Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

a duk
sa'adda
kishirwa ta kamashi,abinda na lura dashi shine
mu
kacal ne kacal bamu sha ruwa ba kuma bamu ci
abinci ba tunda aka fara gudun.Su kansu sauran
manyan jaruman gasar ma wadanda suka
kasance
jajirtattu kuma zakwakurai sunyi matukar
mamakin
yadda akayi ni da Sa Maza Gudu muka jure
wannan
gudu na tsawon sa'a tara da rabi ba tare da mun
tsaya mun huta ba ko munci abinci ko shan ruwa
alhalin suma da yawansu saida suka rinka
tsayawar.Lokacin da muka iso daidai wurin nan
inda
nayi arba da zaki Nurul Maut sai nayi turjiya na
tsaya cak,dama nine kan gaba sai Sa Maza Gudu
na
biye dani da tazarar kamu uku kacal sai kuma
sauran jaruman gasar wadanda adadinsu bai
wuce
mutum saba'in ba,alhalin da farko mun kai mu
dubu
goma sha da yan daruruwa,a can bayanmu kadan
kuwa alkakan gasa ne su dari biyu bisa
dawakai.Gaba dayan wadanann alkalan gasa
basu
gaji ba saboda kasancewarsu akan dawakai
suke,kuma kowannensu bai fuskanci matsalar
yunwa
da kishi ba,amma dawakansu a jigace suke kuma
sa'ar da sukayi a daidai inda aka tsaya din akwai
wata katuwar korama don haka sai suka kama
shan
ruwan a cikinta.Har Sa Maza gudu ya giftani zai
ci
gaba da gudu zuwa gaba saiya fasa ya dawo da
baya ya dubeni cikin nutsuwa yace,naji ance
kuma
ma'abota addinin musulunci bakwa yin karya
kuma
kuna da rike amana gami da cika alkawari
saboda
haka inason ka gaya min gaskiya,menene dalilin
da
yasa kayi turjiya anan ka tsaya?Koda jin wannan
tambaya sai nayi dan guntun murmushi a gareshi
nace,zakin da muke nema mu kashe yanan
adaidai
nan wurin dana tsaya kuma a koyaushe zai iya
baiyana a garemu.Koda jin wannan batu sai kowa
ya
zare takobinsa,masu mashi suka rike da
kyau,masu
baka suka dana kibiyoyi aka kama kalle kalle na
sama da kasa,gabas da yamma,kudu da arewa
domin a gata ta inda zaki Nurul Maut zai fito a
afka
masa.Tsawon yan dakiku banji wannan gurnani
ba
wanda naji a dazu a farkon shigota
dajin,al'amarin
dayayi matukar bani mamaki kenan.Shi kuwa Sa
Maza Gudu saiya dubeni a fusace ya daka mini
tsawa yace,ta tabbata gaskiya cewa ku
makaryata ne
kuma mayaudara,ina zakin yake?kace damu anan
yake,kafin Sa Maza Gudu ya gama rufe bakinsa
sai
mukaji wannan gurnani danaji nan take da yawa
daga cikin jaruman gasar suka firgice suka zube
a
kasa tamkar an zare musu dukkanin karfin
jikinsu,wasu kuwa saboda tsananin razana da
sukayi
kamewa sukayi a tsaye kamar gumaka.Wasu
kuwa
basu san sa'adda suka fara sakin fitsari ba a
wando
alhalin suna kiran kansu JARUMAI.Kalilan ne
daga
cikin jaruman suka iya zare makamansu na yaki
suna kalle kalle da dube dube don ganin ta inda
zakin zai bullo saboda kowa jikinsa ya bashi
cewa
lallai wannan gurnani bana komai bane face na
ZAKI
NURUL MAUT.Tsawon yan dakiku zaki bai
bayyana
ba,kuma ba'a sake jin gurnaninsa ba.Kwatsam
sai
akaji wadansu jaruman gasa kimanin su ashirin
sun
kwarara uban ihu.A firgice su Hibairu suka waiga
suka dubesu,kawai sai sukaga ashe wani irin
mugun
haske ne ya faso gadon bayansu ya burma
cikinsu
saiga hanjin cikinsu na zubowa kasa.Dukkaninsu
suka kife kasa matattu.Koda ganin wannan
al'amari
sai ragowar jaruman gasa da alkalan gasa dake
can
bayansu kadan suka firgita suka kama ihu da
guje
guje kowannensu ya rasa ma inda zai shiga ya
buya
saboda kidimewa har karo sukeyi da juna suna
faduwa wasu kuma suka rinka karo da
bishiyoyi,duwatsu,suna samun mugayen raunika
