Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

sarki zai bashi auren 'yarsa
Gimbiya
Lasmin,sannan zai raba wannan birni na Kisra
biyu
ya bashi mulkinsa,sannan ya maidashi daya daga
cikin manyan fadawa.Koda gama gadin haka sai
aka
buga tambari,kuma aka busa algaita.Faruwar
hakan
keda wuya saiga Gimbiya Lasmin 'yar sarki
Zaldasi
ta fito daga cikin gidan sarautar ta ratso cikin
tsakiyar fadar kuyangi da dakaru na musamman
na
take mata baya.Wohoho Allah shine ke
ikonsa,hakika
halittun Allah yawa garesu,babu wanda yasan
adadinsu saidai shida ya halicci kayansa.Lokacin
da
Gimbiya Lasmin ta ratso cikin tsakiyar fadar sarki
Zaldasi,sai gaba dayan mazajen dake wajen suka
dimauce suka fita daga haiyacinsu saboda ganin
tsananin kyawunta da kyawun siffar jikinta.Wasu
da
yawa basu san sa'adda suka wangame
bakunansu
ba suna dalalar yawu,wasu kuwa sambatu suka
kamayi kamar sun zautu.Kyawun Gimbiya Lasmin
yafi karfin a wassafashi,saidai abinda idanu suka
ganiKawai.Jama'a da yawa suna zargin cewa
Lasmin
ba mutum bace zalla saboda ganin yadda
kyawun
nata ya wuce tunanin mai tunani,babu wani abu
wanda mutum zai iya kwatantashi don baiyana
kyawunta.
Nima ganin tsananin kyawunta yasa na gigice na
tsaya cak ina kallonta saboda tsananin mamakin
kyawunta.thanks agode
Tohm mun ci wajen fiye da rabin Sa Maza Gudu
littafi na Biyar,dan anyi rubutun da yawa..
Daga:
SA MAZA GUDU
Littafi na biyar (5)
Part B
Kyawunta ya wuce tunanin mai tunani.Babu wani
abu wanda mutum zai iya kwatantashi don
baiyana
kyawunta.Kai tsaye gimbiya Lasmin ta wuce
izuwa
inda Sarki Zaldasi ke zaune fuskarta cike da
annuri
tamkar wata daren sha biyu tana tayin wani irin
murmushi mai taushin gaske Wanda ka iya sa
mutum ya manta da duk wani bakin cikin
rayuwarsa.Lasmin ta zauna akan kujera dake daf
da
karagar sarki sukayi kus kus irin na 'da da
mahaifi
cikin raha da annashuwa,sannan ta waigo ta fara
kallon jaruman gasar dake cikin fadar tun daga
kan
jarumi na farko.Koda tazo kaina sai ta tsaya
kyam ta
kura mini ido ko kiftawa batayi a lokacin da ni
kaina
naji zuciyata ta buga da karfi,kuma kunya ta
baibayeni don haka sai nayi kasa na sunkui da
kaina
kas.A wannan lokaci Sa Maza Gudu ne a kusa ni
don haka shine jarumi na gaba wanda ya kamata
ta
kalla amma sai taki ta daina kallona,hakane tasa
jarumi Sa Maza Gudu ya fusata ainun zuciyarsa
ta
kama tafarfasa kamar zata kone nan taje yaji ya
tsane ni kamar yadda ya tsani mutuwarsa saboda
tsananin kishi.Kawai sai ji nayi yayi mini rada a
kunne yace,kai yaro na fuskanci cewa sa'arka
tana
da yawa a cikinmu nan gana dayan jaruman
gasa,kai ne kadai wanda Gimbiya Lasmin ta kura
maka idanu tana raba da kai ta daina cigaba da
kallonmu,to kasani cewa na rantse da darajar
iyayena idan har ban lashe wannan gasa ba na
mallaki Gimbiya Lasmin to babu wanda ya isa ya
mallaketa saidai mutum ya sami wani ladan
dabam.Koda naji wannan batu sai na dubi Sa
Maza Gudu cikin murmushi nace,ai kuwa kishi
zai kasheka a banza domin ina ji a jikina cewa
nine zan lashe
wannan gasa,kuma sai na mallaki Gimbiya
Lasmin
kanaji kana gani.Kafin Sa Maza Gudu ya bude
baki
ya sake maida min da wani martani sai kawai
