Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

shiga ta
jaruman duniya zata taimaka mini na kara sanin
iyakar jarumtakata da iya yakina.Kuma zata
samini azamar das zan kara dagewa don
fuskantar babban aikin dake gabana.Abinda nake
so da kai shine kaima ka shiga wannan gasa
kaga
idan kayi nasara koda ni banyu ba shike nan
daukaka dai tana hannunmu.Koda jin wannan
batu sai sadauki Aryan ya sake duban Malika
cikin
alamun tsananin damuwa da mamaki yace,Haba
ya shugabata ta yaya zan iya lashe gasar
jarumtaka alhalin kina cikinta kuma na tabbatar
da cewar kin fini karfin damtse da iya yaki?Koda
jin wannan tambaya sai Malika ta yi murmushi
tace,yakai Aryan ka sani cewa karfin damtse da
iya yaki basu ne kadai ke sawa a sami nasara ba
akwai sa'a da rabo.Koda gama fadin hakan sai
Malika ta karawa dokinta kaimi tayi gaba ta nufi
masarautar garin..

SA MAZA
GUDU
Littafi na uku(3)
Part D
Haka dai su Malika sukayi ta tafiya suna masu
ratsa dazuzzuka,birane da kauyuka har tsawon
kwana goma sha shida sannan suka iso Birnin
Misra.A cikin wannan tafiya sun sha haduwa da
'yan fashi mugayen aljanu da mugayen dabbobin
daji amma dukansu farat daya suke yi
musu,sannan gimbiya Malika ta rike wasiyar
mahaifinta bata taba kulasu wasu yan fashi ba
sai
sai in sun kula su,suna kula su kuwa saidai su
gama dasu su bar gawarwakin a yashe a wajen
su
kara gaba.Da shigowar su Gimbiya Malika cikin
birnin Misra sai suka iske garin ya cika makil fiye
da koyaushe a duk lokutan da suke zuwa a
baya.Fatake,bokaye da yan kasuwa iri iri da kuma
masu fataucin bayi sun cika garin.Al'amarin daya
baiwa su Gimbiya Malika Mamaki kenan har suka
kasa hakuri.nan take sadauki Aryan yaga wani
almajiri a zaune a gefen hanya rike da dan
'ko'kon yana bara.Shidai wannan almajiri ya
kasance saurayi mai kirar sadaukai,amma kuma
kafarsa guda ta hagu da hannunsa na hagu duk a
shanye suke ko sarrafasu baya iyawa.Aryan ya
zura hannu a cikin aljihunsa ya dauko dinare
guda
daya a lokacin daya tsaida dokinsa daf da
almajirin ya jefo masa wannan dinare a cikin
kokon sannan ya dubeshi yace,ba sadaka na
baka
ba,labari nake nema,mene dalilin wannan cikowa
mai yawa a cikin wannan birni?Koda jin wannan
tambya sai almajirin yayi murmushi yace,da
wannan dan kudin kake son kaji babban labari sai
sunyi kadan.Koda jin haka sai Aryan yayi
murmushi ya sake zura hannu cikin aljihunsa ya
dauko dinare guda ya jefa cikin kokon
yace,yanzu
fah?Almajirin yace da saura domin kuwa labarin
da zan baka zai amfaneku a matsayinku na
manyan jarumai daga babbar kasa.Koda jin
wannan batu sai mamaki ya turnuke sadauki
Aryan yace,A cikin ransa anya kuwa wannan
almajiri ba boka bane,yaya akayi yasan cewa mu
jarumai ne daga babbar kasa,kuma menene zai
amfane mu akan labarin da zai bamu.Koda gama
wannan zancen zucin sai Aryan ya sake fidda
dinare uku ya sauko daga kan dokinsa yazo ya
tsuguna a gaban almajirin ya zuba masa dinaren
a cikin kokonsa ya zama guda biyar sannan ya
dafa kafadarsa yace,Abokina bani labari me yake
faruwa a cikin wannan gari?Almajirin ya sanya
