Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

daga dakin shams na biye da ita suna kaiwa bakin kofar parlour sukayi sallama heedayah na kaiwa bakin gate din ta bude tasa kai zata fita knan alokacin don moha ke dawo wa daga 'yar yawonsa shima yasa kai ze shiga karo sukayi "duum!" Se awch kowa yakeyi kafin ya daga ido ya kalli ko wace wannan heedayah ta matsa da sauri ta fita dan kar ya ganeta, juyowa yayi yana binta da kallo se gani yake kamar ya taba ganinta kokuma kamar ya santa da hannunsa kan goshinsa se gurza wajen yakeyi ya karasa gun baba megadi yace "baba wace wancan?" Baba yace "wace don moha" (se dadi yakeji yau ya kira sunan don moha batareda an samu matsala ba) don moha yayi smiling sannan yace "wacce tashigo gdan nan yau" baba yace "nima bansanta ba amman de qawar sabuwar me aikinku ne" don moha yace "anyi sabuwar me aiki ne a gdan?" Baba yace "eh wai shams sunanta" don moha ya nanata sunan *shams* sannan yace "okay" side nasu mama ya zarce. Heedayah kuwa tun shigarta mota take ta maida numfashi dan ba qaramin tsorata tayi ba ynxu da mistakenkly sunglasses nata ya fadi shknan asirinta ze tonu "gaskia i have to be very careful" tafada ta bude mirror din motar tana kallon goshinta inda suka ci karo da don moha a zuciya tace "don moha is cute, infact he's hot! jibi yadda turarensa yakama jikina (tahau shinshina jikinta) omg! kuma yanada packs, tana murmushi wa kanta tana kallon face nata a mirror din. Don moha na shiga side nasu mama ya zauna kan sofa a parlour ya kwalla wa shams kira "shams kke ko me come here!" Shams tafito tana ware ido tanemi gu ta zauna a qasa "naam yallaboi" a zuci kuwa admiring kyan don moha kawai take how can he be so handsome like this! bayan dayagama qare mata kallo, kallon ma na rashin isa da rainin wayo dan ba lie don moha baida mutunci ko kadan(lol) yace "kece shams din knan I guess" jiki na rawa tace "eh nice" yace "who just left this house some minutes ago?" Wayyo zan so kuga mutumiyar atake ta soma jin fitsari duk ta rude tace "yanzu?" Don moha yace "I guess am not talking to a deaf person" shams tace "aww qawata ce" don moha yace "I see, meh sunanta?" Sanda shams tadan sake fitsari kadan a panties nata dan yadda ta rude takuma kasa amsa mar, don moha yace "hello? Sunan frnd nakin ne baki sani ba?" Jiki na qyarma tace "a..a..aysha sunanta" ta kirkiro murmushi don moha yayi shiru for a while yafara mgn a hankali kaman me magana ma kansa "ohh maybe kama ne ko yanayi" shams tace "naam yallaboi?" Don moha ya kafa idanunsa akanta yakuma kallon ta da kyau kusan na 2mins sannan yayi 'yar murmushinsa me kara masa kyau ya tashy ya fice, kasa motsi shams tayi jikinta duk ya mutu bisa kallon da don moha yamata ni miemie nace "ji banza koke shams ki kalli don moha ki kalli kanki kun dace?"
[10/10, 2:22 PM] ๐Ÿฌ๐Ÿ›๐Ÿ’Salma๐Ÿ’๐Ÿ›๐Ÿฌ: ๐Ÿ‘ฎ๐Ÿ‘ฎ๐Ÿ‘ฉ๐Ÿ‘ฉ๐Ÿ’ฅ๐Ÿ’ฅ๐Ÿ’ฅ๐Ÿ’ฅ๐Ÿ’ฅ
HEEDAYAH!
