Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

bakon jarumi ya shigo
har cikin birnina yana fadin kalmomin
addininsa.Koda jin wannan tambayoyi sai babban
hadimin ya nutsu ya dubi sarki yace ya shugaba
na ai tunda wannan takadirin jarumi ya gudu izuwa
cikin daji bai dawo ba cikin garin nan ba kuma
sautin murya da kaji yanzu ba muryarsa bace wata
bakuwar murya ce wacce ba'a taba jin irinta ba tafi
kama da muryar aljanu ma kuma daga cikin kuryar
daji take fitowa.Har yanzu sarkin yaki da dakaru
dari da suka tafi neman Gimbiya basu dawo
ba.Koda babban hadimin yazo nan a jawabinsa sai
sarki Zaldasi ya dawo cikin haiyacinsa yayi sauri
ya mayar da takobinsa cikin kufe sannan ya nufi
hanyar da zata kaishi can fadarsa yana tafiya cikin
sauri sauri gudu gudu.Da isowarsa fadar,babban
hadimi na take masa baya sai masu gadin kofar
sukayi sauri suka bude musu suka kunna kai ciki.
Maimakon Sarki Zaldasi ya nufi kan karagarsa ta
mulki yaje ya zauna sai ya kama kai kawo tamkar
mahaukaci sabon shiga.Al'amarin daya razana
babban hadimi kenan ya rasa abinda zaiyi saboda
yana tsoron kada yace wani abu tasa tayi zafi.Nan
da nan labarin ya bazu a cikin gidan sarautar da
wajenta cewar ga sarki can ya fito fada a lokacin
da bai taba fitowa ba,ai kuwa sai fadawa da
dukkan hadiman fadar suka rinka yin shirin
gaggawa suna tahowa fadar.Dakarun yaki kuwa sai
suka rinka shiri suna debo makamansu suna
tahowa izuwa fadar saboda a zatonsu lokacin fita
farautar Jarumi Hibairu ne yayi.Kafin sa'a daya
fadar ta cika tayi makil da fadawa gami da dakarun
yakin kasar.Shi kuwa sarki Zaldasi tuni ya koma
kan karagarsa ta mulki ya zauna kuma yayi shiru
sai kallon mutane yakeyi kawai yana ta kulle kulle
da kwance kwance a cikin zuciyarsa.Ana cikin
wannan hali ne labari ya iso cewa ga sarkin yaki
can sun iso kofar gari.Koda jin wannan batu sai
Sarki Zaldasi ya mike tsaye zumbur yace akawo
masa doki.Al'amarin daya baiwa kowa mamaki
kenan bisa ganin cewa sarki bazai ma iya jiransu
su iso ba saidai yaje ya taresu.Nan da nan kuwa
aka kawo masa doki ya hau,take gaba dayan
fadawa,Hadimai da dakaru suka rufa masa baya
aka nufi can hanyar fita daga gari,saida akayi tafiya
ta kusan dakika dubu sannan akayi kicibus dasu
sarkin Yaki.
ME ZAI FARU TSAKANIN SARKI ZALDASI DA
JAMA'AR SARKIN YAKI?
SHIN SARKI ZALDASI ZAI CIMMA BURINSA NA
KAMA JARUMI HIBAIRU?
INA LABARIN GASAR FARAUTAR ZAKI
MAUT,WAZA'A BAWA KAMBUN-SA MAZA GUDU NE
KO KUMA JARUMI HIBAIRU?
Duk Mai son jin amsoshin nan sai ya nemi Littafi
na Takwas(8) don jin cigaban wannan kasaitaccen
labari.An dauko wannan littafi daga shafin www.dlhausanovels.com.ng ku ziyarci shafin na www.dlhausanovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya

Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,

Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan
Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490

A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,

Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu

Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC

Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from www.dlhausanovels.com.ng
You can download more hausa novels there
Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online
It is free we do not charge for uploading novel
Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services

Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us

Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it

Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXTAn dauko wannan littafi daga shafin www.dlhausanovels.com.ng ku ziyarci shafin na www.dlhausanovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya

Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,

Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan
Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490

A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,

Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu

Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC

Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from www.dlhausanovels.com.ng
You can download more hausa novels there
Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online
It is free we do not charge for uploading novel
Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services

Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us

Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it

Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXTSA MAZA GUDU!!!
Littafi Na Takwas (8)
Part A.
TUN DAGA NESA JIKIN SARKI ZALDASI DANA
GABA DAYAN JAMA'ARSA YAYI SANYI.KUMA
HANKALINSU YA DUGUNZUMA BISA HANGO
YADDA AKA LULLUBE GABA DAYAN JIKIN
SARKIN
YAKI DA WANI BAKIN MAYAFI YANA ZAUNE
AKAN
DOKINSA TAMKAR WANI GUNKI KUMA WANI
BADAKARE NA RUKE DA LINZAMIN DOKIN YANA
JA.Koda hango hakan sai sarki Zaldasi yaja
linzamin dokinsa ya tsaya cak take gaba dayan
jama'ar dake bayan sama suka ja suka
tsaitsaya.Da isowarsu sarkin yaki sai gaba dayan
dakarun su dari suka sauko daga kan dawakansu
suka zube kasa suka kwashi gaisuwa.Amma shi
sarkin yakin yana zaune kijam akan
dokinsa,idanunsa ne kadai a bude suna wurkilawa
kuma yayi shiru baice uffan ba.Da ganin haka sai
sarki Zaldasi ya dubi sarkin yaki ya daka masa
tsawa yace me yasa kai ba zaka sauko ka
gaisheni
ba kamar yadda kowa ya gaisheni?Koda jin
wannan tambaya sai daya daga cikin dakarun
darin
yayi zumbur ya mike tsaye ya yaye mayafin da
aka
lullube sarkin yaki dashi,take sarki Zaldasi da
sauran jama'ar sukayi arba da halin da sarkin
yaki
ya shiga wato sukaga bakinsa ya karkace kuma
rabin jikinsa ya shanye.Koda ganin wannan
al'amari sai sarki Zaldasi ya kamu da tsananin
bakin ciki nanfa fuskarsa ta kama yatsinewa
idanunsa suka kada sukayi jajur gaba dayan
jikinsa
kuwa saiya kama karkarwa.Ba zato ba tsammani
sai akaga sarki Zaldasi ya takarkare ya bushe da
mahaukaciyar dariya.Al'amarin daya kara firgita
kowa kenan a wajen domin ba'asan irin matakin
da sarki zai iya dauka ba.Lokaci guda kuma sai
akaga sarki ya tsuke bakinsa kuma yayi shiru tsit
har izuwa tsawon yan dakiku baice uffan ba
kawai
muzurai yakeyi yana tunani.Daga can sai ya dubi
daya daga cikin dakaru darin yace bani labarin