hannunsa mai kyan cikin kokon ya kwashi
dinaren
ya zuba su a cikin aljihunsa na wando sannan ya
dubi Aryan cikin nutsuwa yace,Ai sarkin garin
nan
ne ya shirya gasar jarumtaka ta duniya don haka
jarumai da yawan gaske sunzo daga manynan
kasashe,sarakuna sun zo,kuma attajirai yan caca
sun taru domin baje kolunsu a goben da safe a
gidan sarauta.Duk wanda ya lashe wannan gasa
za'a bashi zabin abubuwa guda uku ya dauki
daya ko dai ya auri yar sarki kokuma a bashi
dinare da rakuma dubu ko a bashi mulkin babbar
jaha daga cikin jahohin kasar nan.Koda jin
wannan batu sai Sadauki Aryan ya kamu da farin
ciki nan take ya aiyana a ransa cewa lallai zai
shiga wannan gasa,amma ba don kawai a bashi
wannan dukiya ta dinare ba.Rakuma gudu dubu
saboda in ya koma gida yayi amfani da ita wajen
cika wani babban buri nasa wanda ya gagare shi
cikawa tsawan shekaru.Kawai sai Aryan ya dubi
wannan Almajiri yace Abokina meye sunanka?
Almajirin yace Sunana Hibairu bin Usman.Koda
jin
haka sai Aryan ya mikawa almajiri Hibairu
hannunsa na dama shima ya bashi nasa hannun
suka gaisa.Aryan yace,ina fatan zamu hadu gobe
a fada muyi kallon wanna gasa tare.Hibairu yayi
murmushi yace,tabbasa zamu hadu,koda gama
fadin haka sai Aryan ya mike da sauri yaje ya
hau
dokinsa ya zabure shi da sauri domin ya riski su
Gimbiya Malika saboda sun bashi tazara mai dan
yawa.Da isar Aryan wajen gimbiya Malika sai ta
dubeshi cikin murmushi tace,me ka tsaya yi a
wajen wancan almajirin?Aryan ya maidawa
Malika
martanin murmushin cikin biyayya yace,na
tambaye shi dalilin wannan cikowa mai yawa a
garin nan shine ya labarta mini cewa Sarkin
garinne ya shirya gasar jarumtaka ta duniya.Koda
jin wannan batu sai farin ciki ya lullube Malika ta
dubi Aryan tace,da zarar mun sauka a
masaukinmu kaje ka nemi sarkin kasuwa ka gaya
masa cewa nima ina son na shiga wannan gasa
don haka yaje ya biya mini kudin shiga gasar tun
kafin na yazo gareshi muyi lissafin kudaden.Koda
jin wannan batu sai tsoro da mamaki suka kama
sadauki Aryan ya dubi Malika cikin alamun
tsananin dimuwa yace,Haba ya shugabata ai
girmanki da darajarki tafi gaban shiga wannan
gasa,saidai ki barmu mu wakilceki kada ki manta
cewa gaba dayan manyan sarakuna kina hulda
dasu kuma babu wanda ya san cewa kina da
wannan jarumtaka bai kamata ki tonawa kanki
sirri ba.Koda jin wannan batu sai gimbiya Malika
tayi murmushi tace,idan kida ya sauya dole ne
rawa ta sauya.Ya kai Aryan ka sani cewa ni
yanzu
tun dana baro gida neman yadda zan kare kasata
daga shirin abokan gaba na daina daukar kaina a
matsayin yar sarki,wannan gasa da zan shiga ta
jaruman duniya zata taimaka mini na kara sanin
iyakar jarumtakata da iya yakina.Kuma zata
samini azamar das zan kara dagewa don
fuskantar babban aikin dake gabana.Abinda nake
so da kai shine kaima ka shiga wannan gasa
kaga
idan kayi nasara koda ni banyu ba shike nan
daukaka dai tana hannunmu.Koda jin wannan
batu sai sadauki Aryan ya sake duban Malika
cikin
alamun tsananin damuwa da mamaki yace,Haba
ya shugabata ta yaya zan iya lashe gasar
