Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ba tare da saninka ba,abu na
farko shine rashin sanar dakai koyan yakina
wanda na barshi sirri saboda wadansu dalilai,abu
na biyu kuma shine huldar kasuwancin dana kulla
da wadansu manyan sarakai da manyan attajirai
na duniya,ina mai tabbatar maka da cewa a
nahiyar nan tamu kaf bababu wata bafatakiya data kaini arziki
da kayan abinci da makaman yaki fiye da harkar
fataucin bayi.Ka sani cewa a yanzu na gano cewa
fataucin bayi wahala ce kawai.Kudi na cikin
fataucin abinci da makaman yaki,duk inda naji
labarin ana yin yaki a duniya to fa nan nake
ratsawa da karfin tsiya nakai tallan hajata izuwa
ga kasashen dake yakar juna kuma bani da
bangare kowa na wane.Ka sani cewa a halin
yanzu ina da rijiyar dinare masu zurfin RIJIYA
GABA DUBU guda dari bakwai.Guda dubu uku
kuma inada rijiyoyin dinare masu zurfin gaba
dubu cike da lu'u lu'u,guda cikin kogon na bude
rijiyoyin da wadansu mukullai na musamman
wadanda dole saida su za'a iya budewa komai
jarumtakar mutum da aljan kuwa,ka sani cewa
ban tara dukiya domin komai ba sai domin na
kare mutuncina dana jama'ar kasar nan saboda
nasan cewa duk ranar da babu kai ya zamana
cewa Yarima Lahaman ne sarki zai iya yunkurin
wulakantani ko cutar dani da sauran
talakawa.Amma a yanzu nayi wannan gagarumin
shiri nafi karfin wulakancinsa,kuma zan iya kare
kaina da jama'a idan naso ma zan iya fita wajen
gari nasa a gina mini fada ta musamman inda
zamu zauna cikin kwanciyar hankali tare da
mahaifiya da sauran masoyana har izuwa karshen
rayuwa.Sa'adda Malika tazo nan wa jawabinta,sai
mamaki ya turnuke sarki Sharkuf kuma ya kamu
da tsananin farin ciki ya kama kafadunta ya ruke
yace,Yake 'yata na rantse da gemun ubana tunda
ake haihuwa acikin zuri'ar wannan gidan sarautar
nami ba'a taba samun mai basira da hangen nesa
kamarki ba.Wannan shirin da kikayi yayi daidai
amma kisani cewa akwai sauran rina a kaba,duk
wannan dukiyar dakika tara wacce kike ganin
cewa tana da yawa to bata kai kaso daya ba cikin
kaso goman wacce ni na tara,kuma na boyeta a
inda babu wanda ya sani,kuma babu wanda ya
taba jin labarinta sai ke a yau,idan na mutu sai
kowa yasan wannan dukiya da kuma inda
take.Kuma idan har dan'uwanki Yarima Lahaman
ya riga ki sanin inda take yaje ya mallake
ta,kashinki ya bushe,domin ya sami damar da zai
iya ganin bayanki,babban bakin ciki na a doron
kasa shine ko a bayan raina ace dayanku ya
kashe dan'uwansa wannan abin gori ne dazai ta
bibiyar zuri'armu har abada,duk abinda Lahaman
zai miki kada kiyi yunkurin kashe shi,saidai kiyi
duk yadda zakiyi ki kare kanki daga dukkan
sharrinsa.Abu na karshe dana keso ki sani shine
har a cikin zuciyata bani da zabi a tsakaninku bisa
wanda zai gajeni na barwa kaddara ta riga fatar
wannan.Koda jin wannan batu,sai idanun suka
ciko ta kwalla tace,haba ya kai abbana ko yanzu
idan babu kai kuma baka bar wasiyar wanda zai
gajeka ba a tsakaninmu yaya za'ayi kenan?Sarki
Sharkuf yayi shiru yana mai ajiyar zuciya sannan
ya dago kai ya dubeta da yanayi mai nuna
tsantsar damuwa,yace ko a yau na fadi na mutu
yan majalisata sun san yadda zasu yi su fitar da
wanda ya dace ya zama ya gajeni daga
cikinku.Sau daya irin haka ta faru a wannan gidan
sarauta a zamanin mahaifina wato su biyu ne
wadanda suka cancanci sarautar kuma acikinsu
aka fitar da gwani ya zamana cewa mahaifin
nawa ne ya zama sarki..Malika ta kama hannun
sarki Sharkuf tace,to baka sanar dani yadda aka
warware wannan matsalar ba tunda da akwai
alamun cewa nima zan tsinci kaina a cikin hakan?
