Join Our WhatsApp Group

Idan ku ka ga kun taba wani wuri ya fitar daku a shafinmu, sai ku danna back kuyo baya, ku sani yanzu muna amfani da tallan Popunder a shafin, so karatu zai muku dan wahala, amma ta hakanne kadai zamu iya cigaba da rike shafinnan. idan har bakwa son talla sai kuje ku yi subscription na shafinnan akan karamin kudi ku runga downloading kawai. SUBSCRIBE


DOWNLOAD

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register
DOWNLOAD

manta nima inada haqqi ga Kareem nan ciwon kai idan yayi ki dauki nauyinsa banida lkc ko kudin da zan kashe abinda kikeso ne anyi miki fine"
Ficewa yayi daidai lkcn da Kareem ya zube a qasa sumamme tayi kansa a guje cikin tashin hankali shikam Mai Martaba yana fita part din Kareem din ya nufa ya ishe Mom tana yima takwararta Ayshatu baby wanka ya zubama jaririyar ido kyakkyawa da ita Masha Allah yayi ajiyar numfashi yace “idan kin gama inason ganinki"
Amsawa tayi da to ya fita Saida ta gama shirya babyn sannan ta kaiwa uwarta ita daki tana kwance tun safe batada walwala hakanan gabanta yake faduwa batasan dalilin ba tun kafin ta haihu rabonta da ganin Rasheed sai jiya takeji a gurin Kumbo Hami wai Yana gurin magani dauke hawaye tayi a fili tace “Allah ya baka lfy Baffa'am" murmushi Mom tayi tace “amin ya Allah Bari naje Mai Martaba yakeson ganina" jinjina kai tayi ta fice itakuma ta dauki yarta tana bata abincinta bayan kamar Awa daya taji Kumbo Hami tana salati tace “saki Kuma Aishatu me yayi zafi haka?" Bataji me Mom tace ba Amma Saida gabanta ya Fadi ta miqe Kumbo ta shigo ta dauki jaririyar tace “aikuwa shima Mai Martaba din bai isaba wlh sai tabar gidannan Mom tanason mgn ta katseta tace “karma kicemin komai idan zaki iya ki nemomin me kaini inda zani" a sanyaye Mom tace “Amma Kumbo magaruba tayi koma me kikeson yi kibarma gobe Mana" murmushi tayi tace “matsiyaci shine yake jira nikam bana jira" da haka ta dubi Meenah data kasa gane komai tace “muje Aminah" mgn takeson yi Kumbo Hami taqi sauraronta ta figi hannunta suka fito suna fitowa taga Muntaz yace “ina Kuma zaku tsohuwa da daren nan" kallonsa tayi tace “yo jiyemin fah dannan wannan Tataccen ne da gantalalliyar uwarsa suka wulaqantamin jiki wai saki a halin jego to debemin albarka gyatuma tayi da zan Bari mukai gobe a gdannan"




Jinjina kai Muntaz yayi yace “Ya Kareem din ne ya saki Meenah Kumbo...." Daquwa ta watsa masa tace “aa tatsunniya nakeyi maka ja'irin yaro zo ka kaini cikin gari akwai wata yar qasarmu mu kwana acan da safe saimu tafi" yasan rikicin Kumbo Hami idan ta fusata hakanan ya debesu da Meenah da taketa matsar hawaye batasan dalili ba sai taji abin yanayi mata yawo a kwanya ta tambayi kanta yafi sau goma ashe Kareem zai iya rabuwa da ita ashe dama duk abinda yake fada mata na ta rayu dashi forever itane zuciyarsa itane rayuwarsa qarya yakeyi mata?
Sosai takejin qunci a zuciyarta batasan zafin saki haka yake da qona zuciya ba hawaye ta rinqa daukewa lkc zuwa lkc har suka Isa unguwar da Kumbo tace akaisu dake tayima matar waya aka taresu gdane babba na masu hali suka shiga bayan Muntaz ya tafi komai ya nutsa Kumbo take fadawa qawar tata abinda ya faru sun jima suna jinjina lamarin Meenah binsu kawai takeyi da ido wani bangare na zuciyarta na ayyana mata lallai dole ta canza takunta lkc yayi da zata tsayawa rayuwarta.




