Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

mai bukatar littafi yaje website namu

Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC

Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from www.dlhausanovels.com.ng
You can download more hausa novels there
Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online
It is free we do not charge for uploading novel
Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services

Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us

Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it

Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT
SA MAZA GUDU
Littafi na biyu(2)
Part A
A tare suka waigo baya suka duba,sai suka ashe
Lasurat ce mahaifiyar Malika.Ta tunkaro su
fuskarta cike da alamun damuwa.Koda ganinta
sai
sarki ya mike tsaye ya taryeta yana mai rike
hannayenta a lokacin da ta kurawa hannun
Malika idanu.Sarki yace kwantar da hankali yake
Ummul Malika,kiyi sani cewa raunin da Malika taji
Karami ne kuma da wuri zata warke.Koda jin
wannan batu,sai murmushi ya kubucewa Lasurat
tayi doguwar ajiyar numfashi tace,to nagode da
abinda ya tsaya iya haka amma yaya akayi ta
sami wannan raunin alhalin nasan cewa duk inda
zata je kana bata tsaro mai kyau na dakaru?Sarki
Sharkuf ya numfasa yace,ni kaina nayi mamaki
yadda al'amarin ya faru,amma hakan bazata sake
faruwa ba.Yanzu ki tafi da ita izuwa turakarki ki
lallabata ta sami nutsuwa da kwanciyar hankali
domin akwai alamun cewa tana cikin damuwa.
Batare da wata gardama ba Lasurat ta kama
hannun Gimbiya Malika tajata suka nausa izuwa
can cikin gidan sarautar.Shi kuwa Sarki Sharkuf
sai
ya bita da kallo cikin alamun tsananin damuwa
gami da tunani mai zurfi.Na take idanunsa suka
ciko da kwallah har hawaye ya zubo masa
saboda
tausayin da ya kama shi.Ba komai ne ya sanya
masa wannan tausayi ba face a binciken da yayi
a
hallarar tsafinsa ya gano cewa bayan mutuwarsa
sai wannan 'ya da uwa sun rabu sakamakon wata
kaddara wacce basu isa su guje mata ba.Tunda
farkon Yammaci Gimbiya Malika ta caba ado tayi
shirin tafiya izuwa wannan Gida na Yarima
Lahaman.Bayan ta hama shiri tsaf,sai hankalinta
ya DUGUNZUMA bisa dalilai biyu,dalili na farko
shine bata san yaya taza sulale ta fice daga
gidan
sarautar ba tare da wani ya ganta ba.Dalili na
biyu kuma bata san ko nawa Yarima Lahaman zai
siyar mata da wannan bawan nasa ba Wanda taji
ta kamu da tsananin sonsa farat daya.Duk da
tasan cewa komai tsadar bawan zata iya
sayensa,amma tayaya zata iya fitar da kudade
masu yawa daga gidan sarautar batare da sarki
ya gane dukkan shirinta ba?Idan tace kogon ta
na
dukiya zataje ta debo kudin tafiyar mai tsawon
gaske ce,ba zai yiyu ba.Bisa wannan dalili ne
yasa
Gimbiya Malika ta kama zarya a cikin babban
falo
na turakarta ta kasa zaune ko tsaye.Kuma
Hankalinta ya DUGUNZUMA,taji kamar ta fashe
da kuka saboda bata da wani buri da kuma 'doki
wanda yafi taje ta gana da wancan bakon bawa
ko don ma ta sake ganin fuskarsa,Zuciya
rta ta
huta da tsananin begensa da tunaninsa.Malika na
cikin wannan hali ne Shugabar kuyanginta wata
mace yar kimanin shekara arba'in da daya mai
suna Lasmira ta shigo cikin falon tare da
wadansu
kuyanci guda uku,domin su gabatar da irin
aiyukan da suka sabayi kullum.Koda Lasmira
taga