Sarki Sharkuf ya gyada kai yace,kamar yadda
bazan iya sanar da dan'uwanki ba haka kema
bazan iya sanar dake ba,saboda an bar al'amarin
sirri a cikin wannan gidan sarauta,in kuwa na
gaya miki tamkar na gaya miki sirrina da zaki
sami nasarar zama sarauniya ne alhalin so ake
kowannenku cancantarsa akeso ta kaishi ga
matsayin.Aikin dake gabanku da yarima Lahaman
ba karami bane,yanzu dai mu manta da wannan
batu mu koma kan batun tafiyar dake gabanki
nan da cikar kwana uku.Shin tunda yanzu nasan
dalilin yin wannan tafiya taki bazaki hakura ba ki
zauna tare dani in yaso ki tura amintattun yaranki
su wakilceki?Koda jin wannan batu sai Malika ta
dubi sarki Sharkuf cikin alamun mamaki tace,me
yasa baka son nayi wannan tafiya alhalin na saba
yinta kuma baka taba hanani ba sai yau?Koda jin
haka,sai sarki Sharkuf ya mike tsaye yayi tafitaku
uku,yana mai juya mata baya,sannan yace yake
'yata kiyi sani cewa ni fa yanzu girma ya fara
kamani tunda yanzu shekaruna sunkai sittin da
takwas a duniya bana son naga kina yin nisa dani
tunda kullum lokacina karewa yake,kuma har
yanzu akwai sirrikana da dama wadanda baki
sansu ba,asali ma dan'uwanki Yarima Lahaman
ya fiki saninsu saboda ya girmeki sosai kuma na
jashi a jikina daga kuruciyarsa kawo izuwa
girmana kafin na fahimci cewar shi azzalumine
wanda baya kishin talakawansa na gujeshi.Lokacin
da Sarki Sharkuf yazo nan a zancensa sai hawaye
ya subuto masa gimbiya Malika ta sake dafe
hannun sarki akan cinyarta ta dubeshi tace,ya kai
abbana kamar yadda bakasan rabuwa dani
daidadi da rana daya haka nima na
kasance,amma ina rokonka alfarmar nayi wannan
tafiya domin itace tafiyata ta karshe akan
harkokin kasuwancina kuma acikin tane nake so
na cika wani buri nawa wanda bani da kamarsa a
raina.Kayi hakuri bazan iya gaya maka wannan
sirrin ba kamar yadda kaima bazaka iya gayamin
hawa KARAGAR MUKIN kasar nan ba,amma zaka
san nawa burin da zarar na dawo kuma nayi
maka alqawain cewa bazan fi wata uku ba zan
dawo.koda jin wannan batu,sai shima sarki
Sharkuf hawaye ya zubo masa ya kamota ya
rungumeta a kirjinsa suka dan jima a kankame da
juna.Suna cikin wannan hali ne Malika taji an
kirawo sunata,a tare suka waiga baya.
SHIN WANENE WANDA YA SHIGO MUSU BATARE
DA NEMAN IZINI BA?
SARKI SHARKUF ZAI BAR GIMBIYA MALIKA TAYI WANNAN
TAFIYAR?
YARIMA LAHAMAN ZAI BATA WANNAN BAWAN?
INA LABARIN BAWAN DA YARIMA LAHAMAN YA KAMO?
TSAKANIN GIMBIYA MALIKA DA YARIMA LAHAMAN WAYE ZAI
GAJE KARAGAR MULKIN SARKI?
MU HADU A CIKIN LITTAFI "SA MAZA GUDU" LITTAFI NA BIYU(2)
DON JIN WADANNAN AMSOSHI.
AMMA MENE HASASHEN KU?
Suleiman zidane kd whatsapp 09064179602


SA MAZA GUDU
Littafi na biyu(2)
Complete book 2
Typing Suleiman zidane kd.
Whatsapp 09064179602
................
A tare suka waigo baya suka duba,sai suka ashe
Lasurat ce mahaifiyar Malika.Ta tunkaro su
fuskarta cike da alamun damuwa.Koda ganinta sai
sarki ya mike tsaye ya taryeta yana mai rike
hannayenta a lokacin da ta kurawa hannun
Malika idanu.Sarki yace kwantar da hankali yake
Ummul Malika,kiyi sani cewa raunin da Malika taji
Karami ne kuma da wuri zata warke.Koda jin
wannan batu,sai murmushi ya kubucewa Lasurat
tayi doguwar ajiyar numfashi tace,to nagode da
abinda ya tsaya iya haka amma yaya akayi ta
sami wannan raunin alhalin nasan cewa duk inda
zata je kana bata tsaro mai kyau na dakaru?Sarki
Sharkuf ya numfasa yace,ni kaina nayi mamaki
yadda al'amarin ya faru,amma hakan bazata sake
faruwa ba.Yanzu ki tafi da ita izuwa turakarki ki
lallabata ta sami nutsuwa da kwanciyar hankali
domin akwai alamun cewa tana cikin damuwa.
