Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

let's give it a try muje Baba na masallaci" gaba kamal yayi Abdallah na biye dashi, tare sukaga tsohon da akalla zaiyi kusan 70 ko 71 tareda Omari dayake biyamai karatun Al Qur'ani, saida suka jira suka kai karshen aya sanan suka fada musu Ya Marwan ba lpy, Omari ma kusan yafisu tashin hankali rufe Qur'ani yayi ya ijiye a inda ake ijiyewa yafita daga masallacin da sauri su Baba biye dashi da sauri yay sama ya bude dakin ya shiga wajen gadon yayi ya tsugunna yana kallon mask din fuskarshi, ganin yanda numfashinshi ke fita ahankali yasa yakai hanunshi ya daura kan wuyanshi da safan fuskan ya sauka har wajen zafi yaji hakan yasa yadan yayi bargon ya kamo hanunshi ya hada da nashi kafin ya daura kanshi akan gadon yay shiru yana sauke tagwayen ijiyan zuciya, dafashi Baba yayi yace "bacci yakene Omari?" gyada kai yayi batare daya dago kaiba, hakan yasa Baba yace "to Allah kara sauki katashi kaje kasiyomai magani ne inya tashi yasha kasan zazzabi batamai kyau" gyada kai yasake yi batare daya juyoba hakan yasa Baba ya juya ya kalli Kamal da Abdallah da idanunshi sunyi jajir yace "ku muje ku barshi yay baccin shi" bayanda suka iya suka juya suka fita suka rufo musu kofan, yafi 5mins ahaka kafin ya dago kanshi ya tashi tsaye idanunshi sunyi ja ya tsaya yana kallon Marwan din saikuma asanyaye ya fita daga dakin ya sauka kasa car key yadauka yawuce waje yadau wata bakar mota kirar Kia yafice.


***
Saukan ruwan sanyi dataji akan fuskarta yasa tawani irin ware ido at once kafin tasaki wani irin uban ihu tana kalle kallen dakin. "malama ki natsu" taji an mata magana, dago kanta tayi atsorace taga wani matashin police ne dabazai wuce 29 hakaba akanta rike da bottle water mai sanyi wanda tana kyautata zaton shi aka zuba mata, bayanshi wasu police ne guda biyu sai HOD dinsu dakuma consultant din data turota zuwa dakin saikuma wata mata da taci uban gayu kanta tasha attachment dake gefe tana goge idanunta dasukai ja sosai dawani farin handky, sai kuma security biyun dake bakin passage dinan, wani irin rawa taji jikinta ya dauka kanta nawani irin ciwo tana binsu da kallo daidai dai dai, farin jaka da aka jefa alluran da wanan mask man yama patient dinnan anyi zipping kan ledan police din ya nuna mata yana mata wani irin kallo yace "a ina kika samo alluran nan?" kallon alluran tayi kanta nawani irin sarawa dan har ga Allah bama ta gane alluran ba, girgiza kai tayi da bakinta daya mata nauyi sosai muryanta narawa tace "ni, ni bansan alluran nan ba" wani irin kallo inspector da aka rubuta Inspector Aliyu Alkali ajikin tag dinshi yamata kafin yamika hannu police din bayanshi yasaka mai ankwa, cije lips dinshi yayi yana kallon fuskarta yace "fine i think zaki fadi gaskiya in munkaikai station" yawani irin kamo hanunta yana handcuff din akai yana kullewa. "you are hereby arrested for injecting a patient with deadly substance, you have the right to remain silence because anything you say or do could be use against you in the court of law" arude ta kalleshi heart dinta nawani irin racing da tunda take a duniya batajin zuciyarta yataba irin gudun nanba, dagata yayi kaman wata kaya hakan yasa tai baya luuuu ta sake sumewa, watsa mata ruwan yayi a fuska yana tsaki hakan yasa tasake bude ido tanajan numfashi nunama police biyun dake gefenshi ita yayi yace "kutafi da ita mota am coming" janta sukai luu sukai waje da ita, binsu kawai take dan sosai kanta ke juyawa hankalin tama baya jikinta kalman arrested kawai ke yawo akanta, kallon Su HOD yayi bayan ya zuba hannu a aljihu yace "keep me posted akan condition din patient din" yajuya yafita daga dakin.

