Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

domin gaba daya birnin namu
bai wuce matsayin wata yar karamar unguwa ba
a
cikin nasu garin,haka muke samun labarin a
bakin
fatakensu.A ranar dana shike shekaru goma sha
takwas ne muka shiga daji tare da mahaifina da
dukkan mai farauta domin yin wata farauta rin
wacce
ba'a taba yin mai tsananin wahalarta ba,kuma
har
dashi kansa a cikin gasar,wanda duk ya kashe
dabbobi uku da sukafi na kowa girma da hadari
shi
kadai ba tare da taimakon kowa ba shi
ne ya lashe gasar.A wannan rana da yawa daga
cikin mafarautanmu sun kusan rasa rayukansu
domin kowannensu da kyar ya dawo gida jikinsa
cike da raunika,shi kansa mahaifina saida ya
sami
manyan raunika guda uku.Nine kadai na dawo
gida
cikin koshin lafiya babu ko rauni daya a
jikina,alhalin
nayi gumurzu da yaki.Damisa da kura Da Zaki
kuma
duk na kashesu na janyo gawarwakinsu a kas har
cikin gari gefin magriba ne na shigo cikin gari
janye
da wadannan dabbobi uku,Tun daga nesa na
hango
gaba daya mafarautan zaune a kofar gari suna
jinyar
jikinsu,wasu na dinke musu raunika,wasu ana
samusu magani.A gefe daya kuma mutanen gari
ne
suka taru sukayi cincirindo suka zuba ido domin
suga wanda zai lashe gasar.Kuma dokar gasar
itace
indai rana ta fadi gaba daya mutum bai shigo
gari
ba to ya fadi gasar sannan kuma anasa ran cewa
mutum sakamakon gumurzun da dabbobin dajin
saidai a tafi neman gawarsa.Adaidai wannan
lokaci
mahaifiyata na tsaye daf da mahaifina wanda ke
zaune bisa kujera likta na dinke raunikan jikinsa
kuma shima dakyar ya kwaso manyan damisoshi
guda biyu.Koda mahaifiyata taga cewa saura
kiris
rana ta gama faduwa amma babu ni babu
doriyata
sai nan take idanunta suka ciko da kwallah ta
fara
zubar da hawaye,Sa'dda hawayen nata ya diga a
kan
kafadar mahaifina sai ya daga kai ya dubeta
cikin
murmushi yace,kwantar da hankalinki yake uwar
gida,zuba idanunki da kyau izuea can cikin daji
zaki
ga wata kura na tashi,takun sawayen danki ne
Hibairu da kuma dabbobin da yake ja a kas.Ai
kuwa
mahaifina bai gama rufe bakinsa ba sai jama'a
suka
hangoni a tafe ina layi kamar zan fadi saboda
tsananin gajiya,kuma na daure da gawar
zaki,kura
da damisa da wata igiya ina janyosu a
bayana.Koda
jama'a sukayi arba dani sai suka rude da shewa
gami da tafi da jinjina ana tayani murnar lashe
wannan gasa,hatta sarki garinmu a wannan
lokaci
baisan sa'adda ya rinka daga hannunsa ba
yanayi
mini jinjina,ita kuwa mahaifiyata rugowa tayi da
gudu ta rungumeni ni kuma ta fashe da kukan
farin
ciki.
Mu hadu a cikin Littafi na biyar (5) don jin
cigaban
wannan labari.An dauko wannan littafi daga shafin www.dlhausanovels.com.ng ku ziyarci shafin na www.dlhausanovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya

Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,

Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan
Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490

A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,

Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu

Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC

Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from www.dlhausanovels.com.ng
You can download more hausa novels there
Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online
It is free we do not charge for uploading novel
Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services

Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us

Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it

Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT
An dauko wannan littafi daga shafin www.dlhausanovels.com.ng ku ziyarci shafin na www.dlhausanovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya

Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,

Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan
Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490

A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,

Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu

Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC

Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from www.dlhausanovels.com.ng
You can download more hausa novels there
Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online
It is free we do not charge for uploading novel
Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services

Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us

Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it

Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXTMAZA GUDU
Littafi na Biyar (5)
Part A
•Ita kuwa mahaifiyata rugowa tayi da gudu ta
rungumeni kuma ta fashe da kukan farin
ciki.Bayan
an bani kambun Sarauta na gasa,wato mahaifina
da
kansa ya kwance kambun daga jikin hannunsa ya
daura a nawa,sai mutane suka rude da kabbara
aka
cigaba dayi mini jinjina,a lokacin ne mahaifina ya
daga kansa da hannayensa sama yayiwa Allah
godiya cikin matukar farin ciki daya sanya dansa
ya
gajeshi.Kwatsam a na cikin wannan dimbin
farinciki
ne aka hango wani mahayi ya durfafo cikin garin
a
guje bisa wani ingarman doki,tun daga nesa aka
gane cewa bako ne kuma yana sanye da tufafi
irin
na dakarun birnin Kisra.Da isowar wannan
badakare
daf da sarkinmu sai ya tsayar da dokinsa ya
sauko
kasa da sauri ya zube a gaban sarki ya kwashi
gaisuwa,sannan yace,ya shugabana,Sarki Zaldasi
Bin
Auzir na birnin Kisra ya aiko ni gareka da
wasika,ni
manzo ne daga gareshi don haka ina jiran amsar
da
zan maida masa.Koda gama fadin hakan sai
badakaren ya sanya hannu cikin aljihun rigarsa
ya
fiddo wasika a cikin fata mai inganci da daraja
ya
mikawa sarkinmu.Nan take kowa dake wajen ya
cika
da dinbin mamaki da tsoro saboda wannan ne
karo
na farko da kasar Kisra ta aiko da manzo izuwa
birnin Nurul Islam.Hannun sarkinmu na karkarwa
ya
karbi wasikar ya warwareta sannan ya fara
karantata
a fili yadda kowa ke iya sauraro kamar
haka:"Wasika
daga hannun sarkin sarakuna mai daraja ta daya
kuma mai birnin Kisra Zaldasi bin Auzir,zuwa ga
sarki Hayat Usman na Birnin Nurul Islam.Bayan
gaisuwa da fatan Alheri,ina mai farin cikin
gaiyatarku
a karo na farko izuwa kasata domin halattar
GASAR
FARAUTA irin wacce ba'a tabayin kamarta ba a
wannan nahiya gaba daya.Saboda girman wannan
Gasa ne yasa nayi alwashin saina gaiyaci duk
kasashen dake nahiyar,har da taka kasar wacce
bamu taba hulda da ita ba,ka sani cewa duk
jarumin
daya lashe wannan gasa yanada zabi uku,ko dai
na
raba kasata biyu ba bashi rabi ya mulka,ko na
bashi
dukiyar da zuri'arsa gaba daya har su kare
bazasuyi
rashi ba.Ko kuma na bashi rikon kasuwancin
nahiyar
nan gaba daya,lallai ka tsaya ka tantance ka
zabo
jarumin daka tabbatar dazai iya shiga wannan
gasar
saboda hadarinta daidai yake da TUNKARAR
AJALI.Duk jarumin dayazo birnina yaji yanayin
wannan gasa kuma ya tsorata yace bazai iya ba
hukuncin kisa ne a kansa."Koda sarki yazo nan a
zancensa sai hankalin gaba dayan jama'ar garin
ya
DUGUNZUMA ainun,shi kuwa sarki sai ya kama
murmushin mugunta da farinciki ya dubi
mahaifina
Uraisu yace,ai shike nan yar manuniya ta
nuna.Babu
wanda yafi cancanta daya wakilcemu a wannan
gasa
sama da danka Hibairu tunda yanzun nan ya
zama
sarki mafarautarmu ma'ana ya gajeka.Koda jin
haka
sai Mahaifina yace haba ranka ya dade,yaza'ayi
a
tura Hibairu izuwa wannan gasa wacce za'a tara
manyan jaruman duniya alhalin shi yaro ne
karami
