Join Our WhatsApp Group

Idan ku ka ga kun taba wani wuri ya fitar daku a shafinmu, sai ku danna back kuyo baya, ku sani yanzu muna amfani da tallan Popunder a shafin, so karatu zai muku dan wahala, amma ta hakanne kadai zamu iya cigaba da rike shafinnan. idan har bakwa son talla sai kuje ku yi subscription na shafinnan akan karamin kudi ku runga downloading kawai. SUBSCRIBE


DOWNLOAD

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register
DOWNLOAD

shima don ya fahimci baya happy da lamarin ne.
Sun shiga jarabawa gadan² kawunansu sun dauki chargi matuqa musamman Juhud data Hana kanta sakewa da farko sunci gaba da zama suna lesson da Kareem tunda ta fahimci duk lkcn da suka zauna Baffa'am din nata zaita zagaye a gurin Yana qwafa yasa dole ta hqr ta janye ta koma yiwa kanta lesson da kanta tanashan wahala Amma saboda baqin nacinta taqi ta hqr hakanan take tursasa kanta, ganin hakan yasa Mai Martaba ya siyo mata tamfatsetsiyar waya Infinix hot 10 yabata tare dayo mata download na manhajoji na bincike da zasu taimakawa brain dinta taji dadi sosai ranar yini tayi da farin ciki a ranta tanajin itama ta faso gari su Ya'isha sa daina daga mata kai.




Da magrib Mom da tayi tafiya zuwa qasar Mali garin babanta ta dawo tana falo anata kwasar gaisuwa Juhud ta fito sanye da wata baqar doguwar riga me matuqar kyau da daukar idanu tana danna wayar da aketa Kira tun dazun ta qarasa gaban Mom tayi kissing hannunta tace “wlcm Mom munyi missing naki long time kin manta damu" murmushi Mom tayi tace “me sunan Yaya kina burgeni jarabawar nan da alamun bata baki kashi dadi tayi miki kinyi wani fresh dake kamar auduga sabon toho" da murnarta tace “alhmdllh Mom dama rashin lesson ne yake wahalar ni Kuma Mai Martaba ya sharemin hawaye ya siyamin sabuwar waya ya saukemin manhajoji ina samu Ina karatuns cikin kwanciyar hankali raba dare nakeyi Ina karatu sai biyun dare nake nafila na kwanta da asuba da Dora da karatu kafin kowa ya tashi ns tsinci abinda na tsinta.




Jinjina kai Mom tayi tace “lallai Mai Martaba yanaji daku sosai kuna sha'aninku muga wayar taki" miqa mata tayi ta fara dubawa tana dariya tace “aa kaga barrister Aminatu Haroon Moddibo wadannan zafafan hotuna haka" rufe idonta tayi tana dariyarta me daukar hankali Rasheed dake zaune ya miqe saboda hakanan idan ya cika kusanci da yarinyar yanzu yake rasa nutsuwarsa har ya taka step na farko ya juyo yace “Meenah" gabanta yabada wani rass ta dago da in....Ina tace “na...am Baffa'am" hadiye wani yawu yayi yace “ki kawomin wayar nan zan duba wani abu ki hadomin da abinci"
Babu wanda ya kawo komai tace “to Baffa'am" ta miqe ta shiga kitchen ta dauka abincin nasa ta dawo ta karbi wayar ta nufi saman a bude ta tarar da qofar hakan ya bata damar sakai tare da sallama yana tsaye yanata kaiwa da komowa shigowar tata yasashi tsayawa ya harde hannunsa a qirjinsa ya zubanta ido tayi saurin kawar da kanta saboda baqin kwarjininsa baya bata damar Sanya idanunta a cikin nasa.
Tsugunawa tayi ta aje abincin cikin ladabi ta dago ta miqa masa wayar ta miqe zata fita har ta murda handle din taji ya Kira sunanta da wata irin murya data sanya tsigar jikinta tashi taja ta tsaya ta kasa motsawa daga inda take qirjinta yana duksn Sha hurhudu, bai tsammaci juyowarta ba hakan yasashi takawa a hankali ya isa bayanta ya zubawa mazaunanta da faffadan qugunta idanu yanajin sautin bugun zuciyarsa da ya zame masa jiki game da ita yana qaruwa.
Hannu yasa ya murda key din qofar ya zare tare da hadawa da kyawawan dogayen yatsunta data qawata da baqin lalle me ratsin ja ya riqe a cikin nasa ya juyo da ita ya hadata da qofar yana qara rage girman idanunsa akanta a hankali yace.




