Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ke kan kafar wata kawar Aunty Jaleela, hotuna nashiga yi mata nakuma ba da wayan a ka ɗaɗɗauke mu tare.
Bikin suna yayi kyau sosai an ci an sha,sai wajen magriba a ka fara watsewa,
tunkafin magriba Dr Faruq mijin Aunty Rafee'at yazo yaɗau keta sukayi gaba,
Iro drever shi yazo ɗau karsu Mamie dan haka nabi motar su muka wuce state locos tare.

Muna isa direct part ɗin Ummi muka wuce ni da su Umma Habiba,
A bedroom muka tadda ta,nan kowa yafara shirin sallah,
nidai zama nayi bakin gado dan ina fashin sallah,
Hotunan da nayiwa jaririyar Aunty Jaleela nashiga laluɓowa cikin wayata ina faɗin
"Ummi kinga yarin yarnan kuwa kyakkyawa fara soll Allah naji haushin da a ka aske mata gashi, gashin ta mai yawa suka kama sukayi mata aski".
Ummi tace
"To in ban da haukarki sai a bar mata gashin ai dole sai an aske in ma suka bari dan gaye ai sunyi wa kansu dan nan gaba kaɓewa zaiyi a bunshi".

Wayar na mika mata nace "Kalleta fa kigani Ummi
Allah naga alama yarinyar nan idan tagirma kama dani zatayi, in lokacin gashin ta yayi yawa kamar nawa".
murmushi Ummi tayi tana duban hotunan,
Umma Habiba da ke zaune kan sallaya bayan ta'idar da sallah tace
"Uhum kinbi kin damemu da maganar wannan mummunar yarinyar".
Aunty Hafsat da fitowar ta daga bayi kenan ta amshi zancen da faɗin
"Ai kam mummuna kam ina wani ƙyan a nan har Asmah tafita kyau".
Baki na buɗe najuyo ina kallon Asmah ƴar Aunty Hafsat ɗin dake ƙwance tana bacci a gefe na,
kumatun ta naja tare da dungurin goshin ta nace
"Haba Aunty Hafsat kirasa wacce zaki haɗa ta dashi sai wannan mummunar yarinyar mai katon kumatun Allah yasa wake mata".

Da sauri Aunty Hafsat ta karaso bakin gadon tasoma jijjiga Asmah da ta fara motsi,tace
"Hannunki sai ya makale kika kara dungurin ta ai ko ke bazaki haifo kyakkyawar yarin ya kamar ta ba".

Fuska na yamusa nace
"Allah in dai kamarta zan haifa gara ban haihun ba".
nafaɗa ina mikewa,
ido Ummi tabi bini da shi tana faɗin "Allah yashirya".
Ni dai jakata na ɗauka nashige bayi dan na kimsa jikina,
Koda nayi wanka kayan jikina na mayar nafi babu kowa cikin ɗakin duk sun koma parlour,sai na haye gado nayi ƙwanciya ta,
ƙwanciya ta baifi da minti 10 ba Ummi tashigo haɓa tarike tana faɗin
"Au ƙwanciya kikayi?to tashi maza gacan Iro na zaman jiran ki nayi masa magana zai mai daki gida".
nace "Ummi a daren nan kawai sai gobe zan tafi".
"Ai to shikenan cigaba da ƙwanciyar har Abba'n ku yazo yasa meki yarage naki".
Mikewa nayi naja jakata da mayafina nabi bayan ta ina bubbuga kafafuna a kasa.

Ko da muka fito parlour Sallama mukayi dasu Umma Habiba sukace idan Allah yakaimu gobe zasuzo min, sa sabo da jibi suke so sukoma Maiduguri.
Har gun mota Ummi ta rakani har sai da taga fitar mu kafin takoma,
Muna isa nafito daga cikin matar Iro yajuya nikuma na nufi ciki,na ɗago kafata zan ɗaura saman step ɗin da zai sadani da cikin part ɗin, nayi saurin mai da kafata kasa cikin hanzari najuyo jin muryar sa a baya na yana faɗin.
"Ina kiƙa fito?".
tsayuwa ta nadaɗa gyara wa dan ba shakka na razana daganin sa a nan ƙwata-ƙwata ni ban ma lura da yana gunba,
"Ina kika fito".
Yakuma jefomin tambayar.

