Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

shekarunsu suka kai ne aka daura masu aure Lariya itace matar da aka bawa Rubado shikuma Haro aka aura masa ni nima kamar yanda aka dauko Aminatu daga Senegal haka nima aka daukoni aka kawoni jumme ce tayi murna da zuwana ita da Suwai sune suka karbenu hannu biyu surukarmu kam ko kallo ban isheta ba mijina kuma dan'uwana dan qanwar mahaifina Haro ya qaunace ya nunamin kulawa dayake dama ba qarama sosai aka kawoni banyi wannan bambadancin da amare sukeyi ba muka zauna lafiya da mijina a hakanne Jumme ta Haihu haihuwar farko ta haifi Abdullahi wanda kuke kira da Hammah Audi shekaru biyu kuma Asubi ta haifi Rubado basa jana nima bana shiga cikinsu daga asubi har lariya Jumme ce kawai muke mutunci matuqa ana haka na samu cikina na farko nasha wahala sosai da yakai haihuwa Na haifi namiji Umaru ya fara girma sosai yakai kusan shekara uku ya kama qyanda wannan qyanda bata barshi ba saida ta tafi dashi munji mutuwar yaron sosai, bayan rasuwarsa ne harin barayin shanu ya addabi Lardin Wandu babu shiri Moddibo ya debo halwarsa muka dungumo Niger daga niger muka tsallako Nigeria muka samu matsugunni a Wannan guri da ya zama sabuwar Wandunmu"





Bamu jima da dawowa ba ciwon Ajali ya kama Moddibo ansha jinya sosai a lkcn da ajalinsa ya rigaya ne yasa aka kira masa yayansa yayi musu nasiha akan zumunci sannan ne ya ware wani kaso me yawa a cikin shanunsa yace wadannan na gadon mahaifiyarsa ne Aminatu daya rinqa kula masa dasu sune sukayi yawa haka, nanfah Bangel da Rubado suka kalli juna sukayi qwafa suka tashi suka fice daga dakin bayan fitarsu ne yake sanar dashi cewa akwai wasu shanun da ya bayar aka tafi dasu kudu kiwo da Buba da Haro ne sukaci gaba da jinyar mahaifinsu har kwana ya qare ya tafi yabar baya da qura qurar da itane kema kikazo kika tadda burbushinta.
Maitar da suke iqirari ta fara ne daga lkcn da nake haihuwa yarana suna mutuwa Asubi ce ta fara cewa wai ni nake cinye kayana saida na haifi yara takwas duk suna mutuwa sannan ne Allah ya bamu ke kika tsaya wai ashe duk yaran dana rinqa haifa maza suna mutuwa Ubayenku ne suka sanya hannu kawai saboda tunanin idan Haro ya mutu yanada da Namiji bazasu samu komai ba kedin ma sunso hallakaki Allah yaqi basu dama kika rayu da tsangwamarsu saboda kyawun da ubangiji yayi miki tun kina qanqanuwa dumurmur dake kamar kazar gidan gona saurin girmanki yafi komai bawa mutane mamaki Hasiya da Adama da Baraka duk sa'anninki ne amma duk kinfisu girma ko tallan nono muka tafi kafin akulasu an kulaki sau dari wannan tasa uwayensu sukejin hasaadar hakan akwai wani furuci da Gwaggo Lami tayi kafin mutuwarta watarana mun dawo daga tallen Nono wani Alhajin birni yabaki kyautar Yar dolin wasa (yar tsana) kinzo gda kuka fara fada da yan uwanki akanta har kika fasawa Baraka baki, ina daki ta kamaki ta zaneki sannan tace indai su baraka jininta ne to saita lalataki sai kinyi abin kunya a rayuwarki ko tana raye ko bata raye, badai kyaune yasa kowa yake nannan dake ba to kyawun saiya zame miki fitinar da zata addabi rayuwarki.............




