Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kofar
gida da zata iya shanye tsawonsa kuma duk inda
zai
kwanta yayi barci sai yafi kamu sabain a tsawo
da
fadi,to wai shin ma wane irin adadin abinci da
abin
sha ne zai ishe shi a kullum?Allah da iko yake
kuma
shike yin halittarsa yadda yaso abinda Hibairu ya
fadi kenan a cikin ransa,kawai bawai Hibairu
daya
kasance GWARZON SADAUKI ba,gaba dayan yan
kallon saida suka firgita bisa ganin sadauki
Ramzan
saboda girmansa da kwarjininsa ya wuce a
misalta
sai abinda idanuwa suka gani.Mata da yara kuwa
basa iya hada ido dashi tsawon dakika goma ba
tare
da sun kauda kai ba,saidai kaga suna rufe
idanunsu
saboda gudun haduwa da mugun mafarki.Masu
bincike da hasashe na wannan lokaci sun
tabbatar
da cewa
a duk fadin duniya babu wani narkeken kati mai
Girma Da Nauyin Sadauki Ramzan.Lokacin da
Sadauki Ramzan yazo daf da Jarumi Hibairu
sukayi
kallon kallo sai hantar cikin Gimbiya Zuhura ta
kada,tsoro ya baibaye zuciyarta taji kamar tace
da
mahaifinta ya dakatar da wannan gasa,amma
saboda
kada kimarta ta zube a gane cewa yau ta kamu
da
son 'da namiji sai ta basar.Gimbiya Malika na
tsaye
a cikin jaruman gasa ta zuba ido ta ga yadda
wanann GUMURZU zai kasnace tsakanin Hibairu
daya sami galaba akanta da kuma Ramzan,sai
akwai
taga wanann bakon Jarumi ma'abocin kyau da
kwarjini wanda yayiwa sadauki Aryan magan
dazu
yazo kusa da ita ya tsaya suna hada idanu sai
yayi
mata murmushi yace,yanzun nan zakiga yadda
za'a
gama da wanda ya kaiki kasa farat daya.Koda jin
wannan batu sai Gimbiya Malika ta dubi bakon
jarumin cikin alamun tsananin mamaki
tace,wanene
kai kuma menene tabbacinka cewar sadauki
Ramzan
zai sami nasara akan Jarumi Hibairu?Koda jin
wannan tambaya sai Jarumin yayi murmushi
yace,sunana Jarumi Alkas dan'uwa ga Sarki
Hilaur
wanda kika ceto rayuwarsa data jama'arsa daga
hannun dan uwanki Yarima Lahaman.Anayi mini
lakabi da SA MAZA GUDU.Nayi bincike a cikin
hallarar tsafina naga duk irin cin mutuncin da
dan'uwanki yayiwa dan'uwana da yadda ya baje
garinmu ya kone shi,nayi niyar naje na baje
birninku
na Madinatul Zauwara na yiawa YARIMA
LAHAMAN
KISAN GILLA amma saina fasa saboda na gano
cewa
dan'uwana ya kamu da tsananin sonki kuma bai
kamata na cutar da wadda ta taimakeshi ba,bisa
wannan dalili ne na biyoku izuwa wannan birnin
domin na ramawa kura aniyarta.Ina nufin saka
miki
da abinda kika yiwa dan'uwana sannan na rabaku
domin aure bazai taba yiyuwa ba a
tsakaninku.Koda
jin wannan batu sai hankalin Gimbiya Malika ya
dugunzuma ainun take idanunta suka ciko da
kwalla
tace saboda me ka fadi haka?Sa Maza Gudu
yace
bazan iya gaya miki dalili a yanzu har sai na
kashe
babban makiyina a duniya.Cikin kaduwa Malika ta
dubeshi tace,wannan babban makiyin naka?Sa
Maza
gudu yace gasi can zai fafata da Sadauki
Ramzan,saboda shi na shiga wannan gasa,nima
inada yakinin cewa Sadauki Ramzan zai iya
kashe
Hibairu amma idan har bai kashe shi ba to nine
zan
kashe shi,sau bakwai muna fafata kazamin yaki
nidashi amma ragas mukeyi tamkar kowannenmu
zai mutu,tsafi baya tasiri a kansa kuma karfin
damtsensa da iya yakinsa kawai zata dore ni a
kansa.Kada ki sanar da dan'uwana kin ganni
anan
sai bayan na kammala wannan gasa in ba haka
ba
kuwa duk farin cikinki da burinki na rayuwa da
alkawarin da kika daukarwa dan'uwana zai
rushe.Koda gama fadin hakan sai Jarumi Sa
Maza
Gudu ya bace bat da karfin sihirinsa na tsafiya
daga
kusa da Malika tamkar bai taba wanzuwa ba a
wajen.Al'amarin dayayi matukar dugunzuma
hankalin Gimbiya Malika kenan ta rasa abinda
yake
mata dadi a duniya.A can tsakiyar filin gasar
kuwa
da akayi kallon kallo tsakanin Jarumi Hibairu da
Sadauki Ramzan na yan dakiku a lokacin da filin
gasar ya rude da shewa gami da ihu da
jinjina.Makada da mawaka kuwa kowannensu na
wasa wanda yake so,kawai sai akaji an buga
gangar
fara gumurzu,take jaruman suka ja da baya a
tare
sukayi taku bakwai bakwai sannan suka tsaya
suka
daya takubbansu sama suka sake rike
garkuwoyinsu
sannan suka ruga da gudu izuwa kan juna suna
suna ruri da kururuwa kai kace a tsakiyar
miliyiyon
mayaka zasu kafsa.
