Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

an gama ya
shugabana.Nan take ya juya ya fice daga cikin
fadar jim kadan saiga wani badakare tare da
Jarumi Sa Maza Gudu sun shigo cikin Fadar.
Zan dakata anan.
SA MAZA GUDU!!!
Littafi Na Bakwai (7)
Part B.
Saiga wani Badakare tare da Sa Maza Gudu sun
shigo cikin fadar.Da shigowarsu sai sarki Zaldasi
ya mike tsaye daga kan karagarsa ta mulki cikin
matukar farin ciki ya tarbi sa maza gudu tamkar
wanda yaga dan uwansa na jini har yana
rungume
shi sannan ya kama shi yaje ya zaunar dashi
bisa
wata kujera suka fuskanci juna.Nan take wata
kuyanga ta kawo musu tambula na ruwan inibi a
kan faranti gami da kofunan zinare guda
biyu,bayan kuyangae ta zuba musu ruwan inibin
sun dan kurba sai sarki zaldasi ya daga
hannunsa
na dama sama yana mai nuni da cewa a fita a
basu wuri.Nan take kuwa kowa ya fice daga
cikin
fadar hatta dakaru na musamman masu tsaron
lafiyar sarki.Saida Fadar tayi tsit tamkar babu
mutum mai numfashi a cikinta sannan sarki ya
dubi Sa Maza Gudu cikin nutsuwa yace yakai
GWARZON wannan KARNI wace shawara ce kazo
mini da Ita.Tabbas idanunka sunayi mini nuni da
cewar akwai magana mai muhimmanci a cikin
zuciyarka.Sa'adda Sa Maza Gudu yaji wannan
batu
sai yayi ajiyar numfashi cikin murmushi sannan
ya
risina cikin murmushi yace ya shugaba na ina
mai
tabbatar maka da cewa baby wanda yasan tuggu
da sirrin Hibairu sama dani mun dade muna gaba
ni dashi kowannenmu nason ganin bayan dan
uwansa.Ka sani cewa Hibairu bera ne mai mugun
wayo wanda kyanwa dubu ba zasu iya kamoshi
ba.Inason ka amince mini nayi muku jagora a
lokacin da za'a fita farautarsa.Bukata ta biyu
itace
inason da zarar an kamo Hibairu kawai kasa a
gaggauta yi masa kisan Gillah a bainar jama'a
kuma a tabbatar mini da nasarata ta lashe
wannan
gasar jarumtaka kuma a daura aurena da
gimbiya.Koda jin wannan batu sai sarki ya bushe
da dariya sannan ya kama hannun Sa Maza Gudu
suka mike tsaye tare ya dubeshi yace ka kwantar
da hankalinka yakai Angon Gimbiya Lasmin,komai
zai tafi daidai kamar yadda kake bukata,yanzu a
hangenka menene kake ganin zai kawo mana
matsala akan ganin bayan Jarumi Hibairu?Koda
jin
wannan tambaya sai Sa Maza Gudu yayi ajiyar
zuciya cikin alamun takaici yace abu daya ne zai
kawo mana cikas kuma ba komai bane ba face
karya zuciyar jama'ar gari akan bada imani ga
addinin Hibairu.Maganar gaskiya itace furuvin da
Hibairu yayi akan nasarar daya samu wajen
kashe
zaki nurul maut ta fara tasiri a cikin zukatun
talakawa a yanzu haka na sami labarin cewa
tsirarun mutane sun fara bayar da imani ga
addinin
Musulunci suna karbarsa a sirrance.Koda Sa
Maza
gudu yazo nan a jawabinsa sai hankalin sarki
Zaldasi ya dugunzuma kuma ransa ya baci ainun
fiye da koyaushe.Koda Sa Maza Gudu yaga
yadda
fuskar Sarki da jikinsa suka sauya yanayi nan
take
saiya dubeshi cikin murmushi yace kwantar da
hankalinka ya shugabana ai magance wannan
matsala abu ne mai sauki kawai ai kasa a kafa
doka kuma ayi binciken duk wanda aka kama da
laifin karbar addinin Hibairu to kisa ne
hukuncinsa
hakan zata sa duk mai sha'awar karbar addinin
ma
ya fasa kuma cikin kankanin lokaci wannan
addini
zai shafe a wannan birni naka mai albarka,dama
nahiyar gaba daya.Koda jin wannan batu sai
hankalin sarki Zaldasi ya kwanta ya bushe da
dariyar mugunta sannan ya dafa kafadar sa maza
gudu yace tabbas inda ka kasance daya daga
cikin
mutanen kasata da ayau dinnan zan maisheka
wazirina ko kuma babban bafade mai bani
shawara
akan harkokin mulki,yanzu na umarceka dakaje
ka
fara shiri na farautar Hibairu da zamu fita yau da
asuba.Ina mai yi maka albishir da cewa da zarar
ka auri Gimbiya zaka zamo daya daga cikin
manyan attajiran duniya.Koda jin wannan batu
sai
jarumi sa maza gudu ya kyalkyale da dariyar farin
ciki ya zube kasa gaban sarki Zaldasi yayi godiya
sannan ya mike da sauri yayiwa sarki sallama ya
juya ya fice daga cikin fadar.Shi kuma sarki
Zaldasi
saiya bishi da kallo kawai yana yin murmushi na
samun nutsuwa da kwanciyar hankali.