wanda suka rinka zama sanadin ajalinsu.Wasu
kuwa
cikin ramuka suka rinka shigewa duk da cewa ma
basu san ma menene a cikin ramin ba.Hakika
idan
masifa takai masifa hankali gushewa yake kuma
indai mutum yaga ajalinsa tofa zai iyayin komai
danganin ya tsere masa.Wasu daga cikin jama'ar
da
suka shigo cikin wannan daji sai gasu suna
falfala
mugun gudun da basu tabayin kamarsa ba a
rayuwarsu tamkar zasu tashi sama.kash duk
wannan
kokari da mutane suka rinkayi domin su tsira da
rayuwarsu duk sai ya zamo na banza saboda
saidai
kawai kaga haske ya burma ciki da kirjin mutum
ya
fadi kasa a sa'adda yake falfala gudu,ko kuma
kaga
an zaro mutum daga cikin ramin daya buya
komai
zurfin ramin an kwakule komai na cikinsa anyi
jifa
da gawarsa babu kyan gani.Nanfa zaki Nurul
Maut
ya cigaba dayin mummunar barna yayi ta kashe
jama'ar da suke shigo cikin wannan daji suna
zubewa kasa mattatu tamkar ana sassabe a
gona.Duk wannan bau dake faruwa Jarumi
Hibairu
da Sa Maza Gudu na tsaye a waje daya kyam
suna
kallon duk abinda yake faruwa.Sudai basuyi
yunkurin
guduwa ba kuma basu zare takubbansu ba domin
su yaki zaki Nurul Maut.Ko Jarumi Hibairu yaga
zakin yana ta kashe dubunnan daruruwan mutane
sai ya kamu da tsananin tausayi har idanunsa
suka
ciko da kwalla ya fara zubar da hawaye,shi
kansa
yasan cewa Allah ne kawai ya kubutar dashi
daga
sharrin wannan zakin sakamakon addu'o'in da
yake
ta karantawa a ransa.Koda ya kura da Jarumi
Alkas
wato Sa Maza Gudu sai yaga shi kuma ashe
wadansu kalmomin tsafi yake ta karantawa a fili
ma
har yana iya jiyo sautin kalmomin kuma duk da
haka
a tsorace yake domin kafafunsa na karkarwa.Duk
sa'adda zakin ya yunkura kamar zai afkawa Sa
Maza
Gudu sai ya fasa ya sake afkawa sauran jama'a
kuma ko kadan ma baya kusantar inda Jarumi
Hibairu ke tsaye domin da zarar ya doshe shi sai
yaji kamar jikinsa zai narke saboda wani
azababben
hucin zafi da yake fesowa.Lokacin da zaki Nurul
Maut yacigaba da kashe jama'a ya zamana cewa
ya
kashe kusan kaso daya da rabi daga cikin kaso
shida na jama'ar da suka shigo cikin dajin sai
hankalin Jarumi Hibairu ya dugunzuma ainun
kuma
ransa ya baci zuciyarsa ta kama tafarfasa bai
san
sa'adda ya yunkura ba cikin zafin nama ya kwala
kabbar da karfi a fili.Faruwar hakan keda wuya
zaki
Nurul Maut ya fadi kasa,amma saiya mike da
sauri
ya tsaya cak a inda yake ya kuma ya rikide ya
zama
haske kuma ya kuwa Hibairu idanu yana wani irin
gurnani mai ban tsoro fiye da wanda yakeyi.shi
kuwa sa maza gudu sai ya noke ya zubawa
Jarumi
Hibairu idanu yaga abinda zai faruwa.A cikin
zuciyarsa yana cewa ya samu tsuntsu daga sama
gasasshe,kawai zai jira Hibairu ya kashe zakin
sannan shima ya kashe shi ya dauki gawar zakin
yaje ya kaiwa sarki Zaldasi kuma ya cinye
gasa.Haka
akayi kallon kalo tsakanin Zaki Nurul Maut da
Jarumi Hibairu tsawon yan dakiku sai
kowannensu
ya rugo da gudu izuwa kan juna cikin mugun
nufi.koda ya rage saura baifi taku biyar ba su
hadu
duk su biyun suka daka tsalle sama tamkar an
harbo su daga cikin baka.Shidai Zakin wangame
bakinsa yayi da nufin ya danki wuyan Hibairu ya
luma masa hakoransa akai,shi kuma Hibairu
takobinsa ya daga sama yakai masa wawar suka
a
ciki.Wani ikon na Allah suna haduwa a saman sai
ya
zamana cewa babu wanda ya sami nasarar
aiwatar
da abinda yayi nufi,domin lokacin da zakin ya
kawowa Hibairu cizo da hakoransa a wuya sai ya
goce cikin zafin nama,zakin ya kadeta
tayi tsalle can gefe daya ta fadi suka rukunkume