🕳🕳🕳🕳🕳

*BOYAYYEN MUTUN*🕳🕳🕳🕳




*Maman Abd Shakur*

6⃣


Tunda polisawa sukazo yan asibiti da students suka taru sakamakon yanda motocin su ke kuka, hana kowa hawa stairs din sukayi akai sama, Fauzy da dawowan ta kenan daga kai matar Blood bank taga polisawa sunyi sama gabanta ya shiga faduwa ta shiga tambayan students din wajen ina Nadeera dan azatonta harta dauko folder tadawo zata wuce common room kenen kaman ance ta daga kai taga polisawa guda biyu nawani irin jan Nadeera dakd kuka suna saukowa gashi sunsamata handcuff, salati Fauzy tayi hawaye na gangaro mata tai bakin benen da sauri tana tuttura mutane tace "Nadeera wat happen" kafin ma tai magana polisawan sunyi waje da ita, goge hawayen dake zubo mata tayi da gudu tai common room dinsu jakarta ta bude hanunta har rawa yake taciro wayarta ta kunna contacts ta shiga tafara dubo number yan gidansu, na Ya Muhsin tafara cin karo dashi hakan yasa tai dailing number shi, har yagama ringing ya katse bai dauka ba tamai na biyu ana ukune ya dauka ahankali yace "sis ya kike?" cikin tsananin tashin hankali tace "Ya Muhsin anyi arresting Nadeera" takarashe maganan muryanta na rawa sosai kuka na neman kufce mata "what! Mene?" Yafada yana mikewa daga kan kujeran office dinshi, gyadamai kai tayi kaman yana gabanta, cikin kuka tace "eh anyi arresting dinta yanzunan polisawan suka wuce da ita, i don't know what happen amma har handcuff sun samata a hannu" katse kiran yayi yadau car key dinshi dake kan table yafita daga office din yana gyara zaman tie din wuyanshi, lift yashiga ya kaishi kasa ya fita yay parking space da sauri ya shiga mota yaja yafita daga building din, tafiyan dabazai wuce na 15 minutes ba yakaishi police station din dayake kyautata zaton nan aka kaita danshine wanda yake close to hospital dinsu, parking yayi yafito yana gyara zaman black suit din jikinshi daya kara fito da kyanshi da kamaninshi da Mum, shiga police station din yayi gabaki daya ranshi abace, police din dake gaban kanta yasama yace "anan aka kulle Nadeera Naseer?" "bari na duba yallabai" bude book din gabanshi yayi yana dubawa kafin ya dago yace "eh nanne amma inkanaso ka ganta saikabi ta hanun Inspecta Aliyu Alkali, bari namai magana" da sauri ya juya yay hanyar office din da aka rubuta inspector ajiki, gabaki daya boiling yake yana girgiza key motar hanunshi yanadan bubbuga kafa akasa, ko minti biyu ba'ayi ba police din yadawo yace "you can go in yallabai" sa kai yayi ya shiga ciki bude kofan office din yayi ya shiga office din yakarasa gaban table din yana kallon Inspecta Aliyu da shima kallon Muhsin din yake, batare daya zauna ba yaciro ID card dinshi ya nunamai yace "Barrister Muhsin Naseer, Am Nadeera's Lawyer and brother as well, on what charges kai arresting sister na? And as her lawyer i demand to see her" gyara zama yayi Inpecta yayi yana kallonshi, ajiye pen din hanunshi yayi kan table yahade hannayen shi yace "munyi arresting dinta sabida tai injecting patient which happen to be the minister of finance dayay hatsari kwanakin baya yasamu bugewa akai da deadly substance, ur sister ka kira ta ko? Ko client dinka nema whatever dai try to intentionally murder a patient daga aikenta zuwa dauko folder, dazaran mun soma interrogating dinta saita dinga mana suman pretense" wani irin kallo Muhsin yamai kafin yace "inaso na ganta nace" "sure" Aliyu Yafada