Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

bude dakin ta shiga gani take kaman zataga Mum tafito daga bayi ko tana zaune akan gado tana danna waya sosai take missing Mum, maida kofar tayi ta fita tana jin wani iri Mum itace annurin gidan idan bata everything looks dull, dudda su Ya Muhsin mazane basa nunawa amma suma basajin dadi in batanan, kitchen ta wuce tafara girkin, simple jellof rice tamusu da salad, ta jera akan dining lokacin karfe shida, fita tayi dan zuwa kiran Ya Muhsin dan yazo suci daidai lokacin aka bude gate, ganin motar Abban sune yasa tai wurin parking da gudun ta. "oyoyo Abba" bude kofa magidanci da zaiyi 57 years yaci farin shaddan gizna sai kamshi yake zubawa ya fito yana mata murmushi yace "princess na missing Mumyn ta daga ganin dis eyes" dariya tayi ashagwaban ce tana bubbuga kafa tace "ah'ah ni bazanyi missing dinta ba, Abbana sannu da zuwa" "yauwa princess, ya kewan Mummyn ki?" kaman zatai kuka tace "lpy lau" murmushi yasake mata yace "dauko tsaraban ki acikin mota dawasu files dina kibiyoni dasu" gyadamai kai tayi tace "to Abba" yawuce yay ciki itakuma tabude motar ta dauko jakar coldstone ice cream data gani tana murmushi sanan ta dau files din data gani ta rufe motar ta wuce ciki itama, afalo ta tarar da Abban zaune da Ya Muhsin suna magana zama tayi gefen Abba bayan ta ijiye file din akan center table ta bude jakar zatasha ice cream din, Ya Muhsin ya watsa mata harara yace "ba abinci za'aci ba bazaki bar ice cream din zuwa anjima ba akwadayya" gyadamai kai tayi asanyaye, Abba ya daure fuska yana nunashi da yatsa yace "kaga kabar min auta tahuta, koma metake so tasha ubanta yasai mata ai, bakaga maman ku batanan bawai bakasan ajiki yakamata kajataba, sha abinki kinji Princess" Abba yay maganan da sigan lallashi, girgiza kai tayi dan tasan inhar tasha ice cream dinan sai Ya Muhsin yaci ubanta ko wlh tace "Abba anjima zan sha muje kaci abinci dana dafa kaji" tashi tayi yana murmushi yace "iyye my princess harta girma ta iya girki" suka mike sukai dining suka zazzauna shida Ya Muhsin, saka ice cream din tayi a fridge tadawo ta xuba musu abincin itama ta zuba nata aka shiru anacin abincin, Abba yafara gama cin nashi ya kalleta yace "iyye princess ke kika dafa abincin nan kuwa?" gyadamai kai tayi tana murmushi, dan dariya yayi yace "masha Allah my princess is now a big girl, sai aure, gaskiya u deserve a reward" dubu goma ya kirga daga uban kudin daya ciro daga aljihu ya ijiye mata kusa da plate dinta yace "naki ne karki raba da kowa d only nurse in my house" akunyace tace "thank you Abbana" tashi Abba yayi daga dining din ya kalli Ya Muhsin dakecin abincin kaman bashi a wurin yace "hurry up son mutafi masallaci" kaman mara son magana yace "to Abba" Abba yawuce ciki yana gyara malummalum dan dauro alwala shikuma yature plate din yabar wajen, bayanshi tabi da harara ahankali tace "dadin abin Abba dai yace abincin yay dadi and see my reward" ta nunama bayanshi kudin kafin ta mike ta atttare plate din takai kitchen ta wanke ta dawo ta gyara dining din ta wuce dakinta danyin salla.

Bayi ta shiga ta dauro alwala tafito tai salla kafin ta zauna tafara karatun Al Qur'ani ana kiran isha kuma ta tashi tayi tai shafa'i da wuturi sanan ta linke dadduman tahau kan gado ta dauko wayarta kirar Samsung A70 tahau watsapp tana duba groups kafin ta bingile da chatting da Fauzy ahaka bacci yay awon gaba da ita.