juna a saman suka fado kasa tim kuma suka
kacame da kokowa wannan ya danne wannan
wancan ya juye da wannan,sukayi ta birgima a
kasa
kowannensu na kokarin kashe dan'uwansa.Koda
Sa
Maza Gudu yaga irin gagarumar jarumtakar da
Hibairu keyi sai hankalinsa ya dugunzuma ainun
domin ya fuskanci cewar tabbas zai iya kashe
wannan zaki,bisa sa'a kwatsam kuma sai yji
motsin
sawun dawakai a bayansu a firgice ya waigo sai
yaga ashe wadannan alkalan gasa ne guda biyu
masu shegen naci da taurin rai tsaye a
bayansu,su
biyu rak suka rage a wajen basu gudu ba alhalin
dasu da dawakan nasu duk manyan raunika ne a
jikinsu,jini na zuba amma sun zuba ido suga
yadda
Hibairu zai kash wannan zakin domin suje sukai
labari.Nanfa hankalin Sa Maza Gudu ya
dugunzuma
ainun ya rasa abinda ya kamata yayi,shidai a
rayuwarsa baya cin zarafin wanda bai takaleshi
ba,don haka baya son ya kashe wadannan
alkalan
gasa amma kuma yanzu idan ya barsu da rai ya
kasance Hibairu ne ya kashe wannan zaki a
gaban
idanunsu zasuje sukai labari.Koda gama aiyna
hakan
a cikin zuciyarsa sai ya zare takobinsa ya daka
tsalle sama ya kaiwa zakin wawan sara a gadon
baya,maimakon takobin ta tsarge zakin gida biyu
sai
ta karye ta rabe biyu,wata irin karace tashi
tamkar
karfe da karfe ne suka hadu.A fusace zakin ya
juyo
ya mangare Sa Maza Gudu da hannu daya yayi
tsalle
sama can da bya ya fado kasa yana man jini
domin
kirjinsa zakin ya nausa da mugun karfi,nan fa sa
maza gudu yaji kamar kirjin nasa fadowa kasa
zaiyi
saboda mugun radadi da zogin da yakeji.Don
haka
sai ya kasa mikewa tsaye bare yaje yacigaba da
taimakon Hibairu wajen yakar zakin.Haka dai
Hibairu
da zaki Nurul Maut suka cigaba da yin bakin
gumurzu a kasa ya zamana cewa zakin yana
samin
nasarar kartar sassan jikin Hibairu da faratan
hannunsa yanayi masa raunkia a jiki,shi kuma ya
rinka samin nasarar gabzawa zakin mugayen
naushi
harma yayi sa'ar fasa kwayar ido guda ya tsiyaye
nan take.Saidai suka shafe sa'a guda suna
wannan
fafatawa ya zamana cewa karfi ya kusan zuwa
daya
domin kowannensu ya jigata ainu,har takai cewa
da
kyar suke motsawa.A na cikin hakanne Hibairu
ya
fahimci cewa indai suka cigaba da wannan
gumurzu
a haka to tabbas zasu iyayin RAGAS,saboda jiri
ya
fara dibarsa sakamakon jinin dake zuba a
kansa.Koda gama aiyana hakan kuwa sai ya
shiga
yiwaAllah kirari a fili yana mai cewa Ya ubangijin
Musulinci ka karfafeni da karfinka ka bani sa'a da
nasara akan wannan zaki.Koda wadannan alkalan
gasa guda biyu da suka rage sukaji Hibairu na
ambaton ubangijin musulunci sai suka cika da
tsananin mamaki kuma hankalinsu ya dugunzuma
ainun.Ba komai ne ya basu mamaki ba face sun
gane cewa ashe duk wadannan gagarumin karfi
da
Hibairu yake amfani dashi akan sihirtaccen zakin
nurul maut ba karfinsaa bane na sihiri,karfin ne
daga
abin bautarsa ubangijin musulunci.Abind
a ya
dugunzuma hankalinsu kuwa shine da wane bakin
zasuje su gawaya sarki Zaldasi cewa da karfin
ubangijin musulunci Hibairu ya sami nasarar
kashe
wannan zaki alhalin sarki zaldasi ya tsani
musulunci
da musulmai kamar yadda ya tsani mutuwarsa
kai
ko labari ya samu cewa ma'abota addinin
musulunci
zasu gifta ta gefan birninsa turawa yake a kashe
mazajensu a kamo matansu a matsayin
bayi,dukiyarsu kuwa ta zama ganinma.Kwatsam
ba
zato ba tsammani sai Alkalan gasar biyu da sa
maza gudu sukaga Hibairu ya suri kafafun zakin
na
baya ya kama hajijiya dashi a sama,take sa maza
gudu ya gano cewa hibairu so yake ya fyada
