Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

su cutar
dani ba
tare dama naga wanda ya cutar dani din
ba.Tunda
gani a cikin turmutsun mutane da babu adadi
haka
dai na ci gaba da tafiya har na samu da kyar na
iso
gidan sarautar,ina isowa bakin kofar na kunna kai
ciki,daga sannan ne naga dakarun sarki sun fara
bani kariya suna hana kowa zuwa kusa dani ko
ya
rabeni face attajirin gasar daya zabeni a
matsayin
jaruminsa wanda ake kira da suna Abu Salif.
Abu Salif ya kasance matashin mutum dan
kimanin
shekaru talatin zuwa arba'in,ya kasance gajeren
mutum kamar wada amma kuma fuskarsa nada
kwarjini,Abu Salif na ganina sai ya taho gareni da
sauri cikin farin ciki ya rungumeni sannan ya
kama
hannuna muka cigaba da tafiya inda ya dubeni
yace,yakai jarumina kayi sani cewa da zarar an
baka
wannan kambun gasa shike nan nida kai mun
gama
yin arziki,yayanmu da jikokinmu ma har abada
bazasuyi talauci ba,sa'adda naji wannan batu sai
nayi murmushi nace,ai duk abinda zaka samu
sakamakon cacar da ka shiga naka ne kai kadai
saboda aini a addininmu caca haramunce don
haka
bana cin kudin caca.Koda jin haka sai Abu Salif
ya dubeni cikin alamun tsananin mamaki
yace,wane irin
addini ne haka?Hibairu yace ni ma'abocin addinin
musulunci ne.Ko da jin haka sai attajiri Abu Salif
ya
tsaya cak a inda yake idanunsa suka zazzaro
kuma
jikinsa ya kama kyarma ya dubeni cikin alamun
tsananin tsoro yace,kada ka kuskura ka baiyana
addininka a garin nan domin an tsani musulunci
da
musulmai fiye da komai,mutane zasu iya yi maka
rajamu a kashe ka a banza.koda jin haka saina
dubi
Attajiri Abu Salif nayi murmushi nace,zan
kasance a
cikin tsananin farinciki idan har kuka kasheni a
lokacin dana jaddada kalmar Allah a gareku
saboda
nasan cewa na sami kyakkyawar cikawa domin
Aljanna ce mako mata a wajen ubangijina.Ina
gama
fadin haka saina cigaba da tafiyata cikin
kwanciyar
hankali da nutsuwa tamkar babu wani abu daya
taba
damuna a rayuwata.Har muka iso tsakiyar gidan
sarautar jikin Abu Salif bai daina tsuma ba
saboda
tsananin tsoro.Muna isowa na fara yin arba da
jarumi sa maza gudu a tsaye a tsakiyar filin shi
kadai a cikin gagarumar shigar yaki,nima sai na
nufi
inda yake naje na tsaya daf dashi,muna kallon
juna
sai yayi mini wani irin murmushi wanda na kasa
gane ko na mugunta ne, ko kuma na farinciki,ina
daga kaina sama sai na hango sarki zaldasi tare
da
gimbiya Lasmin zaune a can sama bisa wani gini
mai tudu bisa kujeru na alfarma tare da
fadawansa
da manyan sarakunan nahiyar da kuma manyan
baki.Ina hada idanu da Lasmin sai naga ta kura
mini
idanu cikin murmushi mai taushin gaske wanda
ke
dauke da alamonin tambaya.Nan take na maida
nata
da martanin murmushin,saboda dadin dataji bata
san sa'adda ta wage baki ba tana dariya.Koda
sarki
Zaldasi ya lura da ita sai ya murtuke fuskarsa ya
daka mata harara.Gaba daya gidan sarautar a
cike
yake da mutane babu masakar tsinke har kan
katanga mutane ne a zazzaune sun zuba idanu
suga
wanda zai zama zakaran gasa.Acan gefe daya
kuma
sabbabin alkalan gasa ne kimanin su saba'in a
zaune rike da alkalami da takarda na rubutu.Koda
na
tsaya a tsakiya filin sai na risina na gaida sarki
sannan na gaisar da sauran jama'ar gari,ai kuwa
sai
filin ya rude da shewa gami da tafi aka rinka yi
mini
jinjima.A wannan lokacin hayaniyar mutane ta
cika
gaba gidan sarautar daya,kowa yana fadin