Nima ganin sun tawo zasu afkawa juna suna ihu
da
kururuwa yasa na dannan okay ban sani ba na
tsaya
domin kallo.
Maybe innaga comments da like anjima Da dare
na cigaba.Amma banda tabbaci.
SA MAZA GUDU
Littafi na Hudu (4)
Part B
Kai kace a tsakiyar milyoyin mayaka zasu
kafsa.Cikin bakin zafin nama Ramzan ya kawowa
Hibairu sara a wuya da nufin ya cire masa
kai,Hibairu ya sunkuya takobinsa ta sari iska a
lokacin dashi ma ya kaiwa Ramzan sara a
kafadarsa
shima sai ya kare da garkuwarsa ya zamana
cewa
kowannensu yayi gaba ba tare da ya sami wata
nasara ba.Nanfa yan kallo suka rude da shewa.A
fusace jaruman biyu suka waigo ba tare da jiran
komai ba suka sake rugowa da gudu izuwa kan
junansu suna haduwa suka kacame da
azababben
yaki,bisa mamaki sai akaga Jarumi Hibairu na iya
kare dukkan sara da sukan Ramzan.Kuma yana
iya
maida martani alhalin ansan cewa babu wani
jarumi
da yake iya tare harin Ramzan.Ai kuwa sai
jama'a
suka dada kaurewa da shewa,aka shiga yiwa
Hibairu
jinjina da tafi ana ambaton sunansa,al'amarin
daya
kara fusata sadauki Ramzan kenan ya kara
fusata
kuma ya dada zage damtse iya karfinsa yana
kaiwa
Hibairu munanen hare hare.Saida suka shafe sa'a
daya da rabi sunayin wannan bakin gumurzu ba
tare
da dayansu ya samu nasarar koda lakutar jikin
dan'uwansa ba,koda gimbiya Zuhura taga haka
sai
ta kamu da tsananin farinciki,hankalinta ya
kwanta
sosai saboda murna bata san sa'adda ta yiwa
Hibairu jinjina ba har ta kira sunansa cikin
jinjina.Koda sarkin Misra ya lura da halin da
yarsa
take ciki sai ya kamu da tsananin mamaki
saboda
wannan ne karo na farko dayaga an sami jarumin
daya burgeta har tayi masa jinjina alhalin duk
shekara akeyin wannan gasa kuma ta halacci
gasar a
kallah sai bakwai.Nan take sai yaji wani irin farin
ciki
ya shigeshi domin ga dukkan alamun ta sami
mijin
data zaba a matsayin abokin rayuwarta.Lokacin
da
jarumi Hibairu da sadauki Ramzan suka ga har
takubbansu sun fara dakushewa saboda tsabar
gogar juna amma babu wata nasara sai
kowannensu
ya fusata ya yarda takobinsa sannan suka yi
cirko
cirko suna kallon juna kamar zakaru suna haki
saboda tsananin gajiya.Daga can kuma sai suka
rugo da gudu izuwa kan juna da nufin su kacame
da
bugu da naushi amma sai Ramzan ya shammaci
Hibairu ya danki kugunsa da hannayensa biyu ya
matse shi.Hibairu ya kurma uban ihu sakamakon
tsananin zafi da zugin dayaji tamkar kasusuwan
bayan nasa zasu karye,amma sai yayi wuf ya
kama
hannayen Ramzan da nasa hannayen biyu ya
fara
kokarin banbare su daga jikinsa.Wohoho!nan fa
karfi
ya fara halinsa domin saigashi kuwa yana neman
ya
cire hannayen Ramzan daga kugun nasa.Ramzan
ya
dage iya karfinsa wajen ganin Hibairu bai cire
nasa
hannayen ba,sai gashi kowannensu ya kasa idda
nufinsa,ma'ana Ramzan ya kasa ci gaba da
matse
gadon bayan Hibairu,shima Hibairu ya kasa
banbare
hannayen Ramzan.A tarihin gumurzun Ramzan
bai
taba yiwa wani jarumi irin wannan kamu ba ya
tsira
da rayuwarsa domin na take yake rugurguza
kasusuwan bayansa yayi jifa da gawarsa amma
sai
gashi ya kasa gamawa da Hibairu.Koda Hibairu
ya
fahimci cewar idan fa baiyi da gaske ba Ramzan
zai
sake samun damar matse masa Gadon baya,sai
shima ya shammace shi ya buga masa tsakiyar
kansa a kan fuskarsa,babu shiri Ramzan ya saki
Hibairu ya fado kasa a lokacin dayaga taurain
wuya
akan fuskarsa,kuma hancinsa ya kama yoyon jini
yaji wani irin zugi da radadi ya shigeshi.Koda
Ramzan ya shafa hancinsa yaga jini sai ya
fusata
ainun ya dunkule hannayensa ya afkawa Hibairu
suka kama naushi da bugun juna sai gashi
kowannensu na shanye dukan abokin
gwaminsa.Nanda nan suka hadawa juna jini da
majina,tun suna tsaye sai da suka durkushe kasa
suka jigata ainun suna layi ya zamana cewa da
kyar
ma suke iya kaiwa junansu bugu.A na cikin
hakan
Ramzan ya sake shammatar Hibairu ya tallafo
wuyansa ya dagashi sama ya fyadashi a