zakin
akan wani katon dutse dake daf dashi,idan kuwa
ya
sani nasarar yin hakan take kan zakin zai
dagargaje
ya mutu,cikin hanzari ya mike tsaye zumbur ya
ruga
izuwa inda takobinsa take ya sureta ya sake
rugowa
izuwa inda Hibairu ke gumurzu da zakin.Adaidai
wannan lokaci ne Hibairu ya maka kan zakin
akan
wannan katon dutsen kuma a sannan ne sa maza
gudu ya dankawara zakin sara a gadon bayansa
ya
tsargeshi biyu,sai gashi kan zakin ya dagargaje
kuma gangar jikinsa ta rabe biyu.Nan fa gardama
ta
sarke a tsakanin Hibairu da sa maza gudu
kowannensu na cewa shine ya kashe
zakin.Adaidai
wannan lokaci ne wadannan alkalan gasa suka
yunkuro da dawakansu suka karaso daf dasu
Hibairu
suka sauko daga kan dawakansu suka shiga
kokarin
tsayar da jinin dake zuba a jikinsu domin su ceto
rayuwarsu sakamakon mugayen raunikan dake
jikinsu.Dawakan na suma sarewa sukayi suka
fadi
kasa suna kakarin mutuwa saboda duk jikinsu a
cike
yake da rauninkan da reshinan bishiyoyi sukayi
musu a lokacin da dajin ya hargitse kowa na
gudun
ceton ransa.Har izuwa wannan lokaci jarumi
hibairu
layi yake yi domin jiri bai daina dibarsa ba
saboda
jinin dake zuba.Koda sa maza gudu ya dubi
hibairu
da wadannan alkalan gasa yaga halin da suke
ciki,ya
tabbatar da cewa shine kadai mai cikakkiyar
lafiyar
dazai iya komawa can bakin dajin dauke da
gawar
wannan zaki indasu sarki zaldasi suke kafa
sansani,sai ya bushe da dariyar farinciki ya dubi
alkakan gasa yace,yanzu zan dauki gawar
wannan
zaki na tafi tare daku gaban sarki ku shaida
masa
cewa nine na lashe wannan gasa.Koda jin
wannan
batu sai alkalan gasar suka zazzaro idanun kuma
suka dubi jarumi sa maza gudu cikin alamun
rashin
gamsuwa,daya daga cikinsu yace,yaza'ayi kace
kaine
ka kashe wannan zaki alhalin kafin kaifin
takobinka
ya dira a kan gadon bayan zakin tuni Hibairu ya
maka kansa akan dutse ya dagargaje kaga kenan
shine ya kashe zaki bakai ba,kuma dole ne muje
mu
bayar da shaidar hakan.Kafin wannan alkalin
gasa ya
gama rufe bakinsa tuni sa maza gudu ya tari
numfashinsa yana mai daka masa tsawa ya
ce ashe kuwa daku da hibairu duk zaku mutu
anan ni kadai ne
zan koma sansani a raye dauke da gawar nurul
maut.Koda gama fadin hakan sai sa maza gudu
ya
ruga da gudu izuwa kan wadannan alkalan gasa
ya
daka tsalle izuwa samansu yakai musu wawan
sara
da takobinsa da nufin ya fille musu kai kawai sai
yaji
an doki kirjinsa da wani irin wawan mugu.Saboda
karfin dukan saida yayi sama da baya ya fado
kasa
tim a cikin galabaita yana dafe da kirjin nasa
sakamakon mugun zafi da radadi dayaji.Yana
dago
kansa yaga ashe jarumi hibairu ne yayi masa
wannan wawan bugu kuma yana tsaye a kansa
rike
da takobi tamkar jiri baya dibarsa alhalin har a
sannan jiki bai daina diga ba daga cikin raunikan
sassan jikinsa.Jarumi Hibairu ya dubi sa maza
gudu
a fusace yace,rai da ajali duk a hannun ubangijin
musulunci suke don haka kai baka isa ka kashe
mu
ba face da yardar ubangijina,ina mai tabbatar
maka
da cewa indai ina numfashi a doron kasa baka
isa
ka kwace gawar wannan zaki ba bare har ka cika
burinka na lashe wannan gasa saidai dayanmu ya
rasa rayuwarsa a nan ko kuma muyi ragas.Koda
jin
wannan batu sai jikin sa maza gudu yayi sanyi
saboda ya fuskanci cewar lallai abinda hibairu ya
fada zai iya faruwa hakan.cikin kankantar da kai
kuma cikin karamar murya sai sa maza gudu
yace,yakai abokina kayi sani cewa nasan
abindake
cikin ranka kuma nasan babban dalilin da yasa