jarumtaka alhalin kina cikinta kuma na tabbatar
da cewar kin fini karfin damtse da iya yaki?Koda
jin wannan tambaya sai Malika ta yi murmushi
tace,yakai Aryan ka sani cewa karfin damtse da
iya yaki basu ne kadai ke sawa a sami nasara ba
akwai sa'a da rabo.Koda gama fadin hakan sai
Malika ta karawa dokinta kaimi tayi gaba ta nufi
masarautar garin
[5/20, 9:00 AM] princeauwal3156: SA MAZA
GUDU
Littafi na Uku(3)
Part E
Koda gama fadin hakan sai Malika ta karawa
dokinta kaimi tayi gaba ta nufi masarautar
garin,sauran tawagar suka bita da sauri a lokacin
da sadauki Aryan ya bita da kallo kawai yana
tunanin wannan kama da ta gaya masa ta
karshe,ya tabbatar da cewa shifa a rayuwarsa
sa'a da rabo take kaishi ga nasara bisa duk
abinda ya a gabansa amma ba wai jarumtakarsa
bace da iya yakinsa.Kamar yadda gimbiya Malika
ta shirya haka al'amarin ya kasance wato suna
sauka a masaukinsu,sai sadauki Aryan ya tafi
izuwa gidan sarkin kasuwa ya isar da sakon
Gimbiya Malika.Koda sarkin kasuwa yaji cewar
gimbiya Malika zata shiga cikin wannan gasa sai
mamaki da tsoro suka kamashi yayi kamar yaki
zuwa ya biya musu kudin shiga gasar saboda
tsoron kada wani abu ya sami Gimbiya Malika
Sarki Sharkuf ya turo a kamashi,amma da ya
tuna
cewa sadauki Aryuan babban badakaren tane
kuma amintaccenta,lallai da yawunta yake
magana kuma idan yaki bin umarninta zata iya
kwace duk harkokin kasuwancinta dake
hannunsa.Sai ya mike tsaye zumbur ya kama
hannun Aryan yaja shi suka tafi izuwa fada.Da
zuwansu sarkin kasuwa ya biya dinare dubu dari
sannan ya bayar da sunan Gimbiya Malika da
Sadauki Aryan a matsayin jaruman da zasu shiga
gasar.Su kansu masu rubuta sunan sai da suka
dago kai suna yiwa sarkin kasuwa kallon
mahaukaci sabon kamu,amma da suka fuskanci
cewa a cikin hayyacinsa yake lafiyarsa kalau sai
suka kamu da tsananin mamaki.Kashe gari da
duku dukun safiya fadar birnin misra ya cika ta
batse da jama'a ya zamana cewa duk inda
mutum ya hanga babu abinda zai gani face
kawunan bil'adama fululu babu matsakar tsinke
duk wani sarki mai isa gami da koshin lafiya ya
halarci wannan taro haka ma dukkan bokaye da
hamshakan attajirai sun zo,masana tarihi da
masu bincike a wannan rana saida suka tabbatar
da cewa ba'a taba kashe makudan kudade ba a
duk tarukan da kayi a duniya sama dana wannan
rana.Attajiran caca kuwa saida suka kure taskar
kudadensu suka fito dasu gaba daya saboda basu
taba yin cacar data kai wannan daraja ba.Duk
wanda ya cinye gasar ya san cewa idan aka
lissafa
attajiran duniya sai ya sami shiga a cikin mutane
goma.Saida kowa ya gama hallara a cikin filin
gasar sannan aka ji an buga gangar sarauta
alamar cewa ga sarkin Misra nan ya fito zai
shigo
filin gasar.Nan fa kowa ya mike tsaye don
girmamawa a wannan lokaci gimbiya Malika da
sadauki Aryan suna cikin jaruman gasa a tsakiyar
filin sunyi shigar kayan yaki kuma gimbiya Malika
ta rufe fuskarta da hular karfe.Nan take sai ga
Sarkin Misra tare da 'yarsa Gimbiya Zuhura sun
shigo cikin filin gasar.Yaune ranar farko da
mutane suka fara ganin fuskar gimbiya Zuhura
