Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

tap idanuna sai na juya da sauri na ɓalle marfin motar nafi ina faɗin "Ina zuwa dan Allah Ya SALEEM".
nafaɗa ina fita a motar da sauri nanufi cikin asibitin ina ji yana kira na ban ko juyo ba...
ina isa bakin kofar room ɗin da Inna take ciki na tura kofar da sauri nashiga,juyowa su Abbu sukayi da su Ummi da suma suka shigo yimata sallama zasu tafi, Inna ta ɗago idanunta tare da yafato ni da hannu da sauri na zo in da take sai ta riko hannuna tace
"Baku tafi ba kai mai sunan malam me kuke jira dare fa nayi".
juyawa nayi jin tana maganar tana kallon kofa, lokacin yake mai da kofar yarufe yakara so ciki,maganar tace tasani juyowa gare ta
"Wannan haske da kema kika kara bayamma ce kawai ai gashi ya bayyano kansa gasu a hannun ki sun fito raɗa-raɗa,bari cikin yayi wata 6 zan zo na ɗauke ki mutafi kisha magani har sai kin haihu,yoo ai ba'a wasa da wannan cutar faraɗ ɗaya yake kashe jariri dole kisha ganyayya ki".
tafaɗa tana jujjuya hannuna,
baki Ya SALEEM ya taɓe tare da faɗin
"Ku wai har yanzu bazaku dai na wannan al'adar takuba garin jinya a kwaso wata cutar".
sai kuma yayi kasa da murya
"Babu inda zata bare aje garin yin wani jinya akashe min ɗaya da wasu gangayya ki".
yayi maganar ne a iya laɓɓansa bai san yafito ba.
murmushi Ummi tayi dan tasan yayi maganar ne batare da sanin yafito ba,
Abbu kuwa dakuwa yayi masa yace
"Kaci gidan ku shine mu bamu mutu ba".
"Shi kanshi ma dai da bai mutun ba".
cewar Mamie,
Inna tace
"Rabu dashi yoo kai ɗin badun taima kon Allah da ganyen ba da kakai nan,kai akwai wan da yakai ka laulayi ma haka a ka haifo ka fari soll da kai jiki duk bayamma kayi ta wahalar da mutane, ai idan ɗan naka yayi gadon ka kam wannan ƴar tashiga uku,bari ma kaga a sallame ni in zan koma tare zamu koma da ita,a tare cutar da wuri tun kafin ɗan naka yazo duniya ya wahalar da mutane".
Mamie tace
"Ai kam dan ita tasha wuyar ka tun ranar da kazo duniya har kayi arba'in".
murmushi nayi dan natuna wani rana Inna tataɓa yimin hirrar har take faɗa min ma ita ta yayeshi.
shiko fuska ya gimtse ganin su Aunty Rafee'at suna dariya,
Inna ta dube ni da murmushi tana faɗin
"To kuje sai da safe,kai kuma mai sunan malam gobe kazo min da farin goro".
sai kuma ta kuma mai da duban ta kai na taci gaba da faɗin
"Idan rayuwa ya juyawa mutum baya kada ya mance da Allah shike yaye da muwa da kunci,duk abun da yasa mi bawa da sanin uban giji,ina daɗa faɗa miki kada juyawar rayuwa tasaki mance wa da Allah kiyi amfani da hakan ki saɓa masa, ki gode masa sai ya yaye miki, ki yawaita ambaton sunan Allah da yawan addu'o'i a duk halin da kike ciki".
yanzu ba ni kaɗai maganar Inna yajefa cikin wani yana yi ba gaba ɗaya mutanen cikin ɗakin sai da jikin su yayi sanyi Ya SALEEM ne yayi karfin halin cewa
"Wai wa'azi kika koma ne a buɗe miki gurin da zaki rika faɗakar da jama'a".
murmushi kawai tayi kana ta kuma duba na tace
"To kuje sai da safe mai sunan malam kar ka man ce gobe kazo min da farin goro".
to ya amsa da shi kana ya nuna min hanya da hannu a hankali nafara ɗaga kafata sai kuma nakuma juyowa na kalle ta kai ta gyaɗa min haɗe da murmushi.
"Inna ina dai zaki kuma zuwa min muzauna?".
nafaɗa ina duban ta yayin da wasu zafafan hawaye naji suna zubo min wan da ban san dalilin zuwansu ba.
kai ta gyaɗa min tace
"Zan kuma zuwa mu zauna takwara ta Aysha, idan aka sallame ni".
kai na gyaɗa yayin da hawayen suka zubo nayi saurin tare su da bakin gyalena,karo na farko da na taɓa ji Inna ta kirani da asalin sunana kuma sunan ta da nace.
murmushi Aunty Rafee'at tayi cikin yanayin mutuwar jiki tace
"To in ma kina so kiji abun da zamu ce ne,to mu munci girman mun yafe wannan karon ma kisake zuwa ki zauna mata".
da sauri na juya nafita jin wani kukan na zuwar min
Ina jiyo muryar ta tana amsa wa Aunty Rafee'at maganar,
tun kafin na isa gun mota kukan ya kwace min nashiga motar na zauna ina ci gaba da kukan.
sai lokacin shima yashigo ya zauna jiki a sanyaye duk yan da yayi dani akan nayi shiru na dai na kukan na kasa da kukan muka isa gida.
yana dai-dai ta parking ya janyoni jikin sa nan yashiga kokarin sai da kukan ta hanyar ai kamin da zafafan sakon ninsa masu nutsar da kwantar da hankali,kana ya ruko hannuna muka fito har bedroom ɗina ya kaini kana yace na zauna zai je masallaci ya dawo,
yana fita na kulle kofar naje nayi al'wala nagabatar da sallar magriba ina zaune kan sallayar har aka kira sallar isha kana na mike na gabatar tare da shafa'i da wutiri. bayan nagama duk kanin addu'o'i na na mike na koma kan gado,babu jimawa ya dawo daga masallacin na buɗe masa kofa yashigo..
ranar a makale a jikin sa na kwana...
Washegari bayan ya dawo daga masallaci ganin inata hamma alamun baccin bai ishe ni ba sai ya janyo ni jikin sa muka kuma kwanciya...★