🕳🕳🕳🕳🕳

*BOYAYYEN MUTUN* 🕳 🕳 🕳 🕳




*Maman Abd Shakur*

3⃣ - 4⃣


Misalin sha biyu da kusan rabi na dare wasu motoci guda uku suke tafiya akan titin hanyar airport ta wajejen daji dajin gefen hanya, titin shiru sosai babu wasu motoci dake wucewa banda su, benz guda biyu ne suka saka wata jeep din Brabus a tsakiyan su, kaman daga sama wani power bike ya yanko daga cikin dajin yahayo kan titin da wani irin fitinannen gudu, rike hanun bike din yay da hannu daya ya janye dayan hanunshi daga dayan hanun bike din yakai hanun tabayan wandonshi ya ciro karaman bindigar shi daya saka mata silencer abakin sabida kartai kara, saita bindigar yayi ya harbe tayan benz din baya, ya harbe na jeep sanan ya harbe na benz din gaba kafin yakara wani irin azababben gudu ya gaba, wani irin juyi motocin sukayi sakamakon fashewan tayan suka bubbuge juna kafin direbobin su tsayar da motocin da kyar suka kashe, bodyguards suka bubbude arude suka fito sukayo wajen motar Ogansu da suke protecting suna gyara bindigar su batare dasun damu da jinin da kansu keyiba sakamakon buguwa dasukayi, bude baya sukayi inda ogan yake dayansu yace "are you okay sir" dan inyamirin daduk ya rude yace "wat is happening" yana maganan yana kara kankame briefcase din hanunshi da kyau yana fitowa, karan fadin abu sukaji awajen kafin kace me teargas yacika wajen dan kusan guda biyar aka wurgo, kokarin ciro waya suke sukira police amma ina tari da yajin teargas yafi karfin su sukai kasa.
Wani irin juyin awizo yayi da machine din ya tsaya yana hango yanda hayakin yacika wajen kaman ana gobara, respiratory mask dake makale a jikin machine din ya dauka yasaka sabida yay protecting dinshi daga shakan teargas din, dawani irin mugun gudu yay wajen, parking bike din yayi agefe yay wani irin tsalle ya dirko daga kan machine din yana gyara zaman respiratory mask din dake fuskar shi, dayake akwai hasken mota awajen hakan yasa ya tsatsalakesu dan duksun zube akasa yay inda oga yake abaje akasa kaman matattce hannu yasa yadau briefcase din dake gefenshi yana wani irin kallon mutumin kafin yace "byeee nigga" tsallakesu yasake yi ya juyo ya kalli bishiyoyin gefen titin inda nan su Omari da kamal dasuka wurga teargas din suke yamusu alamu da gud hakan yasa suka sauko suka shige motar dasuka faka anan cikin daji suka wuce shima yahau kan bike dinshi rike da briefcase din yabi bayansu akan titin ranshi fess yana wani irin azababben gudu.

Wasu motoci dasuka zo wucewa sukaga hayaki koina ne sukai parking nesa dasu sosai suka kira FAAN, airport authority danyan India ne basuda number police, sanan suka fiffito dan zuwa taimaka musu, daidai lokacin kuma hayakin yafara washewa duk suka tashi suna tari, arude mutumin dayaci uban suit ya kalli gefen shi yaga baiga briefcase ba ya shiga dube dube arude kaman tababbe yace "g..guards" bodyguard dake kokarin kakkabe mai jiki yace "yes sir" tureshi ogan yayi ya tsugunna yana leka kasan motocin yace "where..where is my briefcase" "oga ba yana tare dakai ba" "chineke! direba we've been robbed, na shiga uku ina wayana is this how u protect me? Someone call d police cineke woo chaii!" kafin kace me police da press sun cika hanyan ana bincike.