kasa,kafin
Hibairu ya wattsake ya iya mikewa tsaye tuni
Ramzan ya turmusheshi ya zauna dirshen akan
ruwan cikinsa sai gashi Hibairu ya fara kakarin
kumallo saboda tsananin nauyin Ramzan.Koda
Ramzan yaga ya sami wanann nasara sai ya fara
kyalkyalewa da dariyar mugunta da farinciki,su
kuwa
yan kallo masu kaunar jarumi Hibairu sai
hankalinsu
ya dugunzuma ainun suka saddakar da cewa
shike
nan an gama da Jarumi Hibairu,ma'ana tasa ta
kare.Bazai iya ture Ramzan daga kansa ba saidai
ya
mutu a haka,tuni a wannan lokaci Gimbiya
Zuhura ta
fara zubar da hawaye saboda bakin cikin ganin
halin
da Hibairu ya shiga.Adaidai wannan lokaci ne
hankalin Jarumi Hibairu yakai izuwa kan fuskar
Gimbiya Zuhura,koda yaga ta kura masa idanu
har
tana zubar da hawaye saboda son sa da
tausayinsa
sai yaji wani irin gagarumin karfi ya shigeshi,bai
san
sa'adda ya kwalla kabbara ba a cikin
zuciyarsa,kawai sai gani akayi yasa hannayensa
biyu
ya tunkude Ramzan daga kansa,Ramzan ya fadi
can
gefe daya cikin dungure.Abinka da mai nauyi
kafin
Ramzan ya yunkura ya mike tsaye har ya juyo
tuni
Hibairu ya shiga tsakanin kafafunsa kawai sai
gani
akayi Hibairu ya suri Ramzan yai sama dashi
tamkar
kiyashi yayi dokon giwa,take Hibairu ya kwala
Ramzan da kasa.Ramzan ya kurma uban ihu
domin
ji yayi tamkar anzare lakarsa gaba daya,take ya
baje
a kasa ya kasa mikewa ma zaune har izuwa
tsawon
dakiku koda ganin haka sai filin gasar ya rude da
shewar jama'a aka kama yiwa Hibairu jinjina da
tafi,shi kuwan Ramzan sai daukeshi akayi daga
tsakaiyar fili saboda ya kasa mikewa
tsaye.Jarumi
Alkas wato SA MAZA GUDU dake cikin jaruman
gasar saiya cika da tsananin mamaki saboda bai
taba zaton cewa Hibairu zai sami nasara ba akan
Sadauki Ramzan,Bayan an dauke Sadauki
Ramzan
da kamar tsawon dakika ashirin sai alkalin gasa
ya
sake fitowa tsakiyar fikin ya dubi jama'a
yace,yanzu
zamuyi wasa na karshe a wannan rana,a zagayen
farko
Jarumin dazai kara da gwarzonmu na yau shine
Jarumi Alkas daga wata kasa dake kudancin
wannan
birnin namu na Misra.Koda Sa Maza Gudu yaji an
ambaci sunansa saiyayi sauri ya dauko hular
karfe
ya sanya a kansa don kada a shaida shi dama ba
kowane ya sanshi ba a fuska,an dai fi sanin
sunansa
domin ya shahara a ko ina cikin nahiyar.Batare
da
bata lokaci ba jarumi Sa Maza Gudu ya fito cikin
tsakiyar filin,koda Jama'a suka ganshi shima
yanada
sura irin ta Jarumi Hibairu wato siffa irin ta
Sadaukai
kuma tsawonsu da kaurin jikinsu ya kusan zuwa
iri
daya sak sao aka rude da shewa.Hakika dan'uwa
rabin jikine duka dacewa Alkas ya rufe fuskarsa
da
hular karfe saida Sarki Hilairu ya shaida shi wato
ya
gane cewa lallai wannan dan'uwansa ne Alkas
wanda
mutane keyiwa Lakabi Da Sa Maza Gudu.Nan
take
Hilairu ya kamu da tsananin farin ciki amma
dayaga
cewa zai fafata da wannan bakon Jarumi wato
Jarumi Hibairu sai hankalinsa ya dugunzuma abu
na
farko daya fadowa Hilairu a rai shine me yasa
Alkas
bai nemeshi ba sun hadu tun kafin a fara wannan
gasa,ko kuwa baisan cewa yana nan a cikin
birnin
Misra ba?Ai kuwa Alkas yana da karfin Sihirin
tsafi
donhaka dole ne yayi bincike ya gane inda yake
kuma yaga duk irin cin zarafin da Yarima
Lahaman
yayi a birninsu.Sarki Hilairu na cikin wannan
tunani
ne yaji an buga gangar fara gumurzu.Nan take
alkalin gasa ya jefawa Jarumi Hibairu wata
sabuwar
takobin ya cafe sakamakon cewa waccan takobin
tasa ta dakushe.Kafin Hilairu ya gama gyara
tsayuwarsa tuni Alkas ya durfafo shi amma
takobinsa a kas,saida yazo daf da shi yadda suna
iya jin numfashin juna sannan yace,yakai tsohon
abokin gaba,ya gashi mun hadu a inda babu wani
abu dazai raba mu face mutuwa,lallai a yau
saidai ni
ko kai wani ya kashe wani,domin mu kawo
karshen
wannan kiyayya,idan kana da wasiya ta karshe ga
yan'uwanka ko danginka ka hanzarta sanar dani
lallai zan isar da ita.Koda Alkas yazo nan a