*Lokacin da Gimbiya Lasmin ta ruga izuwa cikin
daji bisa doki tana mai tsala azababben gudu
saita
rinka kwalawa Jarumi Hibairu Kira tana waige
waige da dube dube alhalin bata san a inda zata
ganshi ba.Shi kasan dokin nata bai san inda ya
dosa ba kawai yana gudu ne bisa umarninta da
kuma duk inda ta kada shi.Saida suka shafe
kusan
sa'a gudu da rabi sunata ratsa dajin da gudu
amma ko alamun Hibairu Lasmin bata gani ba
har
ya zamana cewa muryarta ta fara dashewa
saboda
yawan kiransa,dokinta kuma ya kamayin sassarfa
kamar zai fadi.Koda ganin haka sai zuciyar
Lasmin
ta karaya kuma hankalinta ya dugunzuma ainun
bata san sa'adda taja linzamin dokin taba ta
tsaya
cak sannan ta sauko daga kan dokin ta zauna
akan
wani dutse ta fashe da kukan bakin ciki,ba komai
bane ya sata wannan kuka ba face tunanin cewa
itafa yanzu tana cikin TSAKA MAI WUYA domin
GABA TSINI ne a gareta Baya Kuma SIYAKI.Abu
na
farko yanzu shine ta gudo ta baro iyayenta da
daular da take ciki ta biyo jarumi Hibairu kuma
gashi bata ganshi ba wata kila ma baya cikin
yanki
kasar gaba daya.Nan take Lasmin ta yanke
shawarar cewa ba zata taba komawa baya ba
koda
kuwa bata ga Jarumi Hibairu ba gwara ta cigaba
da nausawa cikin daji koda kuwa zata rasa
rayuwarta.Ba komai ne yasa ta yanke wannan
hukunci ba face ta gamsu cewa addinin
Musulunci
shine addinin gaskiya,kuma tasan cewa indai
tana
zaune tare da sarki Zaldasi babu yadda za'ayi ta
iya karbar Addinin Hibairu.Gmbiya Lasmin na
zaune a cikin wannan hali tana ta zubar da
hawaye
sai kawai taji an kirawo sunanta daga baya,a
firgice ta waigo baya,koda tau arba da wanda
yayi
kiranta sai ta mike tsaye zumbur ta ruga gareshi
cikin tsananin farin ciki.Ba wani abu bane ba
face
Jarumi Hibairu tsaye shi kadai rike da takobi
yana
kallon.....
SA MAZA GUDU!!!
Littafi Na Bakwai (7)
Part C.
