Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ya tsuma ta tabbas duniya ta jima da cika da azzalumai da Babu hisabi a lahira da anci bulus Allah ka tsaremu da imaninmu...........




Juhud is not free read... regular 300 VIP 600 via👉🏼 0255526235 Fauziyya Tasiu Umar GTbank



Then you show ur evidence via WhatsApp 09013718241...



Juhud ba littafin kyauta bane ki biya 300 regular VIP 600 kafin ki karanta ta wannan account din 0255526235 Fauziyya Tasiu Umar GTbank ko katin MTN pls ban buqatar vtu hoton katin ko digit number ta WhatsApp number 09013718241.....



*Oum Hairan*
[8/30, 8:55 PM] Oum Hairan: Bai bata damar dogon tunani ba ya miqe ya fara Shan tea dinsa da biscuits bayan ya gama ya nufi bathroom ya watsa ruwa ya dawo daure da towel ya shafa mai ya kashensu fitila yaja masu labule suka tsunduma duniyar da duk wani masoyan ma'aurata suke kasancewa a ciki, tun Daren ta farajin yanayin zazzabi hakanan dai ta rinqa daurewa har zuwa wayewar gari bata Bari ya fahimta ba ya fice kasancewar zasuje anguwa da Mai Martaba ita Kuma ta fara hidima da yaranta Saida ta shirya Sarki aka daukeshi zuwa school sannan ta samu damar sake kwanciya nan sabon zazzabi yayi mata dirar mikiya.
Tananan kwance Allah ya jefo mata Aunty Hamida yanda ta tarar da ita a nade tana rawar sanyi yasata fahimtar da matsala. Tambayar ta tayi tayi mata bayani ta dubeta sosai tace “kuma ba cikine dake ba?" Saida gabanta ya Fadi da taji ta ambaci ciki lallai har yanzu da sauranta da sauri tace da Aunty Hamida “nawa ga watan musulumci?" Duba calendar tayi tace “bakwai ga sabon wata" dafe kanta tayi tace “ya Salam wlh akwai yuwuwar hakan ne 23 nake period fah....." Dariya Aunty Hamida tayi tace “banga na biyunki a rashin hankali ba Meenah har yanzu baki hadu gabadaya ba to ai yanzun saiki fara lissafi" jan numfashi tayi ta koma ta kwanta tace “banso ba Aunty Hamida har yanzu Muneefah bata shekara biyu ba fah" murmushi tayi tace “ai kinja lkc kiga fah su Ya'isha da akayi aurensu a bayan naki daga me yara uku sai me hudu kekam biyu haba Meenah ita haihuwa kayita tunda qarfinka"




Batada yanda zatayi dole ta tattara tayima kanta fatan Alkhairi sukaci gaba da tattaunawarsu wajen azahar Rasheed ya shigo Aunty Hamida tace “nice zan fara yimaka albishir mun samu qaruwa Meenah ta kusa sake sunkuto Mana baby kyakkyawa" wani ihu ya saki ya zauna kusa da Meenah yace “haba don Allah da gaske kike Wai hakane My Meenah" kawar dakai tayi cike da kunya ya dago kanta ya saukenta kiss a lips dinta yace “naso wannan Allah ya rabaku lfy Wife kinsan me?" Daga ginin makarantarki nake komai ya kammala primary da Secondary din an zuba duk wani abu da ake buqata na aiki yanzun sauran diban malamai"
Da rashin fahimta ta dubesa tace “Makarantata Kuma?" Murmushi yayi yace “Oh Sorry na manta ban fada miki ba diamond dinki da old gold dinki aka siyar diamond din ansai dashi 5.5 million gold din Kuma ansai dashi 2.7 million so sai mukayi shawari da Mom akan meye zaayi miki da kudin Wanda zai amfaneki ya amfani Al'umma so shine aka Gina masallaci a garinku kasancewar suna fama da matsalar rashin ruwa da rashin gurin ibada in akayi ruwa saidai suyi a dakunansu an Gina Bohol guda biyu a farko garin da tsakiyar Wandu masallacin Kuma a tsakiyar garin aka ginashi da niyyar ubangiji ya rinqa kaiwa iyayenki ladan, so abinda yayi saura sai aka yanke shawarar Gina makaranta Boko ce hade da islamiyya da Kuma tahfeez yanzu haka sun kammalu komai da komai kinada rarar 2.9 million a account din Sarki junior yanzu yau nasa gidan TV na NTA da AIT Da Kuma Arewa24 sunzo sun dauka tallan makarantar zaa fara tallatata mun Kuma fitar da sanarwar daukan qwararrun malamai domin samun abinda ake nema am kisan meye sunan makarantar?"





Girgiza kai tayi hawaye na kwarara a idanunta yayi murmushi ya goge mata hawayen yace “MahfAish academy sunan yayanki Mahfuz Aisha academy....." Rungumeshi tayi ta rushe da kuka tana kissing dinsa ta ko Ina tace “Banjin akwai wata kalma data saura a duniya da zanyi maka gdy da ita mijina Allah ya azurtani da mafi qololuwar alkhairin duniya daya hadani da miji na gari Ina alfahari da samunka matsayin uban yayana Allah yabarmin kai ka dade kayi qarko...."
Gabaki daya sun shagalce a gurin sun manta da anyi ruwan Aunty Hamida itadai data fahimci sun manta da ita sumsum ta miqe tabar musu gdansu suka shagalce a gurin dama tunda aka tafi da Sarki school aka dauke Muneefah
Kwanaki sukayita tafiya komai Yana tafiya cikin nasara rayuwa tanata albarka abubuwa duk suka rinqa shudewa Mom itane ta takura Meenah akan sai ta ziyarci dangin mahaifinta badon taso ba haka Rasheed ya dauketa sukaje har Jos suka shiga rugarsu abin mamaki bata taba ganin rugar data samu ci gababa kamar rufar Wandu an gyara musu ita harda makaranta da hanya ga wutar NEPA ta aminta mutane duniya sukeyima bauta Wai yau itace Baffa Ribado da Baffa Bangel suke kuka suna bata hqr akan abubuwan da suka faru da irin sharrance sharrancen da suka rinqa yi mata.
Murmushi kawai takeyi tana share hawaye lkc bayan lkc da dare ne bayan komai ya lafa take tambayar Ina Hammah Manga nan aka zauna ana bata labarin Wai an kasheshi a dalilin kidnapping din wani Dan siyasa da sukayi sojoji sukaje sukayi barin wuta akansu ko gawarsa baa tsinta ba.




