Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

sukai jajir ya shigo dawani abokinshi Bello dauke da makara dakuma babban tabarma, wani irin nishi Abba yafara yi yana kallon Ahmad din dako kallon inda Abban yake baiyiba suka ajiye komi akasa yazo ta gaban gadon shida abokinshi zasu dagashi da sauri Abba ya mika hannu zai dagashi Ahmad yamai wani irin kallon da idanunshi dasukai mugun jajir saida gaban Abba yafadi ahankali ya janye hanunshi ya maida kirji kaman mai shirin yin salla yana kallon Ahmad din, Ahmad da abokin nashi sukadau Ya Muhsin suka sakashi a tabarman suka sakashi a makara suka dauka suka fita daga dakin Mum nawani irin kuka tabisu da gudu Abba ma yabisu da sauri ko kallon su Ahmad baiyiba suka sakashi cikin motan ambulance din asibitin dasukai haya suka shiga kafin Mum dake kuka sosai da Abba su iso yawani irin rufe motan yacema direban su tafi suka fita daga asibitin, Mum ta tsugunna a wurin tana wani irin kuka kaman zata mutu bama tasan meke mata dadiba, Abba ya tsaya akanta yana kallonta ahankali yace "H...Ha..Hajara, tashi mutafi, kinji tashi muje" ahankali Mum tamike kaman tababba tace "a'a ina zani dakai wajen Muhsin zani shi kadai muka bari adaki" da sauri ta juya zata koma cikin hospital din Abba yarike hanunta da sauri yace "Hajara dubi, kalleni" cikin kuka sosai ta kalli Abba, Abba yace "Allah yafi nida ke son danmu, dama kuma shiya bamu shiko?" yatambayi Mum ahankali, da sauri ta girgiza mai kai hawaye na bulbulowa Abba yace "to Allah yama Muhsin rasuwa, addu'a zamumai ba kukaba kinji, yanzu zomu tafi gida naga banga motar ki a parking space ba, bakizo dashi bane" gyadamai kai Mum tayi tana wani irin kuka, juyawa yayi ahankali rike da hanunta ganin bata hayyacinta yay bakin gate da ita, yatare musu taxi suka shiga suka zauna yaciro wayarshi yafara kiraye kirayen abokan arziki da abokan business.




***
Dan shiru tayi tai dan murmushi kadan ta dauke kai batare datace komiba tadan matsa gefe sabida yanda suke kusa kusa da Marwan daketa daddanna system abinshi kamshin shi na fizganta, dan dago kai tayi karaf suka hada ido da Abdallah daketa kallonta hoping zatace wani abu again, dan hararan shi tayi tana wasa da yatsun ta tana turo baki tana kukkuni kasa kasa tace "ni banason ana kallona fa" "lalalala" Abdallah yafada yana saukar da kafanshi kasa, da sauri ta kallai murmushi yay escaping bakinta, ta wutsiyar ido Marwan keta kallonta, Abdallah ya kalli Ya
Marwan yace "Ya Marwan wlh kama amaryan ka magana ba kaga tanamin kukkuni ba" murmushi sosai tayi, hakanan batasan mesa she always find the guy funny ba, kamanYa Ahmad haka yake mata, ahankali Marwan ya janye system din yana wani irin kallon ta kaman yahadiyeta yakasa magana, turo baki Abdallah yayi kaman zaiyi kuka yace "Ya Marwan bakace komiba kagama dariya takemini" murmushi tayi sosai harda daura hanunta akan fuskarta, daidai lokacin aka bude kofa Omari ya shigo dakin dauke da sallama shima idanunshi akan kanwar tasu da sauri Abdallah ya kalleshi kaman zaiyi kuka yace "Ya Omari kaga amaryan Ya Marwan na tsokanana ko, wlh this nurse ko she's so tsokanacious" fashewa tai da dariya hartana bige kafan ya Marwan, dukansu tsayawa sukayi suna kallonta barin ma Ya Marwan dake gefenta dayakeji kaman ya tsaga jinin shi ya sata ciki, Ahankali Omari daya kasa dena