*THIS BOOK IS NOT FREE... REGULAR GROUP 300 VIP 600 VIA BANK ACCOUNT 0255526235 FAUZIYYA TASIU UMAR GTBANK OR CARD FOR THIS NUMBER 09013718241 ONLY WHATSAPP OR VTU ONLY FOR DIS 09031307566*




*Shares Please*





*Oum Hairan*
[7/12, 9:44 PM] Oum Hairan: *JUHUD*




*(OUM HAIRAN)*



*( Pure love sex nd romantic)*




*FP THREE*



*SUBSCRIBE*
_DUNIYAR LITTAFAN HAUSA TV_

https://www.youtube.com/channel/UCcAjVQ74qod9_dL0e_AqkiQ





*TUNATARWA*
Kowa yakanyi maka jaje a lkcn da wani abunqi ya same idan abin farin ciki ya sameka qalilanne sukeyi maka dariya har zuci, kada kasa dariyar mutane a ranka harta rudeka kaji cewa kowa sonka yake masoyin gaskiya shine wanda yake tare dakai a kowanne irin yanayi farin ciki ko akasinsa.🤏🏼




*CIGABA*
Inajin ciwon abinda Gwaggo Lami take fada akanki amma ban isa nayi magana ba abu daya na sani shine inayi miki addu'a ki kasance ya ta gari abar Alfaharin iyaye, kwanci tashi girma ya fara zuwar miki komanki abin mamaki ne gabbanki sunada saurin nuna girma hakan yasa tun kina qarama na sabar miki da saka hijjab irin na kanawa, sosai kike ganin tsangwama qyama cikin Yan'uwanki Hasiya Adama da Baraka Amma baki damuwa kodan kin taso kinganmu a cikin wannan qangin ne oho.
Wata rana Naje tallan Nono birni na dawo na tarar dake kina kuka na shige daki kika biyoni nake tambayarki meye yake faruwa sai kike fadamin Asubi ce ta bugeki saboda kunyi fada da Baraka tace miki kilakin birni kin bugeta hakanan na hqr bance komai ba ashe mgnr nan har gurin iyayenku maza taje da dare Baffanki yazo yake tuhuma ta wai waye yake zuwa yake siyan nono a gurina a sulluwa (mota) daga birni?"




Dagowa nayi na dubesa nace yaron Alh Idi ne da ka hadamu dashi a kasuwa yake zuwa karbar masa nono" numfashi Baffanki ya sauke ya kira sunana na amsa yace “shin Indo kinasa ido akan Aminatu kuwa?" Sake ware injin idona nayi akansa nace “Wai mekake tunanine Haro nikam bangane inda zantukanka suka dosa ba" sake gyara zamansa yayi ya dafe kansa yace “dazu na dawo daga kiwo na Ishe Ribado da Bangel suna tattaunawa naqarasa domin mu gaisa shine suke cemin wai dazun sunga wani me Sulluwa yazo ya dauki Aminatu a mota sunyi hanyar birni" dafe qirji nayi cikin kidima da gigita nace “aa Haro wlh zancene Juhud yau babu inda taje tallanma nice na fita saboda tacemin batajin dadi" jinjina kai yayi yace “shikenan adai qara kulawa" ashe wasan baa fara ba.




Tun daga wannan lkcn suka dora mamu qahon zuqa babu dama mutum yazo siyan nono gurinmu sai suce iskanci yazo ba keba nima a haka nake a gurinsu duk da cewa Baffanki baya bawa abin muhimmanci, tsaka da haka Hammanku Manga ya dawo daga neman kudi yaganki ya nuna yana sonki da murna baffanku yazo min da mgnr domin a lkcn duk anyiwa su baraka aure saura ke kadai kin rasa ko matayi a rugarmu dama maqota saboda sharrin maitar da suka liqa mana.
Duk da zuciyata bataso ba amma banja ba saboda bansan raayinki ba hakanan baffanki ya nemoki ya tambayeki game da Manga domin shi yace ma kun gama daidaitawa nan kikayi tsalle kikace bakiso naso na matsanki ki karbeshi amma sai baffanki yace tunda bakiso babu meyi miki dole ko bayan ransa hakanan naja bakina na tsuke babu kunya yaje yace da yan'uwansa kince bakison Manga nan suka qara sanya masa tsura ashe dama asali ba manga ne yace yanasonki ba sune suka kitsa masa ya aureki sai susan yanda zasuyi su hallaka babanki su kwashe dukiyarki,
Abu kamar wasa gaba me tsanani ta shiga tsakaninsu ko gaisawa basayi watarana da dare har mun kwanta Bangel yazo yayi sallama da Baffanki ya tashi ya fita bansan me suka tattauna ba nidai naga ya dawo yana huci na tambayesa yake cemin Aishatu don Allah ko bayan raina karki yarda ban aminta Aminatu ta auri Manga ba na haramta hakan idan har hakan ta faru bazanyi farin ciki ba" jikina yayi sanyi ya kwanta ranar kwana yayi yana juyi yana hawaye idan na tambayeshi sai yacemin shidai bai aminta Aminatu ta Auri Manga ba a lkcn inata fama da rashin lfy mukaje gun me magani yace cikine dani amma ya kwanta.