jawabinsa sai Jarumi Hibairu ya kyalkyale da
dariya
sannan yace,ai ba a sanin maci tuwo sai miya ta
kare,sau ashirin da daya muna fafata kazamin
yaki
tsananin ni dakai a cikin garuruwa da dazuzzuka
daban dabam amma baka taba samun nasara ba
a
kaina,nima kuma ban taba samun nasara ba a
kanka,yanzu kai a tunaninka saboda mun hadu a
wannan gasa ta jarumta shine kake ganin cewa
ka
sami damar da zaka iya kasheni?To ka sani sai
an
gwada sannan a kan sanin na kwarai don haka ga
fili ga mai doki dan halak ka fasa.Koda gama
fadin
hakan sai jarumi Hibairu ya dan ja da baya kadan
ya
gyara tsayuwarsa yana mai buda
hannayensa,shima
Alkas sai ya gyara tsayuwarsa ya buda
hannayensa
suka kurawa juna idanu.Lokaci guda sai suka
rugo
da gudu izuwa kan juna suka ruguntsume da
azababben yaki wanda ya baiwa kowa mamak
kuma
yasa hankalin kowa ya dugunzuma ainun.Ba
komai
ne ya haddasa hakan ba face ganin irin tsananin
jarumtakar dasu Hibairu keyi ta ban al'ajabi.Cikin
bakin zafin nama suka rinka kaiwa junansu sara
da
suka ba kakkautawa tamkar jikinsu bana jini da
tsoka bane.Wani lokacin saidai aga suna tashi
sama
suna shawagi akan juna tamkar tsuntsaye masu
fukafukai,saida suka shafe kusan sa'a guda suna
wannan bakin artabu sannan da kyar da sidin
goshio kowannensu ya sami nasarar yankar
dan'uwansa.Shidai Hibairu ya sami nasarar
yankar
Alkas a kan damtsen hannunsa na dama ne
wanda
ke rike da takobi shi kuma akan kafadar Hibairu
ta
hagu ya yanke shi.Duk da cewa kowannensu
saida
inda aka yankeshi ya dare jini yayi tsartuwa
amma
ko gezau basuyi ba,kuma basuyi kokarin daure
raunikan nasu ba don tsaida jini,kawai sai suka
gyara tsayuwars suka sake rugowa da gudu
isuka
kacame da sabon masifaffen yaki,ya zamana
cewa
wannan karon sun hada da kaiwa junansu naushi
da
bugu,saigashi kowannensu na iya shanye dukan
gami da maida martani,abudai kamar wasa suka
sake shafe wata rabin sa'a suna gumurzu.Nanfa
yan
kallo suka gane cewa tabbas karfinsu yazo
daya,su
kuwa attajiran gasar dasuka zabi Alkas a
matsayin
gwaninsu kuma suka zuba kudi mai dumbin yawa
hankalinsu ne ya dugunzuma ainun saboda basu
da
tabbacin cewa shine zai lashe gasa.Al'amarin
Gimbiya Zuhura kuwa tun daga lokacin dataga
Alkas
ya yiwa Hibairu rauni a kafadarsa jini na zuba sai
ta
dimauce hankalinta ya tashi ta rasa abinda ke
mata
dadi,domin jitayi kamar ta roki mahaifinta yasa a
gaggauta tsayar da yakin amma sai ta dake.Tun
Hibairu da Alkas nayin wannan gumurzu da
kwarinsu da karfinsu har saida suka sare suka
durkushe kasa cikin matukar galabaita,kowan
nensu
ma bai san sa'adda takobinsa ta subuce ba daga
hannunsa suka kacame da kokawa.Adaidai
wannan
lokacine aka buga gangar dakatar da gasa don
haka
sai Alkalan gasar suka rugo da gudu izuwa cikin
filin
suka raba Alkas da Hibairu,aka janyesu izuwa
inda
likitoci zasuyi musu magani,shi kuma babban
Alkali
na gasar sai ya tsaya a tsakiyar filin ya fuskanci
jama'a yace,a halin yanzu Jarumi Hibairu na
birnin
Nurul Islam ya sami nasarar shiga zagayen wasa
na
biyu.Gimbiya Malika da Jarumi Alkas kuwa suna
da
sauran wasanni biyu kafin su shigo zagayen na
biyu
don haka a tafi hutu saida yamma za'a dawo inda
za'a fitar da jarumai biyu wadanda zasu kara
dasu
Gimbiya Malika.Yadda za'a fitar da jaruman biyu
kuwa shine za'a hada gaba dayan sauran
jaruman
gasar su yaki juna,wanda duk yaje kasa ya fita
daga
gasar har sai an sami gwanaye biyun da basu
fadi
kasa ba sune zasu kara da Malika da Alkas.Koda
Yan kallo da attajiran gasa sukaji wannan batu
sai
suka rude da shewa suka kamu da matukar
farinciki,sarkin Misra da 'yarsa Gimbiya Zuhura
ne
suka fara mikewa tsaye suka fice daga filin
Zuhura
nata waigen kofar inda aka shiga dasu Jarumi
Hibairu,suka tafi izuwa gidan sarautar,sannan
taro ya watse kowa ya kama gabansa.Jama'a
suka tafi suna ta fadin albarkacin bakinsu.