menene ya faru har sarkin yaki ya sami wannan
lalurar?Ba tare da bata wani lokaci ba badakaren
ya kwashe labarin duk abinda ya faru ya
zaiyanewa
sarki Zaldasi.Koda sarki Zaldasi yaji wannan batu
sai hankalinsa ya dugunzuma ainun kuma ransa
ya
baci fiye da koyaushe.Nanfa ya kara yin shiru
yana
tunani da nazari.Adaidai wannan lokaci ne fadar
tayi tsit tamkar babu mutum daya mai numfashi
a
cikinta.Ba komai ne ya haddasa hakan ba face
tsananin tsoron sarki Zaldasi da kowa keji ana
tsoron kada fushin sarki ya shafe shi bisa
tsautsayi.Kwatsam sai akaga sarki Zaldasi ya
mike
tsaye ya kama kai kawo yana hange hange da
dube dube amma baiga wanda yake nema ba
kawai
saiya wangame bakinsa ya kwalawa Jarumi Sa
Maza Gudu kira,take kuwa akaji Sa Maza Gudu
ya
amsa kiran yana mai ratsowa ta cikin tsakiyar
jama'ar tun daga can farkon fadar.Nanfa aka
rinka
darewa ana bashi hanya,abinda ya daurewa kowa
kai a wajen shine ko makami guda daya babu a
jikin Jarumi Sa Maza Gudu sabanin ragowar duk
dakarun dake cikin fadar wadanda ke dauke da
MUGGAN MAKAMAN YAKI.Lokacin da jarumi Sa
Maza Gudu ya iso gaban sarki Zaldasi saiya zube
kasa a gabansa ya kwashi gaisuwa cikin sauri
sarki Zaldasi ya kama kafadunsa da hannayensa
biyu ya tashe shi tsaye ya dubeshi cikin alamun
tsananin damuwa kamar zaiyi kuka yace yakai
Jarumin Jarumai kayi sani cewa kaine abin
dogaro
na na karshe akan wannan takadirin yaro,saura
kiris ya raba ni da karagata da kuma
addinina,yanzu gashi ya rabani da yata,ta yaya
kake ganin cewa zamu iya zuwa can kogon dutse
mu yakeshi mu kasheshi na karbo yata?Na
rantse
da girman iyayena idan har ka taimaka wannan
bukata ta biya zan cika alkawarina a gareka na
tabbatar maka da zakaran wannan gasar jarumta
kuma zan baka auren gimbiya kuma zan
maisheka
wazirina.Koda Sarki Zaldasi yazo nan a zancensa
sai jarumi Sa Maza Gudu ya kamu da tsananin
farin ciki ya bushe da dariyar murna sannan ya
hade fuskarsa ya dubi sarki Zaldasi cikin
girmamawa yace ya shugabana na rantse da
darajar iyayena da kakanni na ni kadai zanje
wancan kogon dutse na yaki Jarumi Hibairu kuma
bazan dawo nan ba sai tare dashi a wulakance
domin muyi masa kisan wulakanci a gaban
dubban
jama'a.'Yarka kuwa zan dawo da ita gareka a
raye
cikin koshin lafiya,bana bukatar makami kuma
bana bukatar taimakon kowa ni kadai zan tafi
wannan aiki.Yayin da Jarumi Sa Maza Gudu yazo
nan a jawabinsa sai gaba dayan jama'ar dake
cikin
fadar suka kamu da tsananin mamaki.Nanfa
fadar
ta cika da kace nace wasu suce ai wannan
zancen
banza ne ya za'ayi sa maza gudu ya iya zuwa
wannan sihirtaccen kogon dutse wanda fiye da
shekaru dari baya babu wanda ya shigeshi ya fito
a
raye.Koda sarki Zaldasi yaga yadda fadar ta rude
da hayaniya kowa na fadin albarkacin bakinsa
saiya daka tsawa akayi tsit sannan ya dubi Sa
Maza Gudu cikin murmushi yace na baka kwana
