Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

domin ganin cewa
Lahaman baiyi nasara ba?Ina mai tabbatar maka
da cewa a halin yanzu babu mai mulki Azzalumi
mara imani kamar Yarima Lahaman aduk fadin
wannan duniya sannan kuma babu wani matsafi
mai karfin sihirinsa domin a yawon da yayi na
neman ilmin tsafi babu wani bangare a duniya
inda
baije ba duk inda wani mashahurin matsafi yake
sai yaje ya samu dukkan sihirin tsafinsa sannan
kuma ya sami horon yaki na gaban tunani.Karo
da
Lahaman daidai yake da karo da GUGUWAR
ANNOBA.Lokacin da gimbiya Zuhura tazo nan a
zancenta sai sarki Kamzal yayi doguwar ajiyar
zuciya sannan ya dubeta cikin alamun karayar
zuci
yace yake yata duk wannan abu da kika Prince
Auwal auwzab
fadi gaskiya yanzu nasan dasu kuma nasan da
wadansu abubuwan ma wadanda ke baki sani
ba.Tabbas idan Yarima Lahaman ya lashe
wannan
gasa ni ma bazan tsira ba kuma indai ina raye
bazan taba yarda ki zamo abokiyar rayuwarsa
ba,ni
kaina da dukkan bokayen kasar nan munyi bincike
a hallarar tsafinmu mun gano cewa babu wanda
zai
iya maganin Lahaman face Hibairu don haka a
gobe ina tsoron karon Sa Maza Gudu da
Lahaman.Ko kinsan cewa Lahaman yazo garin
nan
da dakarunsa na yaki kimanin su Miliyan uku
suna
can bayan gari sun yada sansani kawai jira yake
ya
lashe wannan gasa ya basu umarnin su shigo su
ci birninmu da yaki.Koda jin wannan batu sai
Sarki
Kamzal ya gyada kai yace yadda duk kike zaton
Yarima Lahaman ya wuce nan domin bai fito ba
saida ya shirya,ina mai tabbatar miki da cewa
inda
gaba dayan dakarun duniyar nan zasu taru a
kansa
ba zasu iya kasheshi ba,mutum daya ne jal nake
sa ran cewa zai iya ganin bayansa kuma ba wani
bane face masoyinki Hibairu kuma shima zai
sami
nasara ne a kansa kawai da taimakon ubangijinsa
ba wani da karfin damtsensa ba ko iya
yakinsa.Yayin da Zuhura taji haka saita dubi
mahaifin nata cikin mamaki tace shin yanzu kana
nufin cewa kaima kayi imani da addinin Hibairu?
Sa'adda sarki Kamzal yaji wannan tambaya sai
ya
sunkui da kansa kas yayi shiru kamar bazaice
komai ba daga can saiya numfasa yace yake
yata
kiyi sani cewa ita gaskiya dokin karfe ce bata
karyewa shi kuwa ramin karya kurarre ne.Fiye da
shekaru dari uki da suka gabata addinin Hibairu
shine kadai addinin da aka kasa shafeshi daga
doron kasa gaba daya,banda wannan addinin
babu
wanda ba'a sauya shi ko aka shafeshi gaba daya
ba.Iyayenmu da kakanninmu duk sunsan da
hakan
amma saboda son zuciya gami da son duniya sai
suka ki yarda da wannan addinin na musulunci
saboda sun san cewa addinin ne wanda zai hana
su yin zalunci kuma ya hana su yin bushasha.Ni
din nan yanzu idan nace zan karbi addinin
musulunci bisa tabbatar miki da cewa yan uwana
da fadawa na zasu hada kai da makiyana suga
bayana.Babu mai iya kafa wannan addinin a
wannan birni namu face irin su Jarumi Hibairu
kuma shima bazai iyayin hakan ba face an zubar
da jini kamar yadda akayi a garinsu Marigayiya
Gimbiya Lasmin.Ni yanzu babban tashin hankali
na
shine na tabbatar da cewa shi kansa Yarima
Lahaman babu wanda yake shakka face Jarumi
Hibairu don haka kafin goben nan zai iya bin
hanyoyi da yawa na ganin ya hallakashi bisa
wannan dalili na tura dakaruna da yawa akan su
baiwa Hibairu tsaro a masaukinsa.Haka itama
Gimbiya Malika da Masoyinta Sarki Hilairu
rayuwarsu na cikin mugun hadari domin suma zai
