Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ciwon haukan nan natane yakuma tashi ganin yan da take maganar tana ɗaga jijiyan wuya,
da sauri na juya na nufi kofa na tura nashige da sauri
Na mai da kofar narufe tare da murza key,
numfashi na sauke kana
nakara sa cikin parlour na zau na
wani numfashi'n nakuma sau kewa
yayin da magan ganun Na'ima ke yawo cikin ƙwaƙwalwa ta
baki na taɓe tuno cewar da take SALEEM ɗin ma natane
"To ni ina ruwa na ma da ita da Ya SALEEM ɗin".
ɗan guntun tsaki naja tare da ɗaukar wayata naciga da buga game ina,
daga bisani na mike na shige bedroom naɗau ƙwanon danbun naman da jiya Mamie ta ai komin nazauna nasoma ci.

A can cikin babban parlour
har HAMDAH tafice cikin parlour'n Na'ima bata dai na kumfar baki ba, bala'in taciga da zazzagawa kamar HAMDAH na gaban ta.


Yau juma'a da safe bayan nayi breakfast ina zaune cikin parlour Rufa'ila tayi sallama tashigo
tace wai nazo in ji Hajiya,
dasauri na ɗago nace
"Nayi mata me?". Kai tasun kuyar tace
"Tace dai muje tare".
Kawar da kai na nayi na mai da idonuna kan tv nayi kamar banji a bin da tafaɗa ba
ita ko tananan durku she,
kamar an zabure ni namike tsaye na nufi babban parlour'n arai na nake ai yana in dai ai kine tofa bazan yiba, zan kuma kira Inna natan baye ta a she da ma ai ki tasa a kawo ni,
Ina gaba Rufa'ila na biye da ni muka shiga parlour'n. kamar rannan tana zaune ta harɗe kafa ɗaya kan ɗaya,
Karasowa mukai cikin parlour'n naja natsaya a gefen ta batare da nace komai ba.
cikin isa da takama ta ɗago tana yimin kallon baki isa ba,
yamusa fuska tayi tare da faɗin
"Kinzo kin tsaya min a kai ko a kan baki san ai kin ki bane ko so kike na sake yimiki bita".

Ido na kaɗa cikin yin ko oho da batun nata najuya ƙwayar idona zuwa kan tv,
Saurin juyowa nayi gare ta jin a bin da taci gaba da faɗa
"Daga yau naraba muku ai ki ke zaki rika share parlour'n nan da gogeshi da kuma wanke toilet in cikin parlour'n da sauran ai kace ai kaci da ya shafi nacikin eriya'n nan, sau ran ai yukan kuma ke Rufa'ila sai kicigaba da yinsu".
Baki nabuɗe da zum mar yin magana najiyo kamshin turaren sa,
Yau shigan manyan kaya yayi har da hula wacce ta daɗa kawata fuskar sa matuka
yayi ƙyau sosai cikin shigar.

tsayuwa ta na gyara tare da ɗan sosa kai ganin mugun kallon da yake wurgamin,
Baki na zunɓura naɗau sinsiyar da nagan shi a jiye a gefen ta nasoma sharar,kamar ranar yau ma mikewa tayi tabi bayan sa tana karai raya.

Shara da mopin kawai nayi ban wanke toilet ɗin ba kamar yan da tace, nakoma part ina ina shiga parlour na haye saman doguwar kujera na kwan ta.
kiran sallar juma'a ne yata da ni.

da misalin karfe 6 na yamma tsaye nake gaban mirror bayan fitowa ta da ga wanka nashirya cikin doguwar riga mara nauyi, na zau na gaban mirror na ɗau mai nasoma safawa
sallamar da nake juyowa sama-sama ne cikin parlour, yasani ɗan sakaita shafa man da nake naɗan kasa kunne ina mai son tan-tan ce muryoyin da nake juyowa,
huf na mike da sauri na nufi kofa jiyo muryar Fauzan da Nusaiba,
Da sassarfa na fito parlour'n,
Cike da murnar ganin su na isa in da suke na rungumesu, cikin muryar dariya haɗe da farin cikin ganin ƴan kannena daɗa washe baki nayi
"La Nusaiba Fauzan kune a she".
Dariya yaran sukayi Fauzan yace
"Eh ai Abbu ne yasa Baba Iro yaka womu kuma yace mumiki ƙwana haka".
yanuna ƴan yatsun tsa biyu, juyowa nayi nakalli in da Iro direba yake tsaye rike da ƴar karamar jakar kayansu,
"Ina yini Baba Iro".
"Lfy Lau" yace tare da mikomin jakar yajuya yana faɗin
"Su Hajiya sun ce a gai da ki".
to na amsa da shi yayimin sallama yafita.