Nima ganin su Gimbiya Zuhura,Jaruman Gasa da
sauran jama'ar gari sun tafi Hutu yasa nima na
tafi Hutu.
SA MAZA GUDU
Littafi na Hudu (4)
Part C
Kowa ya kama gabansa,Jama'a suka tafi suna ta
fadin albarkacin bakinsu. Al'amarin Gimbiya
Malika
kuwa lokacin da ta isa masaukinta ta shiga cikin
turakarta sai ta zauna tayi tagumi kuma ta fada
cikin
kogin tunani mai zurfi,tana cikin wannan hali ne
sarki Hilairu ya shigo cikin turakar yana mai yin
gyaran murya,kamar wacce ta farka daga barci
haka
ta dago kai ta dubeshi cikin firgici.Koda taga
shine
sai tayi ajiyar numfashi gami da murmushi
sannan
ta nuna masa wata kujdera tana mai yi masa
nuni
daya zauna,cikin nutsuwa yake ya zauna akan
kujerar wacce ke fuskantarta sannan ya dubeta a
cikin nutsuwa yace,yake Gimbiya Malika wane
irin
tunani kikeyi ne haka mai zurfi?Shin kinga abin
mamaki ne a cikin wannan gasar jarumtaka da
kika
shiga?Koda jin wannan tambaya sai Gimbiya
Malika
tayi ajiyar zuciya sannan tace,tabbas abinda ka
fada
gaskiya ne,tabbas wannan bakon jarumi wato
Hibairu ina ganin kamar shine bakon jarumin da
mahaifina ya bani labarin cewa zan hadu dashi
kuma
ya umarceni dana yi masa biyayya ya koya mini
yaki
domin na kare kaina daga sharrin dan'uwana
Yarima
Lahaman anan gaba,shi kuma wancan daya
jarumin
dayai gumurzu dashi shine....Kawai sai Malika
tayi
shiru taki karasa abinda take son fadi.Cikin
mamaki
da zakewa sarki Hilairu yace ki gaya mini mana
wanene shi,ni kaina na fara zargin nasan shi,duk
da
cewa ya rufe fuskarsa a cikin hular karfe kuma
ya
rufe jikinsa duka da sutura ina ji a jikina kamar
na
sanshi.Wanene shi,me kika sani akansa,waishin
ma
me yasa ba'a baiyana garin daya fito ba?Sa'adda
Malika taji wadannan tambayoyi daga bakin sarki
Hilairu sai tayi sauri ta juya masa baya don kada
ya
fahimci cewar lallai akwai abinda take boye
masa
sannan tace,ina kyautata zaton shine shugaban
wata
runduna ta mayakan taimako.Koda jin wannan
batu
sai mamaki ya turnuke sarki Hilairu ya zagayo
kusa
da ita suka sake fuskantar juna sannan
yace,wace
runduna ce ta mayakan taimako?Malika tace ai
wata
runduna ce mai yaki da zalunci,ita dai wannan
runduna tana shiga ko ina a wannan nahiya cikin
dazuzzuka ta kawar da yanfashi sannan kuma
tana
kai agajin gaggawa ga garuruwan da suke fama
da
annoba ta fari ko cututtuka,bayanga haka kuma
duk
inda suka ji labarin sarki azzalumi suna zuwa su
saukeshi daga kan karagarsa da karfin tsiya,su
nada
waninsa mai adalci.Koda jin wannan batu sai
Sarki
Hilairu ya gyada kai yace,indai haka ne kuwa
wannan jarumi bazai kasa sanin dan'uwan ba
wanda
ake kira da Alkas mai lakabi da SA MAZA GUDU
saboda ra'ayinsu yazo iri daya,Shi Alkas ma
yabar
gida ne saboda ya shiga duniya yayi yaki da
zalunci
kawai,tun ban hau kan karagar mulki ba ya bar
gida
kuma na tabbatar da cewa idan ya dawo yaga
yadda
dan'uwanki Yarima Lahaman yaci mutuncinmu ya
baje birnin namu zai fusata yace zaije ya yaki
kasarku.Ni ne kadai zan iya hanashi aiwatar da
hakan don haka zan so ace bayan an gama
wannan
gasa ta jarumtaka anan birnin Misra ki barni na
koma izuwa can kasata koda kuwa ba zaki iya
taimaka mini da abinda zan gyara birnin ba a
yanzu.Lokacin da sarki Hilairu yazo nan a
zancensa