iya fara kashesu.Koda Gimbiya Zuhura taji
wannan
batu sai hankalinta ya dugunzuma ainun fiye da
koyaushe tayi shiru tana tunani da nazari har
izuwa lokaci mai tsawo.Daga can sai ta dago kai
ta
dubi mahaifin nata tace ko kadan bana shakkar
Hibairu domin nasan cewa ubangijinsa zai iya
kareshi daga dukkan sharrin Yarima Lahaman
Amma ina shakkar cewa gimbiya Malika da sarki
Hilairu zasu iya kare kansu don haka lallai ka
tura
dakarunka su basu tsaro.Sa'adda Sarki Kamzal
yaji
haka sai ya numfasa yace ai sarki Hilairu yana
tare
da dan uwansa Sa Maza Gudu don haka yana da
kariya,ita kuwa gimbiya Malika ai masaukinta
anan
cikin gidan yake ko kuwa kin manta ne da
hakan.Idan har wani abu zai taba lafiyarta to
lallai
zai taba tamu kenan,ki kwantar da hankalinki
kuma
kiyi addu'a akan Hibairu ya sami nasara akan
Lahaman gobe.Koda gama fadin hakan sai sarki
Kamzal ya juya ya nufi bangaren da turakarsa
take.Koda ganin haka sai itama Gimbiya zuhura
ta
tafi izuwa tata turakar amma sai taji kamar ta
fasa
zuwa turakar tata ta juya da baya ta tafi neman
inda masaukin Hibairu yake saboda tunaninsa da
begensa ne suka turnuke zuciyarta.Haka dai ta
karasa cikin turakar tata ta shige kewaye kuyangi
sukayi mata wanka suka shafeta da mai sannan
suka kawo mata abinci taci dan kadan saboda
tunani.Daga can sukaje suka kwantar da ita akan
gado domin tayi bacci amma sai baccin ya
gagara
domin da zarar ta rufe idanunta babu abinda take
gani face Jarumi Hibairu,idan kuma ta bude
idanun
nata sai taga Jarumi Hibairu a zahiri tsaye a gefe
guda yana yi mata murmushi(Hmm SO kenan).Da
zarar ta mike tsaye sai ta gane cewa lallai
tsananin
begensa ne yasa take ganinsa a zahiri don haka
sai ta kama kai kawo ta kasa kwanciya ta kasa
zama.A karshe dai saita yanke hukuncin cewa
duk
RINTSI DA TSANANI ba zatayi bacci ba a daren
yau
face taga jarumi Hibairu kuma taji muryarsa.
*Al'amarin Yarima Lahaman kuwa bayan filin
gasar
jarumta ya watse ya tafi izuwa masaukinsa a
wani
gida dake can bayan gari sai kuyanginsa sukayi
masa wanka suka wanke duk jinin dake jikinsa
suka sauya masa tufafi yayi fes dashi tamkar
jikinsa bai taba baci da jini ba.Daga nan sai
Lahaman ya dawo cikin filin gidan wanda ya
kayatu
ainun ya zauna akan wata doguwar kujera nan
take
aka kawo masa abin sha sama da kala goma aka
zube a gabansa bisa wani dan teburi mai fadi.Ba
tare da bata wani lokaci ba Lahaman ya fara
kimtsa cikinsa cikin tsananin farin ciki da
kwanciyar hankali tamkar babu wani abu da yake
damunsa a rayuwa,yana cikin wannan hali ne
babban hadiminsa da ake kira Zamnas ya iso
kofar
gidan a sukwane bisa doki kallo daya mutum zai
yiwa Zamnas ya gane cewa daga doguwar tafiya
yake domin hatta guzurin da yake dauke dashi
akan dokin irin na matafiya ne.Take Zamnas ya
baiyanawa Lahaman cewa komai ya kammala
akan
aikin da yasa su.Sannan kuma sun gamu da
yaran
gimbiya Malika mun kama su mun daure kuma
mun kwace duk dukiyar dake hannunsu mun
adana
maka ita.Koda Prince AUWAL AUW.ZAB
wannan batu sai farin ciki ya turnuke Lahaman
baisan sa'adda ya kurma ihu ba ya rungume
Zamnas yana mai cewa da Zamnas aikinka yayi
kyau nayi maka alkawari bayan na hau kan
karagar
mulkina kaine zaka zamo waziri na.Ina labarin
mahaifina ina fatan dai ka kiyaye duk abubuwan
dana shaida maka don kada ya gano shirina?