kallonta ya shigo dakin ya zauna gefen Abdallah gani yayi dariyanta kaman na Momma su, da kyar tai shiru tana murmushin data dade batai irinshi ba dimples dinta nawani irin lotsawa, dukan cinyan Omari Abdallah yayi yace "ehen nurse zokiga Ya Omari yaji ciwo a hannu dama dazu yabige da table ko Ya Omari?" kallon Abdallah Omari yayi, Abdallah ya kannemai ido hakan yasa Omari ya kalleta suka hada ido yace "y..y..uhm" da sauri Abdallah ya fizge hanunshi yaja hanun riganshi sama yace "zoki gani nurse" make kafada tayi ahankali tana leken hanun nashi daga inda take zaune tace "aini banga ciwo a hanunba, in bigewa ne jamai kawai za'ayi zai dena zafi, kajamai" da sauri Abdallah ya kwalalo ido yace "ni? Wai bakiga katon hanun Ya Omari bane kaman na Ya Marwan" murmushi yayi ya kalli hanun ya Marwan din dayay kaman baya jinsu nanko kunenshi nakan duk abinda suke cewa, juyowa yayi ya kalli Nadeera itama shitake kallo ya nuna mata hanun Ya Marwan yana cemata look yana nuna mata manyan muscles dinshi Yana nuna mata ta kalla, makemai kafada tayi taki kallo, turo mata baki Abdallah yayi hakan yasa kaman daga sama tace "wlh kacika shagwaba" hararanta yayi shima harsaida tai murmushi yace "nakai ki?" da sauri tace "ni? Ni ai banda shagwaba" tabe baki yayi yace "wai talle kema audi gori" kama baki tayi tace "wai a ina kaji hausa? You don't look like a hausa man" murmushi yayi yace "kema u don't look like a hausa girl shagwababbiya kawai" makemai kafada tayi ta kalli Omari daketa kallon su kaman yasami film yanajin son kanin nashi aranshi tace "dan Allah waini shagwababbiya ce?" girgiza mata kai yayi ya tallabe keyan Abdallah yace "don't mind him lil sis keba shagwababbiya bace" dan murmushi tayi tana komawa jikin kujera dudda she found yanda yakirata da lil sis a little bit weird amma saita basar tajingina da kujeran tareda lumshe ido kaman mai shirin yin bacci, wani irin faduwa gabanta yayi harsaida taidan ihu tareda bude ido a firgice tana numfashi da sauri da sauri, kallo dukansu suka bita dashi, ahankali Marwan dake gefenta yataso ya matso kusa da ita yana kallon fuskarta murya chan kasa yace "menene?" baki ta tabe tana wani irin nishi tana kallonshi tana shirin yimai kuka, girgiza mata kai yayi tareda daura yatsan shi akan lips dinta yana wani irin kallon ta murya chan kasa danko su Abdallah bazasu iyajin abinda yace ba yace "don't cry for me, menene?" yay maganan yana janye yatsan daga kan lips dinta yamata wani irin kallon ban amsa, ahankali hawaye nacika idanunta ta dafa zuciyarta tace "My heart" ahankali ya kalli kirjin nata kaman mai nazarin abu kafin ya mika hanunshi ya janye nata ya daura nashi akai koshi yaji yanda yake bugu fast fast, fashemai tayi da kuka sosai tace "please kiramin Mum, zanyi magana da ita something is wrong" tafara wani irin nishi bakinta ya bushe sosai, dan juyo da kai yayi ya kalli Abdallah dake kallonsu yace "get me water Abdallah" dasauri Abdallah yatashi yana waigenta yaje kitchen ya dauko bottle water yadawo ya mikamai, budewa yayi ya kai bakinta da kyar ta sha tana fashemai da kuka tace "dan Allah Mummy na" yanda take kukan tana wani irin nishi yasa yajata jikinshi ya rungumeta yana buga bayanta hanunshi daya kuma yana kokarin ciro wayarshi dake bayan wando ya ciro yadawo dashi ta gaba ya bude wayan yay dailing number Mum.