HIBAIRU TSAYE SHI KADAI RIKE DA TAKOBI
yana
kallon gabas da yamma,kudu da arewa saboda
zargin ko tana tare da dakarun sarki a
bayanta.Yayin da Lasmin ta iso dag da Jarumi
Hibairu sai ta bude hannayenta da nufin ta
rungume shi,Hibairu yaja da baya yana mai kauce
mata ta rungumi iska sannan ya dubeta cikin
alamun rashin yadda yace saboda me kika biyoni
izuwa cikin wannan daji?Koda jin wannan
tambaya
sai Lasmin ta dubi Hibairu cikin mamaki tace
saboda me zakayi min wannan tambaya alhalin
kasan amsarta.A takaice dai inason na karbi
addininka kuma bani da wata hanya da zan iya
karbar tasa face nazo wajenka.Hibairu ya gyada
kai
cikin alamun rashin yarda yace yanzu ta yaya
kike
ganin zan aminta dake na gamsu da cewar zakiyi
watsi da mahaifinki ki zabe ni,shin yanzu zaki
iyayi
mini rantsuwa da girman iyayenki cewa ba hada
baki akayi dake ba domin a cutar dani?Koda jin
wannan batu sai gimbiya Lasmin tayi murmushi
tace na rantse da darajar uwata da ubana bazan
taba yarda a hada baki dani ba a cutar dakai,ina
mai tabbatar maka da cewa ni kadai na shigo
cikin
dajin nan kuma ba tare da kowa yasan fitowa ta
ba,to amma babu mamaki daga baya a gane
cewa
na gudo a turo dakaru su biyo sawuna.Ina mai
shawartarka damu gaggauta barin nan kan hanya
tunda komai zai iya faruwa kuma a ko
yaushe.Koda jin wannan batu sai Jarumi Hibairu
yayi shiru yana tunani da nazari a lokacin da
ransa
ya baci ya dubi Lasmin a fusace yace zuwanki
gareni yanzu bazai haifar mini da komai ba face
dakushewar dukkan shirina na ganin na sami
nasarar yada addinina a cikin kasarku amma
kuma
zai iya zama alheri akan hakan,kibar dokinki anan
ki biyoni a baya muje inda zamu cigaba da
tattaunawa a cikin nutsuwa.Koda gama fadin
hakan
sai Jarumi Hibairu ya juya ya nufi cikin wani
surkuki mai duhuwa wata hanya ce wacce kamar
bata bullewa,ba tare da fargabar komai ba kuwa
Gimbiya Lasmin tabi bayan Jarumi Hibairu da
sauri
suka kutsa izuwa cikin wannan surkuki suka bace
bat tamkar basu taba wanzuwa a wajen
ba.Lasmin
ta cigaba da bin Hibairu a baya suna ta keta
kwazazzabai da duhuwoyi har tsawon dan
lokaci,kwatsam sai ta hango wani wawakeken
rami
a gabansu mai tsananin fadi gami da zurfi.Acan
gabansu kuma wani katon KOGON DUTSE ne
saboda tsananin zurfin wannan ramin idan
mutum
ya leka kasansa bai isa ya iya hango karshensa
ba.Koda Lasmin tayi arba da wannan rami da
kuma kogon dutsen saita firgita ainun kuma ta
kamu da tsananin mamaki,ba komai ne ya
firgitata
ba kuma ya bata mamaki ba face ta taba jin
labarin wannan rami da wannan kogon dutse a
wajen mahaifinta sarki Zaldasi inda ya sanar da
itace cewa fiye da shekaru sittin baya babu wani
mahaluki daya isa yazo kusa da wannan rami ko
kogon dutsen walau MUTUM KO ALJAN,dabba ko
tsuntsu face ya zamana gawa.Nan take manyan
bokaye na nahiyar sun tabbatar da cewa wani
gagarumin Sihiri ne a wajen wanda aka kasa
gano
yanayinsa da asalinsa,wasu daga cikin bokayen
sunce aishi wannan kogon dutse asalinsa gida ne
na wani mashahurin boka don haka kafin ya mutu
ne ya sihirce wajen saboda wata dukiya mai
tsananin yawa daya boye.Abinda yafi daurewa
gimbiya Lasmin kai shine yaya akayi Hibairu yazo
wannan wuri wanda ya gagari kowa tsawon
shekaru sittin dasu ka gabata?Da isowar Hibairu
da Lasmin bakin wannan katon rami sai jikin
Lasmin ya kama karkarwa saboda tsananin
tsoro,koda ganin haka sai Jarumi Hibairu ya
dubeta cikin murmushi yace kwantar da
hankalinki
ya gimbiya idan har zuciyarki tayi imani da
ubangijina to kisa aranki cewa babu abinda zai
sameki abinda nake so dake kawai shine ki rintse
idanuwanki.Ba tare da wata fargabar komai ba
sai
Lasmin ta rufe idanuwanta faruwar hakan keda
wuya sai Jarumi Hibairu ya kama gefen cunar