Zamnas ya risina yace na tafiyar da komai daidai
kamar yadda ka umarceni amma dole ne ka
sauya
tsarin shirinka domin a halin yanzu sarki Sharkif
ya yanke shawarar tahowa nan birnin domin yaga
wannan gasa ta karshe da za'ayi ina mai
tabbatar
maka da cewa kafin dare ya raba zai iso nan
kuma
dakaru dubu dari ne kacal sukayi masa
rakiya.Koda jin wannan batu sai yarima Lahaman
ya bushe da dariyar farin ciki sannan ya dubi
zamnas cikin murna yace ai babu bukatar na
sauya
tsarin komai nawa domin sarki ya tafka babban
kuskure daya fito daga cikin birninmu a wannan
lokaci,abinda nake so dakai shine yanzu kayi
sauri
ka koma can baya inda dakaruna guda MILIYAN
BIYU suka yada sansani ka jagorance su ku
danawa su sarki Sharkuf tarko da zarar sun iso
daidai kusa da sansanin ku kashe gaba dayan
dakarun nasa shi kuma ku kamashi a raye ku
daure shi sai ku shigo dashi cikin garin nan ku
kawoshi har filin gasa so nake ya gani da
idanunsa lokacin da zan fillewa gimbiya Malika
kanta a sannan ne zan rama wulakancin daya
dade
yanayi mini na fifita Malika akaina shima na sare
kansa na tsire shi akan mashi kowa ya
gani.Tabbas duniya zata tsorata dani idan akaji
cewa na kashe mahaifina da hannuna.Zamnas
najin haka saiya risina yace angama ya
shugabana.Nan take Zamnas ya juya da sauri ya
fice daga cikin gidan.fitar zamnas keda wuya sai
Yarima Lahaman ya mike tsaye yaje ya dauko
wata
katuwar bakar akwati ya ajiyeta a gabansa
sannan
ya budeta ya fiddo wani murtukeken dogon
maciji
bakin kirin mai faskeken kai,hakika wannan maciji
yana da matukar kwarjini.A cikin yaren tsafi
Lahaman yakama ambaton sunan Jarumi
Hibairu.Kawai saiya ajiye macijin a kas faruwar
hakan keda wuya sai macijin ya bace bat tamkar
bai taba wanzuwa ba a wajen.Da ganin haka sai
Yarima Lahaman ya bushe da dariyar mugunta
yayi ta kyakyatawa kamar bazai daina ba har
saida
wata babbar kuyangarsa tazo ta zauna daf dashi
ta
kama shafa gashin kansa ta dubeshi tace ya
shugabana waishin murnar me kakeyi ne?Koda
jin
wannan tambaya sai Yarima Lahaman yayi shiru
ga barin yin dariyar ya dubi kuyangar cikin
nutsuwa da murmushi yace kinga wancan macijin
sihirin dana saki yanzu duk mutumin daya sara
take zai mutu a cikin dakika biyar domin babu
wani abu da zai iya magance dafinsa,ina mai
tabbatar miki da cewa macijin wajen Jarumi
Hibairu ya tafi kuma nan da cikar sa'a guda zai
shiga har cikin masaukisa ya sareshi.Lallai gobe
da safe wasa daya zanyi domin daya abokin
gamin
nawa mutuwa zaiyi nan da cikar sa'a daya.Koda
jin haka sai kuyangar ta kamu da tsananin farin
ciki ta rungume Lahaman tana mai cewa ai kuwa
idan Hibairu ya mutu a cikin wannan dare kwana
zamuyi muna walima saboda munsan cewa saura
kwanaki kadan ka zame sarkin wannan nahiya
gaba daya.Dajin haka sai Lahaman ya sake
kankame kuyangar a kirjinsa yana mai cigaba da
kyalkyala dariyar murna kuma ya sunkuti tambula
na ruwan giya ya kafa a bakinsa ya kama sha.
