Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ita kuma ya
takarkare ya kwarara Kabbara mai karfi,Hatta
jarumi Sa maza gudu baisan sa'adda ya fadi
kasa
ba Saboda tsananin razana da mamaki bisa
ganin
irin gagarumin karfin da Hibaiur ya samu wanda
ko
a tarihin SADAUKAN DUNIYA bai taba jin mai irin
saba.Nan take fadar ta yamutse gaba dayan
dakarun sarki Zaldasi suka zare takubbansu suka
afkawa Hibairu aka ruguntsume da azababban
yaki.Shidai Hibairu sarkokin dake hannayensa ne
suka zamo makamansa ya rinka kare sara yana
kai
naushi dasu,bama mutum ba ko dirkar gini
Hibairu
ya nausa take take karyewa ta zube
kasa.Wohoho
bala'i da masifa ba'a sa musu rana tabbas duk
wanda kaji yana cewa Allah ya kawo yaki to
baisan
shi ba domin kuwa shi yaki masifa ce wacce ke
shafar kowa da komai.Sakamakon rushewar da
gidan sarautar keyi diraka manya manya na
fadawa
kan gidajen birnin sai suma sauran gidajen
mutune
suka kama rushewa sai gashi mutane maza da
mta yara da manya na hallaka a cikin
gidajen.Hakan ne kuma yasa haddasa gagarumar
girgizar kasa saboda tun fitowar manyan dirkokin
gini daga cikin karkashin kasa bai bama mutane
ba
hatta dabbobi da tsuntsaye guje guje suka
kamayi
suna neman tsira amma tsiran ya gagara mutuwa
ce kawai ke cin kasuwarta.A wannan lokaci da
kyar
sarki Zaldasi da Jarumi Sa Maza Gudu suka ruga
izuwa kan wani katon mumbari suka zare
takubbansu suka zuba ido suma kallon yadda
karshen gumurzun Hibairu zai kasance da
dakarun
sarki.Babban abinda yafi daga musu hankali
shine
Hibairu cigaba yake da ragargazar dakarun domin
duk inda yasa gabansa saidai kaga maza na
zubewa kasa tamkar ana sassabe a gona.Koda
ganin haka sai sarki Zaldasi ya dubi Sa maza
gudu
cikin alamun karayar zuciya yace idan muka
cigaba
da zuba ido nan da kankanin lokaci Hibairu zai
gama da gaba dayan dakarunka.Bamu da wani
zabi wanda yafi mu hada karfi da karfi mu yaki
Hiabairu mu jarraba sa'armu akansa,amma
tabbas
wannan siddabarun nasa yafi gaban sanina da
tunanina.Koda gama fadin hakan sai duk su
biyun
suka daka tsalle sama daga kan mumbarin da
suke suka dira a gaban Hibairu suka rufeshi da
sara da suka amma sai sukaga yana tare dukkan
hare haren nasu cikin bakin zafin nama da
jarumtaka taban al'ajabi yana mai maida musu da
martani.Nanfa aka rasa daya daga cikinsu wanda
zai iya koda shafar jikinsa kuwa duk da irin
tsananin jarumtakarsu da iya yakinsu sai gashi
da
kyar suke iya kare naushinsa da bugunsa.Ana
cikin hakane Hibairu ya shammacesu ya daka
tsalle sama ya doki fuskokinsu da
kafafunsa.Saboda karfin wannan bufu dayayi
musu
saida kowannensu yayi katantanwa a sama sau
uku sannan suka fado kasa suka kife da rub da
ciki jini na yoyo ta cikin hancinsu da bakinsu a
cikin tsananin galabaita.Adaidai wannan lokaci
ne
ragowar tsirarun dakarun sarki Zaldasi da suka
rage a filin dagar suka yarda makamansu sukayi
saranda bisa ganin sarkinsu zube a kasa
wanwar.Kawai sai Hibairu ya hango Gimbiya