muka
ji wannan bafade na sarki yace,yaku jama'a sarki
yace nayi muk albishir da cewa gobe za'ayi shiri
a
tafi dajin Sairul domin fara yin wannan gasa
kuma
za'a kammala tane a cikin kwanaki uku rak,duk
jarumin daya sami nasarar kashe wannan zaki
mai
suna Nurul Maut kafin rana ta fadi bai iso nan
fada
ba to yasha wahalar banza,A wannan rana ta
uku,da
wannan nake muku sallamar kowa sai goben da
safe
ake bukatar kowa yazo nan fada domin ayi
wannan
gagarumar tafiya izuwa cikin dajin Sairul.Koda
gama
fadin hakan sai sarki Zaldasi tare da 'yarsa
Gimbiya
Lasmin suka mike tsaye suka sauko daga kan
tudun
da kujerun suke suka nufi hanyar fita daga cikin
fadar suna rike da hannun juna a lokacin da gaba
dayan jama'ar dake cikin fadar suka dukar da
kawunansu kas saboda biyayya.Saida Lasmin ta
iso
bakin kofar fita daga cikin fadar sannan ta
waigo,ai
kuwa sai muka hada idanu dani da ita tayi mini
wani
irin murmushi mai taushi mai dauke da alamar
tambaya wanda ya dimautani,naji kamar an bani
sarautar duniya sannan ta juya suka kule mana
da
gani gaba daya.A sannan ne taro ya watse kowa
ya
kama gabansa,mutanen gari suka tafi izuwa
gidajensu,mu kuma baki muka tafi izuwa
masaukinmu.Lokacin dana isa masaukina sai
kuyangi suka kawo mini abinci mai rai da
lafiya,amma sai na kurawa abincin idanu na kasa
ci,ba komai ne ya haddasa hakan ba face da
zarar
na dauko loma guda zan kai bakina saina rinka
ganin hoton fuskar gimbiya Lasmin akai.Koda
ganin
haka sai hankalina ya dugunzuma ainun saboda
na
gane cewa tabbas na kamu da tsananin son
wannan
'yar sarki,wata zuciyar tace dani amma dai kai
wawa
ne kuma shashasha,akan wane dalili zaka kamu
dason abinda bazaka samu ba,shin bakaga irin
gawurtattun jaruman da suka shiga wannan gasa
bane wadanda suka fika karfi,jarumta,tsafi da
komai?
Ai ko a mafarki ma kada kayi tunanin zaka iya
mallakar gimbiya Lasmin,haka dai na cigaba da
wannan tunani har na gaji sannan naci abincin
naje
nayi alwala nayi Sallah.Bayan na idar da Sallah
saina daga hannayena sama na shiga yiwa Allah
kirari ina mai ambaton sunayensa tsarkaka
nace,Ya
Sarki da bashida abokin taraiya,kaine mai
Daukakawa da kaskantarwa,babu wani abu dazai
gagareka,Allah ka sani cewa karfina da wayo na
bazai sa su bani nasarar komai ba a cikin
wannan
gasa,don haka bani da wani abin dogaro sai
kai.Na
mika dukkan lamarina a gareka Allah sani cewa
idan
na lashe wannan gasa na sami babbar dama
dazan
tallata addininka da ita,saboda haka ka karfafeni
da
karfinka na sami wannan nasara.Burina shine na
jaddada kalmarka a doron kasa,koda kuwa bazan
mallaki Gimbiya Lasmin ba,haka dai Jarumi
Hibairu
ya cika addu'arsa da sake kiran sunayen Allah
sannan yaje ya kwanta.wa shegari kuwa da safe
kofar gidan sarautar Sarki Zaldasi ya tumbatsa
da
mutane ana jiran sarki ya fito a tafi izuwa bakin
dajin Sairul inda za'a gabatar da gasar
farauta.Inda
ace mutum na tsaye a wannan wuri idan yaga
dumbin jama'ar da sukayi dandazo sai ya zata
gaba
dayan mutanen duniyar ne suka taru.Hakika
masu
mulki sunayin abinda suka gadama kuma duk
wanda
ya tumbatsa a mulki da kudi dole ne ayi masa
biyayya tunda sawun giwa dole ne ya take na