_Kuyi hqr da wannan naso yi muku typing me tsayi wani uzuri ya katseni ma hadu gobe._




Juhud is not free read... regular 300 VIP 600 via👉🏼 0255526235 Fauziyya Tasiu Umar GTbank



Then you show ur evidence via WhatsApp 09013718241...



Juhud ba littafin kyauta bane kada ki biya 300 regular VIP 600 kafin ki karanta ta wannan account din 0255526235 Fauziyya Tasiu Umar GTbank ko katin MTN pls ban buqatar vtu hoton katin ko digit number ta WhatsApp number 09013718241.....



*Oum Hairan*
[8/18, 2:25 PM] Oum Hairan: Batasan ya akayi ba da safe Kumbo Hami ta tasheta suka duma zuwa Kano kwanansu biyu a Kano ta Kira Muntaz tace ya kawo mata passport din Meenah ta bashi address na inda suke ranar ta kama kwanan yarinyar bakwai a duniya hakanan Muntaz ya taho ya kawo musu passport din ya nan yake fadawa Meenah Kareem bashida lfy Amma fita dashi waje.
Fatan sauqi tayi masa da rangwame gurin me ikon bada sauqin ya dauko kudinsa Dubu dari yabawa Kumbo Hami yace “wai Addah ce ta bayar tace a siya rago ayima yarinyar hakika" murmushi tayi ta debi kudin ta watsar tace “kace mata mu harkar arziqi mukeyi bama ta tsiya saboda haka ragon dubu dari yayi kadan a hakikar jinin mu tabarshi ta rage zafi" da wadannan kalamai ya dauki hanyar Katsina sukuma sukaci gaba da abubuwan da zasuyi na tafiyarsu Mali domin taci alwashin Meenah ta gama zaman wannan gda da can a baya ma don bata da ikone da shi kansa Rasheed saita rabasu don sama mata salama da yancin rayuwa.
Sun qara kwana uku kullum suna waya da Mom suka dauki hanyar qasar Mali nan Meenah ta Raina kanta gdan kakanta mahaifin Mamanta ya rikita lissafinta yasata jin sabuwar izza ba gdan sarauta bane Amma barorin gdan sunfi dari ko Ina sukabi zubewa akeyi ana gaishesu har kawo suka isa asalin harabar gdan inda zata sadasu da asalin cikin gdan Hajja Kharimatu tayi tsalle ta rungume Juhud tana dariya tace “wayyoh dadi ga yata ga jikata. Narkewa tayi a jikinta tana murmushi suka zube a falon kafin kace wane wannan falon ya cika maqil da yan uwan mahaifiyarta kowa ta kalla fuskar Innatu take gani a fuskarsa ta share hawaye tace “na yarda na dawo cikin gatana cikin ahlina




Wani dattijo dake shigowa yace “kuma bazaki qara barin ahlinki ba har gaban abada Qanwa inayi miki barka da dawowa cikin zuri'armu bayan wahala da mukasha ta dogon lkc akan neman inda zamu samoki"
Kumbo Hami ce ta nuna matashi tace “tashi kije ga kakanki Meenah yayi kukan boye yayi na fili saboda rashinki ke kadai duk jikokinnan da suka kewayeshi" miqewa tayi da sassarfa ta Isa garesa ya rungumeta yana shafa bayanta tana kuka Yana hawaye yace “tsarki ya tabbata ga ubangijin daya rayani har naga Aminatuh na a raye cikin aminci" janta yayi suka zauna yace “naji quncin watsi da nayi da mahaifiyarki hakan ya jawo tabarbarewar komai naso na gana da Aishatu kodon na nemi gafararta ita da mahaifiyarta ubangiji bai nufa ba saiya kawomin ke madadinta ajiyar numfashi tayi shima ya aje numfashi nan sukayita hidima da ita da Muneefanta har dare sannan aka kaita makwancinta sashine guda da yasha kyau da gyara sosai part din ya qayatar da ita Saida Kumbo Hami ta dafanta ruwan zafi ta gasanta jiki sannan ta qyaleta ta kwanta bacci kuwa me dadin da ta dade batayi irinsa ba ranar shi tayi.