tareda mikewa yadau hulan polisawan shi dake kan kujera ya kafa akai yadau kulkin shi yana wani irin bubbuga wa a hanunshi ya zagayo ya kalli Muhsin yace "follow me" fita yay daga office din Ya Muhsin biye dashi, wani lungu sukabi da cells daban daban da aka kukkulle mutane aciki suke, agaban wani cell ya tsaya ya zare uban keys din daya makala jikin wandonshi ya ciro daya yabude makullin cell din dashi yabude kofan, dakine dababu komi aciki sai simenti saikuma dan dakali haka dawani wash hand basin dayay baki dake gefe, tana zaune akasa ta jingina da bango ta cusa kanta acinya tana kuka farin kayanta duk sunyi stain din datti.
Da hannu ya nunamai cikin cell din yace "gatanan" hakan yasa Ya Muhsin yatako zuwa wajen ya tsaya ajikin kofan yana kallonta sosai heart dinshi yay breaking, ahankali yace "Nadeera" dago fuskarta da hawaye yagama wanke wa tayi jin muryan Ya Muhsin ta kalli Yayan nata idanunta tsabagen kuka har kumbura sukayi wani irin tashi tayi jiri na dibanta tayi kan Ya Muhsin da gudu, fadawa jikinshi tayi tafashe dawani irin kuka mai kara tana shesheka, patting bayanta yayi yace "is okay, stop crying" dago kanta yayi jin yanda jikinta yay zafi sosai yana kallon fuskarta ya tura hannu a aljihun shi yaciro handky, share mata fuskarta tass yayi yace "stop crying, tell me what exactly happen?" rirrikeshi tayi tana nishi tsabagen yanda kuka yaci karfinta tana kokarin magana heart dinta na racing ta kasa ita tsabagen yanda zuciyarta ke gudu kaman zai fito ta baki, tunda take bata taba shiga irin tashin hankalin nan arayuwanta ba ita a police station no, agabanta aka karya mutane biyu dazu, kokarin yima Ya Muhsin bayani take takara tafiya luuu zata zube akasa da sauri ya tarota jikinshi yana kiran sunanta "Nadeera, Nadeera" shiga cell din yayi sosai ya zauna kan dakalin tana jikinshi tapping fuskarta yayi adan rude yace "Nadeera, Hey, Princess" "ahap kaga abinda take tamana kenan tunda muka kawota, dama idan criminal yay committing act aka kamashi he always come up with stuff like this dan mu tausaya musu mu..." "will u shut d fuck up and get me water bakaga ta sumaba ne?" Ya Muhsin yay maganan angrily, wani irin kallo Inspecta yamai yace "suman pretense ba, zama ta farfado ne bata bukatan ruwa" wani irin mugun bacin rai ne ya dira a zuciyan Ya Muhsin ya kalli Inspecta dayakeji kaman ya shake shi yace "am gonna sue you for this, i will sue you for breaching human rights, tanada right tai accessing health care and medication, she's not doing well and u people ignore that calling it a pretense" dan sosa kai inspecta yayi ganin yanda Ya Muhsin is serious kuma yasan gaskiya ne duk abinda yace, dan sassauta murya yayi yace "to ai naga she's a nurse ne she can help her self?" wani kallo Ya Muhsin yamai hakan yasa yace "fine am sending water for her now" yajuya yabar wajen hakan yasa Ya Muhsin yasake tapping kumatun ta yace "princess open your eyes, Nadeera" daura kanta yayi akan kafarshi ya tattare karamin hijabin ta dasuka gama jikawa da ruwa, cirewa yayi hakan ya bayyanar da kananun kalabanta datai parking ya shiga pipitata da hijabin daidai nan wata police woman ta shigo da bottle water ta bashi da sauri ya karba ya bude ya debo ruwan kadan a hannu ya yayyafa mata a fuska hakan yasa ta bude ido dasukai ja ahankali tana kallonshi asanyaye tana sauke ajiyan zuciya, murmushi yamata