๐Ÿ’ฅ๐Ÿ’ฅ๐Ÿ’ฅ๐Ÿ’ฅ๐Ÿ’ฅ๐Ÿ‘ฉ๐Ÿ‘ฉ๐Ÿ‘ฎ๐Ÿ‘ฎ
3โƒฃ4โƒฃ
written by miemie๐Ÿ‘„

Heedayah na isa gda ta nufi dakinta ta watsa ruwa da towel ajikinta ta miqe kan gado ta dau kayarta ta kai hanci a dole ita tana jin qamshin turaren don moha can tayi wurgi da kayan ta zabura tafara magana wa kanta "what is happening to me? Why am I acting strange? Son don moha nake ne? Hell noo ai inna bari sansa ya shiga zuciyata he will weaken me nd baran iya daukan revenge dina against his father ba, i have to be strong" nan ta mike ta dau kayanta tajeta gun washing machine tasa a ciki ta wanke tayi draining sannan tafita shanyawa tana dawowa taga wayarta na kawo wuta alamar ringing dake phone din na silent, tana dagawa call din ta tsinke daman shams ke kiranta nan tayi calling back shams ta daga heedayah tace "hello shams?" Shams tace "heedayah nikam ko kinsan yaron gdan danake aiki, babban yaron gdan muhammad?" Heedayah tace "lafiya meya faru? Why asking?" Shams tace "ko cikakken 2mins da tafiyar beyi ba muhammad din yazo yafara jero min tambayoyi..." tade irga ma heedayah duk yadda sukayi da don moha, heedayah ta mugun tsorata tace "what u did was right kar ki kuskura ki gaya masa true identity na koda me ze faru, kinji ai?" Shams ta gyada kai kamar heedayah na gabanta sannan tace "toh shknan amman nikam heedayah me hadinku dasu muh'd? me kke nema a gdansu? nd me reason naki na sani neman aiki a gdansu? Kinga muna aiki as a team bekamata muna boye wa juna komi ba, tell me" heedayah tace "I know, karki damu u'll find out everything later ynxu de u shud just stick to our plan okay?" Shams tace "toh se anjima" ta katse wayar. Heedayah ta nemi gu ta zauna akan sofa dake dakinta tace "from all seeing wannan shams ba mutuniyar arziki bane ko dashike kar inyi concluding komi zamu cigaba da aiki tare da ita inga iya gudun ruwanta, waima tukunna why is she so curious tasan me hadi na da gdansu don moha?...haka tata sake sake a zuciyarta****
Tun daga ranan da don moha yayi clashing da heedayah wanda yake ma kallon qawar shams me suna aysha, ya jera 3days yana expecting ko zata sake zuwa gdan, anytime 2:00pm yayi seya zauna a garden yana jiran shigowarta amman ko inuwanta bai kuma gani ba dan haka yasake komawa gun shams ya sameta tana share parlour bata ma gansa ba sanda yadanyi gyaran murya sannan ta juyo tana ganin don moha ne wato man crush nata(lol) ta kidime ita kadai "ina wuni yallaboi?" Don moha yayi shiru for a while sannan yace "call me don moha" shams baki na rawa tace "ina wuni don moha?" Ya amsa da "fine, nikam ina friend naki na ranan dinnan?" Shams ta kasa cewa komi sewani admiring don moha take tana masa kallon soyayya, don moha yace "ke are u at all alright? Taya ina miki mgn zakimun shiru do u know who I am? U shud be thankful ma ina miki mgna mstw nd stop looking at me that way" wani kyau ma don moha yake qara yiwa shams ita bama masifan san takeji ba, don moha kamar yasa hannu akai yayi ihu wannan wace erin yarinya ne ko batada cikakken hankali ne? Don moha yace "helllooo?" Nanne shams ta dawo daga duniyar tunanin da ta tafi tace "na'am me kace?" Don moha yaja wata tsuka "seriously?" Yakama hanyan fita shams ta jefar da tsintsiyar hannunta tasha gabansa "yi hkr dan Allah kar kayi fushi dani wlh nafada cikin duniyar tunani ne yi hkr meka ce dan Allah?" Don moha yatsaya kallon ikon Allah sannan yace "ke aljana ce? Are u crazy??" Shams tayi murmushi sannan tace a zuciya "baran ce kayi qarya ba na yarda am crazy, crazy in love with u" nan ta bar zancen zuci tace "a'a yi hkr" don moha ya tsaya yana mata wata erin kallo na rashin isa sannan yace a zuci "if only not bcuz am desperate insan wace frnd nakin can xan ma miki mgn ne? Dirty pig dake" yace a fili "ina frnd naki na ranan?" Shams tace tana nan, lafya?" Don moha yace "call her kice tazo inason ganinta" shams tarasa qaryan dazata qirqira baki na rawa tace "ai tayi tafiya saisa kwana biyu bata zuwa" don moha yace "I see in ta dawo lemmi know inason insan wace ita tamin kama da someone special I know" yana kaiwa nan ya fice. Wata kishi taji ya tokareta a zuci "me wannan don moha yake meaning? yana son heedayah ko me? Kai qarya ne kawai kama ta masa da wata dan ai heedayah tace mun bata san sa ba" takoma kan aikinta ta cigaba da shara. Tana gamawa ta dau wayarta ta kira heedayah ta irga mata yadda sukayi da don moha heedayah tace "don't mind him be wani san niba qarya kawai yake dama an sha gaya mun yaron gdan akoi sa da san mata sbd haka karki wani ta da hankalinki kinji ai?" Shams tace "aikaman nasani besan kibba halan kama kka masa da wata kawai, se anj..." Heedayah ta katse ta "wait! Kince masa nayi tafiya ko?" Shams tace "eh" heedayah tace "good but one thing nasan bada jimawa ba ze sake tambayar ki ko na dawo daga tafiyar danayi, in har kkace masa a'a zece to kibasa number na kinsan me zakiyi? Shams tace "a'a sekin fada" heedayah tace "kibasa number frnd dina zainab, i'll talk to her too" shams tace "toh shiknan ba matsala se anjima" ta katse wayar nan da nan heedayah ta kira zainab ta irga mata komi dakuma yadda zatayi reacting incase don moha ya kirata tace "noted frnd anything for u" heedayah tamata godiya sannan tayi hanging up call din.
One week later! don moha nata jiran mssg frm shams amman shiru shikuma he's so so desperate yasan waye wancan yarinyan da sukaci karo da ita. Seya tashy zasa site nasu mummy dan tambayo shams ko frnd natan tadawo se yakoma ya zauna cuz anytime ya tuna da craziness erin na shams seya ji bare iya zuwa mata mgn ba shi ba abinda ya wasa kamar irin kallon da take masa da kyar ya iya yyi gathering confidence ya tashy ya nufa side nasu mummy ya sameta tana goge dinning table kafin yyi gyaran murya ta juyo tare da fadin "ina wuni don moha?" Yawani bata rai be amsata ba, takuma cewa "ko kana mamakin yadda nagane kana nan ba tare da ka gaya mun bane? Well kar ka damu qamshin turarenka me dadin gaske ne ya buga min hanci" tare da masa wata shu'umar murmushi, fuskar nan nasa kamar wanda zeyi kuka shi besan meyama yarinyan nan take masa haka ba, ji yake kamar yasa hannu aka yayi ihu tsaki yaja sannan ya juya ze koma inda yafito dan yama fasa mata maganar
[10/10, 2:22 PM] ๐Ÿฌ๐Ÿ›๐Ÿ’Salma๐Ÿ’๐Ÿ›๐Ÿฌ: ๐Ÿ‘ฎ๐Ÿ‘ฎ๐Ÿ‘ฉ๐Ÿ‘ฉ๐Ÿ’ฅ๐Ÿ’ฅ๐Ÿ’ฅ๐Ÿ’ฅ๐Ÿ’ฅ
HEEDAYAH!