Mum dake zaune cukin mota kuka take sosai ko mutum daya takasa kira saima kallon wayar nata da Abba yaciro daga purse dinta yasamata a hannu take, shidai Abba sai kiran mutane yake da limamai, ringing wayan Mum din tayi tabi wayar da kallo dudda tagane number Marwan ne amma takasa picking, sai uban kuka take akaro na uku sanan Abba yace "amsa mana Hajara hakuri zakiyi kinji" da kyar ta iya tai picking call din ta kara akunenta tana kuka sosai takasa magana, daga tachan bangaren saida gaban Marwan yafadi a yanda yaji Mum na kuka da sauri Nadeera dake jikinshi ta dago kai tafashe dawani kukan tana kallonshi, cikin kuka tace "Mummy na ta dauka?" jin maganan Nadeera yasa Mum ta katse wayar da sauri tarushe da kuka sosai, sakinta yay ahankali ya mike tsaye dan jikinshi yabashi wani abu matsawa yayi chan bangaren dining ya tsaya yay dailing number da kyar Mum ta iya picking call din ahankali Marwan yace "why are you crying Mum? Did dat man hurt you?" cikin wani irin murya raunanniya Mum tace "d'ana Muhsin dake kwance a asibiti ya rasu yanzun nan" sosai maganan ta dakai harsaida kirjinshi ya buga yadago kai ya kalli Nadeera dake zaune akan kujeran daya barta tana goge kwalla tana kallonshi jira kawai take taji mezaice, dan murmushi yamata danya kwabtar mata da hankali, kafin ya kalli wayar ahankali yace "may his soul rest in peace, and may Allah forgive his short comings" ahankali cikin kuka Mum tace "Ameen" tareda katse wayan, ahankali ya shigo falon yana kallon su Abdallah da sun riga sun karanci something is wrong daga fuskan shi, kafin ma yakaraso cikin dakin ta tashi da sauri ta karaso tana numfashi sama sama ta rike mai hannu tace "uhmm meya sami Mummy na? Metace? Wlh inaji ajikina something is wrong, please kafadamin gaskiya kaji please" ta karashe maganan tana fashemai da kuka, hanunta ya rike ahankali ya kakalo murmushi yace "come" stairs yay da ita tana kuka sosai ya shiga dakinsu da ita, fashewa tai da kuka sosai tana sake kallon fuskanshi tace "kafadamin dan Allah meya sami Mummy na" rungumeta yayi very tight tanamai kuka sosai kafin ahankali ya cirota daga jikinshi ya jata ya bude kofa suka suka tsaya agaban closet wani doguwan fine rigan abaya yaciro mata sai binshi da kallo take tafashe dawani irin kuka tace "ina zamu?" ahankali ya zage zip din bayan riganta batare daya bata amsaba yacire mata rigan tana kallon fuskanshi tana kuka, ajiye rigan yayi yana kallon fuskarta itama asanyaye, cikin kuka ta dafa hanunshi tace "ina zamu meya sami Mummy na?" yana zage zip din bayan skirt dinta yace "nothing, Mum is fine wife" jan skirt din yayi kasa tsabagen rudewa bama tadamu ba yabi santala santala cinyoyin ta da kallo, doguwan rigan ya dauka ya samata da hijabi. Cikin kuka sosai tace "I.. I want to change" gyada mata kai yayi ahankali yasaketa tadau pad dinta ta shiga bayi da gudu tana kuka, wayarshi ya ciro yatura ma su Omari text su shirya d'an Mum na hospital ya rasu yanzun nan, shiryawa yayi shima yasaka wani light blue yadi mai taushi dayamai bala'in kyau ya fesa turare yana jiran tafito, fitowa tayi tana hawaye sosai ta karaso gabanshi tace "am ready" takalmin ta ya nuna mata ta zura flat shoe jikinta na rawa yarike hanunta suka fito daga dakin, akasa suka samu Omari da Abdallah sunci manyan kaya suma sunyi kyau kaman zasuje gasan kyau sai kallonta suke duk suka fice suka shiga babban jeep din Marwan, Omari na mazaunin driver Abdallah na gefe sai shi da ita abaya suka rufo sanan Omari yatada motar yaja suka fita daga gidan, ahankali ya kwanto da ita jikinshi, dago kai tayi ta kalleshi bakinta na rawa sosai cikin kuka tace "are you sure my Mummy is fine?" gyada mata kai yayi tareda lumshe mata ido yana sake kwanto da ita tai lamo ajikinshi tana sauke ajiyan zuciya.


