Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

da kuka sosai tace "please dan Allah ka matsa, wlh am scared zai kamani" ta fashe da wani kukan gani take kaman Abba zai taso ya kamota, girgiza mata kai yayi tareda kama hanunta da karfi yay cikin dakin da ita tana tutturjewa tana makewa abayanshi, zaunar da ita yayi akan kujeran dake facing na Abba tana yunkurin ta mike tsaye ya maidar da ita ya zaunar yace "calm down zaiyi magana dake ne will come back in 10min time, calm down babu abinda zai miki kinji" fashemai ta dawani irin kuka ta dago kai ta kalleshi tana girgiza mai kai tana makemai kafada, ko kadan batason ganin Abba balle ita kadai dashi awuri, juyawa yayi zaitafi da sauri ta rikemai riga ta kara karfin kukan ta, juyowa yayi ya daka mata tsawa yace "i said sit!" da sauri ta zauna tana nishi hakan yasa yajuya yafita ya rufo musu kofan, maida kanta tayi kasa jikinta na rawa sosai tana goge fuskarta da hijabi har cikin ranta jitake da Abba gwara wanan dodon ko kadan batama son ganin Abba hakan ya tuna mata abubuwan daya mata kuma batason hakan, sotake ta manta.

Abba yay kusan minti uku kallonta yake tundaga yatsun kafarta xuwa kayan datasa dayasan bana gidanshi bane, da hijabin datasa har zuwa zufan datake hadawa a goshi, yanda yaga ta shishige boyayyen mutun dinan nawani irin konamai rai, jiyake kaman ya rufe ta da duka amma ba daman yin hakan, gawani dan iskan kuka datake yi saikace yadawo mata dodo, tsabagen yanda zuciya ke cinshi yasa yadau rapan yan dubu daidai dake jikinshi guda biyu na sadakin ta yadau daya yawani irin stoning dinta dashi yay landing a goshinta da sauri ta dago kai ta kallai tana shafa wajen tana kuka, idanunshi taga sunyi jajir hakan yasa ta maida kanta kasa jikinta na rawa ta fashe da wani sabon kukan kaman xai kasheta, daukan dayan rapan kudin yayi ya kara jefa mata akai yace "kinga dodo ko stubborn girl kina wani shegen kuka, badai ni kikama hakaba kinma mahaifin ki butulci ko, kije gashinan ga sadakin kinan yanzunan aka daura auren ki da wanan danaga kina rungumew..." yakasa karasa maganan sabida yanda abin kemai wani irin ciwo arai, a rude ta dago kai cikin kuka ta kalleshi jin kalman aure daga bakinshi, yasake nuna kanshi da yatsa yace "ni, ni ko Princess! ni princess, nidai ni kikama haka ko princes..." yay shiru yana shafa kanshi kana ganinshi kasan abun namai ciwo, sai yanzu daya sata a ido yakejin wani irin dana sanin yarda har akai auren nan, dayaki koma me zasumai sumai, tayaya ma ya yarda ya bada ita? Saikace akwai magic abakin mutumin daya yarda kawai, Yaushe princess ta girma harma tai wayon yin zaman aure? Princess is such a