rakumi.Gaba daya manyan sarakunan da sukazo
wannan gasa saida suka yi jiran fitowar sarki
Zaldasi
har tsawon sa'a biyu sannan ya fito bayan
kowannensu ransa ya baci bisa ganin yadda aka
kaskantar da darajarsu.Da fitowar sarki
Zaldasi,sai
aka ganshi tare da 'yarsa Gimbiya Lasmin bisa
ingarman dawakai farare guda biyu tare da
dakaru,bayi,borori da kuyangi suna take musu
baya.Ba tare da bata wani lokaci ba sarki Zaldasi
ya
dubi sarakunan da sauran manyan baki cikin izza
da
jinkai tade da takama yace,kuyi hakuri na bata
muku
lokaci ban fito da wuri ba,hakan ya faru ne
sakamakon 'yata Gimbiya yau ta makaro bata
tashi
daga barci da wuri ba.Nasan
cewa kowa ya fito da shirin yin kwana uku a
bakin
dajin Sairul,to amma ina mai yi muku albishir da
cewa duk abinda kowa zaici yasha a cikin
wannan
daji na tsawon kwana ukun ni zan samar
dashi,koda
gama fadin hakan sai Sarki Zaldasi ya daga
hannu
yana mai bada inkiya a fara tafiya.Nan take kuwa
dakaru suka fara wucewa gaba sannan alkalan
gasa,jaruman gasa,sai muna yan kallo na jama'ar
gari da sauran baki.A wannan rana Gimbiya
Lasmin
tayi shigar kayane masu launin ruwan kwai,hatta
mayafinta,takalminta da abin adon gashinta duk
launin ruwan kwai ne,hakika shigar ta kara mata
kyau matuka,kuma hakanne yasa mazaje suka
sake
dimautacewa musamman jaruman gasa domin
nan
take suka aiyana a ransu daidai su rasa gimbiya
Lasmin gwara ma su rasa rayuwarsu a wannan
kasa.( Nikam bakin ciki ne ya
ishe da ban shiga wannan gasa ba).Koda
Gimbiya Lasmin taga kowa ita yake kallo amma
shi
jarumi Hibairu ko kallonta baiyi ba sai ta kamu da
tsananin mamaki,kuma hankalinta ya dugunzuma
domin wannane karo na farko data taba ganin
saurayin da bai dimauce ba sakamakon yin arba
da
ita.Abinda bata sani ba shine tsananin kunya da
kawaici ne yasa baya son ya rinka kallonta kuma
baya son sonta da begenta su ci gaba da
addabar
zuciyarsa kamar yadda sauran mazajen dake
wajen,domin ya lura da yadda samari da yawa
suke
neman zaucewa akanta.Saida aka shafe sa'a uku
da
rabi ana tafiya daga birnin Sarki Zaldasi sannan
aka
iso bakin farkon Dajin Sairul.Da isowa sai aka
yada
sansani aka shiga kafa tantuna,kowanne sarki da
jama'arsa suka kafa tantuna a wuri dabam haka
ma
sauran manyan baki da sauran baki.Nan take
akaga
bayi da kuyangin sarki Zaldasi sun fara dora
manyan
tukwane bisa murhu ana kunna wuta don cin
abinci.A sannan ne kuma wasunsu suka fara fito
da
yayan itatuwa iri iri tare da ruwan sha suna
rabawa
izuwa kowanne sansani,saida ya zamana cewa
ko
ina da ina abinci da abin sha ya yalwata babu
wanda ya taba jakar guzurinsa.Tunda Sarki
Zaldasi
da 'yarsa Gimbiya Lasmin suka shiga cikin tanti
basu fito ba har saida rana ta fadi,dajin yayi
sanyi a
lokacin da wata irin iska mai karfi ke
kadawa,sannan
aka busa algaita aka buga tambari.Koda jin haka
sai
kowa ya shiga shiri aka mimmike tsaye aka taho
izuwa sansanin sarki Zaldasi,ba tare da bata wani
lokaci ba sarki Zaldasi da gimbiya suka fito daga
cikin tanti suka tsaya,take Zaldasi yasa ka
kirawo
gaba dayan jaruman gasar suka taru a
gabansa.A
wannan lokaci ne Gimbiya Lasmin ta fara
kallonsu
daya bayan daya domin taga Jarumi Hibairu