๐Ÿ’ฅ๐Ÿ’ฅ๐Ÿ’ฅ๐Ÿ’ฅ๐Ÿ’ฅ๐Ÿ‘ฉ๐Ÿ‘ฉ๐Ÿ‘ฎ๐Ÿ‘ฎ
3โƒฃ5โƒฃ
written by miemie๐Ÿ‘„

Shams na ganin haka ta ajiye towel dake hannunta tasha gabansa "yi hakr in abinda na fada ya bata maka rai, bana son ganin bacin ranka" cikin tsawa don moha ke mgn "that tears it now! Enough of this nonsense in bakida sense to ni inada, maza pack ur bellongings kibar gdan nan na sallameki wacce erin sakariya ce ke?" Shams harda durqushewa a qasa tana kuka tana bama don moha hkr yayi banza da ita tsallaketa yyi ze wuce ta cafko kafarsa tana hada sa da Allah badan yayi niyya ba yace "naji disappear frm here" ta miqe tare da fadin "nagode sosai nasan meya kawoka, batun friend dinanne aysha ko? To har ynxu bata dawo daga tafiyar datai ba sede ga number inta in kanaso seka kirata" don moha yace a zuci "lalle yarinyan nan har kinsan meya kawoni wato, well fine to banaso" a fili yace "haka clueless mind naki ya gaya miki? To bashy ya kawoni ba keep ur number with u" yakama hanya yana tafiya shams tace "dan Allah kayi hkr ka karba kaifa da bakinka kace tamaka kama da someone special u know" don moha ya tsaya cak sannan ya juyo yace "ina number din?" jikinta na rawa ta jeta gun dining ta dau wayarta ta shiga contact list tayi scrolling kan aysha da tai saving ranan ta miqa masa ya amsa ya copying acikin wayarsa ko thanks bece mata ba ya fice, shams se murna take ita a dole man crush nata ya amsa abu gunta, haka tagama aikin ta ranan cikin walwala da jin dadi tana gamawa ta wuce gda inda ta kira heedayah ta gaya mata yadda sukayi da don moha, heedayah tace "aikinki na kyau keep it up!" Tayi hanging call din ta kira frnd nata zainab, bayan sun gaisa take tambayarta "don moha din ta kiraki kuwa?" Zainab tace "a'a be kiraba" heedayah tace "toh ki aje wayarki kusa dake yakusan kiranki" ahaka sukayi sallama. Don moha na kishingide a dakinsa akan gado ya miqa hannu ya dau wayarsa dake kan side drawer'n side dayake kwance ya kai daidai kan contact da ya amsa gun shams wanda yayi saving da aysha seya fara dialing se ya katse dan shegen girman kai irin nasa haka yatayi at last de yasamu ya yi dialing sanda ya kusan tsinkewa sannan zainab ta daga tayi shiru dan haka don moha yace "hello?" Zainab on the other side tace "yes hello" don moha yace "am I speaking with aysha pls?" Zainab tace "yes, aysha c" yace "good, I can't actually remember the exact day but in xaki iya tunawa there was a day kkayi visiting frnd naki shams a gidan aikinta kinxo fita mukayi bombing into each other, remember?" Zainab tace "ohh