Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kika kai shi gidan aure to har tsofa miji bazai taɓa dai na ganin, kima daraja yarda mutuncin kiba, to ni ban yarda da wannan tsiyar ba da sakaci irin nawasu iyaye".

Kai Ummi tajinjina da gamsuwa da maganar Inna dan duk abun da tafaɗa gaskiya ce,
a zamanin yanzu ana samun wannan sakacin ne daga gurin wasu iyayen,
yana da kyau idan kina da ɗiya mace,kijajirce sosai wajen bata tarbiyya ki janyota jikin ki ki zamo kece babbar kawar ta kuma aminiyar ta, kiyi kokarin jajir cewa wajan nuna mata mai kyau da mara kyau da yar dar ubanji bazata taɓa hofanta ba,
"Allah ya shiryar da ɗauka cin al'ummar musulmi baki ɗaya".
Ummi tafaɗa acikin zuciyar ta tana kuma amsawa da
"Ameeeen yarabbil izzati"...
Mamie mace mai kima da dattako murmushi tayi kana tace
"Haka ne Inna Allah yasa mu dace"....

Ko da a ka idar da sallah su Abba suka shigo harda su Dr Farooq da barrs Aliyu su Aunty Jaleela sukam dama tun da aka shiga salla suka baro wajen mazajen nasu domin su sami jam'i,
Abbu yace su Aunty Rafee'at subi mazajen su sukoma gida dare yayi,dan tuntuni lokacin tashin Dr Farooq yayi sabo ina asibitin ne yasa bai koma gida ba.
sai da yadaɗa dubani sosai kana yace zuwa an jima Nurse zata shigo ta ɗaura min ragowar ruwan idan na huta,kana suka tafi.
suna tafiya bada jimawa ba su Abbu Mamie Ummi ma sukayi mana sallama, Mamie tadube ni tace
"Me kike so a girka miki?".
kasa nayi da kaina ina wasa da ƴan tsasuna, murmushi mai sauti tayi kana tace
"Faɗa min abun da kike jin sha'awar sa".
tafaɗa cikin nuna kulawa sosai
A hankali nace
"Wainar fulawa da yaji banda kwai".
fuska ɗauke da murmushi tace
"To yanzu kuwa za'a kawo miki"....

Sai da su Abbu suka tafi kafin Ya SALEEM yashigo dan tun da aka idar da sallah zama yayi a cikin masallacin.
Har lokacin ina zaune Inna na bayi tana al'wala yana shigowa tana fitowa,
duban sa tayi tana faɗin
"Kai mai sunan malam anya kaci abinci ma kuwa yau? ga abinci can nazuba maka kaci".
baki yataɓe yakaraso yazauna bakin gadon tare da soma latsa wayar sa kana yace
"Ni nace miki inajin yunwa ne?".
"Yoo gani nayi tun safiya kana tsaye banga kasa komai a bakinka ba to shike nan kai ai ba a yimaka gwanin ta".
tafaɗa tana gyara mayafin kanta kana tacigaba da faɗin
"Ta'ina ma mutum zaiyi sallah anan ba sallaya ɗazu ma Umar ne yakawo min sallayar sa".
batare daya ɗago ba yace
"Kije masallaci can waje mana kiyi sallar".
"To ai kam gara masallacin".
tafaɗa tana nufar kofa tafita,
duban sa nayi tare da lankwashe kai nace
"Nima zan je nayi sallar ko sallar asuba banyiba".
nafaɗa murya a marairai ina cuno baki gaba,
A hankali yaɗa go kansa yasauke idanunsa cikin nawa sai ya aje wayar a gefe yariko hannuna yahaɗe tafin hannunmu yadunkule shi,
yamiko ɗaya hannunsa zuwa kan cikina sai ya manna tafin hannunsa sosai a hankali ya lumshe idanunsa yakuma buɗe su cikin nawa, a sannu yashiga motsa lips ɗin sa
"Ɗazu ai baki da ikon yine, yanzu kam zaki iya ko?".
kai na gyaɗa ina janye idanuna daga cikin nasa idon,
"Ok". yafaɗa tare da sake hannuna yaciro ɗaya hannunsa da ke manne a kan ciki na yasauka a gadon tsayuwar sa ya dai-dai ta,ganin yana shirin ɗauka tane yasani saurin zamowa bakin gadon nasauko sai yariko hannuna yana faɗin
"Zaki iya tafiya?".
kai na gyaɗa masa,
yana rike da hannuna muka shiga bayin,tsayuwa nayi asakiyar bayin mai kyau da tsaruwa tsaftsaf dashi kamar ba banɗakin asibiti.

