Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

miki har se in ya cika kudin mota" heedayah taji dadin wannan shawara sosai ahaka sukata sorting out abubuwa da dama daga karshe suka yanke hukuncin kai diffrent types of fruits kasuwan tunda aleesha na iya shiga cikin evil forest.
GARIN KANO; motar don moha na hango a unguwar su heedayah, anjima kadan yafito yayi tambaya yakuma komawa motan ya tuqa haka ya tayi har sanda Allah yakowasa gabar gdan su heedayah bayan kwanaki biyar da ya jera yana neman gdansu. Parking yayi a waje yayi knocking me gadi ya bude masa amman kwata kwata mal musa be gane don moha ba shide don moha be ce masa komi ba illa tambayar sa dayayi ko nan ne gdansu heedayah? Mal musa yace "eh nan ne saidai heedayahn batta nan yau kimanin sayi uku knan da batanta ba'a san inda take ba don moha yayi kamar besani ba ya tausayawa mal musa sannan yace "maman ta fa tna nan?" Mal musa ya gyada masa kai "kashiga daga ciki," don moha ya karisa a gaban entrance door din ya tsaya ya danna door bell bayan some seconds nanny ta taho ta bude saidai bata gane fuskar ba dan haka ta tsaya tana kallonsa daga bisani tace "dan saurayi wa kake nema?" Don moha yace "nanny?" Nanne nanny ta gano don moha ne takira sunansa da karfi harda hugging dinsa "yaushe a gari haka? Ashe Allah ze sake hadamu, kai gaskia ka girma sosai ai ban gane ka ba shigo shigo..."
[10/10, 4:40 PM] ๐Ÿฌ๐Ÿ›๐Ÿ’Salma๐Ÿ’๐Ÿ›๐Ÿฌ: ๐Ÿ‘ฎ๐Ÿ‘ฎ๐Ÿ‘ฉ๐Ÿ‘ฉ๐Ÿ’ฅ๐Ÿ’ฅ๐Ÿ’ฅ๐Ÿ’ฅ๐Ÿ’ฅ
HEEDAYAH!
๐Ÿ’ฅ๐Ÿ’ฅ๐Ÿ’ฅ๐Ÿ’ฅ๐Ÿ’ฅ๐Ÿ‘ฉ๐Ÿ‘ฉ๐Ÿ‘ฎ๐Ÿ‘ฎ
5โƒฃ4โƒฃ
written by miemie๐Ÿ‘„

Ya nemi gu akan sofa ya zauna nanny tace "don moha manyan gari, meya kawo ka gdan namu?" Don moha yace "gun mummy na zo," nanny tace "a minute ina zuwa," tare suka dawo da mummy, har qasa don moha ya durqushe ya gaishe da mummy ta amsa cikin fara'arta saidai kallo daya aka mata asan tana cikin tsaka mai wuya, bayan sun gama gaisawa da mummy tace "kode gun heedayah kazo? Ai heedayah batta nan ta bata yau kusan 3 weeks da batan ta knan" sekuma ta fashe da kuka, don moha yace "yi hkr mummy abinda yakawo ni knan nima," cikin rashin fahimta mummy tace "kamar ya knan son?" Don moha yace "nasan suwa suka yi kidnapping heedayah saidai ban san inda suka kaita ba but believe me xanyi iya kokarina in samo ta, inde tana raye," mummy tace "muhammad? Kace kasan suwa suka yi kidnapping heedayah ta?" Don moha ya gyada mata kai, mummy tace "suwaye ne dan Allah, tell me, tell me pls, kaji son?" don moha yama mummy qarya "nima sunce na kuskuara na gaya ma wani zasu kasheni but I assure you zamu samo heedayah sooner or later, akoi abinda nakeson ki sanarda ni mummy, tell me all that you knkw pls karki boye min komi," cikin rashin fahimata mummy tace "mene