★★★★
After 5hr
★★★★

Wani irin zabura nayi na mike zaune firgit jikina nawani irin cirawa babu ko kakkauta wa, gefe da gefe na na waiga baya cikin ɗakin da sauri na duro a gadon kai na babu ko ɗan ƙwali doguwar rigar bacci ce kawai a jikina sai dai doguwa ce har kasa.
da sauri haɗe da sassarfa na fita aɗakin nanufi side ɗin sa,cikin sananin tashin hankalin dana sin ci kaina ciki tun a cikin bacci na da Ni kai na ban san dalilin sa ba, na tura kafar bedroom ɗin sa da karfi nashiga ina kiran sunan sa.
yana tsaye cikin ɗakin yabai wa kofa baya da gudu nayi in da yake ina cigaba da kiran sunan sa da faɗin
"Wayyo Ya SALEEM ina jin tsoro ni dai ka mai dani gurin Inna in aka sallame ta mukoma Dass da ita".
nafaɗa dai-dai lokacin da na iso in da yake na rungume shi tabaya tare da cusa fuskata a tsakiyar bayan sa.
fuskata na rika cusawa cikin basan sa ina juya fuskar da cigaba da faɗin
"Ya SALEEM ni dai ka mai dani gun Inna ni dai Dass zan koma bazan zauna a garin nan ba"..
a sannu ya juyo tare da ruko ni yajuyo da ni yazamo muna fuskantar juna, ya tallafo fuskata da nake ta kokarin mai dashi cikin kirjinsa ido nawaro cikin ida nunsa duk da ina cikin firgici da kiɗima sai da na tsorata da ganin yan da idanunsa suka ka sauya kala daga farare da ɗan ɗigon silver suka rine suka koma ja.
A hankali cikin furzar da huce mai zafi daga bakin sa yace
"Menene me kike wa tsoron".
zillewa nayi na mai da fuskata cikin kirjinsa ina faɗin
"Ni ma ban sani ba ban sani ba Ya SALEEM nidai tsoro nake ji ka kai ni gurin Inna kawai ni na fasa zama a garin nan".
nafaɗa ina mai fashewa da matsanancin kuka.
a hankali yarika shafa kai na yana ɗan bubbuga bayana kana a hankali yace
"Je ki sako hijabi kizo muke".
kafaɗa na make ina faɗin
"A'a nidai tsoro nake ji muje tare".
shiru yayi yana ci gaba da shafa kaina kana zuwa can
yace "To dai na kukan haka muje".
da sauri na ɗago kaina nashiga share hawaye na, ido yaɗan tsuramin sai ya girgiza min kai a hankali nashiga mai da numfashi a sannu kukan yatsaya sai da yaga na dai na kukan kafin yaruko hannuna,ya je gaban mirror yaɗau makullin mota, muka nufi side ɗina tacikin babban parlour yabi dani saboda kayan da ke jikina.
muna shiga bedroom wardrobe yabuɗe yaciro doguwar riga haɗe da hijibi sai hula mai raga,yazo yatuɓe min rigar baccin da ke jikina, zuwa yanzu kam jikina wani irin mutuwa yayi ina tsaye shi yasaka min kayan ban iya yin komai ba,kana yaruko hannuna muka fita,