albarkacin
bakinsa ne dangane da wannan gasa da
akayi,wasu
ma musu sukeyi akan cewa babu yadda za'ayi a
iya
tantance gaskiyar wanda ya lashe wannan gasa
tsakanin Jarimi Hibairu da Jarumi
Alkas,wasu kuma jimami sukeyi akan rashin
da'akayi
na dumbin rayuka.Anan cikin wannan hali ne
sarki
Zaldasi ya mike ya daga hannunsa sama.Nantake
fadar tayi tsit tamkar babu mutane a cikinta
sannan
yayi gyaran murya yace,yanzu zamu saurari
bayani
daga bakin wadannan manyan zaratan jaruman
gasa
guda biyu wadanda su kadai ne suka tsira da
rayuwarsu a cikin dajin Sairul sakamakon yin
arba
da zaki nurul maut,kuma sune kadai suka fafata
dashi har suka sami nasarar kashe shi.A cikin
bayanin kowannensu numa son ya fadi shaidar
da
zata tabbatar da cewa shine ya kashe wannan
zaki.Bayan mun gama saurarin bayaninsu ne
alkalan
gasa zasuyi amfani da hankali da kuma hikima
wajen tantance mai gaskiya,sannan abashi
ladansa
na gasar kamar yadda nayi alkawari,ma'ana zan
baiwa zakaran wannan gasa auren 'yata gimbiya
Lasmin.Zan raba kasata biyu na bashi rabi ya
mulka
kuma zan bashi dukiya mai tsananin yawan da
har
bayan sa ma bazasuyi talauci ba.Koda jin
wannan
batu sai fadar ta rude da shewa gami da
tafi,makada
da mawaka suka kama shagalinsu.Saida sarki
Zaldasi ya koma kan kujerarsa ya zauna sannan
aka
sake yin tsit,a sannanne shugaban alkalan gasar
ya
dubi sa maza gudu yace,kai ne zaka fara yin
bayani,sannan jarumi Hibairu yayi nasa.Ba tare
da
bata wani lokaci ba Sa Maza Gudu yace gyara
tsayuwarsa kuma yayi gyaran murya yana mai
fuskantar miliyoyin jama'ar dake cikin fadar ya
bude
baki yace,kamar yadda aka gani a zahiri mun kai
mu
dubu dari shida da doriya muka shiga cikin dajin
Sairul domin kashe zaki nurul maut,amma mu
biyu
ne kacal muka dawo a raye,ina mai tabbatar
muku
da cewa munga bala'i da masifa irin wacce babu
makamanciyarta a cikin wannan duniya,lokacin
da
mukayi arba da zaki nurul maut,kuma nan take
zaki
nurul maut ya rikide ya zama wani irin mugun jan
haske ya rinka burma gadon bayan mutane da
kirazansu suna zubewa kasa mattatu,wadanda
dama
sukayi yunkurin guduwa ma sai ya rinka binsu
yana
farkewa.Nida Jarumi Hibairu ne kadai zaki nurul
maut ya kasa kusanta farat daya saboda karfin
sihirin tsafin dake jikinmu.Saida zaki nurul maut
ya
gama kashe gaba dayan jama'ar dake tare damu
sannan ya juyo ya fuskancemu nan take
dan'uwana
Hibairu ya firgoce ya ruga izuwa bayan wani
dutse
ya buya,ni kuwa sai na tsaya na fuskanci nurul
maut
a lokacin da zuciyata ta kekashe ga barin jin
tsoron
komai.Koda Sa Maza Gudu yazo nan a zancensa
sai
nayi murmushi kuma na kamu da mamakin yadda
ya tsala karya haka ba tare dayaji kunyata ba.Sa
Maza gudu yacigaba da cewa na take na zare
takobina na afkawa zaki nurul maut suka
ruguntsume da azababben yaki saida muka
kwana
muka yini muna wannan yaki nida zaki nurul
maut sannan na samu da kyar da sidin goshi da
kuma
karfin damtse dana sihirin tsafina na tsargeshi da
takobina na rabashi gida biyu,bayan yayi mini
raunika da yawa ajikina.Koda Jarumi Hibairu
yaga na
sami wannan nasara sai ya rugo da gudu cikin
shammace ya suri rabin jikin zaki nurul maut ya
dubeni ya kyalkyale da dariya yace,kaga yanzu
zan
sami wannan kambun gasa batare danasha
wahalar
banza ba,domin kashe ka zanyi na dauke gawar
zakin na tafi da ita.Koda naji wannan batu sai na
bushe da dariua sannan na murtule fuskata na