sweet innocent girl babu abinda ta sani, batada hayaniya, bata iya fadaba, sunma yaran su wani irin tarbiya da yaran basu iya fadaba, basu iya rashin kunya ba, basu iya gardama ba, basu iya hayaniya ba, waye wanan daya bama auren yarshi da har yanzu bata gama sanin rayuwa ba balle tasan yanda zatai handling wanan phase din life dinba, me zaice ma Yayinta da dama already fushi suke dashi, mezai cema mahaifiyar ta dudda ita ce taja almost all dis problem dahar yaja suka fito cikin dare har wani ya ganta yatafi da ita, innalillahi wa innailahi raji'un, Princess matar manya ce tayaya ya aura ma gang yarshi? Kallonta yasake yi yaga kuka kawai take tana share fuska da hijabi, ahankali yace "My Princess" kin dago kanta tayi, hakan yasa ya cije leben shi in pain yace "an daura aurenki da dat man dazunan a masallacin gidan nan, those money sadakin kine" yay pointing kudin dake jikinta da yatsa, tunda yake maganan kur ta kafe Abba da ido tana kara nanata kalman aure akaro na biyu aranta tana wani irin kallon Abban dawani irin mamaki, wani irin harara Abba ya watsa mata cikin wani irin fushi daya tasomai da baisan koname ba yace "wat? me kike kallona da shegun idanun nan naki masu kama dana mayu? you like him mana ba shi naga kina rurrungume mewa ba agabana princess, ni, niii, agabana kike kakkama wani ko kina tattabashi princess, hmm" yay kwafa yana shaking leg da sauri da sauri kaman yay kuka, jiyake kaman ya kurma ihu, cikin dishashiyar muryanta tace "aure? Abba ni aure?!" cikin wani irin fada yana nunata da yatsa yace "dan gidan ku e, e nace miki, aure aure dai dakika sani an daura miki, ni kika yaudara ko princess, daki taimake ni kin gwanmace kifito gida cikin dare, princess inban samu natsuwa daga yayana ba ina zanje ba maman ki tajamin ba, ai gashinan kinga hanun yan ta'addan dakika fada kuma ya aureki kinma kanki princess, i will never forgive for this, u really hurt me princess, princess am hurt, deeply, am deeply hurt, abin nan namin ciwo ciwooo a zuciyana" da sauri ya dukar da kai yaja bakin rigan farar shaddar shi yana goge idanunshi dasuka kawo kwalla sosai yanajan majina dake shirin zubomai ciki, zuciyarshi zafi takemai kaman ya hadiye ya mutu yakasa bringing self dinshi to the fact dat yanzu nan fa yabada auren princess, yanzu princess matar wani ce, ahankali yadafa kanshi yace "no bani nabada ba".
[9/13, 11:52 PM] Lady: 🕳🕳🕳🕳🕳🕳🕳



