Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

nufa lokacin shikuma ya sauke wayar daga kunnen shi yashige cikin side ɗin shi, nabi bayan shi da sauri ina shi yana shigewa cikin bedroom ɗin sa, sai naja natsaya a sakiyar parlour'n.

Ido nayi ta zubawa kofa dan ganin fitowar sa amma shiru,har nafara jin kafafuna sun gaji da tsayuwa,a sannu na taka na isa bakin kofar, na daura hannu na jikin kofar nasoma knocking a hankali har sau uku kafin na sau ke hannuna,shiru bai buɗe ba nakuma ɗago hannu zan kai jikin kofar, sai ya buɗo kofar da karfi tare da riko hannu na ya fizgo ni cikin bedroom ɗin,yamai da kofar yarufe sai ya tura Ni jikin kofar ya manna baya na da jikin kofar, yayin da hannunsa guda ke rike da nawa,ƙwayar ida nunsa yasanya cikin nawa yana yimin
Kallon cikin ido,
sai kuma ya furzar da iska daga cikin bakin sa kana yace
"Jiranne bazaki iyaba sai kin ƙwanƙwasa min kofa?".
Kai nashiga girgizawa dan narasa ma me zan ce dan tsoro.

Ida nunsa ya janye cikin nawa sai ya juyar da kansa gefe, tare da kuma furzar da iska, sai ya saki hannuna ya juya.
numfashi'n tsoro na sauke jin yasaki hannu na dan nagama ɗauke wuta kan cewa buguna zaiyi,
lai da ya ɗauka kan mirror yamika min da sauri na amsa na juya da sauri sai naji ya..............





Mommyn Twins ce




*🌺HAMDAH🌺*

*NA*

*RASHEEDA S DIRECTOR*


_(Book one)_


*_________________________________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*👇🏻

https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association

*_________________________________*


MARUBUCIYAR👇🏻
*BA ABIN DA BAN GANI BA*
*INA SANE DA HAKA*
*ALFARMA*
*BAZAWARA CE ITA*
AND NOW👇🏻
*HAMDAH*




My no 08034690723




🅿️15




Ya kuma rike min hannu tare da juyo ni,har sai da na ɗan garu da jikin sa, nayi saurin ja da baya sai naji kofa ta tare ni, gani na daf da shi ba karamin tsorata nayiba,
fuska ya suke tare da faɗin
"Abin banza ne Ba kuɗi a kasa a ka siye shiba".
jin a bin da ya faɗa sai nayi saurin ɗagowa na kalle sa, ba shiri nayi kasa da kai na ganin ni yazuba wa ido fuskar sa kuma a suke,
"Zaki ɗau ka ne ko tsayuwar zaki cigaba da yi".
Da sauri na kalli in da yayi nuni da yatsar sa goron ce kwara huɗu a kasa, saurin kallon lai dar da goron ke ciki nayi sai naga laidar taɓule ta kasa, bani raba ɗaya biyu garin saurin da nake ne handle yaɓula laidar, da sauri na zame kasa nashiga tsino su.

Hannun sa ya ɗago yacusa cikin sumar kansa yayin da ɗaya hannun sa ke rike da gungun sa, a hankali ya juya yasoma tafi wata kofa naga yashiga wacce nafi zaton bathroom ne,
ina ganin shige warsa nayi saurin mikewa na fice daga cikin ɗakin da sauri,
Ina fita naja wani irin wawan burki kaɗan yarage muyi karo da Na'ima da tasako kai tana kokarin shiga ɗakin,
Cikin wani irin masha huriyar tsananin tarin mamaki take bina da wani irin kallo wan da yafi kama da kollon tuhuma.
Gefen ta na raɓa nawuce da sauri nafice gaba ɗaya daga cikin side ɗin.


Bayan ta tabi da kallo har taɓace wa ganin ta,wani uban numfashi tasauke tare da furta
"Kutumar uban can uban me take a nan".
Da sauri ta bankaɗe kofar tashiga kamar wacce a ka wurgo,sai tashiga bin ɗakin da kallo yayin da takejin zuciyar ta yana wani irin tafarfasa,
HAMDAH har cikin maƙwancin minta lallai tayi mugun yin sake.
tawani taune baki tare da yin ƙwafa, jin saukar ruwa a bayi yasata nufar kofar bayin ta tura kofar da karfi tasako kanta ciki.