Haka rayuwarta a Mali taci gaba da kasancewa cikin annashuwa dangin mahaifiyarta daga mazan har matan da yayayensu sunata nannan da ita sai janta sukeyi da nuna mata gata ta kuwa saki jikinta sosai duk da zuciyarta bata nutse guri daya, kaso mafi rinjaye na sinadarin tunaninta yana ga Rasheed Wanda kullum saita Kira wayar Mom taji lfyrsa Abu daya take fada mata jiki ana samun sauqi itakam tanason sanin wanne irin sauqi ake samu gashi Kumbo Hami ta kasa ta tsare ta hanata wani motsi koda tasamu Baffa Garbu kakanta da mgnr tanason zuwa Nigeria don ta gano jikin Rasheed hanata yayi gashi shima Kareem yaqi lfy an fada mata ma Addah ta dawo masa da Zahra Amma don masifa yaqi qyaleta batasan inda yasamu number data sake ba kusan kullum sai ya kirata da farko Yana bata tausayi idan yana fada mata halin da yake ciki so batason yasa mata kokwanto akan qudurinta ta qudurce ko zatasha wuya zata rayu da Baffa'am dinta shi kadai a mind dinta domin yafi kowa cancanta da ragamar zuciyarta.
Bata cikason takura ba hakan yasa sometimes tana ganin kiransa takeqin dagawa musamman data fahimci sosai Kumbo Hami ke fushi da ita duk ranar data fahimci sunyi waya da Kareem, Muneefah nata girmanta kwanci tashi har taci wata biyar da haihuwa lkcn tuni Juhud ta hada iddarta hankalinta ya kwanta tayi wani matsiyacin kyau mai rikita isassun mazaje duk inda ta juya ido akanta yake a daidai lkcn ne Kuma kawai Baffa Garbu ya shirya musu tafiya shaqatawa qasashe biyar don sangarta harda wani bata zabi su hudu zasuyi tafiyar shi Kumbo Hami Naila daya cikin jikokinsa sai ita Meenah da yarta Muneefah.




Yanayin yanda suka tsara tafiyar ne yasasu dole Saida suka bi ta Nigeria Kuma ma ba yini zasuyi su tashi ba sai sun kwana biyu qusqus taji sunayi wai zasu barsu a masauki suje Katsina su duba Rasheed daya dawo gida shekaran jiya, ai tanajin haka ta tubure musu kuka baji ba gani dole don basusan bacin ranta suka aminta suka shirya tafiyar da ita tanata murna zataje taganshi tare da addu'ar Allah yasa ya warke sosai tunda suka shigo gdan a mota taji gabanta na faduwa sunayin parking ta daga kanta ta ganshi tsaye saman benen part dinsa corridor din daya zame masa tamkar gurin shaqatawa yanajin nishadin tsayawa a wannan guri musamman idan wani abu na damun zuciyarsa.
Suna tsayawa ta zame batare da ta jira sun fito ba ta saba Muneefah a kafadarta ta nufi hanyar shiga part din nasa cikin saa a bude yake ta shiga ta nufi inda zai sadata da corridor din ta haura da sauri fadi takeyi “Baffa'am wayyoh Baffa'am dina miss you too....." Tsayawa tayi a bayansa ta dafa kafadarsa tace “ayyah dai ubana yafi na kowa alfaharina a duniya bama haka dakai fah" juyowa yayi ya kafeta da idanunsa dake cikin glass baqi ya cije lebensa har Saida suka fashi ya kama hannunta ya cire daga kafadarsa ya furzar da iska ya juya yabar gurin, binsa tayi cikin muguwar kidima tana Kiran sunansa baiko juyo ba Saida ya dangana da dakinsa
[8/21, 8:19 PM] Oum Hairan: Yana shiga tabisa dakin ya tsaya idanunsa na kanta yace “kije kawai banson hayaniya" dubansa takeyi da yanayin rashin fahimta tace “Ya Rasheed nice fah Meenanka" sake daure fuska yayi ya zura hannunsa cikin aljihun wandonsa yayi murmushinsa na isa da indai yayishi tasan ya shiryawa rashin mutunci yace “eh na ganeki fah Juhud Meenah Aminatuh Mom Sarki junior kinsan nasanki nasan wace ke fiye da sanin da kikayiwa kanki? Koda yake ba abin mamaki bane canzawar mutum cikin qaramin taqi Meenah kiyiwa Allah ki ficemin a daki kada kisa ruwa na ya hau wlh banson ganinki...."
Idanunta sosai ya ciko da hawaye ya fara tsiyaya a fili tace “meye nayi maka?" Zaburowa yayi kamar Wanda ta bugawa wani abu yace “zanc...." Sai Kuma yayi shiru jikinsa na Bari yace “ki fice nace da gaske ban qaunar ganinki Meenah kinci amanata kin ha'inceni kin yaudareni kin nunamin Babu wanda kikeso samana ashe qarya kikeyi dama ce kika kasa samu lkcn da kikaga Babu idona kika dauko zabinki kika maye gurbina dashi Abu mafi ciwo wai qanina Meenah Ina raye ki auri Kareem Kuma ki dawo ki fadamin me nace meye zaki fadamin....."
Ya qarasa mgnr da ihu ta dago idanunta da tun kafin ya fara mgnr suke tsiyayar da hawaye tace “wlh ba laif....." Dauketa yayi da Mari yace “idan na qara cewa ki fita kikaqi Tabbas gangar jikinki zata riga Rana faduwa Meenah a yanda nakejin tsanarki tsaf ko zaa kasheni zan iya kasheki" juyawa tayi jikinta a mace bata taba tunanin haka daga gareshi ba tayi tunanin kamar yanda take a baya yafi kowa fahimtarta da bata lkc yaji damuwarta ashe yanzun ta canza zani ba haka abin yake ba “to kodai bai gama warkewa ba?" Abinda ta tambayi kanta kenan lkcn da take tafe kamar mahaukaciya zuciyarta na tafasa gabadaya duhu take gani a idanunta batasan inda take jefa qafarta ba.