Lasmin ta fito da gudu daga cikin gidan sarautar
ta
nufo inda yake kuma gashi kasa na cigaba da
girgiza tana zabtarewa gidaje na cigaba da
rushewa tana neman ta hallaka.Koda sarki
Zaldasi
ya dago kai ya hango yarsa ta nufo inda suke sai
yayi lambo saida tazo daf dashi sannan ya mike
tsaye zumbur ya shakota ya dora kaifin takobinsa
akan wuyanta ya dubi Hibairu yace idan ka
sakeyin
wani yunkuri saina kasheta.Koda jin haka sai jikin
Hibairu yayi sanyi ya tsaya cak a inda yake ita
kuwa gimbiya Lasmin saita dubi Hibairu tace
kada
ka yarda dashi karye yakeyi bazai iya kasheni ba
saboda nice kadai yarsa a duniya kuma babu
abinda yake so sama dani.Kawai kazo ka kashe
shi tunda nasan cewa har abada bazai karbi
addinin gaskiya ba kuma zai taba daina zalunci
ba.Koda jin haka sai sarki Zaldasi ya yanki cinyar
Lasmin da takobinsa wajen ya dare jini yayi
tsartuwa ta kurma ihu sakamakon tsananin zafin
da taji.Sarki Zaldasi ya kara shake mata wuya da
hannaunsa kuma ya bushe da dariya sannan
yace
ke yarinya ashe kin manta da abinda na gaya
miki
kenan a baya cewa zan iya hakura da komai
nawa
akan na rasa karagata,raina da addinina.Na
rantse
da darajar iyayena idan Hibairu yayi wani yunkuri
saina kasheki.Ki sani cewa ke idan na rasaki zan
iya samun wata yar anan gaba,raina,mulkina da
addinina kuwa idan na rasasu a yanzu bazan
sake
samunsu ba,kai jarumin jarumai maza ka mike
tsaye da sauri ka yiwa wannan babban makiyi
namu kisan gilla a gaban idanuna.Koda jin haka
sai Sa Maza Gudu ya mike tsaye zumbur da
dukkan karfinsa yana mai kwarara uban ihu gami
da goge jinin dake yoyo a hancinsa.Kawai saiya
daga takobinsa sama ya rugo izuwa inda Hibairu
ke tsaye.Kaico hakika SO masifa ne,duk da cewa
Hibairu yasan cewa ga sa maza gudu nan ya
durfafoshi zai hallakashi ko waigawa bayansa
baiyi
ba kawai saiya kurawa Gimbiya Lasmin idanu
yana
yi mata kallon karshe domin ya saddakar da
rayuwarsa don ceton tata,ita kuwa Lasmin a
lokacin data kurawa Hibairu idanu hawaye ne
yake zubo mata saboda tuni ta gama aiyana
abinda
zatayi don ceton rayuwar Hibairu ta hanyar
sallama
tata rayuwar.Ashe tuni Lasmin ta kula da cewa
bayansu inda suke tsaye ita da sarki Zaldasi rami
ne mai zurfi wanda ya samu sakamakon girgizar
kasar da akayi kuma cikin can rami duwatsu ne
da
karyayyun itatuwa wanda indai mutum ya fada
kansu dole ne ya hallaka.Shi kuwa Hibairu abinda
ya daure masa kai shine Lasmin Murmushi takeyi
masa duk da cewar tana zubar da hawaye a
idanuwanta.Koda ya rage saura baifi taku biyar
ba
Jarumi Sa Maza Gudu ya riske Hibairu sai
gimbiya
Lasmin ta danno mahaifinta baya da dukkan
karfinta nan take duk su biyun wato ita da sarki
Zaldasi suka fada cikin wannan rami suna masu
tsandara uban ihu,adaidai wannan lokaci ne sa
maza gudu ya dako tsalle sama ya daga
takobinsa
sama da nufin ya sare kan Hibairu amma dayaga
masoyiyarsa ta fada cikin wannan rami tare da
mahaifinta saiya kasa aiwatar da nufinsa bai san
sa'adda ya saki takobinsa ba ta fado kasa shima
