Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

samu har yasa yaran shi sun cika jara kuna manya biyu da ruwa,sukayi ta masa godiya,dan haka koda SALEEM ya'iso unguwar Mamie tayi masa kwatancen gidan yakaraso,shima yayi masa godiya yaran malam Shehu su suka kwashi jara kunan suka saka bayan motar sa yayi musu sallama yatafi bayan ya baiwa malam Shehu kyautar 50k nan su Abbu ma suka koma gida.

Tun fitar sa ban iya kwan ciya ba ina
nan zaune duk tsoro yagama cika ni,motsi naji a parlour da Kuma magana sama-sama, nan take jikina yakama rawa........!★






Mommyn twins ce


🌺 *HAMDAH*🌺




*Na*

*RASHEEDA S DIRECTOR*

*_____________________________________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*_____________________________________*



_BOOK_ _ONE_



Free page


My no 08034690723



🅿️30



_free page saura kaɗan ya kare_🗣️






Sosai jikina ke bari jin motsi da maganar da ake cikin parlour sai dai sam bana jin abun da ake faɗa sai dai ɗan sautin maganar da nake iya jiyo wa shima ɗin nasan sabi da dare ne ko mi motsi kaɗan da zakayi sai an jiyo sautin sa.
tsoro nane ya tsananta jin taku na matsowa bakin kofar ɗakin,
da sauri na kai hannuna natoshe bakina jin kuka na kokarin kwace min, baya narika ja har na isa jikin garu na rakuɓe ina karkarwa cikin matukar jin tsoro hawaye ya gama wanke min fuska,
"Innalillahi wa'inna'ilaihirraji'un".
Ji kawai nayi na furta kalmar sai nashiga nanata kalmar cikin ruɗu da tashin hankali mara misaltuwa,
wani irin zabura nayi jin alamun an taɓa handle ana kokarin murɗa shi,
sama numfashi na keyi tamkar zai bar jikina,dai-dai lokacin kuma najiyo karar shigowar mota cikin gidan,
handle ɗin a ka sake da karfi sai kuma sautin gudu alamun kafa bana mutum ɗaya ba...

Yana gyara parking yafito yabuɗe but yafiddo da jara kunan ya kwashe su duka biyu a kowani hannunsa guda, yanufi side ɗin sa,
direct kitchen yawuce ya aje su ciki kana yaɗau cup yabuɗe jarka guda ya tsiyaye ruwan yanufi bedroom ɗinsa.
kukan da nake ta dannewa ne yakwace da mugun karfi jin an turo kofar,ganin shine sai na mike da gudu na duro a gadon na nufo in da yake cikin kukan da ya tsananta sabo da firgici da tsoro,
cikin hanzare ya ajiye cup ɗin a kasa ya buɗe hannayen sa nafaɗo cikin jikin sa, sai ya haɗe hannayen sa yadaɗa cusani cikin jikin sa sosai.
fuskata nakife cikin kirjinsa ina juyashi da cigaba da kukan yayin da jikina ke matsanancin ɓari.
cikin tashin hankali yake faɗin
"Menene me yasame ki".
ina ban iya bashi amsa ba sai ci gaba da juya fuskata cikin kirjin sa da matsanancin kukan da nake, hankali tashe yarka jero min tan bayoyi ko ɗaya ban iya bashi amsa ba,a hankali ya karkato da kan sa yadire bakin sa sai tin kunnena yashi huramin sassanyar iskar bakin sa cikin kunne yana ɗan bubbuga bayana da shafa kaina.
ajiyar zuciya narka sauke wa a hankali sautin kukan yarika yin kasa a hankali cikin sigar lallashi da yace
"Menene iye *HAMDAHHH*??".
wani dogun ajjiyan zuciya nakuma sauke wa kana cikin muryar kuka nashiga labarta masa abun da naji. shiru yayi sai kuma ya sauke
numfashi, a hankali yace
"Babu komai fa kinsan dare ne yanzu so komai kankan cin motsi zaka iya jiyoshi ta yuwu daga ɓangaren masu ai kine kika jiyo motsin".
kai na girgiza da sauri nace
"Allah Ya SALEEM har kofar nan an taɓa kamar za'a shigo".
nan ma shiru yaɗan yi kana yace
"Babu komai zo ga ruwan na samo miki".
yaciro ni a jikinsa yaɗau ruwan yaruko hannuna muka zauna bakin gado ya mika min ruwan nakarɓa, nakai kofin bakina nasoma shan ruwan da nake jin sa babu ruwan da yakai min shi daɗi,shiko ido yazuba min ganin yanda nake shan ruwan da bashida ko daɗi a ganin sa, niko ji nake babu ruwan da yakai min shi daɗe tas nashanye ruwan ya karɓi cup ɗin ya'aje.
lafewa jikin sa nayi dan har lokacin cikin jin tsoron nake,
babu jimawa aka kira sallar farko,
leko fuskata yayi ganin nafara gyangyaɗi pillow ya janyo a hankali ya cironi a jikin sa yakwantar dani yamike yashige cikin bathroom bayan sa nabi da kallo har ya shige idanuna na maida su na rufe babu jimawa bacci yayi gaba da ni..