Dai-dai lokacin yakashe makunnin panpo dake sauka a kanshi, yazaro towel ya ɗaura a kugun sa, kana yatako yaraɓa gefen ta yafice daga bayin.
Sai a lokacin Na'ima tadawo daga mutuwar tsayen da tayi tana kallon shi, wani irin juyi tayi tarufa masa baya,
tasha gaban sa dai-dai lokacin da yake kokarin zama bakin gado,
da mamaki yaɗan kalleta ganin yan da ta wani sha gaban sa tana bin sa da kallon tuhuma.

"SALEEM me wannan yarin yar take a nan mekuma wannan wankan yake nufi".
Ta jefo masa tan bayar tana girgiza da cika da basewa.
ko mai bai ceba, sai mikewa da yayi yaje yaciro kaya yasoma sawa,
bin sa ta kuma yi cikin ɗaga murya take faɗin
"SALEEM nace menene dalilin shigowar yarin yarnan ɗakin nan ban gane bafa, kafa dai na rai namin hankalin wai...."
Saurin dakatar da ita yayi ta hanyar ɗaga mata hannu batare da yabar ta ta karasa faɗar a bin da take son faɗa ba,dan surutun ta yasoma yi masa yawa, yayi mata a lama da hannu tafita,
Kugu ta rike tana faɗin
"Eh dole kace na fita, sabo da a sirin ka yana daf da tonuwa,na rantse baka isa ka rai namin wayo ba".

Wani uban tsawa ya buga mata da sai da ta taune harshen ta da ta buɗe baki zata kuma ci gaba da maga na.
yatsar sa ya kaɗa tare da nuna mata kofa cikin tsawa yakuma faɗin
*"get out!!"*
Kame-kame tashi ga yi sai kuma tajuya ganin babu a lamar wasa a kan fuskar sa, ta fice tana ciza baki tare da ban ko kafar da karfi.
tsaki yaja ya haye gado ya ƙwanta.


Yau tun da safe goggo Hauwa ta shirya ta tafi gidan su Abbu ganin Inna bata da niyar zuwa,
Da yamma ina ɗakin da Inna take in da nanne yanzu yazame min gurin wuni wani sa'in ma har da ƙwana,
Inna na zaune a bakin gado tana jan jarbi, Ni kuma ina
ƙwance a gefen ta rike da waya ina chatting da ƴan ajin mu,
ɗan gajeren tsaki naja ganin an ɗauke wuta nan da nan kuma zafi yaziyar ci ɗakin,mikewa nayi zaune ina faɗin
"Kai gaskiya yau a na zafi daga ɗau ke wuta ji yadda zafi ya cika ɗakin".
Inna da ta fara ɗan gyn-gyaɗi a zau ne ta buɗe ido tana faɗin
"Ai kam garin a tsaye yake cak sai dai da alama in Allah yaso zai bamu ruwa dan ga hadari na yawo a sama".

"Allah ya kawo shi bari nidai na wasa ruwa gas kiya ina jin zafin nan sosai".
nafaɗa ina zamowa bakin gadon,sam bana shiri da zafi kaɗan ne yake tada min hankali,
Doguwar rigar jikina na zare yarage daga ni sai sket ƴar ciki da bes. nanufi kofar bayi.
baki buɗe Inna ke kallona kana tace
"In ba kalen muraba
ina wani zafin da yan zunnan kikayi wanka kikuma yin wani, wato baki dai na wasan ruwan nan naki bako".
Shigewa cikin bayin nayi ina faɗin
"Kai Inna zafi a ke fa".
"Allah shi sawaka, da kan ka karika kalo cuta wa kan ka".
Ina jin ta tayi ta surutun ta.