yes haka so kaine dude din daya kusan fasa min goishi knan?" Don moha yayi smiling sannan yace "sorry..." nande ya fada mata abinda yake tattare dashy bayan yagama mata bayani zainab tace "ayyah kama ne kawai danni kam i don't know u ko a ynxu akace min ya kamanninka yake baran iya fada ba, kama ne kawai bansan wata heedayah ba nd ni suna na aysha ne" don moha yace "okay toh shiknan thanks kafin ta sake mgn yayi hanging up call din, sede har ynxu yakasa believing dan har ynxu conciousness nasa cemasa yake heedayah yagani amman abun daya keta tambayan kansa shine in heedayahn ne me xai kawota gdanmu? Nd taya zatayi frndship da wancan shams din? Gaskia shes not the one kama ne kawai. Yasa hannu yayi deleting number zainab wanda yyi saving da aysha. Ya shiga gallery yakai kan picture'n heedayah yayi zooming iya face nata yatsaya admiring picture din kamar yadda yasaba a hankali yake mgn "where ever you are heedayah know that I love you nd I will nva rest until the day u become my wife"
Washe gari! Heedayah na zaune da mummy a parlour tare da daddy se hira sukeyi su na dan kallo mummy tace "nikam heedayah se yaushe kuma zaku koma sch ne?" Heedayah tace "wani sch kuma mummy?" Mummy tace "NIGERIAN LAW SCHOOL din mana ba a can bane zaki zama prosecutor din?" Heedayah tace "aww eh se nxt year, xamu danyi hutun one year ai kaminnan mu shiga wancan din" mummy tace "ohh toh Allah taimaka amman nifa kinsan kwata kwata banso wannan idea bako? Tsufa zakiyi a boko wlh ynxu u are 21 akara hutun one year naku 22 + 4yrs da zakiyi acan NIGERIAN LAW SCH din aikingama tsufa knan" heedayah tayi murmushi sannan tace "mummy kenan nikoda it'll take me 100yrs ne I don't care is my duty to revenge for my daddy" mummy tace "toh ni dama kinfi karfita amman Allah sa hakan shiyafi alheri" heedayah tace "yawwa kokefa mummy ta? Ameen" wayarta ce ta soma ringing tana ganin wake kiraan ta miqe da sauri zata haura sama dakinta mummy ta kalleta tayi murmushi a zatonta saurayi ke kiran heedayah (lol) heedayah na kaiwa dakinta ta daga "hello shams? Ya akayi?" Shams tace "heedayah kina lfya? Ki taho ynxu ba kowa a gdan" heedayah tace "to to gani nan zuwa" nan da nan ta canza night gown dake jikinta ko wanka batai ba tadan kwaskware ta fito, mummy tace "ina zuwa haka heedayah da safennan? Karfe 10:30AM nefa ynxu, heedayah tace "gdan frnd dina mummy batada lfya" mummy tace "Allah sa dagaske kke ba qarya ba"



[10/10, 2:25 PM] ๐Ÿฌ๐Ÿ›๐Ÿ’Salma๐Ÿ’๐Ÿ›๐Ÿฌ: ๐Ÿ‘ฎ๐Ÿ‘ฎ๐Ÿ‘ฉ๐Ÿ‘ฉ๐Ÿ’ฅ๐Ÿ’ฅ๐Ÿ’ฅ๐Ÿ’ฅ๐Ÿ’ฅ
HEEDAYAH!