gimbiya a tsaye tana kaii kawo cikin alamun
damuwa,sai ta sallami wadannan kuyangi guda
uku dake tare da ita,suka juya da baya suka fice
daga cikin falon.Lasmira ta karasa gaban Malika
ta
dubeta tace,Ya shugabata menene ya dameki
haka harzaki kasa zama ko tsayuwa?Koda jin
wannan tambayar,sai Malika ta koma kan kujera
ta zauna tayi shiru kamar baza tace komai
ba,tana mai kurawa Lasmira idanu.Daga can sai
tayi gyaran murya ta dubi Lasmira cikin nutsuwa
tace,yake Lasmira kiyi sani cewa na yarda dake
kuma nasan zaki iya rufe sirrina tunda tun ina
yarinya karama kike aiki a karkashin
Mahaifiya,kuma ban taba jinta tayi korafi akankin
yi mata wani laifi ba,bisa wannan dalili yanzu zan
sanar dake abinda ke damuna akan amana kuma
ina son ki bani shawarar abinda zanyi na sami
mafita.Nan take Gimbiya Malika ta zaiyanawa
Lasmira duk bukatunta.Koda jin wannan bayanin
nata,saiLasmirata kyalkyale ta dariya.Al'amarin
daya bawa Malika haushi da mamaki kenan
tace,mene kuma abin dariya a cikin wannan
Al'amarin?Lasmira tace,ai gani nayi ga magani a
gonar yaro amma bai sanshi ba,ai warware
wannan matsala taki abu nemai sauki tamkar
cire
silin gashi daga cikin tandun mai.Abinda nake so
dake kawai shine kibi duk irin umarnin dana
baki,in kikayi haka dake da duk adadin kudin da
kike bukata zaku isa kofar gidan Yarima na can
bayan gari a asirrance kuma zaki dawo a
asirrance
batare da kowa ya sani ba.Ko jin wannan
batu,sai
farincik ya lullube Malika ta dubi Lasmira cikin
zumudi tace,Fadi duk irin abida kike so
nayi.Lasmira tayi murmushi tace,yanzu dai da
farko ina son ki bani Dinare dubu goma kacal
wanda zanje na aiwatar da wadansu ayyuka a
cikin gidan nan dasu,zan dawo nan da kafin cikar
rabin sa"a.Batare da gardamar komai ba kuwa
sai
Malika ta shiga cikin kuryar turakarta ta debo
dinare dubu goma a cikin jakar kudi ta mikawa
Lasmira.Lasmira na karbar wannan kudi sai ta
boyesu acikin rigarta sannan ta juya ta fice daga
cikin turarkar.Lasmira bata zame ko ina ba sai
can
kofar dakin shugaban dakarun dake tsaron gidan
sarautar,wani barden jarumi wanda ake kira da
suna Mahutur bin Kauzif.Da isarta sai ta
kwankwasa kofar dakin sau biyu kacal,faruwar
hakan ke da wuya sai Muhutur yayi magana daga
ciki yace,to Lasmira shugabar yan cuwacuwar
gidan nan yau kuma dame aka zo mini don nasan
cewa unguwa bata jewar banza.Lasmira tace ai
sai
ka fito waje kaji abinda nazo dashi.Muhutur yace
ai zaifi kyau ki shigo daga ciki komai zaifi
sirri.Idan kuma matarka tazo ta ganmu fa sai ta
zata amanarta zanci kuma ka sani cewa kawata
ce
ko?Haka ne to bari na kimtsa gani nan fitowa.Jin
kadan saiga Muhutur ya fito yana goge bakinsa
ga
dukkan alamun abinci ya gama ci.Maimakon
Lasmira ta bude baki tace wani abu,sai ta dauko
kudin Dinare dubu uku ta mika masa.Cikin
kaduwa da Mamaki Muhutur ya karbi kudin yana
mai jinjina su akan tafin hannunsa,sannan yayi
waige waige da dube dube yai sauri ya Soka
kudin a
cikin aljihun wandonsa ya dubeta
yace,wannan kuma fa na menene?shin wani abu
za'a siyowa Gimbiya a boye?Lasmira tace a'a
itace
da kanta take son ta fita daga cikin gidan
sarautar
nan tare da dukiya mai yawa saboda taje ta siyo
wani bawa a can gidan Yarima dake bayan
gari,kuma komai ana sin ayi shine a asirrance ba
tare da sarki ya sani ba.