*A Can Masaukin Jarumi Sa Maza Gudu kuwa
lokacin da suka shiga cikin turakarsa shida dan
uwansa sarki Hilairu sai suka ci suka sha suka
sami nutsuwa sannan Hilairu ya dubeshi yace
yakai dan uwana kayi sani cewa rayuwarmu gaba
daya tana cikin mummunan hadari ina tsoron
karonka da yarima Lahaman.Koda jin wannan
batu
sai Sa Maza Gudu ya bushe da dariya lokaci
guda
kuma ya murtuke fuskarsa tamkar an aiko masa
da
sakon mutuwa yace ya kai dan uwana kasani
cewa
tun muna yara ban taba yin FADUWAR GABA ba
kuma duk abinda nasa a gabana sainayi
nasara.Na
sani cewa zansha bakar wahala yayin gumurzuna
da Yarima Lahaman amma ban taba cire saran
samun nasara ba.Kuma nayi alkawari shima
bazaiyi nasara akaina ba.Fargabata guda daya ce
kawai sa'a uku ne kacal akeyi ana fafatawa a
wannan gasa kuma idan lokaci ya cika dayanmu
bai sami nasara ba tsayar da gumurzun za'ayi a
yi
wasa na gaba.Ina tsoron kada muyi ragas a cikin
sa'a ukun don haka duk yadda zanyi sainayi a
cikin sa'a uku naga bayan Lahaman sannan kuma
naga bayan Hibairu na mallaki masoyiyata.Loka
cin
da sa maza gudu yazo nan a zancensa sai sarki
Hilairu yayi ajiyar numfashi cikin alamun tsananin
damuwa gami da sunkui da kansa kasa yace
yakai
dan uwana har yanzu dai ashe kana kan bakanka
nason ganin bayan Hibairu wannan shine babban
kuskurenka a rayuwa domin kana sone ka kawar
da wanda yake yaki da zalunci ina mai tabbatar
maka da cewa har abada adalci baya kayar da
adalci saidai ya kayar da zalunci ko kuma zalunci
ya kayar da dan uwansa,tun farkon duniya haka
abin ya kasance kuma har karshenta haka zata
kasance.Azzalumai basa dorewa saidai suyi
shahara izuwa wani lokaci kafin wani zamanin
yazo
ya shafesu,ka kiyayi Hibairu domin ya wuce
yadda
duk kake zato.Hibairu ikon Allah ne kuma wata
baiwa ce daga mahaliccinsa kuma mahaliccin
nasa
shine wanda babu kamarsa.Koda jin wannan batu
sai sa maza gudu ya kamu da tsananin mamaki
kuma ransa ya baci ainun don haka bai san
sa'adda ya dakawa Hilairu tsawa ba yace kada
dai
kace dani kaima ka karbi wannan addinin na
Hibairu?Hilairu ya girgiza kai yace ban karbi
addininsa ba amma zan karba da zarar naga ya
sami nasarar kashe Yarima Lahaman.Cikin fushi
Sa
Maza Gudu ya cakumi kwalar Hilairu ya girgiza
shi
da karfi yace nine zan kashe Hilairu a gobe da
safe
kafin ma ya kashe Lahaman. To masu karatu
Yau zamugama wannan littafin Saura post 2
mugama wannan labarin mushiga wani me
suna...........KIBIYA RATSA MAZA wannan shine
sunan littafin da zamufara gobe idan da rai da
lafiya ko kuma kuna ganin mukaishi bayan sallah
karama Sbd azumi da zamushiga????ga dan
kadan daga cikin sabon littafin da zamushiga
gobe............... KIBIYA RATSA MAZA
Littafi na Daya(1)
Part A
Gudu takeyi iya karfinta domin ta ceci rayuwarta
saboda bala'in dya biyo ta,babu abinda za'a
kwatantashi dashi face ajali.Babu abinda zai
baka
mamaki face wannan budurwa dake wannan
azababben gudu,kyakkyawa ce abar
kwatance,kuma
cikin shigar yaki take,ga takobi a hannunta
tsirara
ba'a ciki kufe ba.Saboda karfin gudun da takeyi
tamkar tafin kafarta zai tabo keyarta,amma duk
da
haka waige waige takeyi a cikin alamun tsoro,duk
da
cewa kana mata kallo daya zaka gabe cewa
jarumace ta kwarai mai kirar sadaukai.Kai bama
ita
ba hatta aljanu da tsuntsaye dake cikin wannan
daji
da take gudu a cikinsa tsoron dajin sukeyi da
abinda ya biyota saboda masifu da bala'in dake
tare
dasu ballantana kuma bako irinta wanda bai tana
shigowa dajin ba.

★SA MAZA GUDU★!!!
Littafi Na Tara (9)
Part B. prince AUWAL AUW.ZAB
NINE ZAN KASHE HILAIRU A GOBE DA SAFE
KAFIN
MA YA KASHE LAHAMAN.KADA KA SAKEYI MIN
WANNAN MAGANA.KODA GAMA FADIN HAKAN
SAI
SA MAZA GUDU YA TAFA HANNUNSA SAU
UKU.NAN TAKE DAYA DAGA CIKIN DAKARUN
DAKE
TSARON LAFIYARSA YA SHIGO CIKIN TANTIN
WANI
DOGON SADAUKI NE MAI KWARJINI.Badakaren
ya
zube kasa a gabansa cikin biyayya shi kuma
saiya
dubeshi yace ni zan kwanta nayi bacci
yanzu,kusa
ido sosai akan aikinku kada ku bar mutum ko
daya
ya shigo cikin gidan nan kuma kada ku bar dan
uwana ya fita.Badakaren ya risina yace an gama
ya
shugabana kawai saiya mike tsaye ya fice daga
cikin turakar fitarsa keda wuya sai Hilairu ya dubi
sa maza gudu yace saboda me zaka kafa mini
dokar kin fita alhalin inason naje naga
masoyiyata
gimbiya Malika?Sa maza gudu ya juyo ya dubi
Hilairu a fusace cikin daga murya yace shin baka
san cewa rayuwarka na cikin hadari bane?To ka
sani ana farautar rayuwarka a halin yanzu kamar
yadda mai jin kishi ke neman ruwa ko don
saboda
a kunsa mini bakin ciki.Sa maza gudu na gama
fadin hakan saiya kwanta akan shimfidarsa ya
runtse idanunsa ai kuwa kafin cikar dakika dari
da
ashirin tuni ya fara munshari abinsa tamkar babu
wani abin damuwa a cikin zuciyarsa.Al'amarin
dayayi matukar baiwa sarki Hilairu mamaki kenan
yace waishin wannan dan uwan nawa wane irin
mutum ne shi wanda KARFIN ZUCIYARsa yafi na
zaki.Ban taba ganin ranar da zuciyarsa ta karaya
ba kuma ban taba ganin ranar da yaji tsoron wani
abu mai rai ba walau mutum ko Aljan,dabba ko
kwaro.Wannan shine abinda ya faru tsakanin
jarumi sa maza gudu da dan uwansa sarki Hilairu
acan masaukinsu.