๐Ÿ’ฅ๐Ÿ’ฅ๐Ÿ’ฅ๐Ÿ’ฅ๐Ÿ’ฅ๐Ÿ‘ฉ๐Ÿ‘ฉ๐Ÿ‘ฎ๐Ÿ‘ฎ
3โƒฃ6โƒฃ
written by miemie๐Ÿ‘„

Heedayah tayi murmushi sosai "kai mummy what where u thinking?" Kafin mummy tace komi heedayay tayi waving hand wa daddy ta fice, motarta ta shige me gadi ya bude mata gate ta nufa gdan su don moha straight tayi parking a corner yadda ta saba yau kam harda niqab nata, kafin tafito daga motar ta sa yau kam ba baba megadi ma a bakin gate din dan haka ta shiga hankalinta a kwance a parlour ta tarar da shams, tace "bini" suka shige dakin alhj ismail yauma shams na labe a bakin kofa da tsintsiya a hannunta, haka heedayah tayi duban duniyan nan bataga wannan cctv datake nema ba can ta hakura tace zata duba dakin mamansu ko ya kai can, shams tace da ta bari se gbe dan kar a kamasu hakan kuwa akayi har heedayah ta fice daga gdan ba wanda ya ganta ko me gadi ma. The nxt day again shams tamata waya da ta xo ba kowa a gdan haka tasake shiri taje da niqab nata saidai yau batayi parking motartan a inda ta saba ba tadan fito da ita daga corner din cuz anyi packing wata mota a inda tasaba parking natan abakin gate suka hadu da me gadi ta gaishesa tare da fada masa "aysha ce ta ranan frnd na shams" suka dan gaisa sannan ta shige yau dakin mama suka shiga tayi searching din duniya still shima bata samu ba har cikin pillow sanda ta dudduba duk wayam! Ba komi tayi kusan 25mins a gdan sannan shams tace mata da ta tafi kar aka musu, taqi ita wai a dole se ta samu abinda take nema sanda ta kara 10mins a gdan sannan ta yarda zata tafi har ta fita daga gdan, bayan ta ja gate ta rufe juywanda tayi suka hada ido hudu ita da don moha sun kusan 30seconds suna kallon juna sannan tace "sorry" ta matsa gun da sauri tayi gun motarta ta bude ta shiga ta fice da gudu don moha yace DH836โ€ขLSR (wato plate number in motan ya karanta knan) yakuma nanatawa yadda bare manta ba sannan ya shige ciki suka hadu da baba megadi, yace "baba wace wannan kuma?" Baba yace "ahh don moha ka dawo ne? Ai kawar shams ce aysha" don moha yace "I knew it!" Da karfi "Nasan yarinyan nan dole nasanta but I don't know a ina" site nasu mama ya nufa bega shams a parlour ba haka ma a dining space dan haka ya kira sunanta ta amsa nan da nan tabar du abinda takeyi ta fito "ina kwana?" Yace "ya kke black beauty?" Wayyo zokuga washe baki gun mutumiyar sekace an mata albishir da shiga aljanna tace "lfy qlou" hakwaran nan kamar me tallen maclean azuci don moha yace "mumu am jez using u" yace "ynxu frnd naki aysha ta baro nan ko?" Shams tace "eh ko kun hadu ne?" Don moha ya gyada mata kai tare da mata wannan shegyar murmushinsan mesa mata falling masa yace "ko zaki iya kiranta kice mata tazo gbe? Inason in saba da ita naga she's calm jez like u" shams tayi shiru for a while don moha yace "common shams don't you trust me?" Tare da mata wink mutumiyar bata san sanda tace "toh zan kirata" ba, don moha yace "yawwa black beauty but fa karkice mata i asked u to do so, kinji ko?" Giada kai kawai take kamar shashasha koda shike daman shashashan ce. Don moha yace "yawwa kira ta toh ynxu karki manta anjima" shams tace "kar kadamu har zaka sani abu inqiyi ko ince na manta kasan bazata yu ba" don moha yace "nasani kawai de ki kira min ta ynxun" tayi shiru dan tarasa me zatayi ita harga Allah tana mutuwan son don moha she can do anything dan ya sota tunani kuma take taya zataci amann heedayah, haka de shedan yata mata wasa da yar hankalinta daga qarshe ta yarda biya wa don moha buqatarsa dan shashanci don moha yace "aw baraki kira min itanba knan?" Shams tace "toh me zaka min in na kira maka ita?" Don moha yace "ko me kkeso" ta washa hakwara sannan tace "dgsk?" Don moha yace "sure my black beauty zan kaiki shopping ma in kinaso" dama wayar jahilar na hannunta tanajin haka ta sa number'n heedayah ta kira bugu daya biyu heedayah ta daga tace "hello shams?" Shams tace "kixo gbe kamar time da kkazo yau kinji?" Heedayah tace toh "inade baran sami kowa a gdan ba?" Shams tace "eh mana sekace baki yarda dani ba" heedayah nason sake mgn shams tace "se anjima." (Masu karatu karku manta fa a handsfree akayi wannan waya duk don moha naji). Yace "yawwa black beauty gbe zamuje shoprite ko?" Shams da shashanci wai "eh don moha" yace "yawwa" tare da miqewa yafara tafiya a zuciya yace "ban taba ganin bahuwa, sokuwa, fool like shams dinnan ba" yayi murmushi sannan ya wuce site nasa se nanatawa yake a zuci "yau zanga aysha dan ni har a yau banyarda I dont know this gurl ba gani nake kamar wata wanda nasani ce, we will see 2moro.