rigarta ya rike sannan ya karanta wata addu'a ta
musamman nanfa Allah ya nuna ikon nasa domin
Hibairu na gama karanta addu'ar sai suka bace
bat
daga inda suke basu baiyana a ko ina ba sai
bakin
wannan kogon dutse.Koda Gimbiya Lasmin ta
bude
idanuwanta ta gansu tsaye a bakin kofar shiga
wannan kogon dutse sai gaba dayan tsigar jikinta
ta tashi saboda tsananin mamaki,nan take taji
son
Allah da tsoronsa sun kara kwarara a cikin
zuciyarta don haka bata san sa'adda ta kurawa
Hibairu idanu ba Tana Murmushi tace tabbas
tsarki
ya tabbata ga ubangijin Musulunci lallai inason
ka
gaggauta shigar dani cikin wannan addinin naka
mai daraja.Koda jin wannan batu sai farin ciki ya
mamaye jarumi Hibairu yace kwantar da
hankalinki
yake gimbiya yanzu dai mu fara shiga cikin
wannan gida mu zauna domin mu tattauna cikin
nutsuwa sannan na shigar dake cikin addinin
nawa.Koda gama fadin hakan sai Hibairu ya
kunna
kai izuwa cikin wannan tsohon kogon dutse mai
dimbin tarihi gami da matukar kwarjini da ban
tsoro.Da shigowarsu cikin farkon kogon sai
gimbiya Lasmin ta kamu da tsananin mamaki
domin ta tsinci kanta ne a cikin wani tafkeken
gida
wanda aka gina shi da zallan dutsen zinare kuma
aka kawata shi da kayan alatu na lu'u lu'u.Kai da
ganin wannan gida kasan cewa an shirya aljannar
duniya.Babban abinda yafi daurewa Gimbiya
Lasmin kai shine duk da cewa fiye da shekaru
dari
da daya babu wani mahaluki daya kara shigowa
gidan amma ko ina fes fes yake babu inda
mutum
zaiga koda digon kura.Dakarun yaki kuwa na
Aljanu gami da borori da kuyangi duka na aljanu
gasunan a ko ina cikin gidan amma dukkaninsu
sun kame sun zama gumaka tamkar ruhi bai taba
shiga shiga cikin gangar jikinsu ba,Duk da cewa
Gimbiya Lasmin na biye da Jarumi Hibairu a baya
daf da daf saida jikinta ya kama tsuma saboda
tsananin razanar da

tayi bisa ganin siffofin Aljanun dake cikin wannan
gida domin bata san sa'adda tayi wuf ya kamo
hannun Hibairu ba ta damkeshi da kyau.Koda
Hibairu ya fahimci cewa lallai a tsorace take
ainun
saiya juyo ya dubeta cikin murmushi yace
kwantar
da hankalinki Gimbiya Muddin kina tare dani
babu
wata halitta data isa ta matso a cikin gidan nan
har
ta iya cutar dake ko kuwa har yanzu baki gama
yin
imani bane da addinin nawa?Lokacin da gimbiya
Lasmin taji wannan tambaya sai tayi murmushi
tace ko kadan bani da wani shakku a cikin
zuciyata akan wannan addinin naka kuma na
yarda
dasi dari bisa dari.Haka dai Jarumi Hibairu da
Lasmin suka cigaba da ratsa fadoji,harabobi da
dakuna barkatai na cikin wannan gida har saida
suka isa karshen gidan inda sukazo wani bangare
wanda shine mafi kyau a gidan.Shidai wannan
bangare shine asalin turakar bokan daya kirkiri
gidan,a cikin wani babban falo kasaitacce suka
tsinci kansu wanda aka zuba masa wadansu irin
manyan kujeru na alfarma masu taushin
gaske,ga
yayan itatuwa wato kayan marmari na lambu
gasu
nan birjik bisa farantai nunannu kala kala tamkar
a
sannan aka tsinkosu daga cikin
itatuwansu.Al'amarin da yayi matukar daurewa
Gimbiya Lasmin kai kenan ta sake razana har
tsigar jikinta gaba daya ta tashi jikinta gaba daya
ya dume da wani irin mugun sanyi mai tabbatar
da
tsoronta.Koda jarumi Hibairu yaji hannu Lasmin
ya
dume da mugun sanyi nan take kuma ya cigaba
da
karkarwa saiya juyo gareta da sauri ya ruke
hannayenta biyu yace maza ki maimaita abinda
zan fada yanzu.Nan yake Hibairu ya karanta
kalmar
shahada koda Lasmin ta biya Kalmar sai taji
wata
irin nutsuwa ta shigeta kuma take dukkanin
tsoronta ya yaye tamkar bata taba yinsa ba,saida
Hibairu ya fahimci hakan sai shima ya kamu da
farin ciki kuma yai sauri ya saki hannayenta a
lokacin da suka zauna a kan wata doguwar
kujera
tare suka kallo junansu cikin MURMUSHI.A
sannan