amma
sai taga babu shi a cikinsu sai Jarumi Sa Maza
Gudu wanda shine kusan sa'ansa.Kuma tana
hada
idanu dashi taga ya kura mata idanu yana
murmushi,kawai sai ta daka masa harara ta
kauda
kai tana mai cigaba da kallon sauran jaruman
gasar
cikinalamun damuwa.Nan take Sa Maza Gudu
yaji wani irin kishi ya turnukeshi saboda ya gane
cewa ni
takeso ta gani,kuma rashin ganin nawa ne ya
daga
mata hankali ainun.Ba komai ne yasa na makara
ba
wajen amsa wannan kira ba na sarki Zaldasi face
tun
lokacin da aka sauka a bakin wannan daji
sa'adda
aka shiga tantuna sainaji na kagu dana shiga
cikin
dajin na Sairul ba don komai ba sai saboda a iya
yawan farautar danayi a can birninmu ban taba
ganin daji mai ban sha'awa ba kamar wannan na
Sairul saboda komai nasa dabam ne dana irin
sauran dazuzzuka.Dajin na dauke da manyan
bishiyoyi dogaye ababen sha'awa sannan akwai
manyan koramai da fadamomi,ga tsuntsaye da
sauran kananun dabbobi amma manya dabbobin
ma
tamkar babusu a cikin dajin.Babu wanda yasan
lokacin dana shiga cikin dajin Sairul batare danaji
an baiwa sauran jaruman gasa umarnin shiga
ba,saida na shafe sa'a tara da rabi ina tafiya
acikin
dajin ban hadu da dabbar data haura kare a
girma
ba face manyan macizai wadanda ta gabansu
nake
giftawa amma ko kallo ban isheshu ba.Sudai
wadannan macizai sun kasance manya manya
msu
faska faskan kawuna da kuma kwala kwalan
idanu
ababan tsoro,suna da matukar kwarjini daban
tsoro,koma jarumtakar mutum idan yayi arba
dasu
saiya firgita amma sai gashi cikin ikon Allah ina
wuce ta gabansu lafiya lau ko kyakyawan motsi
basuyi ba bare su kawo mini hari.Duk sa'adda
naji
yunwa ko kishirwa saina bude wata yar karamar
jakata ta guzuru wadda na rataya a kafadata na
dauko gasasshen nama ko ruwa,ko sau daya ban
yada zango ba.Tunda na shigo cikin jejin nake ta
karanta addu'o'i ina neman tsari a cikin
zuciyata,hakan ne ma yasa naji ko tsoro
banaji.Kwatsam ina cikin wannan tafiya sai naji
wani
irin gurnani mai tsananin ban tsoro ya cika dajin
gaba daya,ba wai gurnanin bane ya tsorata ni
face
rashin sanin daga inda ya fiot da kuma rashin
ganin
dabbar da tayishi.Gurnanin naji shine a gabas da
yamma,kudu da arewa da kuma sama da
kasa,hakan
na nufin cewa abin tsoro yana nan a ko ina kuma
akoda yaushe zai iya fitowa ta ko ina.Cikin sa'a
sai
naji bakina yaci gaba da kiran sunayen Allah ina
neman tsarinsa da taimakonsa,maimakon
nacigaba
da tafiya sai na tsaya cak a inda nake na dafa
kufen
takobina ina mai gyara tsayuwar,kawai jira nake
naga ta inda dabbar zata taso mini na tareta mu
fafata.Tsulum!sai naga wani narkeken zaki ya
baiyan
a gabana,tazarar dake tsakaninmu bata wuce
taku
ashirin ba,tunda nazo duniya bantaba ganin zaki
mai
girma,kwarjini da ban tsoro ba irinsa.Kallo daya
nayiwa zakin na tabbatar da cewa rikakke ne
kuma
tsohon gaske,Allah ne kadai zai iya cewa ga iya
adadin shekarunsa a duniya,kai da gani kasan
cewa
yawan dadewar zakin nada nasaba da karfin
sihirin tsafin dake jikinsa.Take na gane cewa
lallai
wannan zakin ne da ya gagari kowa kuma shi ake
so a kashe cikin wannan gasa ta farauta wadda
sarki Zaldasi ya shirya.Nanfa muka kurawa juna