Koda Lasmira tazo nan a zancenta,sai hankalin
Badakare Muhutur ya DUGUNZUMA ainun ya
rasa
abinda ke masa dadi domin yasan cewa hadarin
dake cikin wannan aikiyana da yawa saboda ko
yaya aka sami akasi ya rasa aikinsa kenan .Don
haka sai ya murtuke fuskarsa kuma ya murza
gashin bakinsa yace,kai ungo kudinki bazan yi
wannan aiki ba,hadarin dake cikinsa yafi abinda
kika bani.Koda jin haka,sai Lasmira ta sake saka
hannunta cikin aljihunta ta dauko wani damin
kudin Dinare dubu uku ta wurga masa tace,ga
wadansu dinare dubu ukun kaga ke nan inka
hada dana farko sun zama dinare dubu shida
daidai albashinka na shekara biyu kenan,shin ka
amince yanzu zakayi wannan aiki?Koda jin
wannan tambaya,sai jikin Muhutur ya kama
kyarma ya rasa hukuncin da zai yankewa
kansa,saida yayi duru duru yayi gaba yayi baya
sannan ya juyo ya fuskanci Lasmira yace,to ina
kudin dakarun dake aiki a yau?kinsan cewa suma
sai na raba musu wani abun sannan zasu ki duba
duk abinda za'a wuce dashi.Koda jin haka sai
Lasmira ta zura hannu cikin aljihun rigarta ta
dauko wani kullin kudi na dinare dubu ta mikawa
Muhutur tace,wannan dinare dubu ne nasan ya
isa ka raba musu,wane lokaci za'a fito da
Gimbiya
da dukiyarta?Muhutur yayi shiru yana tunani
sannan yace,ai yau talata ce kuma duk ranar
talata da yammaci ne sakalaiya Sarki ke
kwanciya
domin ya huta ba zai sake fitowa waje ba sai
gobe da safe don haka a daidai wannan lokaci
za'a fito da Gimbiya.Lasmira tayi murmushin
farin
ciki ta juya da baya da gudu taje ta sanar da
Gimbiya Malika duk abinda ya faru tsakaninta da
shugaban dakaru Muhutur.Sannan sai ta dauko
wani shudin magani a cikin wata yar karamar
kwalba ta mikawa Malika tace,ungo wannan
kisha
makurwa biyu kacal,batare da gardamar komai
ba ko tsoron wani abu sai kawai Malika ta karbi
ruwan maganin ta cire murfin kwalbar tasa a
bakinta tasha makurwa biyun kamar yadda aka
umarce ta.Bayan kamar dakika ashirin da
faruwar
hakan sai Malika ta fara jin jiri,ta kama tangadi
daga tsaya sannan ta tafi luu.. zata fadi,amma
sai
Lasmira ta tafa hannunta sau uku,saiga wadansu
hadiman gidan su Gimbiya Malikan guda uku karti
sun shigo,dayansu dauke da wata doguwar
akwatin katako.Da zuwansu sai suka ajiye
akwatin
suka bude shi saiga matattun beraye,kyankyasai
da sauran kananan kwari masu addabar mutane
a gidan.Kawai sai suka daga abinda ke dauke da
wadannan kwari daga cikin akwatin sai ga katon
fiki a kasan akwatin aka saka gimbiya Malika a
ciki
sannan suka dauko katakon dake dauke da
matattun kwarin suka dora a saman Gimbiya
Malika ya zauna darama.Komai kallon
kurilla,mutum bai isa ya iya ganewa cewa akwai
wani abu a kasan akwatin,saidai ayi tunanin
cewa
akwatin cike take da wadannan kwari babu komai
a kasanta.Bayan an rufe Malika a cikin wannan
akwati sai kuma wannan hadimai uku suka shiga
can cikin kuryar turakar gimbiya suka rinka fito
sa
irin akwatunan har guda arba'in,ashe kowacce a
kasanta lu'u lu'u aka zuba dunkim a samanta
kuma aka zuba matattun kwarin.Akwatuna guda
arba'in da daya aka loda su a kan keken shanu
aka tunkari kofar fita daga cikin gidan
sarautar.Saida aka wuce ta cikin kofofi tara,kuma
duk kofar da akazo ko tsayar da keken shanun
ba'ayi,da an hango su daga nesa sai a bude
musu kofa tun kafin ma su iso.Saida kawai su