"To yi al'wala'n". yafaɗa yana dubana,
ɗan kallon sa nayi nace
"Zanyi wanka tukun jikina warin magani yake min".
murmushi'n fuskarsa ne yakaru kana yace
"To yi wankan zai bari".
yafaɗa tare da soma kiciniyar tuɓe min doguwar rigar dake jikina....
sabulu yaɗau ka wan da ke adane acikin ƙwalin sa yazo gaba na, hannu namika ina kokarin karɓar sabulun da faɗin
"Ya SALEEM kafita kar Inna tadawo".
rike sabulun yayi gam a hannunsa yace
"Sai me in ta dawon kina tsoron kar ta yankaki ko shiyasa ɗazu kika faɗa mata sirrinmu ko,harda zame kanki kibani laifin nika ɗai,bakece mai tayani hirar ba?".
yayi maganar idanunsa a kaina
kasa nayi da kaina sai kuma na turo baki gaba,
A hankali yafurta
"Aha bakece ba??".
rau-rau nayi da ido tsorona ɗaya kada yacewa Inna hira yakece natayashi ita kuma ta yarda. cikin rawar murya nace
"Ni dai Allah babu ruwana".
nafaɗa hawaye taf idanuna,
"Kuka zakiyi ba hawaye ba dan kuwa yau fitinanniyar kakar nan taki yankaki zatayi tun da gashi ƴar ke ɗin nan har kin iya karɓar ajjiya wajen hira".
tuni hawayen yafara zuba sai nashiga faɗin
"Wlh Allah babu ruwana ai kai ne".
nashiga bubbuga kafafuna a kasa,
ido yawaro da sauri yasaki sabulun dake rike a hannunsa kasa yajanyo ni jikinsa yana faɗin
"Ke kinutsu fa".
kai narika juyawa cikin kirjin sa ina cigaba da faɗin
"Ni dai babu ruwa na ai kai ne".
cikin hanzari yakai bakinsa saitin kunnena a hankali yace
"Ki nutsu kidai na jijjiga jikin ki dan Allahhhhh".
numfashi yaja kana yacigaba da faɗin
"Babu abun da zata miki duk laifin zan ɗaurawa kai".
tallafo fuskata yayi da tafin hannunsa yasa tafin hannunsa guda yashare min hawaye yana bina da wani irin sihirtaccen kallo mai haɗe da murmushi,nidai ido na zuba mishi dan nagaza fassara irin kallo da kayataccen annurin fuskarsa dake bayyana tun ɗazu na musamman.

Da kansa yawan ke ni tsaf dan duk yanda naso yafita a bayin yaki.
namai da kayan da na tuɓe ina yamusa fuska dan duk da nayi wankan ma ban dai na jin warin da jikina yake yi na magani ba,
nayi al'wala namike ina cigaba da yamusa fuskar.
dubana yayi da kyau yace
"Menene kuma?". cikin zunɓura baki nace
"Har yanzu jikina bai dai na warin maganin ba".
rungumo ni yayi yacusa fuska ta cikin kirjinsa a hankali nake jan numfashi ina shaƙar kamshin jikinsa mai matukar daɗi kana zuwa can yaciro ni har muka fito kamshinsa kaɗai nake ji.
ina zama Inna nashigo wa shikuma yafita zuwa can yadawo rike da sallaya yashin fiɗa a gefen ɗakin na sauko, nagaba tar da sallar Isha da shafa'i da wutiri na sallame.
nabar sauran sallolin sai gobe idan Allah yakai mu acikin kowani lokacin sallar da yawuce ni idan nayi sai na rama wan da ake bina,kamar yan da aka koyar da mu a makarantar islamiyya.
Daga bakin kofa Iro direba yayi sallama aka amsa mishi yashigo ɗauke da kula wan da Mamie tazubo min wainar fulawa aciki,yayi min yaya jiki,kana yayi mana sallama yafita,
Inna tazuba min wainar cikin plt da yaji a gefe.. ido Ya SALEEM yazuba min ganin yadda nake cin wainar. tass na cinye wan da tazuba min har ina suɗe hannu...