"Gida". nafaɗa a takaice,
fuska ya suke kana yace
"Wakika tambaya da zaki fitan".
shiru nayi a kan raina nace
"To in zan fitan wa zan tanbayan in kuma shi yake nufi to a ina zan ganshi har na tanbayan".
Ƙwafa yayi tare da juyawa yasoma tafi batare da yace komai ba. da sauri na haura nashige ciki.

Washegari bayan naga ma gyaran ko ina nacikin side ɗin nashiga kitchen domin kirkawa su Aunty Hafsat abinci kafin su iso.

Gas na kunna na ɗaura tukunya tare da zuba masa ruwa ɗan dai-dai, sannan na ɗauki ɗan ma dai-dai ciyar rubo na je in da fridge yake nabuɗe na ɗibi koda, na a je gefe kana naɗau wata robar albasa da tumatir da attaruhu na ɗiba cikin ta,na aje kusa sannan na ɗauko garin tafarnuwa maggi kori garin citta man gyada koren tattasai,duk na aje su kusa.


Nazuba ruwa cikin robar kodan na wanketa tafita fes. Sannan na yayyanka ta kanana sai na zuba a cikin tukunya tare da ɗan kara zuba mata ruwa kadan saboda ganin nacikin tukunyar yaɗan kone, na rufe.
sai da ya fara nuna har ruwan cikin yakafe sai na wanke kayan miyar na yayyanka albasa da taruhu da tumatir ɗin nazuba a ciki, na sa maggi da garin tafarnuwa da garin citta kadan, Sannan na rage wuta sai na shiga gaurayawa inayi ina zuba man gyada wan da nariga da na soyashi ɗan dai-dai na zuba iya yadda nake bukata kana naci gaba da juyawa har sai da albasa da tumatir da attarugu nan suka nuna,sannan na sauke. tuni kitchen ɗin yagar waye da kamshi.

Wata tukunyar na ɗaura nazuba ruwa ciki na ɗauko couscous na a je kusa.
numfashi na sau ke tare da rike kugu ina bin in da na ɓata da kallo, a sannu na sunkuya nashiga tattara gurin,na junkura zan mike saiji nayi a bu yafaɗo a baya tim,
Wani irin kara nasake cikin tsananin tsoro da firgici da kaɗuwa nakuma zandara wani ihun jin yadda naji faratun a bun ya karceni a baya,sai narika jin yana tafiya cikin rigana yanayin kasa,

Wani uban tsalle natuma nayi gefe, sai ga kadangare yafaɗi kasa tim, nan take naji numfashi na nakokarin barin jikina, da mugun gudu nafice cikin kitchen ɗin nayi waje a guje bana ko ganin gabana,mafaka kawai nake nima dan jinake kamar kadangaren na jikina,kofa nagani kawai a buɗe wan da a cikin yanayin da nake ciki bazan iya tan-tan ce wacce kofa bace nakusa kaina ciki,
Yasa kai zai fito dai-dai lokacin nasako nawa kan sai ji nayi na garu da jikin sa,kara na sake nayi baya cikin kiɗi ma yayi hanzarin riko hannuna,kokarin fizge hannun nake ina jujjuya kaina cikin kiɗima da tashin hankali,yakuma rike hannuna da ƙyau yana faɗin

"Ke meye haka?".
jin muryar sa yasani buɗe idanunna sai kawai nafaɗa jikin sa na kankame shi tare da sakin kuka mai sauti.
baya yarikayi a hankali har yakoma ciki yamai da kofar yarufe kana ya zaroni cikin jikin sa yana cewa
"Ke wai menene hakan?dubi yan da kika fito".
yafaɗa yana zama kan kujera, bai kaiga rufe baki ba na faɗo kansa na kankame shi da karfi na cusa fuskata cikin kirjinsa cikin muryar kuka nace
"Ya SALEEM kacire min kacire min dan Allah wayyo Allah na kacire min Ya SALLEM yana cikin rigana yana bayana wayyo Allah naaa!!!".
Nakuma kankame shi da iya karfina nake cusa jikina cikin jikin shi.

Cikin rashin fahim ta yaɗogo hannun sa yasau keshi kan bayana
"Meye a cikin rigan naki?".
yafaɗa murya can kasa, cikin jan shashsheka nace
"Kadangare kadangare ne yana cikin rigata".
A hankali yarika yin kasa da hannunsa yasau keshi kan zip ɗin rigata, yasoma yin kasa da shi har yakai karshe sai ya ɗan ɗago yakuma sa hannayen sa biyu yaware rigar.