***
Saida Abba ya shigo ya tadata da asuba kafin ya fice yay side din su Ya Muhsin ya tadasu suka wuce masallaci. Bayi ta shiga tafito daure da alwala dadduma tahau ta kabbarta salla koda ta idar azkar tayi kafin tai karatun al'qur'ani, saida gari yadan soma haske sanan ta rufe Qur'anin ta cire hijabi ta linke dadduma tafito tai kitchen, ruwan liptea ta dafa dayaji kayan kamshi wanda ya kasance dabi'ar gidan kullum sai ansha da sassafe kafin ai breakfast, babban flask da karamin flask ta dauko, zubawa tayi acikinsu kafin ta dau babban tasaka a tray da mugs tafita, side din su Ya Muhsin tayi saida tai sallama sanan ta bude kofa ta shiga, Ya Ahmad ne kadai a zaune a falon yana sanye da jallabiya fara yana aiki da system karasowa ciki tayi tace "Good morning Ya Ahmad" dago kai yayi ya kalleta yace "morning princess" ajiye tray din tayi akan center table sanan tadau cup ta tsiyaya takaimai, ajiye system din yayi gefe ya karba yana mata murmushi yace "welldone sarkin bacci jiya koda nadawo kinkai Malaysia a bacci" dariya tayi tace "kai Ya Ahmad banda shairi fa, bankaima Abba tea shiba bari naje na kaimai" da sauri ta fita daga dakin tai part dinsu hada flask da mug din Abba mai kyau a hadadden tray dinshi da mum ke hadamai abinci akai, ta dauka tai dakin Abban dashi abakin kofa ta tsaya turus jin Abba na fada. "Amina, Amina ki kiyayeni fa, baki rasaci ba baki rasa shaba na tsaremiki komi, danwa nake sana'an ni? Badan na kare mutunci gidana na wadataku da abinda kuke bukata ba? Wlh, wlh kidawo gobe goben nan, inba hakaba zaki hadu da bacin raina kinji nagaya miki, ni tafiye tafiye kema tafiye tafiye, bana gida kema baki gida, banajin ta yaranmu maza su sun girma amma Nadeera mace ce tana bukatar mahaifiyarta atare da ita wacce zata bata tarbiya ta dorata akan hanya nagari, kullum saidai kiyita barinta damai aiki kina tafiya abikinki sati daya sati biyu har uku harma wata daya wani zubin baki dawoba dan kinga ina miki hakuri, kidawo gidan nan gobe nace, gobe nabaki tom nagaya miki". Wani irin dadi ne ya lullubeta jin Abba nama Mum fada yana cewa ta dawo gobe, saida ta gyara fuskanta kar Abba yaga alamun farin ciki yasan taji maganan sanan tai sallama Abba yabata izinin shiga ahankali ta tura kofar dakin ta shiga, hadadden falone da yamakusa fin ko ina haduwa a gidan yana zaune akan rug dake shimfide a kasa falon yadan kishingida yay filo da lumstesten pilon kujera daya ajiye a kasan yana kallon tv da tashar channels television news ke aiki hanunshi rike da waya, karasawa ciki tayi ta tsugunna agabanshi ta ijiye tray din sanan ta koma kusa dashi ta lankwashe kafa tace "ina kwana Abba" murmushi yayi yana kokarin danne bacin ran dayake ciki yatashi yace "princess kin tashi lpy jiya ko abani labarin clinic sai aka bingire da bacci" dariya tayi saikuma tai kaman zatai kuka tace "Abba nagaji ne wlh muna aiki sosai ba'a barinmu muhuta" gyada kai yayi yace "dat is gud, my princess is a strong girl ai u can handle anything right?" gyadamai kai tayi tana dariya tanason Abban ta dan mutum ne dake jan yayanshi jiki, wani zubin idan mum tai tafiya tun tana yarinya yakan fasa fita office ya zauna da ita agida saisa wasu abubuwan nata ma Abba ke fara sani kafin Mum, yakoya mata homework, yatayata tsifan kitso. Flask din ya nuna mata yace "zubamin kiga princess in dumama cikina" tashi tayi ta zubamai tea a mug ta mikamai, karba yayi hankalin shi nakan TV hakan yasa itama takoma kusa dashi tamaida hankalin ta kan new din inda ake labarin fashin da akama sanate president Mr Okene chidimanda akan hanyarshi ta dawowa daga airport jiya da daddare bayan jet dinshi ya sauka a Airport, inda aka dauke akwatin da diamond that are worth $8.9b ke ciki, dudda basu iya ganin wanda yay satanba dan teargas aka bude musu ana kyautata zaton wanan notorious arm rubber dinan daya addabi politicians di garin ne, dan wanan shine mutum na shidda dayama fashi, saidai har yanzu police nakan bincike lamarin, sanan suna kara tabbatar ma da jama'an Nigeria koma waye wanan dan fashin yakusa shigowa hannu.

