tsiyayo mata tace “wai da gaske baka ganeni ba?" Daina latsa wayar yayi ya sunkuya ya ciro takalminsa duka biyun ya miqa mata yace “nasan sune sukayi miki kyau to gasunan na baki" noqewa tayi taqi karba tace “meyesa zaka mantani tsayin shekara shidda nakasa cireka a Raina na kasa karbar kowa bayan kai Rasheed ni ban cancanci ka mantani ba....."
Saurin ja baya tayi lkcn daya fara kwance tazugen wandonsa gabanta ya fadi tana kallonsa tanajin ninkin faduwar gaba gani tayi ya zare wandon ya kuma cire rigar ya rage dagashi sai singlet da boxes ya nufeta Yana murmushi yace “nifa kinganni banida rowa idan kinason wadannan dinma zan iya baki wlh Meenah ta tafimin duk abinda na mallaka a duniya Kuma kinsan Meenah ta mutu Ina zuwa kogin maliya zan fada ciki na tsunduma tsundum na mutu nima kowa ya huta yawwa ai kema kinsan zan hadu da Meenah acan ko?"
Tashin hankali Yana matsarta tana matsawa ya damqo hannunta ta rintse idonta ya damqa mata kayan yace “ki riqe nabaki sadaka idan kinason agogon ma da zoben duk na cire miki Ni dama na daina kwalliya takaba nakeyi Kuma bazan qarason wata mace ba a duniya tunda na rasa Meenah"




Girgiza masa kai takeyi tana kuka me gunji ya dora hannunsa a bakinsa yashe “dallah malama kiyi shiru Meenah batason kuka" gumtse bakinta tayi ya juya zai fita Mai Martaba ya budo qofar ya shigo yaja ya tsaya da sauri yace “ya subhanallah Rasheed meye hakan?" Murmushi yayi ya sosa sumarsa yace “ai harkai zan iya kyautarka indai akan Meenah ne" zaro ido Mai Martaba yayi yace “nidin Rasheed" dariya yayi harda riqe ciki yace “kaidin har wata daraja ce dakai ta musamman da zatasa naqi fansar dakai akan Meenah?"
Girgiza kai Mai Martaba yayi yace “naji banida ita Sanya kayan naka muje masauki" juyawa yayi ya kalli Juhud ya tsugunna yace “don Allah mamana kibani aro Allah niba barawo bane zan dawo miki dasu yau dinnan aidai bake kika sani ba nine nasa kaina nabaki kyautarsu ko?" Miqa masa tayi yace “aafah Hajiya in kinsan ba tsakani da Allah kika baniba bar kayanki"
Dauke qwallah Mai Martaba yayi yace “karbi tsakani da Allah tabaka" yasa hannu ya karba Yana sawa Yana waqarsa “Meenal Aso kin matar da zuciyata ta mace! ki tausaya karki sani bangare na yaudara!! Ina gudun duniya!!!"




Da wannan ya fice Mai Martaba ya dubeta yace “likitana ya tabbatar min da zai samu sauqi fah karki damu" ficewa sukayi suka barta da kallon Kareem dake kwance kamar gawa ta juya itama ta fice kamar mahaukaciya ta nufi block nasu ta fada gado domin tabawa zuciyarta hutu daga sabon tashin hankalin daya tunkarota ga Baffa'am dinta a gabanta Amma yakasa ganeta to waima meye asalin dalilin sukurkucewarsa ne haka Shiba Mai mgn ba Amma surutai rarrara kamar Wanda ya qone a qeya miqewa tayi tare da cewa “tabbas lkc yayi da zan sakawa Mafi cancanta Alkhairinsa....."
Tunaninta ne ya tsaya cak da tunawa da Kareem shikuma da yake cikin halin ni yasu dora hannu tayi akanta daidai lkcn da wayarta tayi ring ta wawurota Ya'isha tace “na dade inason tsegumta miki watanni biyu baya anga Big Cele a Tanzania to tsoron jagula wannan dofanannen auren naki da Ya Kareem yasa Mom ta Hanani fada miki wai Kuma yau sainaji me kankat ankawo mikishi har qasarku"
Cikin kuka tace “shine me gata ko rashin galihu yasa kukaki fadamin labari mafi soyuwa a duniyata Ya'isha ko ku fada ko karku fada Rana irin wannan zatazo gashi tazo Baffa'am ya dawo zamana da Kareem ya qare....." Da qaraji Ya'isha ta katseta da cewa bakida hankali ne karki soma wlh Kareem yafi kowa buqatar taimakonki kinaganin fa a halin da yake" jan zuciya tayi tace “meye ribata dama uwarsa ta rantse indai na haihu saiya sakeni to kafin ma na haihu zanbar mata gidan danta nima a dole nake zaune don halacci" magana Ya'isha keson yi mata ta kashe wayarta can Mom ta kirata tace “idan kin kwantar da hankalinki akwai labari me dadin dadi da nakeson baki"