Akofar gida da already mutane sun cika Abba yasa mai taxi yay parking, fitowa yayi yabiya kudi ya zagayo ta bangaren Mum yabude mata ya riko hanunta tafito daga motan da kyar mutane suka karaso wajen yan anguwa anata musu gaisuwa ana tambayan karfe nawane jana'izar dan ga magrib ta kusa yau za'a kaishi ko sai gobe?" Eh yace musu yace "da isha'i za'ai jana'izar" yamusu godiya yaja hanun Mum dake binshi luu suka shiga cikin gidan, kawayen ta tagani yan kwararu agaban barander su, da sauri Maman fauzy da Abba ya kira ma Mum ta tashi tafito ta rungume Mum tana lallashin Mum data fashe dawani irin kuka Abba kuma yawuce shashin su Muhsin, Mum Fauzy tace "ki daure, ki daure Hajiya, nasan abin da ciwo, I know how painful it's to lose a Son, ki daure kinji, kici wanan jarabawan, ubangiji Allah yafimu son Muhsin, yaro mai kirki, shiru shiru, mara hayaniya, baida magana ga kunya, ga kyauta ga yawan sadaka da kyautatama mabukata, me kuma kike nema? Share hawayen ki" tashare ma Mum hawaye, ahankali Mum tace "ina Muhsin ina Ahmad?" shashin su Muhsin ta nuna mata tace "chan aka tafi dashi anje yanko likafani sai amai wanka" gyadamata kai Mum tayi tace "kaini wajen bana gani sosai" gyadama Mum kai Maman fauzy tayi taja hanun Mum ta kaita shashin su Muhsin ta tura kofan suka shiga da sallama ta kurama gawan Muhsin ido ga Ahmad zaune agefe idanun nan sunyi jajir yana kallon gawan shima, sai Abba dake gefen Ahmad kadan shima yana kallon gawan, ahankali Mum tawani irin zube agaban Muhsin tana wani irin kuka tahade hannayenta biyu alamun roko tana kuka tama kasa fadin abinda takeso tace, tai nadama tai nadama tai nadama biyema Abba, maima yasameta? Ya akayi tabari shaidan yaci galaba akanta? Itace ke dambe da namiji? Meya sameta? sosai Ahmad yaji tawani irin bashi tausayi dan yanda take kuka tana nishi saika zata suma zatayi, ahankali ya mike tsaye yaje inda take ya dagata murya chan kasa yace "Mummy is okay, kidena kuka haka is not good for your health, addu'a zakimai" rungume Ahmad tayi tana kuka shima hawaye ya goge da sauri batare daya rabata da jikinshi ba yajata yakoma chan gefe ya zaunar da ita man dogon kujeran falon su ya dago ta ya cirota daga jikinshi, hannunshi yasa ya goge mata hawayen datake yi dasuka kasa dena zuba, Abba da jikinshi yay sanyi sosai sai wani irin kallonsu yake, murya chan kasa Ahmad yace "Mum kinfada ma Nadeera? Yakamata ta sani, yakamata tazo taga Yayanta tamai addu'a kafin akaishi, kin kirata? Because I know kinada masaniyar inda take? Yanzu rasuwa akayi mu manta komi, kin kirata?" da kyar ta iya girgiza kai cikin kuka in a low tone tace "nafada ma mijinta Muhsin ya rasu" ahankali yasake kai hanunshi kan fuskarta yana goge mata hawayen yace "nace kidena kuka be strong, don't break my heart Mum" gyadamai kai tayi tana wani irin kuka, ahankali yamata kiss a goshi yace "is okay Mum" gyadamai kai tasake yi murya chan kasa yace "give me your phone ban number mijin nata lemme call him nace yakawota" gyadamai kai tasake yi tana kuka sosai ta ciro wayar tabude tabashi number, karba yayi yace "stay here am coming" fita yayi daga dakin yafita waje jiri na dibanshi daurewa kawai yake yakira wayar ringing daya Marwan dake mota rungume da Nadeera dayasamu bacci ya fizgeta yay picking ganin number Mum, ahankali Ahmad yace "this is Ahmad yayan Nadeera I hope ina magana da mijin tane?" ahankali Marwan yace "yea" Ahmad da muryanshi tadan fara rawa yace "please i have a request Yayan mu Muhsin yarasu, dan Allah ka kawo Nadeera let her bid farewell to Ya Muhsin please" shiru Marwan yayi hakanan yaji yana relating to the guy's pain yasan ciwon mutuwan your love one, yasan zafin da dacin abin, baka taba gane ya mutuwa take sai wani naka ya mutu, dan ajiyan zuciya yayi yace "we are on our way mun kusa isowa ma" da sauri Ahmad yace "thank you" yay maza ya share hawayen daya zubomai jiyake kaman ya kurma ihu but he's sure ya Muhsin bazai so hakaba, he has to be strong for him, share fuskanshi yayi daidai lokacin Bello ya shigo gidan dasu likafani da sauran su aleda karba yayi suka koma shashin nasu tare.