Babu jimawa Nurse tashigo taɗaura min ruwa kamar yan da Dr Farooq yafaɗa,
a hankali ruwan yafara shiga jikina,
Ya SALEEM nagefe na Inna na zaune a kan kujera ina ɗan saurarar hirar da take yi masa har bacci yaɗau keni...
sai wajen karfe 12:30 Ya SALEEM yatafi abisa tursasawar Inna..★


Washegari da sassafe su Abbu suka zo har da su Fauzan da Nusaiba Ummi ce kawai bata zoba,
Aunty Rafee'at tare suka zo da
Dr Farooq haka ma Aunty Jaleela da barrs Aliyu.
gogan kam tun ana idar da sallar asuba ya'iso.....
Bayan ƴan gwaje-gwajen da Dr Farooq yayi min yabamu sallama ganin jikin da sauki sosai...

Ni da Inna Fauzan Nusaiba amotar Ya SALEEM. Fauzan yazau na a gefen direver, mukuma muka shige gidan baya.
Motar Abbu kuma Aunty Rafee'at da Aunty Jaleela da Mamie suka shiga, su suka rigamu isa Abbu na sauke su yawuce gurin aikin sa Abba kam tun daga asibitin shi yawuce,
a farfajiyar gidan Ya SALEEM yafaka motar a nan muka tadda su Mamie tsaye suna zaman jiran isowar mu.
Mamie ta iso tabuɗe gefen da nake na sauko,
nan ma ai katan gidan kaf suka taho in da muke suna mika gaisu..
Jin hayaniya cikin gidan yasa Na'ima mikewa tafito da sauri dan ganin abun da ke faru wa tana sako kanta waje sai.........!★



*Saura kaɗan Free page yakare waɗan da basu biya ba amaso afara biya*






Mommyn twins ce



🌺 *HAMDAH*🌺




*Na*

*RASHEEDA S DIRECTOR*

*_____________________________________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*_____________________________________*



_BOOK_ _ONE_



Free page


My no 08034690723



🅿️29





Sai ji tayi gaban kirjin ta yayi wani irin bugawa haka kawai,da mamaki take kallon YA SALEEM dake tsaye a gefen HAMDAH Mamie narke da hannu ta tana yi mata magana, yazuba mata ido yana binta da wani irin kallo na musamman,ita kuma ta make kafaɗa tare da cuno baki gaba, gaba ki ɗayan su dariya suka saka mata, gogan ne kawai ya murmusa har sai da jerarrun fararen haƙoran sa suka bayyana. yayin da fuskar sa ke bayyana zallar annuri.
cikin sananin yan da taji zuciyar ta nacigaba da wani irin bugawa cikin jin wani irin bakin ciki ganin yan da gaba ɗaya hankalin sa na kanta,wani irin muguwar tsanar HAMDAH ne yadaɗa baibaye zuciyar ta, ko jiya sai da takirashi take tanba yarsa yaushe zai dawo yace mata babu rana,sai kuma yau gashi ya dawo da wowar ma datatashi ganin sa da HAMDAH dan idanunta yagama rufewa bata ganin kowa agun sai shi da ita da kuma kallon da yake ai ka mata.
da sauri cikin ɗan razana taɗa go wayar ta dake rike a hannunta jin yana tsuwa,ganin kawar ta Raliya ce ke kiran nata yasata koma wa da baya cikin parlour'n ta,
tare da ɗaga kiran tace
"Hello Raliya".

Daga cikin wayar Raliya tace
"Na'ima kina ina ne?kinsan meke faruwa ma kuwa?".

Na'ima tace "Gani anan ina kan bakin gani wannan yarin yar in ba mutuwa tayiba bazan huta ba".
Raliya tace "Au asha dai kin sani".
"Meɗin?"
Na'ima tafaɗa kana yacigaba da faɗin
"Ina zaune najiyo hayaniya nafito sai ganin SALEEM nayi da ƴan gidan su harda uwar sa da wannan kinibabbiya jarabbiyar annobar yarinyar,dan rai nin wayo jiya munyi waya dashi yace min bai san ranar dawowarsa ba sai gashi yau yadawo kuma nagansu tare".
da sauri Raliya tace
"Ganin su kaɗai kika yi baki masan meke faruwa ba,yanzu haka ina (Alheri hospital)ne kin san anan nake yin Implant ɗina yau ne kuma team ɗin dawowa na asibitin,ina zuwa naga SALEEM da ƴan gidan su suna fita daga asibitin,kafin ma nafita amota har sun fita,ina shiga ciki na ga Dr Farooq mijin kanwar SALEEM da Sakeenat Salis kin san a asibitin take ai ki, yana gaba tana binshi abaya rike da files a hannunta,da ta ganni shine tatsaya,shine nake mata tsiya ganin yan da take binsa da sauri, shine tace min
wai ai matar *Parmsec *ABDALLAH Idris ABDALLAH* ne aka kawo ta jiya yau kuma aka sallame ta files ɗin ta ne a hannunta zatakai offece ɗin oga'n su a can za a ajiye ba'a in da ake ajiye na kowa ba".
wani numfashin bakin ciki da tashin hankali Na'ima ta ja sai take ji kamar taje yanzu tashake ta tamutu tahuta.