ne Hibairu ya kawo gwauron numfashi ya ajiye
yace yake gimbiya yanzu kin zama cikakkiyar yar
uwata musulma don haka babu wani abu mai rai
daya isa ya sake tsorataki a cikin wannan gida.Ki
sani cewa a farkon shigowata cikin wannan gida
duk aljanun nan da kika gani a kame kamar
gumaka da ruhi a jikinsu kuma nasha gumurzun
yaki dasu bisa dole sukayi MUBAYA'A a gareni
don
su tsira da rayukansu kuma shugabansu ya
tabbatar mini da cewa nine bil'adama na farko
daya shigo gidan bayan mutuwar ubangidansu da
tsawon shekaru dari da sittin da uku,dukkanin
wadannan aljanu sun tuba kuma sun karbi addinin
musulunci,nine na umarce su dasu kame su
zama
kamar gumaka don kada ki firgice bisa ganin su
a
raye suna kai kawo dayin hidimarsu ta wannan
gida da sula saba yi tsawon shekaru.Yanzu tunda
kin zama yar uwarsu musulma ba zaki tsorata
dasu ba.Kafin Hibairu ya gama rufe bakinsa tuni
wadansu kyawawan kuyangi na Aljanu su uku sun
shigo cikin wannan babban falo a cikin shiga ta
kamala bata tsiraici ba dauke da tambula na
ruwan
inibi gami da abinci na alfarma irin na bil'adama
sun ajiye a gaban gimbiya Lasmin kuma suka
zube
kasa suka gaisheta sannan suka mike suka fice
daga cikin falon suka barsu su biyu rak.Nan take
Hibairu ya dauki cokali da faranti ya zubawa
kansa
abincin sannan ya dubi Lasmin yace da ita kema
ki zubawa kanki abincin nan kici cikin salama na
gaya miki babu abinda zai cutar dake.Koda gama
fadin hakan sai Hibairu ya juyawa Lasmin baya
saboda kunya yayi bismillah a fili ya kama cin
abinsa.Da ganin haka sai itama Lasmin ta
zubawa
kanta abincin ta kama ci bayan tayi bismillah
kamar yadda taji yayi,haka dai suka cigaba da cin
abincin har saida suka koshi.Ai kuwa suna
kammalawa saiga wadansu sababbin kuyangi
guda
uku sun shigo,nan take kuyangin suka dauke
kwanukan da suka ci abincin suka fice,fitarsu
keda
wuya sai ga wani narkeken Aljani mai surar
SADAUKAI a cikin gagarumar SHIGAR YAKI ya
shigo cikin falon.Daga nesa dasu kimanin tazarar
taku ashirin sai wannan Aljani ya zube kasa bisa
guiwarsa guda kansa a sunkuye a kas saboda
biyayye ya bude baki yace ya shugabana muna
da
baki a kofar gidan nan.Koda jin wannan batu sai
Jarumi Hibairu yayi murmushi yace su waye?
Aljanin ya sake risinawa yace ai ba wasu bane
face
Sarkin Yakin Sarki Zaldasi tare da wadansu
dakaru
su dari kacal,tabbas sarki ne ya turo su suyi
farautar Gimbiya su mayar da ita
gida.Dukkaninsu
sunyi cirko cirko a kofar gidan nan sun kasa koda
motsawa gaba da taku daya saboda
TSORO.Lokacin da Aljanin yazo nan a jawabinsa
sai Hibairu ya sake yin murmushi a karo na biyu
sannan ya dubeshi yace yakai Zulfanu kaje ka
baiyana kawai a gabansu kayi shiru kada kace
dasu kala duk abinda kaga ya faru ka dawo ka
sanar dani.Dajin wannan umarni sai Zulfanu ya
risina yace an gama ya shuganana,nan take
Zulfanu ya bace bat daga cikin falon tamkar bai
taba wanzuwa ba a wajen Ba.
*A can Kofar kogon dutsen kuwa sarkin yakin
Sarki
Zaldasi tare da dakarunsa mutum dari ne a tsaye
cirko cirko bisa dawakai suna kallon kogon
kawai,bawai su dakarun ba hatta dawakansu ma
kyarma sukeyi saboda tsoron wannan kogon
dutse.Tun sa'dda suka iso bakin katoton ramin
dake gaban kogon dutsen suka firgita ainun su
da
dawakan nasu har sun zabura zasu kada
dawakan
nasu su juya da baya sai shugabansu wato sarkin
yaki ya daka musu tsawa yace shin baku da
hankali ne?To kusani cewa gabanmu tsini ne
baya
kuma siyaki,idan muka koma gida babu gimbiya
Lasmin gaba dayanmu sai sarki Zaldasi ya kashe
mu saboda bamu da wata hujja wacce zamu iya
nunawa ta ceci rayukanmu bisa cewar munyi iya
kokarinmu wajen samo gimbiya.Kowanne
nku yaga
sawayen gimbiya dana bakon Jarumi Hibairu
har.•••••••••

SA MAZA GUDU!!!
Littafi Na Bakwai (7)
Part D.