jan kafafuna kawai nake har muka isa cikin parking space, ganin naja na tsaya ban shiga motar ba sai ya buɗe motar yayi min alama da hannu a hankali nashige na zauna shima yazaga gefen sa yashi yaja motar muka bar gidan.
ajiyar zuciya nake ta sauke wa acikin motar yana tukin yana waigo ni,
da mamaki na ke kallon hanyar da ya ɗauka madadin hanyar asibiti sai kuma naga yaɗau hanyar gidan mu.
yana sharo kwanar layin mu
tun daga farkon layin har kofar gidan mu jama'a ne tam sai kuma shigowa ake daɗa yi, a sannu ya'isa gefen kofar gidan mu in da motoci suke jere sun fi guda 50 ya gyara parking a gefe,yajuyo ya dube ni yace
"Sauko muje".
ido kawai na bishi dashi sabo da nauyin da naji harshe na yayi min, har yafita a motar ina nan zaune ko kyakkyawar motsi na kasa maganar sa naji yana faɗin
"Sauko mana".
a sannu na juyo in da naji maganar nashi yabuɗe kofar yana rike dashi sai ya miko hannu yakamo nawa a hankali na zuro kafafuna waje na mike tsaye ya mai da marfin ya rufe kana muka soma kusawa cikin jama'a,
duk inda muka gilma sai naji mutanen gurin suna faɗin
"Sannu SALEEM sai hakuri".
hannu kawai yake ɗaga musu baya cewa komai har muka shiga cikin gidan, farfajiyar gidan shima cike yake taf da mutane ƴan uwan mu na garurruwa daban-daban wasu suna al'wala wasu kuma tsuna tseitseye wuce su mukayi yanufi side ɗin Inna muna isa bakin kofar side ɗin sai na fizge hannuna daga rukon da yamin da gudu na shige cikin parlour'n ta ina faɗin
"Inna kin dawo gida ne".
turus nayi ganin mutane tam cikin parlour'n wasu na kuka cikin yin kasa da sauti wasu sun yi jugum, can gefe su Ummi ne sai su Aunty Rafee'at da suke zaune a kasa kowa ta haɗa kai da guiwa, sautin kukan su ne ke fita a hankali, Nusaiba da Fauzan na zaune gefen su suma sai kukan suke.
gefe kuma wasu ƴan uwan Inna ne waɗan da suke Dass dana garinnan sai sharar kwalla suke,sauran mutanen ciki kuma ban ma san su ba. waige-waige na shiga yi da karfi na furta
"Inna kina ina ni dai mutafi kawai yau".
nan hankalin mutanen da suke zaune cikin parlour'n yadawo kaina da sauri su Aunty Jaleela suka ɗago idanunsu ya sun duma alamun sunci kuka sun koshi,
su Mamie ma suka ɗago wan da sai yanzu suka san da shigo wata.
hanyar kitchen na nufa ina ci gaba da kiran sunanta har na shige ciki narika waige-waige babu kowa ciki,
da sauri Mamie ta mike tabiyo bayana lokaci ina kokarin fitowa ita kuma tana isowa bakin kofar hannuna tarike hawaye na sauka a idon ta tace
"Zo nan HAMDAH".
kokarin janyoni take nafizze hannuna da sauri mai haɗe da gudu nayi kofar inna ina cigaba da kiran sunan ta mikewa su Ummi sukayi da sauri suka rufa min baya.