knan?" Don moha yace "yawancin kullum b4 ayi kidnapping heedayah se taje gdanmu dasunan tana neman abu, shin me take nima?" Mummy ta dafe qirji! "gdan ku fa kace muhammad?! Me zekai heedayah gdan ku innalillahi?" Don moha yace "calm down mummy tell me metake nima pls?" mummy tace "wallah tallahi muhammad bansan me heedayah take nema a gdanku ba I have no idea ma gdanku take zuwa kullum cemin take zata gdan frnd dinta" tacigaba da kukan da takeyi don moha yace "is okay bar kuka amman bakida idea ko kadan?" Mummy ta gyada kai, don moha yace "but me tsakaninsu da daddy? Naji ranan ya ambaci sunanta a waya yana cewa bani nayi kidnapping dinta ba," salati mummy kawai takeyi "muhammad na rasa me nayi wa daddy'nka ya gommaci ya riga sa rayuwata cikin matsala a koda yaushe," don moha yace "wacce erin matsala knan mummy? Me daddy ya miki feel free nd tell me pls," mummy ta goge hawayenta tace "babu son, dont mind me" don moha yata insisting amman mummy taqi gaya masa komi dan batasan tayi turning 'da akan mahaifinsa itade ta bukacesa da ya samo mata heedayahnta kawai, don moha yace "in shaa Allah I promise u this," seya bude baki ze gaya wa mummy kan cewa tun farko shi yafara kidnapping heedayah sekuma yayi shiru dakyar ya ce "mummy I need to tell you this," mummy tace "ina jinka son," nan don moha ya kwashe labarin komi yaba ma munmy, sabon kuka mummy tafara "muhammad mesa zakai haka? Mesa?" Don moha hkr de yake ba ma mummy yana neman gafararta amman takasa cewa komi daga bisani tace "na yafe maka muhammad amman dont ever try to do that again kome bekamata kayi kidnapping heedayah ba shes still a child to me kasan wherever she is 2day kaine silan komi muhammad mesa kayi haka?" Hkr still yake bata can ya miqe ze fice mummy tace "muhammad as u said daddy'nka has somethng to do with this is true cuz shekaru dayawa da suka wuce akoi sanda daddy'n heedayah baida lfya dan haka ya mallaka ma daddy'nka arzikinsa tas filayensa ne, companies dinsa harta gdaje da sunan sbd yayi trusting daddy'nka, da daddy'nka ya tashy saqa masa kuma seya dibe komi ma kansa harta gdanmu shi ya siyar mana that was the reason y muka bar gdan namu na unguwarku" bata ma gaya ma don moha prado inda ke gdansu da na heedayah bane dan kar abin yayi yawa. Atake don moha ya soma jin jiri "how can my dad be so evil? Mesa zeyi haka, why, why?" Hawaye yasoma yi mummy na lalashinsa bayan dayagama kukansa ya durqushe har qasa yana neman forgiveness na mummy on behalf of his father ji yake kamar ya kashe daddy'nsa "this means time da heedayah ta taba fada min "nice ride, kamar nawa wanda barayi suka sace min" she means wannan ne motar tatan, omg! Heedayah am terribly sorry if only kin gaya mun meke kaiki gdanmu nd me kke nema u could have been safe with ur family now, mesa kka gommaci boye min wannan muhimmiyar mgn, why heedayah? Can wata zuciya tace bcuz she loves u nd bata son ta raba ka da daddy'nka, don moha yace you should have told me still, kka sa akan gaskiyar ki na riga baki wahala I am so sorry heedayah pls forgive me I promise i'll make it up for you one day****