dubi
Hibairu nace idan har kaga ka sami nasarar yin
hakan to lallai bana numfashi a doron kasa.Nan
take
muka ruguntsume da azababben yaki a cikin
rabin
sa'amukayi mugun yaki ni da Hibairu harta
kaimu
gayinragas muka zube kasa sumammu,saida
muka
jima a kwance cikin suma sannan muka
farfado.Bisa
dole muka hakura da batun yakar juna muka tako
da
kafafunmu da kyar muka dawo sansani.Wannan
shine iyakar abinda dana san ya faru a can dajin
Sairul.Koda jarumi sa maza gudu yazo nan a
labarinsa sai jama'a suka rude dayi masa tafi
gami
da jinjina,har saida alkalin gasar ya daga hannun
sannan akayi tsit ya dubi Jarumi Hibairu yace
kaji
abinda abokin gasarka ya fada yanzu kaima saika
bamu naka labarin muji domin mu tantance mai
gaskiya a tsakaninku.Koda naji wannan umarni
sainayi gyaran murya sannan na dubi gaba dayan
miliyoyin jama'ar dake cikin gidan sarautar
nace,da
farko dai ina mai rantsuwa da girman darajar
ubangijina abin bautata duk labarin dazan fadi
yanzu
zan fada ne bisa gaskiya.Idan har nayi karya a
cikinsa ina rokon mahaliccina da ya kashe ni
yanzu
take a wannan wuri batare danayi koda taku daya
ba
da kafata.Koda jama'a sukaji wannan batu sai
kowa
ya cika da tsananin mamaki yadda Hibairu yayi
wannan ganganci saboda kowa yayi imani da
abinda
yake bautawa a nahiyar,duk wanda akaji ya
rantse da
abin bautarsa na tabbatar da cewa bazaiyi
karyaba.Nan take Hibairu ya kwashe labarin duk
abinda ya faru a cikin dajin Sairul ya zaiyane shi
gaba daya bisa gaskiya ba tare da yayi kari ko
ragi
ba.Daga karshe sai yayi ajiyar zuciya sannan ya
dubi gabas da yamma,kudu da arewa yace,shin
kun
san waye ya bani gagarumin karfin da har na iya
daga wannan zaki na makashi akan wannan
dutse ya
dagargake?To ba wani bane face UBANGIJIN
MUSULUNCI,Tsaya kuyi tunani da hankalinku da
kuma basirarku.Aduk fadin nahiyar nan gaba
daya
babu wanda yafi sarki Zaldasi karfin sihirin tsafi
amma zaki nurul maut ya gagareshi
kashewa,abinda
ya gagareshi kuma shine za'ace jarumi Alkas ya
iya
dashi?Lallai Alkas makaryaci ne bashine ya
kashe
wannan zaki ba,nine na kashe shi da karfin
ubangijin musulunci,ubangijin daya halicci kowa
da
kowa.Koda Hibairu yazo nan a zancensa sai jikin
gaba dayan miliyoyin jama'ar dake wajen yayi
sanyi
har dukkanin alkalan gasar kuwa,domin kowa ji
yayi
ya gamsu da duk abinda Hibairu ya fada Sa Maza
gudu kuwa saiya rude ya kama ihu yana karya
ta Hibairu.Koda Sarki Zaldasi ya fahimci cewa
gaba
dayan jama'ar dake wajen zasu karbi addininmu
na
musulunci sai ya kwarara uban ihu mai tsananin
firgitarwa ya baiwa dakaru umarni yace su kama
Hibairu su kaishi kurkuku su kulle shi saboda
yazo
da sabon addini.Nan take kuwa sama da dakaru
dubu suka afka masa da nufin su kamashi,amma
sai ya zare takobinsa ya taresu aka ruguntsume
da azababben yaki.
SHIN ZA'A KAMA HIBAIRU A KAISHI KURKUKUN
A KULLE?
WAZA'A BAWA KAMBUN WANNAN GASA
TSAKANIN HIBAIRU DA SA MAZA GUDU?
YAYA KARSHEN WANNAN LABARI DA HIBAIRU
KE BAIWA SU SARKI KAMZAL DA GIMBIYA
ZUHURA ZAI KASANCE?
YAYA KARSHEN GABAR HIBAIRU DA SA MAZA
GUDU ZATA KASANCE?
GIMBIYA MALIKA ITA DA DAN'UWANTA YARIMA
LAHAMAN YAYA KARSHEN TASU GABAR ZATA
KASANCE?
Mu hadu A Littafi na gaba Sa Maza Gudu Littafi
na bakwai(7)An dauko wannan littafi daga shafin www.dlhausanovels.com.ng ku ziyarci shafin na www.dlhausanovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya

Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,

Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan
Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490

A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,

Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu

Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC

Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from www.dlhausanovels.com.ng
You can download more hausa novels there
Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online
It is free we do not charge for uploading novel
Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services

Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us

Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it

Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT
An dauko wannan littafi daga shafin www.dlhausanovels.com.ng ku ziyarci shafin na www.dlhausanovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya

Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,

Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan
Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490

A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,

Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu

Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC

Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from www.dlhausanovels.com.ng
You can download more hausa novels there
Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online
It is free we do not charge for uploading novel
Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services

Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us

Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it

Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXTSA MAZA GUDU!!!
Littafi Na Bakwai:(7)
Part Â
LOKACIN DA AKA RUGUNTSUME DA
AZABABBEN
YAKI TSAKANIN JARUMI HIBAIRU DA DAKARUN
SARKI ZALDASI SAI HANKALIN GABA DAYAN
JAMA'AR DAKE WAJEN YA DUGUNZUMA AINUN
SABODA GANIN IRIN BALA'IN DA YAKE FARUWA
DOMIN IHUN MAZAJE NE YA CIKA DODON
KUNNEN
MUTANE GAMI DA KARAFKIYAR KARAFA.Duk
inda
Jarumi Hibairu yasa gabansa saidai kaga sassan
jikin bil'adama na shawagi a sama suna zubowa
kasa a lokacin daya lazimci yin kabbara da
karfi,babu abinda zai baiwa mutum mamaki fave
ganin irin tsananin jarumtakar Jarumi Hibairu keyi
gami da wani irin masiffan zafin nama kuma
yana
kai sara da suka izuwa ko wace kusurwa ma'ana
gabas da yamma kudu da arewa da kuma sama
da
kasa.Nan da nan ya zamewa dakarun alakakai
suka
rasa yadda zasuyi dashi,shi kansa Jarumi Hibairu
yasan cewa wannan karfi da jarumtaka ya daya
samu bayin kansa bane abu ne kawai daga
Allah.Lokacin da bala'i yakai bala'i sai jama'a
suka
kama guje guke da iface iface,kafin shudewar
dakiku masu yawa filin wajen ya dade babu kowa
face tsirarun fadawan sarki dashi kansa Sarki
Zaldasi sai kuma Sa Maza Gudu da kuma
dakarun
dake yakar Hibairu sai kuma Lasmin wacce ke