Muryarta harta dashe tace “kun boyemin abinda na cancanci nasani Mom meyesa" murmushi tayi tace “saboda kada muyi mahaukata biyu a dangi shiyasa Meenah kifa nutsu motsi kadan zakiyi ki fada rami mijinki yafi kowa buqatarki to kibi sannu kada santsi ya debeki"haka Mom ta rinqa bata kalamai wai ita a dole saita kwantar mata da hankali batasan qara tashin hankalinta takeyi ba suna kashe wayar Dr Khazeem yazo ta dubeshi yace “ya naki jikin batason hayaniya hakan yasa tace “naji sauqi so ganin yanayinta yasashi ficewa ta koma ta kwanta kamar bazata koma asibitin ba saidai taji zucciyarta taqi natsuwa dole ta shirya ta nufi asibitin ga mamakinta saita isheshi a zaune shida Mai Martaba ta dubesu suka gaisa da Mai Martaba yace “kema kina buqatar hutu ya kamata ki koma gda ki haihu acan" jinjina kai Kareem yayi yace “dama inada burin hakan sai na kwanta jinyar nan" da wannan sukaci gaba da tattaunawarsu hankalin Kareem na kanta Mai Martaba yace “ki koma masaukinku ki huta zan kwana dashi muga abinda hali zaiyi".......



_Yau fah saidai hqr da qarancin page din_




Juhud is not free read... regular 300 VIP 600 via👉🏼 0255526235 Fauziyya Tasiu Umar GTbank



Then you show ur evidence via WhatsApp 09013718241...



Juhud ba littafin kyauta bane ki biya 300 regular VIP 600 kafin ki karanta ta wannan account din 0255526235 Fauziyya Tasiu Umar GTbank ko katin MTN pls ban buqatar vtu hoton katin ko digit number ta WhatsApp number 09013718241.....



*Oum Hairan*
[8/12, 8:08 PM] Oum Hairan: Duban juna Juhud da Kareem sukayi yayi mata qaramin murmushi ya shafa sajensa tare da nuna mata hanya yace kije ki huta heart kinyi qoqari fah na gde Allah yabada lada" sunkuyar da kanta tayi tare da daukar wayarta tayi musu Saida safe ta fice ta nufi masaukin nasu zuciyarta na kaikawo tsakanin qirjinta da duniyar Rasheed, tana zuwa wanka kawai tayi tayi sallah ta kwanta itakam wannan dare barawon ma kasa satarta yayi gabadaya ta rasa nutsuwarta batajin daidai saina tunanin Rasheed, da asuba tayi sallah ta zauna tanayima iyayenta da Rasheed addu'a tare da fatan sauqi da sassauci cikin wannan jarabawa da suka tsinci kansu a ciki ciwon tabuwar qwaqwalwa a Rasheed abin Babu kyau.
Data tashi da ciwon mara ta tashi hakan yasa bata koma asibitin da wuri ba Saida Tasha magani ta dan samu relief sannan ta fita ta nufi hospital din a qofar dakin da Kareem yake ta ishe Rasheed Yana tsaye yana danna waya kamar ance ya dago suka hada ido ya lumshe idanunsa qirjinsa Yana bugawa itama haka ta matsa gabansa tace “barka da sfy Baffa'am" ja tayi da baya lkcn daya kece da dariya yace “shegiya ashe kinsan sunana ai Meenah ce take kirana da wannan sunan" lumshe idonta tayi hawaye ya ciko ijiyarta ta bude akansa ta girgiza kai tare da cewa “ka manta kowa da komai ka manta kamannin Meenah a zahiri Amma baka manta sunanta ba Baffa'am ya akayi hakan?"