Batare da wata gardama ba Lasurat ta kama
hannun Gimbiya Malika tajata suka nausa izuwa
can cikin gidan sarautar.Shi kuwa Sarki Sharkuf sai
ya bita da kallo cikin alamun tsananin damuwa
gami da tunani mai zurfi.Na take idanunsa suka
ciko da kwallah har hawaye ya zubo masa saboda
tausayin da ya kama shi.Ba komai ne ya sanya
masa wannan tausayi ba face a binciken da yayi a
hallarar tsafinsa ya gano cewa bayan mutuwarsa
sai wannan 'ya da uwa sun rabu sakamakon wata
kaddara wacce basu isa su guje mata ba.Tunda
farkon Yammaci Gimbiya Malika ta caba ado tayi
shirin tafiya izuwa wannan Gida na Yarima
Lahaman.Bayan ta hama shiri tsaf,sai hankalinta
ya DUGUNZUMA bisa dalilai biyu,dalili na farko
shine bata san yaya taza sulale ta fice daga gidan
sarautar ba tare da wani ya ganta ba.Dalili na
biyu kuma bata san ko nawa Yarima Lahaman zai
siyar mata da wannan bawan nasa ba Wanda taji
ta kamu da tsananin sonsa farat daya.Duk da
tasan cewa komai tsadar bawan zata iya
sayensa,amma tayaya zata iya fitar da kudade
masu yawa daga gidan sarautar batare da sarki
ya gane dukkan shirinta ba?Idan tace kogon ta na
dukiya zataje ta debo kudin tafiyar mai tsawon
gaske ce,ba zai yiyu ba.Bisa wannan dalili ne yasa
Gimbiya Malika ta kama zarya a cikin babban falo
na turakarta ta kasa zaune ko tsaye.Kuma
Hankalinta ya DUGUNZUMA,taji kamar ta fashe
da kuka saboda bata da wani buri da kuma 'doki
wanda yafi taje ta gana da wancan bakon bawa
ko don ma ta sake ganin fuskarsa,Zuciyarta ta
huta da tsananin begensa da tunaninsa.Malika na
cikin wannan hali ne Shugabar kuyanginta wata
mace yar kimanin shekara arba'in da daya mai
suna Lasmira ta shigo cikin falon tare da wadansu
kuyanci guda uku,domin su gabatar da irin
aiyukan da suka sabayi kullum.Koda Lasmira taga
gimbiya a tsaye tana kaii kawo cikin alamun
damuwa,sai ta sallami wadannan kuyangi guda
uku dake tare da ita,suka juya da baya suka fice
daga cikin falon.Lasmira ta karasa gaban Malika ta
dubeta tace,Ya shugabata menene ya dameki
haka harzaki kasa zama ko tsayuwa?Koda jin
wannan tambayar,sai Malika ta koma kan kujera
ta zauna tayi shiru kamar baza tace komai
ba,tana mai kurawa Lasmira idanu.Daga can sai
tayi gyaran murya ta dubi Lasmira cikin nutsuwa
tace,yake Lasmira kiyi sani cewa na yarda dake
kuma nasan zaki iya rufe sirrina tunda tun ina
yarinya karama kike aiki a karkashin
Mahaifiya,kuma ban taba jinta tayi korafi akankin
yi mata wani laifi ba,bisa wannan dalili yanzu zan
sanar dake abinda ke damuna akan amana kuma
ina son ki bani shawarar abinda zanyi na sami
mafita.Nan take Gimbiya Malika ta zaiyanawa
Lasmira duk bukatunta.Koda jin wannan bayanin
nata,saiLasmirata kyalkyale ta dariya.Al'amarin
daya bawa Malika haushi da mamaki kenan
tace,mene kuma abin dariya a cikin wannan
Al'amarin?Lasmira tace,ai gani nayi ga magani a
gonar yaro amma bai sanshi ba,ai warware
wannan matsala taki abu nemai sauki tamkar cire
silin gashi daga cikin tandun mai.Abinda nake so
dake kawai shine kibi duk irin umarnin dana
baki,in kikayi haka dake da duk adadin kudin da
kike bukata zaku isa kofar gidan Yarima na can
bayan gari a asirrance kuma zaki dawo a asirrance
batare da kowa ya sani ba.Ko jin wannan batu,sai
farincik ya lullube Malika ta dubi Lasmira cikin
zumudi tace,Fadi duk irin abida kike so