Parking sukayi ata gefen anguwan sabida mutane da maza dasuka cikashi fam, ana parking tabude ido rass tafashe da sabon kuka tana kallon anguwan nasu, kashe motar Omari yayi suka bude suka fito tana kallon mutane ta kalli Marwan tace "na shiga uku maiya faru?" shiru yayi ta kalli Omari da Abdallah dasuka fito daga motar tace "dan Allah kufadamin meya faru maiya sami Mummy na eh?" hanunta yarike suka fara tafiya suna sallama da mutane sai kallon su ake anga larabawa har zuwa gaban gate din gidan, yanayin yanda take yasa yabude kofan gate din suka shiga ciki tana kallon mazan dake compound din duk yan office din Ya Muhsin da Ahmad ne mata na bangaren Mum, gaban shashin su suka tsaya daidai lokacin fauzy tafito itama idanunta sunyi jajir rike da buta ahanunta zata bama baban su dake tsaye cikin wani irin kuka tace "ina Mummy na Fauzy?" kallonta fauzy tayi cike da mamaki kafin ahankali tai pointing shashin su Ya Muhsin, wani irin fizge hanunta tayi daga na Marwan taruga dawani irin gudu tana kuka tafada babban falon nasu ta tsaya chak tanabin kowa da kallo tana kuka, da Abba tafara hada ido daya kafeta da ido kaman yau yafara ganinta kafin ta kalli Mum daketa uban kuka kanta akasa sai Ya Ahmad zaune kusa da Mum da shima kallonta yake da idanunshi dasukai jajir kafin ta sauke idanunta akan gawan data gani akasa a lullube, bakinta har rawa yake kirjinta nawani irin bugawa, ta daura hanunta akan kirjinta dake wani irin gudu, miyan bakinta ya kafe, da kyar ta iya bude lebbanta dataji sun wani irin manne kaman ansa gum tace "Y..Ya..M..Ya..Muh...Muhsin?" baya tayi luuuu asume wani irin ihu Abba yayi yazabura yamike yace "My Princess!".