Ban wani damu ba duk da cewa Baffanki kullum cikin kawomin magani yake hakan baisa cikin nan ya tashi ba wata biyu tsakani sukayi wani gagarumin rikici daya sanya suka qara kullatar juna ashe a wannan dare sukayi taro suka yanke shawarar tunda yaqi basu hadin kai kawai su kasheshi su huta mana inyaso sai manga ya kada shanun yayi kudu dasu kinga zaace barayin shanh ne suka kasheshi.
Maddibo Buba ne yaji wannan shirin nasu a daren kuwa ya kira Haro ya sanar dashi abinda yan'uwansa suke shiryawa yaja fasali tare da murmushi yace “babu komai Allah yafi kowa sanin abindake qarqashin qasa dana ban qasa yafi kowa sanin daidai" daya dawo bai sanar dani ba nidai naga ya tashi cikin dare ya dauko wata qaramar adaka ya bude ya zaro wasu abubuwa masu walwali yabani yacemin Aishatu wannan abin da kike gani ba komai bane face dutsen Lu'ulu'u wanda yan birni suke cewa diamond wannan kuma gwal ne nasan kinsanshi don Allah ki nemi guri kiyi musu mugun boyo asalinsu na Mahaifiyata ne Aminatu naketa ajiyarsu domin Aminatu kada kibari wani yasan dasu a hannunki sunfi shanun can da kike gani garke guda daraja domin kuwa yanzu a duniyar mutanenmu wane da wane ma ba kowane yake iya mallakar diamond ba koda bayan raina zasu qwace komai ya kasance Aminatu ta tsira da wadannan abubuwan"





Na dade ina tunani kafin na tashi na haqa rami a qarqashin gadona na zubasu a ciki insha Allahu a yau zan baki abinki ki daura a qugunki su zame miki jigida iya wuya kada ki bari su kubce miki kinji" jinjina kai tayi Innatu taci gaba da cewa “washegari da safe na damawa Baffanki fura yasha ya kada shanu ya tafi kiwo nikuma na dauki nono na shiga gari acan suka cim masa da rana lkcn kin tafi kaimasa hura suka sareshi akansa da qirjinsa ya fadi jini nata malala kince kinga shanunsa lkcn da aka kadasu akayi hayi dasu amma bakiga wanda ya kada dinba kina binsu har kika ishe inda Gawar mahaifinki take yashe a qasa kece kika dawo kika fadawa Maddibo cewa an sari Baffanki kuka dunguma kuka koma nidai bayan na dawo na ishe wannan mugun labari shine tunda na yanke jiki na fadi bantashi ba nake zaune a wannan halin tsayin shekara biyu kwatsam sai cikina ya fara motsi nasa kika kiramin Jumme na sanar da ita dake tasan da batun kwanciyar cikin ta sanarwa da Maddibo Shi kadai yayi murna ya rinqa karbomin magani ashe a gefe Bangel da Rubado zargina sukeyi da Buba wai yana shigowa dakina ya dade hakanan sukaje suka kitsawa Jumme tazo har dakin nan tayimin tatas ina zaune babu halin magana a cewarsu ma wai wannan cikin na jikina ba na Haro bane na Buba ne Juhud Allah daya tsakanina da buba daga sannu sai idan ya kawomin magani ko nonon da zaki fita dashi talle.