nayi.Lasmira tayi murmushi tace,yanzu dai da
farko ina son ki bani Dinare dubu goma kacal
wanda zanje na aiwatar da wadansu ayyuka a
cikin gidan nan dasu,zan dawo nan da kafin cikar
rabin sa"a.Batare da gardamar komai ba kuwa sai
Malika ta shiga cikin kuryar turakarta ta debo
dinare dubu goma a cikin jakar kudi ta mikawa
Lasmira.Lasmira na karbar wannan kudi sai ta
boyesu acikin rigarta sannan ta juya ta fice daga
cikin turarkar.Lasmira bata zame ko ina ba sai can
kofar dakin shugaban dakarun dake tsaron gidan
sarautar,wani barden jarumi wanda ake kira da
suna Mahutur bin Kauzif.Da isarta sai ta
kwankwasa kofar dakin sau biyu kacal,faruwar
hakan ke da wuya sai Muhutur yayi magana daga
ciki yace,to Lasmira shugabar yan cuwacuwar
gidan nan yau kuma dame aka zo mini don nasan
cewa unguwa bata jewar banza.Lasmira tace ai sai
ka fito waje kaji abinda nazo dashi.Muhutur yace
ai zaifi kyau ki shigo daga ciki komai zaifi
sirri.Idan kuma matarka tazo ta ganmu fa sai ta
zata amanarta zanci kuma ka sani cewa kawata ce
ko?Haka ne to bari na kimtsa gani nan fitowa.Jin
kadan saiga Muhutur ya fito yana goge bakinsa ga
dukkan alamun abinci ya gama ci.Maimakon
Lasmira ta bude baki tace wani abu,sai ta dauko
kudin Dinare dubu uku ta mika masa.Cikin
kaduwa da Mamaki Muhutur ya karbi kudin yana
mai jinjina su akan tafin hannunsa,sannan yayi
waige waige da dube dube yai sauri ya Soka kudin a
cikin aljihun wandonsa ya dubeta
yace,wannan kuma fa na menene?shin wani abu
za'a siyowa Gimbiya a boye?Lasmira tace a'a itace
da kanta take son ta fita daga cikin gidan sarautar
nan tare da dukiya mai yawa saboda taje ta siyo
wani bawa a can gidan Yarima dake bayan
gari,kuma komai ana sin ayi shine a asirrance ba
tare da sarki ya sani ba.
Koda Lasmira tazo nan a zancenta,sai hankalin
Badakare Muhutur ya DUGUNZUMA ainun ya rasa
abinda ke masa dadi domin yasan cewa hadarin
dake cikin wannan aikiyana da yawa saboda ko
yaya aka sami akasi ya rasa aikinsa kenan .Don
haka sai ya murtuke fuskarsa kuma ya murza
gashin bakinsa yace,kai ungo kudinki bazan yi
wannan aiki ba,hadarin dake cikinsa yafi abinda
kika bani.Koda jin haka,sai Lasmira ta sake saka
hannunta cikin aljihunta ta dauko wani damin
kudin Dinare dubu uku ta wurga masa tace,ga
wadansu dinare dubu ukun kaga ke nan inka
hada dana farko sun zama dinare dubu shida
daidai albashinka na shekara biyu kenan,shin ka
amince yanzu zakayi wannan aiki?Koda jin
wannan tambaya,sai jikin Muhutur ya kama
kyarma ya rasa hukuncin da zai yankewa
kansa,saida yayi duru duru yayi gaba yayi baya
sannan ya juyo ya fuskanci Lasmira yace,to ina
kudin dakarun dake aiki a yau?kinsan cewa suma
sai na raba musu wani abun sannan zasu ki duba
duk abinda za'a wuce dashi.Koda jin haka sai
Lasmira ta zura hannu cikin aljihun rigarta ta
dauko wani kullin kudi na dinare dubu ta mikawa
Muhutur tace,wannan dinare dubu ne nasan ya
isa ka raba musu,wane lokaci za'a fito da Gimbiya
da dukiyarta?Muhutur yayi shiru yana tunani
sannan yace,ai yau talata ce kuma duk ranar
talata da yammaci ne sakalaiya Sarki ke kwanciya
domin ya huta ba zai sake fitowa waje ba sai
gobe da safe don haka a daidai wannan lokaci
za'a fito da Gimbiya.Lasmira tayi murmushin farin
ciki ta juya da baya da gudu taje ta sanar da
Gimbiya Malika duk abinda ya faru tsakaninta da