Abin da Inna ta hasashon shi nayi dan kuwa shigewa cikin ruwan nayi na zauna, naɗau lokaci kafin na wanke jikina da zallar sabulo na fita a cikin ruwan na mai da sket da best ɗin da nacire nafito.

nakaraso bakin gado in da na a je rigata na mika hannu zan ɗau rigar, yaturo kofa da sallama,
Inna ta amsa tare da gyara zama tana faɗin
"An dawo ne mai sunan malan". da sauri na juyo karaf muka haɗa ido,
cikin hanzari na ɗau rigar nanufi kofar bayi, na zunɓuro baki ina kunkuni cikin wuya.
"Shi ya'iya cewa wani wai in mutum zai shigo yayi sallama ya tsaya kafin ya shigo amma ai gashi shi da ga yin sallamar ya shigo".
Baki na murguɗa
nashige cikin bayin na mai da kofar na rufe.
Ina saka rigar na fito sai na tadda shi zaune Inna na kan zuba masa hira shiko na ai kin latsa waya,
ɗan ƙwali da waya ta na ɗau ka na raɓa ta gefen sa nayi waje,
Bedroom ɗina na koma naci gaba da chatting ɗina....
Tun da nashiga ban kuma fitowa ba sai da naji da wowar goggo Hauwa...★


Yau farin ciki na ya daɗa karuwa dan kuwa ƴan gidan mune suka taho gaba ɗayan su,duk muna tare a ɗakin da Inna take.
Abbu Mamie Abba Ummi Fauzan Nusaiba,
Ina zaune a sakiyar ahalina yayin da zuciya ta ke cike tap da farin ciki.
Bakina yakasa rufuwa sabo da sabar murna, kusan wuni sukayi a gidan kasan cewar yau karshen mako ne,
Ko da zasu tafi sunyi-sunyi su tafi da Inna taki fir tace suje zatazo gada baya, in taga ma yimin ƙwanakin da ta yanke zata yi min kafin za tazo..

Ranar da Inna tacika sati ɗaya, tun da safe tasa goggo Hauwa tashirya mata kayan ta.
Ina zaune a gefen ta nayi shiru kamar ruwa yaci kai na,
kallon Inna nayi cikin marairaice murya kamar zanyi kuka nace
"Ayya Inna karki tafi yau kikara wani sati dan Allah".
dariya goggo Hauwa tayi tare da cewa
"To kece za a zau na a kare miki kwanakin a nan sannun ki fa".
Muskutawa Inna tayi tana faɗin
"Sati guda zan musu na dawo daga nan kuma nayi shirin koma wa gida".
Kamar an zabure ni na mike nace
"To shike nan ni bari na shirya kayana mutafi gidan to".
da sauri goggo Hauwa tace
"Ki shirya kayan ki kibi wa da izinin wa kuma?".

Baki na ɗan zunɓuro sai kuma nayi saurin cewa
"To ai rakaku zan yi".
"Ai ho to ai sai dai in rakiyar".
Waje nayi ina faɗin
"Ai dama rakaku zanyi na dawo".
A kasan rai na kuwa faɗi nake
"Ai idan natafi bazan dawo ba sai dai mu dawo tare".

Tun da a kayi sallar Isha nakasa zama alla-alla nake muyi mutafi, haushi na ɗaya da Inna tace Ya SALEEM ne zai kai mu gashi har yanzu bai zo ba.

da sauri nafito daga cikin bedroom, na tako bakin kofar da Inna take daga bakin kofar na tsaya ina faɗin
"Inna nikam fa na gama shiri na kuzo mutafi kawai tun da Ya SALEEM ɗin bai zoba".
Nafaɗa ina shiga cikin ɗakin,cak naja na tsaya daga bakin kofar ganin sa tsaye da alama fita zaiyi, goggo Hauwa narike da jakar Inna ita kuma Inna tana gyara zaman mayafin ta,baya nayi a han kali,
shiko yasako Kai yafita muka rufa masa baya.

Ko da muka zo gurin mota kokarin shiga baya nake, goggo Hauwa tace nashiga gaba ita zasu zauna da Inna a baya,babu musu na shiga dan ina alla-alla na ganni a gida,
jakata na da ɗa makale shi dan nasan goggo Hauwa tana gani zatayi magana.
A hankali yayi wa motar ki muka fita a gidan,ganin mun ɗau hanya farin cikina yagaza ɓoyuwa sai murmushi nake,
muna isa nariga kowa sauka nayi sashin Ummi na da sauri, su Inna Kuma sashin ta dake cikin gidan suka nufa ita da goggo Hauwa.