sai gimbiya Malika ta kawo gwauron numfashi ta
ajiye sannan ta dubeshi cikin alamun tsananin
damuwa tace,shin ka manta ne cewa barinka kai
kadai kayi tafiya mai nisa abune mai hadarin
gaske
tunda dan'uwana Yarima Lahaman na nan a raye
kuma yana mugun bakin ciki bisa karbarka da
nayi a
hannunsa,ina mai tabbatar maka da cewa zai
kasance a cikin farautar rayuwarka data
jama'arka,ni
kaina ba kyaleni zaiyi ba,zai cigaba dasa ido a
kaina
ya nemi hanyar da zai iya cutar dani,kafin ma
yaje
ya gama sabon shirin yakata,kada kayi mamakin
cewa a halin yanzu ma akwai yan leken asirinsa
a
nan cikin birnin misra masu sa ido akanmu.Ni
kawai
yanzu babban abinda ya dameni shine bansan ta
hanyar da zan bullowa wannan bakon jarumi
ba,Hibairu ya amince ya koyar dani salon
yakinsa,gashi na lura da 'yar sarkin garin nan
naga
cewa ta kamu da matukar sonsa farat daya,Anya
kuwa nima bazan ribace shi da batun soyayya
ba?
Koda jin wannan tambaya sai Sarki Hilairu yaji
kishi
ya turnukeshi don haka sai ya dubeta cikin
alamun
damuwa yace,ai kuwa gwara ki sauya shawara
domin babu yadda za'ayi ya so ki ya bar gimbiya
Zuhura yar sarkin garin nan tunda tafi ki kyau ta
fiki
mulki,me zai hana ki lallaba wancan daya bakon
jarumin ya baki nasa horon yakin ba tunda
karfinsu
yazo daya,gashi a zahiri kowa ya gani.Koda jin
wannan batu sai Gimbiya Malika ta girgiza kai
tace,a'a ba agareshi mahaifina yace na nemi
horon
yaki ba,ka sani cewa abinda na gaba ya hango
maka,yaro ko ya hau kan tsauni bazai iya
hangoshi
ba,daya jarumin sun banbanta asiffa,addini,hali
da
yanayi don haka ba lallai bane ba na sami
nasarar
abinda nake nema ba a wajen Alkas.Yanzu na
gaji
sosai ina bukatar na kwanta na huta,ina ganin
zaifi
kyau ka tafi izuwa taka turakar.Koda jin wannan
batu
sai sarki Hilairu ya rissina ga Malika yana mai
godiya sannan ya juya ya fice daga cikin dakin
zuciyarsa cike da dumbin damuwa a lokacin da
itama ta bishi da kallo kawai tana mamakin
yadda
akayiya kusan shaida dan'uwansa SA MAZA
GUDU
duk da cewa ya rufe fuskarsa da jikinsa.Acan
gidan
sarautar sarkin misra kuwa tunda Gimbiya Zuhura
ta
koma gida ta shiga cikin turakarta sai ta kasa
zaune
ta kasa tsaye,ta kasa kwanciya da tafiya,da zarar
taje
ta kwanta akan gadonta ta rintse idanunta domin
tayi
barci bata ganin komai face fuskar jarumi
Hibairu.Koda taga tunaninsa da begensa ya
hanata
sakat kuma lallai zata iya cutuwa idan bata
ganshi
ba sai ta mike tsaye zumbur ta tafi izuwa turakar
mahaifinta do
min ta rokeshi yasa aje azo da Jarumi
Hibairu.Zuhura na shiga cikin babbar turakar
mahaifin nata sai ta kame kamar gunki saboda
tsananin mamaki,ba komai ne ya bata mamaki ba
face ganin Jarumi Hibairu tare da mahaifinta a
zaune
su biyu rak suna ciye ciye da shaye shaye,cikin
raha
da annashuwa tamkar sun san junansu da
dadewa.Lokaci guda sarki Kamzal da Jarumi
Hibairu
suka juya suka dubeta suna ganinta suka mike
tsaye
a tare suka kura mata idanu saboda mamakin
rashin
sanin sa'adda ta shigo.Sarki Kamzal ya taho ga
Zuhura da sauri ya tarbeta cikin murna yana mai
ruke hannunta ya janyota izuwa inda Hibairu ke
tsaye a lokacin da Hibairu yake yi mata wani irin
kallo wanda ta kasa gane ko na menene,shin
kallo
ne na so ko kuwa kyawunta ne ya firgitashi?