saboda bata taba fitowa daga gidan sarautar ba
tunda aka haifeta.Koda mutane suka yi arba da
Gimbiya Zuhura suka ga irin tsananin kyawun da
Allah ya bata sai suka dimauce suka kama
surutai
da sambatu,da yawa daga cikin matasan dake
wajen kuka suka kama yi saboda nadamar rashin
shiga wanna gasa ta jarumtaka ko don suyo suna
ace sun taba neman auren wanna 'yar
sarki.Hatta
Gimbiya Malika wacce take ganin kamar babu
mace mai kyanta a gaba daya wannan fili saida
ta
raina kanta ta gamsu a cikin zuciyarta cewa ita
mummuna ce akan gimbiya Zuhura.Tun da
sadauki Aryan ya shigo cikin wannan filin gasar
yake ta ware idanu yana kalle kalle da waige
waige ko zaiga Almajiri Hibairu a cikin yan kallo
amma ko mai kama dashi bai iya ganiba.Koda
Aryan ya juya ya fara kallon 'yan uwansa
jaruman
gasar sai zuciyarsa ta buga da karfi ya kamu da
tsananin mamaki.Ba komai ne ya haddasa hakan
ba face ganin almajiri Hibairu a cikin shigar yaki
kuma a tsaye daram cikin koshin lafiya babu
tauyewar hannu ko kafa.Suna hada ido sai
Hibairu yayi masa murmushi kuma ya dago masa
hannu,cikin alamun takaici Aryan ya ciza yatsa
yace,lallai wancan almajirin ya raina mini
hankali,ashe ba nakasasshe bane amma na dauki
kudina mai yawa na bashi sadaka,ai kuwa sai ya
biya ni kudina,kuma Allah yasa mu hadu dashi a
cikin wannan gasa dukan tsiya zanyi masa nayi
masa lilis amaimakon kudi na daya ci.Aryan yana
cikin yin wannan tunani ne yaji alkalin gasa yayi
gyaran murya a lokacin da filin gasar yayi tsit
kamar mutuwa ta gifta.Kawai sai Alkalin gasar
yace,Jaruman gasa na farko sune Gimbiya Malika
daga Birnin Madinatul Zauwara zata kara da
Jarumi Hibairu daga Birnin Nurul Islam.Koda jin
haka sai mamaki ya turnuke sadauki Aryan kuma
ransa ya baci bisa jin cewar wai wannan
makaskancin jarumi kuma almajiri shine zai
fafata
da gimbiyarsa.Su kuwa 'yan kallo da sauran
manyan mutanen dake filin gasar zazzaro idanu
sukayi saboda bisa jin cewa Gimbiya Malika 'yar
sarki Sharkuf ta shiga wannan gasa.Nan take
Jarumi Hibairu da Gimbiya Malika suka fito
tsakiyar filin gasar suka fuskanci jina
kowannansu
na rike da takobi da garkuwa,kawai sai ji sukayi
an buga gangar fara gumurzu.Dukaninsu sai suka
rugo da gudu kan juna suka runguntsume da
azababben yaki mai mutukar ban al'ajabi da ban
tsoro.
WAYE ZAI SAMI NASARA A WANNAN GASAR
JARUMTAKA TSAKANIN JARUMI HIBAIRU DA
GIMBIYA MALIKA?
WANE IRIN GAGARUMIN KARFIN DAMTSE DANA
SIHIRIN TSAFI YARIMA LAHAMAN ZAI SAMU
KUMA
IDAN YA HADU DA MALIKA ME ZAI FARU?
SHIN MALIKA DA SARKI HILAIRU ZASU KARBI
SOYAYYAR JUNA?YAUSHE NE GIMBIYA MALIKA
ZATA CIKA ALKAWARINTA TA MAYAR DA SARKI
HILAIRU KASARSA YA KOMA KAN KARAGARSA
KUMA A GYARA BIRNINSA?
TSAKANIN GIMBIYA MALIKA DA YARIMA
LAHAMAN
WAYE ZAI HAU KAN KARAGAR BIRNIN
MADINATUL
ZAUWARA YA KASANCE YA GAJI GIDAN
SARAUTAR?
MU HADU A WANNAN LITTAFI SA MAZA GUDU
LITTAFI NA HUDU DON JIN YADDA ZATA KAYA.An dauko wannan littafi daga shafin www.dlhausanovels.com.ng ku ziyarci shafin na www.dlhausanovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya

Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,

Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan
Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490

A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,

Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu

Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC

Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from www.dlhausanovels.com.ng
You can download more hausa novels there
Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online
It is free we do not charge for uploading novel
Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services

Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us

Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it

Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT
An dauko wannan littafi daga shafin www.dlhausanovels.com.ng ku ziyarci shafin na www.dlhausanovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya

Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,

Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan
Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490

A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,

Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu

Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC

Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from www.dlhausanovels.com.ng
You can download more hausa novels there
Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online
It is free we do not charge for uploading novel
Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services

Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us

Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it

Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT
SA MAZA GUDU
Littafi na Hudu (4)
Part A
Lokacin da Gimbiya Malika da Jarumi Hibairu
suka
ruguntsume da azababben yaki sai gaba daya
jama'ar dake cikin filin gasar suka kamu da
tsananin
mamaki da al'ajabi saboda basu taba ganin
gumurzu irin saba.Gaba daya sauran jaruman
gasar
ma saida suka tsorata da ganin wadannan
jaruman
biyu,domin basu taba ganin mutanen da suka iya
sarrafa takobi ba,kuma suna yaki ne da matukar
zafin nama na gaban kwatance tamkar jikinsu
bana
jini da tsoka bane.Da farko saida suka shafe
kusan
rabinsa'a suna kaiwa junansu sara da suka
kowannensu na iya karewa gami da maida
martani
amma Jarumi Hibairu yafi Malika iya yaki,zafin
nama
da iya sarrafa takobi.Domin wata irin gagarumar
jarumtaka da bajinta ya rinka yi yana shawagi a
samanta kamar tsuntsu,kuma ya zamana cewa
da
kyar take iya kare saransa.Tun tana iya karewar
ma
da kyar har ya zamana cewa ta fara durkushewa
kasa saboda gajiya,kawai sai gani akayi Hibairu
ya
buge takobin Malika daga hannunta ta fadi kasa
can
gefe daya kuma ya tsirata da tasa takobin yana
mai
saita makoshinta kuma yana murmushi.Nan take
filin ya rude da shewa a ka kama yiwa jarumi
Hibairu tafi da jinjina.A wannan lokaci gaba
dayan
attajiran cacac mutum daya ne jal ya zabi
Hibairu a
matsayin gwaninsa don haka koda a kaga ya
sami