A haka muke rayuwa har kawo yanzu da komai ya qara lalacewa Juhud kullum mutanen nan basu fadin alkhairi garemu kullum cikin yi mana kalen sharri suke yanzu haka kwanaki uku da suka wucce Jafaru makiyayi ya dawo daga kudu ya kawo shanaye guda dari da ashirin yace na Baffanki ne to tun jiya sukebin kaina akan na yarda a daura aurenki da Manga nikuma gashi Baffanki yabarmin wasicin ko bayan ransa bai aminta a hadaki aure da Manga ba a yau bayan kin fita diban ruwa har barazana sukayi min da rayuwata Juhud bandamu ba indai akan burin Haro ne su kashenin ma kansu sukayiwa.



*ASALIN LABARI*


Jikin Juhud ne ya qara sanyi hawaye na sunturi a kucinta tace “yanzun wadannan sune kadai dalilan da suka sanya Suka kashemin Baffina Amma aka kasa daukar mataki akansu Innatu wannan wacce irin Al'umma muke ciki meson kanta? Shafa nadaddiyar sumarta tayi itama cikin hawaye tace “haka rayuwa ta zama kina gani fah tunda Baffanki ya rasu ko nono sun hanamu tatsa saidai su tatse subawa matansu suje su siyar idan kinga mun samu nono a rugarnan to Moddibo ne ya tatso mana Juhud ya zakayi ne da qaddararka ni yanzu burina a duniya naga kinyi aure kin samu matsugunni saboda wannan rayuwar bata yuwuwa a haka"
Fadawa tayi jikin Innatu tana kuka me cin zuciya itakam da Innatu zata amince da sun bar rugar nan tunda baa sonsu amma tasan bazata aminta ba, da wannan tunanin bacci barawo ya saceta.




Washegari da wuri ta dauki tallan nononta ta tafi tasha cike da doki yau tayi niyyar idan tayo ciniki har Balangu zata sawowa innatu ko tsiren quli tana tafe tana yan waqoqinta harta isa gari koda taje yan nonon gurin ya cika batada guri dole ta koma gefe ta rakuye tana wasanninta na quruciya dagowar da zatayi taga wani baqin hadari ya gangamo tana juyawa taga Fulanin duk suna hade karensu gashu batayi cinikin kirki ba donma ta datsa yariman ne ta dibarwa wani na dari biyu shiyasa da haka zata koma.
Ganin hadarin na gangamowa yasata miqewa jikinta a salube tana juya dari biyun ta gama kasaftata tasai mawa Innatu maganin ciwon jikin hamsin tasai mata balangun dari ta riqe hamsin a hannunta ko batirin fitila sa siya, daukar qoranta tayi ta aza aka ta juya kenan zata tafi taji wata mota tayi horn a bayanta ta juya taga me motar ya zuge glass wani matashin saurayi ne me qwarjinin gaske fuskarsa a daure ya bude bakinsa kamar wanda akayiwa dole yace “na nawa ne?" Cikin fullanci yayi mgnr tayi saurin Amsawa da cewa na dubu Uku ba dari biyu" dubanta yayi yace “harke?" Kallonss tayi da rashin fahimta ya daganta gira yace “inaso ki juyemin da sauri" daidai lkcn taji gabanta ya yanke yabads wani dam ta dafe qirji da sauri tana waige² yace “ko bakiji ne?" Da qaraji yayi mgnr taja numfashi ta miqa masa har qoran tace banida ledar da zata dauka duka kaje da qoran ka dawo mani dasu wataran" karba yayi yasa a bayan motar ya zaro dubu biyar ya bata yace “gashinan har kudin qoranki bana shigowa garinnan sai idan wani babban uzuri ya taso" karba tayi tayi godiya ta juya da sauri ga mamakinsa kawai yaga ta take a guje ya saki baki yana kallonta a fili yace “lkc guda nutsuwarta ta gushe ko meye yaja hakan?" Tabe baki yayi ya daki kansa yace “kaima Cornel Rasheed da shiga abinda babu ruwanka kake" cikin kasuwar ya shiga yayi siyyayarsa ya juya da motarsa yabi wata siririyar hanya.