Qara ta saki lkcn data buga kanta jikin bishiya batare data sani ba tayi baya zata Fadi Kareem dayaketa mata mgn tun dazun ya tareta ta fada hannunsa tafi minti biyar komai Yana juya mata kafin duhun ya yaye ta bude idanunta ta zubasu akansa ta janye dasauri tare da gyara riqon yarta tace “tnks" daga haka ta juya taci gaba da tafiya yabita yace “Meenah Ina gurin Aiki akacemin kinzo nazo dominki ki tsaya Mana mu gaisa" hawayenta ta dauke ta juyo ta dubesa kamar zatayi mgn sai yaga ta dago Muneefah ta miqa masa yasa hannu ya karbi yarinyar ya cillata sama yanajin muguwar qaunarta na zaga ruhinsa Wanda ya tabbatar da tasamo asali ne daga qaunar da yakewa mahaifiyarta.
Juyowar da zaiyi yaga gurin wayam Meenah har takai qofar falon gdan ya bita da sauri yana kiranta Amma ko juyowa batayi ba ta fada dakin Mom ta zube a jikin Kumbo Hami ta rushe da kuka tace “dama saboda irin wannan ranar nace abarni na rayu ni kadai bazan aure ba aka kasa fahimtata yanzu ga irinta nan Ya Rasheed yaqi saurarona tuhuma yakeyi da naci amanarsa Kumbo wlh banci amanarsa ba ki fahimtar dashi ki zai gane....." Gabadaya hankalin Kumbo Hami ya tashi ta qufula an taba mata zuciyar cikarta daidai lkcn Kareem ya shigo suka kalleshi Meenah ta kawar dakai ya zauna Yana share gumi yace “meye ya faru Kumbo?" Qwafa tayi tace “yo Wagga sakarar yarinya damuwarta tana wucce ta Abdulrasheedu ne komai Rasheed Komai Rasheed aiga irinta nan ga wulaqancin da kika jama kanki nan da kinyi zamanki a Kanon gdan Barrister Kabir aida baisamu damar cin mutumcinki ba"