Wani irin tsayuwa nayi ganin su Abba da Abbu Goggo Hauwa durkushe a gaban mutum an rufe shi da zani tun daga kansa har zuwa kafafun sa yana kwance kan taburma.
Goggo Hauwa sai sharɓe hawaye take tana ta kokarin danne kukan da yake ta kokarin kwace mata, su Abbu kuwa ɗan gajerun hawaye ne a karkashin idanunsu sai kai yatsa suke suna ta ɗan goge shi,kamar an zabure ni nakuma faɗin
"Inna Inna Inna wai kina ina ne Inna ni dai kizo mutafi kawai".
nafaɗa ina ta waiga gefe da gefe na,kuka Aunty Rafee'at ta sake da karfe ta rungume ni Aunty Jaleela ma ta taho ta rungume ne. ido nake bin ko wannensu da shi sai kuma na fizge jiki na na juyo gun su Ummi na ce
"Ummi Mamie Inna fa ko tatafi ne Ni dai zan bita mukoma".
hawaye Ummi ta share tamiko hannu tana kokarin ruko Ni da faɗi
"Zo ki zauna tukun".
baya nayi tare da ɓoye hannuna ta baya na.
tuni kukan da Mamie da Goggo Hauwa suke ta ɓoyewa yafito cikin muryar kuka Mamie take faɗin
"Innalillahi wa'inna'ilaihirraji'un² kudubi halin da HAMDAH take ciki wlh bata cikin hankalin ta,kidawo cikin hayya cikin ki HAMDAH!".
tafaɗa tana girgiza ni.
Ido kawai nabita da shi, Abbu ya mike yaruko hannuna yadube ni da kyau yace
"Zo ga Inna nan kiyi mata addu'a Inna ta rasu tariga mu gidan gaskiya".
shima ido kawai na zuba masa har ya jawo hannuna yakawo ni in da suke durkushe yayi kasa da hannuna ya durkusar da ni kamar yadda sukayi, sai kawai na zame kasan nayi zaman dirshem,
cikin karfin hali Abbu yakai hannunsa yaja zanin da aka lulluɓe mutum da naga suna durkushe a gabansa nan farin kyalle ya bai yana,
a hankali yakuma kai hannunsa yakun ce igiyar da aka ɗaure saman farin kyallen da shi kana yaja ƙyallen.
Wani irin bugawa kirjina yayi da mugun karfi har sai da nakai hannuna dai-dai kan kahon zuciya ta na dafe da karfe.
ganin fuskar Inna ya bayyana idanunta a rufe kamar mai yin bacci yayin da fuskar ta ke ɗauke da murmushi kamar a kirata ta amsa.
da sauri na kai hannu nashiga girgizata ina faɗin
"Inna Inna kitashi".
sai kuma na waiga gun su Abbu da tuni hawaye suka shiga zarya kan fuskokinsu nace
"Abbu Abba meyasa Inna ta kwanta a kasa kuce mata ta tashi ta hau godo, shine aka lulluɓe ta aka rufa mata kanta Inna bata son tarika rufe kanta fa in zatayi bacci kar kurufa mata kanta kubar ta a buɗe kuce ta tashi tahau gado".
mai da kallo na nayi kanta nacigaba da girgiza ta
"Inna ba kince zamu tafi Dass idan aka sallame kiba to kitashi mutafi yanzu Inna nidai kitafi da Ni tsoro nake ji,kitashi mutafi Inna Inna kitashi".
nafaɗa da karfi ina jijjigata.
tuni ɗakin yakaure da koke-koke.
Wasu maza su biyu ne suka shigo rike da makara suka sauke kusa da ita suka dubi Abbu sukace
"Alhj mutane suna ta jira a waje an kimsa ku a ke jira".
yagirgiza kai kana ya mika hannu yamai da likafanin ya rufe mata fuska yaɗau reshi kamar na ɗazu kana yaja zanin yakuma rufe ta da shi.
kankame ta nayi da karfi ina faɗin
"Abbu ka buɗe ta Inna bata rufe fuskar ta in zatayi bacci".
mikewa tsaye Abbu yayi kana ya dubi Abba da kansa ke durkushe yace
"Shu'aibu kama mu sata a kan makarar".
binsu da idanuna da babu ko ɗigon kwalla acikin sa nayi sai kuma na
Kife fuskata a jikin ta da karfi nace
"Abbu kusata a kan gado kada kusa ta akan makarar".
Ya SALEEM da shigowar sakenan yadube su yace
"Wai meye hakan kenan kun sata gaba kuna ta wani koke-koke amfanin me kukan zai mata in baza ku iya mata addu'a ba kuje waje dan Allah".
yafaɗa yana nuna musu hanya,yakuma cewa
"Kuje waje".
dukan su suka fita har dasu Mamie karaso wa in da nake kwance jikin Inna yayi yaruko kaɗata yaɗa go ni kana yaruko hannuna su Abba suka ɗagata suka sakata cikin makarar,yajan yo ni muka fito yakusa cikin jama'ar yashige dani cikin wani ɗaki dake kusa da na Inna shima mutane ne dayawa cikin sa harda su maman Rabi da wasu ƴan Dass anan ya zaunar dani kana yafita,lokacin su Abbu suka fito da Inna daga ɗakin ta suka nufi waje shima yarufa musu baya....