KOWANNAN KU YAGA SAWAYEN GIMBIYA DANA
BAKON JARUMI HIBAIRU HAR ZUWA BAKIN
WANNAN KATON RAMI KO SHAKKA BABU SUNA
NAN CIKIN WANNAN KOGON DUTSE,ina mai
tabbatar muku da cewa zan iya tsallakar damu
wannan katon ramin da karfin sihirin tsafina amma
fa bani da tabbacin kare dayanku daga sharrin
wannan kogon dutse.Lallai ku sani cewa bamu da
wani zabi wanda yafi mu shiga cikin wannan kogon
dutse.Koda sarkin yaki yazo nan a jawabinsa sai
gaba dayan dakarun su dari suka firgita ainun,cikin
kowa ya duri ruwa suka rasa abinda zasuyi.Kawai
sai wani zakwakurin Barde daga cikinsu abin
kwatance ya dubi Sarkin Yaki a fusace batare da
wata fargaba ba yace kai sarkin yaki ka tuna cewa
fiye da shekaru dari babu wani mahaluki daya
jarraba shiga cikin wannan kogon dutse hatta sarki
Zaldasi da kansu kuwa,sai wannan shaidanin
bakon jarumi Wato Hibairu,kai ka sani cewa
shigarmu cikin wannan kogon dutse daidai yake da
siyar da rayukanmu.Kada ka manta cewa da
yawanmu nan muna da yaya,mata da iyaye,kuma
ko wasiya bamu bar musu ba muka fito wannan
aiki.Shin kanaso ne mu mutu a banza a wofi
kenan kuma mu bar bayanmu a cikin
maraici,talauci gami da shan wahalar rayuwa,zaifi
kyau mu koma ga sarki mu gaya masa cewa
Hibairu da Gimbiya sun shiga cikin wannan kogon
dutse kuma mun kasa shigarsa.Kaga kenan idan
shi yana ganin zai iya shiga sai yazo ya
jarraba.Koda wannan Barde yazo nan a zancensa
sai gaba dayan sauran yan uwansa dakaru suka
kama shewa suna masu cewa sun amince da
wannan sharawa daya kawo,shi kuwa sarkin yaki
da farko jikinsa ne yayi sanyi don haka sai yayi
shiru yana tunani da nazari daga can sai ya daka
musu tsawa ya dubi badakaren yace baka da
hankali ashe ka manta da halin sarki kenan,to ka
sani cewa idan mukaje masa da wannan labari
cewa mun kasa shiga kogon dutse nan ko dai yasa
a kashe mu ko kuma a yanke mana hukuncin
daurin rai da rai.Shin yanzmu zamu gudu ne
mubar iyalanmu saboda TSORON MUTUWA?Mafitar
mu kawai itace muyi iya kokarin mu koda kuwa
wasunmu zasu hallaka sauran su koma da
raunika,yanzu inason kowa ya rufe idanunsa domin
mu tsallake wannan rami wanda duk yayi yunkurin
gudu daga cikinku ni da kaina zan kure masa gudu
na kashe shi.Koda gama fadin hakan sai sarkin
yaki ya runtse idanunsa kuma ya bayar da umarnin
kowa ma ya rufe idonsa,ba tare da gardamar
komai ba kuwa gaba dayan dakarun suka rintse
idanuwansu.Faruwar hakan keda wuya sai wata irin
guguwa mai karfin gaske ta zagayesu kura ta
turnuke wajen gaba daya dajin yayi bakin kirin
yadda ko tafin hannu mutum bazai iya gani
ba.Daga nan kuma sai kurar da duhun suka dauke
dif tamkar daukewar ruwan sama.Koda kowa ya
bude idanunsa sai suka tsici kansu da dawakansu
a tsallaken wannan katon ramin tamkar mutum ne
yasa yatsunsa guda biyu ya kwashe su su duka ya
tsallakar dasu gefan ramin.Nanfa su duka suka
cika da dumbin mamaki gami da farin ciki basu
san sa'adda suka kamayin murmushi da dariyar
murna ba,amma kuma sai nan take fuskokinsu
suka juye izuwa tsananin tsoro,jikinsu ya kama
karkarwa tamkar an tsomasu a cikin kogin
kankara.Ba komai bane ya haddasa hakan face
ganin Aljani Zulfanu ya baiyana tsulum a
gabansu.Hannayen Zulfanu na makale cikin
hammatarsa,ga tarin MAKAMAN YAKI a jikinsa
sama da kala dari kuma fuskarsa a murtuke take
wacce saboda tsananin muninta da kwarjininta
saida gaba dayan dakarun dari suka rinka sakin
fitsari a cikin wando batare dasun hakan na faruwa
ba.Sarkin yaki ne kadai bai saki fitsarin ba kuma