dan shekara goma sha takwas kacal,kada ka
manta
fa cewa shine babban dana kuma babu wanda
zai
iya karbar matsayinsa daga cikin kannensa,shine
kadai zai iya ci gaba da ruke wannan babbar
sana'a
tamu ta farauta a wannan birnin namu mai
albarka
tunda ni yanzu girma ya fara kamani.Sarki
Zaldashi
bai fadi yanayin wannan gasa ba bare musan irin
hadarin dake cikinta ba,baka tunanin cewa idan
muka tura Hibairu tamkar mun turashi izuwa
FARAUTAR AJALINsa ne?Koda mahaifina yazo
nan a
jawabinsa sai gaba dayan sauran jama'a suka
goyi
da bayansa suna masu nuna cewa basu amince a
tafi dani ba izuwa wannan gasa.Al'amarin da
yasa
ran sarkinmu ya baci kenan ya daka tsawa kowa
yayi shiru sannan ya ce,idan har Hibairu bazaije
wannan gasa ba,saidai mahaifinsa ya
wakilceshi,tunda bamu da wani GWARZON
JARUMI
masanin farauta dayakai daya daga cikinsu in ba
haka ba kuwa saidai a fasa tura kowa in yaso
sarki
Zaldasi ya dauki matakin dayaga ya dace a
kanmu.Koda jin wannan batu sai ran mahaifina
ya
baci,ya dubi Sarki a karo na farko a
zamantakewarsu
ya daka masa tsawa yace,ban taba sanin cewa
kiyayyarka a kaina da ahalina takai haka ba sai
yau,yanzu saboda kawai kaga baya na ka yarda
ayi
asarar daruruwan rayukan jama'a a garin
nan,shin
ka manta ne cewa kai musulmi ne wanda bai
yarda
da azubar da digon jinin mumini ba a banza,shike
nan tunda abin yazo da haka ni na amince zan
wakilci garin nan a wannan gasa,domin bani da
burin dayafi dana ya gajeni kuma ya ci gaba da
karfafa tattalin arzikin garinmu.Koda jin wannan
batu
sai jama'a suka rude da shewa suna masu nuna
gamsuwarsu,kawai sai akaga na kama hannun
mahaifina na jashi izuwa can gefe daya inda
babu
wanda zaiji abinda zamu tattauna,sannan na
dubeshi
a cikin nutsuwa nace,yakai Abbana shin ka
manta
ne ka gaya mini cewa akwai wani babban nauyi a
kan gaba dayan mutanen garin nan wanda a
ranar
gobe kiyama sai Allah ya tuhume mu a
kansa,wannan nauyi kuwa ba na komai bane face
na
yada addinin Allah a wannan nahiya.Saboda
tsoron
karya doka da yarjejeniyar dake tsakaninmu da
manyan kasashen nahiyar nanne yasa muka kasa
tallata addinin Allah a garesu.Na sani cewa ka
dauki
alkawari ga iyayenka da sarkinmu daya gabata
cewa
zaka kiyaye wannan yarjejeniya to amma aini ban
dauki wannan alkawari ba a garesu,ko a
gareka,ka
sani cewa wannan gasa da zanje nayi itace kadai
hanyar dazanyi amfani da ita wajen yada addinin
Allah ga sauran kasashen.Na sani cewa gasar
daza'ayi wahalarta da hadarinta yafi gaban
tunanin
kowa,KARFI ko TSAFI bazai sa mutum ya sami
nasara ba face da taimakon Allah.Zan roki Allah
a
kan ya bani sa'a da nasara a cikin wannan
gasa,idan kuwa nayi nasara agaban miliyoyin
jama'a
da suka taru daga sassan duniya zan fadi cewa
babu wanda ya bani sa'a
da nasara a cikin wannan gasa face ubangijin
Musulunchi.Kaga kuwa ko kasheni akayi a wajen
na
gama samun nasara gami da babban rabo domin
MUTUWAR SHAHADA zanyi.Tabbas idan na fadi
hakan miliyoyin jama'a zasuyi imani su karbi
musulunci.Yakai Abbana shin kana so na sami