Nakallesu nace
"To kuzo mujenku ciki".

Muna shiga bedroom ana kiran sallar magriba jakar hannuna na a je nashin fiɗa sallaya na ta da Sallah,
kasan cewar nayi alawala shigata wanka,
Nusaiba tashiga bayi tayi alawala tafito Fauzan ma yaje yayi gefena suka tsaya suka ta da sallar su.
Koda na idar gefe naɗan masa ina lazumi da zaman jiran idar wansu.

Suna idar wa huf Fauzan ya mike yana faɗin
"Zomuje Nusaiba yanzu ya dawo".
kallon sa nayi nace
"Ina kuma zakuje yanzu?".
yace
"Gaishi da Ya SALEEM muna shigowa muka ganshi zaije masallaci yace mushigo kafin ya da wo, nasan yanzu kam ya shigo tun da an idar da Sallan".
Kai na jin-jina nace
"To kuje amma karku daɗe ina jiran ku". Sukace "To".
Suka fita.

Ina nan zaune kan sallayar ina zaman jiran da wo wansu har a ka kira sallar Isha,namike na gaba tar basu da wo ba.
tsaki naja lokacin da na mike ina ninke sallayar, natako bakin gado nazo nazauna
"Koma tafiya sukayi".
nayi maganar a file
"Cap Allah in dai tafiya sukayi nima sai na tafi nikenan nayita zama ni ɗaya kamar mayya".

Ɗan shiru nayi zaune zuwa can naduba a gogo 9 saura.
da sauri na mike nanufi kofa da zummar zuwa duba su,har in kuwa sun tafi nima bazan zau naba sai natafi. ina ɗaura hannuna kan handle a na turo kofar, numfashi na sauke ganin sune, hannun ko wannensu na riko najawo su ciki ina faɗin
"Banace karku daɗe ba shine kuka daɗe ko?".
Nusaiba ta ce
"Ai Fauzan ne yace zaibi Ya SALEEM masallaci shine Ya SALEEM yace najirasu su da wo sai mu zo".
"Ai tun da muka da wo nace mutafi Ya SALEEM yace muci a binci tukun, ba kece kiketa cin a bincin a hankali bakiyi sauri ba".
Fauzan yafaɗa yana hararan ta.

Ni dai hannunsu najanyo
muka haye saman gado, hira mai haɗe da wasa muka tayi sai da dare tayi nisa sosai kafin mukayi bacci.

Washegari bayan munyi breakfast a parlour muka ya da zangon mu,ko da Aunty Na'ima ta nuro Rufa'ila naje nayi mata shara, tare muka tafi sashin nata da su, yau banji kiwuyan yin sharar ba kasan cewar rabin sharar ma Nusaiba ce tayi, Fauzan kam tun shigowar mu parlour'n yatafi site ɗin Ya SALEEM kasan cewar yau ranar Saturday ne yana gi da.
Muna gamawa muka koma.
Fauzan kam nacan gun Ya SALEEM sai da suka je masallaci sallar azahar kafin ya da wo.nan nashiga kitchen wainar fulawa mai haɗe da hanta na toya mana.
A parlour muka baje mukaci a bincin.

sosai naji daɗin zuwan su Nusaiba dan bakara min ɗebe min kewa suke ba, har nakan ji kamar a gi da nake,
ko da dare yayi yau ma sai da muka raba dare muna hira kafin mukayi bacci.

Washegari yakama ranar lahadi da safe muna zaune a parlour kiran Abbu yashigo wayata, Fauzan da ke rike da wayan yana buga game yamika min, na amsa tare da ɗaga kiran nakara wayar a kunne da sallama.
"Ina ƙwana Abbu".
"Lfy lau HAMDAH ya ƙwanan gidan da kannen naki?".
"Duk muna Lfy".
yace "To madallah kishirya musu kayan su an jima da yamma zan sa a dawo da su gida".