wannan nasara sai kowannensu ya kamu da
tsananin mamaki gami da nadamar rashin
zabarsa,gashi a dokarsu tayin wannan caca babu
damar mutum ya sauya jarumi face an gama
zagayen farko na gasar.A bangaren sadauki
Aryan
kuwa tunda yaga Hibairu Yafi Malika iya yaki da
jarumtaka sai jikinsa yayi sanyi mamaki ya
turnukeshi ainun,bai san sa'adda ya kama yin
zancen zuci ba yana mai cewa a ransa duk
yadda
akayi BASAJA ne ya shiga wannan gasa ta
jarumta
saboda wata bukata tasa dabam,amma badon
ladan
daza'a biya mutum ba,wata kila so yake ya
mallaki
wannan zukekiyar buduwar 'yar sarki Misra wato
Gimbiya Zuhura.Yana cikin wannan tunani ne
yaga
wani jarumin gasar ma'abocin kyau da kwarjini
ainun
yazo kusa dashi ya tsaya fuskarsa cike da
murmushi
kawai sai jarumin ya dubeshi yace,amma
uwargidanka Gimbiya Malika ta bani Kunya domin
yadda nake jin labarin jarumtakarta bai kamata
ace
lokaci kankani haka har an sami galaba a kanta
ba.Koda jin wannan batu sai Sadauki Aryan ya
fusata ya dubi bakon jarumin cikin alamun fushi
yace,in banda abinka ai idan ana ta barawo dole
ne
ayi ta mabi sawu,shin bakaga irin gagarumar
jarumtakar da abokin gwamin naya keyi ba
ne,tunda
dai kana cikin gasar ai zaka kara dashi in yaso
zan
gani ko kaima bazaka bamu kunyar ba.Koda jin
wannan batu sai bakon Jarumin ya bushe da
dariya
yace,hakika ka fadi gaskiya yakai Sadauki
Aryan,domin gani ya kori ji,lokaci zai bambance
komai.Koda gama fadin hakan sai Jarumin ya
bar
inda Aryan ke tsaye ya kara matsawa gaba a
lokacin
da Aryan ya bishi da kallo cikin tsananin
mamaki.Ba
komai ne ya bashi mamaki ba face yadda akayi
wannan bakon jarumi ya san sunansa,abu na biyu
kuma daya lura dashi dangane da jarumin shine
yana kama da sarki Hilairu mutuka.Anya kuwa
wannan ba 'dan uwan sarki Hilairu bane?Kash ina
ma ace bana cikin jaruman gasar nan da nan da
nan
zan ruga naje na kirawo sarki Hilairu yaga mai
kama
dashi,abu na uku daya kara daurewa sadauki
Aryan
kai shine wai shin me yasa tunda ya shigo cikin
garin nanne abubuwa suka zuwar masa kamar
almara?Da farko ya hadu da jarumi Hibairu a
matsayin nakasasshe kuma almajiri amma yanzu
gashi a matsayin lafiyayye sannan kuma yanzu
ya
hadu da wani bakon jarumin wanda ko a mafarki
bai
taba ganin mai kamarsa ba amma gashi yasan
shi
harma ya fadi sunansa dana Gimbiya
Malika.Lokacin
da Gimbiya Malika taga Jarumi Hibairu yasa ta
durkushe kasa a gabansa har ma ya kade
takobinta
daga hannunta sai ta cika da tsananin mamaki
kuma
ranta ya baci ainun saboda in banda Mahaifinta
Sarki
Sharkuf babu wani jarumi daya taba samun irin
wannan nasara farat daya a kanta ba.Cikin
alamun
tsananin fushi Gimbiya Malika ta mike tsaye
zumbur
tana mai gyara tsayuwarta kuma ta dunkule
hannayenta biyu alamar cewa a shirye take a
gwada
'yar gwanji.Koda ganin haka sai Jarumi Hibairu
yayi
murmushi kuma ya mayar da takobinsa cikin kufe
ya
dubeta yace,yake wannan 'yar sarki zaifi kyau ki
sallama akan cewa na lashe wannan gasa a kanki
saboda bana son ko kadan na lalata wannan
kyakkyawan jiki naki da naushi,kiyi duba izuwa ga
masoyinki can Sarki Hilairu ya kura mana
idanu,ga