tsaye daf da sarki Zaldasi tana kallon yakin da
akeyi cikin tsananin tsoro da fargaba domin gani
take yi kamar a ko yaushe dakarun sarki Zaldasi
zasu iya samun galaba akan Hibairu tunda
SARKIN
YAWA YAFI SARKIN KARFI.Koda jarumi Hibairu
yaga barnar da yakeyi ta yi yawa domin ana ta
yin
asarar dubunnan rayuka ne kuma shi ba burinsa
kenan ba.Babban burinsa shine jama'ar kasar su
fahimci ADDININ GASKIYA Kuma su karbe
shi.Koda
gama aiyana hakan a cikin zuciyarsa saiya
budewa
kansa hanya da karfin tsiya ya fice fit daga cikin
dandazon dakarun kuma ya falfala da azababben
gudu.Koda ganin haka sai Sarki Zaldasi yayi wuf
ya
zare takobinsa ya daka tsalle ya haye kan dokin
yabi Hibairu a guje domin ya kure masa
gudu,nanfa akaga abin al'ajabi domin wani irin
gudu na ban mamaki Hibairu ya rinka yi yana
tserewa dakarun da sarki tamkar gudun
tauraruwa
mai wutsiya.Kafin kiftawar ido Hibairu ya fice
daga
cikin birnin gaba daya ya nausa cikin daji kuma
ya
bace bat tamkar ma bai taba wanzuwa ba.Duk
dakarun da suka biyo shi da gudu saida suka
sare
suka zube kasa magashiyan suna haki kamar
ransu zai fita.Shi kuma sarki Zaldasi saida ya
shafe
sa'a uku yana bin sawun Hibairu da gudu akan
dokinsa har ya zamama cewa dokin nasa ya gaji
ainun ya fadi dashi kasa.Cikin tsananin fushi
sarki
Zaldasi ya mike tsaye zumbur ya dada falfalawa
da
gudu izuwa cikin dajin yana neman Hibairu.Shima
gudu yake yi na ban al'ajabi da karfin sihirinsa na
tsafi amma har ya sake shafe wata sa'a uku ko
alamun Hibairu bai gani ba kuma takun sawayen
Hibairu sun dauke dif tamkar daukewar ruwan
sama.Koda ganin haka sai Sarki Zaldashi ya
tsaya
cak kuma ya durkushe kasa bisa guiwoyinsa biyu
yana haki kamar ransa ne zai fita.Daga can kuma
saiya takarkare ya kwarara wawan ihu cikin
tsananin takaici da bakin ciki.Saboda karfin
wannan ihu nasa saida aka jiyoshi a can cikin
birnin nasa.Al'amarin daya firgita komai da kowa
kenan har dabbobi suka kama neman inda zasu
buya,tsuntsaye kuwa suka rinka tashi daga
shekarsu suna sauya matsuguni.Mutane suka
rinka
kulle kofofi da tagogin gidajensu saboda kasar
birnin ce ta kama girgiza gaba dayanta tamkar
zata
tsattsage duk abinda ke samanta ya rufta
kasanta.Saida sarki Zaldasi ya shafe kusan rabin
sa'a a tsugunne yana faman rusa kukan takaici
da
bakin ciki sannan ya mike tsaye ya juya da baya
ya sake falfalawa da azababben gudu domin ya
isa
cikin garin da wuri.Da shigowar Sarki Zaldashi
Cikn gari saiya rinka ganin mutane majalisa
majalisa suna yin kus kus da zarar anga sarki
Zaldasi sai ayi shiru a zube kasa gabansa ana
kwasar gaisuwa.Koda ganin wannan al'amari sai
hankalin sarki Zaldasi ya dugunzuma ainun yaji
zuciyarsa ta buga da karfi,abinda zuciyarsa ta
raya
masa shine anya kuwa mutane basu fara yin
imani
da addinin Hibairu ba?Koda ya yiwa kansa
wannan
tambaya sai ransa ya baci nan take ya kara
karfafa
gudunsa nan da nan ya isa fada.Da isarsa sai
yasa
akayi shelar taro na gaggawa a fada.Ai kuwa