Ido yatsurawa bayana sai kuma yasaka yatsar sa yana bin in da shatin faratun kadangaren ya karceni,gantsare wa nayi tare da kuma kankame shi nace
"Shine kacire min kacire min dan Allah".
nafaɗa cike da muryar tsoro nakuma cusa fuskata sosai cikin kirjinsa.

Numfashi ya fesar tare da faɗin
"Ke ni banga komai ba, da kadangare sai ya zauna a jikin ki kiyita wannan tsalle-tsallen da shi".
nace
"Ya SALEEM kataɓa shi fa shine".
"Ni ban taɓa shiba shatin faratun sa na taɓa".
Yafaɗa yana cigaba da tafiya da yatsarsa kan zanen ciwukan da faratun kadangaren yayi min.


Numfashi nasauke da jin hakan na ɗan sami nutsuwa, sai na mike a jikin sa,na zauna gefe da shi na rakuɓe guri guda ina wiki-wiki da ido, gaba ki ɗaya jikina wani irin yam-yam yake min musamman raɗaɗin da nake ji a bayana, sai ji nake kamar kadangaren ne ke tafiya cikin bayana.

Mikewa yayi yashige bedroom ɗin sa niko sai daɗo rakuɓe wa naji jikin pillow'n kujera.
ya ɗan jima sosai cikin bedroom ɗin sai gashi yakuma fitowa da wasu kayan da ban a jikin sa bana ɗazu da suke jikin saba.
Bin in da nake rakuɓe yayi da ido yayi mamakin ganina har lokacin zaune a gon.

"Zaman me kike baki tafiba".
yayi maganar ida nunsa kan agogon da yake ɗaura wa a hannunsa,
rau-rau nayi da ido cikin rawar murya nace
"A kwai kadangare ne".
ɗagowa yayi ya kalleni sai kuma yacire idanunsa a kai na yajuya yayi waje.

Yana fita direct parlour'n ta yanufa can bakin kofar kicin yahangi ɗanƙwalin ta yashe a gun,a sannu yatako ya'iso gurin daga in da yake tsaye yana hango cikin kitchen ɗin, in da ya hargitse gaba ɗaya kamar an yi dambe a gun, tsaki yaja yatako ciki yana cigaba da bin kitchen ɗin da kallo, can yahangi katuwar kadangare manne a jikin garu ganin window'n kitchen ɗin abuɗe ya tabbatar masa da tanan ne kadangaren yabi yashigo.

Ƙyallen da take sauke tukunya da shi yaɗau ka sai da yarufe glass ɗin window'n kafin ya isa in da kadangaren yake yakama shi da shi sannan yafito yaɗau ɗan ƙwalin ta dake kofar kitchen ɗin yayi waje,
A cikin a Flaw's ya wurga kadangaren yanufi side ɗin shi a in da yabar ni anan ya taddani,
Ganin
ɗan ƙwalina rike a hannunsa sai naɗa go hannuna nashafi kaina sai yanzu nasan cewa babu ɗan ƙwali a kaina sai dai gashina a tupke yake da ribom,

Kujerar dake ɗan nesa da ni ya zauna tare da wurga min ɗan ƙwalin yamaso da table ɗin da system nashi ke ɗaure a kai gaban sa yasoma latsawa,
batare da ya kalleni ba yace
"Tashi kije na cire".
naɗau ɗankwalin na ɗaura jiki a sanyaye namike a hankali nasoma tafiya,har nakai bakin kofa yace
"Zonan".
A hankali nadawo in da yake na tsaya gaban sa,hannuna yariko yajuyani ta baya yakai hannu bayana yaja zip ɗin rigata yayi sama da shi. kasa nayi da kai na dan nagama mancewa da rigar a buɗe take.
"Jeki". yafaɗa yana sauke hannunsa, kai na a sunkuye nafita..................