ya diro kasa ya kama ihu ya fashe da
matsanancin
kuka.Shima Jarumi Hibairu baisan sa'adda ya
kwala ihu ba kuma ya rugo da gudu izuwa bakin
ramin yana lekawa kasan ramin saiya hango
gimbiya Lasmin da sarki Zaldasi a mace dirakan
gini sun soke kirazansu.Kawai sai Hibairu ya
durkushe kasa bisa guiwoyinsa ya fashe da
matsanancin kuka,jarumi sa maza gudu ya
karaso
bakin ramin dakyar koda ya leka ya hango gawar
Lasmin saiya sake kwala ihu a karo na biyu kuma
ya fashe da kuka ya zamana cewa duk su biyun
suna tayin kuka ba sassauci tamkar ba zasu
daina
ba.(Tsananin Tausàyi Nima Yasani Hawaye)Saida
suka shafe sama da sa'a guda suna kuka
gami da begen masoyiyarsu sannan jarumi sa
maza gudu ua dago kai ya dubi Hibairu cikin
tsananin kiyayya da bakin ciki yace yakai abokin
gaba kayi sani cewa masoyiyata ta sallama
rayuwarta ne domin tserar da taka wannan ya
nuna cewa tana kaunarka fiye da kowa da komai
a
wannan duniya.Tabbas ka dasa mini bakin cikin
da
babu abinda zai gusar mini dashi har abada,daga
nan har izuwa karshen rayuwata,ka sani cewa
yanzu ne wutar gaba a tsakanina dakai zata fara
ruruwa kuma babu wani ruwa dazai iya kasheta a
cikin wannan duniya komai yawansa da
karfinsa.A
yau babu sauran yaki a tsakanina dakai zan jira
wani lokacin daya dace anan gaba idan mun
sake
saduwa.Ka sami nasarar yada addininka a
wannan
birni amma nayi murna daya kasance a dalilinka
jama'ar wannan gari sun rasa dubunnan rayuka
ba
zasu taba mancewa dakai ba.Koda gama fadin
hakan sai jarumi sa maza gudu ya mike tsaye a
bakin ramin ya sake kurawa gawar Lasmin idanu
yana mai cigaba da zubar da hawaye izuwa
tsawon
yan dakiku daga can kuma saiya juya ya nufi
hanyar fita daga cikin birnin gaba daya.Nanfa
Hibairu ya bishi da kallo harya kule ya bace
masa
da gani.Sannan shima ya juya ya kurawa gawar
Lasmin idanu.Nan take hawaye ya subuto masa
ya
daga kansa sama yace ya Allah ga Lasmin nan
baiwarka ce kuma ta karfi addininka kafin
mutuwarta amma gashi ta kashe kanta domin
ceton tawa rayuwar.Allah kaine maiyin rahama
ga
bayinsa,kai kasan irin hukuncin da zakayi
mata,ka
gafarta mata da irin gafararka.Koda gama fadin
hakan sai Hibairu ya mike tsaye ya nufi inda
mutane suka nutse a cikin kasa ya taimaka
wajen
tono su saida dare ya raba har gari ya waye ana
tonosu daga cikin karkashin kasa.Wasu a mave
ake tonosu wasu kuma a kakkarye wandasu
dauke
da raunika.Bayan an kammala wannan aiki ne an
binne gawarwaki kuma an yiwa marasa lafiya
magani sannan jarumi Hibairu ya tara gaba dayan
mutanen birnin ya kadamar da addinin musulunci
a kofar gidan sarautar.Daga wannan rana Hibairu
ya zauna a birnin har tsawon wata uku yana
koyar
da mutane ibada gami da ilmin addinin
musulunci.A tsawon wannan lokaci ne mutanen
birnin Misra suka gane cewa ashe da a cikin
muguwar rayuwa suke ta bakin jahilci da zalunci
da kuma kazanta suka gane cewa addinin
musulunci shine addinin dayafi dacewa da
dukkan
al'ummar duniya saboda adalcinsa.A lokacin ne