idanu nida zakin aka rasa Wanda zai afkawa
wani tsakaminmu muka rinka yin kallon kallo,shin
shakkar juna mukeyi ko kuwa kowannenmu akwai
shirin da yakeyi.
Nima ganin wannan gawurtaccen Zaki yasa na
tsorata na tsaya anan.Mu hadu a part c.
SA MAZA GUDU
Littafi na Biyar (5)
Pat C
Ko kuwa kowannenmu akwai shirin da yakeyine?
Amsar dana kasa baiwa kaina kenan,kawai sai na
jiyo sautin bugun tambarin sarki gami da bushin
algaita daga can farkon dajin,kawai sai na jiyo da
baya na falfalo da azababben gudu ina mai
karanta
wata addua ta musamman ai kuwa sai gashi
inayin
wani irin gudu na ban al'ajabi tamkar gudun
kibiya
yayin da aka sakota daga cikin baka da
gawurtaccen
sadauki ya tabe.Nan danan cikin dakiku kadan
naga
na iso inda muka kafa sansani,cikin sauri na
kutsa
ta cikin mutane na isa can gaba inda jaruma
gasa
suke na shiga cikinsu na tsaya ina fama haki
zuciyata cike da zulumi da tunani,ba komai nake
tunani ba face waishin wannan zaki ya biyo ni
kuwa.Amma ai inda ya biyo ni koda bai cimmini
ba
ya kamata ace shima yanzu ya iso nan.A daidai
wannan lokaci ne sarki Zaldasi ya bude baki
yace,yaku jaruman wannan gasa kuyi sani cewa
yanzu ne zan baku umarnin shiga wannan daji
domin ku farauto zakin nan Nurul Maut wanda
duk
ya sami nasarar kashe shi daga cikinku yazo
dashi
nan gabana shine zakaran gasa,wanda zai zamo
mijin gimbiya kuma ya mulki rabin kasata ko ya
karbi dukiya mai tsananin yawan da bayansa ma
bazasuyi talauci ba.Zaku shiga cikin wannan daji
tare da jajurtattun alkalan gasa wadanda sune
zasu
bayar da tabbacin wanda ya lashe gasa bisa
gaskiya.Da wannan furuci nakeyi muku
bankwana,wanda duk ya rasa rayuwarsa a cikin
wannan daji zamu girmama gawarsa kuma mu
daraja kabarinsa yadda har abada baza' manta
dashi ba.Kuma da tsawon kwanaki uku na
farautar Nurul Maut a cikin wannan daji.Koda
gama fadin hakan sai
Sarki Zaldasi ya daga hannun take kuwa aka
busa
wani kaho irin na mafarauta,take gaba dayan
jaruman gasar suka juya da baya suka ruga
izuwa
cikin dajin Hairul.Koda wajen da jaruman ke
tsaitsaye ya zama wayan sai ya rage saura
mutum
daya jal a tsaya kuma ba wani bane ba face
Jarumai Hibairu,kawia sai ya dukar da kansa kas
cikin girmamawa ya gaida sarki Zaldasi da
gimbiya
Lasmin sannan ya dago kai ya dubi Lasmin yayi
mata wani irin kallo mai dauke da murmushi
kuma
ya daga mata hannu yana mai yi mata nuni da
cewa
lallai zai lashe wannan gasa.Kawai sai Hibairu ya
juya da baya ya falfala da masifaffen gudu,bisa
mamaki sai akaga nan da nan Hibairu ya riske
sauran yan'uwansa abokan gasar ya kutsa ta
tsakiyarsu har ya riski wadanda suke kan
gaba.Cikin
kaduwa Gimbiya Lasmin ta dubi Sarki Zaldasi
tace,yakai Abbana anya kuwa wanann matashin
saurayin mutum ne,dubi fa yadda yake yin wani
irin
gudu na ban al'ajabi har yana tserewa manyan
zaratan jarumai.Koda jin wannan tambaya sai
Sarki
Zaldasi ya bushe da dariya.Al'amarin daya baiwa
Lasmin mamaki kenan,daga can kuma sai taga
ya
tsuke bakinsa yayi shiru ga barin dariyar kuma ya
dubeta cikin nutsuwa yace,ai wannan karfin
gudunsa
ba komai bane ba,abin bukata kawai shine yazo
da
gawar zaki Nurul Maut.Wata kila da yawa daga