uku kaje kazo mini da Hibairu da kuma yata
kamar
yadda kayi alkawari.Koda jin wannan batu sai sa
maza gudu ya risina tace kwana uku yayi nana
yawa ya shugabana,ina mai tabbatar maka da
cewa gobe war haka na gama cika aikina.Koda
gama fadin hakan sai Jarumi sai jarumi Sa maza
gudu ya juya ya fice daga cikin fadar.Ai kuwa
sai
jama'a suka biyoshi a baya duu!suna
mamaki.Abinda ya kara daurewa kowa kai shine
sa
maza gudu bai nemi doki ko guzuri ba akan
kafarsa ya kama tafiya cikin sauri daga can
kuma
sai ya fara gudu.Kawai sai gani akayi ya tashi
sama kamar tsuntsu mai fukafuki,nan da nan ya
luluka a cikin gajimare ya bace bat a cikin hadari
tamkar bai taba wanzuwa ba cikin sararin
samani.Jarumi sa maza gudu bai diro kasa a ko
ina ba sai a bakin kofar wannan kogon
dutse,kafafunsa na taba kasa sai kura ta turnuke
wajen gaba daya kuma kasar tayi girgiza tamkar
giwaye uku ne suka fado daga sama saboda
nauyin gangar jikinsa.Shi kansa kogon dutsen
saida yayi rawa kamar zai ruguje.
*Koda jin
hakan sai hankalin gimbiya Lasmin dana gaba
dayan aljanun dake cikin gidan ya dugunzuma
suka firgita.Wannan ne karo na farko da aljanun
suka taba jin sauyin yanayi a dajin gaba daya tun
daga ranar da aka kirkiri gidan.Cikin firgici
gimbiya
Lasmin ta dubi Jarumi Hibairu tace anya kuwa ba
mahaifina bane ya dira tare da dukkan dakarunsa
na yaki?Koda jin wannan batu sai jarumi Hibairu
yayi murmushi yace a'a ba mahaifinki bane ba
yazo tsohion masoyinki ne sa maza gudu
yazo,abinda nakeso dake shine duk abinda kikaga
ya faru a gareni kada ki tayar da hankalinki ki
sani
cewa muna tare da Allah wata kila muyi
azababben
yaki yanzu ni dashi,abinda na sani kawai shine
dai
indai ina numfashi bai isa ya iya rabani dake
ba.Taso ki biyoni a baya ki tsaya kiga yadda zata
wakana.Nan take Hibairu da Lasmin suka mike
tsaye da nufin su fice daga cikin gidan amma sai
Aljani Zulfanu ya baiyana tsulum a
gabansu,Zulfanu
ya risina yace ya shugabana ka barmu da
wancan
shaidanin yaro kuma mun ishe shi.Koda jin haka
sai Hibairu ya gyada kai yace a'a sa maza gudu
yafi karfinku,ka tuna cewa yanzu ku musulmai ne
dukkanin sihirinku na tsafi ya daina aiki bakusan
irin addu'o'in daya kamata kuyi ba na neman tsari
daga sharrinsa zai iya mamayarku ya cutar
daku.Nine kadai zan iya dashi kuma ku tsaya a
bayana ku zama yan kallo kada dayanku ya
kuskura yace zai tayani yakar sa maza gudu idan
har kuna son ku tsira da rayukanku.Gama fadin
hakan keda wuya sai Hibairu ya dauko takobinsa
ya juya ya nufi hanyar fita daga cikin kogon
dutsen.Nan take kuwa gimbiya Lasmin da sauran
dakarun Aljanun gidan suka rufa musu baya.
*Al'amarin Sa Maza Gudu kuwa tunda ya diro
kasa
daga sama ya tashi wannan kura saiya tsaya cak
kawai yana kallon bakin kofar kogon dutsen jim
kadan da tsayuwarsa saiga su Jarumi Hibairu sun