[9/23, 2:26 PM] +91 88002 49616: *idan kika karanta baki biyaba keda Allah*





*Maman Abd Shakur*


Yawani yi irin tsalle yayo kanta zai tareta yaga wasu fararen hannayen dake sanye dawani irin hadadden agogon mai tsada sun tare Nadeera, tundaga kafan mutumin Abba yakebi da kallo yana zaro ido inda yaga yasaka wani hermes half cover shoe na maza black, sai shining yake zuwa dogon wandon yadin jikinshi dakeda wani irin hadadden karin guga, dawani irin sauri yakara sa dago kanshi duka ya mike tsaye yana maida hanunshi baya yana kallon mutumin dake rike da Princess da baida bambanci da ba indiye ya kafe coil hair dinshi dake wani irin shining da kallo ganinshi kaman balarabe, ahankali ya daura hannunshi akan kumatun Nadeera yana dan tapping yana bubbugawa cikin damuwa bude idanunta dasukai jajir tayi tawani irin fashe da kuka tana kallonshi, girgiza mata kai yayi tareda dagata ahankali ta mike tsaye ta kalli inda Ya Muhsin ke kwance wani irin kuka na taso mata kafin ta shiga dakin da sauri tsabagen rudewa ko Abba dake tsaye agefe bata gani ba ta zauna agaban Ya Muhsin Abba shima ya shigo dakin da sauri yana kallonta, takai hanunta dake rawa sosai ta yaye ta bude fuskarshi tana kallo, taushe bakinta tayi wani irin kuka yataso mata kaman zata suma tace "noooooo, Umm Umm wanan ba Ya Muhsin dina bane, Ya Muhsin, innalillahi Ya Muhsin dan Allah karka tafi ka barni kaji" ta fashe dawani irin kuka tana kallonshi, ahankali Marwan yakarasa shigowa dakin batare daya kalli koda fuskan Abba ba su Abdallah biye dashi ya samu daya daga cikin kujerun dakin ya zauna su Abdallah a gefenshi yana kallon yanda Nadeera ke kuka abin nataba shi, da muryanta datai rauni sosai takira sunanshi. "Ya Muhsin, Ya Muhsin, Mummy, Mummy dan Allah kicemai yatashi" ta kalli Mum dake kuka itama, sake kallon Ya Muhsin din tayi tana wani irin kuka kafin ahankali tana girgiza mai kai tace "Ya Muhsin ai baka mutuba ko, suna cewa kamutu please katashi dan Allah" tai maganana cikin wani irin tone din kuka hawayen datakeyi yana diga akan fuskarshi, ta daura hannayenta duka biyu akan fuskarta tarufe fuskarta tana wani irin kuka kaman zata sume hawaye nabin hannayenta, sosai Marwan ya kafeta da ido kafin ahankali yasauke idanunshi akan Muhsin data budema fuska, hujin hancinshi ya kafe da ido ko kyaftawa babu kafin ahankali ya mike tsaye ya tako zuwa wajen duk aka bishi da kallo ya tsugunna agaban Muhsin ahankali ya kara yatsarshi daya a saitin hancinshi, tsabagen kukan datakeyi bama tasan da mutum awajen ba, ahankali yasa hannu ya yaye bargo yacire gabaki daya ya ijiye agefe, gabaki daya aka dago kai aka bishi da kallo, dago Ya Muhsin da jikinshi yay sanyi sosai yayi ya jinginashi a kirjinshi da sauri Abba yace "kai wanan balaraben lafiyan ka? Bakaga wanka za'amai yanzu ba kawani dagashi haka" ko kallon Abba baiyiba ya daga kai ya kalli Ahmad dayake kyautata zaton kanin Muhsin din dan yaga kaman, Ahmad dinma kallonshi yake da jajayen idanunshi cikeda mamaki ahankali yace "ban zamzam water, I can feel his pulse" da sauri Mum da Bello da Abba duk suka dawo wajen suna zare ido suna kallonshi, wani irin nishi Abba yayi yace "Ahmad je dakina akwai ruwan zam zam dayawa ka kwaso duka ma kakawo" dawani irin gudu Ahmad yafita daga dakin yaje dakin ya kwaso ruwan zamzam da gudu ya dauko wuka a kitchen mutane sai kallonshi suke yadawo ya bude yamika ma Marwan ahankali yay addu'a ciki ya kafamai abaki yadan shiga bakinshi sanan yamika ma Mum ta karba yace "he's alive, I think doguwar suma yayi dayasa heart dinshi yadena aiki, he need