*Al'amarin jarumi Hibairu kuwa lokacin daya tafi
nasa masaukin wanda ke can wani bangare
daban
na gidan sarautar.Bayan ya idar da sallar
magriba
sai yayi addu'a ya roki Allah akan ya kareshi
daga
sharrin abokan gaba kuma ya bashi nasara bisa
abinda yasa a gabansa na jaddada Addinin
Musulunci a nahiyar gaba daya kuma ya bashi
ikon komawa gida lafiya domin ya sadu da
iyayensa.Koda gama wannan addu'a sai ya sake
karanta wata addu'ar ta musamman ta neman
tsari
ya tofa a jikinsa ya shafe ko ina sannan ya
kwanta
domin ya dan huta.Faruwar hakan keda wuya sai
bacci ya daukeshi sakamakon tsananin gajiyar
dake jikinsa.
*Acan turakar Gimbiya Zuhura kuwa lokacin da
taga ta kasa yin komai sakamakon tunani da
begen Hibairu daya addabi zuciyarta sai kawai
tasa
aka kirawo mata shugaban dakarun dake tsoron
lafiyarta Barde Sharmas ta dubeshi tace inason
kayi mini rakiya yanzu izuwa masaukin jarumi
Hibairu domin inason nayi magana dashi.Koda jin
wannan batu sai idanun Barde Sharmas suka
zazzaro ya dubeta cikin alamun matukar tsoro
yace ya shugabata sarki yayi mana gargadi a kan
kada mu bari ki tafi ko ina saboda hadarin da ake
ciki,idan har wani tsautsayi ya sameki zan iya
fuskantar babban hukunci.Cikin matukar fushi
gimbiya Zuhura ta dubi Barde Sharmas tace haka
kuma zaka fuskanci kaidi irin namu na mata idan
baka bi umarni na ba a yanzu,shin kasan sharrin
da zanyi maka kuwa yanzu idan kaki rakani
masaukin Hibairu?Koda jin wannan batu sai jikin
Barde Sharmas ya kama karkarwa muryarsa na
rawa yace ke kuwa wane irin sharri zakiyi
mini.Gimbiya Zuhura tace zan yayyaga tufafin
jikina kuma na fasa bakina da hancina su kama
yoyon jini sannan na kwala ihu nace kayi
yunkurin
yi mini fyade.(Uhmm Kuji Kadan daga Kaidin
Mata).Koda jin haka sai Barde Sharmas ya
durkusa
bisa guiwoyinsa ya kama rokon gimbiya akan ta
rufa masa asiri kada tayi masa wannan
sharri.Koda
ganin haka sai tayi murmushi tace ka cika
umarnina idan kana son ka kubuta.Ba tare da
gardamar komai ba sharmas ya mike tsaye cikin
alamun tsananin sanyin jiki ya juya ya fice daga
cikin turakar ita kuma ta bishi a baya da
sauri.Duk
inda suka ratsa a cikin gidan sarautar sai suga
dakaru,bayi da hadimai suna kallonsu cikin
mamaki saboda sani dokar da sarki ya kafa
amma
sai aka rinka ratsewa ana basu hanya kuma ana
gaishe da gimbiya haka dai suka cigaba da tafiya
har suka iso kofar turakar da jarumi Hibairu ke
ciki.Da isowarsu sai masu gadin dakin suka dare
suka basu hanya.Kawai sai Gimbiya Zuhura ta
dakatar da Barde Sharmas tace ka tsaya anan ka
jira ni bazan dade ba zan fito mu tafi.Cikin
karayar
zuciya Barde Sharmas ya sunkui da kansa kasa
ya
kasa cewa komai saboda ya tsorata da Gimbiya
Zuhura.Take gimbiya Zuhura ta kunna kai cikin
turakar tana mai murmushi taje kansa ta tsaya ta
kura masa idanu.Kwatsam ba zato ba tsammani
sai taji wani irin mugun huci a bayanta gami da
wani babban motsi,a firgice ta juyo da baya da
sauri kawai sai tayi arba da wani murtukeken
bakin
dogon maciji ya fasa kansa zai kaiwa Hibairu
sara,kawai sai Gimbiya Zuhura ta daka tsalle
tasha
gaban macijin ai kuwa sai ya sareta akan
kafadarta.Take ta kurma ihu,kafin macijin ya juya
ya sari Hibairu tuni Hibairu ya daka tsalle sama
daga kan gadon da yake kwance.Yana saman ya