*inkika karanta baki biyaba na barki da Allah*



Bakin riganshi yasake sawa ya share hawayen daya zubomai ya sake dago kai ya kalleta yanda take kuka tama kasa magana ya daka mata wani irin uban tsawa yace "kimin shiru anan" ko kallonshi batayi ba saima uban kukan datake yi wani irin bakin ciki takeji yanzu banda irin abubuwan daya mata shine kuma yakama yamata aure, bakin rigan shi yasake sawa ya share hawayen daya zubomai ya sake dago kai ya kalleta yanda take kuka tama kasa magana tana gogewa da hijabi yasa yaji wani irin zuciya ta tasomai ya daka mata tsawa yace "kimin shiru dan gidan ku" ko kallonshi batayi ba sheshekan kukan datake yi wani irin bakin ciki takeji kaman ta mutu, dudda irin abubuwan daya mata shine kuma yakama yamata aure, aure, nice matan aure? Tunanin hakan yasa takara karfin kukan datake yi, takalmin dake kafanshi Abba ya cire ya jefeta dashi da sauri ta tashi tsaye tana kuka sosai tana komawa baya, nunata yayi da yatsa yace "ke ko, keko Princess hmmm" saikuma yay shiru yama rasa mezaice, sake dago kai yayi yasake kallonta yanda kukanta ke addaban ranshi yahana shi sukuni yasa yaciro dayan takalmin kafarshi yana nunata dashi yace "wlh idan kika bari natashi a yanda nakeji dinan sainai miki dukan daban tabamiki irinshi ba tunda na haife ki, shashashan yarinya mara wayau kawai, kimin shiru naji da abinda ke damuna ko, shut up princess" ko kallonshi batayi ba saima tsugunnawa datayi ahankali tana dafa kujera ta cigaba da narka uban kukan datake yi tashi Abba yayi yayo kanta a harzuke da mugun gudu ta mike tai hanyar kofa tana kuka daidai lokacin Marwan ya bude kofan ya shigo mistakenly ta fada jikinshi ta kankameshi tayi tana kuka sosai tana kallon Abba, da sauri Abba ya koma kan kujeran dayake zaune ya saka fuskarshi a tafukan hanunshi zuciyarshi namai wani iri dashi kanshi baisan kona meba, sosai Marwan ke kallonshi kafin ahankali ya dagota daga jikinshi share mata hawayen yayi kafin ahankali ya saukoda hanunshi kan lips dinta ya daura akai yace "shiiiiii" shiru tayi ta dago manyan idanunta dasuka cika da ruwan kwalla ta kalleshi muryanta narawa tace "Abbana yace yay mana aure da gaske ne?" gyada mata kai yayi hakan yasa tafashe dawani sabon kukan kaman zata mutu, ahankali ya kamo hanunta ya bude kofar dakin ya fita da ita ya kulle kofan sukai shashin su, akan gado ya zaunar da ita ya zauna kusa da ita ahankali yace "Stop crying" makemai kafada tayi cikin kuka tace "ni kakiramin Mumy na tazo ta dauke ni" yanda tai maganan yakusan sa numfashin shi daukewa hakan yasa ya mike tsaye da sauri ya juya yabar dakin da sauri yay dakin Abdallah ya bude ya shiga yana kallon Abdallah dake zaune malt a hannunshi ya daura system akan jikinshi da earpiece akan kunenshi kallo cikeda nishadi alamun shigowan mutum dayaji yasa ya dago kai ya kalli kofan ganin Ya Marwan ne yasa ya zare earpiece din daga kunenshi ya ture system din yace "Yayan mu wat is it" zama yayi kusa dashi batare daya kalleshi ba yadan fuzar da iska cikeda damuwa yace "she's crying" kallonshi Abdallah yayi ganin sai wani dadddauke kai yakeyi kuma daga gani kasan yadamu amma yana basarwa, murmushi Abdallah yayi yace "to Ya Marwan kaje ka lallasheta mana Ya Marwan kasan normally haka amare sukeyi, ranan danaje bikin abokina Mus'ab ma haka amaryan shi ta dunga kuka nan kasan ko mata basa raina abin kuka, kasan meyayi dayasa tai shiru ta dena kukan?" yay maganan yana danne dariyan dayakeji da duka karfin shi yaci serious yana kallon shi yanda yawani basar yana daddana agogon hanunshi kaman baya yaji hakan yasa Abdallah yadau earpiece dinshi zai maida yace "okay o tunda bakaso am watching game of thrones dama" da sauri batare daya kalleshi ba yace "talk am listening kai" wani irin yangan ce ya karasa maganan, dan murmushi Abdallah yayi yana shafa gemu yace "share mata hawayen yayi da hanunshi, saiyay hugging nata yana patting bayanta, and u know d funniest thing he was whispering something a kunenta da bamuji komeba, kaga luv ko yayan mu is something da kaine zakai creating your own unique formula, this is your first luv so make it memorable bro" agogon shi yasake dannawa ya daura kafa daya kan daya yace "I told you am not in luv I just want to save her from dat old man shikenan" tabe baki Abdallah yayi ya maida earpiece dinshi yacigaba da abinda yakeyi. Sosai ya dinga danne kanshi yana hana kanshi abinda yakeyi da kyar ya daure har sai bayan sallan isha'i yaje dakin ahankali ya bude kofan ganin tai bacci yasa ya tsaya daga kofan dan tsoron shiga ciki yake bayaso yaji abinda yakeji, ahankali ya rufe mata kofan ya juyo ya shiga dakin Omari yana tareda Abdallah da kamal kallon su yayi yace "kun kaima dat old man abinci?" atare suka amsa da eh hakan yasa yace "tommorow by 1 kukaishi gida" tom sukace ya fice daga dakin da bayason hayaniya dakin Abdallah ya shiga ya kwanta yakasa komi fuskarta kawai yake gani.