yace "hey karki kara suma am here, karki karajin tsoro" handky yasa ya goge mata fuskar tass ya dagata, fashe mai da kuka tayi tana rikemai hannu tana kallon kofan cell din, kankameshi tayi sosai tafashe da kuka tana kallon kofa tace "Ya Muhsin dan Allah karka tafi kabarni wlh karya mutane sukeyi, agabana suka karya ma wani hannu, wani kuma kafa" takara she maganan tana wani irin nishi zata sake suman hakan yasa yace "Nadeera look" bottle water ya kafa mata abaki dan yanda lips dinta suka bushe shows she's dehydrated da kyar tasha ruwan sanan ya ijiye yasa kanta akan kafadarshi yana shafa kanta hakan yasa tasomajin natsuwa sunfi 2min ahaka sanan ya saketa ya kamo habarta yace "fadamin maiya faru no more cry babu abinda zasu miki am here" gyadamai kai tayi kafin ta shiga bashi labarin komi. "Ya Muhsin BOYAYYEN MUTUN dinan ne, i have nothing to do with all wat they're saying wlh" "is okay tashi muje" dagata yayi yadau hijabin ta yasaka mata ya kamo hanunta yarike ganin yanda kafafunta ke rawa suka tafi office din inspecta, kafesu da ido Inspector Aliyu yayi harsuka karaso gaban table din ya zaunar da ita akan kujeran gefenshi, kallonta yayi yace "tell him wat you saw" gyadamai kai tayi tana kokarin hana kanta hawayen dake shirin zubowa ya juyo ta kalli Inspecta dake kallonta tafada mai duka abinda yafaru, murmushi yamusu yace "to tayaya BOYAYYEN MUTUN din dakike cewa yawuce 2 security dake bakin passage din yaje dakin? And how did he get out batare da kowa ya ganshi ba? Koshi aljani ne?" hawaye ta share tace "wlh am saying d truth ba karya nakeyiba" ganin yanda takeyi yasa Ya Muhsin yace "since the patient is still alive inaso nai bailing dinta" hulan kanshi yacire yace "okay fine amma with the condition duk lokacin da muka bukace ta zaka bayyanata, anytime her presence is required she will appear" jiyayi kaman ya buge bakin dan iskan inspecta, cije lips yayi yace "fine!" bail documents yatashi ya dauko yabashi yace "sign" byro yaciro Nadeera na binshi da kallo yay signing sanan ya mikamai takardan mikewa yayi ya dagata yarike hannunta sukai kofa. "bye queen of suma" wani irin kallo Ya Muhsin yamai itako ko juyowa batayi ba hakan yasa Inspecta yay dariya yace "Yayan mu zaka bani ai ko dan gaskiya ina ciki" wanan kara juyowa Muhsin yayi completely yana rike da hanunta ya kalleshi nakusan 2min fuskarshi babu alamun wasa yace "stay within ur limit" yaja hanunta tareda bude kofan suka fice a kanta suka hadu da Abba da Ya Ahmad dake tsaye suna jiran Muhsin dan police din wajen yace musu lawyer ta yariga yazo hakan yasa suka gane Fauziya ta kira Muhsin kenan shima, kafinma su karaso Abba da Ya Ahmad sukai wurinsu hankali tashe suna kallon yanda Nadeera tadawo mara lpy mara lpy, fadawa jikin Abba tayi ta fashe dawani kukan, Ahmad ya kalleta sanan Ya kalli Ya Muhsin yace "what happen bro Fauziya ce dukta kiramu tace anyi arresting dinta" yatsine fuska yayi yana kokarin ciro phone dinshi daga aljihu yace "is a long story muje gida kawai, Abba mutafi" "kagama komine?" Abba yay maganan yana share mata fuska tareda rike mata hannu, ahankali yace "eh nagama kuwuce da ita gida am going to the hospital now" fita duk sukayi atare Abba da ita suka shiga bayan motar Ya Ahmad ya Ahmad kuma ya zauna a mazaunin driver shikuma Ya Muhsin yay wurin motarshi ya shige yaja yay dan zuwa hospital dinsu.