Ido naɗan waro sai kuma na marairaice fuska tare da langwaɓar da kai gefe na ce
"Ayya dan Allah Abbu kabarsu su kara ƙwana".
"A'a HAMDAH su dawo kinga gobe Monday a ƙwai makaranta kema kuma kinga goben zaki fara zuwa makarantar, kibari idan suka sami hutu mai yawa sai suzo miki har sai sun kare hutun kafin su koma".
"Ayya Abbu to muzo tare?".
da sauri yace
"A'a baƙyaso sukuma zuwa miki hutun ne HAMDAH?".
"Ina so". Yace to kiyi hakuri suna samin hutu nayi miki alkawari zan kawo miki su kinjiko?".
Kai na gyaɗa kamar yana ganina jiki ba ƙwari nasauke wayar.

Tun da mukayi waya da Abbu walwala ta taragu,
hankalina bai kara tashi ba sai da yamma tayi ganin guri yafara duhu nasan komai a kayi zuwa yanzu Baba Iro direba yana hanyar zuwa ɗaukar su Nusaiba.
Muna zaune a parlour suna cin abincin da na girka mana ni dai nakasa ci, natasasu gaba nayi jigum ina kallon su,
Da sauri na ɗago jin a na knocking jiki ba ƙwari namike na isa jikin kofar na buɗe,
rau-rau nayi da ido ganin baba Iro tsaye, ɗan guntun ƙwallar da tatsiraro daga idona ɗaya na share tare da amsa sallamar da yake.
Ya ce "Jeki kirasu suzo mutafi ga hadari ya taso kar ruwa ya iske mu a nan".
Baki na turo najuya a hankali ina tafiya a hankali wai ko dun ruwan zai sauko su fasa tafiyar.
Har gun mota na rakasu da ɗan guntun ƙwalla ta ina tsaye har motar tafita a gidan muna ɗagawa juna hannu.
A hankali kali najuya nakoma bakin kofar side ɗin na haura saman step uku wan da dole sai ka haura kan waɗan nan matakalar kafin ka shiga cikin side ɗin, natsaya kan step na karshe tun ban shiga cikin part ɗin ba naji part ɗin yamin girma.
zuru nayiwa bayan motar da nake hangowa daga in da nake tsaye wan da sai yanzu yasami damar haurawa titi sabo da a baben hawa da suke wucewa.
wani walkiya ne mai haɗe da tsawa ya welga dai-dai san da suka haura kan titin cikin tsananin tsoro da firgicin ganin hasken walkiyar ya hasko fuskata, bashiri na rufe ida nuna tare da calla kara na kame guri guda jikina na ƙyarma, numfashi na yayi wani irin fizga kamar zai bar jikina.
A hankali ruwa yafara sauka mai ɗauke da wata sassanyar iska mai matukar daɗi, a hankali nashiga sauke numfashi yayin da sassanyar iskarnan mai matukar daɗi ke kaɗawa ina jinsa cikin ilahirin jikina, a sannu narikajin zuciyata na sanyi tsoran na tafiya,
A sannu nashiga buɗe ida nuna har na buɗe shi gaba ɗaya.

wani murmushi ne ya suɓuce min ganin ruwa na sauka a gabana, tabbas nayi missing ɗin shi rabon da nashiga ruwa tun ƙwana uku da suka wuce, dan ƙwana biyun da mukayi da su Fauzan bana samin damar da zamu gana da ruwa da zaran Nusaiba taga na tuɓe kayana nashiga bayi tarika buga kofar bayin wai nayi na fito itama zata yi wankan.

zama nayi kan step ɗin da nake tsaye a kai naja sket ɗina sama nasaukar da kafafuna kasa na mikar da su ruwan na sauka a kansu, hannuna biyu na mika ina tarar ruwan ina wasa shi a duskata yana gangara cikin kirjina na...