Mommyn Twins ce




*🌺HAMDAH🌺*

*NA*

*RASHEEDA S DIRECTOR*


_(Book one)_


*_________________________________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*👇🏻

https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association

*_________________________________*


MARUBUCIYAR👇🏻
*BA ABIN DA BAN GANI BA*
*INA SANE DA HAKA*
*ALFARMA*
*BAZAWARA CE ITA*
AND NOW👇🏻
*HAMDAH*


*Free page*


My no 08034690723




🅿️14




A kofar parlour natsaya ina leka cikin parlour'n, najima sosai a tsaye a bakin kofar da ƙyar na iya tattaro jarumtata nashe ciki,
cikin sanɗa nake ɗaga kafata duk in da zan sauke kafar sai na kalli gurin da ƙyau, dan gani nake kamar zan sauke shi kan kadangaren.
cikin sanɗa nashige cikin bedroom, Ina shiga kira na shigowa wayata,nakarasa bakin gado in da wayar ke ajiye, sunan Ummi ce yabai yana kan screen ɗin wayar, da sauri na hayo kan gadon na ɗau wayar nayi picking call ɗin na kara wayar a kunne tare da yin sallama.

Daga bangare Ummi ta amsa sallamar tare da amsa gaisuwar da nake mata,kana ta ɗaura da tan bayata lafiya ta da nagi dan, nace duk muna Lafiya,
tace
"To madallah da ma su Umma'n ku Habiba ce suka ce na faɗa miki bazasu sami zuwa gidan kiba,dama Sadeeq ne ya kawo su shi yawuce Jos to sai gashi ya juyo ɗazu yanzu yace sushirya suwuce gida yanzu."

Langwaɓar da kai nayi cikin marairaice murya nace
"Ayya shine zasu tafi bazasu zo bako kicewa Uncle Sadeeq ɗin dan Allah yayi hakuri yabarsu suzo".
"Hm Sadeeq ai bazai ma yar da ba nima yanzu muka gama yi da shi sukara ƙwana dan yahuta gobe suyi sammako, daga nan zuwa Maiduguri ai ba karamar tafiya bace da ke shi tafiyar dare baya damin shi,sai dai kawai in sun Kuma zuwa wani lokaci".
Nace "To Allah ya kiyaye musu hanya".
tace
"Amin". Mukayi sallama na sauke wayar.

Yau wuni nayi a ɗaki ban ko leka parlour ba, har yamma zuwa lokacin nasoma jin cikina na murɗan yunwa, bana da wani zaɓin da yawuce nasamar wa cikin na a bin da zan saka masa, dan ko breakfast banyi ba,
A hankali namike na nufi parlour daga ɗan nesa na tsaya ina kollon kofar kitchen,har yanzu gani nake kamar kadangaren yana ciki.
Numfashin tsoro naja tuno da yan da naji shi cikin rigata ɗazu.
juyawa nayi naje na buɗe fridge ɗin da ke nan cikin parlour naɗau drinks guda biyu nakoma ɗaki, ranar shi nasha madadin abinci.

Washe gari
Ban fitoba sai wajen karfe 11 kasan cewar mun sami hutu a makaranta,
Yau kam yunwar da nake ji yagirmi nasha drinks kaɗai dan bazai ɗauke ni ba.
Naɗau gyale na na yafa shi a kaina, tare da ɗaukar waya ta da kuɗi na nufi waje.

Can na hangeshi zaune cikin wasu Flaw's masu ɗauke da jerin kujeru na alfarma, sanye yake dawasu fararen kaya riga da wando wandon iya guiwar sa,daga kasan irin mai roba ɗinnan ce tasuke takasa sai igiyoyi a bakin,rigar kuma mai dogon hannun ce sai dai sakiyar rigar a buɗe take daga kirjin sa zuwa dai-dai mafarin cikin sa, ya sarkafe kakafun sa da suke mike kan wata kujerar dake gaban sa, yaƙwanto da bayan sa jikin kujerar da yake kai, a hankali yake ɗan karkaɗa kafafun sa yayin da idanun sa ke lumshe. fuskar sa na kallon tacan ya baiwa hanyar fita baya.

A hankali nake tafiyar harna ɗan gotashi sai naji yace
"Ke zonan". cak naja natsaya,
in badun hankalina na kan shi sabo da alla-alla da nake nayi na fita a gidan kada yajuyo ya ganni ba, da bazan ji a bin da yafa ɗa ba, sabo da muna da ɗan rasa sakanin mu, kuma maganar a hankali ya furta, bugu da kari kuma fuskarsa bama ta hanyar take kallo ba, gakuma idanunsa da suke a lumshe.