“Haqiqa ko a tarihi bantabajin lbrn yar da take neman zabar duniya fiye da babanta ba Meenah abubuwa da dama suna bani mamaki na yanda sama da wata guda kikayi watsi Dani a gdannan ko arziqin gaisuwa bana samu daga gareki kawai saboda Ina qoqarin karenki mutumcinki ko?" Hawaye yafi komai arha a rayuwarta nandanan idanunta ya ciko da qwallah yasa hannu ya dago kanta yace “bance kiyimin kuka ba Meenah ai kin girma na gama aikina saura naki gashinan Kuma kin fara babu abinda na isa na sani game dake saidai najishi a gari kamar yanda barori da bayin gdannan zasuji babu abinda na isa kizo ki sanar dani matsalarki yanzun ta zama ba tawa ba kin fifita matsayin kowa saman nawa duk Ina kallonki"
Da sauri ta dago bakinta Yana rawa tace “wlh ba haka bane Baffa'am tsoronka nakeji banason na sake bata maka rai shiyasa kaga Ina gujewa kusantarka....." Zubawa bakinta idanu yayi yana ayyana abubuwa da yawa kafin ya furzar da iska ya janye daga gareta daqyar ya koma ya zauna yace “rabona da cin abinci na qoshi tun Ina Benin shima din ba qoshi nakeyi ba Meenah kawai hqr nakeyi saboda tunaninki yafimin cin abincin dadi komai nawa kece nakasa samun sukuni sabodake hatta abokan aikina sunsan idan ba Meenah sukace min ba basa ganin walwalata meye yasa ke kika kasa sanya Rasheed aranki kika kasa bashi matsugunnin da bazai goge ba a ruhinki abin baqin cikin wai kewarki ta hanani sakewa na taho domin ganinki Ina murna yata ta girma kawai ki rasa da labarin da zaki tareni saina samarinki haba Meenah alqawari yace haka?"




Duk da babu abinda ta tsinta cikin kalamansa wadanda ta gane Basu taka Kara sun karya ba Amma taji jikinta yayi sanyi a haukanta ta yarda batayi masa adalcin ba tace “kayi hqr bazan qara ba" murmushi yayi dama abinda yakeso kenan a duniyarsa yanason abashi hqr koda kuwa shine me laifi, fara zubansa abincin tayi ta dauka ta miqa masa ya lumshe idonsa tare da budewa yace “hannuna ciwo yake ya kamata a fara ramawa kura aniyarta" yanda yayi mgnr ya bata dariya tayi murmushinta me kashe masa jiki ta miqe ta zauna a gefen gadon ta rinqa bashi abincin da hannunta yanaci Saida ya qoshi ya kawar dakai ta turo baki tace “kuma ai baka cinye albarkar ba" murmushi yayi ya miqe yace “inason kiyi albarka nabar miki ki hada da taki" babu yanda zatayi tasan qin cinye abincin ma sabuwar masifa ce hakanan ta rinqa turawa Saida ta cinye ta miqe ta wanko hannunta ta dawo tana hada kwanukan ta dago domin yimasa mgn taga ya bude wani hotonta da tayi da rigar bacci da dare Amrah tayi mata a swimming din gdan a jiqe take gashinta ya manne a jikinta riqar me santsi ta kwanta itama a jikinta tayi luf cinyoyinta a waje santala santala kamar na balarabiya babban abinda ya fadar mata da gaba babu ko bra a jikinta hatta shatin pant dinta ana iya gani idan kuwa ka tsayi yima hoton qurillah har kan nononta baqi zaka iya hangowa.
Gabadaya ta gama firgita duk jikinta ya dauki Bari tasan ta kade har ganyenta yau dagowa yayi ya sauke idanunsa akanta cikin sarqewar murya yace “waye yayi miki wannan hoton?" A gaggauce tace “Am....Amrah ce shekaran jiya a Swimming munje wankan dare....." Mgnr ce ta maqale lkcn da taga ya miqe taja baya da sauri tunaninta dukanta zaiyi maimakon haka sai taga ya bude qofar ya nuna mata hanya yace “jeki Saida safe".................