kuma jama'ar suka shaku ainun da jarumi Hibairu
suka kaunace shi ainun don haka sai suka bukaci
daya zauna ya zama sarkinsu.Koda jin wannan
batu sai Hibairu ya kwashe tarihin rayuwarsa ya
zaiyane musu da kuma dalilin da yasa ya baro
kasarsa da iyayensa.Bisa dole mutanen birnin
Misra sukayi bankwana da Hibairu suna kuka
shima yana kuka suka rakoshi har karshen gari
ya
hau dokinsa ya nausa cikin daji suna kallonsa har
saida ya bace musu da gani.Lokacin da Jarumi
Hibairu yazo nan a cikin labarin da yake baiwa
sarki Kamzal da 'yarsa Gimbiya Zuhura saiya duk
su biyun suna zubar da hawaye saboda
tausayinsa
gami da abin al'ajabin dake cikin labarin.Sai
bayan
kimanin dakiku arba'in da biyar sannan sarki
Kamzal ya dago kai ya dubi Hibairu a lokacin da
yayi ajiyar zuciya sannan yace yakai wannan
babban jarumi kayi sani cewa wannan labari naka
dana ji izina ne ga dukkan sarakunan duniya da
kuma duk wanda yake ja da ubangijinka da kuma
addininka.Tabbas nayi imani da ubangijinka kuma
lallai zan kaddamar da wannan addinin naka a
birnina bayan an kammala wannan gasa dana
shirya,yanzu dai kaga yadda kukayi ragas da
jarumi sa maza gudu ya zamana cewa saura kiris
duk ku biyun ku rasa rayukanki.Shin kana ganin
cewa nan gaba zaka sami nasara a kansa?Koda
jin
wannan tambaya sai gimbiya Zuhura tayi caraf ta
tari numfashin sarki Kamzal tace haba yakai
Abbana idan har kana yin shakka akan nasarar
Hibairu akan sa maza gudu tamkar kana shakku
ne
a kan addininsa da ubangijinsa.Ni yanzu inaso na
yi wata magana da Hibairu inda bazaka damuwa
ba.Koda jin haka sai sarki Kamzal yayi murmushi
kawao saoya mike tsaye ya basu wuri ba tare da
uffan ba.Koda Gimbiya Zuhura taga mahaifinta
ya
fice daga cikin turakar ya barsu su biyu kadai
saita
dubi Hibairu cikin murtuke fuska tace menene
tsakaninka da gimbiya Malika?Koda jin wannan
tambaya sai Hibairu yayi murmushi yace kwantar
da hankalinki Gimbiya ki ajiye kishinki a gefe
daya
ki sani cewa babu komai a tsakanina da Malika
face tana bukatar kawai na koya mata yaki
domin
ta kare kanta daga sharrin dan uwanta Yarima
Lahaman wanda ke kokarin ganin bayanta da
kuma
bayan Masoyinta.Koda jin wannan batu sai
mamaki
ya turnuke Zuhuta tace wanene wannan masoyin
nata kuma me yasa dan uwanta Yarima Lahaman
yake son ganin bayansu?Sa'adda Hibairu yaji
wannan tambaya sai yayi doguwar ajiyar zuciya
sannan yace labari ne mai tsawo amma kiyi mini
hakuri yanzu ki bari sai bayan an gama wannan
gasar jarumtaka sannan zan baki labarin.Koda
gama fadin hakan sai Hibairu ya yunkura da
nufin
ya mike tsaye ya fice daga cikin turakar amma
sai
Zuhura tayi wuf ta ruko hannunsa ta zaunar
dashi
kasa tace ai ban sallameka ba harda kake son ka
tafi.Inason ka sani cewa nice zan maye maka
gurbin marigayiya Gimbiya Lasmin don haka
inason kayi mini wani alkawari guda daya.An dauko wannan littafi daga shafin www.dlhausanovels.com.ng ku ziyarci shafin na www.dlhausanovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya

Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,

Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan
Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490

A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,

Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu

Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC

Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from www.dlhausanovels.com.ng
You can download more hausa novels there
Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online
It is free we do not charge for uploading novel
Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services

Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us

Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it

Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT
An dauko wannan littafi daga shafin www.dlhausanovels.com.ng ku ziyarci shafin na www.dlhausanovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya

Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,

Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan
Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490

A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,

Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu

Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC

Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from www.dlhausanovels.com.ng
You can download more hausa novels there
Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online
It is free we do not charge for uploading novel
Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services

Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us

Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it

Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT★SA MAZA GUDU★!!!
Littafi Na Tara (9)
Part A.
Prince Auwal Auwzab
KODA LAHAMAN YAGA YA SAMI WANNAN
NASARA
SAIYA DAGA TAKOBINSA SAMA YA TAKARKARE
YA
KWARARA UBAN IHU SANNAN YA SHIGA YIWA
KANSA KIRARI YANA MAI CEWA INA RAGOWAR
JARUMAN GASAR NE,IDAN SUN ISA SU SHIGO
SU
DUKA NI KADAI NA ISHE SU.Na rantse da
karagar
Ubana yanzun nan zan kashe su na lashe wannan
gasa.Lokacin da Yarima Lahaman ya fara yin
wannan kuri sai Sa Maza Gudu ya fusata ainun
zuciyarsa ta kama tafarfasa cikin tsananin fushi
ya
zare takobinsa ya yunkura zai ruga izuwa cikin
filin
gasar amma sai alkalan gasar suka sha gabansa
suka hanashi.A lokacin ne suka kurawa juna
idanu
shida Lahaman suna harara kamar zasu cinye
kansu danye.Shi kuwa Jarumi Hibairu yana tsaye
kusa da Malika cikin nutsuwa ko kaduwa baiyi ba
sai murmushi ma yakeyi.Ita kuwa Gimbiya Malika
hankalinta yafi na kowa tashi bisa ganin cewa
Yarima Lahaman shine babban makiyinta a
duniya
kuma gashi ya sami jarumtakar da babu mai
kamarta.Lokacin da sarki Hilairu ya fahimci
cewar
hankalin Malika ya dugunzuma saiyazo kusa dasu
ya tsaya sannan ya dubeta yace kwantar da
hankalinki ya masoyiyata ni nasan cewa ko dan
uwana Sa Maza gudu zai iya maganin
Lahaman.Dajin haka sai Hibairu ya dubeshi yace
kai ai san an gwada akan san na kwarai.Ni kaina
ban taba ganin mutum mai mugun zafin nama da