Al'wala yayi yafito yahaye kan sallaya yafara nafilfilu bai tashi kan sallayar ba sai da yaji ana shirin shiga sallar asuba,yazo in da nake yana kai hannu jikina nabuɗe idanuna da sauri cikin razana nashiga yunkurin mikewa. kansa ya ɗan dafe yace
"Ke ba komai fa kinutsu".
numfashin tsoro na sauke kana yaci gaba da faɗin
"Tashi kiyi sallah lokacin sallah yayi".
da sauri na mike zaune cikin marairaice murya ganin sa da shirin tafiya masallaci nace
"Dan Allah Ya SALEEM kar ka tafi tsoro nake ji".
Ido yatsura min batare da yace komai ba sai kuma yajuya yanufi kofa yabuɗe yazaro key ya dawo in da nake yamika min kana yace
"Karɓi idan nafita ki kulle".
kai nagyaɗa tare da karɓar key ɗin jiki a sanyaye,na mike tsaye yafita yaja min kofar nikuma na zura key na kulle...
duk da na kulle kofar amma cikin ɗar-ɗar nake ina idar da salla nakoma kan gado na rakuɓe,koda yadawo yayi knocking sai da na tabbatar shi ɗin ne kafin na buɗe..

(11:30 AM)
Zaune muke a parlour'n sa ina cikin jikin sa ina shaƙar kamshin sa, da yanzu hakan yazame min sabo da kuma samin zaman lafiya ta har in ba haka ba kuwa to ba shakka zan wuni cikin jin warin magani a jikina da tashin zuciya.
hannunsa na kan cikina dayake a shafe kamar babu hanyi bare kuma wani halitta acikin sa, yanata shafa cikin.
Yayin da kofin ruwan da ya samo min jiya ke gaba na da safen nan nasha ruwan yafi sau biyar,
hannu na mika ina kokarin ɗau kar cup ɗin nakuma shan ruwan yayi saurin kai hannunsa kan cup ɗin yace
"Ya isa haka shan wannan ruwa a kawo miki me kyau kisha mana dubi wannan ruwa ni sai yauma naga kalar sa".
fuska na kwaɓe nace
"Nidai wannan yafi min daɗi".
zai kuma yin magana
wayar sa ta soma ringing,da sauri yayi picking call ɗin ganin Abbu ne ke kiran nashi yakara wayar a kunnen sa tare dayin sallama yace
"Barka da safiya Abbu".
ɗan shiru yayi daga bisani yace
"Subhanallah Inna'r a wani asibiti?".
"Ok to gani zuwa".
yafaɗa tare da sauke wayar.
Ido nawaro da sauri nace
"Me yasa mi Inna?".
yace "Su Abbu sun je gaishe tane suka samu bata da lafiya shine suka taho da ita suna asibiti yanzu".
Ido nakuma warowa nace
"Ayya shekaran jiya mukayi waya da ita naji muryar ta wani iri na tambaye ta takece min wai mura ne ke damin ta,
ayya Allah sarki Inna bari na je na shirya mu tafi".
nafaɗa ina kokarin mikewa ajikin sa da sauri.
cikin hanzari yaruko ni tare da sanya idanunsa cikin nawa yaɗan girgiza min kai kana a hankali cikin yanayin nan nasa yace
"Kirika bi a hankali kidai na jijjiga jiki da yawa fa".
fuska na marairaice dan yanzu hankali na nagurin Inna nace
"Toh".
idanunsa ya lumshe tare da kuma buɗe su sai ya mike yaruko kafaɗu na yamikar dani,da sauri na juya nanufi kofa nafita.