Fito warsa daga bedroom kenan da shirin sa na tafiya masallaci da ɗan sauri yake tafiyar jin karar hadari sonsa ruwan ya'iskeshi cikin masallacin dan bayason rasa jam'i ko kaɗan.
ko sakiyar parlour bai isa ba ruwa ya kece dai-dai lokacin yaji sautin kararta tsaki yaja dan yasan itace mai wannan ihun,juyawa yy zai koma bedroom yagabatar da sallarsa a can, dan daga in da yake yana jiyo sautin tada ikama da ake a masallaci.
sai kuma yaja ya tsaya yana nazarin ta in da yajiyo sautin karar nata wan da yafi masa kama da tawaje ne ba taciki ba, kuma tun da tayi ihun sau ɗaya bata kumaba, da ɗan sauri yajuya yashige bedroom, in da laima ke aje ya isa ya ɗauka yafita.
Yana fita da mamaki yaja yatsaya bakin kofa duk da guri yayi duhu gakuma ruwan saman da a ke, hakan bai hanashi hangota ba sabo da hasken wuta da ya haske ko ina nacikin gidan.
Yayi mugun mamakin ganin ta zaune cikin ruwan da magriban nan.
Cike da ɓacin rai yabuɗe laimar yanufi in da take.

Saukar ran ƙwashi naji a kaina ƙwarara guda uku ba zato ba sammani, wani irin firgitaccen kara na sake a matukar razane na mike tsaye naduro daga saman step ɗin na ɗaura hannaye na duka biyu a kaina nashiga yamutsa gashin kaina har sai da ɗanƙwali na yafaɗi kasa, na mugun fir gita dan ni a tunanina aljanine yaran ƙwasheni dan da ma Inna tasha faɗa min na daina zama a bakin kofa da rashin ɗaura ɗan ƙwali da almuru in ba haka ba watarana sai aljanu sun min ranƙwashi a ka.

A kiɗime nashiga ja da baya nakuma rufe idanuna gam naki buɗewa dan karma naga aljanin, cikin tsananin firgici da tsoro nakuma ƙwallal kara ina faɗin
"Wayyo Allah Inna kizo aljani ya ranƙwashe wayyo Allah na wayyo Ummi na".
Ban kaiga rufe baki ba naji an damko hannuna, kuma dibirbir cewa nayi nashiga kokarin janye hannuna jin rikon bana wasa bane sai kawai nasaki kuka, har lokacin ida nuna a rufe ban kuma fasa kokarin janye hannun nawa ba.
muryarsa ne ya doki kunnena cikin tsawa yace
"Ke rufemin baki Sha-sha-sha kawai".

Duk da sautin muryarsa dake yawo cikin kunnen na bai sa na yar da shi ɗin bane kawai nafi yar da aljanine,
Sosai nake kukan kamar zan sheɗi sai fizge-,fizge nake,hannuna da yake rike da shi yamatse da karfi dare da kuma bugamin tsawan. "Kina hauka ne wai ke wate iri ce a daren nan kifito cikin ruwa kizauna dan sabo da tsabar sakarci cikin ruwa gurin zamane!!!". naɗiye kukan nayi ba shiri na buɗe idanuna jiki na rawa na zuba idanuna kan fuskar shi,kura masa ido nayi sosai ganin shiɗin ne dai, kai nashiga girgizawa,
Yace "Cire marasa kunyar ida nunanan naki a kai na wuce kibar nan sha-sha-shar banza kawai!.
Yafaɗa tare da sakarmin hannu wan da nake Jin sa kamar ya ɓalla min shi, da sauri mai haɗe da sassarfa najuya nanufi ciki,
yana tsaye har sai da yaga shige War ta yaja tsaki yanufi masallaci.

Ban tsaya ko ina ba sai bedroom nashige bathroom da sauri natuɓe kayan jikina na shan yasu naja towel na ɗaura nafita nafaɗa kan gado naja blanket na dukunkune ciki,
tsit nayi cikin blanket ɗin a haka bacci ya ɗauke ni".

Washegari bayan nayi sallah nakuma komawa bacci karfe 7 yunwa ta tadani dan rabona da abinci tun jiya da rana, bayi na shiga a gaggauce nayi wanka haɗe da brush na ɗauro towel nafito.
Ina fita nanufi kitchen batare da nasaka kayaba da towel ɗin ɗaure a kirji na dan yunwan nakeji bilhakki,
Ina shiga kitchen nashiga kokarin haɗa breakfast mafi sauki.