A hankali najuyo natako nazo in da yake,natsaya batare da nace komai ba,
Shima kuma idanunsa suna nan a lumshen.
ƙwayar idanuna na juya nasau ke shi kan kirjin sa, da bakin gashi ke ƙwance lip-lip kan farar fatar sa.
saurin janye ida nuna nayi daga kallon sa,jin wani abu mai kama da tsoro ya gilmamin ganin wani sashi na kirjin sa a bayyane.
"jibi yadda yabuɗe jikin sa ko zafi yakeji da wannan sanyin da ake yi oho, amma ya iya cewa ana sanyi ina jika jina shikuma fa".
Nayi maganar a kasan raina.
laɓɓansa yashiga mosasu batare da yabuɗe idanun nasa ba, cikin wani irin murya da yafi kama da mai jin bacci yace
"Ina zakije?".
yayi tanbayar a gajarce, baki na turo gaba sai nashiga kame-kame ina faɗin
"Um..um.." sai kuma nace
"Gida zani yunwa nake ji".
ɗan sakaita kaɗa kafar da yake yayi, sai yaɗago hannun sa ya shafi sajen fuskarsa zuwa kan ɗan gyemun sa,
cikin sautin muryar da yayi magana da shi dafari.

yace "Babu a binci a gidan nan ne?".
kai na girgiza sai kuma nayi rau-rau da ido na ce
"Ai a ƙwai kadangare ne a cikin kitchen nikuma yunwa nake ji".
Sai yanzu ya buɗe idanunsa ya ɗan zubamin su,saurin yin kasa da kaina nayi nashiga wasa da bakin gyale na,
"Ban cire ba kenan, karya nake yi?".
Yafaɗa ida nunsa a kaina,ɗagowa nayi da sauri nashiga girgiza kaina.

Kuma mai da idanun sa yayi ya lumshe su kana yace
"Wuce ki koma ciki". yafaɗa kamar maiyin raɗa,
Ido nawaro jin a bin da ya faɗa, in koma yunwar takashe ni.
ji nayi kamar in rushe da kuka, a hankali na juya na ja kafafuna na koma ciki,
koda nakoma tsayuwa nayi a cikin parlour ina hangen kofar kitchen,
duk da cewa ina da tabbacin cewa tabbas da gaske yacire kadangaren,
amma hankali na yakasa ƙwanciya sai gani nake kamar in nashiga zan ganshi,
gyalen jikina nazare shi na a je saman kujera tare da wayata,
a hankali nataka zuwa kofar kitchen dan bana da zaɓin da yawuce wannan,
koda nazo bakin kofar leko da kaina nayi narika dud dubawa,
naɗau lokaci kafin nashige ciki, sosai
nabaza idanuna ina dubawa banga wani alama na abin da nake wa tsoron ba,
dan haka cikin dai ɗar-ɗar ɗin nashiga ƙwashe kayakin da nayi ɓarinsa cikin kitchen ɗin, har da
miyata da nayi jiya duk suka ɓare, nakimsa gurin tsaf,
duk a binda nake cikin dau riya nakeyi dan ko ni nataɓa a bu yayi motsi sai na
razana, haka nagama kimsa gurin cikin ɗar-ɗar,
Ina gamawa na
ɗaura girki mafi sauki, koda na gama nazubo shi cikin plt nafito....


★★★
2 week later
★★★


Zaune nake a parlour najiyo knocking ɗin kofa sai da a kayi har sau uku kafin na mike na isa jikin kofar na ɗan buɗe shi kaɗan batare da na wangale kofar ba,
Salele nagani tsaye rike da jaka a hannun sa,
Bin jakar nayi da ido sai na mai da kallona kanshi ganin yan da yaketa washe baki nace
"Salele wannan jakar fa?".
nayi tan bayar ina nuna jakar da yatsa,
Kuma washe baki yayi tare da faɗin,
"Jakar Inna ce gasucen" yafaɗa yana nuna farfajiyar gidan.