Idanuna narika ware wa ina bin ɗakin da nake cike da kallo maganar maman Rabi naji tana faɗin
"Sai hakuri HAMDAH Inna tazo kan ka ida iya rayuwar kenan Allah ya jikan ta yamata rahama halayen ta nagani yabita".
A sama naji maganar ta sai kuma kamar an zabure ni na mike da sauri nafice cikin ɗakin nanufi kofar bita daga parlour,
cikin hanzari Mamie ta mike tana faɗin
"Tsaya HAMDAH ina zakije".
tuni nayi waje dai-dai lokacin a ka sallamar da sallar da aka mata da gudu nayi gun lokacin ake kokarin ɗago makarar sai na faɗa kanta na rirrike ta da karfi ina faɗin
"Ina zaku kai ta kar ku tafi da ita Inna ki tashi kar su tafi da ke".
ɗagoni yayi cak a kanta kana ya juyo ni muna fuskantar juna,sai Abbu da Abba da wasu ƴan'uwan Inna su biyu suka ɗago makarar suka nufi in da motar kai gawa da aka shigo dashi cikin get,da sauri na waiga sai nashi kokarin janye hannuna ina faɗin
"Ya SALEEM ka sake ni zasu tafi da ita, kace kar sutafi da ita karku tafi da ita Inna wayyo Inna wayyo Inna karki tafi kibar niii......"
wani irin luuuu idanuna sukayi...★
da sauri yataro ta tafaɗo jikinsa dai-dai lokacin su Mamie suka karaso in da suke ihu Aunty Rafee'at take tana faɗin
"Wayyo HAMDAH ki tashi".
tafaɗa tana jijjigata ajikin Ya SALEEM,Mamie da Ummi kuwa salati suka shiga yi,
cikin azama ya cicciɓe ta yayi hanyar part ɗin Mamie wan da yafi kusa da inda suke, direct bedroom ɗin ta yashiga da ita yashin fiɗata saman bed,
Suma suka rufa masa baya ban da Ummi da ke tsaye tana ambaton sunan Allah.

A can cikin bedroom ɗin Mamie kuwa da sauri Mamie Aunty Rafee'at Aunty Jaleela da su Nusaiba da suka shigo da gudu yanzu duk suka nufi bakin gado in da yakwantar da ita yana tsaye a kanta yana kallon ta gaba ɗaya babu numfashi a jikin ta,
da sauri Mamie ta iso tashiga girgiza ta tana kiran sunan ta,sai kuma ta juya taɗau gorar ruwa dake ɗaure kan bedside tabuɗe ta yayya fa mata, nan ma ko gizau tana nan kamar ɗazu,
jin karar motoci alamun an fara tafiya makabar ta, kallon su Aunty Rafee'at da suke ta rusar kuka yayi kana yace su fita dukan su dan tanan ne kawai zai sa Mamie taji karfin guiwar kulawa da ita yadda yakamata in suna nan suna wannan kuka to fa bazata iya taɓuka mata komai ba.
a gaba yasasu suka fita yakuma ce musu kar su kuskura ya dawo yasa mesu agun,nan yanufi gun motar sa yashiga yabi bayan sauran ragowar motoci suka ɗau hanyar makabarta...