Itakuwa koda ta kwasa a guje duk nisa dake tsakaninta da rugarsu haka ra rinqa cin gudu harta fara hango rugar tasu nesa sosai gabanta ya qara yankewa ya fadi ganin wani baqin hayaqi yana tashi ta sashin da bukkarsu take, da sassarfa ta nufi gurin kawai taji an wafci hanunta da qarfi dagowar da zatayi taga Moddibo Buba ne idanunsa sharkaf da hawaye yana janta yana kallon bukkar tasu dakeci da wuta,
Da qarfin gaske ta turje cikin fitar hayyaci tace “Innatuuuu!" Saurin rufe mata baki yayi yaci gaba da janta bai qyaleta ba saida yabar sashin rugar da ita ya tsaya jikin wata itaciya yana sharce hawaye ya dubeta yace “Haka Allah yake ikonsa Aminatu a wannan qarnin babu wani abu dazan iyayi miki face na saki a hanya kibar yankin nan gabadaya Su Bangel basu da Imani Ina zargin sune suka sanyawa dakin Indo wuta suka qoneta ina daji Audi yaje yake fadamin har yana cemin yanzu Hakama Ribadu da Manga sunacan suna nemanki kema sunason kasheki ne tunda uwayenki sunqi amincewa su bawa Manga Aurenki harma suna masa sharrin zai lalataki............




*THIS BOOK IS NOT FREE... REGULAR GROUP 300 VIP 600 VIA BANK ACCOUNT 0255526235 FAUZIYYA TASIU UMAR GTBANK OR CARD FOR THIS NUMBER 09013718241 ONLY WHATSAPP OR VTU ONLY FOR DIS 09031307566*




*Shares Please*





*Oum Hairan*
[7/12, 9:44 PM] Oum Hairan: *JUHUD*




*(OUM HAIRAN)*



*( Pure love sex nd romantic)*




*FREE PAGE FOUR 4*




*SUBSCRIBE*
_DUNIYAR LITTAFAN HAUSA TV_

https://www.youtube.com/channel/UCcAjVQ74qod9_dL0e_AqkiQ




*TUNATARWA*
Tabbas gafalalle shine wanda yake take laifinsa yake kallon na waninsa asara da tabewa ta tabbata garesa, kada ka damu da kuskuren wani domin bakasan boyayyen sirrin dake tsakaninsa da Allah ba, yi qoqarin ganin ka samu kusanci da mahaliccinka wannan shine cikar hankali🤏🏼





Dubanshi takeyi da yanayi na gushewar hankali tanason ta bude bakinta tayi magana amma yayi mata nauyi gabbanta gabaki daya rawa sukeyi na tashin hankali zuciyarta tayi matuqar quntata, daqyar ta iya hada kalmar Moddi sun kashemin Innatu me tayi musu kana ina ka bari suka kashemin Innatu na Moddi shin Ina gatana???" Tana mgnr ne cikin gushewar hayyaci inda shikuma yaketa qoqarin janyewa daga gareta har ya samu ya yakice ta ya juya yana tsiyayar da hawaye batare da ya iya bata amsa ba.
Saida ya bata tazara sosai tana tsaye kamar sassaqe sannan ya tsaya batare daya juyo ba yace “ki miqe hanyar nan tabbas nasan zasu biyoki koma suna kusa ki tafi Juhud kada su hallakaki burinsu ya cika banason burinsu ya cika nafiso su rinqaji a ransu cewa bayan Haro da Indo akwai wani abu da ya zame musu alaqaqai din da suka rasa samun damar cimma buri akansu tabbas taimakon Allah zai riskeki ta inda baki zata ba....." Daga haka bai kuma cewa komai ba ya tafi yabarta a kan kwanar ta durqushe a gurin ta rushe da wani marayan kuka na tunanin rashin madafa wanda bataji yana bawa zuciyarta sanyi ba saima qarin tafasa da takeyi.