*Oum Hairan*
[7/20, 9:37 PM] Oum Hairan: *JH014 littafina na kudine idan kinsan baki siya ba don Allah kada ki karanta, bansanki ba bare na yafe miki haqqina dake kanki*

*Regular group 300 VIP 600 via bank Account 0255526235 Fauziyya Tasiu Umar GTbank or card for This number 09013718241 only WhatsApp or vtu only for dis 09031307566*
*Ga yan Niger da suke son wannan littafi basusan ya zasuyi ba ga number da zasu tuntuba 94775574 zasu tura katinsu daidai da kudin littafin sai suyimin mgn na gde*


_Barkanmu da sallah baki daya al'ummar musulmi fatan munyi sallah lfy ubangiji ya maimata Mana da Alkhairi🙏🏼_




Da sauri har tana neman faduwa ta fice daga dakin gabanta naci gaba da faduwa ta nufi qasan ta aje kayan abincin ta nufi dakinsu Ya'isha ce a dakin tana waya ta nemi guri ta zauna ta rafsa uban tagumi tsoronta ya nunku yanzu wanne irin hukunci Baffa'am din nata zashi dauka akanta shine damuwarta yanayinsa ya nuna baiji dadin ganin wannan gantafalfalin hoton ba gashi kusan irinsu sunfi hamsin a wayar tata, “dana sani na goge" ta furta batare da tasan kalmar ta fito ba Ya'isha ta aje wayar tace “meye Kuma ya faru?" Numfashi ta sauke tace “Baffa'am ne yace nakai mass abinci shine ya amshi wayana bansan meye yakaishi Gallery ba kawai sai gani nayi Yana kallon wannan dan iskan hoton da Amrah tayimin a Swimming shekaran jiya" dariya Ya'isha tayi tace “tabdi yau Big Cele an samu kayan dadi a bagas wlh in nine shi kwana zanyi Ina kallo harsai na samu nutsuwa tunda kin hana mutane su lolewa dadinki kinata nuqu² da kaya waike mumina" tsaki tayi ta miqe ta shige bathroom tayi wanka ta dawo tasa rigar baccinta ta kwanta saboda tanason ta tashi tayi karatu da dare tana kwanciya kuwa bacci ya dauketa.
Da safe ta riga kowa tashi tayi wanka tayi brush ta shirya dake alhamis ce azumi ta tashi dashi suka fita domin tafiya makarantar lkcn shima ya fito zai fita tun daga nesa ya zubanta ido yanda take tafiya a nutse yana karyar da zuciyarsa bata lura dashi ba Muntaz ne tagani yana training a harabar gdan ta dauke fuska hakanan takejin tsanar Muntaz don ta fahimci shima ba qaunarta yakeyi ba driver ya gama saita motarsa domin kaisu yaji an kirashi ya juya da ladabi cikin isarsa da izzarsa ta jini yace “kaje kayi abinda ke gabanka zan saukesu" jinjina kai Mal Wada yayi Kareem dake fitowa yace “Ya kabari kawai zan kaisu....." Dagowa yayi ya sauke idanunsa masu firgita mazan gaske akansa bai samu arziqin Amsa ba yace.



“Ku shiga" Gabadaya Juhud a firgice take da yanayinsa suka bude baya suka shiga dukkansu yaqi tashin motar ya dora qafarsa saman sitiyarin ya kashe A.c ya kwantar dakansa saman kujerar ya lumshe idanunsa shi kadai yasan irin azabar da zuciyarsa takeyi masa game da yartasa yanajin tsoron yin abin kunya a tunaninsa kamarshi ya bude baki yace yanason Meenah matsayinsa da darajarsa ta fado bawai don bata isa ba aa kawai shi tsarinsa ne hakan babu macen data isa yace yanasonta a duniyarsa Yana ganin hakan matsayin raini da rashin aji.
Amrah ce tayi qarfin halin cewa “yaya takwas zamu fara paper fah Kuma yanzun bakwai da arba'in" batare daya dago ba ya furzar da iska yace “Meenah!" Yanda ya ambaci sunan ba itaba hatta su Ya'isha Saida sukaji yar a jikinsu suka dubeta ta dago a kasalce tace “na...na'am" ajiyar zuciya yayi yace “idansu qanne nane ke meyece a gurina?" Tambayar tazo mata a bazata, cikin rawar murya tace “ya" ya miqe ya zubawa fuskarta ido ta cikin mirrow yace “kuma kikeso na zama driven ki" bata fahimci abinda yake nufi ba Ya'isha tace “ki koma gaba don Allah mu samu yakaimu" sai yanzun ta fahimta ta bude motar ta fita ta bude gaban ta shiga ta rufe ya juyo ya kalleta ya dauke kai ya tada motar suka bar gidan"