EDO STATE; kwanaki da dama sun ja yau kimanin 2 weeks knan, heedayah da aleesha se shiri sukeyi dake yau saturday ce akoi kasuwa, bayan sun gama shirin heedayah ta dauko basket of fruits din ta rike a hannu tace da aleesha "mu tafi ko?" Aleesha tace "yes 'yata" suka rufo hut nasu sannan suka fice tafiya me nisa sukayi sannan suka iso kasuwar cike yake da mutane dam wanda kowa harkan gabansa yakeyi, suka nemi gu suka ajiye basket nasu can wani kyakkyawan matashy fari sosai da ka gansa kaga igbo, bare gaza shekaru 26 ba, ga gashy nan ko ta ina sajen nan ya hade da 'yar gemun da yake tarawa, sanyaye yake cikin jeans da polo shirt red wanda ya amsa skin nasa, ga dukkan alamu yazo siyan kaya ne, ta gefen su heedayah ya tsiya ya siyo wata 'yar gyale kalan na tsofi haka dagani wa mamansa ne, heedayah de kallonsa takeyi suna hada ido ta sa da kanta qasa, wannan saurayi yayi murmushi tare da matsowa kusa da basket nasu heedayah "how much does this apple cost each? N50?" Heedayah taja tsuka mstw "'inyamuri da san banza, no its N200 da fuskar nan tata a tamke tana kallon gefe a ganinta wani erin iskanci ne zece mata apple N50 ai duda anan kudu apple ba tsada amman worth nasa yafi N50 mana saidai N100, saurayin yayi murmushi wanda ya sake fidda kyansa dimples nasa suka bayyana dan sarai yanji abinda tace yace "koh emmata?" Heedayah ta zaro dara daran idanunta dan koda wasa bata zata yana jin hausa ba sede data lura da kamanninfuskar sa siririya ce ba kamar na inyamurai me fadi ba, duk setaji kunya tafara kau da kai yasa hannu a aljihu yaciro wallet nasa ya miqa ma heedayah N400 ya dibi apple biyu heedayah na "hey, hey wait your change I was only kidding" yana jinta yaqi juyawa ya cigaba da tafiyarsa. Heedayah ta kalli aleesha tace baba kiga wannan guy din? Aleesha tace "lets be thankful yana da kudin ne," bayan shi mutane 'yan kadan ne wanda basu fi 3 ba suka dan sayi lemo shknan, heedayah bata ji dadin hakan ba amman aleesha ta kwantar mata da hankali
[10/10, 4:42 PM] ๐Ÿฌ๐Ÿ›๐Ÿ’Salma๐Ÿ’๐Ÿ›๐Ÿฌ: ๐Ÿ‘ฎ๐Ÿ‘ฎ๐Ÿ‘ฉ๐Ÿ‘ฉ๐Ÿ’ฅ๐Ÿ’ฅ๐Ÿ’ฅ๐Ÿ’ฅ๐Ÿ’ฅ
HEEDAYAH!
๐Ÿ’ฅ๐Ÿ’ฅ๐Ÿ’ฅ๐Ÿ’ฅ๐Ÿ’ฅ๐Ÿ‘ฉ๐Ÿ‘ฉ๐Ÿ‘ฎ๐Ÿ‘ฎ
5โƒฃ5โƒฃ
written by miemie๐Ÿ‘„

Ahaka har suka isa gdah, suka aza girkin rana heedayah har ynxu mamakin wancen guy din takeyi, "how is it even possible? N400 a zamanin nan, chab! He must be rich."