ka
shiga wannan gasa.Ka shigeta ne bawai don ka
mallaki gimbiya Lasmin ba ko don ka mallaki
dukiya
ko mulki ba,sai domin kawai ka sami damar yada
addininku na musulunci,abinda daya gagareku
kenan
tun iyaye da kakanni tsawon shekara da
shekaru,ni
kuwa bani da burin da yafi na mallaki gimbiya
Lasmin saboda tun ban fi shekara shida ba a
duniya
na kamu da tsananin sonta kuma nake fama da
begenta dare da rana,bani da wata dama ta
mallakarta face wannan,ina mai rokonka daka
taimaka mini ka barni na zama zakaran wannan
gasa don cika burina ni kuma nayi maka
alkawarin
cewa da zarar na auri gimbiya Lasmin zan karbi
addininka kuma na jaddashi a nan birnin.koda
kuwa
yin hakan zai janyo na yaki sirikina sarki zaldasi
tare da taimakonka.Lokacin da jarumi sa maza
gudu
yazo nan a zancensa sai jarumi hibairu yaji
kamar
ya daure shi da jijoyoyin wuyan jikinsa,don haka
sai
yayi shiru yana tunani da nazari har izuwa
tsawon
yan dakiku daga can sai ya dago kai ya dubi sa
maza gudu yace,babu yanda za'ayi na baka
yardata
da amincina saboda zaka iya yaudarata ka zamo
mara alkawari,ka sani cewa kamar uadda kake
tsananin son gimbiya Lasmin to nima yanzu na
kamu da tsananin sonta har takai cewa dare da
rana
ina ganinta a cikin barcina da zahiri tamkar
tanayi
min fatalwa.idan bazaka iya rungumar kaddara ba
ka yarda dacewa nine na lashe wannan gasa to
kayi
duk abinda zakayi wanda kake ganin cewa shine
zai
fissheka.Sa'adda Jarumi Hibairu yazo nan a
zancensa sai sa maza gudu ya gyara tsayuwarsa
kuma ya murtuke fuskarsa ya fuskanci hibairu
yace,ai kuwa saidai mu mutu anan nida kai kowa
ya
rasa.Koda gama fadin hakan sai sa maza gudu
ya
gyara tsayuwarsa ya daga takobinsa da
hannayensa
biyu ya riketa da kyau,awannan lokaci hibairu
maye
yake yana layi daga tsaye kamar zai bingire
kasa,amma sai yacigaba da kiran sunayen Allah
yana mai neman taimakonsa,aikuwa nan take
yaji
wani sabon gagarumin karfi ya shige shi.A lokaci
guda duk su biyun suka ja da bya taku uku uku
suna yiwa junansu wani irin kallo na kar ta
sankar
kuma kowannensu na lura da irin motsin da
dan'uwansa zaiyi.Kawai sai suka rugo da gudu
suka
ruguntsume da masifaffen yaki mai tsananin ban
tsoro da ban al'ajabi.Hakika duk sa'adda zarto ya
hadu da gwarzo dole ne ayi bakin artabun da zai
firgita komai da kowa dake wajen domin ana fara
wannan gumurzu ne bishiyoyi da koramai dake
cikin
wannan daji suka san cewa babbar masifa tazo
don
sa'adda zaki nurul maut ya baiyana ba'a hargitse
haka ba,saidai kawai kaga bishiya komai
tsawonta ta
karye ta fadi,ruwan koramai da fadamomi kuwa
ya
rinka fantsama a lokacin da wata irin iska mai
karfin
gaske ta addabi duk wani abu mai rai dake
wajen.Duk sa'adda takubban jaruman biyu suka
hadu kuwa saidai kaga tarwatsin wuta na tashi
gami
da tsawa,ba komai ne ya haddasa hakan ba face
sihirin tsafin da sa maza gudu ke amfani dashi
don
ganin ya hallaka jarumi hibairu,shi kuma Allah na
bashi kariya sakamakon adduar da yake
tayi.Saida
suka shafe sa'a biyi da yan dakiku masu yawa
suna
wannan mugun yaki ba tare da dayansu ya sami
nasarar komai ba,har ya zamana cewa sun gaki
likis
da kyar ma suke iya daga takubban nasu suka
kacame da kokawa su fadi can su mirgina nan
duk
inda sukayi wadannan alkalan gasa na biye dasu
a
firgice duk da cewa suma a galabaice suke
ainun,kawai fatansu shine hibairu ya sami
nasarar
kashe sa maza gudu domin suma su tsira da
rayuwarsu.Haka dai Hibairu da sa maza gudu