Raliya tace gaba da faɗin
"To da naga ma abun da yakawo ni har zan fita sai kuma nabi gurin Sakeenat ɗin cikin dabara na tambaye ta in da bazata gane ko wani abun bane,
nan take faɗa min
ai an shigo da ita asibitin jiya a sume gwajin farko a ka gano ciki ne da ita a take a gun *Parmsec ABDALLAH Idris ABDALLAH* yayiwa Dr Farooq kyautar miliyan 2 cikin murna take faɗa min dan ita ma Dr Farooq kyautar 200k yabata.da gidan ki nayi niyyar zuwa na faɗa miki wannan mummunar labarin naji kafin na iso ma ɓata lokaci ne wlh kawata wagga batu ya jijjiga ni bakaɗan b".
Tun kan Raliya takara sa maganar Na'ima da tuni jikinta yakama tsuma wani irin muguwar gumi ne ta karyo mata cikin masifar tashin hankalin ta mulmulo wani babban ashar ta auna tare da faɗin
"Ciki!? ciki take dashi cikin ma na SALEEM!!,
kutumar uban can wlh karya kike HAMDAH baki isa ki haifi ɗa acikin gidan nan ba har in ina numfashi,sai na nuna miki kasawar ki sai na shayar dake ɗaci fiye da wan da kika cusa min wlh baki isa ki haifi ɗa acikin gidan nan ba,dani kike zancen!!!".
wurgi da wayar tayi takama kai kawo cikin parlour'n tarasa ma mezata yi guda ɗaya sabo da sabar tashin hankali. jin karar buɗo kofa na gefen side ɗin HAMDAH dake tanan cikin babban parlour'n yasata yin wani irin juyi dan bataki ace HAMDAH ne ke kokarin shigowa cikin parlour'n ba tashake wuyar ta sai ta kaita lahira.
Ya SALEEM ne yafito daga cikin side ɗinta da ta kofar dake nan cikin babban parlour'n, wayace kare a kunnensa yana magana cikin sakin fuska yake faɗin
"Jikin da sauke sosai ɗazu aka sallame mu, ah babu wata matsala da ita da baby suna cikin koshin lafiya sosai yanzu kam,to ya karatu?".
daga cikin wayar Masa'ud dake jin kansa cikin wani irin muguwar farin ciki har yakeji inama yanzu ya ganshi a Nigeria cikin matukar happy yace
"Alhamdulillah ai ina ga a satin nan ma zan zo ayi rainon Baby'n nan dani,barima yanzu nashiga kasuwa nayiwa baby tsaraba".
"A'a kada kazo kabari kusa mi hutu tukun".
Ya SALEEM yafa fuska ɗauke da annuri.....
wani irin das karewa Na'ima tayi tana bin sa da ido har yashige corridor ɗin da zai sadashi da side ɗin sa,wato ma bai masan nata gurin ba dan ko in da take bai kallaba hankali sa gaba ɗaya ya mai da kan maganar da yake wan da dakaga yanayin sa kasan yana cikin zallar farin ciki da jin daɗi.
nan hankalin ta yatsanan ta wajen tashi sai take jin tashin hankalin da take jin kanta ciki yanzu yaninka wan da ɗazu take ji sau dubu,cikin cushewar ƙwaƙwalwar ta daya cushe a lokacin taɗaura hannu aka tanufi ɗakin ta tana faɗin
"Boka ya zakayi min haka yazaka bari yarin yarnan ta tasamu ciki bayan ga in da mukayi da kai".....