kafin
cikar sa'a guda fadar ta cika makil da mutanen
gari
har da gaba dayan fadawansa da
dakarunsa.Lokacin da sarki Zaldasi ya mike tsaye
ya karewa fadar kallo gaba dayanta yaga cewa
hatta mata,yara,tsofaffi sun halacci wannan taro
sai
ransa yayi fari,amma kuma daya lura cewa akwai
mutum daya jal wanda bai halacci wannan taro
ba
sai ransa ya baci zuciyarsa ta kama tafarfasa
tamkar zata kone.Bayan sarki Zaldasi ya gama
kallon kowa da kowa sai yayi gyaran murya yace
yaku jama'ar wannan birnin mai albarka,kun sani
cewa fiye da shekaru dubu a wannan kasa tamu
muna tafiyar da addininmu wanda muka gada tun
iyaye da kakanni ba'a tba samu wani shaidani ko
wani takadari dayazo ya la'ance addininmu ba ko
kuma yazo mana da wani sabon addinin daya
fifita
shi akan namu.Yanzu akan wane dalili zamu
yarda
da jarumi Hibairu ya yaudare mu da siddabarunsa
yace damu wai ubangijinsa ne ya bashi sa'a da
nasara har ya kashe zakin daya addabi gaba
dayan
jarumai.Sarakai da bokayen wannan nahiyar kada
ku kuskura ku yarda a hillace ku da siddabaru ko
sihiri a canja muku addini.Ina mai sanar daku
cewa tunda wannan yaro yazo yaci mutuncin
addinin iyayenmu da kakanninmu to ba zamu
kyaleshi ba dole ne mu kamo shi a duk inda ya
buya a cikin dazuzzukan dake cikin kasar nan
domin muyi masa kisan Gilla.Ku sani cewa na
bishi izuwa cikin daji kuma nayi amfani da
dukkan
karfin sihirin tsafina domin na kama shi kona
hallaka shi amma abu ya faskara.
°Abubakar Haleefah Physicist°
Yanzu na yanke hukunci cewa zamu sake hada
runduna ta zaratan mayakanmu wadanda muke
takama dasu mu tafi neman jarumi Hibairu kuma
da zarar mun kamo Jarumi Hibairu zamu zo dashi
har nan fada muyi masa KISAN GILLAH a bainar
jama'a domin ya zama abin misali ga sauran
mutane irinsa masuyin mafarkin kawo mana
sabon
addini.Muna gamawa da wannan shaidanin yaro
zamu baiwa Jaruma Sa Maza Gudu kambunsa na
wannan gasar jarumtaka bisa nasarar daya samu
ta
kashe zaki Maut.Koda gama fadin hakan sai
sarki
Zaldasi ya waiga bayansa ya dubi Sarkin Yakinsa
yace aje a fara shirin fita farautar da zamuyi ta
Hibairu kuma a sanar da duk masana daji da
dukkan mafarautan kasar nan ban daukewa kowa
wannan fita ba.Gama fadin hakan keda wuya sai
Sarki Zaldasi ya sauko daga kan mumbarin da
yake tsaye ya juya ya shige izuwa cikin GIDAN
SARAUTA.Faruwar hakan keda wuya sai jama'a
suka watse kowa ya kama gabansa,mutane suka
tafi izuwa gidajensu jikinsu a sanyaye kai da gani
kasan cewa mutane suna cikin shakku gani da
wasi wasi bisa duk abubuwan da suka faru yau a
gasar jarumtakar da akayi.Lokacin da sarki
Zaldasi
ya shiga cikin gidan sarautar ya isa babban
falonsa
saiya iske Gimbiya Lasmin zaune ita kadai bisa
kujerar daya saba zama fuskar gimbiya a murtuke
take ko kadan babu annuri a tare da ita sannan
kuma idanunta sun ciko da kwallah.Koda ganinta
a
cikin wannan hali sai hankalinsa ya dugunzuma
yazo daf da ita ya zauna kuma ya dubeta cikin