Tunda suka taho babu me cewa qala har suka isa makarantar yayi parking suka bude zasu fita ya riqo hannunta ta zauna ta juyo suka fuskanci juna ta sunkuyar da kanta yace “ina kwana" da sauri ta rufe idonta kunyarsa ta lullubeta yayi murmushi yace “nawa zanke siyan gaisuwarki ne Meenah?" Dariya tayi ya kafeta da ido nandanan ta shiga hankalinta yace “idan kun tashi ku jirani kar wacce ta tafi" jinjina kai tayi ya bude mata ta fita yace “ki kulamin da kanki" sake jinjina masa kai tayi ta nufi cikin makarantar yabita da ido baija motar ba Saida ya daina ganinta sannan ya tafi.




Hudu saura suka fito daga exam din Ya'isha da Amrah suna Shirin kiran driver Kira ya shigo wayar Ya'isha ta daga da sallama jin muryar yayan nasu yasasu shiga taitayinsu yace kuzo Ina jiranku inda na saukeku, Basu so ba donsu nufinsu ba gda sukayi ba gdan Aunty Hamida zasu wucce ganin babu hali yasasu nufar inda yayi parking suka bude suka shiga.
Hudu saura suka fito daga exam din Ya'isha da Amrah suna Shirin kiran driver Kira ya shigo wayar Ya'isha ta daga da sallama jin muryar yayan nasu yasasu shiga taitayinsu yace kuzo Ina jiranku inda na saukeku, Basu so ba donsu nufinsu ba gda sukayi ba gdan Aunty Hamida zasu wucce ganin babu hali yasasu nufar inda yayi parking suka bude suka shiga,
Yana driving din yana satar kallonta inda ita Kuma gabadaya hankalinta yake akan titin har suka isa gdan babu me cewa qala suna zuwa ta bude motar ta riga kowa fita saboda kanta da yake ciwo “idan kun shiga kuce ta kawomin abinci" abinda ya fada kenan suka fita shima ya fito ta baya yabi ya shiga bangarensa ya zauna a falo kallo yakeyi Amma hankalinsa baya gane komai tsayin lkc yaji ana qwanqwasa qofar yabada izinin shigowa ta murda ta shigo da sallamarta ya Amsa mata idanunsa akanta wasu riga da skirt ne na atamfa sunyi mugun karbar jikinta ta ajiye abincin ta dago tace “barka da hutawa Baffa'am"
Lumshe idonsa yayi ya bude akanta yace “kamar wani abu na damunki ko?" Dagansa kai tayi ya gyara zamansa yace “meye shi?" Sunkuyar dakai tayi tace, kaina ke ciwo sosai" sake quranta ido yayi yace “kinsha magani?" Girgiza masa kai tayi ya miqe ya bude bedside drower ya dauko magani ya miqa mata ta karba ya tsiyaya mata ruwa a cup ya bata tasha ya sauke numfashi yace “ki gyaramin dakin nan" miqewa tayi ta fara gyara dakin ta wanko bathroom din ta fito Yana zaune inda tabarshi ta rusuna tace, na gama" jinjina kai yayi ya nuna mata abincin ta zuba masa ta miqa masa ya karba ya faraci kamar bason cin yakeyi ba itadai tana zaune so take yabata damar tafiya saboda shima kallonsa ya fara takurata sosai ta kasa sakewa maimakon hakama sai ce mata yayi “wacce paper kukayi yau?"