Kofar na daɗa wangale shi gaba ɗaya naleko kaina waje can nahangi Inna tafito daga mota kenan tana gyara ɗaurin zanin ta, goggo Hauwa na tsaye Ya SALEEM na gefen su,
Wani irin ihun murna na sake nayi waje da gudu har sai da na ture Salele Allah yakare yarike jikin kofa,
In da suke nayi a guje ina faɗin
"Oyoyo Inna!".
rungume ta nayi cike da tsananin farin ciki ina ci gaba da faɗin Oyoyo Inna.
Dariya goggo Hauwa tabimu da shi ganin Inna'r ma ta rungume Ni tana washe baki tabbas tasan munyi kewar juna.
Nan muka ɗun guma mukayi ciki,
Ni dai ina rike da hannun Inna har muka shiga cikin parlour.


Suna zama nawuce naje na ɗibo musu drinks, da ma na ɗaura a binci ban ko sauke ba nashiga kitchen na tadda yanuna sai nazuzzu ba musu cikin plt nakawo musu,suna ci muna hirar yaushe gamo,
Nan Ya SALEEM yashi go ya zauna gefen goggo yana yi mata ya hanya.
tun kan yakai ga rufe baki Inna tace
"Mu da ba'a tan baye muba Allah bai kimu ba,yo ko dai baka tan baya ba ka dai ga kalau na iso a bina"
dariya goggo Hauwa tayi tace
"Kin dai tari numfashi'n sane Inna, ba gashi nan zaune ba ai zai gai da ki".


"Ai kin hofi ni Ina ruwana ma da gai suwar sa, gai suwan uwa na bayan aure ma ko kafar shi na gani,to bana son wannan ma yarike kayan shi,ni za'a yiwa iya shege, hali Lantai tafini ko iya karfin hali a kan abin mutum duk da kuɗi na da taci, bai hanani kaɗa keyar Idris yaje yayi mata gaisuwar bayan aure na mamar kaba".
Inna tafaɗa tana gyara zama da buga cinya.
Girgiza kai goggo Hauwa tayi tare da yin murmushi tadubi Ya SALEEM wan da ya taɓe baki ya mai da idanun sa kan tv yayi kamar baya gurin. tace
"Kai SALEEM ya zaka yi haka ai dai kasan ita mazau nin uwa ce ya dace ka kai mata gai suwan bayan aure".
Sai kuma ta juyo gun Inna tace
"Yihakuri Inna in kika koma zai je har gida ya gai sheki".


Ido na bisu da shi gaba ɗayan su a bin nasu yaso bani dariya ganin yan da Inna ta hakikan ce shi kuma gogan yayi kamar ma bada shi a keba,
dariyar ce ta suɓuce min ganin yan da Inna tawani murtuke fuska sai taunar goro take.
Hannun ta da ke rike a hannuna ta fizge tana faɗin
"Sha-sha-shar banza ba duk wake nakewa yakin ba, sabo da yasame ki a bulus, dole yaki daraja ni, to bai san mahimmanci da darajar ki da nawa ba,baga shi ina magana yayi banza da niba".
Saurin kunshe dariya ta nayi ganin wani irin kallon da yabini da shi.

Goggo Hauwa takuma girgiza kai dan ita ma dariyar ce ke kunshe cikin bakin ta tace
"To Inna kiyi hakuri yayi kuskure".
Inna dai hanci tarika hurawa a dole Ya SALEEM yayi mata laifi shiko mikewa yayi yana kokarin barin gurin,
goggo Hauwa tace
"SALEEM bari muzo ka sauke mu gidan su Yaya Inna muje ko?".
tafaɗa tana duban Inna.
Inna ta ɗaga hanci sama tana faɗin "Ina nan babu in da zani bagurin kowa nazo ba gun jikata nazo, je kishigar min da kayana wancan ɗakin".
tanuna ɗakin da ke gefe da dinning,
Da sauri na mike cike da zumuɗi nace
"Bari na buɗe kofar".
Nayi saurin nufar bedroom ɗina,
muryar Inna naji tana faɗin
"Mai sunan malan nisa zakayi ne".
ban dai ji amsar da yabata ba, sai ji nakuma yi tace
"Kazomin da goro".
dariya nayi dan nasan faɗan su baya nisa yanzu zakaji tana yimasa an jima kajisu suna hira.