shugaban dakaru Muhutur.Sannan sai ta dauko
wani shudin magani a cikin wata yar karamar
kwalba ta mikawa Malika tace,ungo wannan kisha
makurwa biyu kacal,batare da gardamar komai
ba ko tsoron wani abu sai kawai Malika ta karbi
ruwan maganin ta cire murfin kwalbar tasa a
bakinta tasha makurwa biyun kamar yadda aka
umarce ta.Bayan kamar dakika ashirin da faruwar
hakan sai Malika ta fara jin jiri,ta kama tangadi
daga tsaya sannan ta tafi luu.. zata fadi,amma sai
Lasmira ta tafa hannunta sau uku,saiga wadansu
hadiman gidan su Gimbiya Malikan guda uku karti
sun shigo,dayansu dauke da wata doguwar
akwatin katako.Da zuwansu sai suka ajiye akwatin
suka bude shi saiga matattun beraye,kyankyasai
da sauran kananan kwari masu addabar mutane
a gidan.Kawai sai suka daga abinda ke dauke da
wadannan kwari daga cikin akwatin sai ga katon
fiki a kasan akwatin aka saka gimbiya Malika a ciki
sannan suka dauko katakon dake dauke da
matattun kwarin suka dora a saman Gimbiya
Malika ya zauna darama.Komai kallon
kurilla,mutum bai isa ya iya ganewa cewa akwai
wani abu a kasan akwatin,saidai ayi tunanin cewa
akwatin cike take da wadannan kwari babu komai
a kasanta.Bayan an rufe Malika a cikin wannan
akwati sai kuma wannan hadimai uku suka shiga
can cikin kuryar turakar gimbiya suka rinka fito sa
irin akwatunan har guda arba'in,ashe kowacce a
kasanta lu'u lu'u aka zuba dunkim a samanta
kuma aka zuba matattun kwarin.Akwatuna guda
arba'in da daya aka loda su a kan keken shanu
aka tunkari kofar fita daga cikin gidan
sarautar.Saida aka wuce ta cikin kofofi tara,kuma
duk kofar da akazo ko tsayar da keken shanun
ba'ayi,da an hango su daga nesa sai a bude
musu kofa tun kafin ma su iso.Saida kawai su
wuce.Haka dai direban keken shanun ya cigaba
da wucewa har ya iso kofar karshe,har masu
gadin sun janyo kofar sun bude masa zai fita
kenan,sai sukaji an daka mus tsawa,a firgice
direban keken shanun tare da dukkan masu
gadin kofar kimanin su dari suka waiga suka duba
inda sautun tsawar ya fito saboda sun dauki
murya.Ba muryar wani bace face ta sarki Sharkuf
yana tahowa daga cikin gidan sarautar bangaren
da turakarsa take.Sarki Sharkuf ya kara so garesu
fuskarsa a murtuke ko kadan babu annuri,ya dubi
direban keken shanun ya sake daka masa tsawa a
karo na biyu yace,ya kai Zarhus yau kuma wace
irin sharace za'a fitar da ita da wannan yammaci
sakaliya haka?Koda jin wannan tambaya,sai jikin
Zarhus ya kama tsuma ya sauko daga kan keken
shanun ya zube a kasa gaba Sarki tamkar zai
masa sujjada,sannan ya bude baki cikin rawar
murya yace,Ya shugabana sharace ta matattun
kwari kuma tayi yawa ne shi yasa kafin mu gama
kwasheta lokacin ya kure mana.Koda jin wannan
batu,sai Sarki Sharkuf ya sake bata rai yace,ban
yarda ba a bude akwatunan gaba dayansu na
gani.Dajin haka sai dakaru suka rugo izuwa kan
keken shanun suka kama bude akwatunan sarki
Sharkuf yazo kan akwatin farko wacce a
karkashinta ne Gimbiya Malika ke kwance tana
fama sharar barci kamar gawa.Koda sarki Sharkuf
yaga matattun beraye da kunamai da kyankyasai
har sun fara doyi sai yayi sauri ya toshe
hancinsa.Har ya yunkura zai duna cikin ta biyu sai
ya dawo da baya ya daga kwagirinsa da nufin ya
lumata cikin akwatin farko domin ya jiyo karshen
zurfinta,kawai sai yaji an kwala masa kira,yana
waigawa baya yaga ashe shugaban tsaro na gidan