Jinjina kai Kareem yayi yace “ayi hqr Kumbo kinsan halinsa shi dama fahimtarsa ba daidai take data mutane ba ni kaina gaba yakeyi dani a gdannan akan abinda bamu Isa mu canzashi ba Kumbo ya zanyi da rabon Muneefah ne dake tsakanina da Meenah itanma da taqini take kallona a matsayin maci amanar dan'uwa ya zatayi da ita wlh na tabbata inda Mai Martaba bai hada auren nan ba ko ta wacce hanya sai Muneefah ta fita ajikina ta shiga nata Kuma saita haifamin ita tunda haka qaddarar take a rubuce"
Shiru ta ratsa ta dogon lkc Kareem ya dago ya dubi Juhud da har yanzu take kwance jikin Kumbo tanata matsar hawaye ya miqe yace “kiyi hqr komai zaizo qarshe Allah shine yasan abinda ke cikin qasa a binne" daga haka ya fice a dakin dauke da Muneefah ya nufi gidansa da ita Zahrah tana ganinsa da yarinyar ta zabura ta miqe ya dubeta ya kawar dakai itama saita waske ya shiga kitchen ya daukowa yarinyar biscuits da yourghut ya zauna Yana bata yana murmushi dadi yakeji a ransa rabonsa da ita tun tana jaririya gata har ta tafi shekara guda ji yake dama ace mahaifiyarta ce a gefensa.




Share hawayen daya tsiyayo masa yayi Zahrah na kallonsa tana kada qafa takaici yana qara kamata tace “waikai yar wace ka dauko?" Murmushi yayi yace bakisanta ba ko?" Tabe baki tayi tace “ya zaayi nasanta tunda baa cikin ahlinmu ta fito ba" sake kallon Muneefah yayi yace “qwarai kuwa baa cikin ahlinku take ba tunda kinada ikon canzata daga jinina Zahrah na dade da fahimtar Ina kika dosa koma dai meye a ranki kibi a sannu domin Aisha itace ya babba a gurina Kuma ko zaki haifi duniya bayanta zasu biyo abu na qarshe da nakeso ki sani a aurenki ma arziqin Meenah kikeci saboda haka ki taka a sannu"
Tashi yayi ya dauki yarsa ya nufi hanyar ficewa daga gdan tayi dariya tace “iska kuwa na wahal dame kayan kara wahalalle Meenah dai tafi qarfinka saidai kaganta ka hanga kayi sake dan zaki ya girma me ita ya dawo son maso wani qoshin wahala"




Bai saurareta ya tsaya bata Amsa ba ya fice ya nufi wani shop yayima yarsa siyayya ya juya ya koma gdan sarautar har sun shirya suna zaman jiran dawowarsa domin Alh Garbu yace ba kwana zasuyi ba a ranar zasu koma Kano Meenah bataso haka ba taso ta samu cikakken lkcn fahimtar da Baffa'am dinta gskyr lamari Amma batada wannan damar, tana kallonsa Yana kallonta ya dawo daga yawonsa a mota sukayi sallama da Kumbo Hami da Alh Garbu itakam ko kallo bata isheshi ba wani takaici ya cika mata zuciya abin nasa harda wulaqanci juyawa yayi yayi tafiyarsa tabisa da kallo ta girgiza kai ta shiga motar suka tafi tana waiwayensa hankalinta baimakai ga Kareem da yaketa daga mata hannu ba.
Suna tafe tana furzar da iska a haka suka Isa Kano goma na dare suna Isa gdan da suka sauka ta shige daki ta kwantar da Muneefah dake bacci ta zauna zaman karatun wasiqar jaki batada mafita ta miqe ta shiga bathroom ta watsa ruwa ta dawo ta kwanta bacci ya gagareta sai juyi kawai da takeyi cikin dare ta lalubi wayarta ta fara neman layinsa ta kasa jurewa Kira biyar tayi baa dagaba ta rubuta masa gajeran saqo na ban haquri, tana qara Kira taji wayar a kashe taja fasali ta kashe tata wayar ta zubawa Muneefah idanu tana sharar kwallah Tabbas duk abinda yasa Rasheed daukan wannan matakin akanta ba qarami bane, da wannan tunanin bacci ya dauketa da asuba ta tashi suka fara shirye²nsu domin tashi zuwa Dubai, Tara suka tashi itadai badon tanajin dadin komai ba donma Naila tana dauke mata hankali da dan karen surutunta.