Har yamma muna tare dasu Mamie in da su Aunty Jaleela suka sharewa Inna ɗakin da wancan zuwan ta tasau ka,dan tace bazata koma ba har sai ta daɗa ganin saukin jikin nawa sosai,
sai a lokacin mazajen su suka zo suka kwashe su,bayan sallar magriba kuma Ya SALEEM yamai da Mamie gida...
Zaune nake gaban mirror ɗaure da towel sai mulke jikina da turaruka nake,dan har yau ban fasa jin jikina nayi min warin magani ba,sai dai duk tulen mulke turaren nan da nake baisa na daina jiba,fuska na kwaɓe kamar nasa kuka haka nake ji dan har cikin wuyana nake jin warin maganin sai kuma narika jin zuciya ta nason tashi.
yaturo kofar da sallama yauke a bakinsa,tsayuwa yayi daga bakin kofar daga cikin mirror ina hango shi yayin da shima yake iya kallona daga in da yake tsaye tacikin mirror,wani irin kallo yake bina da shi na musamman, niko ɓata fuska nayi kamar zan fashe da kuka.
a sannu yatako yazo in da nake yatsaya daf dani tabayana, yayin da yake cigaba da kallona tacikin mirror,a hankali ya saka hannunsa kan kafaɗa ta sai yarika tafiya da shi yazagayo shi ta saman kirji na, a sannu yaruko bakin towel da ke ɗaure a kirjina yakunce shi yasaka yatsarsa yaɗan ture shi sai yazame kasa,
A hankali yacigaba da tafiya da hannunsa har yasau keshi kan ababen kirjina, wani numfashi ya sauke da sai da najiyo sautin sa,
A sannu cikin wani irin salo yake sarrafa breast ɗina da hannunsa,baya nayi da kai na na manna shi sosai a jikinsa duk da bayana ne a jikin nasa amma ina jiyo kamshin sa mai sa na dai na jin warin maganin da nake jin kijina keyi min,
a hankali yarika tafiya da hannunsa ɗaya zuwa kan ciki na, yayin da hannunsa guda ke kan breast ɗina,
tafin hannunsa yamanna kan cikina sasoi wani numfashi yasau ke wan da yafi na farkon, a hankali yarika shafa cikin yayin da yasanya ida nunsa cikin nawa tacikin mirror'n.

a sannu yarankwafo da kansa gefen wuyana ya manna min kyakkyawar sumba, sai yayi sama da bakin sa yakawo shi sai tin kunnena a hankali yamosa laɓɓansa yace
"Menene yafaru ake ta ɓata fuskar".
baki na zunɓura nace
"Allah Ya SALEEM turaren ka yafi daɗi nayi ta shafa waɗan nan turarukan amma har yanzu ina jin warin maganin".
ido yatsurawa lips ɗina kana a hankali ya lumshe idanunsa tare da buɗe su lokaci guda kana cikin yanayin nan nasa yasaki murmushi mai karawa fuskar sa annuri yace
"Ok to ina zuwa"
yafaɗa tare da cire hannunsa a jikina yanufi kofa yafita,
zuwa can sai gashi ɗauke da turare har kala uku masu tsadar gaske da kamshi na musamman, sai dai dawowarsa na yanzu yasauya shiga yanzu singlet da gajeren wando ne ajikin sa.
miko min su yayi yana faɗin
"To gashi ki aje kirika shafasu idan nafita gobe zan karo miki wasu".
murmushi nayi ina feshe turarukan a jikina ina mai jin daɗin kamshin su..
abin da yaso bani mamaki shine da Ya SALEEM yamasa a jikina yakoma bakin gado sai naji kamshin yarage min daɗi sosai,ido naɗan zuba mishi daga cikin mirror da hannu ya yafato ni namike nazo in da yake ina zama kusa dashi sai naji kamshin yadawo yimin daɗi irin wan da nake so.
kwanciya yagyara kan gadon tare da janyoni jikinsa yaja mana blanket yarufe mu....★

Washegari bayan yatafi masallaci ɗakin da Inna take nakoma acan nayi salla,haka kawai nake jin tsoron zama ni kaɗai..

Satin Inna ɗaya takoma,kullum muna tare da Ya SALEEM ina cikin jikin sa yanzu nagama yar da bawai kamshin turare sa keyi min daɗin ba kamshin jikin sa ne keyi min daɗin har in ina jikin sa banajin warin magani da tashin zuciyar da nake ji har sai nabar jikin sa.
shima daya fahimci haka sai ya rage fita yanzu kusan kullum muna tare da shi ko a side ɗina ko side ɗin shi,yanzu bana yin girki Mamie ke girkawa tasa direba yakawo kullum sau uku a rana...