karfin damtse ba irin wanda Lahaman kedashi
yanzu abin ma yafi gaban misali.Anya kuwa ba
aikin sihiri bane wannan?Malika tayi ajiyar zuciya
tace tabbas wannan aikin sihiri ne domin kuwa ni
kaina nasan cewa na fishi jarumtaka ada amma
yanzu bazan iya tararsa ba.Gama fadin hakan
keda
wuya saiga sadauki Aryan yazo garesu duk
jikinsa
ya baci da jini sakamakon raunikan biyar da
Lahaman yayi masa a lokacin daya shiga cikin
zugar dakaru dubu da suka yakeshi duk raunikan
biyar an dinkesu.Cikin murna Malika ta dubeshi
tace nayi murna daka tsira da rayuwarka daga
hannun wannan azzalumin.Aryan ya gyada kai
yace ya shugabata ai in badon na gudu ba so
yayi
yayi min kisan gillah ina mai shawartarku da kada
ku kuskura ku cigaba da yin wannan gasa.Koda
jin
wannan batu sai Hibairu yayi murmushi yace
babu
abinda zai tsaida ni akan tunkarar kowane jarumi
koda kuwa sabon jarumi zai sake baiyana wanda
ya ninka Lahaman Jarumtaka sau dubu domin
ubangijina dashi na dogara.Koda jin wannan batu
sai sarki Hilairu ya tafi izuwa inda Sa Maza Gudu
yake yazo daf dashi suka kurawa juna idanu.Nan
take kowannensu idanunsa suka ciko da kwallah
suka fara zubar da hawaye kawai sai suka
rungume junansu saida suka shafe yan dakiku a
rungume da juna a wannan lokaci ne alkalan
gasa
sun ware gefe gyda suna ta tattaunawa akan
yadda
ya kamata su bullowa wannan gasa tunda duk
tsarin gasar ya sauya bisa yadda aka shirya shi
da
farko.A tsakiyar filin gasar kuwa an kwashe
gawarwakin dakarun da Lahaman ya kashe babu
kowa a wajen sai shi kadai a tsaye ruke da
takobinsa yana muzurai yagaji da surutunsa na
kirari sai huci yake kamar wani rikakken
zaki.Sarki
Hilairu ya janye jikinsa daga cikin na sa maza
gudu suka fuskanci juna sannan yace yakai dan
uwana ina mai rokonka daka fita daga cikin
wannan gasa domin idanuwa na bazasu iya ganin
mutuwarka,ka tuna cewa bani da kowa a duniya
yanzu face kai na rushe kasarmu an tarwatsa
jama'armu kuma nasan cewa kaima kana da
burin
mu koma mahaifarmu mu sake rayata.Inason ka
manta da komai da kowa kazo mu sulale mubar
garin nan mu koma kasarmu.Sa'adda sarki
Hilairu
yazo nan a zancensa sai Jarumi Sa Maza Gudu
ya
bushe da dariya.Al'amarin daya sake razana
Hilairu
kenan lokaci guda sa maza gudu ya turbune
fuskarsa ya dubi Hilairu a fusace yace kana sone
muyi gudun gara mu tarar da zago,to ka sani
cewa
ko mun gudu sai yarima Lahaman yabimu har
can
kasar tamu ya kashemu ya sake baje komai kaga
kenan munyi aikin banzaWaishin ma ka manta da
suna na ne wato SA MAZA GUDU,har abada
bazan
taba gudar wani da namiji ba komai
jarumtakarsa.Ina mai tabbatar maka da cewa
komai jarumtakar Lahaman kuma komai karfin
sihirin tsafinsa baikai na Hibairu ba.Tunda naki
gudun Hibairu bazan guji Lahaman ba har sai na
dauki fansar jinin matarka daya kashe da kuma
jini
jama'armu kasani cewa bayan na rasa gimbiya
Lasmin a yanzu kuma nayi arba da gimbiya
Zuhura yar sarkin wannan gari sai naji na kamu
da
tsananin sonta fiye da yadda ma naso Lasmin
don
haka dole ne kota wane hali na lashe wannan
gasa.Yanzu makiya na sun zama gudu biyu
wadanda babu gudu babu jada baya dole sai
naga