Amsar
data kasa baiwa kanta kenan,abinda ya burgeta
dangane dashi shine irin shigar da yayi ta kamala
kuma data dubi kan teburin da suke cin abinci sai
taga babu tambulan din giya ko guda daya a
gaban
Hibairu face tambula na ruwan inibi,shi kuwa
mahaifin nata akwai tambulan giya sama da kala
uku
a gabansa.Sarki Kamzal ya zaunar da Gimbuya
Zuhura akan kujera ta uku dake karkashin teburin
da
suke cin abinci sannan shima ya zauna kuma ya
dubi Jarumi Hibairu yayi masa izinin sake
zama.Take Hibairu ya zauna amma saboda
kunyarsa
sai ya sunkui da kansa kasa bai yarda ya cigaba
da
kallon fuskar gimbiya Zuhura ba,shi kansa sarki
Kamzal wannan halaiya ta jarumi Hibairu ta bashi
mamaki kuma ta burgeshi saboda wannan ne
karo
na farko dayaga saurayin dayayi arba da 'yarsa
bai
rude ba.Nan take Sarki Kamzal ya gabatar da
Zuhura a wajen Jarumi Hibairu yace,wannan
itace
gimbiya kuma 'ya ta guda daya jal a duniya
wacce
nakeso fiye da komai a duniya,duk da cewa ka
ganta
a filin gasa dole ne na sake gabatar da ita a
gareka
kuma naji dadi datazo nan yanzu ta samemu
saboda
akwai tambayar da nakeso ka amsa mini ita a
gabanta.Tambaya ta kuwa itace,wanene kai?
ma'ana
inason naji tarihin rayuwarka duk da cewa naji
ance
ka fito ne daga birnin Nurul Islam garin nan na
ma'abota addinin musulunci,addinin da ko kadan
bashida farin jini a wannan nahiya gaba
daya,menene dalilin dayasa ka baro kasarku
harka
zo ka shiga wanann gasa ta jarumtaka wacce
nake
shiryawa duk karshen shekara?Idan ka lashe
wannan
gasa me kakeso a baka?Shin zaka bukaci auren
'yata ne ko kuwa zaka karbi dukiya ne?Sa'adda
sarki
Kamzal yazo nan a jawabinsa sai Jarumi Hibairu
ya
dago kai ya dubeshi sannan ya dubi Gimbiya
Zuhura
cikin alamun girmamawa da kawaici sannan
yace,yakai wannan sarki mai daraja ina rokon
alfarmarka bari sai bayan na lashe wannan gasa
sannan na fadi ladana amma ba yanzu
ba.Dangane
da labarina kuwa abune mai tsawo amma zanyi
kokari na dan gajarce muku shi cikin yan
sa'o'i.Koda Jarumi Hibairu yazo nan a zancensa
sai
yayi gyaran murya sannan ya yiwa Gimbiya
Zuhura
wani irin satar kallo yace,da farko dai...
SA MAZA GUDU
Littafi na Hudu (4)
Part D
Da farko dai kamar yadda kukaji na fito ne daga
birnin Nurul Islam garin dake can kudancin birnin
Kisra kuma wannan birni yana bisa wani tsibiri ne
zagaye da kogi don haka sai anyi tafiyar sa'a uku
kacal a cikin kwale kwale ake isa garin.Gari ne
karami wanda gaba dayansa Al'ummar dake
cikinsa
bai wuce da dari bakwai da arba'in ba.Ina nufin
mazanmu da matanmu,yaranmu da manya,kuma
muna yin addinin musulunci wanda shine addinin
bautar Allah Sarki Guda wanda bashi da abokin
taraiya,ba a hade komai dashi,muna zaune a
wannan tsibiri cikin zaman lafiya da kwanciyar
hankali gami da nutsuwa da wada.Addininmu
nada
dokoki wadanda muke binsu sau da sau,shan giya
haramunne,caca ko zina da sata duk
haramunne,muna da alkawari a tsakaninmu,muna
da
ruke amana,kuma duka abinda zamu fada sai
gaskiya,wani baya danne hakkin wani,talaka da
attajiri,bawa ko ubangida duk daya ne babu
wanda
yafi wani face wanda yafi tsoron Allah,kewaye da
wannan tsibiri namu akwai dazuzzuka masu
dauke
da tarin ni'ima gami da dimbin dabbobin daji iri
iri,bisa wannan dalili ne ya zamana cewa bamu
da
wata sana'a wacce tafi farauta kuma idan muka
farauto dabbobin daji muna haurawa izuwa
kasashen
makwabtaka muna siyar musu da fatoci da
sauran
sassan jikin dabbobi,kamar hauwan giwa da
kasusuwa wadanda ake amfani dasu wajen yin
wadansu kayan amfani na yau da kullum.Wannan
sana'a tamu itace kadai hanyar kasuwancinmu
kuma
itace hanyar cinmu da shanmu.Kuma babban
arzikin
kasarmu domin kasar garin namu bata yin
noma.Tsakanin Birninmu na Nurul Islam da