wuce.Haka dai direban keken shanun ya cigaba
da wucewa har ya iso kofar karshe,har masu
gadin sun janyo kofar sun bude masa zai fita
kenan,sai sukaji an daka mus tsawa,a firgice
direban keken shanun tare da dukkan masu
gadin kofar kimanin su dari suka waiga suka
duba
inda sautun tsawar ya fito saboda sun dauki
murya.Ba muryar wani bace face ta sarki Sharkuf
yana tahowa daga cikin gidan sarautar bangaren
da turakarsa take.Sarki Sharkuf ya kara so
garesu
fuskarsa a murtuke ko kadan babu annuri,ya dubi
direban keken shanun ya sake daka masa tsawa
a
karo na biyu yace,ya kai Zarhus yau kuma wace
irin sharace za'a fitar da ita da wannan yammaci
sakaliya haka?Koda jin wannan tambaya,sai jikin
Zarhus ya kama tsuma ya sauko daga kan keken
shanun ya zube a kasa gaba Sarki tamkar zai
masa sujjada,sannan ya bude baki cikin rawar
murya yace,Ya shugabana sharace ta matattun
kwari kuma tayi yawa ne shi yasa kafin mu gama
kwasheta lokacin ya kure mana.Koda jin wannan
batu,sai Sarki Sharkuf ya sake bata rai yace,ban
yarda ba a bude akwatunan gaba dayansu na
gani.Dajin haka sai dakaru suka rugo izuwa kan
keken shanun suka kama bude akwatunan sarki
Sharkuf yazo kan akwatin farko wacce a
karkashinta ne Gimbiya Malika ke kwance tana
fama sharar barci kamar gawa.Koda sarki
Sharkuf
yaga matattun beraye da kunamai da kyankyasai
har sun fara doyi sai yayi sauri ya toshe
hancinsa.Har ya yunkura zai duna cikin ta biyu
sai
ya dawo da baya ya daga kwagirinsa da nufin ya
lumata cikin akwatin farko domin ya jiyo karshen
zurfinta,kawai sai yaji an kwala masa kira,yana
waigawa baya yaga ashe shugaban tsaro na
gidan
ne ya tawo da gudu yana sassarfa da tuntube
kamar wanda zai fadi yana cewa,ka gafarceni ya
shugabana nayi kusjure da baka riskeni ba anan
bakin kofa.Koda jin wannan batu,sai sarki
Sharkuf
ya basa luma kwagirinsa a cikin akwatin ya juyo
ya fuskanci Badakare Muhutur yana mai
kyalkyala
dariya yace haba yakai Muhuru ai bazaka tabayin
laifi ba a wajena saboda yau shekara arba'in da
biyar kenan kana aikinka na tabbatar da
tsaro,ba'a
taba kama da laifi ba,wata almundahana ko
rashin
gaskiya ba.Shin ka caje wadannan akwatunan
guda
arba'in da daya na shara ka tabbatar cewa
sharace
zalla a ciki ba'a boye wani abu ba?Muhutur ya
gyada kai yace,na caje su gaba daya ya
shugabana,babu wani abu a ciki sabanin wanda
ka
gani.Koda jin haka sai Sarki Sharkuf ya saki
ransa,hankalinsa ya kwanta,ya kyalkyale da
dariya
sannan ya dafa kafadar Muhutur yace,na yarda
dakai
dari bisa dari nasan cewa ba zaka taba cin
amana
taba,kuma bazaka taba yarda ayi wani abu ba
wanda
zai cutar dani koya cutar da wani nawa.Koda
gama
fadin haka sai Sarki Sharkuf ya dubi Zarhus yace
ko
kayan laifi ka dauko a yaudai ka sha.Zarhus ya
risina yayi godiya sannan ya sake hawa kan
keken
shanun ya saki linzami ya fice daga cikin gidan
sarautar.Sarki Sharkuf ya bishi da kallo kawai a
lokacin da Muhutur yaji idanunsa sun ciko da
kwalla
kamar ya fashe da kuka,saboda yasan cewa
tabbas
yasha cin amanar sarki ana shigowa gidan da
abubuwan da basu dace ba ko kuma a fitar da
wasu.
Tafiyar rabin sa'a kacal direba Zarhus yayi ya iso
kofar gidan yarima Lahaman dake bayan gari.Da
isowarsa sai shugaban masu gadin gidan ya
dubeshi ya daka masa tsawa yace,kai kuma
wane
irin wawa ne da zaka kawo shara nan gidan?