suka
cigaba da fafatawa har suka sake mikewa tsaye
suka
rinka gabzawa junansu naushi da bugu da hannu
da
kafa duk wanda aka yiwa mugun naushi a fuska
saidai kaga yana furzar da ruwan jini.Nanda nan
fuskokinsu da idanunsu suka kumbura tun suna
tsaye saida suka durkushe kasa bisa guiwoyinsu
suka cigaba da gabzar juna har saida takai cewa
sun
baje kasa sumammu.Jim kadan da faruwar hakan
sai duk su biyun suka fardado a lokaci guda cikin
shammace da matukar zafin nama,sa maza gudu
ya
zaro wata siririyar wuka daga cikin rigarsa ya
kawai
hibairu suka a ciki,hibairu ya yunkura domin ya
kaucewa sukar amma sai da wukar ta nutse a
cinyarsa,hibairu ya kurma uban ihu sakamakon
bakin zafin da yaji,amma sai yayi ta maza yayi
wuf
ya zare wukar jini yayi tsartuwa daga cikin cinyar
tasa,shi ma ya lumawa sa maza gudu wukar a
tasa
cinyar ta dama har saida ta bullo ta bayan
cinyar.Sa
maza gudu ya rusa uban ihu a lokacin da duk su
biyu suka zube kasa a matukar galabaice suka
kasa
ci gaba da yakar juna.Kowannensu ya kasa
mikewa
tsaye sakamakon jini dake zuba a jikin cinyoyinsu
mai yawa.A guje wadannan alkalan gasa suka
rugo
izuwa kan jarumi hibairu suka taimaka masa suka
daure raunin dake kan cinyar tasa suka tsaida jini
suka tashe shi tsaye,sannan suka zare
takubbansu
suka nufi kan sa maza gudu da nufin su kashe
shi,amma sai hibairu ya daka musu tsawa.Cikin
matukar takaici suka sauke takubbansu kas,suka
jiyo
suka dubi hibairu sukace saboda me ka hanamu
kashe makiyinmu alhalin yayi furucin kashe mu a
gabanka?Hibairu yace ai bana son ku kashe shi
da
hannunku saboda kasancewarsa babban
jarumi,lallai
bai kamata manyan mazaje suyi mutuwar banza
ba
a hannun wadanda basu da karfin iya kashe
su,ku
kyaleshi ya mutu sakamakon jinin dake zuba a
jikinsa mai yawa,tunda babu mai taimakonsa
anan
dajin,idan ya mutu a nan yayi irin mutuwar da
sauran jaruman gasa sukayi kunga kenan za'a
tabbatar da cewar jarumatakarsa bata kai tawa
ba,kuma lallai ya kasa fafatawa da zaki nurul
maut,ta
tabbata kenan nine makashin nurul maut bashi
ba.Koda gama fadin hakan sai jarumi hibairu ya
dingisa kafarsa da kyar yaje ya dauko rabi gangar
jikin zaki Nurul Maut mai hade da dagargajajjen
kansa ya rataya a gadon bayansa suma alkalan
gasar sai suka taimaka masa suka dora
hannayensa
akan kafadunsu suka juya suka nufi hanyar
dazata
kaisu can inda sansanin sarki zaldasi yake suka
bar
jarumi sa maza gudu kwance a kas yana aman
jini
yana mutsu mutsu tamkar ruhinsa na daf da
makoshinsa.Haka dai jarumi hibairu dalkakan
gasa
suka cigaba da tafiya da kyar cikin matukar
karfin
hali,wani lokacin har yanke jiki sukeyi suna
faduwa
kasa saboda galabaita,kishirwa da yunwa,amma
saboda naci da matukar juriya saikaga sun sake
mikewa sunci gaba da tafiya.A haka dai suka
samu
suka fara hango sansanin su sarki zaldasi daga
nesa
kadan.Al'amarin dayayi matukar jefasu cikin
matukar
farinciki kenan suka kara sauri domin su isa can
din,nan fa suka fara bude bakunan su suka kwala
kira domin a kawo musu agajin gaggawa,amma
saboda bakinsu ya bushe kuma muryoyinsu sun
dashe babu wanda ya jiyosu.Ana cikin wannan
hali
ne kwatsam jarumi Hibairu yaji wadannan alkalan
gasa biyu sun kife kasa da rub da ciki a
gabansa,kawai sai ganin kibiyoyi yayi a gadon
bayansu.A firgice ya waigo bayansa yayi arba da
wanda ya harbosu su ba wani bane ba
face....rike
da KWARI DA BAKA.
Anan zan dakata,anyi fiye da rabin littafi na
shida,sai
mu tara a part B.