A parlour na tadda Ummi tana ganina tamike tana faɗin
"Har Inna'r ta iso kenan".
"Eh tana part ɗin ta".
nafaɗa ina karaso wa ciki, Ummi ko kofar fita ta nufa,
aje jakata nayi saman kujera, na bi bayan ta muka tafi part ɗin Inna,a nan muka tadda su Mamie,hira sosai a ke cike da jin daɗi da kaunar juna,
ko minti 5 ban yi da zama ba Fauzan yashigo da gudu yace
"Aunty HAMDAH wai kizo".
tun kan na am sa yajuya yayi waje da gudu.

Bayan sa nabi da sauri ina faɗin
"Kai wake kirana".
nafaɗa da karfi.
bai tsaya ba bai kuma amsa ni ba sai da ya isa jikin motar Ya SALEEM, in da shi ke jingine jikin motar,
ɗan nesa da su naja na tsaya.
A bu ya mikawa Fauzan daga in da nake tsaye bazan iya gane ko menene ba kasan cewar dare ne gurin kuma babu hasken wuta sosai,
ga yanayin yan da Fauzan ɗin yakarɓi a bun yajuya da murna yayi sashin Inna, nasan komai a kayi abun ƙwalama ne.

Ina tsaye ban koma ba ban kuma karaso ba duk da nasan cewa shine mai kira nan, gefen direver yazaga yabuɗe marfin sai yajuyo in da nake yaɗan kalle ni
"Naci gaba da jiran ki kenan".
ido na waro jin a bin da yafaɗa sai kuma naturo baki nace
"Nifa kwana zanyi"
wani kallo ya wurgamin
tare da shige wa cikin motar batare da ya kuma cewa komai ba.

Tuni idanuna suka ciko da ƙwalla, ganin yata da motar sai na karaso jikin motar nabuɗe nashiga, muna fita a gidan hawaye suka fara gangarowa kan fuska ta,
har muka isa hawayen bai tsaya ba,yana dai-dai ta parking nafito daga motar da sauri nanufi kofar side ɗina, ina ɗaura hannun na kan handle natuna nabar makullin side ɗin a cikin jaka a parlour'n Ummi,
dasauri najuyo dai-dai lokacin yafito daga cikin parking space yana kokarin wucewa side ɗin sa,daga in da nake tsayen na dubeshi tare da share hawayen da yazubo min nace
"Nabar key ɗin kofar a gida".
tafiya yasoma tare da faɗin
"To sai ki ƙwana a gurin".
baki buɗe nabi bayan sa da kallo har yashige side ɗin sa.
"Naƙwa na anan, ai na rantse gida zan koma".
Najuya da sauri da niyyar nufar get sai kuma na tsaya ganin karfe 10 tayi nasan ko na fita ma ba lallai bane na sami a bin hawa,wani hawaye naku maji na zubo min, baya nayi sai na zame na zauna kan step ɗin kofar,nacusa fuskata sakankanin cinyoyina,jin wani
kuka ya zo min sai kawai na fashe da kukan...★

A hankali narika jin kamshin sa na masoni,zuwa can sai naji motsi kusa da ni. duk da nasan shine dan kamshin sa ya sanar min da hakan,
ban ɗago ba sai ma sautin kuka na da nakara,
Jin karar buɗe kofar sai na ɗago da sauri dai-dai lokacin yake zare key ɗin da yabuɗe kofar da shi,
da sauri na mike na sako fata saman step ɗin da yake kai tare da jan guntun tsaki, nawuce shi nashige ciki da sauri.


Direct bedroom na shige cike da bakin cikin a bin da ya min, nayi niyyar kwana a gida amma yahana ni yaɗau koni yadawo da Ni sannan kuma yace wai na kwana a waje,
Ina shiga ɗaki nazube kan gado naci gaba da kuka na.