Waye
ya baka umarnin yin hakan?To kayi sauri ka bace
daga nan tun kafin Yarima ya fito ya ganka yasa
takobi ya sareka.Maimakon Zarhus yace wani
abu
sai kawai ya sauko daga kan keken shanun ya
bude
wannan akwatin ta farko.Yana budewa saiga
Gimbiya
Malika kwance a ciki tamkar gawa bayan ya
dauke
matattun kwarin dake samanta.Cikin kaduwa da
mutukar firgici masu gadin gidan sukayi kamar su
ruga izuwa cikin gidan amma sai suka fasa
sakamakon ganin Malika zaune a cikin akwatin
tamkar gawa ta faso kabari.Ashe dama can
kuyanga
Lasmira ta auna iya tsawon lokacin da Malika
zatayi
barcin kuma ta farka adaidai lokacin da Zarhus
ya
iso kofar gidan Yarima Lahaman.Shiyasa tace da
ita
tasha wannan maganin barcin makurwa
biyu.Koda
Malika ta bude idanunta ta tsinci kanta a cikin
keken
shanu,ga akwatuna arba'in a bayanta kuma gata
a
kofar gidan Yarima Lahaman,sai farin ciki ya
lullubeta ta sako kasa daga kan keken shanun
sannan ta dubi shugaban masu gadin ta daka
masa
tsawa tace zakaje ka gayawa ubangidan naka
cewa
gani na iso ko aa?Kodajin haka sai badakaren ya
juya da sauri ya fada cikin gidan.
Acan cikin gidan kuwa sarki Hilairu tare da
ragowar
jama'arsa bayi mutum dari na zaune sunyi jugum
jugum suna tunanin halin da suka tsinci kansu ta
rayuwar kunci,damuwa dakuma wahala.A yau
dinma
tun safe da aka basu abinci ba'a sake basu
ba.Gashi har rana ta fadi magariba ta doso
kal.Dukkanninsu jikinsu yayi sanyi lagwab tamkar
jikakkun tsumokara musamman matan cikinsu
wadanda dole ne mutum ya kamu da tausayinsu
Idan ya kallesu saboda su masu rauni ne basu da
juriya irinta maza.
Kwatsam sai ga Yarima Lahaman ya shigo cikin
dakin dakarunsa na take masa baya fuskarsa a
murtuke babu alamar annuri.Kai tsaye Lahaman
ya durfafi inda sarki Hilairu ke zaune ya dube shi
yace,ya kai wannan sarki naga alama cewa kai
mutum ne mai sa'a domin gashi ina shirin na
siyar dakai gobe ga manyan attajiran da zan sami
babbar riba,amma sai gashi 'yar uwata tazo
yanzu domin ta siyeka.To ka sani cewa karkon
kifi
zakayi domin babu wani abu da ya taba shigowa
hannuna kuma ya kubuta.Nayi maka alkawarin ko
ka subuce mini yanzu nan,ba da dadewa ba saika
dawo hannuna,kuma saina siyar dakai ga inda
za'a tafi daku izuwa wani bangaren na duniya
mai nisan gaske inda ko duriyarka ba za'a sake
jiba.Koda gama fadin hakan,sai Yarima Lahaman
ya fice daga cikin dakin tare da dakarunsa masu
take masa baya suka nufi can wajen
gidan.Gimbiya Malika na tsaye kusa da keken
shanunta mai dauke da akwatunan kudi saiga
yarima Lahaman ya fito daga cikin gidan.Koda
yaga Malika a gaban keken shanu mai daukar
akwatunan sharar gidan sarauta saiya bushe da
dariya yace,yanzu yar sarki ce guda a cikin kekn
daukan shara,to yanzu ina kudin da zaki siyi
bawan?Koda jin wannan tambaya,sai Malika ta
turbune fuskarta tace,a ina ka taba ganin anyi
cinikin kifi a ruwa,muje ka nuna min abinda nazo
siya na ganshi a raye cikin koshin lafiya sannan
muyi cinikin ba biya.Koda jin haka,sai Yarima
Lahaman yayi murmushi yace,Tabbas kina da
wayo da dabara ki biyo ni a baya muje kiga
muradinki.Yana gama fadin hakan sai ya juya ya
shige cikin gidan.Kawai sai Malika ta dubi
dakarun
dake kofar gidan tace,ba baku ajiyar keken
shanuna da direbansa,idan na fito na iske wani
abu ya taba lafiyarsu abaka cin rayuwarku.Tana
gama fadin hakan sai tabi bayan Yarima
Lahaman
da sauri har suka iso dakin dasu Sarki Hilairu ke
ciki.Da zuwansu aka bude musu kofa suna shiga
sai Sarki Hilairu da Gimbiya suka hada Idanu
take
yaji zuciyarsa ta buga da karfi karo na biyu na