Tsaye yake jikin mota cikin shigarsa ta alfarma sai baza kamshi yake, a hankali yabuɗe marfin mota yana kokarin shiga sai kuma yaja baya tare da dai-daita tsayuwar sa,yaɗanyi shiru alamun nazari,makullin motar dake rike a hannunsa yake ɗan kaɗashi,mai da marfin motar yayi yarufe kana yajuya a hankali yanufi side ɗin ta.

Cikin kankanin lokaci na haɗa breakfast ɗina soyeyyen ƙwai da tea naɗau plt ɗin ƙwan da cup ɗin tea ɗin na nufi kofa,
Ina fita daga cikin kitchen ɗin sai ganin Ya SALEEM nayi ya.............





Mommyn Twins ne





*🌺HAMDAH🌺*

*NA*

*RASHEEDA S DIRECTOR*


_(Book one)_


*_________________________________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*👇🏻

https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association

*_________________________________*


MARUBUCIYAR👇🏻
*BA ABIN DA BAN GANI BA*
*INA SANE DA HAKA*
*ALFARMA*
*BAZAWARA CE ITA*
AND NOW👇🏻
*HAMDAH*


*Free page*

My no 08034690723



🅿️10




Yana tsaye cikin parlour, burki naja a bakin kofar kitchen ɗin sai kuma na turo baki tuno razanina da cin zalina da yayi jiya.
Shiko fuska ya suke ya ɗago hannun sa yakalli a gogon da ke ɗaure a hannunsa kana ya mai da dubansa kai na.
yace
"Mekike yi har 7:30 a gida baki shirya kin tafi makaranta ba!?".

Langwaɓar da kaina na nayi gefe nadaɗa cuno lip ɗina ina ɗan mui-mui da su tare da tsurawa cup ɗin dake rike a hannuna ido kamar shi yake min maganar.
A hankali nake magana cikin raina
"Nifa bason wannan makarantar nake ba ni ina da makarantar da na zaɓa Inna tasa Abba yacan zamin makarantar da nake yasani a wan da na zaɓa sannan kuma yanzu yazo ya canza min ni dai b..."
"Zaki wuce ne ko sai nazogun ina miki magana kina tsaye!?"
Maganar sa yazo min a sama
Zabura nayi wan da yayi sanadin motsawar ruwan tea ɗin da ke cikin cup ya fantsalu yazubo min kan kafa, jin saukar ruwan tea mai zafi kan kafata ban san san da nasaki cup ɗin yafaɗi kasa, tsalle natuma nayi gefe tare da sakin kara ina yarfe kafan da tea ɗin yaɗan zubamin,
baki na ɓare ina faɗin
"Wayyo Allah na wayyo zafi wayyo kafata".
Rai ɓace ya ke bina da wani mugun kallo cikin fusa tacciyar murya yace ,Zaki rufamin baki ki wuce kije kiyi shirin ne ko sai na tattakaki a nan!".
Da sauri naraɓa gefen sa ina ɗin gisa kafar da yarfe hannu sai mammatse ido nake nawuce ɗaki,
A bakin gado na zauna na a je plt ɗin ƙwan.
"Mugu yasani na ɓarar da tea ɗina bai san wahalar da nayi na girka ba".
Hannu nasaka nasoma ciki, ina gamawa namike naje na ɗau gorar ruwa dake ɗaure kan bedside nasha, kana nawuce bathroom nayi wan ka a gaggauce nafito.

Mai kawai na shafa nabuɗe wardrobe na zakulo laidar kayan makarantar da tun ranar da yakawo na wurgasu ciki,
Naciro wan da nafi tunanin shine na bokon, nazame towel ɗin kasa na ɗaurashi a kuguna nafara kokarin sa rigar kenan naji an banko kofa.
Cikin hanzari naɗago kai na karaf muka haɗa ido da shi da sauri najuya na bawa kofar baya, tsaki yaja yajuya yana faɗin "5min na baki idan kika wuce hakan"
Yakaɗa yatsarsa yabata sautin kat-kat,kana ya juya yafita.