shine kadai ya iya hada idanu da Aljani Zulfanu
suka kama kallon juna cikin harara.Tsawon yan
dakiku kadan suna yin wannan kallon kallo sai
sarkin yaki ya zare takobinsa ya kwarara uban ihu
mai tsananin firgitarwa.Tabbas inda a filin yaki ne
ya kurma wannan ihu da komai yawan abokan
gabansa sai sun zube kasa a firgice kuma a
nakashe.Kafin sarkin yaki ya gama kwarara wannan
ihu sai akaji muryarsa ta shake nan take kuma ya
kame kyam kamar gunki.Koda da dakarun suka
dago da kawunansu suka dubseshi sai sukaga
bakinsa ya karkace rabin jikinsa kuwa bangaren
dama ya shagube ya shanye ko motsashi baya
iyawa.Koda ganin abinda ya sami sarkin yaki sai
dakarun dari suka sake dimauce ainun fiye da
karon farko basu san sa'adda suka cure gaba
dayansu a waje guda ba.Da kyar sarkin yaki ya
wurkila idonsa na hagu bangaren da bai shanye ba
Kenan.Nan take wannan guguwa mai karfi ta sake
baiyanaa ta daukesu duka ta tsallakar dasu wannan
katon ramin a sannan ne hankalinsu ya dawo
jikinsu.Sarkin yaki ya dubi dakarun nasa da kyar
cikin karfin hali ya bude karkataccen bakinsa yace
to yanzu ne zamu iya komawa ga sarki tunda mun
sami shaidar da zamu iya kare kanmu.Yana gama
fadin hakan sai hawayen bakin ciki ya subuto daga
cikin idanuwansa yace ni kam shike nan a haka
zan karasa sauran rayuwata,na gama zama
nakasasshe,babu wani magani ko sihiri da zai iya
warkar dani.Koda jin wannan batu sai gaba dayan
dakarun suka kamu da tsananin tausayinsa nan dai
wasunsu suka kama tayashi kuka,Batare da bata
lokaci ba suka juyar da dawakansu suka nufi
hanyar da zata mayar dasu izuwa cikin birnin
Misra.
*A can cikin wannan gida na kogon dutse kuwa
bayan jarumi Hibairu ya sallami Aljani Zulfanu ya
fita ya barshi da gimbiya Lasmin sai Hibairu ya
dubeta yace yake Gimbiya kiyi sani cewa ban gudu
daga cikin birninku ba don tsoro ba,sai domin na
tsayar da salwantar da rayukan dakarun
mahaifinki,burina shine jama'arku gaba daya su
gane gaskiya kuma su karbeta bawai nayi ta zubar
da jininsu ba,kuma guduwata izuwa nan zaisa
zuciyoyin jama'arku su karaya su karaya
bada gaskiya da addinin Gaskiya.Kowa ya gani da
idanunsa cewa nine na lashe gasar Jarumtaka da
mahaifinki ya shirya,amma saboda son zuciya irin
na mahaifinki gami da kiyayyarsa akan addinina
saiya take gaskiyar yace a kamani a kaini kurkuku
yanzu gashi an kasa kamani na tsere musu kuma
gashi ya turo dakaru su kamani sun kasa,shin
kinsan me zai biyo baya idan sarkin yakinsa da
dakarunsa daya turo suka koma gareshi babu ni
babu ke?Koda jin wannan tambaya sai gimbiya
Lasmin ta girgiza kai alamar cewa bata sani
ba.Kafin na bude baki na bata amsa saiga Aljani
Zulfani ya sake baiyana tsulum a gabanmu yana
mai yimana alamar sallama gami da durkusawa a
gaba na Kansa na sunkye cikin biyayya saiyace Ya
shugaban dakarun sarki Zaldasi sun firgita ainun
da gani na kuma koda sarkin yakinsu ya zare
takobinsa da nufin yayi yaki dani sai na shafeshi
kadan,take rabin jikinsa ya shanye da kyar ya
iyayin tsafi suka gudu daga bakin kofar gidan
nan.Koda jin wannan labari sai Farin ciki ya
turnuke jarumi Hibairu ya dubi Aljani Zulfanu yace
da kyau aikinka yayi,zamu sake zubo ido daga nan
zuwa kwanaki biyu muga abinda zai biyo
baya.Tashi ka tafi na sallameka.Kafin Hibairu ya
gama rufe bakinsa tuni Aljani Zulfanu ya bace
bat.Hibairu ya duni Gimbiya Lasmin cikin
murmushi yace kiyi amfani da wannan dama ta
kwanaki biyu ki koyi yadda akeyin bautar
Allah.Koda gama fadin uakan sai Hibairu ya mike