bayansu.Koda sa maza gudu yazo nan a
zancensa
sai hawaye ya zubowa sarki Hilairu yace ai kuwa
ganin bayan wadannan jarumai biyu a wajenka
daidai yake da neman jaki mai kaho.Nasani cewa
bakayin magana biyu kuma duk abinda kayi niyar
yi ko zaka mutu saika aiwatar dashi din haka ban
isa na hanaka ba amma ina mai shawartarka
daka
janye gabarka akan jarumi Hibairu saboda shi bai
kasance azzalumi ba kamar yadda lahaman ya
kasance.Ka tuna cewa ba komai ne ya haddasa
kiyayya a tsakaninku ba face Soyayya dakai dashi
duk kunyi asarar wacce kuke so,shin yanzu ma
kana so ne ku sakeyin asarar wacce kuke so din?
Idan har soyayyarka akan gimbiya Zuhura ta
gaskiya ce ai ba zaka so bakin cikinta ba ko
salwantar rayuwarta,kaje kayi tunani.Koda sarki
Hilairu yazo daidai nan a zancensa sai sukaga
shugaban alkalan gasar ya shigo cikin tsakiyar
filin
gasar ya tsaya.Nan take kuwa filin gasar yayi
tsit
tamkar babu mai rai a cikinsa saboda kowa ya
saurara yaji hukuncin da aka yanke akan wannan
gasa.Alkalin gasar yayi gyaran murya sannan
yace
yaku jama'a kamar yadda kuka gani a idanu a
halin yanzu saura mutum hudu kacal suka rage a
cikin Prince Auwal Auwzab Auwzab
wannan gasa kuma a cikin mace guda daya
ce.Maza uku,Mazan sune Jarumi Hibairu,Sa Maza
Gudu da Kuma bakon jarumi Yarima Lahaman
mai
jarumtakar ban al'ajabi dole ne a cikin wadannan
jarumai hudu a fitar da mutum biyu wadanda
zasu
yi wasan karshe saboda haka yanzu mu alkalan
gasa mun yake hukuncin cewa yanzu gimbiya
Malika zata sake karawa da Hibairu a zagaye na
biyun karshe Jarumi Sa Maza Gudu zai kara da
Yarima Lahaman wanda sukayi nasara sune
zasuyi
wasa na karshe a gobe.Koda jin wannan batu sai
filin wasan ya kaure da shewa gami da ihu da
tafi.Shi kuwa sarki Hilairu hankalinsa ne ya
dugunzuma ainun bisa jin cewa dan uwansa zai
kara da Lahaman amma a bangaren masoyiyarsa
gimbiya Malika ko kadan bai damu ba saboda
yasan cewa Hibairu bazai kasheta ba.Nan take
batare da bata wani lokaci ba aka buga gangar
fara
gumurzu aka kirawo gimbiya Malika da Jarumi
Hibairu don haka sai Yarima Lahaman ya fito
daga
cikin filin gasar ya basu wuri.Maimakon Lahaman
yaje inda jaruman gasa suke tsayawa saiya nufi
inda Sa Maza Gudu yake yazo daf dashi yadda
suna iya jin numfashin juna suka kurawa junansu
idanu cikin tsananin kiyayya da fushi har
fuskokinsu nayi gyatsinewa.Lahaman yace nasan
cewa ka dade kana farautata domin ka daukarwa
dan uwanka da jama'arku fansa ni kuma na dade
ina neman yadda zanga bayan yar uwata Malika
na
haye kan Karagar Ubana sai gashi na rigaku
samun abinda nake nema.Ayau din nan zan
kashe
ka sannan na kashe Jarumi Hibairu na mallaki
Gimbiya Zuhuran da kukeso ku biyun.Asannan ne
zan zama GAGARABADAU kuma dodon dukkan
sarakunan da jaruman Nahiya.Lallai zan sami
dukiyar da babu mai irinta kuma zan shimfida
mulki irin wanda ba'a taba yin kamarsa ba a duk
nahiyoyin dake nan.Koda Lahaman yazo nan a
zancensa sai Sa maza gudu ya bushe da dariya
lokaci gudu kuma ya turbune fuska yace kai
wawa
ka manta da wani abu guda daya karfin damtse
da
karfin sihirin tsafi bashi kadai suke kai mutum ga