***
Wuraren karfe uku saura sukai parking akofar gidansu Abba, zare mishi bakin kyallen Omari yayi daga kan fuskanshi ya kwance ma igiyan hanunshi sanan ya bude kofan motan yace "fita" ahankali Abba da jikinshi ya mugun yin sanyi ya fice daga motar, sukaja motar dawani irin arnen gudu suka bar anguwan, yakai kusan 10min tsaye yana kallo hanyar dasukabi jiyake kaman yay kuka ko halan hakan zai sa yaji saukin abinda yakeji, juyawa yayi yabude gate ahankali ya shiga gidan da sauri mai gadi yataso yace "barka da zuwa Alhaji" ko kallonshi baiyiba yawuce ciki ya shiga barrander ya bude kofar dakinsu ya shiga Muhsin yagani da Ya Ahmad zaune akan dining ko wanensu ga abinci gaban su amma baci sukeba, Muhsin yay wani irin rama kaman bashiba, dukansu dago kai sukayi suna kallonshi shima kallon su yake jiyake kaman yaje ya rungumosu koyaji saukin abinda yakeji amma yasan sun tsaneshi hakan yasa yajuya ahankali jiki asanyaye yay hanyar corridor, tashi Ahmad yayi a zuciye yace "Abba daga ina kake? Abba where is Nadeera wai, ina kakaimana kanwarmu ne Abba?" dagamai hannu Abba yayi cikin kunan rai yace "Ahmad! please not now son" cikin fushi Ahmad yabude baki zaiyi magana hanunshi Muhsin yakama ya girgiza mai tareda zaunar dashi, binsu da kallo Abba yayi kafin yawuce ciki yay dakinshi zama yay akan kujera ya kama kanshi da duka hannayen shi biyu yana salati yana goge kwalla zuciyar shi na zafi sosai da kyar ya mike tsaye ya shiga ciki yayo wanka yafito, farar jallabiya kawai yasaka ya dauro alwala yafito falo bai tarar dasu Muhsin ba hakan yasa ya wuce masallaci yayo sallan la'asar ana idarwa yadawo cikin gidan afalo ya zauna yana huci yace "wlh bazan yarda ba" saikuma ya mike da sauri ya wuce dakinshi, wayarshi ya dauko yadawo falo ya zauna yakira commissioner of police ringing daya ya dauka tsabagen yanda ranshi ke tafarfasa dishewa muryan shi tayi da kyar yace "kwamission i want to file a complain yata kidnapping dinta akayi fa, first thing tomorrow morning zanzo danna baku statement dina yanzu am really not feeling well, banda lpy sosai" magana commissioner yamai kafin Abba ya gyada kai ahankali yace "ok thank you so much friend" katse wayar yayi ya jefar akan kujeran dake kusa dashi, shigowa Muhsin da Ahmad sukayi dakin kan dogon kujera suka zauna suna kallon Abban daya kafe tv da ido saikace yana gane me ake cewane dan hankalin shk baya wurin, ahankali Muhsin yakira sunanshi yace "Abba" dagamai hannu Abba yayi batare daya kallesu ba yace "please not now am begging you people kurabu dani inji da abinda ke damuna, Muhsin Ahmad kurabu dani, you boys should leave me alone, let me be" ya maida kanshi jikin kujera yana bubbuga kafa tsabagen yanda zuciyarshi ke tafarfasa, azuciye Ahmad yabude baki zaiyi magana sukaji maganan Mum daga waje, daga kai dukansu sukayi suna kallon kofan harda Abba bude kofan tayi ta shigo tana sanye cikin wani irin shiga ta alfarma, wani ubansu material ne blue ajikin ta daya amsheta sosai ta zuba warwarayen gold da sarkan gold ajikinta, fatanta yay wani irin haske tai wani fresh da lumu lumu da ita, inka ganta zata rantse ba ita ta haifi su Muhsin ba yanda takeda kyau fatarta har wani irin shining take tana wani irin kamshin turaren larabawa nan, hanunta daya rike da wayarta kirar iPhone x dake kunenta tana magana da harshen turenci dayan hanunta kuma rike da hadadden handbag dinta na vintage, gateman biye da ita yana gunguro jakan tafiyarta na LV, matsa mai tayi ya wuce ciki ya ijiye ya fito ta cigaba da wayan datake yi tana maganan kudi, wani irin kallon haushi Muhsin da Ahmad ke mata yarta ta bace saiyau zata dawo yau dinma business magana take, wani irin tashi tsaye Abba yayi yayo inda take ko kunyan su Muhsin baijiba yasa hannu yawani irin jata matsar da wayan tayi daga kunenta tana binshi tace "Alhajina is an important business call wait please mana" ko jinta baiyiba yajata suka shiga corridor tana kallon su Muhsin dasuke binsu da kallo dakinshi Abba ya shiga da ita ya fizge shigeyar wayar dake kunenta ya yar nanfa labari ya chanza salo....