naje in da na aje makullen da Aunty Rafee'at ta bani tun ranar da nazo gidan tace na aje,makullan kowani kofa na side ɗin nanne.
Na laluɓo su a in da na saka su nafita da sauri naje na buɗe kofar,
ba wani kuran kirki ɗakin yayi ba kasan cewar nakan buɗe lokaci zuwa lokaci na share,shi yasa ban wani sha wuya wajen garashi ba, ina gamawa nafito muka ƙwashi kayan da goggo Hauwa muka shiga da shi ciki.sai min tsiya take wai ni na ƙwashe musu uwa gashi tace bazata gidan ƴaƴan taba a guri na zata zauna,
Ni dai sai dariya nake dan yau ina jina cikin masanan ciyar farin cikin zuwan sun,
muna gama shiga da kayan muka dawo parlour'n, nan Inna ta cicciro min tsarabar da ta zomin da su, nata murna wan da zan iya ci naci a gun sauran nakwasa naje na aje.
sai da a ka kira sallar magriba kafin Inna tashige ɗakin da a ka buɗe mata,nima can nabita wanka da sallah ma duk a can nayi.

Ina makale da Inna mun raba dare muna hira, nan Inna ke faɗa min an sa auren Rabi wata mai kamawa za'a yi bikin,nace in Sha Allah zanje bikin,
Ranar kam a ɗakin nakwana, washe gari da sassafe nashiga kitchen nashirya mana breakfast muna zaune bayan mun yi breakfast, Ya SALEEM yashigo da sallama.

Yakaraso ya zauna kan ɗaya daga cikin kujeru 1-1str da ke cikin ɗakin, goggo Hauwa yafara gai sarwa sannan ya gai da Inna tare da saka hannun sa cikin aljuhu ya zaro goro da ke ɗaure cikin laida ya mika mata,ta amsa tana faɗin
"Ma dallah Allah yayi albarka".
hira Inna tashiga yi masa shi dai um yake bin ta da shi
kamar mai ciwon baki.

Tun shigo war sa Idanu na na kan waya ban ko ɗago ba, sai da naji an ɗan dungure kafata, naɗa go sai naga goggo Hauwa ce,
nuna min shi tayi da ido kasan cewar muna jere da ita.
"Baki ganshi bane ko kinje kin gaishe shi a ɗakin sa ne?". rausayar da kai nayi kana nace
"Ina ƙwana Ya SALEEM".
bai amsa ba sai ɗaga kiran da yashi go wayar sa yayi yamike yafita.
Baki na taɓe
Na mai da idanu na kan wayar nacigaba da a bin da nake.

ƙwanan su Inna uku da zuwa sai a ranar na ukun Na'ima ta zo ta gaishe su, shima ɗin sai da Inna ta tanbayi Ya SALEEM ko bata gidan ne, bayan fitar sa shi ne tazo.

Zaune muke a ɗaki yashigo kamar yan da yasa ba tun zuwan su Inna, zai shigo da safe kafin yatafi offece, bayan ya dawo daga offece ma zai kuma shigowa,sai dai yau ga dukkan alamu da shirin fita yashigo dan ko zama bai yiba yagai shesu yajuya yana kokarin fita, Inna tace
"Mai sunan malan kazo min da goro wan da ka kawo min ranar ya kare".
To kawai ya ce yayi waje.

Bayan sallar Isha muna zaune Inna ta dubeni tace
"Tashi maza kije ki karɓo min goro gun Mai sunan malam, ni na iya irin wannan zama babu a bun mosa baki".
mikewa nayi nafita.

Ina fita daga ɗakin yana turo kofar parlour'n,naɗan tsaya yakara so ciki ganin yana kokarin wucewa ɗakin da Inna take ciki nayi saurin cewa
"Ya SALEEM wai kabani goro in ji Inna".
ɗan gajeren tsaki yaja sai ya juya yasoma tafi har yakai bakin kofar parlour sai yace
"Zo ki karɓa mata".
yafaɗa tare da buɗe kofar yafita.

Bedroom nawuce na ɗau hijabi na zura kan doguwar rigar baccin da ke jikina nayi waje,ina fita na hango shi tsaye rike da waya a kunne Shi dai kullum da waya a kunne. In da yake na

3 Comments On HAMDAH
avatar
zarrah

1 year ago

Reply

Amazing story

avatar
taskar

1 year ago

Reply

Replying to zarrah

Thanks for your feedback

avatar
taskar

1 year ago

Reply

Littafi

Please Login or Register in order to submit comment