Ina shiga bedroom ɗina kaya kawai na sauya kasan cewar nayi wanka a side ɗin sa,naɗau mayafi da waya ta nayi waje,a kusan tare muka fito yana isa parking space ina karaso wa na buɗe motar nashiga shima yazauna mazau ninsa kana yaja motar muka ɗau hanyar asibiti...

Acan muka tadda ƴan gidan mu gaba ɗayan su, da sauri na isa da Inna ke kwance nace
"Sannu Inna ayya murar ce har yanzu bata sake kiba?".
cikin karfin hali da ɗan jin jiki da ciwon nata ta ce
"Ke dai bari ƴar nan ai har zazzaɓi yasa min amma da sauki tun da aka ɗaura min ruwan nan nake jin ɗan daɗin jikin".
nace
"Sannu Inna Allah ya sawaka".
Ya SALEEM ma yakara so yana yi mata ya jiki,
Aunty Jaleela dake tsaye a gefe ta gurin kanta tace
"Uhum ina gashi ƴar gwal ɗin taki sai yanzu ta iso amma kin iya zuwa garin nan kiki zuwa gidajen mu sai nata".
"Ungo naki Jaleela".
Abbu yafaɗa yana yi mata dakuwa,Aunty Rafee'at tace
"Allah da gaske ne Abbu ko tazo garinnan bata zuwa gidan kowa haka wancan zuwan natama data jima a garin nan bata je gidajen muba har da wani wai ita gidan jikar ta tazo to mu basai ki kwashe mu kizuba mu a kwandon shara ba".
Ido kawai Ya SALEEM yamusu kowa tashiga taitayin ta kana yaɗaura da faɗin
"Ku baku da hankali ne mutum na kwance ba lafiya kubi kucikashi da surutu oya kuyi waje".
yafaɗa yana nuna musu kofa.
Inna tace
"Rabu da su mai sunan malam ai sa faɗa nan gaba Allah ya kai mu ni ko kofar gidan wata ma yaushe zan kalla,yoo ai dama ba gida jen ku nazo ba tun daga can nayi niyyar zuwa nata gidan ne sai ku bari idan na koma nakuma fitowa da shirin zuwa naku gidan, maganan nu kawai".
hannunta da aka ɗaura mata ruwan narike ganin tana faɗan tana ɗagoshi gashi maganar ma da ka ganshi kasan cikin karfin hali take nace
"Inna kinga sun fita ma ki sai da hannunki kar ya goce"...
to kawai tace min bata kuma yin magana ba zama nayi a bakin gadon ina rike da hannunta a hankali tarufe idanunta nan bacci ya ɗauke ta,
ido na ɗan zuba mata sai naja wani dogon ajiyan zuciya jinsa kawai nayi batare da nasan da zuwan saba,sai na daɗa rike hannunta da kyau.
kaf ɗakin sai da suka juyo da kallon su gare ni Abbu yace
"Menene HAMDAH wani abun ne?".
kai na girgiza masa da sauri nace
"Ba komai".
sai kuma nayi hawaye yacika min ido har suna kokarin zuba cikin dabara na ɗago bakin gyalena nataro waɗan da suke son zubowa, ina ɗago kaina karaf muka haɗa ido da Ya SALEEM ida nunsa a kai na da fuskar tambaya, murmushi nayi ina gyara zama na yayin da naji wasu hawayen suna kokarin zubowa haka kawai narasa dalilin da yasa nake jin hawayen da kuma son yin kuka,
hannun ta na aje kan gadon naɗan gyara na tokare shi da mayafin ta ta in da zai zauna dai-dai ruwan yasa mi damar shiga yadda yakamata.
sai namike naɗan ja gyalen kaina yaɗan kare fuskata sai na nufi kofa.
Ina fita da sauri nayi ta bayan room ɗin in da wasu kananun bishiyoyi ke jere nashige cikin su da sauri ina toshe bakina jin kukan nason kwace min..