dukkan alamun hankalinsa a tashe yake baya son
muyi wannan fafatawa.Koda Hibairu yazo nan a
zancensa sai Gimbiya Malika ta cika da tsananin
mamakin Hibairu ta ayyana a cikin ranta
tace,anya
kuwa wannan mutum ne?Ina ganin dai aljani ne
ya
shigo cikin mutane in ba haka ba ya za'ayi yasan
ko
ni wacece har ma ya san abinda ke cikin
zukatanmu
nida Sarki Hilairu.Ai da ganin wannan tsananin
kyawin nasa ma kasan cewa ba mutum bane
aljani
ne.Duk da haka sai na jarraba karfin damtsena
akan
nasa koda kuwa zai cutar dani domin ta hakane
ma
zan dada ganewa idan mutum neshi.Koda gama
fadin hakan sai Gimbiya Malika ta ruga izuwa kan
Jarumi Hibairu,koda ya rage saura baifi taku uku
ba
su hadu sai ta daka tsalle masa ta kai masa
mugun
duka a kirjinsa.Cikin bakin zafin nama ya
kaucewa
dukan nata kafarta ta naushi iska,kawai sai ta
wuntsila jikinta ta kawo masa wani dukan da
daya
kafar tata akan fuskarsa.Kawai sai ya cafi kafar
tata
da hannun yayi hajijiya da ita a sama tamkar yar
tsana ce a hannunsa yayi kamar zai fyada ta da
kasa
a lokacin da hankalin kowa ya dugunzuma a filin
saboda indai ya fyadata da kasa zata iya
kakkaryewa
koma ta rasa rayuwarta gaba daya.
Tuni a wannan lokaci kowa ya mike tsaye an
bude
baki ana jimami kowa ya saddakar da cewa
Gimbiya
Malika ta mutu,ba zato ba tsammani sai akaga
Jarumi Hibairu ya ajiyeta a hankali ya juya da
baya
yana mai daga hannayensa sama alamar cewa
yayi
nasara,ai kuwa sai filin gurin ya rude da shewar
jama'a aka kama yi masa tafi da jinjinaCikin
sanyin
jiki gami da mamaki Gimbiya Malika ta mike
tsaye ta
koma cikin jaruman gasa ta tsaya.Ba komai ne
ya
bata mamaki ba face abu biyu,abu na farko shine
bata taba gumurzu da jarumin data kasa taba shi
ba
ko kaishi kas ba face Jarumi Hilairu,abu na biyu
kuma shine tayi matukar mamakin dalilin da yasa
Jarumi Hibairu yaki kwalata da kasa?Shin
tausayinta
yaji a matsayinta na 'ya mace ko kuwa dai akwai
wani dalilin dabam?Amsar da Malika ta kasa
baiwa
kanta kenan,a wannan filin gasa gaba daya babu
wanda yafi Sarki Hilairu farin ciki bisa gani cewa
ba'a yiwa Malika rauni ba,shi kuwa Sadauki
Aryan
hankalinsa ne ya dugunzuma ainun bisa ganin irin
tsananin jarumtakar da Jarumi Hibairu wanda bai
taba zaton cewa nada karfi haka.Nan take yaji
zuciyarsa ta karaya a cikin wannan gasa bisa
ganin
yadda Gimbiya Malika ma ta wulakanta duk da
tsananin jarumtakarta da kuma tunanin yana mai
cewa a cikin ransa anya muwa zan iya tsianana
wani
abin arziki a cikin wannan gasa.A can bangaren
da
Sarkin Misra ke zaune tare da sauran abokansa
manyan sarakai babu abinda suke tattaunawa
face
maganar Jarumi Hibairu saboda kasancewarsa
bakon jarumin da babu wanda ya sanshi a
nahiyar.Ita kuwa sarauniyar kyawawa wato
Gimbiya
Zuhura tun a karon farko da idanunta sukayi arba
da
Jarumi Hibairu sai ta kasa sukuni da nutsuwa
domin
nan take taji zuciyarta ta kama bugawa da
karfi.Lokacin dataga irin tsananin jarumtakar da
Allah ya bashi kuma ta kare masa kallo taga irin
kyawun fuskarsa da kyawun surar jikinsa tamkar
shiyayi kansa sai taji ta kamu da matukar son
sa,al'amarin dayayi matukar bata tsoro da