Da sauri nakarasa sa rigar cikin hanyar zari na kammala shirin naɗau school bag na rataye nafito da sauri,har lokacin yana tsaye cikin parlour yana ganina yajuya yanufi waje nabi bayan sa cikin sauri,
Direct parking lot yawuce ni dai ina biye da shi ganin yashiga mota sai naja na tsaya,
leko kansa yayi tawaje cikin faɗa yace
"Kina ɓatamin lokaci fa!".
A sannu natako na buɗe gefen mai zaman banza nashiga na zauna tare da mai da marfin narufe, yatada motar yana jan tsaki,
tuni mai gadi yawan gale masa get yasakai yafita.
Ido nazubawa titi har muka isa cikin makarantar wanda ke cikin unguwar, bai bar makarantar ba har sai da yaga nashiga aji, bayan yagama jamin kunne kan rawan kai, yaku ma ce idan yaji ko yaga wani a bun da ba dai-dai ba sai ya tattakani, samun lfyta na nanitsu na mai da hankali kan abin da ya kawoni,sannan yaciro kuɗi yamika min 5k yace idan a ka tashi na hayo adai-daita nadawo gida.


Karfe 1:30 a ka tashe mu, kamar yadda yace nahayo napep na dawo gida.
Tun daga ranar kullum da kai na nake zuwa makarantar kuɗin da ya bani dashi nake biyan kuɗin abun hawa yakai ni makarantar, wani Sa'in ma bana hawa napep ɗin kasan cewar ba wani nisane sakanin mu da makarantar ba, duk ran da naji kafata na kaikayi sai na taka da kafa natafi.

Yau kimanin sati uku kenan da fara zuwana makaranta ban taɓa fashi ko jin kiwuya ba saboda ina son karatu sosai,
kasan cewar yau juma'a da wuri muka taso, ina shiga gida abinci nasoma ci ina gama wa nashiga wanka,
Ban wani ɓata lokaci ba nafito sabo da yau na kudura niyyar zuwa gida.
Nashirya cikin atamfa riga da zani simple makeup nayi naɗau gyale da jakata da na shirya kayana kala uku a ciki nazari wayata da ragowar kuɗin da Ya SALEEM yabani nayi waje,
Ina fita na hangi Na'ima tsaye ita da wata mata sai shekewa da dariya suke suna tafawa,
taɓe baki nayi tare da kawar da kai na
Na kulle kofar side ɗin gaba ɗaya nazare key ɗin najefa shi cikin jaka, ina juyowa suka kuma shekewa da wani irin matsiyacin dariya suka tafa.
Ko in da suke ban kuma kallaba nayi gaba a bina.


Bayan ta matar nan tabi da kallo har tafice a cikin gidan
kana tamai da dubanta kan Na'ima tace
"Kawata da ma wannan abar ce a ka kawo miki har kike niman ta da hankali? haba kawata karki ba da ni mana, ƴar da a cikin mintuna kalilan zaki shafe babin ta a wuce gurin".
Wani shu'umin murmushi Na'ima tayi tace
"Aminiya ta Rariya kenan, sai kace kin mance wacece Na'ima ai da ita da babu duk ɗaya suke acikin gidan nan, ai ba a yi macen da ta isa ta aure min miji ba, kinsan meye matsayin zaman ta a cikin gidan nan?. zamane na kanwa tana zaune a gidan wanta."

Wacce takira da Raliya tace "Nasan ki ai kawata baƙya wasa to dai kikara kulawa kinsan irin waɗan nan yaran ba'a gane al'kiblarsu, kinibabbu ne bare wannan danaga kamar ida nunta a soye yake bakiga irin kallon da take mana ba".
Yamusa fuska Na'ima tayi kana tace
"Babu komai a gun sai shirme wawuyace na karshe da zaran lokacin da na ɗibar mata yacika zata yi gaba".
Dariya suka saka Raliya tace
"To kawata ya ake ciki wancan a bun yayi ai ki kuwa?".

Kasa tayi da muryar ta tace
"Ai ban faɗa mikiba bayan nayi amfani da shi da ƙwana uku kamar yan da kika cimin ranar ƙwana uku zan ga a bin da zai faru, sai gashi da kanshi yazo da bakin sa yake furta bukatar sa, duk da ranar in Ina cikin ɓacin ran wancan shegiya mai jan fuskar, amma karkiji wani gefen zuciyata in da yacika da farin ciki ba,duk da bai buɗe min sirrin bukatar tasa ɓaro-ɓaro yanuna min ba, cikin halin nan nasa na isa da kasaita izza miskilanci, yagwada min a lokacin nasan nesa takusa zuwa kusa. sai dai fa tun wan can ranar harfa hau baikuma tinkarata da bukatar sa kwatan kwacin irin na wancan ranar ba, sai dai ni idan naji lungu na namin kaikayi na kai masa yasosa min."