fito.Koda Hibairu yaga babu makami ko guda
daya
a hannunsa sa maza gudu saiya cika da mamaki
kuma sai yaga fuskar sa maza gudu cike da
annuri
yana tayi masa murmushi.Cikin kallo na rashin
yadda Hibairu ya dubi sa maza gudu yace
menene
ya kawoka nan?Kazo ne domin mu karasa
gasarmu ta jarumtaka ko kuwa kazo ne da wata
manufa?Koda jin wannan batu sai jarumi Sa
Maza
Gudu ya cire gaba dayan layu da gurayen tsafin
dake jikinsa ya ajiye kasa a gefe daya sannan
yace
yakai abokin gabata ada kayi sani cewa nazo
gareka da salama bawai da nufin gaba ba.Duk
abinda ya faru dazu tsakaninka dasu sarkin yaki
na gani a cikin madubina na tsafi kuma naga
yadda kazo wannan gida ka yaki duk aljanun
dake
cikinsa ka sami nasara akansu da karfin
ubangijinka sai jikina yayi sanyi zuciyata ta
karaya.Nan yake naji na fara gamsuwa cewa
lallai
mune akan karya kai kuwa kana kan gaskiya.A
yanzu dai nazo ne domin ka karayi min cikakken
bayani akan wannan addinin naka sannan na
karbeshi.Har jarumi Hibairu ya budi baki domin
yayi magana amma sai gimbiya Lasmin tayi caraf
ta tari numfashinsa tace kada kayi sauri yarda da
wannan abokin gaba naka domin makiyi abin
tsoro
ne.Koda jin haka sai Hibairu yayi murmushi yace
tabbas abinda kika fada gaskiya ne amma inaso
ki
sani cewa makiyi yana iya zama masoyi kuma
masoyi yana iya zama makiyi,samun irin su
jarumi
sa maza gudu a cikin addinin musulunci ba
karamar nasara bace da gagarumin cigaba.Lallai
zanyi farin ciki ainun idan har na sami nasarar
mayar dashi dan uwanmu.Koda jin haka sai
fuskar
Sa Maza Gudu ta sake fadada da murmushi ya
nufo su Hibairu kai tsaye ba tare da fargabar
komai ba.Da isowarsa sai Hibairu ya kama
hannunsa yaja shi suka kunna kai izuwa cikin
gidan gaba dayansu.Lasmin na daman Hibairu sa
maza gudu na hagunsa yana satar kallonta cikin
murmushi.Haka dai suka cigaba da tafiya har
suka
iso babbar fada ta gidan wacce tafi ko ina
kawatuwa.Nan take Hibairu yaja sa maza gudu
izuwa kan wata doguwar kujera suka zauna
tare.Lasmin ta zauna akan wata kujera dake
fuskantarsu sauran dakarun Aljanu kuwa wato
sau
Aljani Zulfanu sai suka yiwa fadar
kawanya.Faruwar
hakan keda wuya saiga kuyangin gidan sun shigo
dauke da ruwan inibi a cikin tambula da yawa
gami da kofuna.Ba tare da bata lokaci ba aka
zubawa kowa ruwan inibin a kofi aka bashi yasha
hatta su Aljani Zulfanu saida suka sha wannan
ruwan inibi.Lasmin,Hibairu da sa maza gudu ma
duk saida suka sha.A sannan ne kowa ya
nutsu,Hibairu yayi gyaran murya kuma ya dubi sa
maza gudu yace kafin na farayi maka bayanin
komai akan addinina da ubangijina inason kayi
abinda zai tabbatar mini da cewa ba kazo gareni
da nufin cutarwa ba.Sa'adda jarumi sa maza
gudu
yaji wannan batu na Hibairu saiya bushe da
dariya
sannan yace haba yakai abokina wace shaida
kuma kakeso na baka wacce tafi zuwan da nayi