Littafi na Shida (6)
Part B
Ba wani bane face Jarumi Sa Maza Gudu rike da
wata KWARI DA BAKA yana dingisa kafarsa da
kyar
kuma ga rabin gawar zaki nurul maut rataye a
kafadarsa fuskarsa cike da annuri sa murmushin
mugunta yake yiwa Hibairu.Tsananin mamaki ne
yasa Hibairu ya kasa yin wani yunkurin komai har
ya
iso daf dashi domin bai taba zaton cewa zai sake
ganin jarumi Sa Maza Gudu ba a raye sakamakon
halin daya baro shi a can dajin Sairul.Sa Maza
Gudu ya cigaba da dingisa kafarsa da kyar har ya
iso daf da jarumi Hibairu ya dubeshi yace,kana
dauke da
rabin zaki nurul maut,nima haka kuma ga alkalan
gasar da zasu bayar da shaidar zakara a cikinmu
kwance a kasa matattu.Ta yaya za'a gane
wanda
shine ya kashe zakin bisa gaskiya.?Kamar yadda
kace dani in dai kana raye a doron kasa burina
bazai
taba cika ba,to kaima naka bazai cika ba muddin
ina
raye,bakar wahalar zubar da jini basu ne mutuwa
ba,rai baya gushewa face wa'adinsa ya cika
kamar
yadda kukayi imani da addininku.Koda gama
fadin
hakan sai jarumi sa maza gudu ya wuce gaba
yana
mai cewa zomu karasa sansanin inyaso muga
wanda
za'a baiwa kambun wannan gasa tsananin nida
kai.Zamu ga wanda zai zamo mijin gimbiya
Lasmin.Nan take jarumi Hibairu yabi sa maza
gudu suka jera tare suka durfafi sansanin.Daga
nesa
kadan suka hango su sarki Zaldasi tare da
tsirarun dakarun da suka je dajin Sairul suka tsira
da
rayuwakansu da kyar amma gaba daya yan kallon
da sukaje da alkalan gasa dayansu bai dawo ba a
raye.Koda su sarki Zaldasi suka hango Jarumai
biyu
kacal sun dawo daga cikin dajin Sairul kuma
kowannensu na dauke da rabin gangar jikin zaki
nurul maut,sai suka cika da tsananin
al'ajabi.Nanfa
mutane suka rude da shewa gami da tafi da
jinjina,duk wanda ya dubi Hibairu da sa maza
gudu
yaga irin mugayen raunikan dake jikinsu sai ya
kamu
da matukar tausayinsu,kuma ya jinjina musu
ainun.Ita kuwa gimbiya Lasmin koda ta hango
jarumi Hibairu a raye ya durfafo sansanin goye da
kan zaki nurul maut a kan kafadarsa sai ta kamu
da
tsananin farin ciki mara misaltuwa,bata san
sa'adda
ta yunkura ba da nufin ta ruga da gudu ta
rungume Hibairu,amma sai sarki Zaldasi yayi wuf
ya riko
hannunta ya dubeta a fusace yana mai yi mata
rada
a kunne,yace,baki da hankali ne ko kuwa kin
makance ne bakya gani,to ba Hibairu bane kadai
ya
dawo cikin nasara ba dubi can bayansa ga jarumi
Alkas can tafe goye da wani bangaren na zakin
nurul maut.Dole sai mun bincike mun gano
ainihin
wanda shine ya kashe zakin bisa gaskiya sannan
mu
bashi aurenki.Kafin sarki Zaldasi ya gama rufe
bakinsa sai aka hango Jarumi Hibairu da Jarumi
Sa Maza Gudu sun yanke jiki sun fadi kasa
sumammu,nan take sarki Zaldasi ya bayar da
umarni aka ruga aka dauko su a ka shigar dasu
cikin tanti,likitoci suka dukufa a kansa.Al'amarin
sarki zaldasi kuwa cikin rudewa ya hada taro na
gaggawa ya hada gaba dayan manyan sarakuna
da
manyan bakin da suka halacci wannan gasa da
kuma dukkanin attajiran gasa suka taru a tsakiyar
sansanin suka zazzauna domin a tattauna akan
wannan al'amari.Sarki Zaldasi ya mike tsaye
fuskarsa a murtuke,kana kallonsa kasan cewa
ransa
a bace yake,ba komai ne ya bata masa rai ba
face
ganin abinda yake son ya faru bai baru ba,shi a
tunaninsa dole ne su jarumi Hibairu su mutu a
cikin
dajin sairul a hannun zaki nurul maut,amma sai
gashi sun dawo a raye,kuma gaba dayan
jama'arsa
daya tura dajin da jaruman gasa duk sun mutu
kalilan ne suka dawo.Tuni Sarki Zaldasi ya
aiyana a
ransa cewa zai aurar da Gimbiya Lasmin ne ga
dan
kaninsa Yarima Zaiyan,farin cikinsa guda daya ne
jal
an kashe zaki nurul maut,zakin daya gagare shi
kashewa tsawon shekara da shekaru.Gaba daya
sansain sai yayi tsit tamkar babu mutum daya
mai
numfashi wajen ana sauraron aji bayanin
dazaiyi.Sarki Zaldasi yayi gyaran murya sannan
yace,yaku jama'a kun gani da idanunku cewa a
gaba
dayan jaruman da suka tafi wannan gasa mutum