Yarfa hannu yayi yace “nima to nasani kawai dai kema kinsan idan na kama Wanda ya kashemin Meenah a gabana saina dirmeshi da alburushi ke barima kiji fah koda yake na daina kulaki Meenah kishine gareta batason a hadata da wata a mafarki Ina ganinta kullum Kuma fah tana dan kama dake kadan Amma bakikai kyaunta ba" Mai Martaba ne yajiyo mgnr ta Rasheed tayi yawa ya leqo yaga ashe shida Meenah ne tasashi a gaba sai hawaye takeyi ya qwala mata Kira tayi saurin goge hawayen tace “ok ganinan" ta juya zata tafi ya riqota yace “shifa Wannan mutumin dan raini ne ya rainani yama zaayi Ina mgn da mutum ka kirashi to kaima ka kiyayeni kafin na qundumeka" zaro ido sukayi dukkansu ya dora hannunsa a bakinsa yace “lalalah ashe fah sabo nakeyi kayyy ke haihuwa zakiyi me zaki Haifa?"
Ganin batada niyyar tahowa ne Mai Martaba ya fito yaja hannunta yace “idan kika biyewa wannan saiku raba Rana da dare yanayi miki soki burutsunsa" sosai sautin kukanta yake fita batare da tasan kalmar ta subuce ba tace “ta Ina zan fara taimakonsa?"
Dubanta Kareem yayi ya kawar dakai yanajin wani abu nayi masa yawo a qirji da sauri ta share zancen da cewa “Mai Martaba ya jikin nasa?" A gajarce yace da sauqi sosai dama lkcn hutunsa yayi zamu tafi gabadaya daku saboda dukkanku kuna buqatar kulawa" jinjina kai tayi tabbas tana buqatar kulawa sosai Kuma taji dadin hakan domin itace damarta ta fuzgo yancinta zuciyarta na raya mata dolene Kuma wajibi akanta ta qwaci kanta domin Baffa'am dinta.





Kwanaki biyu suka qara a asibitin aka sallamesu cikin kwanakin ta fahimci abubuwa da yawa game da Baffa'am dinta hakanan wani lkcn sai yayi shiru yaqi yima kowa mgn ya rinqa kallon kowa daidai idan Mai Martaba ya cika damunsa saiya tashi kawai yakoma jikin tagar dakin yana hango waje yana cewa “kawai don anga Aminatuh batada gata sai a takurawa mijinta nifa idan kunsan takurawa na Meenah nazakuyi to kubarni ko da qafa zan koma Tanzania harda Sudan naje naci gaba da gadin kabarin Meenah ta"
Zantukan nasa a sukurkutacce suke ba kowa ke fahimtarsa ba Amma ita tana gane wani abu cikin maganganunsa ta fahimci kamar akwai hoton abinda yake masa yawo a kwanya da yake bashi gizon mutuwarta tunda dukkan wata kalma tasa mutuwa yake cewa Meenansa tayi to ya akayi haka?" Abin da yafi komai bata al'ajabi ita daya yafi yiwa wannan soki burutsun zantukan nasa marasa kan gado inda ta fahimci Kareem ko kadan bayason yaga Rasheed ya fiye mata mgn shi kansa Mai martaba yana nuna alamun hakan wannan take sanyata cikin jimami domin da tazo asibitin kafin sallamarsu zai tareta da cewa yawwa qawata zo na baki lbrn Meenah a duk sanda ya fadi haka sai takanga fuskar Kareem tayi duhu inda ita Kuma takan shiga tunani da zullumin wannan lamari.
Kwana uku suka qara komansu ya kammala suka dauki hanyar 9ja ko a cikin jirgin da Rasheed ya fara mata mgn sai Mai Martaba ya katseshi da cewa kai wai meye yake damunka ne Rasheed shikuma gashi ko yayi shiru baa minti biyar zai sake zungurota yace mata “yawwa qawata akai kaza akai kaza" haka Mai martaba zai sake mata tsawa itadai ta kasa jurewa ganinta wannan ai takura dan adam ne Kuma ma meye don ya zabeta matsayin abokiyar hirarsa aikuwa tayi kicin kicin da fuska ta juya gabadaya gareshi ta kamo hannunsa tace “labarin me kakeso ka bani Baffa'am?" Dago kansa yayi da yasa cikin cinyarsa ya dubi Mai Martaba da Kareem yace “ai dama batun yanzu ba na fahimci wadannan Gayun basasona da qawance dake Kuma na daina kulasu"