zare takobinsa yana mai kwala kabbara ya sare
kan macijin take macijin ya sulale kasa
matacce.Adaidai wannan lokaci ne su barde
Sharmas suka fado cikin daki a gigice ruke da
makamansu tsirara.Koda sukayi arba da gawar
macijin sai suka kame,shi kuwa Hibairu sai yaga
Gimbiya Zuhura ta sulale kasa ta baje kamar
gawa
kuma yayi arba da inda macijin ya sareta kan
kafadarta.Sai ya durkusa ya kafa hakoransa akan
wajen ya rinka zuko dafin macijin yana furzarwa
a
kasa saida Hibairu ya zuko dafin sau tara yana
furzarwa a kas.Su kuwa su barde Sharmas sun
zuba idanu kawai cikin alamun tsananin
tsoro.Yana
gama cire mata dafin sai su kaga shima ya
sulale
kasa ya baje jikinsa na
Prince Auwal Auwzab
makyarkyata alamar cewa shima dafin ya shige
cikinsa.Adaidai wannan lokaci ne gimbiya Zuhura
ta farfado daga dogon suman da tayi ta mike
zaune zumbur tamkar wani abu bai sameta
ba.Koda taga Hibairu kwance a kasa yana
makyarkyata sai ta fada kansa ta rungumeshi
kuma
ta fashe da matsanancin kuka.Ba zato ba
tsammani sai taga Hibairu ya kama yin
kumallo.Nan take ya amayar da dukkanin dafin
daya shiga cikinsa a kas wanda ya kasance bakin
kirin tamkar an jika shuni.Nan take ya sami lafiya
ya dawo cikin haiyacinsa.Koda ganin haka sai
farin
ciki ya lullube zuhura ta rungumeshi tana mai
rusa
dariyar murna.Cikin hanzari Hibairu ya janye
jikinsa
daga cikin nata ya dubeta a cikin fishi yace
menene ya kawo ki dakina kuma saboda me zaki
siyar da rayuwarki don kare tawa?Lokacin da
gimbiya Zuhura taji wannan tambaya saita bushe
da dariya a karo na biyu sannan tace na kasa
zama na kasa kwanciya na kasa tsayuwa kuma
na
kasa tafiya duk saboda tsananin begenka da
tunaninka wannan shine dalilin da yasa na baro
turakata na taho nan.Na siyar da rayuwata don
kare taka domin na tabbatar maka da cewa ina
kaunarka kamar yadda Marigayiya gimbiya
Lasmin
ke kaunarka,shin yanzu ka gamsu cewa nafi
Lasmin sonka?Sa'adda Gimbiya Zuhura tazo nan
a
jawabinta sai idanun su barde Sharmas ya
zazzaro
suka cika da tsananin mamaki,shi kuwa jarumi
Hibairu saiya dubeta cikin murmushi yace na
yarda
kina kaunata tamkar yadda marigayiya ke
kaunata
amma ban yarda cewa kin fita kaunata ba.Dajin
haka sai gimbiya Zuhura ta mike tsaye zumbur a
fusace ta dakawa Hibairu harara tace shikenan
sai
gobe a filin gasa zan tabbatarwa da duniya cewa
babu wata 'ya mace dake kaunarka sama
dani.Tana gama fadin jakan sai ta juya ta fice
daga
cikin dakin da sauri shima BARDE Sharmas saiya
ruga ya take mata baya.Dul wannan abu da yake
faru a turakar Hibairu Yarima Lahaman ya gani a
cikin MADUBIN TSAFI.Koda yaga cewa wannan
maciji bai sami nasarar kashe Hibairu ba kuma
yaga yadda Zuhura ta sallama rayuwarta don
kare
ta Hibairu saboda soyayya sai zuciyarsa ta kama
tafarfasa bai san sa'adda ya rotsa madubin
tsafin
nasa a kasa ba ya kma tattakaeshi da kafafunsa
yana huci da gurnani tamkar bakin kumurci.Kashe
gari kuwa tun kafin alfijir ya keto filin gasar
jarumta ya cika ya batse da mutane babu inda
za'a
iya sanya koda tsinke.Ba komai ne ya janyo
hakan
ba face zumudi da dokin al'umma nason ganin
yadda karshen wannan gasa zai kasance.Saida
gari
ya waye sosai rana ta take sannan sarki Kamzal
da
jama'arsa suka shigo cikin filin gasar da kyar
dakaru suka buda musu hanya suka isa inda