nutsuwa fuskarsa na nuna alamun matukar
damuwa yace yake yata na sani cewa ban yiwa
jarumi Hibairu hukunci na adalci ba amma ki sani
cewa in banyi hakan ba bazan iya tsare mutuncin
addininmu ba wanda muka gada tun iyaye da
kakanin.Koda jin wannan batu sai gimbiya
Lasmin
ta dago kai ta dubi Sarki Zaldasi ranta a bace
tace
na sani cewa zaka iya hana mutane karbar
wannan
sabon addinin na jarumi Hibairu ta hanyar
tsoratar
dasu ta batun azaba ko kisa amma ta yaya zaka
iya goge abin al'ajabin da idanuwansu suka gani?
Ta yaya zaka iya lullube rashin adalcin daka yiwa
Hibairu daga kan idanu da zuciyoyin jama'a,ka
sani cewa bawai kawai anan iya cikin birninka
matsalar ta tsaya ba,a halin yanzu duk kasashen
dake wannan nahiya tamu babu inda labarin
jarumtakar Hibairu bata kai ba bisa abin al'ajabin
da yayi a wannan gasa kuma na tabbatar da
cewar
baza'a rasa wadansu ba daga cikin
sarakunan.Ina
mai tabbatar maka da cewa komai yawanku da
shirinku ba zamu iya kama jarumi Hibairu ba a
wannan farauta tasa ta zaku fita.Koda jin
wannan
batu sai ran sarki Zaldasi ya baci,zuciyarsa ta
kama tafarfasa kamar zata kone saboda tsananin
fishin da yayi bai san sa'adda ya dakawa Lasmin
tsawa ba mai karfin gaske wacce tasa ta firgita
ainun har ta fadi kasa dirshan.Sarki Zaldasi ya
matso daf da Lasmin ya sunkuyar da kansa daf
da
fuskarta yace kada ki fusata ni nayi miki abinda
ban taba yi miki ba a rayuwata wannan shine
karo
na farko dana tabayi miki tsawa irin wannan akan
mulkina,al'adata da addinina zan iya salwantar da
komai nawa na hakura dashi.Yana gama fadin
hakan saiya mike tsaye ya shige izuwa cikin
dakinsa da sauri a fusace ya banko kofar da karfi
karar rufewar kofar ta sake razana gimbiya
Lasmin
taja da baya ta zauna.Saida Gimbiya Lasmin ta
shafe sama da sa'a guda a zaune tana tunani da
nazarin wannan al'amarin cikin bakin ciki,hawaye
na shatata bisa kumatunta,kawai saita mike ta
fice
daga cikin dakin da sauri sauri gudu gudu,duk
inda tazo wucewa sai kaga ana darewa ana bata
hanya da sauri walau kuyangi,borori da
dakaru.Kai
tsaye Gimbiya Lasmin ta nufi inda bargar
dawakai
take,koda mai kula da bargar ya hango gimbiya
Lasmin ta durfafo shi saiya taho gareta da sauri
ya
zube kasa gabanta ya kwashi gaisuwa ya dago
kai
ya dubeta yace ya shugabata lafiya kuwa naga
kinzo nan da kanki alhalin baki taba ba?Koda jin
wannan tambaya sai Lasmin ta dubi Hadimin a
fusace ta daka masa tsawa tace maza ka kamo
mini kosassan doki guda kuma lafiyayye wanda
zan hau yanzu.Sa'adda hadimin yaji wannan batu
sai jikinsa ya kama kyarma ya dubeta cikin
alamun
tsoro yace ya shugabata kiyi mini rai idan na baki
dokin kika hau kika fice daga cikin gidan nan
sarki
kashe ni zaiyi.Koda jin haka sai Lasmin tayi wuf
ta
zare takobin hadimin daga jikinsa ta dota kaifin
takobin akan wuyansa tace yanzu saika zaba
shin
kana so ka mutu ne yanzu yanzu bisa kin bin
umarnina ko kuwa so kake ka mutu bayan kabi