haduwarsu.Ita kuwa Malika ji tayi gaba dayan
tsigar jikinta ta tashi kuma sai kwarjinin Hilairu
da
tsananin kyawun fuskarsa suka dimantata tayi
sauri ta dauke mazansu da matansu.Take taji ta
kamu da tsananin tausayinsu don haka sai ta
dubi yarima Lahaman tace ciniki ya sauya salo
yanzu ba mutum saya kadai nake so ka siyar min
ba,gaba dayan bayin dake cikin dakinnan nake
bukata.Koda jin wannan batu,sai yarima
Lahaman
ya bushe da dariyar keta yace,yaya ke da bakizo
da kudin siyan mutum daya ba ma amma kike
tunanin siyan mutum dari?Malika tace,ai sai ka
bari mu gama cinikin tukunna idan kaga na kasa
biyanka kudinka shine kake da bakin
magana.Lahaman yayi gyaran Murya sannan
yace,shidai wannan saurayi ma'abocin kyawu da
kike son ki fansa sai kin biyani kudi dinare dubu
dari biyar.Su kuwa ragowar yan'uwan nasa ko
wane dayansu sai kin biya dinare dubu hamsin
sannan zaki mallake su.Koda jin wannan batu,sai
Gimbiya Malika ta dubu Yarima Lahaman cikin
alamaun fishi da bakin ciki tace,haba yakai
yarima ai ko ranar kasuwar garin nan ba'a taba
siyar da bawan da darajarsa takai dinari dubu
biyar ba amma kai yanzu gashi kace na siyi
kowane daya akan farashin dubu hamsin.Shidai
wanacan saurayin ma'abocin kyau da kwarjini na
yarda na siye shi a farashin da ka fada,domin
darajarsa ma tafi haka,amma ina neman sassauci
akan ragowar bayin.Koda jin haka sai Yarima
Lahaman ya turbune fuskarsa yace,ai ba neman
kai nake yi ba dasu,idan ba zaki iya siyansu ba a
wannan farashin saidai ki hakura gaba
daya.kuma
inda kina bukatarsu sai ki biya kudinsu yanzu
take
sannan ki kada ki tafi dasu.Malika tayi murmushi
tace,kudi ba matsalata bane yadda zan kashe su
shine matsalata.muje wajen keken shanun na
biyaka kudinka duka,amma lallai kasa a kwance
wadan nan bayi daga cikin sarkoki su biyo mu
izuwa waye.Batare da wata gardamar komai
ba,yarima Lahaman yasa dakarunsa suka kwance
bayin daga cikin sarkoko aka tusa keyarsu izuwa
wajen gidan Sarki Hilairu ne akan gaba ana
ingiza
keyarsa ana kai masa bugu.Da fitowarsu kofar
gidan sai aka jera bayin akan layi sahi sahu
sannan Lahaman ya tsaya a gabansu dakarunsa
kuma suka yiwa bayin KAWANYA,nan take Malika
ta dubi Zarhus tace ina dukiyata?Zarhus na jin
wannan tambaya sai ya sauko daga keken
shanun
ya bude akwati ta biyu ya cire shimfidar sama
mai dauke da matattun kwari,sai ga lu'u lu'u
birjik a kasan mai yawan gaske wanda ya isa
Malika ta biya gaba daya kudin da aka siyar mata
da bayin gaba dayansu har sarki Hilairu
kuwa.Koda Yarima Lahaman da dakarunsa sukayi
arba da wannan duki mai yawa haka,sai suka
cika
da tsananin mamaki yadda akayi ta
mallaketa.Kawai sai Malika ta dubi Lahaman
tace,kasa yaranka amintattu su debi iyakar kudin
daka siyar mini da wadannan bayi duka su bar
mini ragowar.Cikin rawar jik Lahaman ya dubi
wasu mutum biyu daga ckin su yace,ku kirga
adadin dinare dubu dari biyar da kuma dinare
dubu hamsin sau dari.Nan taje kuwa dakarun
biyu suka shiga kirga lu'u lu'u suna zubawa a
cikin buhu saida suka shafe sa'a uku suna
wannan aiki sannan suka kammala amma duk da
haka sai da suka gama dibar iyakan adadin da
aka umarce su kuma suka rage kudade da
yawa.Bayan an dankawa yarima Lahaman ya
karba yana ta farin ciki da walwala sannan an
saki bayin sunzo bayan Malika sun tsaya.Sai
Malika ta bude ragowar akwatunan da hannunta
sai gashi kowacce akwati cike take da dinare da
lu'u lu'u fal wadanda in da za'a bawa mutum
guda daya jal to zai shafe shekaru dubu a
rayuwarsa yana cin abinci yana sa irin suturar
dayake so yana walwala batare da sun
kareba.