mazauninsu yake saboda cikowa.A wannan
lokaci
sarki Kamzal na ruke da hannun yarsa gimbiya
Zuhura suna ta kalle kallen filin gasar suna
mamakin irin tsananin cikowar da akayi wacce
ba'a taba yin kamar taba a tsawon shekaru goma
sha biyar da fara shirya wannan gasa.Saida sarki
da mukarrabansa sukaje suka zauna a
mazauninsu
sannan aka buga tambari jaruman gasa suka fito
mutun uku ne kacal jaruman gasar kuma ba
wadansu bane face jarumi Hibairu,Jarumi Sa
Maza
Gud da kuma Yarima Lahaman.Dukkani
nsu sunyi
gagarumar shigar yaki mai tsananin
kwarjini.Koda
shigowarsu cikin filin gasar sai jama'a suka
kaure
da shewa gami da tafi kowa na koda gwaninsa.A
wannan rana attajiran caca kuwa sunfi mutum
dubu arba'in kuma kowannensu saida ya zazzage
gaba dayan dukiyarsa don gudanar da wannan
caca.Bayan jaruma gasa sunje sun tsaya a inda
suka saba tsayawa suna kallon juna cikin harara
sai alkalin gasa ya shigo tsakiyar fili ya tsaya
domin ya gabatar da gasar.Kwatsam ba zato ba
tsammani sai aka hango wani mahayi ya surfano
doki a sukwane izuwa cikin taron jama'a gaba
daya jikin mahayin a rine yake da jini hatta
fuskarsa da dokinsa kuwa.Har dakarun sarki
Kamzal sun yunkura zasu tareshi sai sarki ya
daga
hannu sama yayi musu inkiyar su tsaya.Kai tsaye
mahayin ya durfafo inda sarki Kamzal yake da
isowarsa sai sarki Kamzal ya mike da sauri ya
ruke masa dokin da kansa ya sauka sannan suka
rungume juna.Nan take sarki Kamzal yaja
mahayin
har izuwa kan kujerarsa suka zauna tare.Kawai
sai
sarki Kamzal yace a cigaba da gabatar da
gasa.Al'amarin daya daurewa kowa kai kenan
domin hankalin kowa ya tashi bisa ganin mahayin
a cikin jini kace kace gashi ko fuskarsa ba'a iya
gani bare a gane ko waye.Alkalin gasa ya duni
jama'a yace yanzu zamu kirawo jarumi sa maza
gudu tare da yarima Lahaman domin su fafata a
zagaye na biyun karshe.Nan take aka buga
tambari
sa maza gudu da Lahaman suka shigo cikin
tsakiyar filin,a guje alkalin gasar ya fice daga
cikin
filin.Ai kuwa yana fita sai sa maza gudu da
Lahaman suka rugo izuwa kan junansu suka
ruguntsume da azababben yaki mai tsananin ban
tsoro da ban al'ajabi.Saida suka shafe sa'a guda
cif suna kaiwa junansu sara da suka batare da
dayansu ya sami wata nasara ba har takubbansu
suka dakushe garkuwoyinsu suka farfashe amma
ko alamar gajiya babu a tare dasu,bisa dole suka
watsar da takubban da garkuwoyin suka kacame
da naushi gami da bugun juna ya zamana cewa
sun hadawa junansu jini da majina suka galabaita
ainun amma saboda bakin naci da tsananin juriya
da jarumtaka har wata sa'a gudan ta sake
shudewa
dayansu baije kasa ba.Adaidai wannan lokaci ne
aka buga ganga suka tsaya ga barin fadan,alkalin
gasa ya shigo ya dubesu yace yanzu saura sa'a
daya kacal gumurzun ya kare kuna bukatar a
sake
baku makami?Cikin hadin baki sai sukace suna
so
nan take aka kawo musu manyan takubba da
manyan garkuwoyi sababbi suka buda,alkalin
gasa
ya sake rugawa waje aka buga tambari.Wohoho
idan karfi ya hadu da karfi sadaukantaka da tadu
da
Prince Auwal Auwzab Auwzab
takwaranta kuma tsafi yayi karo da tsafi dole ne
gumurzu yayi zafi.Saida sa maza gudu suka sake
shafe rabin sa'a suna mugun artabu cikin sauya
salon yaki iri iri sannan kowannensu ya sami
nasarar yiwa abokin gwaminsa rauni uku.Gashi