3 days later aleesha ta tashy da rashin lfya, batta jin dadi sosai dan haka taba heedayah bucket da ta je ta dibo musu ruwa acan gaba da evil forest, dan tasamu tayi curing kanta, haka heedayah ta soma takawa tayi tafiya medan nisa sannan ta iso gun famfon, da mutane dayawa dan haka itama tabi layi, daidai anzo kanta bayan ta ajiye bucket nata zata fara pumping ruwan knan, hannu kawai tagani kan nata meshi yace "let me" juyawanda zatayi suka hada ido hudu da guy na ranan wanda ya siye apples nata guda biyu kan N400 yau ma jeans ne da wata yellow T shirt a jikinsa tace "you! Again" yamata murmushi, pumping ruwan ya soma yi da hannu daya abinda mutane biyu keyi kokuma in mutum daya ma seyayi da qarfi da hannu bibbiyu, kallonsa kawai heedayah keyi yadda muscles na hannunsa ke going up nd down in yana pumping ruwan, yana gamawa ta matso zata daga yace "noo a princess like u is not allowed to carry a bucket full of water, let me" heedayah tace "am not a princess," guy din yace "you are to me, so where are u heading to?" Heedayah tace "argh! 'Inyamuri banda san banza harda maita mstw," sanda ta gama maganan a fili sannan ta tuna ashe yana jin hausa hannu biyu ta aza kan lips nata "omg! he must have heard me, what do I do now?" Dariya guy din yayi sosai ba qarya wannan lady is so funny, heedayah tace "gimmie my bucket, I have to go" yace "lets go" badan tana so ba suka soma tafiya tare yana riqe da bucket din bawanda yace ma wani ko uffan daga bisani guy din yace "princess whats ur name?" Heedayah tace "I don't have a name" guy din yayi murmushi sannan yace "well i'll say your name is Zainab? Aysha? Fatima? Maryam? Hafsat?..."se jero sunaye yakeyi, daga qasa qasa heedayah tace "duk maitab ka baraka taba iya guessing suna na ba," jin haka guy din yace "koh? Baran iya guessing sunanki ba?" Heedayah tace "eh!" Yace "lol okay na yarda u've won this, can u guess my name also?" Heedayah tasoma lissafo sunayan 'inyamurai kamar haka; ozioma? Osinaci? Emeka? Chika? Sopuluchi? Azuka? Chi.. Guy din yayi interrupting din heedayah "AZUKA! Thats my igbo name, my islamic name is RAYYAN, you really are intelligent, kin iya kinyi guessing name dina ni nakasa," seya bama heedayah dariya yadda yake maganan kamar yaro tace "dont be such a girl, suna na HEEDAYAH!...Kace ur islamic name is rayyan?" Ya gyada mata kai daga can kasa tace "toh dama 'inyamuran nan akoi muslims ne?" Jin haka rayyan yace "yes princess, what a nice name heedayah! But what is the meaning?" Can qasa qasa heedayah tace "ohh ni wannan inyamuri kacika surutu" ashe gogan namu kan yaji ta yace "toh shknan nayi shiru," abin yabama heedayah mamaki kowani magna tayi a hankali seyaji wani erin kunne ne dashy? Tace "heedayah means guidance (kaariya)" rayyan yace "excellent starting today u'll be my guider(me bada kariya)" tadau a zuci take mgna tace "koba guider ba, dan rainin sense nida kai wa ze guiding wani?" Ashe kam a fili tayi maganan rayyan can't help it ynxu kam dariya yakeyi sosai, heedayah tace "wai nikam meka maidani sekace mahaukaciya daga nayi mgn ka tsaya kana min dariya, pass me my bucket i'll walk it frm here" rayyan yace "sorry princess..." heedayah ta katse sa "nifa na gaya maka am not a princess" Rayyan yace "pardon me, so tell me where are you frm sbd frm all seeing keba yar nan bace," heedayah tayi kmr bata jisa ba rayyan yace "hello?" Nan ne tace "eh ni ba 'yar nan bace am frm maiduguri state," rayyan yace "so its true dama ance 'yan maiduguri are slim and beautiful so are you," heedayah ta masa murmushi yace "yes princess ina jinki what brought u to our land, the igbo land?" Heedayah tace "am not telling you" rayyan yace "haba princess plsssss lets find somewhere nd sit" heedayah zatayi mgn yace "shhh" akan wata dutse suka zauna gaba da evil forest, ya ajiye bucket din agefensa sanan yace "ina jinki princess" heedayah taja numfashi sannan tafara basa labarinta kamar yadda taba ma aleesha...tana gamawa tace "kaji abinda ya kawoni igbo land knan"...rayyan yace "what a pitiful life you've lived, don moha da daddy'nsa have to pay for everythng," heedayah tace "in shaa Allah nd thats why nake nemar hanyan da zanyi in fita daga nan inje in qarisa karatu na inyi taking revenge," rayyan yayi sjiru heedayah tace "lfya?" Rayyan yace "its not as simple as u see kinga har yau elders namu sunqi gaya mana sunan wannan waje da muke, we are just living like this taya zaki iya barin nan harkisan where u are heading to?" Heedayah tace zanyi whatever it takes, rayyan yace "me too I'll do whatever it takes inga kinyi taking revenge naki heedayah, i'll help u whenever u needed any help," heedayah tace "thank you, kaifa? Tell me about yourself too," rayyan yace "ready?" Heedayah ta gyada masa kai tare da yin murmushi yace "mahaifina is an igbo man whereas mahaifiyata kuma fulani," heedayah kallonsa take cikin rashin fahimta, yace "I know u must be confused Ko? Taya fulani da igbo zasui aure? Kar kidamu zakiji komi" yacigaba...