A can cikin ɗakin Mamie kuwa,duk wani ruwan da take ta yayya fawa HAMDAH a banza dan ko gizau batayi ba tana kwance kamar gawa,cikin sananin tashin hankali tafito waje ta nufi side ɗin Inna dan ɗazu in ba idanunta bane suka gane mata ba dai-dai ba to ɗazu taga wata mako ciyar su wata ma ai kaciyar asibiti.
tana shiga parlour'n kuwa ta hango ta da sauri ta isa ta ruko hannunta tare da faɗin
"Dan Allah Hajiya zo muje ki duba HAMDAH tana kwance babu numfashi tare da ita".
tayi maganar hankali tashe, matar ta mike suka fita da sauri suna shiga ɗakin tacewa Mamie tabata ruwa,
tamiko mata wanda ta yayyafa mata ɗazu tace
"Mai sanyi zaki bani".
da sauri Mamie ta isa in da fridge yake taciro ruwa mai sanyi tazo ta mika mata,takarɓa ta buɗe marfin ta tsiyaye ruwan a hannunta ta yayyafa mata daga fuskar ta zuwa kirjin ta tayi hakan har sau uku kana nan ma bata mosa ba.
sai ta mikawa Mamie gorar ruwan kana ta shiga ɗan danna kirjin ta a hankali a hankali.
cikin tashin hankali ganin har lau babu wani alamar motsi
Mamie tace
"Hajiya kodai asibiti za'a kai ta abun yayi mata yawa gashi tana ɗauke da jaririn ciki".
numfashi Hajiyar ta sauke tace
"To gaskiya kam in dai haka ne gara a hanzarta kai ta asibitin
dan gudun faruwar wata matsalar, amma dai bani ruwan nagani".
takuma karɓar ruwan tazuba da yawa a hannunta tawasa mata a fuska,
wani irin dogon numfashi taja, takuma wasa mata, nan ma takuma jan numfashi.
hamdala Mamie tashiga yi da godiya wa Hajiyar tace
"Ba komai amma dai kada a barta a gida a kaita asibiti a dubata da kyau".
Nan tayiwa Mamie sallama ta fita ta koma side ɗin Inna.

Sama-sama nake jiyo maganar tasu sai kuma na mike da sauri ina kokarin durowa a godon,
Mamie tace
"Tsaya HAMDAH ki nutsu kinji".
tafaɗa tana mai dani zaune ido naɗan tsura mata,sai ta gyaɗa min kai tace
"Zauna ki huta,zakici abin ci?".
kai na girgiza mata,tace
"To in haɗa miki tea kisha ko kaɗan ne ko HAMDAH kisha kaɗan kawai".
shiru nayi,sai ta sake ni ta juya kan bedside ɗin da kayan tea suke jere agun tashiga haɗa wa kana ta miko min cup ɗin tana faɗin
"Karɓi kisha kinji?".
tayi maganar cikin muryar lallami.
A hankali na miko hannu na karɓi cup ɗin nakai bakina wani irin bugawa naji zuciya ta tayi da sauri na ciro cup ɗin batare da na kurɓi tea ɗin ba,na aje cup ɗin kan bedside na mike da sauri yayin da nake jin kaina
yana wani irin juya min da mugun sara min.
muryar Mamie naji tana faɗin
"HAMDAH hakuri zakiyi zamukuma yi baki ɗaya Inna kwana ya kare yanzu addu'ar mu shine kaɗai tafi bukata a yanzu".
da sauri na kalli ta cikin fizgar numfashi nace
"Mamie da gaske wai Inna rasuwa tayi bazan sake ganin taba daga yau kuma bazata tafi da niba zata bar ni a nan".
Wasu zafafan hawaye ne suka shiga zubowa Mamie tace
"HAMDAH duk wani wan da kika gansa a duniyar nan tofa karshen sa kenan yanda mukazo da ɗai-ɗai haka zamu koma lokacin Inna ne yayi mutuwa akwai zafi amma hakuri shine maganin".