Wani irin kallon Corridor Muhsin yayi yatashi fuuu yafice Ahmad ma yay tsaki yana hararan corridor yafice sukai shashin su. Sai bayan Isha'i wuraren 9 suka shigo gidan dan Ahmad kai Muhsin asibiti yayi bayan sunyi Isha dan sosai yake rashin lafiya ko kadan bayajin dadin jikinshi ga rashin cin abinci, ahankali suka shiga falon Mum suka gani tana zaune tasa wani free gown na atampa tana danna waya, tana ganinsu tai murmushi ta ijiye wayan gefe ta mike tsaye tana kallon Muhsin dataga ya rame mata sosai tace "Son menene kadawo haka? don't worry I've spoken to the commissioner myself and he assured me zasuyi kokarin nemota koma waya dauketa zai fito da ita and we will bring him to justice, ur momma is here kaji my darling" ta kalli Ahmad dake kallon ta irin kallon nan mai kama dana harara tai murmushi tace "Ahmadudu are you still angry with me? Nariga nai magana da mutanena koma ina Princess dina take za'a ganta, u guys should pray for her okay, but wai tayaya aka saceta ne wat exactly happen?" cikin fushi Ahmad yace "ki tambayi mijinki mana" wani irin kallo tamai saikuma ta daure fuska zatai magana Muhsin yawani irin ja hanunta yay hanyar fita da ita daga dakin Ahmad biye dasu yabude kofa suka fita arude Mum ta kalleshi ganin yanda yawani irin daure fuska tace "Muhsin, Son Son ina zaka ina zaka kaini, why are u dragging me like this?" wani irin bude dakin CCTV footage yayi ya shiga da ita tsayar da ita yayi agaban computer yayi ya duka ya shiga tattaba computer tana kallon computer kafin yamata playing abinda yafaru ranan yace "watch" Ahmad dake dayan gefenta yace "yes watch it Mum kitambayi mijinki where is our sis" kafe System din tayi da ido tana kallo kirjinta nawani irin bugawa, wani irin fadawa kan kujeran roban dake wurin tayi ta dafe kirji tana kallo har abin ya kare arude take fadin "innalillahi wa inna ilahi raji'un, innalillahi, innalillahi, wayyo Allah, innalillahi Alhaji???" fashewa tayi da kuka da sauri ta taushe bakinta tana goggoge idanunta ta dago idanunta ta kalli su Muhsin dasukai folding hand a kirji suna kallonta, da sauri ta tashi tafita daga dakin tana goge kwallan dayake zubo mata bada izininta ba, cikin wani irin fushi ta shiga falonsu, corridor tayi kafin ta bude dakin Abba ta shiga yana zaune kan kujera fuskarnan tashi tai shar dan yadan sami natsuwa abinda ke damunshi, tsaya mai tayi aka tana goge kwalla tace "where is Princess Alhaji?" dagokai Abba yayi ya kalleta yace "kaman ya where is princess ta bace and case din na hanun police ko and u know that very well" ihu Mum tamai tace "Alhaji ina kakai min Nadeera?" wani irin kallo Abba yamata yace "are you okay ko bakijina ne, ance tabata, ba saida nahadaki awaya da commissioner dazu ba" cikin tsawa Mum tace "am tired of your silly lies, Alhaji where is my daughter wlh koka fitomin da yata ko i will use all the money i have in this world na kulleka saika fitomin da