A gajarce tace “English" yaja gemunsa yace Kuma kina ganewa?" Daga masa kai tayi ya dauki wayarsa ya kunna wata waqa ya miqa mata yace “inason ki saurari waqar nan sosai ki fadamin meye kika fahimta game da ita?" Sauraron waqar takeyi cikin nutsuwa a hankali ta kwantar da kanta saman dayar kujerar tanajin kalaman baitocin da mawaqin yakewa masoyiyarsa suna ratsata musamman wani baiti da yake cewa “kece ta farko, kece ta qarshe kece kike samin nishadi! idan na waiga ke zana hanga kada ki kasa cikan muradi!! sonki na kama bani nadama kyawun hawan doki da sirdi!!! in kika yarda dani bazani yarda ki wahala ba Rahma!!!" Akwai dalili zanyi misali sunnarki yau na cika buri! nayi su'ali nakwance qulli kedayace zan baiwa sirri!! Samun halali boye da fili,,, shine yakesa rai sururi inda na shaqu dake aso bazaiyi na makara ba!!!......."
Sakkowa yayi ya karbe wayar yasa hannu ya dago kanta idanunta suna lumshe yace “me kika fahimta?" Wata wawuyar ajiyar zuciya ta sauke tace “baitukan sun kashemin jiki Baffa'am Amma ban fahimci komai ba" iska ya furzar yace “bakisan soba ko Meenah?" Daga masa kai tayi ya zuba mata ido Yana lasar lips dinsa yace “nikuma Yana wahalar dani sosai Meenah son wata yarinya Yana neman tarwatsamin zuciya abin takaicin ni jarumi ne a filin daga na iya riqe kunamar bindaga da sakin ruwan harsashe Amma a gabanta matsoraci nake zama na kasa fada mata Meenah"




Cikin yanayin tausayi ta dago tace “Allah sarki Baffa'am meye yasa bazaka fada mata ba to babu wani abin tsoro a lamarin soyayya Kuma ma fah zai iya yuwuwa itama tanasonka bazata iya fada maka bane" tunda ta fara mgnr yake kallon bakinta har tayi shiru yaja zuciya ya dafe kuncinsa yace “idan tanasona me yasa bazata fadamin ba ita tunda ni nakasa?" Murmushi tayi daya qara bayyanar da sihirtaccen kyaunta tace “kaima dai Baffa'am to kaima namiji da aka sanka da jarumta akan muradinsa ka kasa tararta ka fada mata sai ita da take mace da aka sani da yakana da kunya kaima kasan bame yuwuwa bane ai"
Sake sanya hankali yayi akanta yace “ta yaya zan gane idan tanasona Meenah ita yarinyar ta kasance tana matuqar ganin girmana fiye da kowa tana mutumtani batason bacin raina batason damuwata har tana kirana da babanta........ Dagowa tayi da sauri yayi murmushi yace “haka nake nufi sunan babanta ne dani babana haka take kirana a gaban kowa Meenah wlh inason Aminatuh fiye da son da nakewa kaina banjin zan iya rayuwar aure da wata mace ba Aminatuh ba na Raina kaina ranar dana fahimci ba shaquwa ce tasa nake tsananin kishinta ba sone, nayi qoqarin mayar da lamarin mafarki Amma ya faskara har takai zuwa yanzun duk wani fitar numfashi nawa da tunaninta yake fita please ki bani shawara ya zanyi na fahimtar da Aminatuh inasonta?".........




*Oum Hairan*
[7/21, 6:31 PM] Oum Hairan: *JH015- littafina na kudine idan kinsan baki siya ba don Allah kada ki karanta, bansanki ba bare na yafe miki haqqina dake kanki*

*Regular group 300 VIP 600 via bank Account 0255526235 Fauziyya Tasiu Umar GTbank or card for This number 09013718241 only WhatsApp or vtu only for dis 09031307566*
*Ga yan Niger da suke son wannan littafi basusan ya zasuyi ba ga number da zasu tuntuba 94775574 zasu tura katinsu daidai da kudin littafin sai suyimin mgn na gde*