Sosai ta jinjina lamarin tare da yimasa fatan rahama ta kwana dayanta a dafe wai saigashi sune harda soya mata manshanu da tatso mata danyar Madara Baffa Moddibo yayima Sarki da Muneefah kyautar saniya aikuwa Sarki yace saidai a daukar masa abarsu dake ba wata babba bace Rasheed da taya bera Bari yasa aka daureta aka sanyata a mota sunata yi musu dariya suka dauki hanya cike da jin dadi zuciyar Juhud yan uwan da suke qyamarta yau itace suke qauna sunata Sanya mata albarka da abubuwan alkhairin da suka samu ta dalilinta.
Cikin wata biyun da sukayi suka juya Lagos hada kan yayansu suka tafi daga Muneefan har sarkin aka Sanya a makaranta taci gaba da rainon cikinta suna qara samun shaquwa da kula da juna da haka cikinta ya isa haihuwa ta dawo Daura Kwananta uku da komawa kuwa ta sunkuto yaranta uku wannan abu ya tsuma dangi ita kanta tayi mamaki saboda cikin nata ba wani shararren girma yayi ba sannan ko a hoto biyu suke cewa da ita sai gata da uku duk maza nan fah wannan family ya kacame kowa mgnr haihuwar yakeyi ranar suna yaran sukaci sunan Babban Haroon mai bi masa Abubakar sai Abdulkareem qaramin aikuwa ansha shagali kamar baa taba yiwa wannan Fam Haihuwa ba kama daga Daura Mali da Jos kowa yayi bajinta su Rasheed harda kyautar kujerar hajji yayima mutum uku Baffa Moddibo da Baffa Ribado da Baffa Bangel saboda murnar wannan haihuwa.




Bayan komai ya lafa yaso su koma Lagos ta kafe Saida tayi arba'in sannan suka koma da qarin me raino daya Ladi itama mutuniyar kirki sukaci gaba da rayuwarsu cikin gdyr Allah da amincewarsa Rasheed kullum likkafa ci gaba takeyi yau matsayin General Rasheed Gen Mahfuz yake amsawa inda makarantar Meenah kullum take qara habaka abin gwanin birgewa da hamdala shekara biyu Meenah ta qara haihuwar ya mace daga kanta tace ta gama abinka da yan bokon qarshen zamani suka fita India aka juyar da mahaifar gabadaya ta dawo taci gaba da kula da yaranta.
Sannu a hankali maqiyanta irinsu Fadila Dada Hanne Hajiya Bilki da wasunsu na boye sai gashi duk sun zama yan koranta idan taje Daura har zuwa sukeyi gaisheta musamman Fadila data zame mata kamar aminiya yanzu duk duniya bata da qawar data wucce Meenah hakan ya samo asali ne daga yanda Meenah ta shiga ta fita taga sun daidaita da mijinta ya mayar da ita dakinta cikin yayanta, itama Addah Abulle daqyar bayan auren datayi Mai Martaba ya dawo da ita dakinta inda ta dauki soyayyar duniya ta dorawa yaran Meenah guda biyu Muneefah da take yar danta da Kuma Kareem qarami da yaci sunan danta duk wani tanadinta nasune sauran jikokin gdan har tsiya sukeyi mata wai ita ta fiye son kai, itadai Meenah saidai tayi dariya tana mamakin yanda komai ya wucce kamar ma baayi ba idan tai tsai sai kawai taji hawayena tsiyaya a idanunta da zaran ta tuna yanzun muma duka wataran shudaddu ne gushewa zamuyi a manta da tarihinmu mu dusashe kamar baa haliccemu ba, a wannan ritsin tsoron Allah yake qara ziyartar ruhinta takanji duk duniya tayi mata zafi kullum addu'arta Allah kada ya jarabci yaranta da irin jarabtarta Allah ya Basu qaddara me sauqin dauka ya Sanya musu albarka cikin cinsu da shansu da motsinsu a kowanne yanayi yabawa mijinta qarfin gwiwar nemo halal a ko Ina take.





_Tammat bi Hamdullah_




_Tabbas komai yayi farko zaiyi qarshe yau dai Juhud yazo qarshe Ina gdy ga ubangijin bayi me kowa me komai daya bani ikon farashi da kammalashi lafiya kamar yanda na tsara._
_Kurakuran dake ciki ubangiji ya yafe Mana badon halinmu ba amfanin ciki Allah ya bamu ikon amfana baki daya._
_Bazan rufe ba sai nayi gdy gareku masoya da baku qasa a gwiwa wajen qarfafamin gwiwa da kudadenku da lkcnku tabbas Ina alfahari daku Ina fatan ubangiji ya sadamu a dausayin zumunci na masuyin soyayya dominsa._



_Kada ku manta next book dina _*YAFI ZAMAN AURE!*_ _yananan tafe da irin tasa rikita rikitar very soon insha Allahu._

_*Oum Hairan*_


An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels


Please Login or Register in order to submit comment