[10/10, 4:43 PM] ๐Ÿฌ๐Ÿ›๐Ÿ’Salma๐Ÿ’๐Ÿ›๐Ÿฌ: ๐Ÿ‘ฎ๐Ÿ‘ฎ๐Ÿ‘ฉ๐Ÿ‘ฉ๐Ÿ’ฅ๐Ÿ’ฅ๐Ÿ’ฅ๐Ÿ’ฅ๐Ÿ’ฅ
HEEDAYAH!
๐Ÿ’ฅ๐Ÿ’ฅ๐Ÿ’ฅ๐Ÿ’ฅ๐Ÿ’ฅ๐Ÿ‘ฉ๐Ÿ‘ฉ๐Ÿ‘ฎ๐Ÿ‘ฎ
5โƒฃ6โƒฃ
written by miemie๐Ÿ‘„

"Shekaru dayawa da suka wuce there was a time grandfather na da father na suka jesu yola neman wani magani da zeyi healing rashin lfyar grandmother na wanda a yola kawai ake samun maganin bayan sun iso wata qauye mesuna FUFORE, duk fulanin garin suka ki accepting nasu, kinsan fulani da kishin addini da al'ada sanda grandpa ya musu bayani kan muslims ne su amman daga kudu can, still wadannan mutane sunqi basu mazauni, da kyar sukka sami wani fulani me mutunci wanda ya kaisu gdansa inda suka sauka for the meantime, acan ne father na ya hadu da lovely daughtern wannan fulani wanda soyayya me karfi ya shiga tsakaninsu within just one week, sunyi sati sannan suka samu abinda suke nema akan washegary zasu koma nan igbo land, daddy na yasamu mahaifinsa ya gaya masa what is on his mind, mahaifinsa ya masa bayanin komi kan fulanies basu aura ma 'ya''yansu bare wanda ba fulani ba so tun wuri daddy na yacire soyayyan wannan budurwa, amman ina my dad was blinded with her love yace ma mahaifinsa in har bara a daura musu aure ba ze kashe kansa, mahaifinsa kuwa na bala'in sansa he cant lose his only child dan haka yaje yasamu baban mami na ya gaya masa halin da ake ciki, granpa yace masa hakan bame yuwa bane sbd kaga har miji hajjo(mum din rayyan) tanada nd ko ba dan haka ba elders namu sun haramta mana aurar da 'ya'yayenmu ma bare, grandfather na yayi yayi dashy amman ina wannan fulani yaki yarda haka yaje yasamu daddy na ya irga masa yadda sukayi da abban hajjo, jinsa kawai daddy na yayi amman shikam sun riga sunyi planning abinsu da hajjo kan zasu gudu, acikin daren ranan suka gudu da mami, da safe aka nemesu aka rasa su haka grandfather na yakoma igbo land shi kadai a yayinda daddy na da hajjo kuma suka bar garin yola to yobe state acan suka nemi imam da waliyinsu da shaidu wanda basu fi 4 ba aka daura musu aure kan sadaki N500 ko gdan da zasu zauna babu, acikin ikon Allah daddy na ya fara sana'a Allah yata masa budi har suka gina gdan kansu amman na qasa" heedayah tace "how cute ina jinka," yacigaba "a shekaransu na biyu da aure ne Allah ya albarkacesu da angel like me," heedayah tace "lol kai dinne angel? Comot frm here," yayi dariya sannn ya cigaba, "shekaruna uku aka min qanwa igbo name nata AMARACHI whereas islamic name nata ALEEYA," heedayah tayi interrupting nasa "so kanada sister?" Ya gyada mata kai sannan ya cigaba "bayan shekaru biyu da haifan aleeya parents dina sukyi deciding komawa gun parents nasu for thier blessings, yola suka fara zuwa inda fulanin garin su mum dina suka masu koran kare aciki harda