cikin
jaruman gasar sun fishi karfin gudu,kawai sunki
nuna wane saboda ai sai miya ta kare sannan
ake
sanin maci tuwo,me akayi yanzu wasa farin
girki.Kada ki manta cewa kwana uku za'ayi a
cikin
wannan daji ana farautar zakin,kinga ashe duk
jarumin daya baiyana dukkanin karfinsa da
dukkan
shirinsa a yanzu ya zama cikakken wawa,koda jin
wannan batu sai Lasmin ta gyada kai tace,kai
nidai
ina ganin cewa juma'ar da zatayi kyau tun daga
laraba ake ganeta,akwai alamun cewa wannan
yaro
zai iya tabuka abin kirki.Koda jin haka sai sarki
Zaldasi ya murtuke fuska ya dubi Lasmin a
fusace a
karon farko a rayuwarsa a gareta.Al'amarin daya
razanata kenan ainun,jikinta ya kama
kyarma.Sarki
Zaldasi yace,inda kinsan wanene Hibairu da kuma
hadarin da zamu shiga idan ya lashe wannan
gasa
da baki fadi haka ba,idan ma baki san dalilin da
yasa na kaiwa kasarsu takardar gaiyata ba izuwa
wannan gasa to yanzu ki sani cewa bisa binciken
da
nayi a hallarar tsafina na gano cewa nan gaba
mutanen kasar zasuyi karfi sosai har suzo su
mulki
wannan nahiya gaba daya,kuma su rushe
addininmu
da al'adarmu wadanda muka gada tun iyaye da
kakanni su shimfida tasu,hanya daya ce zamu bi
muga bayansu,ba wata hanya bace face mu
kama
sarkin mafarautansu da dukkanin zuri'arsa mu
kashe
su saboda ta tsatson sane za'a sami wanda zai
kawar da komai namu.Bisa binciken nawa sarkin
mafarautan nasu matarsa daya jal a duniya kuma
dan sama daya ne jal kuma ba wani bane dan
nasa
face wannan yaro Hibairu wanda suka turo ya
wakilci
kasartasu a wannan gasa.Burina shine Hibairu ya
mutu a cikin wannan gasa a cikin dajin
Hairul,kuma
tabbas nasan cewa mutuwar zaiyi tunda duk
duniyar
nan banga wanda zai iya kashe Zaki Nurul Maut
ba
kuma kin sani cewa duk wanda yayi arba dashi
sai
ya mutu.Ina mai tabbatar miki da cewa gaba
dayan
jaruman gasar nan har dama alkalan gasar da
suka
bisu mutuwa zasuyi.Koda Sarki Zaldasi yazo nan
a
zancensa sai hankalin Gimbiya Lasmin ya
DUGUNZUMA ainun,tausayin gaba dayan jama'ar
da
suka shiga dajin ya kamata nan take idanunta
suka
ciko da kwalla har hawaye ya zubo mata ta dubi
sarki Zaldasi cikin fishi tace,haba yakai Abbana
yanzu ashe saboda rai guda jal kakeson ka
hallakar
da wadansu dubban rayuwakan kuma shine kadai
dalilin da yasa ka shirya wannan gasa ashe
badon
ka samo mini mijin aure bane?Idan har wannan
saurayi Hibairu kakeso ka kashe me yasa ba
zaka
kashe shi ba shi kadai ka bar sauran jama'ar su
koma izuwa garuruwansu?Kada faka manta cewa
zaka raba iyaye da yayansu ne kuma zaka raba
mataye da mazajensu,ka mai dasu
gwagware,kuma
zaka zama BAKIN TAKOBI mai raba yan uwa da
masoya.Koda tazo nan a zancenta sai mahaifinta
ya
juyo a fusace ya dubeta,wannan dalili yasa tayi
shiru cikin shakku.
Nima ganin Sarki Zaldasi ya fusata,ni dake bayan
Gimbiya Lasmin yasa na firgiçe na tsaya
tsak.Wannan shine karshen Sa Maza Gudu 5
Mu hadu a Sa Maza Gudu littafi na shida(6) don
jin cigaban wannan kasaitaccen kayataccen
labari.
Insha Allahu anjima zamu cigabaAn dauko wannan littafi daga shafin www.dlhausanovels.com.ng ku ziyarci shafin na www.dlhausanovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya

Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,

Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan
Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490

A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,

Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu

Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC

Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from www.dlhausanovels.com.ng
You can download more hausa novels there
Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online
It is free we do not charge for uploading novel
Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services

Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us

Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it

Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT
An dauko wannan littafi daga shafin www.dlhausanovels.com.ng ku ziyarci shafin na www.dlhausanovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya

Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,

Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan
Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490

A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,

Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu

Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC

Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from www.dlhausanovels.com.ng
You can download more hausa novels there
Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online
It is free we do not charge for uploading novel
Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services

Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us

Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it

Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXTSA MAZA GUDU
Littafi na Shida (6)
Part A
KAFIN Lasmin ta gama rufe bakinta tuni Sarki
Zaldasi
ya tari numfashinta yana mai daka mata tsawa
yace,shin kin manta ne cewa tun kafin zamanin
ubana ma ba'a hulda da mutanen kasar su
Jarumi
Hibairu akan auratayya,iyayenmu da kakanninmu
sun hane mu da hakan kuna sun tabbatar mana
da
cewa mu zage dantse don gano hanyar da
zamuga
bayansu kafin suzo su shafe addininmu da
mulkinmu.Idan har na ce zan kashe wannan yaro
da
hannuna ko nasa wadansu su kashe shi to bazan
yi
nasara ba amma na gano cewa tabbas wancan
Zakin Nurul Maut zai iya kashe shiDa farko nayi
farin
ciki dana ga zuciyarki a kansa ne kadai ta
karkata
amma da na tuna illarsa a tare damu sai bakin
ciki
ya baibayeni naji na tsaneshi fiye da komai.Koda
gama fadin hakan sai sarki Zaldasi ya bushe da
dariyar mugunta har ya juya ya koma cikin tantin
bai
daina yin dariyar ba.Ita kuwa Gimbiya Lasmin sai
ta
bishi da kallo kawai cikin tsananin takaici a karo
na
farko taji ta tsaneshi duk da kasancewarsa
mahaifinta wanda ke nuna mata tsananin
kauna.Nan
taje Lasmin taji kamar ta ruga da gudu taje ta
gayawa jaruman gasar da sauran alkaln gasa da
yan
kallo duk sirrin da mahaifinta ya gaya mata
yanzu
domin su fasa shiga cikin dajin na Sairul domin
su
tsira da rayuwarsa.Kamar Sarki Zaldasi yasan
abindake cikin zuciyar Lasmin har yaje ya
kwanta a