Washegari! exactly time da heedayah ta iso gdan su don moha jiya haka ta hallara ma yau tayi parking motrta a inda tasaba duk don moha na labe daga wata lungun shima yana kallonta ta daura niqab nata sannan ta fito ta kusa kaiwa bakin gate nasu don moha ya fito daga gun buyarsa yakarasa yaga plate number din sak erin na jiyan ne yayi murmushi sannan ya bi bayanta takai bakin gate din knan tasa hannu zata bude don moha yasa hannu acikin aljihu yaciro wata hanky dagani yasamata erin wannan magani ne me sumar da mutum dinnan nan da nan ya manna mata a hanci kafin tayi kokarin kwatan kanta inaa! Mgnin yabi hancinta ta kwanta ajikinsa a sume nan ya dagata ya maida ita cikin motar ya ajiyeta a baya sannan ya taho gaba ya kunna motar suka bar unguwan.
[10/10, 2:25 PM] ๐Ÿฌ๐Ÿ›๐Ÿ’Salma๐Ÿ’๐Ÿ›๐Ÿฌ: ๐Ÿ‘ฎ๐Ÿ‘ฎ๐Ÿ‘ฉ๐Ÿ‘ฉ๐Ÿ’ฅ๐Ÿ’ฅ๐Ÿ’ฅ๐Ÿ’ฅ๐Ÿ’ฅ
HEEDAYAH!
๐Ÿ’ฅ๐Ÿ’ฅ๐Ÿ’ฅ๐Ÿ’ฅ๐Ÿ’ฅ๐Ÿ‘ฉ๐Ÿ‘ฉ๐Ÿ‘ฎ๐Ÿ‘ฎ
3โƒฃ7โƒฃ
written by miemie๐Ÿ‘„

Driving don moha yake kamar ze fire sama, yana gudu yana kallon heedayah ta mirror wanda niqaf nata har ynxu na fuskarta be since ba ahaka har suka isa sharada phase 2 a daidai gabar gdan wata flat gda ya tsaya ya fita ya bude gate sannan ya kuma dawowa ya shiga da motar cikin gdan ya rufo gate din yasa lock ta ciki harda datsewa da kwado, direct kofar entrance ya wuce ya bude sannan ya nufa gun motar ya bude kofar bayan ya dauko heedayah kamar baby a hannu yashige da ita cikin gdan ya kaita wata daki ya kwantar da ita akan gado. Kujerar da ke gefen gadon ya jawo kusa da inda ya kwantar da heedayah sannan ya miqa hannu ya since niqab din waro idanunsa yayi sosai kamar ze ciresu sanda yakusan cin tuntube a kan kujerar dayake kai da kyar ya iya ya dawo kan kujerar da hannunsa bibbiyu akan bakinsa cuz he can't believe what his eyes are seeing da ihu yace "HEEDAYAH! Is this really you?" Yasa hannu ya murmurza idanunsa still heedayah yake gani a gabansa ya miqa hannu ya soma shafa fuskarta "you are real heedayah, its really you!" besan sanda yayi hugging nata ba yakusan 2mins rungume da ita sannan ya sakota ya cire mata hijabin dake jikinta mistakenly ribbon data kama gashinta dashy ya since gashin nan suka zuzzubo kan kaykkayawar fuskarta kyanta ya sake bayyana ya matso da kujerarsa kusa da ita

Please Login or Register in order to submit comment