gareka babu makami ko guda daya.A gaban
idanunka na cire dukkan layu da gurayena na
tsafi
na barsu acan wajen domin na shigo nan a
tsarkake.Koda jin haka sai Gimbiya Lasmin tayi
caraf tace inda da gaske ne kana son ka rabu da
gurayenka na tsafi ai ba ajiye su zakayi ba a gefe
daya saidai ka jefasu cikin wancan katon rami na
kofar gidan nan mai zurfin tsiya.Ni inaji a jikina
cewa kazo ne da nufin ka yaudaremu ka cutar
damu.Kafin Gimbiya Lasmin ta gama fadin
abinda
ke bakinta sai tari ya sarketa ta fara wani irin
kakari kamar zata yi kumallo.Nan take shima
Jarumi Hibairu ya kamayin kakarin haka sauran
gaba dayan dakaru da hadiman gidan kowa ya
rinka jin kamar ransa ne zai fita yayin da
idanuwan
kowa ya sauya launi izuwa launin ja,wasu ma sai
suka rinka faduwa kasa suna birgima kuma sai
jikin kowa ya mutu sukaji kamar babu laka a
jikinsu ko hannayensu basa iya dagawa.Koda
Jarumi Sa Maza Gudu yaga hakan dasu Hibairu
sun
shiga wani hali saiya bushe da mahaukaciyar
dariya ta farin ciki,yayi ta kyakyata dariyar kamar
ba zai daina ba har yana faduwa kasa daga can
kuma saiya mike tsaye yaje kan jarumi Hibairu ya
tsaya ya dubeshi yace kai yaro ni nan da kake
gani
na MURUCIN KAN DUTSE ne ban fito ba saida na
shirya,kayi babban kuskure daka yarda da
zancena.Tun a farko nayi amfani da dabara tane
ta
yaudara domin ganin bayanka.Layu da gurayen
tsafina dana cire daga jikina na ajiye a kasa ga
sunan a jikina dasu na shigo nan.Koda gama
fadin
haka sai sa maza gudu ya bude rigar dake jikinsa
wacce ta kasance falmaran ta fata saiga layu da
gurayen manne a jikinsa.Sa maza gudu ya cigaba
da cewa ruwan inibin da kowa yasha dazu na
zuba
wata guba a cikin mai kashe lakar jiki.Babu
wanda
zai sami karfin jikinsa a cikinku sai nan da bayan
cikar sa'a ashirin da hudu.Ko bakinka ba zaka iya
motsawa ba bare ka iya karanta wadannan
kalmomin na siddabarun daka saba yi ba domin
samun taimakon ubangijinka.Yanzu zan dauke ku
kai da masoyita na tafi daku izuwa can birnin
Misra gaban sarki Zaldasi.A gaban taron jama'a
za'a bani kambun gasar wannan jarumta kuma a
daura aurena da masoyita Lasmin kana ji kana
gani sannan muyi maka KISAN GILLAH.Koda sa
maza gudu yazo nan a jawabinsa sai hawayen
takaici ya zubowa Gimbiya Lasmin tace a cikin
ranta ina ma yanzu take Allah ya dauke
ranta.Hakan zai fiye mata komai farin ciki akan
taga yadda za'a yiwa Hibairu kisan wulakanci a
gaban idanunta kuma a daura mata aure da
mutumin data tsana fiye da komai.Tana cikin
wannan tunani ne taji sa maza gudu ya dauketa
ya
dorata akan kafadarsa ta dama sannan saiya
dauki
Hibairu ya dorashi akan kafadarsa ta hagu kawai
sai gani tayi ya tashi dasu sama ya ratsa ta
saman
ginin gidan kamar yadda danshi ke tsattsafowa
daga cikin karkashin kasa,nanfa ya luluka izuwa
kokoluwar sama yana tsala wani irin azababben
gudu tamkar na tauraruwa mai wutsiya.