Haka tanaji tana gani Moddi ya rinqa ratsa Kalgo da Sabara har ya bacewa ganinta haka ta wanzu a gurin tsayin lkc tana dama ace itama Allah ya aiko abinda zashi dauki rayuwarta ta huta, yanzun idan tabar guringa ina ta nufa.......
Tana tsaka da wannan tunanin ta rinqajin qarar yayi alamun tahowa akeyi gareta tayi saurin saita nutsuwarta duk tsoro irin nata yau zuciyarta ta soye mutuwa tafi buqata fiye da rayuwa, ji tayi an tsaya can ta fara hango duhun mutane har uku Muryar Baffa Ribado tajiyo yana cewa “yawwa gata cen...." Ai bata gama jin cewarsa ba ta zabura ta miqe daidai lkcn da suka zagayeta kowa da makami a hannunsa jikinta ya dauki tsuma ta dubi fuskokinsu zatayi mgn kawai Manga yakai mata sara ta goce ta fadi qasa warwas.
Ya sake daga Addar Hannunsa ya saita qirjinta ta rintse idonta tanajin saukar saran daya sanyata sakin wata razananniyar qara data cika dajin.
Ya sake daga Addar zai qara mata suka ga wani haske me dogon zango ya haskesu tuni suka saki makaman suka juya da sauri suka tsuke suka shige cikin duhun dare domin a lkcn magaruba ta jima da wuccewa.



Hasken yaci gaba da kusantota har ya iso daf da ita cambala qafarsa da yayi a cikin jini ne yasashi saurin haska qasa yaga jinine yake malala a qasa kamar ruwa, da sauri ya saita fitilarsa a wajen da yaga jinin yana gangarowa ya matsa da sauri ya zubawa yar fulanin ido tare da russunawa ya haske fuskarta da fitilarsa sosai yaji faduwar gaba daidai lkcn da ruwan saman ya kece da qarfin gaske, yace “Cornel Rasheed yar fillon da kasai nono a gurinta ne dazun"
Safa ya zaro cikin jakar dake goye a bayansa yasa a hannunsa ya daga rigarta tare da zaro ido waje saran ya shiga sosai, jinjina kai yayi tare da zaro wata qatuwar waya a aljihunsa ya danna wasu numbers ring biyu aka daga bai jira cewar me mgnr ba yace “ku tsare dukkan qofofin dajin nan guda hudu akwai yan ta'adda a cikinsa yanzu na tsinci wata sabuwar gawar bafulatana da alamun sun kasheta ne sukaji motsina suka gudu...." Qit ya kashe wayar ya sanya hannu ya sake gyara mata rigarta ya miqe ya debo ganyen bishiya ya rufa mata ya tsallake ya tafi.
Ajiyar zuciyar da yaji ta saki ne yasashi tsayawa cik tare da juyowa ya haske fuskarta da wannan dalleliyar fitila tasa yaga ta bude idanunta ta sake mayarwa ta lumshe hakan ya tabbatar masa da sauran rayuwarta, raba daya biyu zuciyarsa keyi akan ya taimaka mata ko yayi tafiyarsa?





Ji yayi zuciyarsa ta karye tabbas Dan'adam daraja ce dashi maybe idan ya taimaketa Allah ya qadarta tashinta idan kuma ya tafi yabarta wasu halittun na daji zasu iya zuwa su qarasa ta, da wannan tunanin ya tsugunna ya sanya hannunsa ya dagota cak ya sabata a kafadarsa ya miqe ya nufi Camp dinsu da ita, tafiya ce me tsayi sosai tsakanin gurin daya tsinci Juhud da camp dinsu haka yayita kurdawa cikin wannan duhuwa har ya fito sarari ya fara hango Camp din nasu kuratan sojojin da suke basu fita duty ba suna zazzaune cikin ruwan sunata hirarsu da iface²nsu.
Duk inda ya gifta kallonsa akeyi da fuskar mamaki idan ya wucce su kalli juna su gimtse saboda sanin tsagwaron rashin imaninsa yanzu ne zai sabawa mutum halitta ko yabaka gwale²n da sai kayi sati kana ruwan dumi, kai tsaye clinic din Camp din ya nufa ya wucce kowa ya shiga har dakin duba marasa lfyr ya kwantar da ita saman gado ya juya zai fita Likitan dake kan aiki yayi qundunbalar cewa “Tnks Sir" jinjina masa kai yayi yace “kayi aikinka akan wannan yarinyar banason a samu matsala ka bari ta mutu kaima saika mutu domin alamu sun nuna zamu samu wani haske game da yan ta'addan nan da suka damemu" sake sara masa yayi cikin ladabi ya sanya kai ya fice wani Soldier ya dafashi yace “A tsarin aikinmu babu dauko petiant mu kawoshi garemu domin magani Cornel Rasheed meye yasa kayi hakan shin baka tunanin matsala zata iya afkuwa?"