breeze" da sauri suka mammasa baya, da sauri Nadeera tacire hanunta daga fuska tawani irin rarrafo tazo gaban Ya Marwan din dake rike da Muhsin ta dafa cinyar Ya Muhsin arude takira sunanshi cikin kuka tace "Ya Muhsin, Ya Muhsin" ahankali bayan idanunshi sukai wani irin rawa batare daya budesu ba wani irin kabbara akai adakin Allahu Akbarrr!!! Wani irin fadawa jikin Ya Muhsin din tayi tafashe da kuka sosai tana kiran sunanshi. "Ya Muhsin Open your eyes kaji, dan Allah kabude idanunka ganinan nadawo, gasu Mummy na" sosai Marwan ke wani irin kallonta ahankali Muhsin yakarasa bude idonshi duka ahankali yana kallon yan dakin dai dai, Mum dinshi yafara ganin da fuskarta gabaki daya tai jajir, gefen bakinta afashe tana kuka tana kallonshi, kafin ya kalli Ahmad da shima idanunshi sunyi ja, sai abokin Ahmad Bello dake gefenshi hanunshi rike da farin yadi da turare, sai Abba dayake atsaye shima yay zuru zuru yana kallonshi kaman ya sami tv, saikuma wasu mutane biyu dake kan kujera masu kama da larabawa suma suna kallonshi, saikuma wani mutumi wanda yake limamin anguwan su yasa hand glove a hanunshi ya tattare hanun riga yana kallonshi shima murmushi kan fuskarshi, sai kuma wani karan kuka da yakeji da kuma alamun mutum dayaji akan jikinshi, ahankali yana dan layi ya dago daga jikin Marwan dayake kai ahankali yana daga hanunshi da kyar yana dafa kanshi, da sauri Ahmad ya rikeshi muryanshi na rawa sosai yace "Ya Muhsin, My brother" da sauri Bello ya ruga da gudu yafita daga dakin yana ihu "doguwar suma ce, jama'a doguwar suma ce, da ranshi, kafin ma aamai wanka yatashi, doguwar suma ce wlh" sosai ake binshi da kallo mutane nayin hanyar shashinsu ana lekasu, ahankali ta dago da rinanun idanunta ta kalli Ya Muhsin dake numfashi sama sama ahankali cikin muryan kuka tace "Ya Muhsin" fadawa tayi jikinshi tawani irin kankameshi tana kuka sosai sosai kaman zata shide, ahankali Marwan yatashi yakoma inda yake kusa da kaninshi ya dukar da kanshi kasa yanadan bubbuga kafa daya akasa, tsaki Abba daya cika fam yayi ya kalli Nadeera data rungume Ya Muhsin daketa tapping bayanta yace "ke Princess sakeshi, cikashi nace" ya kalli su limam yace "Imam nagode sosai, sai nazo har gida yima godiya, zamu maidashi asibiti yanzu ne" ya mikama Imam hannu yana kallon Bello yace "Bello zo tatttara makaran kutahi dashi" gyadamai kai Bello yayi ya shigo yadau komi yafita imam nagaba, Abba ya kalli su Marwan yace "larabawa naga ku kuka dawomin da princess ko aiko nagode sosai, a ina kuka ganta? Ya akayi kuka rabata da wanan dan iskan terrorist din? Anyways nagode nagode yanzu Princess dina tadawo gida, Dana kuma yafarfado komi ya daidai ta, wlh am so happy my princess is back" yay maganan yana kallon Nadeera dahar lokacin kuka take ajikin Ya Muhsin amma kasa kasa, Muhsin kuma ya lumshe ido natsuwa na shigan shi ahankali abubuwan dakemai ciwo ajiki yanaji suna denawa, zuciyarshi datamai nauyi sosai da zafi da yaji ya dena, cikin fushi Abba ya tsaya akansu yace "wai bazaki sakeshi ba Princess?" dan murmushi Muhsin yayi yadago Nadeera, ahankali ta taso daga jikinshi tana kallonshi ahankali ta koma gefenshi tai lamo ta daura kanta a hanunshi ta rike hanunshi gam tana share kwalla idonta, wani irin buga kafa Marwan ya shiga yi da sauri da sauri yawani irin dunkule hanunshi yanadan fuzar da iska Omari daya gama lura dashi ne ya daura hanunshi akan cinyarshi yay patting batare dayay magana ba, ahankali

1 Comments On BOYAYYEN MUTUM
avatar
barira-umar

2 months ago

Reply

Address

Please Login or Register in order to submit comment