Da karfi a ka turo kofa jin kamshin sa yasanar min shine, yatako bakin gadon sai ji nayi ya zauna daf da ni kokarin, matsawa nake dan jin yan da yamannu da jikina sosai, sai jinayi ya yasako hannun sa ta kasan ciki na yaɗa go ni gaba ɗaya ya rungume ne tare da
matseni da karfi har sai da naɗan saki kara, cak na sai da kukan da nake sa bo da tsoro mai haɗe da mamaki, ban kaiga dawowa daga duniyar mamakin da natafi ba naji ya sauke hannun sa kan.......★




*Kuyi maneji bayawa*
*Gaskiya yanzu ina busy bana da time sosai ba lallai bane kurika jina kullum*





Mommun Twins ce



*🌺HAMDAH🌺*

*NA*

*RASHEEDA S DIRECTOR*


_(Book one)_


*_________________________________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*👇🏻

https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association

*_________________________________*


MARUBUCIYAR👇🏻
*BA ABIN DA BAN GANI BA*
*INA SANE DA HAKA*
*ALFARMA*
*BAZAWARA CE ITA*
AND NOW👇🏻
*HAMDAH*




My no 08034690723




🅿️16





Kan bakina yakamo lips ɗina ya haɗa ya matse da ɗan karfi,
musu-musu na soma yi ina jujjuya kai, dan naji zafin yadda ya matse min baki ga matseni da yayi a jikin sa ko ƙwakƙwaran motsi nakasa, kallon cikin ido yake min yayin da sautin numfashin sa ke ɗan fita da sauri-sauri, niko tsorone yadaɗa rufeni ganin yanayin nasa,
A sannu yashiga
sassauta rikon da yayi min, sai ya
saki lips ɗin.

Da sauri na kai hannuna kan baki na dan, kafin yasaki lips ɗin sai da ya ja shi, yunkurin mikewa nashiga yi amma na kasa sabo da yanzu hannun sa da yacire kan bakina, baya na yamayar yadaɗa zagaye ni da shi.

Hawaye nasoma dan ganin yaki sakeni,
Idon sa ya saka cikin nawa da ke siyayar da ƙwalla da sauri na rufe idanuna, dan kallon nasa tsoro yafara bani, jin yadda jiyoyoyin idanuna ke wani irin fisga a duk harbawan second da idanunsa ke cikin wana, cikin wani irin murya da yafi kama da mai jin bacci yasoma magana
"Ni kikewa tsaki ni sa'arki ne?".
da sauri na buɗe idanuna tare da girgiza kai nace
"Dan Allah kayi hakuri wlh ba da kai nake ba".
Nayi maganar hawaye na ciga ba da zuba a ido na,
Hannunsa ya cirosu a bayana da sauri na mike a jikin sa na diro a gadon na masa can,
Mikewa tsaye yayi ya ya mika hannu yafisgoni na dawo jikin sa cikin suke fuska yace
"Rufamin baki kishare hawayen nan".
Da sauri natoshe bakina da tafin hannuna,
"Cire hannun kishare hawayen kikuma dai na kukan".
Yafaɗa idanunsa a kai na,
hawayen nashiga share wa sai dai kukan ne nakasa dai nashi, sai ma ji nayi kamar daɗa karuwa yake da kanshi.

Shiru yayi yana kallo na a hankali yadaɗa maso da ni jikin sa, yasaka yatsar sa ya lakato hawayen da ke bin fuskata, sai ya ɗago yatsar zuwa saitin
fuskar sa yaɗan sura masa ido sai
kuma ya soma magana.
"Ban ce ki rufamin baki ki dai na kukan nan ba?".
Yakarashe maganar yana mai da idanun sa kaina,
kai nashiga gyaɗa wa da sauri ina kokarin sai da kukan, ganin yan da ya suke fuskarsa a karshen maganar,
tafin hannuna na saka na share hawayen tare da ɗan jan shashsheka sai kuma na shiga faɗin
"Dan Allah kayi hakuri Ya SALEEM Allah ni bawa kai nayiwa tsaki ba".