Ajiyan zuciya Abba ya sauke yace "Allah kyauta, Allah kara tsaremu da ahalin mu" ya kurbi tea dake mug din hanunshi, janye idanunta tayi daga tv tace "Abba wai waye dan fashin ne?" "ina aka sanshi princess? idan fa zaiyi fashin kaman matsafi, duka wayanda yamawa basu taba ganinshi ba" tabe baki tayi tace "Allah kyauta Allah tsaremu daga shairin shi, bari naje na shirya Abbana karnai latti" "kinyi breakfast ke?" girgiza kai tayi hakan yasa Abba ya daure fuska yace "oya maza je ki dafa indomie ku kici, kidai saman ma kanki something kafin kitafi kina jinako" gyada kai tayi tawuce tafita, kitchen taje ta dafa indomie da egg taci sanan ta wuce dakinta wanka tayi agurguje ganin har 7:45AM tai maza ta shirya cikin clean white iron uniform dinta tadau jakar ta da after dress dinta tafito, dakin Abba taje tamai sallama yabata 1k sanan tafito ta shiga mota Adamu yawuce da ita, yau gabaki daya murna take Abba yace mum tadawo gobe. A gate din hospital suka hadu da Fauzy daidai lokacin itama ta sauko daga mota rungume juna sukayi Fauzy tace "kai Nadeera yau kinyi kyau" fari tamata da ido tace "zaki farako" jan hanunta tayi suka wuce ciki yau saida suka fara signing in sanan suka je suka ijiye jakunkunan su kafin su wuce kowacce su ta tafi ward dinta suka fara aiki ba hutu harsai lokacin azahar sanan aka basu izinin tafiya masallaci, wucewa masallaci sukayi suna fitowa suka shiga cafeteria Fauzy tamusu order chips, juyar dakai tayi tana kallon premises din hospital din yanda iska ke kadawa kaman za'ayi ruwan sama, flowers din premises din sai kadawa suke suna making sounds, wani irin taji zuciyarta namata da bazata iya cewa exactly ga yanda yake mataba wani iri iri dai takeji, tabata fauzy tayi hakan yasa ta juyo dakai ta turo baki tace "me?" "to naga kinata kallon wajene ni bansan mekike kallo ba, are you okay?" ahankali tace "nima bansan menake kallo ba kawai nasami kaina da kallon wajenne maybe duk yunwan ce" daidai lokacin aka kawo chips din, karba sukayi suka faraci saida sukaci sukai nak sanan suka biya kudi suka fito sukai cikin hospital suna shiga sukaci karo dawata consultant wacce lecturer suce tana magana dawata patient agaban GOPD, gaisheta sukayi ta amsa musu da murmushi akan fuskanta harzasu wuce tace "ahhh Nadeera Naseer" da sauri suka juyo tace "please go to room 17F a 3rd floor namanta da folder patient din akan bed dinshi and i need it, ki kawomin am going to my office now and you Fauziya show dis woman blood bank tanaso tasai jini" atare sukace "okay ma" wajen staircase din asibitin Nadeera tayi itakuma Fauzy ta wuce da matan yayinda lecturer tasu ta wuce office dinta.