Nadeera, Alhaji, Alhaji yanzu yarmu kake nema? How could you, yaushe kadawo haka, wani irin shameless man ne kazama haka? Yarmu kake nema Alhaji?" zaiyi magana Mum ta nunamai yatsa cikin kunan rai tace "wlh karka sake like karka fara ka shararamin karya, I've seen everything a CCTV footage, Alhaji yarmu yarmu, OMG am hurt, how could you? How could you? Wlh bazan taba yafema ba" share kwallan datakeyi tayi tana kallonshi yanda jikinshi ya saki yakuma kasa musawa, tace "tell me inda kakai ta naje na daukota? Alhaji princess zaka nema? wlh bazan taba yafema ba duniya wa lahira, inhar kama yarinyar nan wani abu wlh kotuce zata rabani dakai, like how could you, yaushe ma princess ta girma mema takeda shi ajiki dahar zakayi sha'awan ta eh? She's just 22, our poor little girl, wlh banyafe ma ba, Kai wani irin bunsur...." wani irin saukan mari dataji akan fuskarta yasa takasa karasa maganan datake shirin yi tai karan azaba tana kallon Abba dake wani irin huci yana nunata da yatsa yace "tunda kin riga kinsan komi good and fine, ubanwa yasani a matsalan danake ciki bake bace? Dakika tashi kikai tafiyan ki kin tambayen? Kafin nadawo daga Kadunan danaje ai dawowa nayi natarar kinyi tafiya, kina kula dani? When was d last time danaci abincin this your two hands acikina?" yakamo hannayenta yanuna mata yace "when was the last time da nida ke muka hada shimfida? when was d last time dana kiraki kika amsani, everyday kina meeting meeting, meeting, ni dan iska ne? Kin taba ganin nai iskanci? Tun kafin muyi aure kin sanni banda ra'ayin aure auren? What do you want me to do? Kina bani kulawa?" yawani irin daga mata murya cikin tsananin fushi yace "listen and listen very well, kin riga kinga komi so am going to tell you this Hajara, banyi regretting act dinaba kinsan mesa? Because I love her, tafiki komi, tafiki iya girki, ke saurara kiji idan inacin abincin princess jinake kaman na sume dan dadi, tafiki hankali inta ganni wani iri she always ask Abbana menene are you okay mekakeso? dawanan melodious calm babyish voice dinta dinan, tafiki taushin jiki, tafiki diri, ke tafiki komi dakika sani na ya mace, koda nai wani abu da princess i have good intention because i want to marry her and make her mine, auren ta zanyi ban yarda mun daukota tun tana yar 3month mun raineta just to give wani kato ya aure kiwon danayi ba kinajina Hajara? so am going to the court after an ganta zama araba shegen aurenta da wanan dan iskan gangster dinan ne, but get this straight to your business head i love princess and auren princess zanyi, kije chan continue with your business business tycooner, princess tafimin ke sau miliyan akan miliyan, I love her, love ma batun nayauba, kina jina? Take me to the end of the world ba court kadai ba, inhar kan princess ne nima am ready to burn down my cash sai inda karfina ya kare useless woman".
[9/13, 11:52 PM] Lady: *inkin karanta baki biyaba keda Allah*