wannan shahada ko kuwa kafison mu tafi lahira
da
wannan babban nauyi.Allah ya tuhumemu a
kansa?
Koda nazo nan a zancena sai hawaye ya zubowa
mahaifina take ya rungumeni a lokacin dani ma
na
fara zubar da hawaye yana mai cewa.Yakai dana
hakika yau ka nuna mini cewa na dade a cikin
sabon Allah don haka daga yau zanyi ta istigifari
har
izuwa ranar mutuwa ta,tabbas mu da iyayenmu
da
suka gabata muna dauke da katon nauyi wanda
kai
kadai ne a yanzu zaka iya sauke mana shi.Idan
jama'r birnin Nurul Islam suka shude gaba daya
ba
rahamar Allah,saboda haka na yarje maka ka tafi
izuwa wannan gasa,RAI da MUTUWA duk na
Allah
ne,dama fatanmu kawai shine mu sami yardar
Allah.Koda gama fadin haka sai mahaifina ya
kama
hannuna ya jani izuwa gaban sarki ya damka ni a
hannunsa yace,da izinina da kuma yardata na
baka
dana Hibairu a tafi dashi izuwa Birnin Kisra
domin
ya wakilci garin nan namu mai albarka a wannan
gasa.Koda jin wannan batu sai kowa ya cika da
matukar mamaki,mahaifiyata kuwa sai ta rugo ta
rungumeni ta fashe da matsanancin kuka ta dubi
sarki tace,ina neman alfarmar ka barmin dana
daga
nan zuwa wayewar gari domin muyi bankwana
saboda nasa cewa in ya tafi bazai dawo.Koda jin
haka sai tausayinta ya kama kowa a wajen,da
yawan
jama'a suka kama kuka,shi kuwa sarkinmu sai
farinciki ya lullubeshi ya dubi mahaifiyata
yace,jeki
da danki kiyi masa kallon karshe amma ki sani
cewa
ana idar da sallar asuba zan hadashi da wannan
manzo na sarki Zaldasi su tafi izuwa birnin
Kisra.Sarki na gama fadin hakan sai ya juya ya
nufi
cikin gari,fadawansa da dakarunsa na take masa
baya tare da wannan manzo na sarki
Zaldasi.Nanfa
jama'a suka fara yiwa iyayena jaje tamkar ma na
mutu,saboda gani ake lallai bazan dawo ba gida a
raye ba,dani da iyaye na da sauran jama'ar gari
muka dawo gida a cikin jimami da bakin
ciki,amma
ni a cikin zuciyata ko kadan bani da tunanin idan
na
tafi bazan dawo baAbinda nayi imani dashi shine
babu abinda zai gagari Allah.A wannan rana dai
mahaifiyata batayi barci ba,duk sa'adda na farka
daga barci saidai na ganta a zaune a gefen
gadona
ta kura mini idanuwa tana zubar da hawaye,da
kyar
na rarrasheta muka kwanta tare tana rungume
dani
har barci ya saceni bata sani ba.Mahaifiyata
Samsira
tana tsananin kaunata,saboda nine kadai danta a
duniya,kuma daga kaina Allah bai sake bata
haihuwa
ba,bata da kowa a duniya face ni da mahaifina
don
haka duk abinda taga zai rabamu shine babban
makiyinta.Bayan anyi sallar asuba mun dawo
daga
masallaci nida mahaifina,sai muka iske
mahaifiyata
zaune a falo fuskarta a murtuke kuma idanunta
sunyi sharkaf da hawaye,koda ta hangomu mun
shigo falon sai ta taso da sauri ta taremu ta dubi
mahaifina a fusace karo na farko a rayuwarta
tace
saboda me zaka bayar da dana shi daya jal daga
cikin 'ya'yanka goma sha biyu domin aje a kashe
shi?Ashe dama baka kaunarsa haka ban sani ba
kuma nima baka kaunata tunda kanaso ka rabani
da
rabin jikina?Koda mahaifiyata tazo nan a
zancenta
sai nida mahaifina muka kamu da tsananin