Kumbo Hami ta fahimci abinda yake damun jikar tata koda suka isa dinma bata wani saki jiki ba har suka Isa masauki sukayi sallah sukaci abinci sukayi wanka kowa ya nemi makwanci sai dare suka fice daga masaukinsu, suka shiga gari itadai Meenah yaqe kawai takeyi lkc zuwa lkc tana gwada layin Rasheed Amma har yanzu yaqi dagawa har dole tasa ta saduda ta qyaleshi.
Sai asuba suka koma gda sukayi sallar asuba suka kwanta rayuwar taci gaba da gudana a haka baqin naci ya hana Juhud daina kiransa shikuma yaqi dagawa kamar yanda Kareem yake nacin kiranta itama tana jizgashi idan abin ya dameta saidai ta Kira Ya'isha tasa mata kuka tace ta tayata bawa Baffa'am dinta hqr saidai Ya'isha tayi murmushi tace “wlh Meenah baqin kishine yake damun Ya Rasheed Amma Ni shaida ce bai daina sonki ba" da haka take dan kwantar mata da hankali take samun nutsuwa.
Satinsu biyu suka daga zuwa Malay daga Malay sukayi India daga can sukayi Saudi sukayi Umarah daga nan sukayi Turkey daga Istanbul suka gangaro Nigeria daga Nigeria suka zarce Mali, watanni hudu suka kwashe a yawon nasu suna dawowa suka shiga bikin Naila da Hameen dake abin duka na family ne yayi armashi sosai.




Mom ita da Ya'isha da Aunty Hamida duka sunzo tunda sukazo take maqale da Mom tanata zubanta shaqwaba washegari suna gurin dinner Rasheed ya dira a qasar Basu dawo gida ba sai wajen 12:30am suna kowa baccine akansa tana shigowa tana cewa “ni Allah Mom badon kin takura ba bazanje wannan dinner ba gara na kwanta nayi chat....." Mgnr ce ta maqale mata lkcn da idanunsu ya sarqe ana juna ya wani maze tunaninsa zatayi masa mgn ga mamakinsa sai yaga taba banza ajiyarsa ta Kara wayarta a kunne tana cewa “double sorry na shiga yanayine wayar na jakka bansa ka kiraba sai yanz...." Iyakar nan Rasheed yaji ta shige daki yaji gabansa na mugun faduwa ya dubi su Mom da suketa faman dariya ita da yan'uwanta ya miqe zuciyarsa na tafasa yace.
“Gobe da wuri zan wucce Ghana ba lallai mu samu haduwa ba" bai jira amsar Mom ba ya fita ya ishe Alh Garbu da fadawansa sunata hira gda kamar kasuwa ya lura suma dabi'ar qasar kamar basa bacci sosai da dare, daquwa Alh Garbu yayi masa yace “dan boko dan qaniyarka shine ka shige cikin mata ga qannenka da yayyaenka da iyayenka duka bazakazo cikinsu ba" yaqe kawai Rasheed yakeyi ya isa garesu ya gaishesu wasunsu da yawa yasansu qannen Mom ne wasu Kuma jikokin gdanne nan aka baje sabuwar hira Nan Alh Sulaiman babban yayan su Mom ya kaikaice yace “Alh dama tun kusan sati uku nakeson yi maka mgn wai ya mgnr yaran nan Najeeb da Ameenah....." Tunda ya Fadi haka Rasheed ya zubansa ido duk da baisan wacce Aminan ake nufi ba Amma yaji saukar saqon faduwar gaba.