🕳🕳🕳🕳🕳

*BOYAYYEN MUTUN*🕳 🕳 🕳 🕳




*Maman Abd Shakur*

7⃣

Wuraren shida na yamma yatashi awahale sai atishawa yake, addu'an tashi daga bacci yayi kafin ahankali ya sauko daga gadon yana atishawa juyawa yayi ya kalli ac yaga ko akunne ne amma akashe hakan yasa yajuya ya bude kofan bathroom ya shiga, wani irin hadadden babban bathroom ne mai hade da closet an raba wajen part biyu bangaren dama wani irin hadadden closet ne komi na wajen blue, ga kaya kala kala dake jikin hanga ga kuma yar stool a tsakiyar wajen sai bangaren haggun kuma koface wacce bayi ke ciki bude kofan yayi ya shiga.

Yay kusan 15 minutes kafin yafito daga bathroom din sanye dawani maroon hoodie da aka rubuta gifted agaban daya daura hulanta akai sai dogon bakin wando da bakin safa akafanshi sai uban kamshi yake, jinginar da kanshi yay ajikin bangon dakin kafin ya dago kai ya dunkule hannu ya daki bangon dakin da karfin bala'i yana tsaki ganin hoton fuskar Nadeera yakara flashing aranshi, dadduma ya shimfida yay sallan la'asar koda ya idar akan dadduman ya zauna ya daura kanshi akan gwuiwanshi, tsaki yaja yace "damn it" fuskar mace bai taba tsayamai arai kaman na yarinyar nanba but why?! Kiran sallan dayaji daga masallacin gidansu yasa ya mike tsaye, slippers ya zira da sauri yana atishawa yana hamdala yabude kofa yafita daga dakin, sauka yayi yafice yay masallaci danyin sallan magrib. Ko amasallacin magrib da isha'i aka hada sabida hadarin daya hadu sosai yana idar da azkar ya mike yafice daga masallacin kafin su Abdallah su rikeshi da magana dan ko kadan bayaji magana, stairs yahau ya bude kofa ya shiga dakinshi mayar da kofan yayi ya rufe harda saka key ya jingina da kofar yana sauke ajiyan zuciya, atishawa yayi yay hamdala kafin ahankali ya daura hannunshi kan heart dinshi da duk single beat remains him of her in his arms, ahankali ya daga kai ya kalli plain white chiffon curtains din dake jikin babban window dakinshi dake kadawa sosai sakamakon iskan da akeyi na shirin ruwa, garin yay duhu sosai kaman irin tsakar dare dinan sabida hadari sai walkiya sama take, ahankali yatashi daga jikin kofan yafara tafiya kaman kwai yafashe mai aciki yay wurin window ya tsaya ahankali ya mika hannunshi ya shafa labule slowly kafin yakai dayan hanunshi yasa duka hannayen shi ya raba curtains din kowanne yatafi bangare daya hakan ya bayyana window daya dan budu kadan, hannu yatura ya bude window duka waaa, yadaga kai yana kallon sama, bai damu da ko sauro ko wasu kwarin su shigo mai dakiba, shiru yayi yana kallon sama iska da kamshin kasa dana trees yawani irin blowing suna ratsa duka jikinshi suna karasashi jin wani iri da baitaba jin kanshi aciki ba, ahankali ya mika hanunshi ya fitar dashi waje ta window yana feeling yanda iska ke dukan hannu dan yayyafin da ake na zuba akan hannun, hanun ya kafe da ido jikinshi namai wani iri ahankali yace "what is happening to me?".