cikin tantinsa da nufin yasa akirawo makada da
mawaka su debe masa kewa ta farin ciki bisa zai
cika burinsa daya gagari iyayensa da
kakaninsa,sai
ya fasa ya kirawo manyan dakarunsa yace
dasu,kuje
kusa a zuba ido sosai akan 'yata kada a kuskura
a
barta tabi bayan jama'ar da suka nufi cikin daji
nan
don kada ta baiyana sirrinmu ga
dayansu.Dakarun
suka risina suka an gama ya shugabanmu,nan
take
suka juya suka fice daga cikin tantin suka
rarrabu a
cikin sansanin don tabbatar da tsaro,ita kuwa
gimbiya Lasmin sai ta juya ta koma cikin nata
tantin
zuciyarta cike da tsananin bakin ciki gami da jin
kiyayyar mahaifinta saboda bataga hujjar da
zatasa
ya hallaka dubunnan daruruwan rayuka ba
saboda
rai guda daya jal.Baya ga haka kuma saitaji ta
kara
kamuwa da tsananin son Jarumi Hibairu fiye da
karon farkon ganinta ma dashi don haka sai ta
aiyana a cikin ranta cewa idan har wadannan
mutane
da suka shiga cikin dajin Sairul suka mutu kuma
ya
zamana cewa Jarumi Hibairu bai lashe wannan
gasa
ba itama kashe kanta zatayi,wannan alkawari ne
ta
daukarwa kanta a cikin zuciyarta.Koda gama
aiyana
hakan sai Lasmin ta kwanta akan shimfidarta
dake
cikin tantin a lokacin da kuyanginta suka
baibayeta
suka zazzauna suka zagayeta suna jiran kowane
irin
umarni amma sai sukaji tayi shiru.Jim kadan
kuma
sai sukaga Hawaye na zuba daga cikin
idanunta.Al'amarin dayayi matukar dugunzuma
hankalinsu kenan,shugabar kuyangin ta dubeta
tace,ya shugabata wanene ya bata miki rai haka
ki
gaya mana ko wanene muje mu gayawa sarki
yanzun nan yasa ayi masa KISAN GILLA.Koda jin
wannan batu sai Gimbiya Lasmin tayi ajiyar
zuciya
tace,idan na gaya muku abinda yasani zubar da
wannan hawaye nawa sai kun tsani komai da
kowa
hatta rayuwarku kuwa don haka kawai ku bar
wannan magana sirri karku sanar da kowa.Tana
gama fadin hakan sai ta lumshe idanunta tamkar
so
take tayi barci,amma a zahiri bata sone
kuyanginta
su cigaba da ganin zubar hawayenta.Wannan
shine
abinda ya faru a sansanin su Sarki
Zaldasi.Al'amarin
jaruman gasa,alkalan gasa da sauran yan kallo
kuwa
masu taurin rai da karfin zuciya,lokacin da muka
nausa cikin dajin Sairul muna ta tsala gudu baji
ba
gani saida aka shafe sa'a uku ana gudu ba tare
da
an tsaya ba,wadanda basu saba yin gudu ba
kuwa
suka fara sarewa suna faduwa saboda gajiya da
rashin sabo.Sudai jaruman gasar sunayin wannan
gudu ne saboda kowannensu burinsa shine ya
kasance shine jarumin farko da yayi arba da zaki
Nurul Maut domin ya sami nasarar kashe shi ya
dauko gawarsa.Tabbas inda wannan jaruma
gasar
sunsan yaya zaki Nurul Maut yake da basuyi
tunanin
yin arba dashi ba.Da tuni ma kowa ya hakura da
shiga wannan gasa,saboda ninasan abinda na
gani,ni kaina karfin imani ne yasa na cigaba da
gudu
a cikin dajin ina fuskantar inda zakin
yake.Lokacin
da muka shafe sa'a tara da rabi muna tayin gudu
zallah a cikin dajin sai kusan kasa biyu cikin
kaso
uku na jaruman gasar suka sare suka fadi kasa
saboda tsananin gajiya duk da cewa kuwa kowa
na
tafe tare da battar ruwansa yanasha

1 Comments On SA MAZA GUDU 1 to 9
avatar
adamu-3

1 year ago

Reply

Masha Allah Allah ya Kara basira Aboki

Please Login or Register in order to submit comment