umarnina bisa hukuncin sarki?Har hadimin yayi
yunkurin yayi gardama sai yaji wani mugun zugi
a
wuyansa inda Lasmin ta dora masa kaifi,a
dimauce
yasa hannunsa ya shafi wuyansa ai kuwa sai
yaga
jini,a dimauce yaja da baya sannan ya ruga
izuwa
cikin bargar dawakai ya kamo wani farin
ingarman
doki ya daura masa siddi sannan ya kawo
mata.Bisa mamaki sai kawai yaga gimbiya ta
daka
tsalle sama ta haye dokin ta zabure shi da gudu
ta
nufi hanyar fita daga cikin gidan Sarautar.Abinda
ya daurewa kowa kai a gidan sarautar shine
ganin
gimbiya akan doki tana sarrafashi yadda take so
babu wanda ya taba sanin cewa ta iya doki
domin
yaune karon farko da aka tava ganin ta hau
doki.Nan dai Hadimin ya bita da kallo yana
murmushi bai san sa'adda maganar zuciyarsa ta
fito fili ba yace ai kin cece ni tunda kinyi mini
rauni
a kan wuyana,kin bar min shaidar da zata
kubutar
dani a wajen sarki.Lokacinda Gimbiya ta iso
bakin
kofar gidan sarautar ta isketa a rufe sai dakarun
dake gadin kofar kimanin su arba'in suka taso da
sauri suka sha gabanta.Sarkin kofar ya dubeta
yace ranki ya dade lafiya kika fito a sukwane
haka
ke kadai kuma ga takobi a hannunki?Koda jin
wannan tambaya sai gimbiya ta murtuke
°Abubakar Haleefah Physicist°
fuskarta ta dubi sarkin kofar tace gori akayi min
wai ban taba yin wani abin gwaninta ba shine
nake
son na basu mamaki.Maza ku bude miki kofa na
fita ko kuma nayi amfani da kaifin takobina a
kanku,kun sani cewa duk wanda ya bata mini rai
daga cikinku a bakacin aikinsa.Koda jin haka sai
jikin sarki kofa ya kama rawa ba shiri ya bayar
da
umarni aka bude mata kofa ta fice da gudu tana
mai karawa dokin nata kaimi.Sai bayan kamar
sa'a
guda da tafiyar Gimbiya Lasmin sannan aka farga
cewar bata cikin gidan sarautar.Al'amarin daya
dugunzuma hankalin mahaifiyarta kenan ta ruga
da
gudu izuwa turakar sarki ta sanar dashi.Koda
sarki
Zaldasi yaji cewar gimbiya Lasmin ta fice daga
cikin gidan sarautar sai ya kamu da tsananin
bakin
ciki don haka bai san sa'adda ya takarkare ya
kwarara uban ihu ba.Take Mahaifiyar Lasmin ta
sulale kasa sumammiya saboda tsananin razanar
da tayi,saida kuyangi suka ruga suka dauketa
izuwa cikin turakarta sunayi mata fifita.Nan take
sarki yasa aka kirawo sarkin yaki yace dashi yayi
sauri ya dauki dakaru dari su bazama neman
gimbiya Lasmin sai bayan sunzo da ita zai yanke
hukunci akan wadanda sukayi sakaki har ta fice
daga cikin gidan.Lallai ku dawo kafin dare ya
raba
saboda da asubar fari nake son zamu fita
FARAUTAR JARUMI HIBAIRU.Koda jin haka sai
sarkin Yaki ya risina yace ya shugabana jarumi
Sa
Maza Gudu na tsaye a kofar fada yana son yayi
magana da kai.Dajin haka sai sarki Zaldasi yayi
murmushi yace maza kaje kasa a shigo dashi
gareni kai kuma ka tafi izuwa aikin dana baka
yanzu,sarki yaki ya risina yace

1 Comments On SA MAZA GUDU 1 to 9
avatar
adamu-3

1 year ago

Reply

Masha Allah Allah ya Kara basira Aboki

Please Login or Register in order to submit comment