*Maman Abd Shakur*

*22 Years Ago*!!

_Egypt Cairo_

Wata matace data dan manyanta fara haka tana sanye da doguwan riga baka har kasa tana gudu sosai kana ganinta kaga balarabiya da tsohon ciki agabanta haihuwa yau ko gobe, tana gudu agalabaice dan batada ragowan karfi gefenta kuma wani farin yarone balarabe dabazai wuce 12 years ba yana goye da wani namiji abayanshi da bazai wuce 6 years ba, yarike hanun wanda bazai wuce 8years ba duk suna gudu suna waigen baya, baya mai cikin tayi zata fadi agalabaice hakan yasa babban cikin yaran yay ihu yace "Umm" ya saki wanda ya rike yataro ta da sauri amma harta sume hakan yasa ya saukar dana bayanshi daya fashe da kuka kasa cikin harshen larabci ya kalli dan kimanin shekara takwas dake gefenshi yace "yi wasa da Abdallah" cikin kuka ya daga Abdallah dake kallon maman nasu yana jijjigashi yana wasa da hanunshi shikuma babban ya shimfidar da maman tasu da kyar akasa dajin wajen idanunshi sunyi jajir ya janye dan handbag din hanun maman tasu ya bude dan goran ruwa yaciro yabude da sauri ya yayyafa mata a fuska hakan yasa ta farfado dawani irin azababben ciwon mara da ciwon baya sosai, wani irin nishin azaba tayi tana cije baki ta kama hanun yaron tarike gam tana numfashi, arude cikin harshen larabci yaron yace "Umm menene, meke miki ciwo?" kasa magana tayi saima juyawa idanunta suka fara tanaso takara suma, da sauri wanda ke rike da Abdallah ya zo wajen ya tsugunna shima yana share hawaye ya dafa babban yana kallon maman tasu data rufe idanu cikin kuka sosai yace "meke damun Momma Ya Marwan?" rungumeshi yayi tareda karban Abdallah dake kuka sosai yana sharemai hawaye ya kwantar da Abdallah a jikinshi yana sharema Omari hawaye shima, girgiza mai kai yayi cikin murya datai rauni sosai yace "don't cry" gyadamai kai Omari yayi sanan ya sakeshi, sake yayyafa ma Maman nasu ruwa yay a fuska hakan yasa ta bude ido wani irin nishi tayi tai juyi cikin azaba sukaga jini nabin kafanta takara yin kara takara sumewa, kiran sunanta sukayi amma shiru hakan yasa ya mike tsaye, goya Abdallah yayi abaya ya kalli Omari yace "stay with Umm lemme call help" da gudu yajuya yafara bin dajin nan yana gudu da Abdallah dake kuka abayanshi yay kusan gudun 8min sanan yakai bakin titi duk wacce yagani saiya tsayar da ita yace dan Allah ataimaka musu maman su zata haihu amma ba'a kulashi ba, da kyar yasamu wata yar tsohuwa dattijuwar balarabiya ta tsaya itama dan yanda taga Abdallah na kukane ga wannashi yay zuru zuru saisa suka bata tausayi tambayarshi tayi menene yace mata maman su nada ciki jini nabin kafarta kuma sai suma take, shiru tsohuwan tayi saikuma tace nakuda ce su kaita asibiti, cikin tsananin tashin hankali yace tayakuri basu da kudin kaita asibitin ne da kyar tsohuwan ta yarda ta biyoshi masifa ma tadinga mai ahanyar dajin wai wajen yay nisa kodai yan cinkai ne, rantse rantsr ya dinga mata kafin da kyar ta yarda tabisu koda suka kai sun tarar Omari na kuka sosai Maman tasu asume jini yay

1 Comments On BOYAYYEN MUTUM
avatar
barira-umar

2 months ago

Reply

Address

Please Login or Register in order to submit comment