Raliya tace "Kada ki damu zan zo mukoma gurin nan tare idan yaga idon ki sai yafi bamu manyan makamai".
"An gama kawata sai na ganki".
Nan suka cigaba da kulle-kullen su wan da su suka san ma a narshi.


Ina fita adai-daita natara zuwa gidan mu da ke state locos har kofar gida yakai Ni nasauka nabiya sa kuɗin sa nanufi ciki,
Da sallama na turo karamar kofa da ke gefe da jikin get,
da sauri baba mai gadi dake zaune nan gefen ɗakin sa yana al'wala yamike yana faɗin
"Wane ne haka ba ƙwanƙwasa kofa?".
Zai kuma magana nakarasa shiga ciki, baki ya washe yana faɗin
"A'a HAMDAH ce Barka da zuwa".
Nace "Ina yini Baba mai gadi".
Ban jira amsawar sa ba nayi cikin gidan da sauri, da direct part ɗin Ummi na na nufa tun daga kofar parlour nafara faɗin
"Ummi, Ummi na nazo".
Shiru parlour'n babu kowa nashige cikin bedroom Ina cigaba da kiran sunan ta.
Kasake Ummi da ke zaune bakin gado tayi, da sauri haɗe da sassarfa na karaso in da take na wurga jakata kan gado nafaɗa jikin ta ina faɗin
"Oyoyo Ummi nazo".
girgiza kai Ummi tayi tare da yin murmushi taɗago ni tana cewa
"To sai kin nukurkusani kafin nasan kinzo".


Baki na washe namike nazauna gefen ta
"Ummi ai duk murnar ganin kine".
tace
"Sai Kuma a haɗa da shiririta".
Murmushi nayi itama murmushin tayi tana bina da kallo na tabbata itama tayi missing ɗina.
Nace "Ummi Abba fa?".
"Ai bai dawo daga offece ba".
Nace "To Fauzan fa".
tace "Yana can sashin Mamie'n ku yanzu suka bar nan shida Nusaiba da Adil da Abid".

Da sauri na mike tsaye ina faɗin
"Laa sun zo ne har da su Aunty Rafee'at da Aunty Jaleela ɗin?".
Tace "A'a babanun su ne suka kawo su".

Gyalen jikina na zame na aje bakin gadon najuya zan sa gudu Ummi ta ruko hannuna najuyo ina fuskan tarta,
tace
"Kitafi a nutse ki dai na wannan guje-gujen".
Kai nagyaɗa mata na zame hannuna nafita da sauri na nufi part ɗin Mamie..

A parlour na iskesu gaba ɗayan su Mamie
Nusaiba Fauzan Adil Abid. suna ganina suka taso da gudu suka rungume ni muka sa ihun murna muna tsalle,
dariya Mamie tabimu da shi, nasakesu na karaso in da take na zauna gefen ta tare da ƙwantar da kaina a kafaɗar ta, murmushi mai sauti tayi tashafa kai na tana cewa
"A'a HAMDAH anzo ne?".
cikin muryar dariya nace "Eh Mamie ina yini".
ta amsa ɗauke da dariya a bakin ta.
Nan muka buɗe hira sai da a kafara huɗuba a masallaci kafin Mamie tace wa Fauzan yakama Adil da Abid sutafi masallaci ni da Nusaiba kuma muje muyi al'wala muyi sallah.koda mukayi sallar a binci mukaci muka ɗaura daga in da mukatsaya.


Har yamma ina shashin Mamie sai da na dumfari dai-dai

3 Comments On HAMDAH
avatar
zarrah

1 year ago

Reply

Amazing story

avatar
taskar

1 year ago

Reply

Replying to zarrah

Thanks for your feedback

avatar
taskar

1 year ago

Reply

Littafi

Please Login or Register in order to submit comment