tausayinta saboda munsan cewa tsananin
soyayyarta
a gareni ce yasa tayin wannan kalami.Nan take
mahaifina ya janyota ya rungumeta a kan kirjinsa
a
lokacin da hawaye ya subuto masa.Cikin rada
yadda
babu mai jin abida yake gaya mata ya zaiyane
mata
duk maganganun da yasa ya amince na tafi
izuwa
wannan gasa.Koda mahaifiyata taji cewa wannan
tafiya da zanyi daidai take da JIHADI,sai farin
ciki ya
lullubeta ta janye jikinta daga cikin na mahaifina
ta
rungumeni tana mai sa mini albarka gami dayi
mini
fatan sa'a da nasara.A gidanmu gaba daya saida
aka
cika da tsananin mamaki bisa ganin yadda
mahaifiyata ta daina bakin cikin wannan tafiya
tawa,ya zamana cewa ta dawo tana farin ciki
fiye da
kowa,kuma bata sake zubar da hawaye ba,har
saida
muka zo yin bankwana na karshe a lokacin datayi
mini sallama ta juyo mini baya ina kan doki,saida
ta
kusan shigewa cikin gida sannan ta waigo naga
hawayen a cikin idanunta.Daga wannan rana
kawo
iyanzu dana cika shekara ashirin da biyar ban
sake
ganin iyaye na ba kuma ban sami labarin su bare
nasan halin da birninmu ya shiga ba bayan
tafiyata
saboda babban bala'in dana fuskanta.Lokacin da
Jarumi Hibairu yazo daidai nan a labarinsa sai ya
daga kai ya dubi Gimbiya Zuhura da sarki,bisa
mamaki saiyaga idanun Zuhura cike da hawaye
saboda tausayi,amma shi sarki Kamzal idanunsa
a
bushe suka kuma fuskarsa a murtuke take babu
annuri.Kawai sai ya dubi Hibairu cikin zakuwa
yace,ina sauraronka maza ka cigaba da bani
wannan
labari mai ban Al'ajabi.Da kuka isa birnin Kisra
me
ya faru kuma yaya yanayin wannan gasa ya
kasance.Koda jin wannan tambaya sai na dubi
sarki
Kamzal cikin alamun rashin yarda nace yanzu
kana
nufin kace dani baka halacci wannan taro ba
alhalin
a nahiyar nan kaf babu sarki da bai amsa
gaiyatar
sarki Zaldasi ba a wannan lokaci.Cikin rawar
murya
da alamun rashin gaskiya Sarki Kamzal yace
tabbas
na amsa gaiyatar sarki Zaldasi kuma na isa birnin
Kisra amma akasin da aka samu shine har aka
gama
gasar ina kwance a masaukina banda lafiya,ban
sami damar halattar dajin da akayi gasar ba.Koda
jin wannan batu sai jarumi Hibairu ya ajiye
numfashi
gami da gyaran murya sannan ya ciga da bayar
da
labari kamar haka."Ni da manzon Sarki Zaldasi
ne
kadai muka kama hanya muka baro birnin Nurul
Islam.Lokacin da muka iso
bakin gabar kogin daya zagaye birninmu,muka
iske
wani babban jirgin ruwa na fatake,ba tare da
bata
lokaci ba wannan manzo ya biya aka shigar
damu
cikin jirgin harda dawakanmu a ka cigaba da
tafiya a
cikin tekun.Fataken dake cikin wannan jirgi
sunkai a
kalla mutum saba'in da biyar,kuma maza ne da
mata,matasa da tsofaffi,kowa ka gani a cikin
jirgin
yana dauke da guzurinsa kuma da yake jirgin na
sarkin Birnin Kisra ne akwai dakaru a cikinsa
masu
tabbatar da tsaro don haka babu wani bafatake
dake
cikin tsoron salwantar da dukiyarsa.Daga
kasarmu ta
Nurul Islam zuwa birnin kisra a jirgin ruwa sai da
muka shafe kwani goma sha daya muna ratsa
teku,mu sauka a wancan gari mu huta mu cigaba
da