A ɓangaren Na'ima kuwa wani shiri take da ita kaɗai tasan ma'anar sa,abin da zai baka mamaki bata taɓa nuna cewa tasan da cikin ba in da shima gogan bai faɗa mata ba haka zalika bata nuna masa ta sani ba, bata kuma nuna wani abun da zai nuna cewa tasanin ba...🤔



Haka rayuwa yacigaba da tafi kwanaki sunata shuɗe wa, yanzu watannin cikin biyu kena,nuna kulawa da tarairaya gun Ya SALEEM ba'a magana,duk da kuwa irin yana yin rayuwar sa narashin yin doguwar magana.
Zaune muke a parlour ina shan kunun nono da yau Mamie ta dama min shi cikin flaks,
ina zaune a jikin sa a kasan carpet,ya mike kafafunsa ya ware su ya sanyani cikin su.
Aje cup ɗin kunun nayi jin cikina ya cika,hamma nayi jin bacci yafara fizgata,
ɗan karkato da kansa yayi yaleko fuskata, a hankali yace
"Tashi kije ki kwanta bari naje nayi wanka".
kafaɗa namake nace
"Ni dai tsoro nake ji muje tare".
ido yaɗan tsuramin da mamakin yawan faɗan tsoro da nake yi yanzu yace
"Ok to tashi muje".
yunkurin mikewa nake sai yayi saurin mikewa yariko kafaɗu na yamikar da ni tsaye kana yariko hannuna muka nufi side ɗin sa,
A bakin gado yazaunar dani kana shi kuma yashige cikin bathroom bayan wasu mintuna yafito ɗaure da towel a kugunsa,
zuwa lokacin kam nama kwan ta dan jin baccin sosai a ido na,
boxes da singlet ya saka ya hayo gadon ya janyo ni jikin sa. lumshe idanuna nayi jin yan da yake ai kin shafani da tsotsar sassan jikina da zafi-zafi,
hannunsa narike jin yana cusa shi cikin pant ɗina cikin muryar jin bacci nace
"Ya SALEEM bacci nakeji".
a hankali cikin ɗan fizgar numfashi yace
"Yau kam ki tayani hira ko ba mai yawa ba".
fuska na maraice
"Allah bacci fa nake ji sosai".
pant ɗin ya murzashi kasa tare da faɗin
"Ki daure kin ji kaɗan zanyi hirar ba jimawa zanyi ba".
shiru nayi badun komai ba sai dun yanzu yarage cemin zaiyi hirar tashi tun lokacin da aka sallamo ni a asibiti ya kai sati kafin yace nataya shi hira tun da yayi sau ɗaya sai da yakuma kai wani satin kafin yakara,yanzu kuma satin sa biyu kena acikin sati biyun baifi sau uku ya kusan ceni ba duk da ina ganin ɗinbin bukatar hakan a idon sa. amma yakan iya bakin kokarin sa wajen hakura ya kyaleni a cewar sa wai har yanzu ban warke ba sai bayan watanni biyu nan gaba...
Bayan komai yalafa yakai ni bayi mukayi wanka yadawo da ni muka kwanta nan take kuwa baccin da ke cike tam a idona ya sure ni...