ne ya tawo da gudu yana sassarfa da tuntube
kamar wanda zai fadi yana cewa,ka gafarceni ya
shugabana nayi kusjure da baka riskeni ba anan
bakin kofa.Koda jin wannan batu,sai sarki Sharkuf
ya basa luma kwagirinsa a cikin akwatin ya juyo
ya fuskanci Badakare Muhutur yana mai kyalkyala
dariya yace haba yakai Muhuru ai bazaka tabayin
laifi ba a wajena saboda yau shekara arba'in da
biyar kenan kana aikinka na tabbatar da tsaro,ba'a
taba kama da laifi ba,wata almundahana ko rashin
gaskiya ba.Shin ka caje wadannan akwatunan guda
arba'in da daya na shara ka tabbatar cewa sharace
zalla a ciki ba'a boye wani abu ba?Muhutur ya
gyada kai yace,na caje su gaba daya ya
shugabana,babu wani abu a ciki sabanin wanda ka
gani.Koda jin haka sai Sarki Sharkuf ya saki
ransa,hankalinsa ya kwanta,ya kyalkyale da dariya
sannan ya dafa kafadar Muhutur yace,na yarda dakai
dari bisa dari nasan cewa ba zaka taba cin amana
taba,kuma bazaka taba yarda ayi wani abu ba wanda
zai cutar dani koya cutar da wani nawa.Koda gama
fadin haka sai Sarki Sharkuf ya dubi Zarhus yace ko
kayan laifi ka dauko a yaudai ka sha.Zarhus ya
risina yayi godiya sannan ya sake hawa kan keken
shanun ya saki linzami ya fice daga cikin gidan
sarautar.Sarki Sharkuf ya bishi da kallo kawai a
lokacin da Muhutur yaji idanunsa sun ciko da kwalla
kamar ya fashe da kuka,saboda yasan cewa tabbas
yasha cin amanar sarki ana shigowa gidan da
abubuwan da basu dace ba ko kuma a fitar da
wasu.
Tafiyar rabin sa'a kacal direba Zarhus yayi ya iso
kofar gidan yarima Lahaman dake bayan gari.Da
isowarsa sai shugaban masu gadin gidan ya
dubeshi ya daka masa tsawa yace,kai kuma wane
irin wawa ne da zaka kawo shara nan gidan?Waye
ya baka umarnin yin hakan?To kayi sauri ka bace
daga nan tun kafin Yarima ya fito ya ganka yasa
takobi ya sareka.Maimakon Zarhus yace wani abu
sai kawai ya sauko daga kan keken shanun ya bude
wannan akwatin ta farko.Yana budewa saiga Gimbiya
Malika kwance a ciki tamkar gawa bayan ya dauke
matattun kwarin dake samanta.Cikin kaduwa da
mutukar firgici masu gadin gidan sukayi kamar su
ruga izuwa cikin gidan amma sai suka fasa
sakamakon ganin Malika zaune a cikin akwatin
tamkar gawa ta faso kabari.Ashe dama can kuyanga
Lasmira ta auna iya tsawon lokacin da Malika zatayi
barcin kuma ta farka adaidai lokacin da Zarhus ya
iso kofar gidan Yarima Lahaman.Shiyasa tace da ita
tasha wannan maganin barcin makurwa biyu.Koda
Malika ta bude idanunta ta tsinci kanta a cikin keken
shanu,ga akwatuna arba'in a bayanta kuma gata a
kofar gidan Yarima Lahaman,sai farin ciki ya
lullubeta ta sako kasa daga kan keken shanun
sannan ta dubi shugaban masu gadin ta daka masa
tsawa tace zakaje ka gayawa ubangidan naka cewa
gani na iso ko aa?Kodajin haka sai badakaren ya
juya da sauri ya fada cikin gidan.
Acan cikin gidan kuwa sarki Hilairu tare da ragowar
jama'arsa bayi mutum dari na zaune sunyi jugum
jugum suna tunanin halin da suka tsinci kansu ta
rayuwar kunci,damuwa dakuma wahala.A yau dinma
tun safe da aka basu abinci ba'a sake basu
ba.Gashi har rana ta fadi magariba ta doso
kal.Dukkanninsu jikinsu yayi sanyi lagwab tamkar
jikakkun tsumokara musamman matan cikinsu
wadanda dole ne mutum ya kamu da tausayinsu
Idan ya kallesu saboda su masu rauni ne basu da
juriya irinta maza.
Kwatsam sai ga....

Suleiman zidane kd .