Wani gwauron numfashi Meenah ta saki tace “idan har kace saika Bari ta gane da kanta to kuwa da jan aiki a gabanka Baffa'am idan Irina ce me qarancin fasaha wajen gane abubuwa hannunka Mai sanda bazai wadatar wajen fallasa mata sirrin zuciyarka ba misali kamar ni duk da har yanzun ban karbi tayin qaunar Ya Kareem ba, Ganin nidin bame ganewa bace yasa ya fito ya sanar dani abinda ke ransa ko banza nasan zai samu sauqi game da ciwon dake cin zuciya balle ma ni......"
Dagowa tayi ta dubesa tsoro ya kamata ganin yanda lkc daya ya hargitse yanayinsa ya canza daga na walwala zuwa matsananciyar damuwa, da sauri ta miqe tace “kayi hqr don Allah Baffa'am kaine kace duk wani abu dake damuna na rinqa sanar dakai kafin na sanar da kowa......" “Shut-up Meenah!" Abinda ya fada da qaraji kenan ya miqe jikinsa na rawa zuciyarsa na motsawa da qarfin gaske maqwallatonsa kamar zai faso maqogwaransa tsabar bala'in dake cinsa suka fara zagaya dakin cikin tashin hankali ganin guri ya qure matane ta zame a qasa kawai ta saki kuka me sauti tace.
“Na shiga uku ni Aminatuh Baffa'am meye laifina ne don naso Ya Kareem wlh ko zaka kasheni saina fada maka inasonsa saboda yanada cikar Kamala da nagartar da tayi qarancin a samarin zamanin nan inasonsa saboda zuciyata tana fadamin shine ya dace da maraici na Baffa'am Ya Kareem baitaba sani dole ba baitaba hanani dole ba saidai akan aya da hadisin ma'aiki (S.A.W) baitaba takuramin akan nasoshi ba saidai ya roqi alfarmata duk da kasancewar banida alfarmar shine yake da ita domin a cikin da'irar arziqinsu nake rayuwa, Ya Kareem baitaba nuna yanason jikina ba hasali ma yaqi yakeyi da duk abinda zai tarwatsa mutumcina Kuma, Ya Kareem ya fadamin cewa Allah Yana maraba da bayinsa da sukayi soyayya dominsa wannan dalilin yasa naji inasonsa domin Allah Kuma zan rayu das......"




Bata iya qarasa kalamin nata ba saboda wani gigitaccen mari daya sanyata kifawa ya nunata da yatsa zuciyarsa na tuquqi yanason yayi mgn Amma harshensa ya sarqe a hankali ya janye ya koma ya zauna yana furta “Innanillahi wa innah ilaihir raji'un" ya maimata ta takai sau goma kafin yaji nutsuwa ta fara saukar masa ya dago idanunsa da suka kada sukayi jawur kamar garwashi bakinsa da jikinsa har yanzu rawa yakeyi yace “kina sonsa ko Meenah?" Dagowa tayi idanunta shabe² da hawaye yace “bakiyi qarya ba duk gdannan babu wanda ya tara wadannan suffofin da kika lissafa sai Kareem nima shaida ne saboda haka ya cancanci kisoshi tabbas Amma Kuma yanzu ya zakiyi da wanda ya daukoki tun baki cika mutum ba yajaki jikinsa ya mayar dake mutum ya bata darensa da ranarsa dominki ya Hana kansa farin ciki sai yaganki cikin farin ciki yake shiga damuwa da damuwarki koda kuwa bakwa tare motsinki ya zama nasa lfyrki tasa ciwonki nasa Aminah ya zakiyi dashi wanne halacci zakiyi masa da zaiji a ransa kin saka masa da kwatankwacin tausayinsa da qaunarsa gareki?"