tafiya har muka isa can.Ana sauke mu a gabar
ruwa
aka fito da dawakanmu muka hau,ina biye da
manzo
Imsar a baya muda sauran fataken muka nufi
hanyar
dazata kaimu cikin birnin kisra.A wannan lokaci
dare
ya raba kuma wannan shine karon farko a gareni
dana tabayin tafiya mai nisa duk yawona baya
wuce
iyakar wadansu yan kauyukan dake kusa da
garinmu
amma ban taba zuwa wani babban birni ba saidai
naji ana labarinsu a na cewa sun kawata da gine
gine na zamani.Tun daga nesa na hango birnin
kisra na zama cikakken dan kauye saboda hango
gidaje masu hawa hawa na gani tubali,duk da
cewa
dare ne amma an kawata birnin da fitulu tamkar
rana,su kansu fitulun da akayisu a cikin wadansu
irin kwalabe mamaki suka rinka ba.Abinda na
aiyana
a cikin raina shine anya kuwa ba aljanu bane
suka
kawata wannan birni?Da muka iso bakin kofar
garin
saida dakarun tsaro suka duba kowa kuma aka
duba
kayan kowa sannan aka bude mana kofa muka
shiga.Wohoho ai muna shiga cikin birni na kisra
na
wangame baki saboda tsananin
mamaki,musamman
muka durfafi hanyar zuwa gidan sarautarsu,duk
inda
muke takawa da kafafun dawakanmu babu
kasa.Ko
ina dutsen Jauhar ne aka shimfida a katangar
gidan
sarautar kowacce da dutsen murjani akayi
ta,muna
shiga cikin harabar gidan sarautar kuwa sau naga
gaba daya ginin gidajen ciki da dutsen Yakutu
akayi
su,duk kofar da muka iso sai mun iske masu gadi
a
kalla mutum arba'in kuma sun kasance
samudawan
dakaru masu tsananin kwarjini da kira ta
sadaukai
dauke da muggan kayan yaki amma da zarar
sunga
manzo Imsar sai su bude mana kofa mu shiga.A
haka dai saida muka ratsa ta cikin kofofi
tara,fadoji
goma sha daya,ina ta kalle kallen abin al'ajabi ina
mamakin yadda mutane suke shagala da duniya
haka tamkar bazasu mutu ba a binne su cikin
kasa.Abinda zuciyata ke wassafani shine wai
shin
yaya cikin turakar sarkin Kisra zata kasance
kuma a
cikin wacce irin daula 'ya'yansa da matansa
suke.Lokacin da muka iso fada ta goma sha daya
ne
aka tsayar damu,muka sauko daga kan
dawakanmu
wadansu bayi biyu suka karbi dawakan suka tafi
dasu.Kawai sai Imsar ya kama hannuna ya jani
izuwa wani bangare dabam yakai ni izuwa cikin
wani
kasaitaccen gida,ashe nanne masaukina.Koda ya
shiga dani cikin dakin barci nayi arba da wani
luntsumemen gado mai dauke da shimfidu masu
tashi sai yace dani anan zaka kwana sai gobe da
safe zanzo na kaika wajen sarki na gabatar masa
da
kai.Koda jin haka sai tsoro ya kamani domin gani
nake ina hawa kan gadon zai hadiye ni.Kafin na
budi
baki nace wani abu tuni Imsar ya janyo kofar
dakin
ya rufe ruf ya barni ni kadai a cikin dakin cikin
alamun tsananin tsoro.Naje na rinka danna
shimfidar
gadon da hannayena biyu domin na gani ko bazai
cutar dani ba,koda naga babu wata matsala sai
na
fada kan gadon ba kwanta.Abinka da gajiyayye
nanda nan barci ya sace ni ban farka ba saida
gari
ya waye,hasken rana ya shigo cikin dakin ta taga
ya
bugi fuskata,a firgice na mike zaune
zumbur,kawai
sai nayi arba da wadansu kyawawan kuyangi
guda