Kwatsam sai ga Yarima Lahaman ya shigo cikin
dakin dakarunsa na take masa baya fuskarsa a
murtuke babu alamar annuri.Kai tsaye Lahaman
ya durfafi inda sarki Hilairu ke zaune ya dube shi
yace,ya kai wannan sarki naga alama cewa kai
mutum ne mai sa'a domin gashi ina shirin na
siyar dakai gobe ga manyan attajiran da zan sami
babbar riba,amma sai gashi 'yar uwata tazo
yanzu domin ta siyeka.To ka sani cewa karkon
kifi
zakayi domin babu wani abu da ya taba shigowa
hannuna kuma ya kubuta.Nayi maka alkawarin ko
ka subuce mini yanzu nan,ba da dadewa ba saika
dawo hannuna,kuma saina siyar dakai ga inda
za'a tafi daku izuwa wani bangaren na duniya
mai nisan gaske inda ko duriyarka ba za'a sake
jiba.Koda gama fadin hakan,sai Yarima Lahaman
ya fice daga cikin dakin tare da dakarunsa masu
take masa baya suka nufi can wajen
gidan.Gimbiya Malika na tsaye kusa da keken
shanunta mai dauke da akwatunan kudi saiga
yarima Lahaman ya fito daga cikin gidan.Koda
yaga Malika a gaban keken shanu mai daukar
akwatunan sharar gidan sarauta saiya bushe da
dariya yace,yanzu yar sarki ce guda a cikin kekn
daukan shara,to yanzu ina kudin da zaki siyi
bawan?Koda jin wannan tambaya,sai Malika ta
turbune fuskarta tace,a ina ka taba ganin anyi
cinikin kifi a ruwa,muje ka nuna min abinda nazo
siya na ganshi a raye cikin koshin lafiya sannan
muyi cinikin ba biya.Koda jin haka,sai Yarima
Lahaman yayi murmushi yace,Tabbas kina da
wayo da dabara ki biyo ni a baya muje kiga
muradinki.Yana gama fadin hakan sai ya juya ya
shige cikin gidan.Kawai sai Malika ta dubi
dakarun
dake kofar gidan tace,ba baku ajiyar keken
shanuna da direbansa,idan na fito na iske wani
abu ya taba lafiyarsu abaka cin rayuwarku.Tana
gama fadin hakan sai tabi bayan Yarima
Lahaman
da sauri har suka iso dakin dasu Sarki Hilairu ke
ciki.Da zuwansu aka bude musu kofa suna shiga
sai Sarki Hilairu da Gimbiya suka hada Idanu take
yaji zuciyarsa ta buga da karfi karo na biyu na
haduwarsu.Ita kuwa Malika ji tayi gaba dayan
tsigar jikinta ta tashi kuma sai kwarjinin Hilairu
da
tsananin kyawun fuskarsa suka dimantata tayi
sauri ta dauke mazansu da matansu.Take taji ta
kamu da tsananin tausayinsu don haka sai ta
dubi yarima Lahaman tace ciniki ya sauya salo
yanzu ba mutum saya kadai nake so ka siyar min
ba,gaba dayan bayin dake cikin dakinnan nake
bukata.Koda jin wannan batu,sai yarima
Lahaman
ya bushe da dariyar keta yace,yaya ke da bakizo
da kudin siyan mutum daya ba ma amma kike
tunanin siyan mutum dari?Malika tace,ai sai ka
bari mu gama cinikin tukunna idan kaga na kasa
biyanka kudinka shine kake da bakin
magana.Lahaman yayi gyaran Murya sannan
yace,shidai wannan saurayi ma'abocin kyawu da
kike son ki fansa sai kin biyani kudi dinare dubu
dari biyar.Su kuwa ragowar yan'uwan nasa ko
wane dayansu sai kin biya dinare dubu hamsin
sannan zaki mallake su.Koda jin wannan batu,sai
Gimbiya Malika ta dubu Yarima Lahaman cikin
alamaun fishi da bakin ciki tace,haba yakai
yarima ai ko ranar kasuwar garin nan ba'a taba
siyar da bawan da darajarsa takai dinari dubu
biyar ba amma kai yanzu gashi kace na siyi
kowane daya akan farashin dubu hamsin.Shidai
wanacan saurayin ma'abocin kyau da kwarjini na
yarda na siye shi a farashin da ka fada,domin
darajarsa ma tafi haka,amma ina neman sassauci
akan ragowar bayin.Koda jin haka sai Yarima
Lahaman ya turbune fuskarsa yace,ai ba neman
kai nake yi ba dasu,idan ba zaki iya siyansu ba a