Ina shiga nasaki kuka mai tsuma zuciya cikin yin kasa da sauti..
ganin sa kawai nayi a gabana yanaɗe hanyayen sa a baya yazuba min ido,da sauri na ɗago ina duban sa hawaye naciga ba da zuba a idanuna.
"Me yasa ki kuka?".
yajefo min tan bayar idanunsa a kai na,
kai nashiga girgizawa sai nafaɗa jikin sa ina faɗin
"Nima ban sani ba ban sani ba bansani ba Ya SALEEM".
nafaɗa cikin muryar kuka sosai.
a sannu yazaro hannayen sa dake goye a bayan sa yazagaye ni da shi shiru yayi batare da yace komai ba yayin da zuciyar sa keta bijiro masa da yanayin ta na ƴan kwanakin nan, numfashi yasau ke yadaɗa rungume ni sosai kana a hankali yafurta
"Ya isa kiyi shiru haka duk san da kika ji tsoro ko wani abu maka mancin haka kirika furta innalillahi wa'inna'ilaihirraji'un kinji".
kai na gyaɗa masa tare da soma nanata karmar cikin zuciya ta da fatar bakina,
a hankali yatallafo kaina yasaka ƙwayar idanunsa cikin nawa dasuke siyayar da ƙwalla, sai ya girgiza min kai idanuna na ɗan lumshe hawayen da suke ciki suka zubo kana na buɗe su a kan sa a hankali yamaso da fuskar sa daf da nawa sai ya sauke kyawawan lips ɗin sa kan nawa, yazuro harshen sa yakamo lip ɗin na na kasa yaɗan tsosa sai ya zura harshen cikin baki na sai da ya tabbatar da yasai da kukan da hawayen kafin yazare harshen sa. gaba ɗayan mu fitar numfashi'n mu sai da yasau ya cikin ɗan lokacin.
tafin hannunsa yasaka kan fuskata yashare min hawayen da ke kwance kan fuskar kana yaruko
hannuna muka koma cikin room ɗin.
har lokacin Inna tana bacci Mamie da Ummi ne kawai muka tadda cikin ɗakin su Abba sun tafi masallaci,hannuna yasake shima yanufi masallacin...

Har dare muna asibitin sai bayan sallar isha muka koma gida badun naso ba dan cewa nayi ni a nan zan kwana Abbu yace mutafi ga goggo Hauwa da Mamie su zasu kwana,
har muka isa gida hankali na nacan asibiti gun Inna babu abun da yafi tada min hankali in da naga haka ta wuni a kwance bata kuma ci komai ba, da yammacin ma ɗan hirar da idan anayi tana ɗan amsawa shima ta daina tana dai kwance.
haka ranar nakwana da tunanin Inna.
Washegari da sassafe naje ni side ɗin Ya SALEEM da sallama natura kofar bedroom ɗin sa nashiga
yana zaune a bakin gado boxes ne kaɗai a jikin sa, Na'ima na kwance a gefen sa ta wani ware kafafu daga ita sai zani shima ɗin ba a ɗaure yake ba rufe jikin ta tayi da shi.
kallo ɗaya na musu daga su har gadon da suke kai wan da bedsheet ɗin sa ya yamutse, na kawar da kai na gefe sai kuma na juya da sauri na koma da baya,
wani dogun tsaki Na'ima taja tare da faɗin
"Ya zaki shigo wa mutane ɗaki kai tsaye haka ba sallama in da kin shigo kin sami mutum cikin wani yanayi kuma kice me da alla malama kidai na faɗo wa mutane ɗaki kai tsaye haka".
ban ko tankata ba sai handle da na kama nabuɗo kofar.
muryar sa najiyo yana faɗin
"Wani abun ne *HAMDAHHH*?".
"Dama gurin Inna zani".
nafaɗa ina ficewa daga cikin ɗakin.