dai
jini na zuba a jikinsu amma basu fasa kokarin
hallaka junan suba duk da cewa jiri na dibarsu
suna layi kamar zasu fadi.A lokacin da jini ke
zuba
a jikinsu ne lokaci na dab da cika ne Lahaman ya
shammaci sa maza gudu ya doki kafafunsa sa
maza gudu yayi sama ya wurkila jikinsa kafin ya
diro kasa Lahaman ya daka tsalle sama ya doki
kirjinsa ya fado kasa a matukar galabaice.A
daidai
wannan lokaci ne aka buga gangar tsayar da
gumurzun saboda lokacin ya cika amma duk da
haka sai Yarima Lahaman ya falfalo da gudu
izuwa
kansa yai sama yana mai daga takobinsa domin
ya
soke cikin sa maza gudu.A wannan lokaci sa
maza
gudu bazai iya kare kansa ba saboda ko kada
babu karfi a jikinsa idanunsa ma lumshewa
sukeyi
yana gani dishi dishi.Koda Hibairu ya hango
abinda ke shirin faruwa sai ya falfalo da
azababben
gudu ya dako wawan tsalle daga inda yake
tamkar
an harbo shi daga cikin BAKA.Saura kiris tsinin
takobin Lahaman ya tsire sa maza gudu sai
kawai
akaga Hibairu ya doki kirjin Lahaman da kafarsa
guda saboda karfin duka saida Lahaman yayi
baya
tamkar an janyeshi da majaujawa kuma ya fado
kasa a galabaice ya furzar da gudan jini daga
bakinsa.A sannan ne Hibairu ya diro da
kafafunsa
ya dubi Yarima Lahaman yace ka karya dokar
gasa
kayi yunkurin kashe abokin gwaminka yayin da
lokacinku ya cika.Kaje likitanka yayi maka
magani
kuma ka sami hutu sannan kazo muyi wasan
karshe.Koda jama'a sukaji wannan batu na
Hibairu
sai suka rushe da ihu gami dayi masa jinjina shi
kuwa yarima Lahaman bakin ciki ne ya turnuke
shi
ya mike tsaye a fusace ya nuna Hibaiur da dan
yatsa yace zanje na dawo nayi maka alkawari sai
nayi maka kisan gilla irin wanda ba'a taba yiwa
wani mahaluki ba a doron kasa ba.Yana fadin
hakan saiya juya ya fice daga cikin filin gasar ya
nufi inda likitansa ke zaune.Shi kuwa jarumi Sa
Maza Gudu tun sa'adda yaga Hibairu ya ceci
rayuwarsa a lokacin da Yarima Lahaman ya dako
tsalle zai tsire shi da takobin a ciki.Mamaki ya
turnuke shi saboda bai taba zaton cewa akwai
ranar da wannan babban makiyansa zai iya yi
masa wani taimakon ba.Nan take jikin sa maza
gudu yayi sanyi kuma ya kurawa Hibairu idanun
kawai yana mai tambayar kansa a cikin zuciyarsa
yace waishin su wadannan ma'abota addinin
musuluncin wace irin zuciya ce dasu haka mai
tausayi da imani?Yana cikin wannan tunani ne
yaga Hibairu ya durfafo shi koda ya iso gareshi
saiya kama hannayensa ya tashe shi tsaye
sannan
ya goyashi a bayansa yakai shi har inda likitansa
yake yana kwalawa likitan kira cikin tsawa akan
ya
gaggauta yi masa magani.Saida Hibairu yaga an
gama dinke raunikan jikin sa maza gudu ansa
masa magani sannan ya juya zai koma cikin filin
gasa kawai sai Hibairu yaji sa maza gudu ya riko
hannunsa.Cikin tsananin mamaki ya juyo ya
dubeshi sai yaga yanayi masa murmushi kuma
hawaye na zuba a idanunsa.Sa maza gudu ya
dubi
Hibairu yace sai yau ne na tabbatar da cewa
makiya na iya zama masoyi,yakai Hibairu ina
neman gafara a gareka bisa duk abubuwan
danayi
maka kuma halaiyarka da karfin imaninka akan
addininka sunsa yanzu take nayi imani da
ubangijinka maza ka shigar dani

1 Comments On SA MAZA GUDU 1 to 9
avatar
adamu-3

1 year ago

Reply

Masha Allah Allah ya Kara basira Aboki

Please Login or Register in order to submit comment