sauran
kasashen dake makwabtaka damu akwai
yarjejeniya
ta zama lafiya gami da dokoki,yarjejeniyar itace
kuma ba'a yarda muyi tallan addininmu ba ga
kowa
kuma ba'a yarda muyi auratayya da dan wata
kasa
ba,ma'ana baza'a bmu aure ba,muma bazamu
bayar
ba.Sama da shekaru dari da ashirin da muke
zaune
lafiya a cikin wannan yarjejeniya ba'a taba samun
wani sabani ba saboda mutanenmu suna matukar
kula da kiyayewa.Mahaifina shine Sarkin
Mafarauta
na birnin Nurul Islam,ana kiransa da suna Uraisu
bin
Hannaf.Mafarauci Uraisu ya shahara ainun ko ina
a
cikin kasashen dake makwabtaka damu sabida
duk
sa'adda akayi gasa ta farauta a kowacce kasa
shike
zuwa na daya.Mutum ne shi mai tsananin
jarumtaka,sanin sirrin daji da kuma tsananin sa'a
da
rabo.A cikin wannan sana'a ta sa ne Allah yayi
masa
arziki sosai har ya zamana cewa a gaba daya
birninmu na Nurul Islam babu attajiri
kamarsa,amma
ko kadan dukiyarsa bata dameshi ba,kulluma a
cikin
rabar da ita yake ga miski da almajirai da masu
bukata,hakanne ya janyo masa matukar farin jini
a
wajen jama'a har ya zamana cewa ana
girmamashi
fiye da yadda ake girmama sarkinmu.Wannan ne
dalilin daya haifar da 'yar tsana tsakaninsa da
Mahaifinmu saboda gani yake kamar ma wata
rana
mahaifin nawa zai iya kwace masa sarautarsa,shi
muwa mahaifina ko kyauta aka bashi mulkin
bazai
karba ba.Lokacin da arzikin mahaifina ya
bunkasa ya
zamana cewa ya auri mataye har uku dadin da
uwata hudu kenan,ya zamana ceqa ya fara tara
iyali
sai yasa aka fadada gidansa akayi gini mai kyau
wanda ma yafi gidan sarki kyau.Hakanne ya kara
janyowa mahaifina bakin jini a wajen sarkinmu
yaji
ya tsaneshi sosai amma a zahiri baya nuna
hassadarsa,saidai ma muna tsantsar soyayya a
gareshi saboda kusan bukatun gidan sarkin
mahaifina ne ke daukar nauyinsu.A wannan
lokaci
ina da shekara goma sha tara a duniya kuma
inada
kanne gosha sha biyu wadanda suka kasance
kananan yara babu dan sama da shekaru
goma.Nima na taso da jarumtaka,sanin sirrin
daji,iya farauta gami da mutukar sa'a bisa duk
abinda nasa a gabana tun banfi shekara shifa
ba,mahaifina ke fita dani daji yana koya mini
yadda
ake farauta kuma ya koyar dani yaki don baiwa
kaina
tsaro daga harin yan fashi da yan
sumame.Lokacin
dana kai shekara tara ne na fara yin abubuwan
ban
al'ajabi na jarumtaka,domin komai girman dabbar
daji da hadarinta ina iya tararta na kasheta kuma
komai yawan yanfashi ina zame musu alakakai
na
kashe na kashewa masu gudu su gudu,in
tarwatsa
su.Birnin kisra shine birnin da yafi dukkan birane
girma da daukaka gami da karfin masarauta,gaba
daya sarakunan kewayen suna tsoron sarkin
birnin
Kisra saboda karfin mayakansa da kuma tsananin
zaluncinsa.Bisa dole ma suke kai masa haraji
mai
tsoka don gudun kada ya yakesu,ana kiran
wannan
sarki da suna Zadasi bin Auzir.Babu wata hulda
data
taba shiga tsakanin mutanenmu na Nurul Islam
da
birnin Kisra,asalima babu wani dan garinmu daya
taba shiga cikin birnin kisra a tsawon shekarun
da
birnin namu ya kafu,amma su mutanen birnin
kisra
suna shigowa cikin birnin Nurul Islam domin
siyan
fatocin dabbo da kasusuwa.Wani babban abin
mamaki shine kafin sarki Zaldashi anyi sarakuna
arba'in da daya a birnin kisra amma daya daga
cikinsu bai taba sa ido akan birninmu na Nurul
Islam ba kuma bai taba neman harajiba.Gaba
daya
sarakunan dake nahiyar suna mamakin wannan
al'amari,mu kanmu mutanen birnin Nurul Islam
muna mamakin haka tunda dai munsan cewa
mutanen Kisra ba tsoronmu suke ji ba,sun fimu
tarin
mayaka da kayan yaki.A yawa kuwa sun
ninkanamu
sama da sau dubu

1 Comments On SA MAZA GUDU 1 to 9
avatar
adamu-3

1 year ago

Reply

Masha Allah Allah ya Kara basira Aboki

Please Login or Register in order to submit comment