Ina komawa part ɗina bayi nashiga nayi wanka nafito nasoma shiri yayin da nake jin wani bakon lamari can cikin kasan zuciya ta,tun ganin da nayiwa Ya SALEEM da Aunty Na'ima naji wannan abun a can kasan zuciya ta.
cigaba da shirina nayi ina gama sa kaya nayafa gyale na isa gaban mirror inda na aje wayata na ɗauka ina juyowa, yanaturo kofar yashigo,
kafe ni da ido yayi niko nayi saurin kawar da kaina daga kallon sa, a sannu yatako ya iso gabana yaruko hannuna yana ɗan murza shi yayin da idanunsa ke kaina ya kafe ni da su kamar maison gano wani abun a hankali yafurta
"Ina zaki na ganki da mayafi?".
da sauri na ɗago na dube shi sai kuma nakuma kawar da kai na, wato ma bai san ina zani ba ko ba ɗanzun nan naje nace masa zani gun Inna ba, sabo da yana tare da matar shi dole ya mance mema nace.
"Ke tambayar ki nake?".
baki na turo gaba nace
"Asibiti gun Inna".
nafaɗa a takaice ina kuma janye hannuna daya riƙe.
wannan kallon yaci gaba da bina da shi kana yace
"Baza kije ba kijira na dawo nakai ki yanzu Na'ima zan kai unguwa sai in mun dawo".
Wani irin waro ido nayi yayin da abun da nake jinsa can kasan zuciya ta yakaru, da sauri naɗa go kaina na sauke idanuna cikin nasa sai kuma na juya da sassarfa nafaɗa kan gado da ciki tare da sakin kuka.
da sauri ya nufoni yaɗa go ni yana faɗin
"Ke baki da hankali ne akan cikin zaki faɗi!!!!!".
fizge-fizge nashiga yi daga rukon da yayi min cikin muryar kuka nace
"Ni ka kyaleni ka sake ni kaje gurin Na'ima ka kai ta ni ko baka kai ni ba ni nasan hanya zanje"...
cigaba da kokarin kwace kaina nake,
yace
"Ke ki nutsu, kinutsu nace!!".
yakuma faɗa cikin tsawa
sai da fizge-fizge'n da nake nayi sai hawayen dake zuba a ido na,yaci gaba da magana cikin kakkausar murya
"Kiyi wasa da komai banda wannan".
yafaɗa yana nuna cikina. sai kuma ya sassauta muryarsa yasan ya idanunsa cikin nawa yana yi musu wani irin kallo kamar wani abun yake son gani cikin su, sai kuma yasaki wani murmushi'n gefen baki kana yakuma gimtse fuska.
sannan yace
"Cewa nayi kijira mu dawo ko baki gane abun da na faɗa ba ne?".
idanuna na lumshe hawaye suka zubo kana a hankali na zame jikina na kwan ta gefe batare da nace komai ba.
shiko mikewa yayi yafita...
ina jin tashin motar sa sai naji wani kuka yazo min sai dai ban bashi damar fitowa ba.
najima sosai a ƙwance jin wuyana ya hure na mike jiki a saɓule nanufi side ɗin sa nashiga kitchen natsiyaye suwan shana nasha kana nakuma tsiyayar wani a cikin cup nafito rike da shi dan nasan anjima zan buka ceshi,
ta babban parlour nabi dan yafi sauke shi ba zagaye bane ina shiga cikin parlour'n na hangi Na'ima zaune Rufa'ila na masa mata kafafun ta,
da mamaki nakalle ta ita da suka fita ya akayi kuma na ganta zaune anan.
dogun tsaki taja wan da yadawo dani daga tunanin da natafi,nazo daf zan gota su takuma jan wani tsakin tace
"Munga farkon sa zamuga karshen sa!".
ko in da take ban kuma kalla ba nawuce abina.
sai dai har nakoma cikin bedroom Ina nanata kalmar da tafaɗa
"Ko me take nufi"
nafaɗa a fili sai kuma na kawar da zan cen ma da faɗin
"Ko ma me ita tasani"...