abbanta, they've got only one hope ynxu shine su je igbo land, daddy na was sure bara a koresu ba cuz babansa qanin sarkin garin ne, motan kasuwa suka shiga ,sukayi tafiya me nisa sannan suka iso Edo state," heedayah tace "Edo state? Kace bakasan sunan inda muke ba, nd just now kace nan Edo state," rayyan yace "we are nomore leaving in Edo state before ne muke can kafin aka sami misunderstanding btw elders namu muka bar garin Edo batareda munsan inda muke zuwa ba har Allah ya kawomu nan," heedayah tace "but still ai zaku iya komawa Edo'n?" Rayyan yace "we are forbidden to, duk wanda yakoma penalty din is death!" Heedayah taja baki tayi shiru, rayyan ya cigaba; "daddy na yakawo mu family house nasu inda kowa ya ganmu seya sha mamaki, dakin mahaifinsa ya shige damu mahaifinsa yaji dadin ganinsa yayi blessing marriage nasu ya daddauke mu yakai mu gaban Igwe(sarki) shima yabamu blessings nasa, mutane sunajin mami ba igbo bace fulani ce suka fara qananun maganganu su basu so, haka mgn yazama big talk har ya kaiga dole muda king namu mu bar garin EDO state hakan kuwa akayi muka tattara komin mu muka dawo nan inda bawanda yasan sunan wajen sede aji rumor cewa igwe yasani amman yace bare fada ma kowa ba..., kinji history dinmu knan tare da ma heedayah murmushi, heedayah tace "wow kunyi experiencing alot so u've never attended sch?" Rayyan ya gyada mata kai tace "but how come..." kafin ta gama rayya ya katse ta "how comes na iya turenci?" Heedayah ta gyada kai yace "my dad taught me well, nida sister na," heedayah tace "thats sweet" nanne ta tuna aleesha ta aike ta dibo ruwa ta zabura "ina bucket din? Baba zatayi pepper soup dani," rayyan yace "whats going on?" Heedayah tace "I need to go now, baba nata jiran ruwan," rayyan yace "lets go" suna tafiya suna hira har suka isa hut nasu heedayah ya ajiye mata bucket din sannan yamata ba baye itama ta masa sannan ya fice, ta bude kofar tana "baba ga ruwan nan" da dubanta kan inda baba ta kwanta taga ba kowa dan haka tafito can taga baba kamar ba ita ke kwance daxu ba lfya ba, ta jira ta iso sannan tace "baba ya haka? Kin warke knan? Ga ruwa fa nakowo," aleesha tadan bugeta da karan hannunta "naughty girl xan jira ki ne? Kinje kina hira da prince charming kin barni anan, na iya nayi using magic nayi curing kaina," heedayah ta soma sosa keya taya aleesha tasani? Can ta tuna ashe tanada magic, tace "baba! Bafa prince charming bane he's not even my frnd, wanda yasayi apples N400 dincan nefa..." aleeaha tayi dariya irin tasu ta tsofi sannan tace "we'll soon find out koba prince charming din bane" ta wuce ciki heedayah tabi bayanta suka soma cin abinci
[10/10, 4:43 PM] ๐Ÿฌ๐Ÿ›๐Ÿ’Salma๐Ÿ’๐Ÿ›๐Ÿฌ: ๐Ÿ‘ฎ๐Ÿ‘ฎ๐Ÿ‘ฉ๐Ÿ‘ฉ๐Ÿ’ฅ๐Ÿ’ฅ๐Ÿ’ฅ๐Ÿ’ฅ๐Ÿ’ฅ
HEEDAYAH!