tsaye kuma ya tafa hannayensa faruwar hakan keda
wuya saiga shugabar kuyangin gidan ta
baiyana,wata kyakkyawar sankaceciyar budurwa a
cikin wata doguwar farar riga,shugabar kuyangin ta
risina a gaban Hibairu ta kwashi gaisuwa shi kuma
saiya dubeta yace Ga Gimbiya nan a kaita
masaukinta kuma ki koyar da ita yadda akeyin
wankan tsarki,alwala da sallah kuma ki koya mata
fatiha da falaki da nasi.Koda jin haka sai shugabar
kuyangin ta sake risinawa ga Hibairu tace an gama
ya shugabana,kawai sai ta kama hannunta da nufin
ta janyeta ta tafi amma sai Gimbiya Lasmin ta noke
ta dubi Hibairu cikin alamun matukar damuwa tace
ta yaya wadanda ayau dinnan suka koya daga
gareka zakace su koyar dani?Ka sani fa cewa nifa
mutum ce kamarka su kuwa jinsi ne dabam nifa
har yanzu tsoronsu nakeji kuma ban saba dasu
ba.Koda jin haka sai Jarumi Hibairu yayi dariya
sannan yace kamar yadda kike ganin cewa baki
saba dasu ba aini ma yaune ranar farkon haduwata
dasu to amma saboda karfin imani na da
ubangijina sai nake jin kamar dama can sun
kasance yan uwana na jini tunda sun karbi
addinina,kiyi kokari ki sami irin wannan imani dana
samu a cikin zuciyarki.Idan kikayi haka zaki daina
jin komai a ranki dangane dasu,kuma ina mai
tabbatar miki da cewa babu dayansu dazaiyi
yunkurin cutar dake domin suna matukar kaunarki
fiye da yadda suke son kansu saboda tuni su
imaninsu ya tabbata ga ubangijin musulunci ba
zasu taba cutar da dan uwansu musulmi ba.Koda
jin wannan batu sai nan take gimbiya Lasmin taji
kishi ya shigeta bisa jin cewa wadannan Aljanu sun
fita karfin imani.Nan take ta tambayi kanta a cikin
zuciyarta tace yanzu ta yaya kenan nima zan iya
karfafa nawa imanin yafi nasu?Kafin ta iya baiwa
kanta amsa tuni an janyeta an tafi da ita izuwa
masaukin nata.Tafiyarsu keda wuya sai Hibairu ya
mike tsaye yaje yayi alwala sannan ya jagoranci
gaba dayan aljanun dake cikin wannan gida yayi
musu sallar magriba a matsayin limaminsu.Tun
kafin a gabatar da wannan sallah sautin murya na
kiran sallar da akayi ya cika dajin gaba daya da
amsa kuwwa kuma iska ta dauki zazzakar muryar
datayi kiran sallar ta kaita har cikin birnin
Misra.Koda jama'ar birnin misra suka jiyo wannan
sauti wanda basu taba ji ba a rayuwarsu kuma
sukaji yadda ake ambaton Allah da manzonsa a
cikin kiran Sallar daga can cikin kuryar daji sai
tsigar jikin kowa ta tashi suka fara jin cewa lallai
akwai alamun cewa wannan addinin shine addinin
gaskiya.Adaidai lokacin da sautin muryar kiran
sallar ta doki kunnen sarki Zaldasi yana kwance ne
akan doguwar kujera ta turakarsa don haka saiya
mike zaune zumbur a firgice yayin da zuciyarsa ta
kama dukan uku uku,dama kawai a kishingide yake
kawai cikin tsananin bakin ciki kuma zuciyarsa na
tafarfasa kamar zata kone bisa takaici da tunanin
yadda al'amara suka sauya farat daya a cikin
birninsa na gargajiya wanda suka gada tun iyaye
da kakanni.A fusace sarki Zaldasi ya zare
takobinsa saboda shi a tsammaninsa Jarumi
Hibairu ne ya shigo cikin birnin yana karanta
wannan kiran sallah.Koda ya fito daga cikin turakar
tasa ya iso cikin harabar gidan sarautar sai yaga
dakaru da hadiman gidan sun bishi da kallo cikin
mamaki don haka saiya nutsu ya dubi wani babban
hadimi nasa yace me ake ciki ne shin sarkin yaki
bai dawo bane daga aikin dana tura shi?Saboda
me kabar wannan shaidanin

1 Comments On SA MAZA GUDU 1 to 9
avatar
adamu-3

1 year ago

Reply

Masha Allah Allah ya Kara basira Aboki

Please Login or Register in order to submit comment