Haka nayita jiran Ya SALEEM har yamma bai dawo ba sai daf magriba najiyo shigowar motar sa,
bai shiko side ɗina ba kuma sai bayan sallar isha.
koda naji knocking a hankali na mike dan yanzu bana barin kofata a buɗe har in ba yana waje na bane, in muna tare shine zaka sami kofar a buɗe yana fita kuma na kulle.
jin shine yasani buɗe kofar kafin ya shigo najuya nakoma bakin gado, yamai da kofar ya rufe yatako in da nake yazau na gefe na yaɗan sauke numfashi alamun gajiya kana yace
"Mun dawo dare kuma yayi yanzu sai dai gobe ke ma na kai ki in da zaki je ɗin".
kallon sa kawai nayi ban ce komai ba, janyoni yayi jikin sa kana yace
"Ko kin hakura da tafiyar ne?".
yafaɗa yana tura hannunsa cikin rigata ta yacaf ko ababen kirjina yashiga wasa da su.
nan ma shiru nayi tare da cuno baki gaba.
"To shike nan tun da goben ma kin hakura".
yafaɗa tare da curo hannunsa yayi sama da rigar baccin jikina sai ya kwantar dani da baya ya kafa bakin sa kan ababen kirjina yashiga tsotsar ko wannensu,yaɗau lokaci yana tsotsar su kana ya zare bakin sa yana mai da numfashi.
a sannu ya mike yafita yana fita naje na kulle kofar na dawo na kwanta....

Washegari da safe yashigo cikin shigar kananun kaya sai kyalle yake kamar tauraru. kamshin sa na shaka tare da lumshi idanuna
"Muje ko".
yafaɗa yana janyo ni jikin sa, fuskata na cusa cikin kirjinsa ina shakar kamshin sa.
leko fuskata yayi yace
"Ok na tuna ma kince yau ɗin ma kin haku ra ko".
da sauri na ɗago tare da make kafaɗa, sai na zame a jikisa na ɗau gyalena muka fita...

Koda muka iso cikin asibitin sai naga yabi tawani hanya ba ta inda shekaran jiya muka biba, da mamaki nake kallon kofar room ɗin da muka iso,ganin yashige ciki yasani bin bayan sa da sauri,can na hango Inna ƙwance da alama bacci take sai goggo Hauwa zaune akan kujera a gefen ta,
su biyu ne rak cikin room ɗin, da sauri nakaraso bakin gadon nace
"Goggo Hauwa ya jikin Inna yaushe kuka dawo nan ɗakin kuma??".
tace
"Yau kam jikin ta alhmdllh bakamar na jiya ba ai tun shekaran jiya bayan fitar ku jikin yafara birkice wa, jiya kuwa jikin yabir kice sosai amma yau gashi har ta sami bacci".
numfashi nasau ke tare da mai da kallona kan Inna tayi wani fayau da ita fuskar ta yayi wani haske hancinta yadaɗa fito wa yayi zarr da shi.
Ya SALEEM ya gaida goggo Hauwa da tan bayar ta ya mai jiki kana yajuya yanufi kofa tare da ɗaga kiran da yanzu yashigo wayar sa.
juyowa nayi nace
"Goggo Hauwa su Abba fa".
tace
"Suna can waje ai wannan room ɗin ba a barin mutane cikin sa sai mutum ɗaya kawai".
kai na girgiza jin hawaye yacika min ido nace
"Ayya goggo Hauwa shekaran jiya taci abincin kuwa?".
"Shayi kawai tasha garama jiya da yamma da jikin yaɗan lafa SALEEM ya kafe sai da ta ɗan ci wani abu".
da mamaki nace
"Jiya Ya SALEEM yazo nan ne?".
tace
"Ai tun safe da shi muka wuni anan shi yasa aka canza mana ɗaki ma".
numfashi na sauke kana na mai da kallona kan Inna datake ta baccin ta...
ban bar ɗakin ba har sai da naga farkawar ta har muka ɗan yi yira duk da muryar ta baya fita sosai...