mamaki
kenan,domin ko a mafarki bata taba zaton cewa
zatayi soyayya ba.Komai kyan saurayi da iya
adonsa
komai matsayinsa idan yazo wajen Gimbiya
Zuhura
da sunan soyayya sai ya wulakanta kuma ya
raina
kansa,har kirari ake yiwa Gimbiya Zuhura da Sa
Maza Gudu.Sau dayawa idan dan sarki yazo
wajenta,to ko duniya za'a bashi gaba daya bazai
yarda ya sake dawowa ba saboda shi yasan irin
wulakancin daya gani.A kullum Gimbiya Zuhura
tana
yiwa mahaifinta kuri da alwashin cewa ita fa har
yanzu bata ga wani 'da namiji ba wanda ya
burgeta
bare ta bashi soyayya.Bayan Jarumi Hibairu ya
lashe
gasar jarumta akan Gimbiya Malika wacce ta
koma
cikin jaruman gasa ta tsaya ta barshi shi kadai a
tsaye a tsakiyar filin gasar jama'a nayi masa
shewa
gami da jinjina,attajirin daya zabe shi a matsayin
gwaninsa na caca yana tsalle da murna sai
alkalin
gasarya shigo cikin tsakiyar filin gasar ya
tsaya.Faruwar hakan keda wuya sai filin gasar
yayi
tsit yamkar babu mutane a cikinsa domin a
saurari
abinda alkalin gasar zai fada,nan take kuwa yayi
gyaran murya sannan yace,yaku jama'a kamar
yadda
kuka gani da idanunku a zagayen farko Jarumi
mai
suna Hibairu daga Birnin Nurul Islam ya lashe
gasa
a kan Gimbiya Malika daga Birnin Madinatul
Zauwara.Bisa ka'idar wannan gasa duk Jarumin
dayayi nasara a karon farko sai ya sake fafatawa
da
mutum biyu,idan yayi nasara to ya haye zagayen
farko na wannan gasa saura zagaye biyu cakal a
gabansa.Koda jama'a sukaji wannan batu sai
suka
rude da shewa sannan alkalin gasar ya daga
hannu
aka sakeyin tsit yace,yanzu Jarumi Hibairu zai
kara
da Jarumi na biyu wanda ake kira da Ramzan
daga
Birnin Sin.Koda jin wannan suna sai gaba dayan
filin
ya rude da shewa take da yawa daga cikin yan
kallon suka fara tausayin Jarumi Hibairu don sun
tabbar dacewa ajalinsa ne yazo.Shidai Jarumai
Ramzan ya kasance narkeken kato mai katon ciki
gashi dogo kuma gashi mai kauri da kibar
gaske,masana yaki sun tabbatar da cewa karfin
saransa da nauyinsa yakai nauyin giwa guda
kuma
takobinsa lafceciyace mai fadin gaske gami da
kaifin
tsiya tamkar zabira don haka duk abinda ya sara
da
ita ko bishiya ce kuwa sai ya rabata gida biyi
komai
kaurinta idan kuwa ya matse gadon bayan
mutum
da hannayensa biyu saidai a rinka jin karar
karyewar
kasusuwansa haka kuma idan ya zauna akan
cikin
mutum saidai aga mutum na aman jini ta hanci
da
baki take zai sheka barzahu.A tarihin gasar
jarumtakar da akeyi a ko ina a duniya indai ya
shigeta shi yake karbar Kambu.Batare da bata
lokaci
ba Jarumi Ramzan ya shigo cikin filin gasar yana
taku dai dai karfin takun sawayen nasa ne suka
haifar da karamar girgizar kasa gami da tashin
kura,shi Kansa Hibairu sai daya dan tsorata da
yayi
arba da wannan narkeken katon domin da farko
ma
ya zata bishiya ce tazo gabansa saboda take ya
zama dan wada a gabansa.Abind aya fara daure
masa kai shine ta yaya wannan mutum yake iya
rayuwa a cikin sauran al'umma? Babu wata

1 Comments On SA MAZA GUDU 1 to 9
avatar
adamu-3

1 year ago

Reply

Masha Allah Allah ya Kara basira Aboki

Please Login or Register in order to submit comment