biyu ne kacal suka dawo a raye kuma dukkaninsu
suna dauke da rabin gangar jikin zaki nurul
maut.Alkalan gasa kuwa ko mutum daya jal bai
dawo ba a raye,a kallah mutum dubu dari shida
da
sittin da uku ne suka rasa rayuwarsu a cikin
wannan
daji na Sairul,yanzu tunda dai an kashe zaki Nurul
Maut zan aika da dakaru su debo gawarwakin
jama'a
domin azo ayi musu jana'iza.Dangane da bayar
da
kambun gasa kuwa dolene mu jira wadannan
jarumai guda biyu sun sami lafiya kuma
hankalinsu
ya dawo jikinsu,sannan dole ne muyi bincike na
gaskiya domin mu tabbatar da wanda ya kashe
zakin bisa gaskiya tsakanin jarumi hibairu da
jarumi alkas.Da wannan furuci nake baiwa kowa
umarnin
yayi shirin barin bakin wannan daji domin tafiya
izuwa cikin birninmu mai albarka,sakamakon
wannan
gasa kuwa sai nan da cikar kwanaki uku za'a
bayyana shi.Koda gama fadin hakan sai jama'a
suka
rude da shewa,wasu kuwa da yawa a wannan
lokaci
yan gari da baki kuka sukeyi da bakin ciki
sakamakon yan uwansu da suka rasa a cikin
dajin
sairul.Duk wannan bayani da sarki zaldasi yayi ni
da sa maza gudu muna jiyo su daga can cikin
tantin da aka kwantar damu sa'adda likitoci keta
kokarin ceto
rayuwarmu.Koda naji wannan bayani na sarki
Zaldasi sai hankalina ya dugunzuma ainun
saboda
na fusakanci cewar akwai yiyuwar a rushe
dukkan
shirina da burina.Abu na farko dai akwai alamun
cewa babu tabbacin za'a bani zakaran wannan
gasa,tunda babu cikakkiyar shaidar da zata
tabbatar
da cewa nine na lashe gasar.Abu na biyu kuma a
yanzu yadda nake a kwance cikin jinya za'a iya
shirya mini wata manakisar dazan kasa aiwatar
da
nufina na jaddada kalmar Allah a cikin bainar
taron
miliyoyin jama'a da zasu halac
ci filin sanar da sakamakon gasar.Idan ma na
fadi
cewa ubangijin musulunci ne ya bani sa'a da
karfinsa har na iya kashe zaki nurul maut,babu
mai
bayar da shaidar hakan tunda sa maza gudu ya
kashe alkalan gasa biyu wadanda sukaga faruwar
hakan da idanunsu.Koda nazo nan a tunanin
zucina
sai hankalina ya dugunzuma ainun na rasa
babinda yake mini dadi a duniya amma dana tuna
cewa
komai da kowa na karkashin ikon Allah saina
kama yin addu'a a cikin raina,nan take hankalina
ya
kwanta na sami nutsuwa.A ranar da muka koma
cikin birnin Kisra aka kaini masaukina shima sa
maza gudu aka kaishi masaukinsa daga sannan
bamu sake haduwa ba sai bayan kwanaki uku cur
a
tsakiyar filin gidan sarautar sarki Zaldashi.A
wannan
rana birnin gaba daya ya cika makil ya batse da
tarin bil'adama fiye da ranar ma da aka gabatar
da
wannan gasa ta farauta,duk inda ka gusa a birnin
saidai kaga kawunan bil'adama fululu babu
masakar
tsinke sai da kyar mutum zai iya kutsawa ta cikin
mutane ya wuce.A cikin kwanaki ukun dana yi a
masaukina naga tashin hankali domin sau goma
sha
daya ana kawo mini hari domin a hallaka ni
amma
sai Allah ya rinka kareni amma ba karfina bane
ko
dabarata.Bayan ga wannan kuma sai na tsinci
kaina
a cikin rashin ishesshen bacci,zulumi da fargaba
da
yawan tunani,ba komai ne ya haddasa mini hakan
ba face yawan begen gimbiya Lasmin da kuma
tunanin yadda karshen al'amura zasu
kasance.Duk
da cewa zargi haramun ne sai dana rinki zargin
jarumi sa maza gudu da sarki zaldasi bisa laifin
kokarin kashe ni da akayi saboda basa son ya
kasance nine na lashe wannan gasa.Lokacin
dana
baro masaukina na durfafi fadar sarki zaldasi ni
kadai ina kutsawa ta cikin miliyoyin jama'a sai
naji
zuciyata tayi fari sakamakon dalilai guda biyu.
Dalili na farko shine zanje naga fuskar
masoyiyata
gimbiya Lasmin wacce nake fama da azabar
begenta
da kewarta dare da rana,dalili na biyu kuma shine
ina murna gami da godiya ga ubangiji na wanda
ya
bani kariya har kawo izuwa wannan rana domin
in
ba don kariyarsa ba a yanzu haka nake yin
wannan
tafiya makiya zasu iya shammata ta

1 Comments On SA MAZA GUDU 1 to 9
avatar
adamu-3

1 year ago

Reply

Masha Allah Allah ya Kara basira Aboki

Please Login or Register in order to submit comment