Ido kawai ya tsura min batare da yakuma cewa komai ba,niko baki na turo gaba,ina kokarin janye jikina da ga gare shi,
Sakeni yayi yajuya yasoma tafiya ya isa bakin kofa ya ɗaura hannusa kan handle sai ya juyo tare da faɗin
"Allah yasa wani yakuma zuwa kice zaki bishi wani gurin kigani tun da ke baki da hankali,
kuma kada ki kuskura na fita kici gaba da kukan nan idan kuma ba haka ba....."
Sai ya kaɗa yatsar sa, tare da buɗe kofar yafita,
Komawa nayi da baya nazau na bakin gado,
na turo baki tare da murguɗa shi
"Ina ruwan shi idan ma nayi kukan, dan mugun ta Inna'r ce zai hanani bi, kuma tana dawowa ma tare zamu koma Dass da ita".

Washegari
Ranar haka na wuni gidan gaba ɗaya babu daɗi sai naga gidan yayimin faɗi haka,
tunanin Inna duk yabi ya dame ni ina son na gan ta, sai dai na tabbata Ya SALEEM bazai taɓa barina naje gida ba,
narasa me yasa yanzu yake hanani fita, da zarar nazo fita a gidan zai ganni yakuma hanani fitan,
da kuwa har nafita bai ma san nafita ba har naje na kwana ma a gidan mu bai sani ba,
amma yanzu da zarar nayi yunkurin fita zai ganni yakuma hanani fitan.

Haka nan dai ranar nawuni babu daɗi gashi babu makaranta bare na fake da zuwa makaranta naje gida.

fito wata daga bayi kenan ɗaure da towel a kirjina,
nanufi parlour da ɗan sauri jin wayata da na barshi cikin parlour'n na ringing, kafin na isa ma Kiran ta katse,
Na ɗau wayar ina duba mai kiran nawa da kusan karfe 10 na daren nan,ganin Number ne sai nashi ga kokarin mai da kiran dan sanin ko wane ne,
dai-dai lokacin a ka turo kofa da sauri na juyo,
lokacin yake mai da kofar yarufe,
yana rike da jakata da na barshi a parlour'n Ummi na,
yatako cikin parlour'n a hankali,
kafata na ɗaga ina kokarin barin gurin duba ga a bin da ke jikina towel ne kaɗai, kai na ma babu ko ɗan kwale yana ma jike sabo da wan keshi da nayi.
kafin nayi yun kurin barin gurin har ya isoni cikin parlour'n, ya tsaya ɗan nesa da ni
"Ke zo". yafaɗa, ida nunsa a kai na, a hankali natako nazo in da yake,
laɓɓansa yasoma masasu cikin yana yinnan nasa wan da yafi kama da dole a ka sashi maganar kokuma bacci yake ji
yace "Kina gani na da jakar ki baza kizo ki karɓa ba ni ɗan ai ken ki ne?".
komai ban ce ba sai tura bakin da nayi na miko hannu ina kokarin amsar
jakar, sai ya riko hannun nawa yarike cikin na shi,
ya janyo ni daf da shi,a sannu ya a je jakar a kasa,
yadube ni
yana cigaba da faɗin
"Ni ɗan ai ken kine da zan ɗauko miki a bin ki baza kiyi min godiya ba".
bakin nakuma turowa gaba nace
"Kayi hakuri".
"Godiya nace ba hakuri ba".
kasa nayi da kai na ganin irin kallon da yake wurgamin mai sani jin wani irin a bu a cikin jikina wan da yafi min kama da tashin tsigar jiki,
"To nagode".
nafada ina ɗan jan hannu na da tafin hannuna ke cikin nashi, ya sarkafe yatsunmu guri guda .


Ɗaya hannunsa yasaka yaɗa go haɓata tare da jefa idon sa cikin nawa
"Ok, to ma zakice irin bazaki faɗe shi kai tsaye ba sai kin sa to ɗin baki goden ba kenan".
"Ya ilahi Ya SALEEM yafiye korafi wannan wani irin mutum ne,ko mai zakayi wai shi sai yaci gyaran ka".
Katse min tunani yayi da jin irin a bin da yake daɗa yiwa tafin hannuna,
"Nagode".
nafurta da sauri,ina taɗan jajjan hannuna, bai kuma cewa komai ba sai cigaba da haɗe tafin hannun mu yake,
zuwa can kuma sai ya cire hannunsa da ya ɗago haɓata da shi, ya cusa hannun cikin suman kansa tare da kawar da fuskar sa gefe ya furzar da iska cikin bakin sa, sai ya saki hannuna.