Murmushi tayi tace “to Kuma meye na kukan aini Inasonka da qawancen...." Ihu yayi yace “don Allah da gaske?" Daga masa kai tayi yace “wayyoh dadi zan baki alawar madarar dana siyawa Meenah zankai mata lahira idan munje gda" murmushi tayi me hade da hawaye tace “Baffa'am ai wanda ya mutu baici baisha baya mgn fah" hannunsa yayi a baki yace “dallah ware sunguma malohuwa ita Meenah an fada miki irin mutuwar kowa tayi ne ai ita kullum tare muke kwana da asuba saita bace bana qara ganinta sai wani daren Kuma in fada miki kullum cemin takeyi Inasonka Baffa'am dina bazan taba rayuwar farin ciki ba tare dakai ba kaji a ranka ko bana duniyarka to Ina fadar zuciyarka daka bani nini kadai....."ba itaba dukkansu Saida suka kalleshi sak muryar Juhud yayi amfani da ita wajen furucin tayi dariya sosai tace “Kana bani nishadi....."
Wata tsawa Kareem ya daka mata yace “yaci gaba da baki nishadi zan datse duk wata alaqa dake tsakaninku kuwa muga qaryar baki nishadi" dama a qufule take dashi da Mai Martaba ta kuwa hayayyaqo masa tace “zaka iya Kuma? Kanajin kanada qumaji da qwarin gwiwar raba hanta da jini ne? To karka soma shidin bangare ne na rayuwata da bashida tamka wlh a duniyata yafi iyayena domin na rasasu tun bansan dadinsu ba shine ya mayemin gurbinsu ya zamemin uwa uba Yaya qani aboki qawa sannan ya........" Dauketa da mari taji anyi ta dafe gurin da sauri kafin ta kanta ya gama juyawa taji qarar wani Marin ta bude idanunta da sauri taga Kareem dafe da kunci Mai Martaba a tsakiyarsu Rasheed sai huci yakeyi yana hanqoro so yake ya samu dama ya damqi Kareem Mai Martaba ya hanashi yace “kasheka zanyi in kashe banza wlh don akan qawata Babu ruwana dakai qanina ne inma yayana ne saina aikaka inda na aika Wanda ya kashemin Meenah"