Zubansa idanu Alh Garbu yayi Yana nazarinsa can yayi murmushi yace “to ai lamarin Aminah ne akwai rikitarwa kaga mijinta na farko ko igiya daya bai yanke mata ba nemansa akayi aka rasa shari'a tabata damar aure ta auri qaninsa shikuma qaddara ta rabasu da saki daya to mijinta na farko din ya bayyana Kuma tanasonsa shima na shaida yanasonta wani dalili ne ya hanashi magantuwa saboda haka indai sunason juna to sunfi dacewa da juna wannan dalilin yasa nace da Najeeb ya hqr wannan abu duk na gidane dashi da Rasheed duk jikokin gdannan ne rashin zumincinsu yasa basusan juna ba"
Tunda Alh Garbu ya fara mgnr gumi ke karyowa Rasheed baqin kishinsa ya motsa ya dago idanun nan kamar gauta Yana Shirin yin mgn wayarsa tayi ring ya zaro ya duba aqogo daya na dare harta gota ganin number Ya Arman yasashi tunanin akwai dai wani abu daya faru daga wayar yayi ya Kara a kunnensa numfashi ya sauke me nauyi yace “ina Kareem din?" Huci ya furzar yace “Har matarsa aka kashe ko iya shi kadai ne?" Sake jan numfashi yayi yace “ok zan dawo gobe" daga haka ya kashe wayarsa.
Ya miqe ya nufi makwancinsa ya soma safa da marwa Yan fashi sun shiga gdan Kareem sun kasheshi shida matarsa? To akanme?" Tambayar da ya rinqa yima kansa kenan mara Amsa a hankali yaji wasu hawaye sun zubo masa ya nemi guri ya zauna Yana tuno haduwarsu ta qarshe da kalmar qarshe ta Kareem ya fada masa, “Kai dan uwana ne na jini Ya Rasheed a tunanina murna ya kamata kayi da ya kasance nine na kula maka da iyalanka a halin bakanan ba gaba yakamata kayi dani ba! Ya Kareem har gobe inason Meenah bazan taba daina sonta ba har fitar numfashina na qarshe na hqr da Meenah ne badon zuciyata ta hqr ba saidon bata damar kasancewa dakai domin kaine zabinta, dani qaddara ta rubutawa bacewa ka auri matata idan na dawo gdy zanyi maka badon bana kishinta ba aa saidon nasan ta cancanta ne shiyasa ta zama matar gado cikin ahlinmu"..........





A daren nan Rasheed bai rintsa ba kwana yayi Yana tuna abubuwa da dama da suka faru tsakaninsa da Kareem tun daga ranar farko da suka fara qullah soyayya da Meenah kawo lkcn daya aureta ta qarfi da irin wahalar da Kareem ya rinqa Sha ta ciwon zuciya duk akanta kawo yanzu yanayin da suke ciki da irin bibiyar da Kareem ya rinqa yi masa akan yayi hqr ya daina gaba dashi sosai yayi kuka da baitabayin irinsa ba a duniya tabbas ya tafka kurakurai masu wuyar gyarawa Kareem baya duniya labarinsa ya shude balle yaje ya nemi afuwarsa akan abinda yayita qoqarin ganar dashi yaqi bashi qofa.
Da asussuba kuwa ya dokawa Mom Kira itanma yanda ya kwana haka ta kwana saboda tun Daren itama aka fada mata abinda ke faruwa Meenah kam batasan meke faruwa ba Amma ranar ta kasance cikin wani yanayi domin a daren waya sukeyi da Kareem Yana mata wasu kalamai data kasa fahimtarsu can taji yace “Meenah kada ki manta wannan wlh tallahi duk duniya nafi kowa sonki ban barki don biyayya ga umarnin Addah ba nabarki ne don nasan kedin banine a zuciyarki ba Meenah in son samuna ne Muneefah ta rayu a qarqashin kulawarmu ni dake nasan hakan bazata samu ba wani abu yana gaf da faruwa dani, Ina kukan rabuwa da abubuwa biyu da nafi qauna ke Meenah da Kuma yarmu Muneefah Amma a wani sashin Ina farin cikin kasancewar zata rayu da cancanta madadina wato Rasheed Meenah ki komawa Rasheed don Allah don taimakon maraicin Aishatuna kinji......" Daga haka ya tsaya da mgnr taji wata qara can taji yace “ina zuwa zan kiraki kamar Yan fashi sun shigo unguwarmu" daga wannan tajishi shiru kalamansa sun tsayanta a rai zuciyarta ta karye tabbas lamarin Kareem akwai taqawa da tsoron Allah baitabayin Abu don jin dadin kansa ba komai zaiyi yanayine don mafitar Al'umma Kareem yakai masoyi a gurinta.
Miqewa tayi zumbur lkcn da taji Ya'isha ta rushe da kuka tana cewa Innanillahi wa Inna ilaihir raji'un Allahumma ajirni fih musibati Mom da gaske Ya Kareem sun kasheshi ya mutu shikenan bazai qara dawowa duniya ba Muneefah ta zama marainiya....."






Juhud is not free
DOWNLOAD
DOWNLOAD

Please Login or Register in order to submit comment