Tunda ya fara mgnr ta kafesa da idanunta da yake tsiyayar da hawayen tashin hankali tasowa yayi ya matso gabanta ya miqar da ita yace “idan ya kasance kin kasa saka wancan Alkhairin da abu mafi daraja wato qaunar da wannan mutumin yake nema a gurinki to tabbas ke ba yar halak bace domin dan halak shine yake jiran gabar saka Alkhairi da komansa koda kuwa gurin bai cancanci sakayya ba shidai burinsa yaji a ransa babu bashi tsakaninsa da wannan mutumin"
Sakinta yayi ya juya zai shiga bathroom har ya bude ya juyo yayi mata murmushi yace “kije kiyi tunani akan kalamai na" a mugum kasalce ta bude qofar ta fito ta nufi cikin gdan zuciyarta na kai kawo akan kalamansa tana shiga dakinsu ta zube a bakin qofar tana mayar da numfashi Amrah dake fitowa daga bathroom taja ta tsaya sake da baki ganin yanda ta cure jikinta tanata rera kuka takaici yasa Ya'isha miqewa tace “dallah malama ke baki rabo da kukane meye Kuma akayi miki" dagowa tayi ta kwantar da kanta jikin Amrah tace “nikam Ina ganin rayuwa Amrah don Allah meye wadannan kalaman suke nufi......"
Zayyane musu komai tayi ta qarashe da cewa “bansan meye yasa qwaqwalwata bata gane abubuwa ba" numfashi Amrah da Ya'isha suka saki tare Amrah tace “kan ubancan lallai akwai qura a gdannan Juhud bafa wani abu Big Cele yake nufi ba kece yakeso kece Aminan da yake baki lbr ke kadai ce me wannan siffar daya suffanta" Ya'isha ce tayi murmushi tace “ke saiyau kika fahimta ai dake da Aminah dukkanku kallonku nakeyi Amma wlh batun yanzu ba na fahimci Big Cele son Juhud yakeyi tsabar miskilanci ne da girman kai ya hanashi bayyanawa yake wani bada fadi da hura hanci kamar kyankyaso aikin banza na dade da gano damuwarsa kekam ta bakin naki kina ganin rayuwa ga Mai Martaba yayima Ya Kareem alqawarin aurenki" cikin mutuwar jiki ta dago tace “nikam ya zanyi wlh da gaske bantaba daukar wannan gundumemen lamarin zai fadomin ba banyi masa muhalli a bangarena ba bantabajin Baffa'am zaice yanasona ba kai bama abinda yake nufi ba kenan babu abinda zaiyi dani"




Dariya sukayi dukkansu ta zubansu idanu Amrah tace “waima to shi ya gani wlh yarinya tun wuri ki takansa birki inba hakaba zakisha wahala Big Cele bashida mutumci gashi da ganinsa zaiyi wuta babban tashin hankalin ma mgnr aurensa da Zulaihat tayi mugun nisa harma fah ankai kudin tambaya sa rana kawai zaayi anasa rana Kuma raqashewa zamuyi Kinga kenan bakida gurbi kawai batankin gomanki zaiyi dayanki bata gyaru ba"
Tagaji dajin wadannan kalaman hakanne yasata miqewa ta shiga bathroom ta sakarwa kanta ruwa ta fito taji ana kiran magrib ta dauki dabino ta tauna ta fita ta dauko ruwa tana dawowa Amrah ta miqa mata waya ta Amsa ganin number Kareem ta Kara a kunnenta tace “nasha ruwa lfy Habiby kaifa?" Murmushi yayi yace “yanda kikasha Luv ya exams?" Kwanciya tayi tana lumshe ido tace “inajin dadin exams din da taimakonka" hirarsu sukaci gaba dayi tama manta da batun Shan ruwa saida yace “kije kisha ruwanki zan kiraki anjima" ta aje wayar ta tayar da sallah tayi buda bakin.




Tun daga wannan ranar salon rayuwar gdan ta canza musamman tsakanin Juhud da Rasheed duk inda tasan zasu hadu gujewa gurin takeyi saboda ita har cikin zuciyarta bataji a ranta zata iya soyayya dashi ba bayan haka ma sannu a hankali Kareem ya gama siye zuciyarta da salon qaunarsa me tsayawa a rai da wuyar gogewa kullum idan sunyi waya kalmarsa daya itace don Allah Aminah ki kulamin da kanki nayi miki tanadin kaina na tsare kaina tsayin shekaru burina ya kasance a halali na na fara shuka inason gonata tayi kyakkyawan yadon da yabanyarta zata burge kowa idan amfanin ya nuna ya isa moro ya morawa duniya baki daya Aminah samawa yayana uwa ta qwarai shine abinda na dade Ina
DOWNLOAD
DOWNLOAD

Please Login or Register in order to submit comment