Zama Kareem yayi Yana huci Yana cije lebe shima Rasheed ya zauna yace “saqagon banza dashi dabai iya komai ba sai cin zali" shidai bai kulashi ba don ya fahimci idan yaci gaba da kulashi mahaukata biyu zaayi Amma yaci alwashin ta qarfin tsiya saiya raba Meenah dashi suna sauka a Kano Lado driver yazo ya daukesu suka nufi Katsina Mai Martaba motarsa daban shida Rasheed shikuma shida Meenah ko a tafiyar babu me cewa wani qala har suka isa Katsinan a yanda Mai Martaba ya tsara dole haka sukabi gdan sarautar suka nufa anan yace su zauna harta haihu.
Yana qunci da cin magani suka shiga cikin gdan kai tsaye ya figi hannunta suka shige part din nasa ya kulle qofar ya saki hannunta Yana huci ta juya ta nufi kujera ta zauna ko kallonsa batayi ba ya gama kumburinsa ya nufi dakin baccinsa ta tabe baki a ranta tace “ka kuwa hadu da aiki" batabi ta kansa ba itama ta shige dayan bangaren tayi wanka ta bude Jakarta ta dauki doguwar riga ta sanya tasa mayafinta ta sulale tabar part din ta nufi cikin gdan ta matsu taga Mom tana shiga falon Mom ta taso da gudu ta tareta da cewa “oyoyo oyoyo Aminah ta" dariya tayi suka zube a kujera tace “ashe kema kinyi kewata Mom Ina Sarki" juyawa tayi inda suke zaune shida babansa tace “au shine bazaka kulani ba" dariya yayi ya taso ya fado jikinta yace “kin tafi kin barni inata kewanki Dad dina ya dawo inaso kizo ki ganshi kullum na saci wayan Mom na kiraki sai najita a kashe"




Murmushi tayi me hade da hawaye tace “Allah Sarki My Son kana Raina ya kakeji game da dawowar Dad dinka?" Kwantar dakai yayi jikinta yace “happy Mom kinsan me Dad dina fah bashida lfy baya gane kowa harni" share masa hawayensa tayi tace “ka daina damuwa zai ganeka zansa ya ganeka kaji" daganta kai yayi Rasheed dake zaune yace “kuma itace qawata da nake baki lbr Mom Kinga ashema tasanku tasan wannan yaron da yaketa cemin Dad" tare suka share hawaye da Mom Mom tace “hakanma mun gode Allah Meenah wai a hakan fah an samu sauqi farkon lkcn da aka tsintoshi abin baa cewa komai sai gdyr Allah Amma yanzu yaji dama"
Jinjina kai tayi ya taso ya dawo kusa da ita tayi saurin sanya Sarki a tsakiyarsu yace “dariya ma kike bani" dukkansu sukayi dariya Daidai lkcn da Addah Abulle ta fito daga sashin Mai Martaba idanunta akan Meenah sukayi kallon kallo taja baya da sauri tace “na shiga uku ni Zainabu wato shegen yaron nan da yace sun zubar da cikinga ashe qarya yakeyi" murmushi Meenah tayi zuwa yanzu zuciyarta ta fara tsikewa tace “sannu fah Addah ya gda mun sameku lfy?" Wata uwar qwafa tayi ta nufi dakinta fuuuuu Meenah ta tabe baki ta mayar da hankalinta ga Mom sukaci gaba da hirarsu tanata dariya abinta shirmen da Rasheed yake buga musu ko Sarki bazaiyi ba suna haka Fadila ta fito ta debesu ta watsar Meenah tayi murmushi tace “Allah Sarki wannan fah Mom?" Girgiza kai tayi tace “au Fadila auren ne yaqi dadi mijin neman mata har ksn gadonsu na sunnah shine tayo yaji ya aiko mata da takarda saki daya" dafe qirji tayi tace “ya salam Abin tausayi Allah ya daidaitasu" murmushi Mom tayi tace “kayyah dai itama Amrah jiya ta koma aure mijin ya qara shine zatayi masa haukanta ya korota uwar mijin tace ita dama batason wannan auren daidai ya nace ne daqyar dai aka sasanta ta koma kayy Meenah munga jarabawa dan ritsin nan " jinjina kai tayi tace Allah yasa ta zamo kaffara amsawa tayi da Amin sunata hirarsu ta yaushe gamo Kareem ya shigo suka gaisa da Mom ya dubi Juhud yace “bansan kin fito ba fah Saida na leqa dakinki naga bakinan" murmushi tayi tace “nazo mu gaisa dasu Mom ne"