Koda Yarima Lahaman ya kyallara ido
yaga
wannan dukiya mai dumbin yawa sai kishi ya
turnukeshi gami da tsananin mamaki yadda akayi
Malika ta tara wannan dukiya.Shidai ya sani
cewa
babu yadda za'ayi sarki Sharkuf ya iya bata duk
irin tsananin son da yake mata saboda ya
kasance mutum mai kwatanta adalci a tsakanin
'ya'yansa.Bayan Malika ta gama nunwa Yarima
Lahaman wannan dukiya sai ta dubeshu tace,Ya
kai Yarima ashe burinka gajere ne ban sani ba.A
zatona zaka bukaci dukiya mai yawan da tafi
wannan danazo da ita,kuma tabbas dana baka na
sake baka wata ninkinta,saboda ina da ira ninkin
baninkin.Ina so ka sani cewa ni Gimbiya Malika
MURUCIN KAN DUTSE nake ban fito ba sai dana
shirya.Kabar ganin cewa babu kamarka a
harkokin cinikin bayi a wannan nahiyar har kayi
tunanin cewa kafi kowa kudi da arziki.,to ina mai
tabbatar maka da cewa ni Malika a halin yanzu
na tara dukiya da baka da kaso daya cikin
gomanta.Duk harkokin na cinikin abinci dana
kayan yaki da ake yi da manyan Kasashen duniya
a wannan zamani nice babbar dilar da babu
kamarta.Itama harkar cinikin bayin ka zauna
cikin
shiri kwanan nan zan karbeta na zama na ni ke
sarrafata a duniya,ba don komai ba sai domin
nayi maganin manyan azzalumai irinku.Yanzu dai
gani ni kadaice na zo babu wani badakare ko
guda daya daya rakoni don bani tsaro.Idan ka
gadama ka turo min gaba daya dakarun naka su
tare mini hanya kafin na isa cikin gari suce zasu
kwaci wannan dukiya da wadannan bayin dana
siya wajenka.Na rantse dabgemun Mahaifinmu
dayansu bazai tsira da rayuwarsa ba.Idan kuma
kana ganin cewa kai ne da kanka zaka tareni to
ina jiranka ai KAR TA SAN KAR ce kuma shege
ka
fasa.Koda Malika tazo nan a jawabinta sai ta
dubi
su sarki Hilairu tace,wuce gaba mu tafi izuwa
inda
zan ajiye ku.Cikin tsananin farin ciki su sarki
Hilairu suka wuce gaba sannan Malika ta hau kan
keken shanu Zarhus ya tuka suka bi bayan su
Hilairu.Dama tunda Gimbiya Malika ta fara
bayaninta ga Yarima Lahaman sai jikinsa ya
kama
tsuma,idanunsa suka kada sukayi jawur ya kamu
da tsananin bakin ciki kuma ya rinka ji kamar ya
zare takobinsa yaje ya afka mata da yaki,amma
sai ya daure ya hakura sa'adda ta fadi kalma
mai
zafi da muni a gareshi sai dakarunsa su yunkuro
zasu afka mata,amma sai ya dannesu,saboda
yasan cewa AJALIN su zasu gaiyata kuma shi
kansa bazai iya karesu ba da komai.Har Saida
Malika tayi nisa da barin kofar wannan gidan
nasa
har ya daina hangosu ita da dukan bayin data
siya a hannunsa,sannan ya takarkare ya kwarar
uban ihu mai tsananin ban tsoro sannan kuma ya
durkushe kasa bisa guiwowinsa ya fashe da
matsanancin kuka na bakin ciki.Adaidai wannan
lokaci ne hadari ya gangamo aka fara tafka
walkiya da tsawo amma saboda tsananin bakin
ciki sai Yarima Lahaman yaki tashi ya shiga cikin
wannan gida nasa.Aikuwa take aka tsuge da
ruwan sama kamar da bakin kwarya,koda ganin
yadda ruwa yake dukan Yarima Lahaman kuma
gashi ruwa ne mai karfin gaske dauke da iska,sai
daya daga cikin wannan dakarun nasa ya matsa
daf dashi yace,ya shugabana zaifi kyau ka tashi
daga cikin ruwan nan domin zai iya cutar da
lafiyar...Kafin badakaren ya gama rufe bakinsa
tuni Yarima Lahaman ya shammaceshi cikin
bakin