3rd floor din taje gabaki daya bangaren F din single single rooms ne, inda ake kwantar da masu kudi haka kuma irin masu matsalan brain da basuson hayaniya ko kadan ko irin wayanda akaima brain surgery dinan, babu ma hayaniya a floor din ko kadan ba'a cika barin visitors ba, wasu bodyguards tagani a passage din dazai kaika room 17F din guda biyu, dakin shi kadaine a lungun, hakan yasa tadan tabe baki aranta tai wajen batare dataji ko dar aranta ba tana kaiwa wajen ta tsaya tace "Dr ce ta aikoni" matsa mata sukayi ta wuce tai dakin bude kofan abinta tayi ta shiga tana hararan su, maida kofar tayi ta rufe ta juyo, wani Dr tagani ajikin gadon daya bata baya yana sanye da white lab coat tsaye kusa da gadon patient din hanunshi rike da alluran dayake kokarin yima drip din patient din dake kwance kan gadon, bakin abun dataga ya rufe keyanshi har zuwa side din face dinshi tabi da kallo dan kanshi sanye yake da p-cap, tsaye tayi kikam kaman gunki tacigaba da kallonshi, yana sanye da black straight trouser dayaji karin guga, sai black socks akafanshi dake cikin black Gucci cover shoe, dakin sai wani irin kamshin mayen turare mai dadi yake wanda take kyautata zato daga jikinshi ne, tsira alluran yayi a ruwan drip din da aka makalama patient din gabaki daya farin ruwan yakoma sea blue hakan yasa tabi hanunshi daya rike alluran da kallo kaman wata wawiya, ganin safan hannu akan hanunshi yasa da sauri tayo inda yake ta zagayo ta gabanshi tana magana. "Dr Mashood is it you menene a fuskark...?" kasa karasa maganan tayi ganin mutum gabaki daya fuskarshi rufe cikin mask ga bakin glass a idonshi ko lips dinshi bata gani bare hanci, wani irin kafewa tayi ta kwalalo ido heart dinta nawani irin beating tana kallonshi shima kallonta yake batare daya zaro alluran daga jikin ledan drip dinba, wani irin girgiza da patient din kan gadon yafara yasa ta kalli patient din ta wutsiyar ido batare data janye asalin idanunta daga kanshi ba jikinta yafara wani irin rawa, wani irin kumfa kumfa ne yafara fitowa daga bakin patient din hakan yasa amugun tsorace ta wangale baki zatai ihu, wani irin fizgo hanunta yayi ta taho luuu zata fado jikinshi da sauri ya matsa baya, hannu yasa abayan wandonshi yaciro bindigar dake bayan wandonshi, bindigar tabi da kallo ya daura mata akan goshi dawani irin murya dataji kirjinta yana amsawa yace "if you scream am gonna shoot you" wani irin kallon bindigar dake forehead dinta take da idanunta dataji yana jujjuya wa, numfashinta na neman daukewa idanunta na lumlumshe wa kafin dip numfashin ya dauke ta sume, luuuu tafado jikinshi asandare da sauri ya zare bindigar daga goshinta yay baya shima zai fadi dan tunda yake ko hanun mace bai taba rikewa tunda yay girma balle mace gabaki dayanta tafado jikinshi, da kyar ya iya ya dafa bango da hanunshi dake rike da bindiga, dayan hanunshi kuma akan bayanta yana kara danneta kanta na kwance a kirjinshi gudun karya saketa tafadi tai kara aji ashigo, gabaki daya jikinshi mutuwa yayi yakasa tureta yarasa yanda zaiyi ya mike baimasan mezaiyi ba first thing in history! Yayi kusan 1 minute ahaka da kyar ya tattaro dan kuzarin daya ragemai ya sanya hanunshi akan kafadunta ya fito da ita daga jikinshi ya zaunar da ita gefenshi akasan wajen, luu kanta yataho zai fada jikinshi da sauri ya mike tsaye hakan yasa ta baje a kasan tiles din, ya tsaya jikin gadon ya maida bindigarshi bayan wandonshi, sake dan kallonta yayi yanda take kwance akasan wajen saikuma ya dauke kai da sauri yana kokarin dawo da natsuwar shi, hannu yasa a aljihun lab coat din dake jikinshi yaciro wata yar karaman abu mai kama da camera, kokarin kunna ma abun yakeyi yakasa gabaki daya ya rasa natsuwar shi hanunshi sai rawa yake, ahankali yasake kallonta da sauri ya kawad dakai yace "damn it" wani irin wahalalliyar tsaki yaja jin tafiyan mutane daga ta wajen dakin, da sauri yay wurin window dakin yahaura yabi jikin pipe din bangon yay kasa ko tsoro bayaji kafin ya dirka kasa batare da kowa ya ganshi ba dan yawancin babu mutane ata back yard din hopital din, gyara zaman p-cap dinshi yayi da lab coat din ta yanda koda mutane zasu hangoshi ta window ne zasu zaci wani Dr ne, yafara tafiya kaman zaki yay wurin yar karaman kofan dake wanjen dabakowa, budewa yayi ahankali ya fice daga asibitin, wani jeep ya shiga dake pake cikin layin uban motocin da akai parking a wurin da bishiyoyin yacika, yana shiga aka tayar da motar aka bar wajen, lab coat din jikinshi yacire ya dukunkule ya yar cikin wani irin fushi da yadade baiyiba, da sauri Abdallah dake driving yace "menene Ya Marwan bakasamu kai Scanning idon nashi bane?" rungume kujeran gaba yayi kafin ya saki kujeran tareda kaima kujeran wani irin duka yawani irin mike jikinshi, jikinshi na wani irin rawa yana wani irin nishi kaman zaki, arude Abdallah yay parking abakin hanya ya fito ya zagayo ta bayan ya bude kofan ya shigo ya maida kofan ya rufe arude ya dafashi yace "Ya Marwan, Ya Marwan menene meya bata maka rai haka?" wani irin dagowa yayi wuf kaman zaki yawani irin shako wuyan Abdallah yana wani irin junjuyar dakai, arude Abdallah ya dafa hanunshi yana bubbugawa idanunshi najuyawa da kyar yace "Ya..Ya Marwan control yourself, bani bane, bani bane, is me, Abdallah ne, let me..g.."