Zuwa yanzu bana gane mema take faɗa da sauri na nufi kofa ina ji tana kira na tuni nayi waje da gudu na nufi side ɗin Inna,
a guge nafaɗo cikin parlour'n har lokacin mutane na nan dam dan sai karuwa mutane suke daɗa yi,
ɗakin Inna nashige da gudu nafaɗa saman gadon ta sai a lokacin naji wani irin kuka sai kawai na fashe da wani irin kuka mai karfi cikin sananin tashin hankali.

Hankali tashe su Ummi da wasu daga cikin mutanen da suke zaune cikin parlour'n suka rufamin baya Ummi na kokarin hanani kukan,
wata ƴar baffan su Abba Aunty Halima tace
"A'a kada ki hanata kuka kibar ta tayi shine samin sassaucin zuciyar ta, ɗazu ai kasa yin kukan tayi barta tayi kukan zuciyar ta zai ɗan sami sassauci"...
kukan nake babu kakkau tawa har numfashi na nawani irin tafiya yana dawowa kamar zan shiɗe...
nakai tsawon awa guda ina kukan zuwa lokacin har muryata ta toshe bata fita da karfi. sai a lokacin suka shiga rarrashi na amma ina bana ko jin abun da suke fa....

A ɓangaren Ya SALEEM kuwa yanzu da muwar sa ta kasu kashi biyu,har suka isa makabarta yana tunanin yanzu wani hali take,ɗaya ɓarin zuciyar tasa kuwa ɗin bin damuwar rashin Inna ne aciki,
Kakar su abin alfaharin su yau sun rabu da ita rabuwa na har abada.
har aka kamla bisu suka juyo yana alla-alla ya'iso gida yaga awani hali take yanzu.
koda suka iso gida kan cewar har lokacin da mutane a kofar gidan ga waɗan da suka dawo daga makabarta sai ya faka motar a in da yafaka ɗazu yafito yashiga cikin gidan da sauri,
direct part ɗin Mamie yawuce ganin basa nan sai ya fito ya nufi part ɗin Inna,
haka yakusa cikin jama'ar yashige ɗakin inda yake jiyo sautin kukan ta,
nan ya iske su Ummi suna ta faman lallashin ta a sannu ya raɓa gefen su suka bashi hanya yakarasa bakin gadon,
" *HAMDAHHH*".
yakira sunana a hankali,ban amsa ba sai dai sautin kukan da naɗan rage dan zuwa lokacin wani irin masifaffen ciwon kai nake ji,
a sannu ya mika hannu yakamo nawa yaɗa go ni zaune, idanuna sunyi wani irin kunburi sabo da sabar kuka har bana iya buɗe su duka.
hannun nawa yarike da kyau yaɗan jawo ni na sauko a gadon, kana yanufi kofa yana rike da hannuna har lokacin kukan nake muka fice daga cikin side ɗin gaba ɗaya.
haka mukayi ta gilmawa cikin jama'a duk wan da ya kallene sai ya kuma kallona da fuskar tausaya wa,waɗan da suka sanni kuwa faɗi suke
"Dole kiyi kuka".
ɗakin shi nada dake ta nan farfajiyar gidan yanufa da ni a cikin makullan dake haɗe dana motar sa yazura ɗaya daga cikin su yabuɗe kofar,
muka shiga, ɗakin tsaftsaf kamar da mai kwana cikin sa sai tashi da daddaɗan kamshi yake.
a bakin gado ya zauna tare da zaunar dani a jikinsa ya..........!★




*Free page saura kaɗan yakare waɗan da basu biya ba su hanzar ta*






Mommyn twins ce



🌺 *HAMDAH*🌺






3 Comments On HAMDAH
avatar
zarrah

1 year ago

Reply

Amazing story

avatar
taskar

1 year ago

Reply

Replying to zarrah

Thanks for your feedback

avatar
taskar

1 year ago

Reply

Littafi

Please Login or Register in order to submit comment