***

Gida suka wuce suna shiga har dakinta Abba ya kaita yace "jekiyo wanka ki chanza kayan nan kici abinci zai aika Ahmad ya siyo miki magani karki damu everything will be fine" gyadama Abba kai tayi ta wuce bayi tana atishawa tanajin wani irin sanyi ajikinta hakan yasa ta shiga bayi da sauri, wanka tayo da ruwan zafi ta dauro alwala kanta nawani irin ciwo tafito, gaban wardrobe dinta taje tajawo wani dogon riganta baki ta zira ta saka hijabi tahau kan dadduma da kyar tai sallan la'asar dan sosai kanta ke mata ciwo gashi sanyi takeji sosai tana idarwa tacire hajabin tafada gado ta lullube da bargo tana godema Allah da ya tsareta yau bata mutu ba da wanan BOYAYYEN MUTUN dinan fa ya harbe ta, atishawa tafarayi tayi sunkai biyar ajere hakan yasa takara jan banrgo ta dukunkune ahaka bacci yay gaba da ita koda Abba ya shigo dan kiranta taci abinci bacci yaga tanayi hakan yasa ya kashe mata wuta yafita da Ya Ahmad sukaci karo shima zaizo dubata hakan yasa yace "tai bacci son" gyada kai yayi yajuya yay falo shikuma Abba ya wuce dakinshi dake nan corridor zama yay akan daya daga cikin kujerun falon ya zauna wayanshi yaciro daga aljihu number dayay saving da Sweetheart yaciro yay dailing har yagama ringing ba'a dagaba, nabiyu ma haka ana uku ne aka dauka daga ta chan bangaren Mum tai magana ahankali tace "Alhajina please ina meeting da some investors ne, i will call you back i promise Alhajina" ta katse wayar dip, wayar Abba yacire daga kunenshi yabi wayan da kallo yanajin wani irin haushi a ranshi, ajiye wayar yayi ya gyara zama yana kallon news, saida aka kira magrib sanan yatashi ya shiga bayi dakenan falon shi ya dauro alwala ya chanza kayan jikinshi zuwa jallabiya brown sanan ya fito, dakinta yafara shiga har lokacin bacci take tadata yayi ta tashi sanan ya wuce masallaci, da kyar ta lallaba ta shiga bayi alwala ta dauro ta fito tasaka hijabi tai magrib rashin karfin datake dashi yasa bata iya karanta Al Qur'ani yauba, tashi tayi ta bude kofa tafito tayi falo kitchen ta shiga ahankali ta jona ruwa a heater kettle yana tafasa ta hada tea mai kauri ta dawo dining ta zauna tana juya spoon a cup din tana kallon tea, wani irin kewan Mum takeyi bana wasaba sokawai take ta rungume Mum taji dumin mahaifiyar ta kotaji natsuwar datake nema, ahankali ta cire spoon din ta ijiye ta dau cup din takai baki tafara sha sanan ta sauke cup din tana kallon tea dako kadan baya mata dadi, sake kafawa abaki tayi ta kwalkwale sanan tadau spoon din tasaka acikin cup din tamike ahankali ta shiga kitchen din tsayawa tayi awajen tap din tana dauraye kofin tana kallon window kitchen din yanda gari yay duhu sosai sakamakon hadarin daya hadu sai walkiya ake, wani irin abu taji yana fizgar ta hakan yasa ta ijiye kofin ahankali tai wajen kofan dazai sadata da backyard tabude wani irin iska ne ya hurata hakan yasa tadan lumshe ido kafin ahankali ta budesu, kallon sama tayi yanda ko ina yay bakinkirin hazo sai tafiya yake wani irin iska mai dadi dake kamshin kasa na shiga hancinta, sosai take kallon sama jikinta nawani iri, lumshe ido tayi sakamakon yayyafin da aka fara wani iska dayazo ne ya feso da yayyafin akan fuskarta runtse ido tayi sosai kafin ta bude idon ahankali tana kallon sama tace "maisa nakeji kaman wani abu zai faru da rayuwata? Why do I feel as if something is about to happen? Ya Allah please protect me, am very very scared of him, ko rufe ido nayi saina ganshi, i can't get his face out of my head, Ya Allah am afraid of this mask man, ya Allah ka kareni ka tsareni" jinkinta ta rungume yayyafin na feso mata tana kallon saman da wanan karan yay duhu sosai, tai nisa acikin tunani, hannu taji akan kafadarta hakan yasa tasaki wani irin ihu tajuyo afirgice Ya Muhsin tagani tsaye abayanta yana mata wani irin kallo yace "Ke mehaka wai mekikeyi anan bakiga ana yayyafi bane jibi yanda ruwa ya jikaki" yanda ta kwalalo ido tana kallonshi fuskan shi na rikadan mata zuwa fuskan boyayyen mutum, runtse ido tayi da sauri ta kankame jikinta breath dinta na neman daukewa, jijiga kafadunta yayi yace "Nadeera" ahankali ta bude ido ta kalleshi ta lankwasa kai ahankali tace "Na'am" matsar da ita gefe yayi ya kullo kofar kitchen din sanan yajuyo ya kalleta yace "are you okay? Me matsalar ki?" girgixa kai tayi hawaye na taruwa a idonta ahankali tace "am just missing Mum" "don't worry takusa dawowa, Ahmad yakai miki magani daki jeki sha" gyadamai kai tayi tabi gefenshi tafice daga kitchen din da sauri, bin kofar databi yayi da kallo kafin ya bude fridge yadau cold maltina yafita daga kitchen din yay dakin Abba.