Miqewa yayi ya nufi part din uwarsa yace “ok ku gaisa sosai Amma ki nemamin abinci yau girkinki nakeson ci....." Rasheed dake tura motar wasan yara shida Sarki ya dago yace “lahhh zaka sammin?" Tsayawa Kareem yayi ya juyo ya dubeshi da tausayawa yace “in kanaso ma kullum ka rinqa zuwa kana karba Aminah ta iya girki sosai" tsalle yayi ya dafesa yace “itama sunanta Meenah nima tawa Meenan ta iya girki nifa tunda Meenah ta mutu ban qara cin abinci me dadin nata ba"
Tsayawa yayi kamar zai juyo sai Kuma yasakai ya shige ciki sama² suka rinqa jiyo hargowar Addah Abulle basajin dai abinda suke cewa Meenah ta miqe tace “bari na koma Mom duhun magrib ya fara shiga saida safe" ta juya ga Rasheed daya zuba mata ido tace “Baffa'am Saida safe" daga mata hannu yayi yace “zanzo na karbi abincin naki ai" murmushi tayi ta juya ta fice ta nufi sashinta taji an bangajeta taja baya da sauri tare da cewa A'uzubillahi....." Tana duban Wanda ya bangajeta din Fadila ce qanwar mijinta tayi murmushi kawai ta juya taci gaba da tafiyarta a bayanta taji tana cewa “gayyar na ayyah gayyar tsiya an dawo zaaci gaba da dorawa uwarmu ciwon zuciya jarababbiya qalatacciya da wani shegen cikinki a gaba irin masifa irin maita......"
Kalamin sun daketa ta cije lebe tare da tsayawa batare data juyo ba tace “hakane saidai kin manta abu daya bani na liqe mawa dan'uwanku ma shine qalatacce jarababben daya liqemin wlh da zaku bashi shawarar ya rabu dani ma ya dauka da dadi nikaji domin zan yar da qwallon mangwaro na huta da qudaje"




Tana fadin haka ta shige tabar Fadila sake da baki lallai yarinyar ta riqa wato sune qudaje Kareem ne mangwaro tab yau da tashin hankali a gdannan, fuuuu ta shige ciki ta nufi sashin uwar tasu tana shiga ta fara karanta mata qarya da gaskiya aikuwa ta hau ta zauna ta dauki waya ta Kira Dada Hanne ta zayyane mata abinda ke faruwa Dada Hanne tace “ai Ni wannan jaraba na rasa dame tayi kama yarinya ta zamewa mutane qarfen qafa an kasa kwanceta a yar shima Mahfuz din kwanaki kamar abin arziqi aikin da mukayi ya fara cinsa yanzu Kuma yaqi kullum abubuwa lalacewa sukeyi"
Takaici ya cika zuciyar Addah Abulle tace “ni takaicina ma cikin nan da yake jikinta ashe bai fadaman lissafin daidai ba boyemin yayi yanzu kawai Ina ganinta naganta da tsohon ciki haihuwa kusa" wata uwar ashar Dada Hanne ta qunduma tace “au ke yanzu kina zaune sakarai kika bari tayi ciki kema zaa jorner miki tsiyar?" Da muryar takaici tace “to ya zanyi kefa kika sani na rinqa rabar da kudi tsakanin gurin malamanki dana Hajiya Bilki nidai banga wata nasara ba saita dawowa ta gdannan"
Qwafa Dada Hanne tayi tace “ai shegiyar gantalalliyar yarinyar ce masifar taurin kaine da ita bansan wanne irin shiri ne a jikinta ba Amma bari intasan wata batasan wata ba" sun jima suna saqarsu a mugun zare sannan sukayi sallama da shirinsu na cimma matsaya.
Meenah kam tana shiga part dinta idanunta ya sauka qasan tiles din taga wani garin magani duk an barbadar dashi kiyayewar Allah ce kawai tasa taga maganin saboda shima arsh ne kalar tiles din, taja baya da sauri tana a'uziyya a fili ta fara dube dube bataga Wanda zata Kira ba ta koma gefe ta tsaya tsam jikinta na tsuma tsoro ya cikata tana nan tsaye Allah ya jefo mata Kareem taja ajiyar zuciya, qarasowa yayi da sauri yace “meye kikeyi anan Kuma?"
DOWNLOAD
DOWNLOAD

Please Login or Register in order to submit comment