Har yamma muna asibitin ina kuma room ɗin tare da Inna, yau nayi iya bakin kokari na wajen danne kukan da nake ji irin na shekaran jiya da zarar na ji kukan sai na shiga nanata kalmar da Ya SALEEM yace narika faɗa aduk san da naji kukan wato innalillahi wa'inna'ilaihirraji'un. karshe dai ranar goggo Hauwa fita tayi tabar ni kasan cewar tsarin zama kan mai jiya nacikin room ɗin mutum ɗaya ne. sai daf magriba Ya SALEEM yashigo shi da su Abba yace mutafi,
sai a lokacin naji kukan na kokarin kwace min,kallon Inna nayi nace
"Inna zamu tafi sai da safe Allah yakara sauki".
amin tace tana bina da murmushi har nakai bakin kofa sai naku dawowa nace
"Inna sai yaushe ne zaki ci abincin kince sai anjima gashi har dare yayi tun ɗazu fa kika ci kikara yanzu".
tace
"Zanci anjima kafin nayi bacci yan zu bana jin yunwa".
kai na gyaɗa tare da faɗin
"Allah Inna kinga yanda kikayi wani haske kuwa yau".
murmushi tayi kana tace
"Ai dan baki sanni a kuruciya ta bace fara ce ni soll dai na ganin hasken da kike dashi ɗin nan nafiki haske da nake kuru ciya ta yo duniya ce kawai me mai da akawu kuku,
ai ko mai sunan malam ma kyan mai tunan nashi yaɗau ka, dan Malam kyakkyawan mutum ne gashi ya samma mai sunan shi".
dariya dukan mu mukayi abin mamaki har da Ya SALEEM da ban taɓa jin dariyar saba da sauri na ɗago na kalleshi fatabarakallah masha allah.
ajiyan zuciya na sau ke jin kukan yakuma taho min cikin dariyar da nake nan kuma hankalin su yadawo kaina da jin doguwar ajiyar zuciyar da na sauke wan da yafi na shekaran jiya tamkar wacce akayi wa dukan tsiya tagaji da kuka,
juyawa nayi ina kokarin barin gurin sai naji ta ruko hanuna a hankali najuyo gare ta,
murmushi takuma yimin kana tace
"Kiyi hakuri da rayuwa a duk in da tazo miki ki karɓi ƙaddara mai kyau ko mara kyau jiki a ranki Allah shi ya ɗaura miki kuma shi zai yaye miki,
duk inda rayuwa tazo miki kada ki mance da Allah kada kiyi ammafa ni da juyawar rayuwa ki jefa kanki cikin halaka duk musulmin kirki godiya yake wa Allah idan jarabawar rayuwa tazo mishi, mai kyau ko mara kyau,ki gode masa sai yayi miki zaɓi da sauyi nagari,a duk san da kika ji fargaba cikin ranki kirika nanata kalmar innalillahi wa'inna'ilaihirraji'un zaki sami sassaucin lamuran ki".
tun da Inna tafara maganar hawaye ke wanke min fuska sai na rike hannunta da karfe ina kokarin fashewa da kuka
tayi saurin cewa
"Yoo kujimin yarin ya meye kuma abun kukan je kutafi sai da safe".
kai na gyaɗa mata hawaye nacigaba da zuba a ido na Ya SALEEM yaruko hannuna muka fita ina zama cikin mota sai na fashe da kukan yajuyo da sauri yace.......!★





*Free page saura kiris ya kare*




Mommyn twins ce


🌺 *HAMDAH*🌺




*Na*

*RASHEEDA S DIRECTOR*

*_____________________________________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*_____________________________________*



_BOOK_ _ONE_



Free page


My no 08034690723



🅿️31



_Sanarwa sanarwa sanarwa🗣️🗣️ ina ɗauke muku da wani daddaɗan albishir💃 wata baiwar Allah ta biya kuɗin karatun book ɗin nan wa mutane 25 tace na sanya mutane 25 a cikin group ɗin da zaku rika samin littafin batare da sisin kuba burin ta kawai kuyi mata addu'a fatan samin nasara ga abin da tasa gaba. dan haka nake yimuku albishir duk wan da Allah yasa da rabon sa ya biyo ni pc idan kuma ka makara shikenan barabon ka bane_😅






Yace "Menene na kukan daga anyi miki nasiha sai ki kama kuka ke baƙya gajiya da kuka ne?".
kai na haɗa da guiwa naci gaba kuka na wan da nake jin sa har cikin raina. tada motar yayi kana yajuyo ya dube ni tare da faɗin
"Ya isa". da sauri na ɗago kamar an zabure ni na kalleshi hawaye

3 Comments On HAMDAH
avatar
zarrah

1 year ago

Reply

Amazing story

avatar
taskar

1 year ago

Reply

Replying to zarrah

Thanks for your feedback

avatar
taskar

1 year ago

Reply

Littafi

Please Login or Register in order to submit comment