🕳🕳🕳🕳🕳

*BOYAYYEN MUTUN*🕳 🕳 🕳 🕳



*Maman Abd Shakur*

8⃣ - 9⃣

Sallama yayi Abba yabashi izinin shigowa hakan yasa ya shiga yana shan malt din dake hanunshi ya maida kofar yarufe yakaraso nan kusa da Abba a kasan carpet ya zauna yace "sannu da hutawa Abba" alamu Abba yamai dakai na yauwa dan ranshi abace yake har yanzu Mum bata sake kiraba, ajiye malt din hanunshi gefe yayi yace "Abba I've been calling Mum yafi sau uku she's not answering, gaskiya Abba tadawo this girl need her mana, she looks lonely gatanan duk kalan tausayi tausayi, yanda zatai feeling taji tamanta da matsalolinta a jikin Mum bahaka zataji a wurin muba, please Abba Mum should come back kace tadawo." "and kana tunanin bance mata tadawon bane?" Abba yay maganan yana raising ma Ya Muhsin voice ranshi abace, yanda Ya Muhsin ya tsaya kallonshi da mamaki ne dan da wuya kaga Abba yay fushi hakan yasa ya dafa kanshi nayan sakannni kafin ya shafa fuskarshi ya sassauta muryanshi yace "Muhsin lemme advice akan wani abu, inhar lokacin auren ka yatashi karka sake ka yarda da any conditions da wacce zaka aura zata kawoma na zata dinga tafiye tafiye tana business, Mum dinku ko hmm" sai kuma yay shiru kawai batare daya kara wata maganan ba, ganin yanda Abba is

1 Comments On BOYAYYEN MUTUM
avatar
barira-umar

2 months ago

Reply

Address

Please Login or Register in order to submit comment