samun nasarar abinda yasa a gabansa ba.Akwai
sa'a da rabo saboda haka kasa wannan aranka
ina
mai tabbatar maka da cewa gobe idan muka
hadu
idan har ban kasheka ba kaima ba zaka kasheni
ba
saidai muyi RAGAS.Rana bata karya saidai uwar
ya
taji kunya.Gama fadin hakan keda wuya sai
sukaji
an buga gangar fara gumurzu a filin daga don
haka
sai suka juya suka fuskanci filin gasar.Malika da
Hibairu na tsaye a tsakiyar filin kowannensu na
ruke da takobi da garkuwa kuma tazarar dake
tsakaninsu takai taku goma sha biyar.Koda sukaji
an buga gangar fara gumurzun sai suka rugo da
gudu izuwa kan junansu suka kacame da
masifaffen yaki mai tsananin ban tsoro domin
nan
take suka rinka kaiwa junansu sara da suka da
dukkan karfinsu sai kace dama can sun kasance
tsofaffun abokan gaba masu farautar rayukan
juna.Koda ganin yadda sukayin wannan gumurzu
sai hankalin sarki Hilairu ya dugunzuma saboda
bai taba zaton cewa hakan zasuyi wannan yaki
ba
domin a koyaushe dayansu zai iya cutar da wani
amma koda suka shafe yan dakiku suna fafatawa
sai yakin ya sauya salo.Domin nan take karfin
saran Hibairu ya danne na Malika ya zamana
cewa
da kyar take iya karewa kuma bata iya maida
martani.Ana cikin hakan ne Hibairu ya shammace
ta ya daka tsalle sama ya gabza mata wani
wawan
naushi a fuskarta da kafarsa.Saboda karfin
naushin
saida tayi katantanwa a sama sannan ta fado
kasa
ta baje sumammiya.Koda ganin haka sai filin ya
kaure da shewa gami da tafi aka rinka yiwa
Hibairu
jinjina.A guje likitoci suka shigo cikin filin suka
tsaya akan Malika amma anan aka yayyafa mata
ruwa saida ta farfado kuma ta mike zaune
zumbur
tana mai goge jini akan hancinta.Koda Sarki
Hilairu
yaga ta mike tsaye saiya cika da farin ciki.Nan
take
Malika ta mike tsaye da kafafunta ta fice daga
cikin
filin gasar.Nan dai filin gasar ya watse jama'a
suka
tafi suna ta tattaunawa akan gasar karshe da
za'ayi
ta gobe wasu suna cewa ai tabbas Yarima
Lahaman ne zai lashe wannan gasa wasu suna
cewa ai Hibairu ne zai lashe gasar wasu kuma
suka rinka cewa ai saidai an ga abinda ya faru
tsakanin Lahaman da sa maza gudu tukunna
kafin
ayi wasa na karshe.Lokacin da sarki Kamzar tare
da yarsa Gimbiya Zuhura suka isa cikin gidan
sarautar sai duk suka tsaya cak a inda suka saba
rabuwa domin kowa ya tafi izuwa turakarsa.A
tare
suka dubi junansu suna mamakin dalilin da yasa
suka kasa tafiya kawai sai sarki ya dubeta yace
yake yata waishin menene yake yawo a cikin
zuciyarki?Lallai akwai magana a cikin bakin nan
naki.Ashe har akwai wani abu da zaki iya boye
min?Sa'adda gimbiya Zuhura taji wannan
tambaya
sai tayi ajiyar zuciya sannan ta dubeshi cikin
alamun tsananin damuwa tace yakai abbana kayi
sani cewa tunda aka shirya gasar jarumtaka a
duniya ba'a taba shirya mai hadarin wannan
ba.Nayi bincike na gano cewa idan wannan bakon
jarumi wato yarima Lahaman ya lashe wannan
gasa to gaba dayan kasashen dake nahiyoyin sai
sun zama a karkashin mulkinsa yanzu babu wata
dabara da kake ganin zamuyi

1 Comments On SA MAZA GUDU 1 to 9
avatar
adamu-3

1 year ago

Reply

Masha Allah Allah ya Kara basira Aboki

Please Login or Register in order to submit comment