Fuskarnan kamar hadari yace “nayi ne don inada ra'ayin hakan kuma hakan nakeson yi saboda haka ayi hakan kawai" yana fadin haka ya juya ya sake nufar dajin domin yin abinda ya fitar dashi dazun, bashi ya dawo Camp din ba sai 11:30pm sabe da wata qatuwar gada a kafadarsa yana zuwa ya cillawa kuratan sojojin da ido yabasu umarni suka mike suka fara gyarata tantinsa ya nufa ya cire kayansa gabadaya ya fito dagashi sai gajeran wando ya nufi wani zagayayyen guri ya watso ruwa ya dawo ya shafa mai ya fesa turare yasa wasu kayan shan iska ya kwanta a dan gadonsa ya lumshe idonsa zuciyarsa na kai kawo tsakanin Joss Da Katsina Birnin Daura ya kwana hudu rabonsa da mahaifarsa yanason zuwa amma aiki ya riqeshi.



Taba qofar akayi alamun ana neman sahalewar shiga garesa yayi juyi tare da cewa “a shigo" shigowa likitan yayi ya qame a gabansa yace “Sir wannan Petiant din aikinta yafi qarfinmu saidai akaita Barreck ayi treat nata saboda ciwon nata babbane akwai abubuwan da bamu dasu anan da dole sai dasu zaayi amfani"
Baice masa komi ba ya dauki wayarsa ya kira wata number ba bata lkc aka daga yace “ya nemi izinin gaggawa na komawa barreck cikin yan mintuna aka basa ya miqe suka fita da likitan yana tafe yayiwa drivernsu mgn ya Zama ready ya shiga da kansa ya zare ledar jinin da suka sanya mata ya sabeta ya fita yasa a mota suka dauki hanyar cikin gari barrack dinsu nesa take da gari sosai hakan yasa basu isa ba sai daya saura suna zuwa kai tsaye asibitin ya kaita likitoci sukayi mata cah aka fara jorner mata na'urori saida aka gama saita komi sannan ya juya a gajiye ya nufi gdansa, budewa yayi ya shiga ya bude qofar Falon ya tsaya yana qarewa falon kallo yanajan qwafa.
Wato Christiana bata gyara masa gidan ba tunda ya tafi, iska ya furzar me zafi ya bude dakinsa ya shiga shima kaca² Tsaki yayi ya cire kayansa ya dauki towel ya daura sai yanzu asalin siffarsa ta bayyana dogone kakkaura kirar mazan faman gaske wankan tarwada shiba fari ba shi ba baqi ba, yana da fadin qirjin sosai me cikakkun nonuwa da suke rangaji kamar na mace gargasa ta kewayesu abin gwanin sha'awa gabadaya jikinsa lullube yake da suma fuskarsa me qarancin fara'a faffada me madaidaicin tsayi hancinsa dogone amma ba kamar biro ba lol.




Yayi daidai da dan qaramin bakinsa me dauke da siririyar wushirya a tsakiyar shiryayyun haqoransa sajensa baqi sidik daya hade da gajeran gemunsa sumarsa baqa kwantacciya ta fulanin asali ta qara armasa sirrin boyayyen kuma bayyanannen kyansa.
Cornel Rasheed Mahfuz kenan haifaffen garin Port-Harcourt da asalin Jahar Katsina cikin Daura L.g.a Wanda aikin soldiar yakai General Mahfuz wato mahaifinsa da mahaifiyarsa Salma Part-Harcourt ta haifesu su shidda acan, Captain Salman shine Babba Sai Dr Arman da yake bi masa sai Hamida Sannan Raseed sai Muntaz sannan auta Ya'isha,
Zainab matar babansu ce wacce suke kira Adda Abulle tana da yara hudu Kareem Shine Babba baikai Rasheed ba ya girmin Muntaz sai Fadila da Urwat sannan Auta Amrah, shekaru sunata turawa har zuwa lkcn ritayar Gen Mahfuz ritayar tasa tazo daidai da lkcn da Wansa da yake mulkar masarautar Daura ya rasu hakan

Please Login or Register in order to submit comment