🕳🕳🕳🕳🕳

*BOYAYYEN MUTUN* 🕳🕳🕳🕳



*Maman Abd Shakur*


5⃣


Da sauri ya sakeshi kaman wani zararre hakan yasa Abdallah yafara wani irin tari, sake dukan kujera yayi kaman zaki zuciyarshi na tafarfasa yace "I will kill her" kakkabe jikinshi yashiga yi sabida yanda yaji yake kamshinta, gabaki daya kamshin jikinta kawai yakeji ko ina a jikinshi keyi duk inda yajuya kaman zaiyi hauka haka yakeji, ihu yayi ya dunkule hannu ya daki iska yace "damn, damn, damn it! saina kasheta, ubanwa yace tai hugging dina". Dago jajayen idonshi yayi tsabagen shakan dayasha ya kalli wan nashi da sauri ya kara matsawa kusa dashi ahankali yace "calm down, calm down Ya Marwan, have you forgotten what momma told you about your anger issue eh Ya Marwan?" juyo dakai yayi ya kalli kanin nashi, shiru yayi yana kallon yanda wuyanshi yay ja abunku da fari yay shaida da sauri ya matsa kusa dashi ya taba wuyanshi ahankali yace "who did this to you?" shiru Abdallah yayi saikuma yay murmushi yace "nevermind, ai am fine" rungume kanin nashi yayi da wata irin murya datai rauni sosai yace "am sorry Abdallah i know is me, nasan ninayi ma haka please forgive me, i don't know what got into my head, Abdallah am sorry okay" dan dariya yayi yace "am fine trust me Ya Marwan but meya bata maka rai haka ne, wakake cewa u wanna kill?" sakin shi yayi yakoma gefe ya daura kanshi akan kujera yay shiru batare daya bashi amsa ba, hakan yasa Abdallah ya juya yabude motar yafita, binshi yay da kallo kafin ya juyar da kanshi dayan side din ya lumshe ido da sauri ya bude ganin fuskar yarinyar dake sanye da kayan nurses ta kwalalomai ido tana kallonshi, dukan kujera yasake yi yace "damn it, i will kill her, saina kasheta" Abdallah dake kallonshi ta madubi jiyayi kaman yama yayan nashi kuka, kafin sukai gida wani irin mugun zazzabi yarufe shi, shi arayuwan shi baitaba jin abinda yaji yauba, yasaba rayuwan shi dagashi sai kaninshi, mace dai saidai yagansu ahanya ko awani wurin suna tafiya. Sunyi tafiyan dayakai kusan 35 minutes kafin Abdallah yay horn agaban gidansu kamal ya bude musu, shiga yayi ya kashe motan ya fito ya zagayo ya bude bayan ahankali yana dafa kujera yafito daga motan ya tsaya da sauri ya dafe motan jin jiri na neman kwashe shi, da sauri kamal wanda yake abokin Abdallah daya gama kulle gate yakaraso wajen yana kallon Marwan din daya dafe mota yace "wah happen to him Friend? Why is he like this baida lpy ne?" Abdallah dake kokarin kama hanunshi yace "wlh i have no idea" tattaro karfinshi yayi ya tashi daga jikin motar yay cikin gidan yabude kofa ya shiga ciki jiri na dibanshi, upstairs yayi ya bude kofar wani daki ya shiga hadadden dakine da akai komi off white dakin kaman nawani dan president, kan lumtsatsen gadon ya fada yaja bargo yarufa ya dukunkune dan wani irin sanyi yakeji sosai.

Kamal ne ya dafa Abdallah dayay mutuwar tsaye jikinshi duk yay sanyi yanabin kofar da wan nashi yabi ya shige ciki da kallo hawaye sun taru a idonshi sosai, jijjiga kafadarshi Kamal yayi yace "dalla chill karka damu kanka he will be fine yasaba fushi haka ai" hannu yasa ya sharce dan gutun hawayen daya bullo daga idonshi ya girgiza kai har lokacin bai janye idonshi daga kofan ba yace "i don't think so, this anger is different from wanda yasaba yi, kamal i don't want anything to happen to my brother, he has suffered enough a duniyan nan, i hate, hate, hate it wen he's suffering wen he's mind is not at peace" ya karashe maganan hawaye na gangarowa daga idanunshi, "kai wai me haka dalla kadena kuka dont break my heart as well, muje mukira mai Baba maybe yafada mai wat d problem is" Kamal yay maganan yana janshi amma ko motsi baiyi ba ahankali yace "kana ganin zai fada?" yay maganan yana janye idonshi daga kofan ya kalli Kamal, gyadamai kai kamal yayi yana murmushi yace "sosai ma kasan he has alot of respect ma Baba,

1 Comments On BOYAYYEN MUTUM
avatar
barira-umar

2 months ago

Reply

Address

Please Login or Register in order to submit comment