uka a tsaye a gabana ga abinci a faranti a
hannun
kowacce.Nan take suka ke suka ajiye abincin
bisa
wani babban tebur dake kusa da gadon
barcina,sannan suka kamani suka tasheni tsaye
suka
kaini keaye da nufin suyi mini wanka,kawai sai
na
daka musu tsawa suka firgita na korasu waje
sannan
nayi wankana,a zuciyata cewa nakeyi in banda
aikin
kafirci yaza'ayi ace 'YAN MATA su yiwa
SAURAYI
kamata wanka.Bayan na gama wanka na kintsa
kuma na gama cin abinci kenan sai na jiyo
tambura
gami da bushin algaita daga can wani bangere
na
gidan sarautar.Hakan ne yasa na gane cewa
Sarki
Zaldasi ya fito fada.Faruwar hakan keda wuya
saiga
Imsar ya shigo da sauri a cikin tufafi irin na
fadawan
sarki Zaldasi,cikin hanzari ya kama hannuna
muka
fice muka nufi fadar,muna sauri sauri gudu gudu
muka nufi babbar fada ta gidan sarautar.Nanfa
na
rinka ganin mutane da yawa ka kala daga sassan
duniya duk sun nufi babbar fadar ta sarki
Zaldasi.Idan mutum yaga tsananin yawan
jama'ar
dake kokarin shiga wannan fada sai yayi zaton
cewa
mutanen duniya ne kaf zasuyi taro.Lokacin da
muka
shigo cikin wangamemiyar fadar kuwa wacce
girmanta ya ninka na birninmu Nurul Islam sau
uku
sai na cika da dimbin al'ajabi abinda ya firgita ni
shine dutsen lu'u lu'u ne saboda haskensa da
kyallinsa ma mutum na iya ganin fuskarsa da
jikinsa
akai tamkar madubi,saman rufi fadar kuwa gaba
daya da jan Zinare akayi shi.Kafin mu kusanci
inda
karagar sarki Zaldasi take saida mukayi tafiyar
sa'a
uku a kasa har saida na gaji kuma na kosa,A
gefen
dama na fadar tun daga farkonta har izuwa inda
karagar mulki take fadawan sarki Zaldasi ne a
tsaitsaye gaba da baya.A bangaren hannu hagu
kuwa jaruman gasar farautar ne a jere su da
yawa,a
bayansu kuwa dakarun sarki Zaldasi ne wadanda
suka zagaye fadar gaba daya.Koda na dubi
jaruman
gasar sai zuciyata ta buga da karfi kuma
hankalina
ya DUGUNZUMA ainun,ba komai
ne ya haddasa hakan ba face ganin cewa gaba
dayan jaruman gasar babu dan kasa da shekara
ashirin da biyar,kuma duk kaninsu sun kasance
girda girda,wato dogaye ga kauri kuma ga kira ta
sadaukantaka,kuma kowannensu
hannayensa,kaurinsa da kugunsa cike yake da
guraye da layu na tsafi,ni kuwa in banda wata
yar
guntuwar laya guda daya dake wuyaba bani da
komai,ita ma wannan laya ba komai be a cikinta
ba
Face KALMAR SHAHADA.Haka mahaifina ya bani
labari.Hakai dai nayi ta wuce yan'uwana jaruman
gasa ina kare musu kallo zuciyata nacigaba da
daka.Su kuwa sai kyalkyala mini dariya sukeyi
suna
nuni cewa ga wani yaro wanda iyayensa suka
gaji
dashi.Ni dai ban tankawa dayansu ba har muka
iso
daf da karagar sarki Zaldasi muka zube a kasa
bisa
guiwoyinmu don girmama shi.Ina dago kaina nayi
arba da wani jarumin gasar a gefen hagun sarki
Zaldasi wanda yayi matukar girgizani ya bani
mamaki,ba wani bane face matashin sarauyi
wanda
shima shekarunsa ba zasu haura nawa ba.Ko riga
babu a jikinsa sai tarin guraye da layu na
tsafi,jikinsa a murde yake fiye fa nawa,ya tara
kwanji
da jijiyoyi.Kai da ganinsa kasan cewa ya cika