๐Ÿ’ฅ๐Ÿ’ฅ๐Ÿ’ฅ๐Ÿ’ฅ๐Ÿ’ฅ๐Ÿ‘ฉ๐Ÿ‘ฉ๐Ÿ‘ฎ๐Ÿ‘ฎ
5โƒฃ7โƒฃ
written by miemie๐Ÿ‘„

KANO STATE; Yau kimanin sati buyu da kwanaki knan, don moha yabar gda bekuma leqawa bakuma, se shirya kayakinsa yake da alama komawa zeyi yau bayan ya gama ya dau wayarsa ya kira mama, bugu daya ta daga "hello muhammad? Ya kake? Ina kake? Ka dawo gda pls," don moha yace "calm down mama ynxunnan zan dawo," mama tace "really? Muhammad zaka dawo? Ina kake inje in dauko ka?" don moha yace "kar ki damu mama in the next 25-30mins zan shigo," mama tace "toh Allah kare muhammad sekazo ko?" Ya katse wayar yaja trolley'nsa ya nufa gun biyan bills bayan ya biya ya hau hanya. Mama taje tasamu alhj ismail se murna takeyi, "alhj ynxu muhammad ya kira," alhj ismail yace "meyace? Ina yake?" Mama tace "yana hanya ma ynxu ze dawo gda!" Alhj ismail ya miqe tare da fadin "alhamdulillah dauko mayafinki muje mu siyo masa favorite dishes nasa," mama ta amsa da "toh" nan da nan ta shirya tafito suka wuce wata eatery inda suka siyo duk wani favorite abincin da don moha yakeso sannan suka nufa gda aka kintsa masa dakinsa tsaf sannan aka jera abincin kan dining kowa ya shirya yana jiran zuwansa ciki harda baba me gadi, bayan 10mins akayi honk a bakin gate baba me gadi ya karisa ya bude motar don moha suka hango bayan yayi parking yafito mummy ta qarisa dagudu tayi hugging dinsa haka daddy da safyan ma, safyan ya ciro masa jakarsa daga booth suka nufi site nasu, mummy kamar ta cinye don moha dan wani kyau da fresh daya qara, ya shiga bathroom ya watsa ruwa sannan yafito sukaci abinci dukansu bayan sungama daddy yace "muhammad inason mui mgn," don moha ji yake kamar ya kashe daddy dabanda yana planning wani abu bama da ba abinda zaisa ya dawo gda daga bisani yace "ok," suka fice zuwa garden suka zauna daddy yace "muhammad am sorry, am so sorry if only nasan inda heedayah take da na sa andawo da ita," cikin rashin fahimta don moha yace "taya zaka ce baka san inda take ba? Ba kai ka tura a dauketa ba?" Daddy yace "bani bane muhammad," don moha yasake shiga cikin duhu, "ba kai ba? Then waye?" Se alhj ismail ya bude baki zeyi mgn sekuma ya kasa, don moha ya gano hakan yace "shknan daddy na gane mesa kasa aka dauketan we don't have to talk about it any further" ya mike ni zan shiga daga ciki ya fice dakinsa ya nufa sannan ya kwanta kan gado ya zura wa ceiling ido, "why is my brain not thinking fast? Mesa na kasa figuring me heedayah ke nema a dakin daddy?" ya juya yana kallon gefe, "i have to find out bari daddy ya fita sallan la'asar"
Bayan fitar daddy sallan la'asar don moha ya shiga dakinsa yayi locking sannan yafara bibiya yana neman abinda besan meyake nema ba, can hannunsa yakai gun da daddy ke ajiye files nasa ya duba tas yaga duk files na daddy ne wannan to ina wannan tsohon ze kai files na daddy'n heedayah badan yana so ba ya fice daga dakin har ya kai bakin kofar dakinsa seya jiyo muryan daddy da alhj lawal

Please Login or Register in order to submit comment