SA MAZA GUDU!!!
Littafi Na Takwas (8)
Part B.
TAMKAR NA TAURARUWA MAI WUTSIYA.
*A CAN FADAR SARKI ZALDASI KUWA TUN
BAYAN
TAFIYAR JARUMI SA MAZA GUDU SARKI
ZALDASI
BAI SAMU NUTSUWA BA DA SUKUNI DOMIN
DUK
BAYANIN DA SA MAZA GUDU YAYI MASA BAI
GAMSU BA,JI YAYI KAMAR TATSUNIYA YAYI
MASA
DON GANI YAKE CEWA BAZAI IYA ZUWA YAZO
DA
HIBAIRU DA GIMBIYA BA.Yadda Sarki Zaldasi
yaga
rana haka yaga dare a wannan rana.Wato ko
rintsawa baiyi ba tare ya sami bacci kuma ko
abinci baici ba har gari ya waye rana ta sake
takewa ta fadi har dai izuwa faduwar rana yana
zaune akan karagarsa yana tunani da zulumi
gami
da bakin ciki saidai kawai idan ya gaji ya
muskuta
nan ya juya can.Abinci da abin sha kuwa an
kawo
sama da kala arba'in a gabansa amma ko guda
daya bai dandana ba.Gaba daya fadawansa sa
hadimansa ma sai sukayi koyi dashi sukayi
AZUMIN DOLE gami da tsayuwar dole a gabansa
ta
tsawon sa'a ashirin da hudu saboda biyayya gami
da tsoronsa.Ana cikin wannan hali ne kwatsam
sai
akaga Jarumi Sa Maza Gudu ya shigo Hibairu da
Gimbiya Lasmin bisa kafadunsa ya dire a gaban
karagar sarki.Koda Zaldasi ya kyallara ido yaga
Hibairu da Lasmin a gabansa sai ya mike tsaye
zumbur cikin matsanancin farin ciki da mamaki
mara misaltuwa ya daka tsalle daga inda yake ya
rungume Sa Maza Gudu ya rinka sumbutar
fuskarsa da goshinsa yana sa masa albarka.Gaba
jama'ar dake cikin fadar sai suka rude da shewa
gami dayin tafi da jinjina ga jarumi sa maza
gudu.Sauran jama'ar gari kuwa wadanda imani
ya
ishesu sukaji sun aminta da addinin musulunci
sai
hankalinsu ya dugunzuma suka rasa abinda yake
musu dadi.Koda sarki Zaldasi ya lura da halin da
Hibairu da Lasmin ke ciki na mutuwar jiki da
rashin kuzari tamkar gawarwaki sai hankalinsa ya
dugunzuma ya dubi sa maza gudu yace menene
ya faru ga yata kuma?Koda jin wannan tambaya
sai sa maza gudu yayi murmushi yace kwantar
da
hankalinka ya shugabana nan da cikar sa'a daya
kacal yarka zata dawo daidai amma dole ne mu
kashe Jarumi Hibairu kafin wannan lokaci.Koda
jin
wannan batu sai sarki yasa aka dauke Gimbiya
Lasmin aka tafi da ita can turakarta aka
shimfideta
akan gadonta,shi kuwa jarumi Hibairu sai aka
daukeshi aka tafi dashi izuwa can babban fili na
gidan sarautar bayan an daure hannayensa da
kafafunsa da wandasu manyan dogayen sarkoki
na
karfe.Nan da nan sarki yasa aka busa babban
kaho
na birnin wanda ke nuni da cewa ana gaiyatar
kowa izuwa filin fada.Ai kuwa cikin kankanin
lokaci
filin ya cika ya batse da al'umma duk inda
mutum
ya hanga gabas da yamma kudu da arewa babu
abinda zai gani face kawunan bil'adama rututu
babu masakar tsinke.Adaidai wannan lokaci ne
sarki Zaldasi da jarumi sa maza gudu suka iso
filin,nan da nan aka bude musu hanya suka iso
tsakiyar filin inda aka ajiye jarumi Hibairu.Tamkar
an shanya tsumma da isowarsu kansa sai Sarki
ya
hau kan mumbari ya dubi gaba dayan jama'ar
dake
wajen yayin da akayi tsit tamkar mutuwa ta gifta
yace yaku jama'ar wannan birni mai albarka ina
wadanda wannan jarumi ya ribaci zuciyarsu da
addininsa suka bayar da gaskiya a gareshi to
kuzo
kuga yadda zanyi masa KISAN GILLAH.Ina
addinin
nasa kuma ina ubangijin nasa?Me yasa ba zasu
zo
su cece shi ba yanzu?Koda gama fadin hakan
sai