Da misalin karfe 3 na dare na farka jin wani bala'in kishin ruwa wuyana ya bushe kayau,a hankali nazare jikina a nashi namike zaune,ina haɗiye miyau da kyar jin yadda wuyana yabushe,
a hankali yabuɗe idanunsa yazuba min tare da faɗin
"Ya dai".
nace
"Kishin ruwa nake ji".
"Ok". yafaɗa tare da mikewa da ɗan sauri yasauka a gadon in da ɗan ma dai-dai cin fridge yake aje nan gefen ɗakin yanufa yabuɗe yaciro gorar ruwa yahaɗo da cup yadawo in da nake,yasiyaye ruwan ya mika min,da sauri nakarɓa nakai bakina kurɓa ɗaya a nabiyu naciro kofin,na kalleshi kamar zan fasa kuka nace
"Ya SALEEM ba irin wannan ruwan ba".
da mamaki yace
"Wani iri to?".
rau-rau nayi da ido jin yadda kishin ruwan ke azalzala ta gashi dana sa wannan ruwan a bakina sai naji yayi min ɗaci sam ba irin sa nakejin kishi saba.
nace "Irin ruwan rijiyan gidan Inna"
ido yaɗan waro yace
"Ruwan rijiya kuma??".
yayi tan bayar da mamaki,kai na gyɗa, numfashi yasauke tare da zuba min ido sosai, ni dai fuska na marairaice kamar zanyi kuka,duban agogo yayi 3:15 AM.
sai ya mai da kallonsa gare ni kana yace
"Sha wannan ɗin idan gari ya wayen sai a kawo miki na rijiyar".
da sauri nagirgiza kai
"Allah wannan ruwan da ɗaci".
nayi maganar hawaye na sauka a idona dan ba shakka inajin muguwar kishi.
shiru yayi yana nazarin ta in da zai samo ruwan rijiya a eriyar unguwar tasu.
sauka yayi a gadon yaɗau jallabiyar sa yazura ya dube ni yana faɗin
"Ya isa bari a samo miki".
kai na gyaɗa ina binsa da kallo har yafita.

Yana fita bakin get ya nufa ya kwankwasa kofar mai gadi,koda yafito mai gadi yasha mamakin ganin sa cikin sakiyar daren na,
yadube sa da fargaba yace
"Ranka shi daɗe lafiya kuwa?".
Ya SALEEM yace "Lafiya,a ina zan sami ruwan rijiya yanzu"
Ido mai gadi ya zaro tare da dafe kirji yace
"Ruwan rijiya? a unguwar nan kuwa gaskiya dakamar wuya sai dai in a wajen unguwar nan tacan wani unguwar za'a iya samu, ranka shi daɗe kuma ai yanzu ko an fita ma da wuya a samu sabo da duk gidan da za'aje yanzu kam baza a sameshi a buɗe ba,kaduba lokaci kuwa yanzu oga??".
ɗan gajeren tsaki SALEEM ya ja yajuya batare da yace komai ba yaɗa go wayar sa yalaluɓo number Mamie ya dannawa kira tare da nufar parking space,
har sai da wayar takusa sinkewa kafin ta ɗaga cikin muryar bacci haɗe da fargabar ganin yakira ta acikin wannan tsohon daren hankali tashe tace
"SALEEM meke faruwa!??".
motar yabuɗe yashiga yazauna kana yace
"Mamie wai tanajin kishi kuma wai ruwan rijiya zata sha".
numfashi Mamie tasauke dajin akasin abin da take zato ta ce
"To SALEEM a nemo mata mana ba a son masu laluri irin nata subukaci abu surasa".
"Ai Mamie a unguwar nan kam baza'a sami ruwan datake so ɗin ba".
tace "Eh kwarai baza'a samu ba kam to bari nayi Wa Abbu'n ku magana akwai wani gida atacan karshen layin mu naga gidan akwai rijiya tun da laluri ne sai aje a rokesu".
yace
"Imma baza su bada kyauta ba sufaɗi ko nawane a biya su gani nan zuwa".
dariya Mamie tayi tace
"Kai haba bazasu faɗa ba ma bari na sami Abbu'n kun.".
kamar yan da tafaɗa tanufi ɗakin Abbu tasanar masa tare suka fita a cikin daren suka nufo get, koda baba mai gadi yafito yaji uzurin su,
Allah yasa aka taki sa'a baba mai gadin yana da number mai gidan tasana diyyar wani harkan da suka taɓa yi kwanakin baya.
nan Abbu yakira sa yagabatar masa da kansa sannan yayi masa bayanin abun da yake so.
A ɓangaren mutu min kuwa wato malam Shehu
da jin Abbu ne ke kiran nasa da niman wani abun a gare sa sai yaji daɗi dan kuwa yasan Alhj Idris da ɗan uwan sa Alhj Shu'aibu mutanene nagari masu tai makon al'umma da sada zumunci sakanin makota duk da sakanin gidan sa da nasu da ɗan rata amma alkairansu na isar masa.
yace babu damuwa suzo akwai ruwa ko duk rijiyar zasu ɗiba.

Ko da su Abbu suka isa gidan suka

3 Comments On HAMDAH
avatar
zarrah

1 year ago

Reply

Amazing story

avatar
taskar

1 year ago

Reply

Replying to zarrah

Thanks for your feedback

avatar
taskar

1 year ago

Reply

Littafi

Please Login or Register in order to submit comment