SADAUKI.Ina hada ido dashi sai ya murtuke
fuska
tamkar yaga bakin kumurci,koda ganin haka saina
yi
sauri na sake sunkuyar da kaina kasa.Adaidai
wannan lokaci ne Imsar ya gabatar dani a gaban
sarki Zaldasi a matsayin jarumin gasar dazai
wakilci
birnin Nurul Islam.koda jin haka sai sarki Zaldasi
ya
mike tsaye daga kan karagarsa ya taka gajeriyar
matattakalar dake gabansa ya sauko ya kama
kafaduna Ya tashe ni tsaye ya kura mini
idanu,kawai
sai ya bushe da dariya.Aikuwa sai fadawansa da
sauran gaba dayan jama'ar dake cikin fadar ma
suka
kama kyalkyala dariya.Harsaida sarki Zaldasi ya
tsuke bakinsa sannan fadar tayi tsit tamkar babu
mutum daya mai numfashi a cikinta.A sannan ne
Zaldasi ya nuna mini wannan jarumin gasa
sa'annan
yace kaga wancan yaron shine SA MAZA
GUDU,kabar ganinsa yaro kamar kai ka raina shi
to
yafi manya da yawa a cikin jaruman nan hadari
kuma zai iya lashe wannan gasa.Tabbas
mutanen
birninku sunyi ganganci da suka turoka ka
wakilcesu kuma inda basu turo kowa ba da saina
afka musu na baje garin gaba daya,duk da cewa
garinku ne kadai garin da yake baiwa dukkanin
sarakunan nahiyar nan tsoro.Tabbas iyayenka da
sarkinku basa kaunarka kawai so suke ka
mutu.Kofa
gama fadin hakan sai sarki Zaldasi ya juya ya
koma
izuwa kan karagarsa ta mulki ya zauna sannan
ya
dubi wani bafadensa yayi masa inkiya.Take
bafaden
ya fito tsakiyar filin fadar ya tsaya ya dubi
jama'a
sannan ya dubi jaruman gasar yace,manyan baki
daga sassan kasashen duniya,sarakuna,atta­
jirai,talakawa da jaruman gasa sarki Zaldasi ya
gaisheku kuma yanayi muku lale marhaban da
kuka
amsa gaiyatarsa kuka halacci wannan gagarumar
gasa ta farauta wacce ba taba yin kamarta ba a
duniya.A halin yanzu muna da jaruman gasa
mutum
dubu Ashirin da daya,da saba'in da bakwai daga
birane dabam dabam na wannan nahiya tamu da
sauran nahiyoyi na duniya.Ina mai sanar daku
cewa
gobe za'a fara wannan gasa,za'a shiga cikin dajin
Sairul ne gaba daya wato jaruman gasa,alkalan
gasa
da kuma yan kallo wadanda zasu iya siyar da
rayukansu ko su kare kansu domin morewa
idanuwansu da kallo.Yanayin wannan gasa shine
za'a shiga farautar wani takadarin Zaki ne mai
suna
NURUL MAUT domin a kashe shi azo da gawarsa
nan gaban sarki Zaldasi.Fiye da shekaru tamanin
baya wannan zaki mai suna Nurul Maut ya hana
shiga dajin Sairul,domin duk wanda ya shiga baya
fitowa kuma har abada ya bata kenan ko
gawarsa ba
za'a gani ba.Shidai wannan zaki sihirtaccene an
tabbar da cewa KAIFI da TSINI basa tasiri a
jikinsa,kuma komai yawan dakaru,komai iya
yakinsu
da karfin sihirinsu indai sukayi arba dashi
sunansu
gawa.Shi kansa Zaldasi kimanin shekaru bakwai
baya daya shiga dajin Sairul domin ya kashe
Nurul
Maut da kyar ya dawo gida a raye cikin mugayen
raunika.Bisa wannan dalili ne sarki Zaldasi ya
shirya
wannan gasa kuma duk wanda ya kashe wannan
zaki
ladansa shine

1 Comments On SA MAZA GUDU 1 to 9
avatar
adamu-3

1 year ago

Reply

Masha Allah Allah ya Kara basira Aboki

Please Login or Register in order to submit comment