sarki Zaldasi da jarumi Sa Maza Gudu suka
bushe
da dariyar mugunta sukayi ta kyalkyalawa kamar
ba zasu daina ba.Jama'ar da imani ya shigesu
kuwa take zukatansu suka karaya kuma jikinsu
yayi sanyi ainun hankalinsu ya dugunzuma.Lokaci
guda sarki Zaldasi da Sa maza gudu sukayi shiru
ga barin yin dariyar sannan Zaldasi ya dubi sa
maza gudu yace yakai JARUMIN JARUMAI yanzu
wane irin kisa ya kamata mu yiwa wannan
tsinannan yaron domin na huta da takaicina a
kansa?Koda jin wannan batu sai Sa maza gudu
yayi murmushin mugunta yace inason kasa a
kawo
kosassun dawakai guda dari da sittin,za'a daura
guda arba'in arba'in a kan kafafuwansa biyu
sannan a daura arba'in arba'in a kan hannayensa
sannan a zaburesu a lokaci guda domin su
tsinkashi a lokaci guda.Koda jin wannan shawara
sai sarki Zaldasi ya bushe da dariyar mugunta
yace da kyau BABBAN JARUMI tabbas wannan
shine irin kisan gillar daya dace da wannan
babban
makiyi namu domin ya zama abin misali ga
wanda
duk yakeson yazo mana da irin rainin dayazo
mana
dashi.Nan take sarki Zaldasi yasa akaje aka kawo
kosassun dawakai guda daro da sittin aka
daddauresu a jikin hannayen da kafafuwan
Hibairu.Duk wannan abu dake faruwa Hibairu naji
kuma yana gani amma ko kadan babu wata
damuwa a kan fuskarsa face ma murmushi da
yakeyi.Duk da cewa bashi da ikon ya bude
bakinsa
ya kira Allah domin ya nemi taimakonsa sai yace
a
cikin zuciyarsa Ya Allah kana ganin bawanka ne
wanda yayi imani dakai kuma ya baro kasarsa
domin yada addininka,ga wadannan mutane da
suka jahilceka suna son hallakani.Idan mutuwa ta
zatasa addininka ya kara yin rauni kada ka basu
sa'ar kashe ni idan kuma rayuwata ce zata
karfafi
zukatansu to ka cire mini wannan kasala da aka
sa
mini kuma ka karfafeni da karfinka yadda zan iya
ceton kaina na yakesu kuma na sami galaba a
kansu.Adaidai lokacin da Jarumi Hibairu ya
kammala wannan addu'ar ne a cikin zuciyarsa
aka
gama daure hannayensa da kafafunsa a jikin
kosassun dawakai guda dari da sittin kuma nan
take yaji wani irin gagarumin karfi na bazato ya
shigeshi wanda tunda yazo duniya bai taba jinsa
ba.Kawai sai sarki Zaldasi ya daga hannunsa
sama
yana mai bayar da umarnin a zaburi dawakan
guda
dari da sittin domin su tsintsinka sassan jikin
Hibairu.Koda ganin haka sai gaba dayan masoyan
Hibairu dake filin suka sunkuyar da kawunansu
kas
domin ba zasu iya kallon mugun
Kisan da za'ayi masa ba suka fara kukan bakin
ciki.Yayin da dawakan guda dari da sittin suka
yunkura domin suyi gaba sai akaga sun kasa
motsawa gaban sun kama turjiya a waje guda
suna
kuka da haniniya maimakon a jiyo ihun Jarumi
Hibairu,kawai sai akaga ashe Hibairu ne ya janyo
su da karfin damtsensa ya hanasu motsi.Nan
take
kwanjinsa ya kumbura rigar jikinsa ta yayyage ya
mike tsaye zumbur kawai sai gani akayi ya daga
dawakan su arba'in da suke daure da hannunsa
na
dama yayi hajijiya dasu a sama ya makasu da
kasa.Take dawakan su duka suka zama
gawa,haka
ma yayiwa dawakan hannunsa na hagu sarkar
data
daure kafafunsa kuwa da karfin tsiya ya cisgeta
daga jikin kafafunsa yayi wurgi da

1 Comments On SA MAZA GUDU 1 to 9
avatar
adamu-3

1 year ago

Reply

Masha Allah Allah ya Kara basira Aboki

Please Login or Register in order to submit comment