wannan farashin saidai ki hakura gaba
daya.kuma
inda kina bukatarsu sai ki biya kudinsu yanzu
take
sannan ki kada ki tafi dasu.Malika tayi murmushi
tace,kudi ba matsalata bane yadda zan kashe su
shine matsalata.muje wajen keken shanun na
biyaka kudinka duka,amma lallai kasa a kwance
wadan nan bayi daga cikin sarkoki su biyo mu
izuwa waye.Batare da wata gardamar komai
ba,yarima Lahaman yasa dakarunsa suka kwance
bayin daga cikin sarkoko aka tusa keyarsu izuwa
wajen gidan Sarki Hilairu ne akan gaba ana
ingiza
keyarsa ana kai masa bugu.Da fitowarsu kofar
gidan sai aka jera bayin akan layi sahi sahu
sannan Lahaman ya tsaya a gabansu dakarunsa
kuma suka yiwa bayin KAWANYA,nan take Malika
ta dubi Zarhus tace ina dukiyata?Zarhus na jin
wannan tambaya sai ya sauko daga keken
shanun
ya bude akwati ta biyu ya cire shimfidar sama
mai dauke da matattun kwari,sai ga lu'u lu'u
birjik a kasan mai yawan gaske wanda ya isa
Malika ta biya gaba daya kudin da aka siyar mata
da bayin gaba dayansu har sarki Hilairu
kuwa.Koda Yarima Lahaman da dakarunsa sukayi
arba da wannan duki mai yawa haka,sai suka
cika
da tsananin mamaki yadda akayi ta
mallaketa.Kawai sai Malika ta dubi Lahaman
tace,kasa yaranka amintattu su debi iyakar kudin
daka siyar mini da wadannan bayi duka su bar
mini ragowar.Cikin rawar jik Lahaman ya dubi
wasu mutum biyu daga ckin su yace,ku kirga
adadin dinare dubu dari biyar da kuma dinare
dubu hamsin sau dari.Nan taje kuwa dakarun
biyu suka shiga kirga lu'u lu'u suna zubawa a
cikin buhu saida suka shafe sa'a uku suna
wannan aiki sannan suka kammala amma duk da
haka sai da suka gama dibar iyakan adadin da
aka umarce su kuma suka rage kudade da
yawa.Bayan an dankawa yarima Lahaman ya
karba yana ta farin ciki da walwala sannan an
saki bayin sunzo bayan Malika sun tsaya.Sai
Malika ta bude ragowar akwatunan da hannunta
sai gashi kowacce akwati cike take da dinare da
lu'u lu'u fal wadanda in da za'a bawa mutum
guda daya jal to zai shafe shekaru dubu a
rayuwarsa yana cin abinci yana sa irin suturar
dayake so yana walwala batare da sun
kareba.Koda Yarima Lahaman...


Zidane kd..


Koda Yarima Lahaman ya kyallara ido yaga wannan dukiya mai dumbin yawa sai kishi ya
turnukeshi gami da tsananin mamaki yadda akayi Malika ta tara wannan dukiya.Shidai ya sani cewa
babu yadda za'ayi sarki Sharkuf ya iya bata duk
irin tsananin son da yake mata saboda ya
kasance mutum mai kwatanta adalci a tsakanin
'ya'yansa.Bayan Malika ta gama nunawa Yarima
Lahaman wannan dukiya sai ta dubeshu tace,Ya kai Yarima ashe burinka gajere ne ban sani ba.A
zatona zaka bukaci dukiya mai yawan da tafi
wannan danazo da ita,kuma tabbas dana baka na
sake baka wata ninkinta,saboda ina da ira ninkin
baninkin.Ina so ka sani cewa ni Gimbiya Malika MURUCIN KAN DUTSE nake ban fito ba sai dana shirya.Kabar ganin cewa babu kamarka a
harkokin cinikin bayi a wannan nahiyar har kayi tunanin cewa kafi kowa kudi da arziki.,to ina mai
tabbatar maka da cewa ni Malika a halin yanzu
na tara dukiya da baka da kaso daya cikin
gomanta.Duk harkokin na cinikin abinci dana kayan yaki da ake yi da manyan Kasashen duniya
a wannan zamani nice babbar dilar da babu
kamarta.Itama harkar cinikin bayin ka zauna cikin
shiri kwanan nan

1 Comments On SA MAZA GUDU 1 to 9
avatar
adamu-3

1 year ago

Reply

Masha Allah Allah ya Kara basira Aboki

Please Login or Register in order to submit comment