ZAFIN NAMA ya zare takobinsa ya share masa
makogwaro,kawai sai gani akayi jini yayi feshi
daga cikin wuyan badakaren sannan ya fadi
matacce.A sannanne Yarima Lahaman ya mike
tsaye ya goge jinin dake jikin takobinsa akan
gawar badakaren sannan ya mayar da takobin
cikin kufe ya daga kansa sama yayi KURURUWA
mai razanarwa tamkar zaki yayi GUNJI a
dawa.Nan take duk wani abu mai rai dake kusa
ya dimauce,hatta ragowar dakarunsa dake tsaye
a
wajen da wanda ke cikin gidan saida suka firgice
suka rikirkice suna neman su cika wandonsu da
iska,amma sabida tsoro sai suka kasa guduwa
izuwa ko ina.A sannanne Yarima Lahaman yayi
rantsuwa da darajar uwarsa yace,daga yau
Malika
baza ta sake yi masa wulakanci ba,kuma komai
dadewa sai ya kasheta da hannayensa ya huce
takaicinta,koda samun nasarar yin hakan na nufin
mutuwar duk wani abu mai rai dake cikin kasar
nan.Yana gama fadin hakan sai ya mike tsaye ya
shige izuwa cikin wannan gida nasa.
Al'amarin Gimbiya Malika kuwa lokacin da suka
yi
dan nisa ga barin gidan Yarima Lahaman tare
dasu sarki Hilairu itana bisa keken shaun su
kuma
suna tafiya a kasa bisa kafafunsu kuma taga
hadari ua gangamo an fara walkiya,sai ta bayar
da umarni aka rugu cikin wani kogon dutse domin
a fake.Ai kuwa suna gama shiga cikin kogon
dutsen nan ruwan saman ya tsuge,nan fa
kowannansu maza da mata ya sami wuri ya
zauna,aikuwa aka fara ruwan saman mai dauke
da iska mai sanyi ya addabi kowa.Koda ganin
haka sai Malika tayi amfani da karfin sihirinta na
tsafi ta kunna wutar jin dumi har guda uku.Daya
sai gaba dayan matan suka kewayeta dayar
kuma
sai mazan suka kewayeta,ya zamana cewa zaura
wutar guda daya babu kowa a gabanta,shi kansa
Zarhus tuni ya zaro bargo a cikin keken
shanunsa
ya kwanta ya lullube jikinsa gaba daya.Nan fa ya
rage saura Gimbiya Malika da sarki Hilairu a
tsaye
a can gefe daban daban suna kallon juna,kuma
suna kallon wannan wuta guda daya data rage
wacce babu kowa a gabanta,kamar hadin baki
sai
duk su biyun suka taho izuwa gaban wutar a
lokaci guda suka zauna suna jin dumin kuma
suna
fuskantar juna.Tsawon 'yan dakiku dayansu bece
uffan ba kawunansu na sunkuye suna kallon
kasa.Kawai sai suka dago kai a tare kuma
kowannasu ya bude baki da nufin yace wani
abu,koda muryoyinsu suka sarke a lokaci guda
sai
suka kyalkyale da dariya saboda mamakin yadda
al'amarin ya kasance haka.A sannane Gimbiya
Malika ta dubi Sarki Hilairu cikin murmushi mai
taushi tace,ya kawai wannan saurayi Ma'abocin
kyau da kwarjini waye kai kuma yaya akayi ka
tsinci
kanka a cikin wannan rayuwa ta bauta?Kasani
cewa
a karon farko dana ganka jikina ya bani cewa ka
fito
daga babban gida kuma asalinka baka kasance
bawa ba.Koda Malika tazo nan a zancenta sai
taga
hawaye a zubowa sarki Hilairu,al'amarin daya
karya
zuciyar kenan taji ta kara kamuwa da tsananin
tausayinsa.Ta dubi Sarki Hilairu cike da tsananin
tausayi tace,yakai wannan sarki me yasa kake
zubar
da hawayenka alhalin ka tsira daga hannun dan
uwana kuma kasan cewa bazan taba cutar dakai
ba,kayi sani cewar bana kubutar dakai bane

1 Comments On SA MAZA GUDU 1 to 9
avatar
adamu-3

1 year ago

Reply

Masha Allah Allah ya Kara basira Aboki

Please Login or Register in order to submit comment