Da sauri na sun kuya na ɗau jakar na nufi kofar bedroom har nakai hannuna zan buɗe kokar ya kuma dakatar da ni ta hanyar faɗin
"Ke". sai naja natsaya nan bakin kofar a sannu yatako in da nake sai ya saka hannun sa kan kafa ta, in da gashi na ke kwance a gun,
yaɗan murza gashin da yatsun sa kana ya furta
"Haka kike yawo kanki a buɗe".
da sauri nace
"Wan ka nayi".
"To idan a kayi wan ka sai baza a ɗaura ɗan ƙwali ba".
Shiru nayi ina jin yadda yake cigaba da murza gashi na, sai ya saki gashin da sauri na shige cikin bedroom ɗin.

Ina shiga ciki na a je jakar nawuce da sauri naje na ciro kaya nasa ka....


Yau kwanan Inna huɗu da tafiya kullum sai mun yi waya nayi ta ce mata ta dawo ni nagaji da zama ni kaɗai kokuma tace wa Ya SALEEM yabar ni naje, tace a'a nabari ai takusa karasa satin da zata musu ta dawo...


Na'ima ce zaune ita da kawar ta Raliya, da yanzu ta kawo mata ziyara, suka kule can cikin ɗaki,
wani uban numfashi Raliya tasau ke bayan kawar tata tagama koro mata a bin da ke a zal'zarar ta a zuciya,
tadubi Na'ima tana faɗin
"Tabɗi jan wato tafito daga cikin ɗakin sa?ai da shakure banza kika yi sai kin ji dalilin da yakai ta ɗakin mijin ki".
"Him ke dai bari wai dan na shiga ina tan banyan shi Dalilin shigo warta,baki ga yan da yake yiba, kamar zai mare ni, badun na fita ba na tabba da sai ya kai min hannu,wlh yarin yarnan bazan taɓa barin taba sai na nuna musu nawa malamin yafi nasu".
Raliya tace
"Ƙwarai kuwa dan kuwa suma nasan ba haka suka zau na ba, kina sammanin uwarta zata zauna haka ne taga ƴarta cikin wannan daular tazauna haka babu tai mako,ai ni bana raba ɗaya biyu haɗin auren nan na su ma ba a banza ba".


Zama Na'ima ta gyara ta daɗa fuskantar Raliya da kyau tasoma magana
"Nifa kawata bama wannan ba,
nafara zargin SALEEM a duk san da nazo jikin sa wani kamshi najeji na daban ba nashiba".
"Kamar yaya".
Raliya tafaɗa da fuskar mamaki.
"Ina nufin kamshin wani turare na daban, ba nashi ba, dan ni babu kalar kamshin sa da ban sani ba, kuma nayi ta bin cike cikin turarukan da yake amfani dasu banji mai rin kamshin ba, tabbas ina zargin sa".

Na'ima taci gaba da faɗin.
"Yanzu kam gaskiya hakuri na ya kare,
dan nakasa gane me malam na kan tudu yake nufi, shekaran ta uku yanzu tun tana wata uku a ke abu ɗaya kuma kullum magana ɗaya yake faɗa,
ai ki ya gamu sai dai a jira lokaci.
gaskiya Ni ina tunanin yanzu ai kin sa baya wani ci,gara kawai na can za wani tun lokaci bai kure ba,
dama a kwai wani malamin da a kayi min kwatancen sa kuma shima an ce ai kin sa kamar yankan wuka yake".

Hannunta Raliya ta rike tana faɗin
"Ni ina jin mamakin ki idan naga kina kokarin ganin gazawar malam na kan tudu, a tunanina kafin kowa ya gode masa

3 Comments On HAMDAH
avatar
zarrah

1 year ago

Reply

Amazing story

avatar
taskar

1 year ago

Reply

Replying to zarrah

Thanks for your feedback

avatar
taskar

1 year ago

Reply

Littafi

Please Login or Register in order to submit comment